Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwa" ya juya ya kalli Shubai'a yace "my princess, kinajin barci ya Kamata Kije ki kwanta kinji" Ummee tace "seka dawo" Shureim yace "adawo Lpy" Shubai'a tayi Mai byeΒ², ya lakace kumatun ta yace "my sleepy princess πŸ‘Έ" dariya kurum Shubai'a tayi, daga Haka ya fice, Ummee ta kalli Shureim tace "my boy Dan Allah ka kiyaye banason ku k'ara samun matsala da Abieynka kacigaba da hak'uri komai ya kusa zuwa k'arshe in sha Allah, kome ze had'aka da wannan P.A d'in karka rabu da'ita se Idan Ita dakanta tace bataso kaji" Kai ya d'aga yace "in sha Allah Ummee bazan koreta ba kuma bazatayi nasara akaina ba" Ummee tace "in sha Allah" Shubai'a ta kalleshi tana murmushi take nuna mishi "waishi besan yayi girma da yawa bane, yakamata yayi aure fa" bugun wasa yayi Mata yace "ai danaki za'a had'a y'ar nema" tana dariya ta tab'o Ummee tayi Mata nuni da "Aiko ze mutu ba aure" Ummee tace "Ashema Aiko very soon zan aurar daku in huta"


*KATSINA*

*BAYAN SATI BIYU*


"Ummah dan Allah kidena kukan nan Nima Zaki karyar min da zuciya ne dan Allah kiyi hak'uri" Ummah ta goge hawayen ta tace "dan Allah Sarauta ki kula kinji, banason matsala ki kula kinji Sarauta na, Allah ya bada sa'a Allah yasa kin tafi a sa'a ubangiji ya kareki daga sharrin Abun cutarwa na fili Dana b'oye Allah ya kareki" Ameen ummah "shine abunda ta fad'a tana rungume ummah, Nabil yace" Ummah ayi hak'uri, kizo muje saura minti 20 jirgin ku ya tashi "Ummah ta k'ara rungume ta tace" zanyi kewar ki yarinya ta "Sarauta tace" Nima hka Ummah " haka suka gama sallama da Ummah, har ta bud'e mota zata shiga suka jiyo sallamar Maryam, dagudu suka rungume juna suna fashewa da kuka, Maryam tace" na kasa yin fushi dake, naso ace mun rabu saboda abunda ya faru, Sarauta Ina k'aunar ki sirrinki sirri nane, Babu wanda zeji shi, Allah ya kaiki lafiya ya bada sa'a yasa alkhairi ne ya kaiki " ta k'arashe tana kuka, Sarauta tace" Ameen Maryam Nima Ina k'aunar ki ki temakamin ki yafemin laifin danayi miki kinji " Maryam tace" wallahi na yafemiki duniya da lahira, haka Allah ya rubuta kiyi hak'uri na yafemiki " Haka akai ta bankwana, ita kad'ai ta tafi, nan tabarsu da kukan kewa, (Allah sarki Maryam mutuniyar su akwai hankali da hak'uri)


Aranar jirgin su ya sauka a JIDDA, tana zuwa ta Kira Maryam da Ummah ta shaida musu, a hotel zata Kwana kafin gobe a had'a ta da Prince MS....


*to Allah yayi su Sarauta an sauka a JIDDA, Allah ya bada sa'a Yakuma sa alkhairi ya kaiki*


KARKU MANTA AKAN KUDI K'IRK'IRARREN LABARI NE WANDA NAYI SHI DOMIN FAD'AKARWA, NISHAD'ANTARWA TARE DA KUMA TUNATARWA NICE TAKU ME NISHAD'ANTAR DAKU A KULLUM DA KO YAUSHE.


@ *SHERNTEE GHAYU*


07064706167

πŸ’΅ πŸ’΄ *AKAN KUDI* πŸ’΄ πŸ’΅

(A poor lady story)

..... 2nd May, 2023.

*Story & writing*
*By*

@ *sherntee Ghayu* 😍😍


πŸ””πŸ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* πŸ“š


πŸ‘‘J. W. A πŸ‘‘



*agaskiya Ina matuk'ar godiya a gareku baki d'aya ba k'aramin faranta mun kuke ba har k'aguwa Nike na turo page dan nasan se inda k'arfin ku ya k'are a gurin comments Ina matuk'ar alfahari daku fan's d'ina, wannan page d'in naku ne, much luv* πŸ˜‡πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ‘¨β€οΈπŸ’‹πŸ‘¨πŸ‘¨β€οΈπŸ’‹πŸ‘¨πŸ‘¨β€οΈπŸ’‹πŸ‘¨




πŸ…Ώ..... 015 & 016



*BAYAN KWANA BIYU*

*AT M.S GLASSES COMPANY*

Zaune yake Akan kujerar shi yanata aiki a laptop, agogon hannun shi ya kalla 06:00am, gashin kanshi daya rufe mishi rabin fuskar shi yasa hannu yayi baya dashi, da Alama aiki yayi mishi yawa, juyawa yayi ya kalli tulun files d'in dake gefen shi yayi ajiyar zuciya hak'ik'a Yana buk'atar P.A amma me hankali da tunani, ringing bell d'in k'ofar tank'amemen office d'in shi ce ta dawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi, bell d'in dake gefen shi ya danna yayi k'ara dan Koda yayi magana ba lallai na wajen ya jishi ba, a hankali cike da tak'ama Khameel ya shigo office d'in kamar na ubanshi, Khameel ne yayi gyaran murya yace "ya office d'in?" Shureim yace "fine" Khameel yace "komai na tafiya daidai ko?" seda ya d'anyi Jim, Jin irin tambayar da Khameel ke mishi sekace shi yasa shi Aikin, da Kai kurum ya amsa mishi, Khameel yace "P.A d'inka na waje ko zata iya shigowa ta fara aiki" nanma Kai ya d'aga mishi, murmushi yayi yace "Ohk nizan koma Allah ya temaka" cikiΒ² ya amsa da Ameen, daga nan Khameel ya juya ya fita.

Da sallama d'auke a bakin ta ta shigo office d'in, sanye take cikin black suit, har neck tail tasa, gashin kanta yasha gyara anyi mishi baby park ya sauka har gadon bayanta, kwalli ne kawai a idonta, lips d'inta kuwa Sunan a kalar su suba ja ba suba maroon ba, fuskarta Babu Alamar murmushi hakan seya k'ara fiddo Mata da ainahin kyanta, (Wai dama Haka Sarauta Keda kyau, zaman Nigeria ne kawai, Kai aradu koni naje k'ilanma na fita kyau ai ita 9ja duniya ce), k'afarta sanye cikin black half cover shoe, wayarta ce kawai a hannun ta, wannan kyan se masha Allah πŸ˜‡.

Kallo d'aya yayi Mata ya kauda Kai, duk da shi dama bawani gane kallonshi ake ba tunda ba kasafai yake bud'e beauty eyes dinshi ba, sedai Kai dayake Kallo kaji ajikinka.

Gaban teburin shi ta k'araso, cikin harshen larabci tace "Barka da rana SIR" ko kallonta beyi ba, da turanci yace Mata "ga Aikin ki nan" ya k'arashe Yana nuna Mata tulun files d'in dake gefen shi, tare da teburin ta da bekai naahi ba, ta yunk'ura zatayi magana ya dakatar da'ita ta hanyar d'aga Mata hannu, Yana mik'ewa Yana nuna Mata komai yake fad'in "Idan kika ga file's Anan to complains ne daya danganci company, Kece Zaki dunga duba komai akai, Idan kuma Anan kika gani Toh nawata buk'atar ne, imma temako imma kuma ana neman saka hannun jari Anan company, nan kuma Akan duk wani meeting ne, ga laptop nan dakuma printer zaki dunga printing important documents, Zaki iya kirana da Shureim kefa " ta kalleshi tana jinjina ma irin ayyukan da kyaklyawan mutuminnan daya Kira kanshi da Shureim ya had'ata dasu, ajiyar zuciya tayi tace" nikuma Sarauta " kallonta yayi na d'an dak'ik'u kafin a zuciyar shi ya maimaita Sunan *Sarauta* Yana zama yace" full name " Sarauta tace" kaima Sir Shureim kawai ka sanar min " d'agowa yayi ya kalleta kafin yace" ki fara Aikin ki " gurin teburun ta wuce taja kujerar ta zauna, wayar ta dake ringing ta d'auko ganin ummah ke Kira yasa tayi murmushi zata d'aga ta tsinkayi muryar shi yana fad'in" Idan aka shigo nan ba'a amsa waya ki aje kiyi abunda ya kawo ki " daga Haka ya cigaba da Aikin shi, d'an had'e fuska tayi kafin tasa wayar a silent ta aje, takardun ta soma dubawa, kafin tasa hannu setayi mishi bayanin yanda file d'in yake, wani ya d'aga Mata Kai wani ya girgiza.


Zuwa gurin k'arfe biyu Sarauta tayi ligiΒ² ta gaji sosai so take taji yace sun tashi amma shuru ga yunwa data addaba Mata, tana cikin tunani taji yace "keeh" ai dasauri ta mik'e tana d'aukar Jakarta, d'an harararta yayi murya can k'asa yace "Kije kiyi sallah ki dawo" b'ata rai tayi tace "Wai bamu tashi ba?" da farko Banza yayi da'ita daga baya kuma yace "cikin files d'ari biyu kin gyara 25 to me kikayi kenan, Ina kallonki ma ajiye Aikin kikayi, to wallahi a yau sekin gama Aikin nan Duka Kindai ji na rantse, kuma Kije minti 5 na baki ki dawo" ajiyar zuciya tayi tana controlling d'in kanta karta gurza mishi rashin mutunci, ta ajiye Jakarta tafita, mosque d'in dake cikin companyn taje, cikin minti biyar Aiko segata ta gama ta dawo, nan ta duk'ufa aiki ta dage sosai, ranar Anan suka wuni, duk lokacin sallah ze bata minti biyar, se gurin 12 suka tashi ahakan ma seda ta tafi dasauran files sukai 40,gidansu ya tafi da'ita dan hakan shine k'a'idarshi, asaman shi ya bata d'aki harta kama handle d'in k'ofar zata shiga taji yace "tomorrow at 6:00am" ad'an zabure tace "what" ko kallonta beyi ba ya wuce ciki, kamar tayi kuka tashiga cikin d'akin, akwai main falo, two bedrooms, kitchen da dining area, ba laifi taso gurin saboda dama kalar burinta kenan, se gurin 4:30am ta Gama Aikin datazo dashi, tana kwanciya aka Kira sallah, tanaso ta tashi amma ta kasa saboda barci yaci k'arfin ta, se around 8:40am ta tashi.



A hanzarce ta farka tasoma shiri, cikin black suit ta shirya, top D'inma a hannu ta rik'eta tsabar sauri, ga files masu yawa a hannun ta, gashin nata ma sakinshi kurum tayi, nan tsagwaran kyan ta ya fito, dasauri sauri take saukowa daga stairs d'in, a stairs na biyu ta had'u da Shubai'a, Sarauta tace "please Sir Shureim?" murmushi Shubai'a tayi ta d'aga mata hannu dan bataji me tace ba, daga haka ta wuce, Abun bak'aramin b'ata ma Sarauta rai yayi ba, dogon tsaki taja kafin tace "bala'innan ni wannan y'ar rainin wayon zata maida y'ar iska, Wato irinma bata jini d'innan ba ko, to indai wulaqanci ne gidan shi kika zo y'ar Matsuzaka kawai" ta k'arasa tana sauka down stairs d'in, su Hajja ta gani su duka a falon sunata shiryeΒ²n tarar jikokin su dazasu zo, aranta taso ta tanka musu amma tuna abunda ya faru tsakanin ta da waccan y'ar rainin wayon yasa ta d'auke Kai zata wuce, Hajja Mubeena ce tace "ke bakiga mutane bane" juyowa tayi tayi musu Kallon sama da k'asa takuma juyawa, hajja Neenah tace "ke y'ar rainin wayo ke kuma daga Ina" Khaleesat tace "Uhm Uhmm aidaga ganinta kunga y'ar aikatau masu nuna Isa Akan abunda basu Isa dashi ba" se sannan Sarauta ta juyo ta kalli Khaleesat tace "wannan Haka yake kuma Idan muka nuna isar wani be Isa ya dakyar ba ko d'an ubanwaye shi" dasauri Hajja jumaima tace "ke baki da tarbiyya ne iye ko bakiga gurin harda manya bane ba, Wai tsaya kinfi k'arfin ki gaida mu ne" tsaki Sarauta taja tace "Au wai da mutane a gurin..." daga Haka ta juya tayi ficewarta tana jinjina rainin wayo irin na ahalinnan, ba oganta ba ba y'an matan gidanba bakuma tsoffin ba, Aiko bazata d'auka ba, Sir Shureim takema aiki basu ba dan haka duk wanda ya taka ta seta Rama.

A waje ta iske driver na jiranta Aiko taji dad'in hakan cikin mintunan dabasu wuce 15 ba ta k'arasa office d'in. Tana shiga ta gaishe shi amma ko Kallon inda take beyiba balle tasa ran amsawa, zuwa tayi ta aje top d'inta da kuma files d'in data shigo dasu, ta d'auko guda uku ta koma gefen shi tana fad'in "Sir wa'inna files d'in sune the important files a cikin wa'incan, wannan buk'ata ce aka turo da'ita daga kamfanin ABC dake Malaysia suna son saka hannun jari acikin wannan company kimanin πŸ’²700 dalar America, shikuma wannan sak'o ne daga JAY GLASSES Akan xasu bamu kwangilar yi musu Aikin daya Kai kimanin CARO 10, wannan kuma sak'one daga cibiyar ma'aikatar gilasai wanda za'ayi meeting nan da sati d'aya me zuwa, gaba d'aya ana buk'atar saka hannun shaidarka ne "ta k'arashe tana mik'a Mishi files d'in, kamar bada shi take ba yace" acikin albashinki na watannan an cire Caro 2 saboda kin b'ata lokacin company yau, kuma miye amfanin iya signing d'ina dakikayi Kije kisa hannun mana Aikin Banza " Yana kaiwa nan ya tashi ya d'au top d'inshi yayi hanyar fita Yana fad'in" ki same ni a mota saura kibari na k'ara jiranki " daga Haka ya fice, ko kwakkwaran motsi ta kasa yi sakamakon kud'in ta daya rage ita dataci burin harta gama aiki kud'inta bazasuyi ciwon kaiba shine bak'in azzaluminnan zeyi Mata haka, dasauri ta d'au top d'inta ta bishi zuciyarta falll da Allah ya Isa harsuka Kai bank d'in GOLDING MONEY BANK d'inshi, nanma tunda sukaje take aiki tayi liss, ranar 7:30pm suka tashi aiki amma duk da hakan seda yabata Aikin yin fira da asibitin shi na Saudi, domin Jin matsalolin su.


Suna shiga gidan ya wuce b'angarenshi, a falo ta zauna domin ta gaji sosai, takai ak'alla 10mins a gurin kafin taji motsin mutum, dasauri ta mik'e tsaye, murmushi Ummee tayi Mata tare da cewa "P.A..." tayi maganar dason tabbatarwa, murmushi Sarauta tayi domin tana ganin matar taji ta kwanta Mata, tace "Uhm Ina wuni" gashin kanta Ummee ta shafa tana zaunar da ita tace "sannunki da aiki kinji ki zauna Anan na kawo miki coffee" kafin Sarauta tayi magana Ummee ta tafi, murmushi tayi tana Jin wannan matar itace zata zamo maye gurbin ummahnta, itama Ummee Haka, duk da kyauta tawa d'abi'arta ce gaduk wanda yazo gidan wannan yasha banban domin taji k'aunar yarinyar har cikin zuciyarta, lafiyayyen coffee me kore gajiya ta had'o Mata, seda ta kusa shanyewa sannan Ummee tace Mata "Zaki iya kirana da Ummee kamar Dai sauran yarana, yanzu Kije ki kwanta kinji, Idan kika Kwana dacewa 6 Zaki tashi tofa Zaki farka d'in, bayason jira Arayuwar shi tsabar rashin son jiran shi wata tara zeyi acikin mahaifiyar shi amma bakwai yayi, dan Allah ki kiyaye kinji " murmushi Sarauta tayi tana k'ara jinjina ma karamci irin na Ummee tace" shikenan " murmushi kurum Ummee tayi duk da ita dama za'a iya cewa ita Shubai'a ta biyo saboda da dad'i babu dad'i zakaga fara'a Akan fuskar su, daga Haka ta juya domin tafiya up d'inta, kamar yau aka tab'a kiranta da Ummee Haka taji da Sarauta tace Mata " Ummee " tsaya tayi har Sarauta ta k'araso ta rik'e hannun ta tace "Nagode miki sosai Ummee" Ummee tace "Humm kintab'a ganin inda y'a ta godema mahaifiyar ta Akan abunda ya zamo Mata dole, to kidena, yanzu yayane Sunan Jarumar?" murmushi tayi ta sunkuyar da Kai tace "Sarauta" "Sarauta..." Ummee ta maimaita da zallar mamaki, mutum d'aya tasani da Sunan nan duk fad'in duniya shine *Muhammad Shureim (Sarauta)* Kai ta d'aga ma Sarauta tace "Kije ki kwanta karku maakara" daga haka Ummee ta wuce itama Sarauta ta tafi....



Akwana a tashi Babu wuya a gurin Allah, wasaΒ² yanzu Sarauta watan ta d'aya da y'an kwanaki a JIDDA, zuwa yanzu duk ta saba da aikinta sosai ta maida hankali kamar gaske, ba shakka kuma shima Shureim Yana matuk'ar Jin dad'in aiki da ita, tana yin komai yanda ya Kamata, ta saba da Ummee sosai, amma sedai har yanzu inzata ga Shubai'a to fuska zatayi ko kuma ta Bar wajen ko ta b'ata rai, tun Shubai'a bata lura harta ankare da Hakan kuma Sam batajin dad'i.


Su Hajja kuwa sun d'auka itama kamar sauran P.A d'in ce da aka kawo a baya zatayi musu biyayya amma Sam Babu wata jituwa a tsakanin su, Babu girma Babu girmamawa.



Gimbiya Shuwaiba da Gimbiya Juwaira da kuma Gimbiya Khaleesat duk suna masarautar kuma kowa burinshi be wuce samun Shureim a matsayin miji ba, sedai abunda suka lura dashi Sam bamashi da lokacinsu, hakan ya tinzura su yasa suka had'a Kai a zahiri wajen ganin sun yak'i Sarauta dan aganin su duk Ummee ce sila dama ba wani girmanta suke ganiba to su dama girman wa suke gani.



Ba laifi yanzu a sati sukan bar k'asar ak'alla sau biyu ko sau uku, duk ran da zasu bar k'asar se 12 suke fita kuma tana matuk'ar Jin dad'in hakan.


TA d'aya b'angaren kuma duk wani Abun ci gaba dukiya ko kuma meeting takan sanar dasu Khameel duk da tasan hakan ba dacewa bace ba, ganin yanda Sir Shureim ya d'au yarda ya bata saboda Idan kud'i sunkai trillions to zece tasaka hannu ko kuma taje Suyi magana da mutanen ko company, Anan ne taga yanda ake yarda a zahiri, da taso zuwa yanzu ta gama aikinta amma kasantuwar tanason komai tayi shi a tsari yasa take bin komai a hankali.


Yanxu ma sunata shiryeΒ²n zuwa bangalorer domin yin bikin cikar companyn shi na jewelry store πŸͺ shekara biyar tare kuma da amsar lambar yabon kyauta tawa.




*KATSINA*



*Karku manta AKAN KUDI k'irk'irarren labari ne danayi shi domin fad'akarwa, Nishad'antarwa tare kuma da tunatarwa nice taku me Nishad'antar daku akullum da ko yaushe*


@ *sherntee Ghayu* πŸ₯°πŸ₯°



@07064706167


πŸ’΅ πŸ’΄ *AKAN KUDI* πŸ’΄ πŸ’΅

(A poor lady story)

....... 5th May, 2023

*Story & writing*
*By*

@ *sherntee Ghayu* 😍😍


*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS*

πŸ‘‘J. W. AπŸ‘‘



*na sadaukar dawannan page d'in zuwa gareku my triplets, much love 😍 Ina matuk'ar k'aunar ku, Ina godiya Akan kulawar ku agareni Nagode my triplets* πŸ’

πŸ…Ώ......... *017 & 018*



*KATSINA*


"Ummah wallahi ba k'aramin kewar Sarauta Nayi ba nifa jiya har mafarkinta seda Nayi" Maryam dake juya miya a kitchen ta fad'a, ummah dake d'auraye kwanoni tace "Kedai Bari Maryam gashi inka kirata dakun fara waya zatace karatu ko ga malannan su kullum cikin karatu suke Allah Dai ya temaka ya bada sa'a" Maryam ta kalli ummah cike da tausayin ta tace "ai Insha Allah ankusa yin hutu zatazo ta ganki ma" Ummah tayi murmushi har cikin zuciyarta taji dad'in maganar Maryam tace "Allah ya nunamin wannan ranar" Maryam tace "Ameen" kafin wani yayi magana suka jiyo sallama, Maryam ce ta fito domin duba ko suwaye, tsalle ta daka tare da rungumesu don taji dad'in zuwan su, Spincy ce tace "shegiya kinga yanda kika koma kuwa tab lallai" zeena tace "shegiya Maryam Nasir harda fari kin k'ara" Maryam tace "ku tsaya Wai Taya akai kukasan Ina nan" meelarge tace "ai gidanku muka fara zuwa" Ummah data fito daga kitchen tace "Maryam hayaniyar me Nike Jine" Maryam tace "Ummah y'an ajinmu ne suka zo" duk duk'awa sukayi suka gaisheta fuskarta cike da fara'a ta amsa musu sannan tasa Maryam ta kawo musu drinks.


Zaune suke suna fira, suna Taya meelarge murna Akan Fara rubutun novel da tayi, spincy tace "Wai Maryam da farko ai ba Sarauta taci scholarship dinnan ba amma kuma ya akai ta tafi outside" Zeena tace "kwarai ma kuwa Nima Abun da ya kulle kaina kenan" Meelarge tace "to Wai ya akai hakane" Maryam na lek'en kitchen kar ummah taji tayi k'asa da murya tace "dama fa itace taci, Kingane mistaken akai agurin rubuta Sunan sedaga baya aka gano gaskiya ai harma ta tafi karatun" Zeena tace "to ai itama Hauwa Mansour ta tafi kenan cikin su..." saurin dakatar da'ita Maryam tayi tana cewa "Haba Zeena kema fa kinsan hauwa d'iyar me kud'i ce maybe babanta ne ya kaita amma Dai Sarauta gwamnati ta kaita kin gane" Meelarge tace "ki kwantar da hankalin ki Maryam miye na d'aga murya haka, ai Muna son tabbatar wa ne" Maryam tace "ai kun tabbatar" Haka suka ci gaba da fira har sukayi sallama.



*JIDDA*



" Sir Shureim wannan shine file d'in Mara lafiyar nan daka aikeni kace na amso" amsar file d'in yayi yana dubawa, yad'au tsawon minti biyar Yana dubawa kafin ya d'ago ya kalleta yace " ki shirya yanzu zamu tafi" tayi saurin shan gaban shi tace "but sir maganar Mara lafiyar ba" be tanka Mata ba ya fice " Yana fita tayi ajiyar zuciya, afili tace " maye kawai ai aikina dakai ya kusa k'arewa " daga Haka ta d'auki top d'in ta da iPad ta bishi a baya, a cikin company prvt jet d'insu ya tashi zuwa India, suna kaiwa aka soma meeting wanda gaba d'aya da Sarauta sukayi meeting d'in d'anshi Prince ko A beceba har aka gama, sunata shirin tafiya inda saketa gaisawa da mutane ana jinjina ma iya aikinta, itako murmushi kurum take, kamar daga sama taga anmik'o Mata hannu, kallon kyakkyawar fuskar shi tayi me d'auke da murmushi, itama murmushin tayi tana mik'a mishi hannu sedai kafin su gaisa Shureim yasa hannun shi suka gaisa, Yana Kallon Sarauta yace "you know bake zan tsaya jira ba" sannan ya kalli wanda yake rik'e da hannunshi yace "Shureim CEO na company M.S Companies" shima murmushi yayi yace "ALI KHAN CEO na A.K.R companies" Shureim yace nice to meet you " Ali khan yace" same too " sannan ya kalli Sarauta yace" nice to meet you too Dia " Sarauta tayi murmushi tace" Sir Shureim personal assistance nice to meet you " Shureim be tsaya ba ya wuce, kallon Ali khan tayi tace" sorry on my way " yayi murmushi yace" please kozan samu number ki " tace why not" tana amsar wayar shi tana saka number, murmushi yayi yace "wane suna zansa ka kenan" tace "Sarauta" yace "Sunan ya dace dake Amman dan yanzu zansa beauty saboda kinci Sunan ke me kyau ce" batasan Sanda tayi murmushi ba tana tafiya tace "have a wonderful day" shima da hannu yayi Mata bye bye Koda ta shiga jirgin Babu abunda Shureim yace da'ita, itama kuma bata tanka Shiba har suka k'arasa.


"wash Allah Ummee na gaji sosai" Ummee tayi murmushi tace "Eyyah sorry Aikin ne seda hak'uri Bari akawo miki coffee seki sha kokin samu sauk'in gajiyar" Sarauta ta rik'e Mata hannu tace "Laaa kibarshi Ummee nama sha yanzu a fly" kafin Ummee tayi magana Sega Shubai'a ta sakko fuskarta kamar ko yaushe d'auke da murmushi ta nufo su, "sekace da gaske bata da wulaqanci amma nan muguwar y'ar rainin Wayo ce ko magana bata iya yima mutum" ta k'arashe maganar zucin ta tana d'aure fuska Wai ita kar a rainata (ikon Allah kizo gidan su kice kuma karta rainaki lallai Sarauta akwai Sarauta) kusa da Ummee Shubai'a ta zauna tana Mata nuni da

Please Login or Register in order to submit comment