Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace "Ina ruwana da wasu su hajjas suke kome zanyi ma mutum rashin mutuncine kawai ni Babu ruwa na, Bari kuma naje asibitin Naji gaskiyar lamarin" tana gama fad'ar hakan ta fice fuuuu kamar iska, Ummee kuwa dataji abunda ya faru mik'ewa tayi tare da Kallon su tace "zaku iya cutar da kowa nawa Nayi shuru amma banda daughter in-law d'ita, wallahi Idan harna tabbatar da abunda kukayi gaskiya ne cikin ya zube zan d'au mataki akai sannan kuma zanyi abunda ya Kamata a matsayina na sarauniya" tana gama maganar ta Haye sama, kowa da Kallon mamaki ya bita saboda basu tab'a Jin ta tanka ba kome za'ayi Mata kuwa, Safiyatu ta mike tana Kallon su tace "kun ban mamaki wallahi" daga Haka ta wuce abunta, Haka kowa ya soma tafiya Jiki asanyaye yau Dara taci gida.





Zaune take a gefen gadon daga gani waya take yi amma kuma batajin dad'in yin wayar, sosai Ummah take Mata fad'an kafin kuma tace "uban me ma ya had'aku" Sarauta na xumb'uro baki tace "Ummah Maryam fa munafuka ce" Ummah tace "Amma Kin bani mamaki Sarauta to koma ubanme tayi miki Ina me umartar ki daki kirata yanzunnan Idan ba haka ba Zaki gamu da fushi na" Sarauta tad'anyi tsaki yanda ummah bazata ji ba, tace "Toh Naji, nifa ummah koma lafiya Banida ita" Ummah na basarwa tace "Allah ya kyauta" daga Haka ta yanke wayar.




Tad'au tsawon 10mins, tana Kallon number kafin tayi dialing, ringing biyu Maryam tad'au ka cike da farin ciki tana murnar ai dama k'awar ta bazata iya dogon fushi da'ita, kafin tayi sallama taji Sarauta na cewa "to munafuka yanzu munafurcin naki harya Kai ki had'a uwa da d'iyar ta, to Bari kiji wallahi Maryam Nidai Nayi miki Nisan da Koda gudu baxaki iya kamoni ba nagaba fa yayi gaba, waike bakiji menace miki bane Babu nifa Babu ke, Kewai baki fahimta ne, to Bari kiji ko a gaban kaaba na ganki kowa yayi ta kanshi Babu ni Babu munafuka kuma....... " bata k'arasa ba Maryam ta katseta tana kuka tace" to Sarauta seme, nace seme fa dan mun rabu, kefa ba Nasir bace kuma ba Saadiya bace to Akan me zan zauna kina azabtar dani da Bak'ak'en naganganu, kuma Bari kiji nidan Allah Nike sonki badan wani abuba Nida xanyi miki munafurci datun Sanda ake cemin ke shegiya ce danayi miki to ni ba wannan bane agabana, dan anrabun seme nace seme fa, zan mutu ne" ta k'arashe cikin kuka me had'e da tsawa, Sarauta dake hawaye tace "Nagode kwarai Maryam, ashe batun yanxu kike min munafurci ba na yanzu ne ya fito, kinaji kawai ki goge number na domin bata da amfani Nima zan goge taki Allah ya had'a kowa da alkhairin sa" Maryam ta d'aga Kai tace "Nima Nagode Allah ya sadamu da alkhairi" daga Haka ta yanke wayar, Sarauta na gama wayar ta goge number Maryam.





Wani irin kuka ne me cin rai ya kwace Mata kuka kawai take yi kamar ba'itace tayi rashin mutuncin ba, dasauri Sirayya da Safiyatu suka k'araso d'akin, Sirayya ce ta rik'e ta tana cewa "Subhanallah Sannu Sarauta ko jikin ne, maza Safiyatu Kira mana likita, shi wannan sakaran ma ko Ina ya tafi ya barta" Safiyatu tace "to yaya" kafin ta juya Sarauta dake k'ok'arin yin controlling d'in kanta tace "Babu komai Aunty" Sirayya ta lafta Mata harara tace "gidanku sakara kawai, maza Kira min doctor Safiyatu" Aiko shuru Sarauta tayi batace komai ba, doctor tazo ta dubata Haka sama² kafin ta fita, Sirayya ta galla Mata harara tace "Haka suka tafi suka barki Anan Babu kowa" ta girgiza Kai tace "Shuwaiba da Shubai'a sunje Su dawo" kafin wani yayi magana akaji shigowar su, ai irin hararar da Sirayya keyi musu ne yasa basu k'araso ba, duk nutsuwa sukayi kafin suka Ida shigowa, bugu ta kaima Shuwaiba amma bata samu ba tana cewa "banzaye marasa amfani kawai daga gidan ubanwa kuke kuda bakwa da amfani" Shubai'a tace "Munfa je mud'auko Mata Jakarta ne" Sirayya tace "ubanki nace, Wato kinyi baki ko, Dallah ku fice ku bani guri marasa amfani kawai" duk fita falon sukayi suna gunguni, Sirayya takalli Sarauta tace "Dagaske cikin naki ya zube" Sarauta tayi Mata Kallon mamaki tace "ciki kuma" Sirayya tace "bansani ba 😏, maganin abortion fa suka baki kika sha amma Zaki wani cemin Haka na bigeki..." Safiyatu tace "yaya kiyi Mata ahankli kinga fa bata lafiya" Sirayya tace "to y'ar iya, bazan bi ahanklin ba nace bazan bi ahanklin ba ki kiyaye ni fa Safiyatu to" ta juya ta kalli Sarauta tace "inajin ki" Sarauta tace "dama Babu cikin, kawai dai Nayi bleeding ne" Sirayya ta mik'e tana cewa "Allah ya temake su wallahi yau da anga tashin hankali tsirara, ke kuma Allah ya sauwake na tafi" daga Haka sukayi sallama da'ita suka tafi.





"Wai ita wannan d'in Wacece" Sarauta ta tambayesu data kasa hak'uri, Shuwaiba tace "Uhm Goggon mu Sirayya kenan bata barin Kota Kwana, duk wanda ya shiga harkar ta setayi mishi ko Wanene Koda kuwa hajjas ne, kuma Ance Sanda sarki na Raye harshi Idan yayi Mata seta yi mishi, shysa kowa shakkarta yake yanzu seta sharara maka Mari" Shubai'a tace "ai zaman lafiya yafi zama d'an sarki shysa duk kika ga kowa Yana binta, amaida Mata aniyar ta" Sarauta tace "Allah ya kyauta tana jingina," Ina Mr.. " ta tambaya, Shubai'a tace" nagan shi agidan shi yayi wanka ya fita" Sarauta ta zauna tana cewa "Ina kuma yaje" Shuwaiba tace "mu Ina zamu sani tunda ko Kallon mu beyi ba" Sarauta ta tab'e baki ta koma ta zauna.





*KATSINA*




"Mama mun rabu da Sarauta yau" Mama dake yanka alayyahu ta ajiye tace "wani fad'an kuka k'arayi" Maryam tayi murmushi tana Kallon photon su da Sarauta tace "ah ah haka nan kawai, ta buk'aci Hakan ne" Mama ta cigaba da Aikin ta tace "Allah ya kyauta amma baku kyauta ba, duk da bakuyi wannan sakarcin ba se yanzu" Maryam ta mik'e tana d'aukar Hijab d'inta tace "zanje na gaida ummah bazan jima ba zan dawo" Mama tace "ki gaishe ta" daga haka ta fice.





Tana fitowa ta had'u da doctor a waje, murmushi yayi yace "Barka da fitowa ma'abociyar kyau da Amana" Maryam na d'aure fuska tace "sannunka, lafiya kuwa" yace "Humm Maryam Kenan nasan Sarai kinsan Ina sonki amma kike wahalar dani" Maryam tayi murmushi tace "Uhmm dama nan Nike son azo, doctor kayi hak'uri amma ni wallahi Inada wanda Nike so kayi haquri" Jin maganar yayi kamar saukar aradu yace "amma kuma Malam yace baki da tsayayye" Maryam tace "shima besan Shiba amma kwanan nan zezo, kayi hak'uri kurum" daga hka tasa Kai ta wuce, tabarshi tsaye zuciyar shi na tafasa.




Ita kad'ai take tafiya tana tunanin wani lokaci da bazata manta dashi ba suna tafiya itada Sarauta ( Kan Titi tahau da niyyar tsallake titin Sam ita bata lura da motar data taho ba, da sauri Sarauta ta janyo ta baya tana cewa "baki da hankali ne baki ganin mota" Maryam ta kalleta tayi dariya ganin yanda Sarauta ta tada hankalin ta, tace "da motar ta kad'e ni da yazakiyi" Sarauta tayi tsaki tace "Yazanyi fa, iyaka na Kira gida nace kinyi accident, shikenan na baki hak'uri akai ki asibiti" Maryam tace "ni kuwa danice da Babu wanda ze iya gane halin danike ciki ko kad'an nasan da k'ilama had'a ni za'a had'a akaini asibitin" Sarauta tayi dariya tace "Nima wasa Nike miki k'awas ai bansan halin dazan shiga ba ai tsakanin mu se Allah" Maryam tace "ked'in" Sarauta tace "Nid'in fa Babu abunda ze rabamu yarinya ko yakai girman miye kuwa" Maryam tayi dariya tace "to Nidai Muje tunda Allah yasa ba a asibitin zan Kwana ba" Sarauta ta daketa a kafad'a tace "Dallah me bak'in baki kawai Muje") hawayen dataji sun zubo Mata tasa hannu ta goge Jin ana Mata horn yasa ta juya, wani tsohon saurayin ta ne, tsaki tayi ta wuce batare data tsaya ba.





" Nidai na Gaya maka, Idan har Dagaske sona kakeyi to kazo kayima Malam magana, wallahi kwanan nan Abun yayi tsauri da yawa se fitowa ake, nama rasa yanda zanyi gashi har mama ta fara tunanin ko aljani ne ya kamani" seda yayi dariyar maganar ta ta k'arashe kafin yace "shikenan ki kwantar da hankalin ki zuwa gobe ko jibi zamu zo Nida iyayena, karki wani ji kin damu Idan zamu taho zan kiraki" tace "to Nidai koma miye nagaya maka Idan yakai sati me xuwa kawai zan amince ma doctor" yayi saurin cewa "Wai don Allah *mah (my) Mee* kinason ki kashe ni ne" tayi dariya tace "ni Ina zanso mutuwar ka" ta k'arashe tana dariya, fira suka cigaba dayi kamar ko yaushe.






*JIDDA*





Dukkan su zaune suke da Alama jikinsu yayi matuk'ar Sanyi da abunda yake fad'a Kallon Khameel yayi yace "dazamu had'a kanmu mu zauna da juna tsakani da Allah dahar iyayenmu Sunyi matuk'ar murna Akan hakan, Khameel Kaine d'an uwana dazan iya cewa mun RAYU kusan atare amma Kai ko kad'an baka d'auka hakan ba hasalima bayana kake son gani" kafin ya maida Kallon shi ga sauran yace "dan Allah y'an uwana Idan wani Abu Nayi muku wanda yasa kuke Jin tsana ta ku yafe min bazan iya d'aukar irin wannan tsantsar tsanar daga gareku ba" dasauri Nabil da jabber suka rik'e mishi hannu suka ce "ah ah yaya kayi mana afuwa mune da laifi wallahi sharrin shed'an ne amma Muna matuk'ar k'aunar ka dan Allah d'an uwa ka yafe mana" Shureim yayi murmushi yanajin dad'i har cikin rashi ya kalli Hisham dake musu murmushi ya jinjina Mai Kai, duk rungumosu yayi ajikin shi, Jin sheshshekar kuka yasa ya d'ago ya kalle shi, kuka sosai Khameel yakeyi, dasauri yaje ya rungumosu d'an uwan nashi Yana cewa "Inada komai yaya, Abiey yayi min komai Yama fifitani Akan ka amma nabari shed'an yayi min hud'uba AKAN KUD'I yayana ka yaye min wallahi nasani duk laifina ne ka duba girman zumunci ka yafeni" Shureim ya share mishi hawayen shi yace "stop crying my darling Bro, Aini dama bance maka na tsane kaba ko, Tohm, Yawwa se batun Shubai'a" Khameel yayi Mai hararar wasa yace "shima na fasa, Lil sis ta fiddo wanda yayi Mata kuma take so amma Nidai makaranta zan koma inason na cika burina na zama kamar dai Kai d'innan" Shureim yayi dariya Yana rungume su Duka, a yau Shureim Yana matuk'ar farin ciki sosai jinshi yake kamar yayita tsalle dan murna.





Yanzu ma tafe yake shida Hisham bayan Sunyi dinner da y'an uwanshi ya rakasu sun tafi, ya kalli Hisham yace "ashe haka mutum yake ji Idan Yana farin ciki, hmm kamar dai yanda Ummeena ke fad'a ne, mahak'urci mawadaci, tace Idan Nayi hak'uri zanga wani abunma kamar ba'ayi ba" Hisham yayi dariya yace "Toh yanzu Dai kasamu farin ciki kenan" Shureim yace "tabbas na samu amma begama cika ba" Hisham yace "tose yaushe kenan" Shureim yace "zaka gani" Hisham yace "Humm kaini inason na sanar maka cewa jibi jibin nan za'a d'aura min aure" Shureim yace "da Maryam d'in" Hisham yace "bansan iskanci da da Sarauta za'a d'auramin" Shureim yace "aikasan nagaba kuma yayi gaba, Hum ni na wuce asibitin ma tuntuni hankali na Yana can" Hisham shiyayi dropping d'inshi a asibitin.





Zaune take ita kad'ai a d'akin ta jingina kanta da gadon gurin gaba d'aya ji take ranta ya b'aci tun d'azu take baza idon ganin shi amma shuru, Aiko tana cikin wannan tunanin taji shigowar su shida Hisham, ji tayi kamar ta tashi ta rufe shi da Duka, ko sallamar dasu kayi bata amsa ba, ganin hakan ne yasa Hisham ya dafa Shureim Yana kwantar da murya yace "da girman kujerar ki Mrs M.S wallahi wani aiki ne me mahimmancin gaske ya rik'e mu shysa kikaji mu shuru yau amma ayi mana afuwa kinji" murmushin dole tayi tace "Babu komai" Hisham yace "to matsoraci gashinan na rakoka kuma na bada hak'uri ka kwantar da hankalin ka bazata bigeka ba" yana gama fad'an hakan kawai seya wuce yana dariya Abun shi. Kallon ta Shureim yayi kafin ya k'araso ya zauna a kusa da'ita Yana kama hannun ta yace "Mah Mrs am so sorry naje wani guri ne shysa but am sorry" ya k'arashe maganar Yana kama kunnen shi, d'aure face ta kuma yi, marairaicewa yakuma yi yace "company ne fa yashiga cikin matsala dole seda mukaje" ta kalleshi tace "companyn yafini ne" yayi saurin girgiza Kai yace "ai nasan Nayi laifi dan Allah ayi hak'uri" tayi murmushi tace "shikenan to Ina tsaraba ta" yace "gani" tayi dariya tana kwantawa jikin shi, a hankali suka soma fira har barci ya d'auke ta, kwantar da'ita yayi yana Kallon kyakkyawar fuskarta me cike da haiba.





"agaskiya munyi kuskure sosai Idan banda Allah ya bamu d'an uwa kamar yaya da wallahi Babu wanda ze iya yafe mana laifin nan namu wanda har rayuwar sa muka farauta" Nabil ya fad'a Yana k'ara jinjina ma irin shirmen dasukayi, Khameel yace "kaidai Bari mah man wallahi Naji a yau duk kunya ta kamani Nayi danasani sosai gaskiya bamu kyauta ba kuma dole gobe Muje mubama sis Shubai'a da Ummee hak'uri" duk suka ce in sha Allah, jabber yace "wallahi yau bakuji dad'in danaji ba lokacin da muke cin abinci atare" duk suka yi murmushi, Fawax ya mik'e Yana cewa "tonidai dama Inada magana, kawai injiran wannan ranar ne sena sanar muku" Khameel yace "ahh to munaji" yace "Nidai agaskiya inason Shubai'a kuma auren ta Nike son yi tsakani da Allah ya kuke gani" Khameel yace "Kai masha Allah Aikuwa k'anwa ta yarinyar karkice Zaku Dace sosai" jabber yace "irin sosai d'innan fa" Nabil yace "Kai amma fa munji dad'i" Fawax yayi farin cikin yanda y'an uwan nashi suka goyamai baya Akan abunda yazo musu dashi, sosai sukayi kwanan bak'in ciki a wannan ranar.





"sorry mah diamond mom wallahi d'azu Ina aiki ne shysa ban d'auki wayar ki ba" tace "Babu komai Allah, Yawwa lafiyar Sarauta kuwa" Shureim yad'anyi shuru yace "lafiyar ta klau tamayi barci" Ummah tayi ajiyar zuciya tace "Tohm shikenan kanajina..." yace "Uhm ummahna inajinki" tace "munyi waya da Hisham yace jibi za'a d'aura auren shi da Maryam to Idan an d'aura zan taho tare da'ita nan da Kwana biyu dan haka a shirya mana jirgi, prvt jet nikeso" ai besan Sanda yayi wani ihun murna ba Yana fad'in "are you serious, Wayyo Allah kice farin cikin ahalin mu ze Ida cika tunda farin cikin zata dawo, shikenan my diamond in sha Allah zanyi iya k'ok'arina," Ummah tayi murmushi tace "Allah yasa yayana yayi farin ciki kamar dai yanda kakeyi" yayi murmushi yace "tabbas ma kuwa gaba d'ayan su zasuyi murna da ganin ki sosai" Haka suka cigaba da wayar su har sukayi sallama ya koma ya gyara ma Mrs dinshi kwanciya Yana Jin wani sabon farin cikin Yana ratsashi.





*Karku manta AKAN KUD'I k'irk'irarren labari ne danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa tare kuma da tunatarwa, nice taku me nishad'antar daku a kullum da ko yaushe*





@ *sherntee Ghayu* 🥰🥰





@07064706167

💵 💴 *AKAN KUD'I* 💴 💵

(A poor lady story)




........ 23rd June, 2023




*Story & writing*
*By*



@ *sherntee Ghayu* 🥰🥰





🔔 📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* 📚





👑J. W. A👑






🅿.......... *061 & 062*






Zaune take a d'akin ita kad'ai tana danna laptop, hajja jumaima ta shigo d'akin ko Kallon ta batayi ba taci gaba da abunda take, almost 6mins tana tsaye kafin Sirayya ta d'aga Kai ta kalleta tace "Sarai kinsan banason atsaya min a ka ko to Idan bakida Abun fad'a Zaki iya tafiya" se sannan Hajja jumaima tace "Uhmm Dama tun jiya ne babu abunda yarinyar nan taci duk tabi tashi ga damuwa shine....." kafin ta k'arasa Sirayya ta katse ta da cewa "shine me, nace shine kika zo Nida Banida abunyi naje na lallab'a ta taci, to dan ubanta ta mutu da yunwar, HAJJA kifa fita a idona Sanda kukaje kuka shirya makircin ku nifa bansani ba dan Haka ku kama min kanku Tohm" kafin Hajja tayi magana Khaleesat ta shigo d'akin cikin muryar kuka take cewa "dan girman Allah my kiyi hak'uri ki saurare ni wallahi na gane kuskurena kuma bazan sake ba amma bazan iya rayuwa Babu mijina ba dan Allah kiyi hak'uri ki saurare ni" Sirayya ta d'ago ta kalli d'iyar ta ta kafin tace "jeki kici abinci Idan kin gama mayi magana akai" Babu musu aikuwa ta tafi domin taci abincin





"shikenan Naji duk abunda kika ce kuma zanje na samu yaya Akan maganar, amma wallahi ko makamancin hakan kika kuma aikatawa sena d'auki mummunan mataki kuma daga ciki zan maida ke can gurin dangin ubanki masu mugun Hali Idanma kashe ki zasuyi kunfi kusa" ta k'arashe tana mik'ewa, Khaleesat tace "wallahi my bazan sake ba na tuba" Sirayya ta tab'e baki tana tafiya tace "wannan kuma damuwar kice" daga Haka ta wuce ciki abunta.






"waike baki da hankali ne kinsan abunda kike fad'a kuwa kamar ya bazaki koma d'akin ki ba" Safiyatu ta fad'a tana Kallon Juwaira dake zaune tana danna Waya ko ajikin ta tace "ummmahna baya biyamin buk'ata ta to miye amfanin zama dashi, kuma karki wani ji kin damu zan amshi kud'ad'e masu tsoka a gurin shi kinji kafin nan na auri wanda Nike so da gaske har zuciya ta" Safiyatu tace "Aikuwa kinyi asara ba k'arama ba Banza kawai tashi ni ki bani guri" tashi Juwaira tayi tana cewa "oho dai Nidai Allah ya rabani da alak'akai" Hajja Mubeena dake Kallon komai tana kuma Jin tsanar Sarauta aranta domin gani take itace taja komai, kwata tayi kafin ta soma tunanin wannan Karan dole su biyo ta wata hanyar ba wannan ba.






"karku damu kanku yarana kuma fa yarana ne kamar dai Shureim da Shubai'a meyasa zaku damu kanku Akan sekun bani hak'uri shikenan ai komai ya wuce dama wannan lokacin niketa addua Allah ya kawo minshi kuma gashi yazo Humm yanzu dai ku taso mu tafi our breakfast is ready "Ummee ta k'arashe tana mik'ewa tare da Kallon su Khameel dake gabanta, suma duk dariya sukayi kafin suka tashi suka bita suna tsokanar juna kamar dai k'ananan yara, dakanta duk tayi serving d'insu harma tasoma Bama kowannen su abaki datazo Kan Fawax ne taga yanata sunkuyar dakai, murmushi tayi tace "Ahah Fawax yarona lafiyan ka kuwa" Nabil ya tab'o k'afar jabber shikuma jabber ya tab'o k'afar Khameel lokaci d'aya suka tuntsire da dariya kafin Khameel yace "Ummee ai kinsan surkun taka" Ummee tace "surkuntaka kuma akanwa kenan" Nabil yace "eh Ummee son Shubai'a yake kuma wallahi son tsakani da Allah yake mata hasalima auren ta yake son yayi" jabber yace "eh Ummee kuma kinga shi yayi karatun shi yana da abunyi bakamar mud'innan ba please" Khameel ya kamo hannun ta yace "dama ai harda neman aure muka zo Idan uwa me daraja ta amince ai semuje anjima ko mu Ummeen mu" Ummee ta kama hannun Fawax tana murmushi kafin tace "Haba mana my son wane irin kunya kuma a tsakanin mu kaima fa yarona ne karka damu kaji anjima da kanmu zamuje mu nema maka aure agurin sarki kaji *son in-law* karka wani ji ka damu" Khameel yace "yes kaji uwar albarka" kafin wani ya kuma magana suka jiyo muryar Shubai'a tana fad'in "Allah sarki rayuwa kowa da ranar sa yaude ga ranar Shuwaiba datana nan da tun dazu ta tadani tace tanajin yunwa amma saboda bata nan gashinan na maka......" mak'alewa maganar ta tayi sakamakon ganin wa'inda batayi tsammanin gani ba, saurin juyawa tayi zata Bar gurin domin Jin zuciyarta na bugawa, kamar daga sama tajiyo muryar Khameel Yana cewa "Aifa su sis Shubai'a anyi baki magana kuma se an samata waigi" saurin juyowa tayi domin tabbatar ma da kanta shine yayi maganar da gaske, ai kuwa shine, abunda zuciyarta tace Mata kenan, kashe Mata ido Fawax yayi, Ummee tace "Yawwa k'araso mana kiyi breakfast" har yanxu idonta be gama gasgata abunda ta gani ba, seda taje ta zauna sannan ta fahimci komai nanfa suka hau bata hak'uri domin su kansu sunsan Sunyi laifi sosai, Aikuwa harda kukan murna seda tayi, ganin bazata Dena kukan bane yasa suka fara zolayar ta Akan itace matar Fawax....






*KATSINA*





"amma gaskiya Malam ba'ayi min adalci ba wannan ai Sam ba adalci bane ya daga zuwan mutun kawai zaka d'auki auren yarinya ka basu kodai Malam kud'in ne suka rufe maka ido" Malam Nasir yace "Haba saadiya maganar ki ta fara yawa kina nufin AKAN KUD'I zan aurar da Maryam Kenan, Sam ba haka bane Allah ne ya rubuta Maryam matar bawan Allahn nan ce kuma kamar yanda na Gaya miki munyi magana da Ummah Sarauta, gobe in sha Allah zata tafi da'ita kuma xasu dawo kafin nan kema seki je kuma a matsayina na mahaifin Maryam Nike magana "daga Haka ya wuce ciki yabar Maman Maryam da rashin fahimtar ta saboda ya lura Sam bata fahimta.





" Yawwa yaron kirki ka shirya komai kafin goben da safe zamu taho "Ummah dake zaune Saman kujera ta fad'i hakan tana shafa Kan Maryam, seda ta Gama wayar kafin ta kalli Maryam tace" Amaryarmu kenan "murmushi Maryam tayi tana b'oye fuska kafin ta kalli ummah tace" yanxu ummah daman kinsan komai amma kika dunga nunamana kamar baki sani ba kika barmu munata haukan banzan mu" Ummah tayi murmushi tace "Haba Maryam Nima fa uwace kamar ko wacce dole xan shiga damuwa Idan wani Abun ya faru da yarinya ta tun farkon rayuwar Sarauta Nike bibiyar komai nata to kuma Taya harzaata kwatanta yimin wayo kawai dai nabarku kuyi ku gama ne" Maryam tace "ammafa duk da Hakan kinga kin had'a ni da aminiyata" Ummah tace "Kedai kika sani, yanzu tashi ki d'au matafinki driver ya mik'a ki gida kafin angon nan ya kuma kirana"......





*washe gari*





Sirayya tayi magana da yayanta inda dakyar aka samu Shureim ya maida Khaleesat amma ita kuma Juwaira an murza dambu taliya Abun yak'i yiyuwa tak'i amincewa ta koma Haka kowa ya kyaleta, yayin da wani b'angaren kuma Khaleesat take k'ara Jin wata wutar tsanar Sarauta saboda gani take gaba d'aya dalilin ta ne komai ya faru harda fad'an da my d'inta tayi Mata.





Kamar yanda Ummee ta fad'a harda ita akaje gurin sarki domin nemawa son in-law d'inta aure Aikuwa sarki yayi murna kuma ya amince inda ya Kira mahaifin Fawax ya sanar mishi komai har aka tsaida wata me zuwa za'ayi auren, Aikuwa sosai suke murna da farin cikin hakan.






"wallahi yau tunda na tashi Naji gabana Yana faduwa Allah Dai yasa alkhairi ne" Abiey ya fad'a Yana Kallon Ummee, tace "Ameen Ameen dia Nima wallahi tunanin da Nike kenan, yau duk najini wani irin ganinan dai" yace "addua kawai zamuyi, Uhm Yawwa yame jikin nan kuma ta kuma ji" Ummee tace "Jiki ya warware amma tsallame su tana d'akin shi kafin ta Ida warwarewa kawai su koma gida" sarki yace "to masha Allah, Allah ya kyauta gaba" Ummee ta amsa da Ameen.






Yau tun safe take

Please Login or Register in order to submit comment