Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lura dashi, Yana matuk'ar farin ciki, motsi kad'an taga yayi murmushi, yanzu ma wankan ya fito yayi kwalliyar shi mekyau, yau harda y'ar wak'a taji yanayi, dimples dinshi Duka biyu a lotse se faaraa yake, gefen ta ya koma ya zauna kafin ya Kama hannun ta yace "Mrs zanje na dawo" wani irin k'ududu taji ya tsaya Mata a wuya kardai soyayya ya fara Aikuwa daseta kashe kanta dan bak'in ciki, "Ina zaka" ta tsinci kanta dayi mishi tambayar, Yana murmushi yace "just 30mins yanzu xan dawo" tace "nifa yau tunda muka dawo asibitin nan Naji jikina duk Babu dad'i" ya kuma kama hannunta yace "mah Mrs addua xakiyi kinji kidena cewa hakan Ohk" Sarauta ta d'aga mishi Kai kafin ya mik'e ya kuma yimata sallama sannan ya tafi, "gaskiya karna tsaya Kallon ruwa kwad'o yayimin k'afa, *INA SON MUHAMMAD SHUREIM* koma meze faru zan sanar mishi shima nasan Yana sona" ta k'arashe tana k'ara k'arfafama kanta gwiwa, "tabbas nasani kamar yanda Nike sonsa Haka yake sona, lokaci d'aya soyayyar sa tashigeni ayanzu inajin bazan iyayin rayuwa me kyau ba bata re dashi ba *MUHAMMAD SHUREIM SHINE RAYUWA TA*" Haka Dai take tayin magana ita Kad'ai kamar zautatta.






"sannun ku da zuwa, Ummah na sannun ki da dawowa" ya fad'a yana kamo hannun ta daga stairs d'in, kallon gurin take tanajin zuciyar ta nak'ara tsananta bugu, kallon Shureim tayi tare da goge hawayen ta tace "mah golden booo yakake ganin zamuyi da brother Zabvier" Shureim ya jawota jikin shi yace "karki wani ji kin damu inanan ai kuma yayan ki baze iyayin fushi dake ba" murmushin yak'e tayi Mai Don ita kad'ai tasan halin da zuciyar ta take ciki, Maryam kuwa dama tunda suka taho take kuka tun ummah na lallashin ta Akan xasu koma 9ja very soon harta gaji, itama data gaji da kukan barci me nauyi ya d'auke ta, seda suka k'araso sannan ta farka ( *tab Ai wallahi Idan Naga kaina a jirgi Babu wata harkar barci sena k'arema duniya Kallo daga sama Ahhh akwai selpie kenan* 🤣🤣)





A Haka suka sauko daga Saman companyn inda jet d'in su ya sauka, suna saukowa suka tarar da Hisham, kallon Maryam yayi tare da bud'e Mata hannuwa Alamar ta taho yayi hugging d'inta, Allah sarki ku nigeriawa akwai kunya, balle kuma katsinawa kunya garemu badai tsoro ba, sunkuyar dakai tayi batare dataje ba, gurin Ummah ya k'arasa yana sosa Kai kafin suka gaisa da'ita, ummah na b'oye halin datake ciki tace "to gadai amarya nan amma nita rako, banason Jin wata magana bayan wannan Idan ta koma 9ja kaje ka d'auko ta" Hisham ya kalli Maryam kafin ya sunkuyar dakai yace "to ummah Allah ya bani iko" Shureim yace "kamar ya" Sarai Hisham ya gane wulak'anci Shureim yake shirin yi mishi shysa be tanka Shiba Haka suka shiga mota, jerin gwanon motocin suka d'auki hanya.






Suna shiga gidan ummah ta soma zubar da hawaye an kuma gyara masarautar, Anan fa tayi rayuwa kamar gimbiya aka nuna Mata so fiye da kowa amma data tashi seta saka musu da Abunda tayi se ayau ne takejin kunya ta lullub'e ta ta abunda tayi tabbas bata kyauta ba.




Yana shiga falon ya tsaya inda ummah na abayan shi yanda Babu wanda ze ganta, ita kuma Maryam Hisham ya kama mata hannu suna gefe atsaye, cikin d'aga murya sosai Shureim ya soma Kiran sunayen mutanen gidan "Ummee, Abiey, Shubai'a, Shuwaiba, hajjas, goggo ta Sirayya, goggo ta, Ni'imatu goggo ta Safiyatu, Khameel, fawaz, jabber, Jameel, jameelerh, khairy, Aunty Rama, duk kuna Ina ne uncle Yusuf kuna Ina ne ku fito mana" kusan duk a lokaci d'aya suka fito Abiey na cewa "Anya kuwa lafiyan ka Yarima kake ma mutane irin wannan Kiran ko yauma matar taka aka kuma ta b'awa" Shureim da farin cikin shi ya kasa b'oyuwa yace "kasan Mena kawo maka ne" sarki ya girgiza Kai cike da mamaki, Shureim yayi dariya yace "daga baya ka bani goron albishir d'innan" Yana gama fad'ar hakan ya matsa gefe inda ummah ta bayyana kamar aljana, kowa dake falon seda ya firgita da ganin ta, murya na rawa Abiey ya nunata tare da cewa.....








*Karku manta AKAN KUD'I k'irk'irarren labari ne danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa tare kuma da tunatarwa, nice taku me nishad'antar daku a kullum da ko yaushe*






@ *sherntee Ghayu* 🥰🥰







@07064706167

💵 💴 *AKAN KUD'I* 💴 💵

(A poor lady story)



....... 26th June, 2023




*Story & writing*
*By*



@ *sherntee Ghayu* 🥰🥰






🔔 📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* 📚





👑J. W. A👑






🅿........ *063 & 064*






....... Tare da cewa "Nur" k'arasawa tayi gaban shi tare da zubewa k'asa cikin kuka me tsuma zuciya ta soma cewa "Yayana nice, nice nan na dawo yaya ku yafe ni tabbas nasan ni me laifi ce amma in sha Allah na tuba kuma baxan sake ba wallahi yaya Naga rayuwa, tabbas ni nasan Inada son Kai yayana dan Allah ka yafe min tabbas son kaina be Haifa min komai ba yafiyar ku itace abunda nafi buk'ata awannan lokacin dan Allah" sarki na kauda Kai gefe ya juya ya kalli inda Shureim yake tsaye yace "Waiku bana hanaku barin kowane mutum Yana shigowa masarautar nan ba, wasu fa ba Abun yarda bane, baiwar Allah ke Wacece eye, kiyi hak'uri ki tashi ki tafi kinyi b'atan hanya ne" cike da mamaki ta mik'e tana Kallon sa kafin ta soma girgiza tana cewa "ahahh yayana tabbas na sani ko amafarki ka ganni zaka gane Idan ana mutuwa a dawo to Idan ka mutu ka dawo seka gane ni ya...." bata k'arasa ba ya daka Mata tsawa tare da cewa "bamu da had'i dake nace ki fita" hannu tasa ta goge hawayen ta kafin ta juya ta nufi inda Neenah ke tsaye, hannun ta takama tasoma cewa "nasani ke uwace dole zakiji Babu dad'i Akan abunda na aikata, amma kuma nasan Zaki yafemin abunda Nayi miki, wallahi Mahh Allah ya Gama saka muku abunda Nayi muku tunda harya azurtani da yarinyar data fini son Kai, hajjana ki temaka ki yafe min wallahi.... " bata k'arasa ba Hajja ta katse ta, tabbas Hajja Neenah mace ce me k'arfin zuciya ba kasafai kake ganin raunin ta ba, tabbas tanan b'angaren zamu iya cewa Sarauta kakarta ta biyo, kallon ummah tayi tana k'ok'arin b'oye kukan ta daya taho tace" Wai baiwar Allah ked'in Wacece, nifa Banida wata d'iya bayan Ni'imatu Wacece ke" Ummah ta soma zubar da hawayen k'unci da danasani tace "ahahh Hajja ta Kece fa, tabbas nasan dama Zaki hukunta ni dan Allah karki aikata min hakan please Hajja" hajja Neenah bata kuma cewa komai ba ta juya ta tafi b'angaren su, juyawa tayi tare da nufar inda Sirayya take, sedai tun kafin ta k'arasa Sirayya ta d'aga Mata hannu tare da cewa "karki soma, bamu da waya y'ar uwa, bayan tsawan lokaci damuka d'auka Muna jiran ki zuwa wannan lokacin kuma mun cire ki a ranmu, kafin mutuwar Abba kullum bashi da Abun fad'a se Wai Ina MADINATUL MUNAWWARA tadawo kuwa yaushe zata zo, abunda yake fad'i kenan harya mutu, shine se yanzu Zaki dawo ma rayuwar mu, Nur mu munriga mun cire ki Arayuwar mu kamar dai yanda kika yi abaya kema" tana gama fad'ar hakan ta samu guri ta zauna tana Jan dogon tsaki, ummah na juyawa Ni'imatu ta rungumeta lokaci d'aya suka fashe da kuka, cikin kuka ummah ke cewa "yah Ni'imatu ki yafemin nasani nayi ba daidai ba Nid'in nan Inada son kaina da yawa dan Allah ki yafemin" itama Ni'imatu cikin kuka take cewa "Haba y'ar uwata ni Babu abunda kika yimin laifin ki d'aya dakika yi nisa dani alokacin da nafi kowa buk'atar ki amma shima yanxu kin wanke kanki tunda gashi Kin dawo gareni" nanfa wa'innan y'an uwan suka had'e Kai sukayi ta kuka.






Babu wanda ya lura da Sarauta data daskare a tsaye tama rasa me zata ce, tabbas wannan mafarki ne to Idan ba mafarki ba uban waye ya kawo ummah JIDDA kuma me takeyi acikin larabawan nan Kai ina wallahi wannan mafarki ne, inama ace wani ze tashe ta daga wannan mummunan barcin, datana farkawa k'asar ta zata koma domin kar mafarkin nan ya tabbata, tana cikin wannan tunanin kawai, taji muryar ummah da take duk'e a gaban sarki tana cewa "tabbas nasan Nayi kuskure amma ka yafeni d'an uwana, koba komai Nima Allah ya jarabce ni da yarinya wacce ta fini son Kai yaya ka temaka Idan ma bazaka iya ba Ina rok'on daka yafemin saboda y'ata d'aya tilo Sarauta" ta k'arashe tana juyawa ta kalli Sarauta dake tsaye har lokacin itafa bata yarda ba mafarki take. Abiey ya juya ya kalli Sarauta dake gefe tsaye, mamakin abunda wannan k'anwar tashi ta fad'a Yama Hana shi yin magana, ganin hakan ne yasa ummah ta mik'e tare da zuwa ta kamo hannun Sarauta ta Jefar da'ita agabanshi, se yanzu Sarauta ta k'ara tabbatar da ba mafarki take ba, nanfa wani kukan takaici da bak'in ciki had'e da danasani ya Kamata, ummah dake kuka itama ta soma cewa "Idan har bazaka yafemin domin yarinya ta ba ainasan zaka yafemin domin mahaifin ta ko" Abiey ya kalleta yace "mahaifin ta kuma.." Ummah tace "kwarai ma kuwa saboda itad'in ba d'iyar kowa bace face d'iyar *BROTHER M.S SARAUTA* itad'in y'arshi ce" ba Abiey kad'ai ba duk wanda ke falon seda ya razana tare da maimaita Sunan data fad'i, se kuma Anan suka k'ara hango tsantsar kamar dake tsakanin Sarauta da mahaifin ta Sarauta, Allah me iko Ashedai d'an uwana seda ya cika muradin shi na auren Nur ashe seda Allah ya had'a su a wata k'asar tabbas wannan Abun ya wuce gaban kwatance Abiey yake wannan tunanin, k'arasawa yayi inda Sarauta take tare da kama hannun ta Yana Jin tamkar d'an uwanshi ya kama suka soma Hawa upstairs d'in falon yayi shuru se k'arar takun ta kalmin Sarauta da yake tashi, harya kusa kaiwa k'arshe suka jiyo muryar shi yana cewa "ku bata d'aki" daga Haka ya wuce sama tare da y'ar d'an uwan shi, ummah tayi ajiyar zuciya ta juya ta kalli Shureim lokaci d'aya suka sakarma juna murmushi kafin ta juya ta kalli Ummee dake hangen upstairs domin ganin ko sarki ya Haye sama, ummah t k'araso inda take tare da d'ora hannuwan ta Duka biyu Akan kafad'arta tace "har yanzu dai kina nan da tsoron mijin naki kenan" Ummee ta Harare ta tace "Dallah sakarni bayan kin tafi kin manta dani Koda sau d'aya baki tab'a yin kuskuren kirana domin kiji lafiya ta Kota yaron ki ba" Ummah tace "Haba aminiyas to Bana bada hak'uri ba kuma" Ummee tace "hakan be wadatar ba" Ummah tace "shikenan anjima xan Kira miki yayana" ta fad'i maganar domin zolayar Ummee saboda alokutan baya Idan Sunyi fad'a hakan kawai take yi Mata seta hak'ura, duk su biyun dariya sukayi tare da rungume juna.







*SOME HOURS LATER*





Duka ahalin zaune suke a falon inka cire, hajjas, hajja Neenah, da Abiey da Sarauta, amma gaba d'ayan su zaune suke a falon, Shuwaiba datayi filo da cinyar ummah tace "Haba no wonder ashe shysa nikejin first Lady har cikin jini na ashe kanwata ce" Ni'imatu ta buge ta tana cewa "mudallah d'aga mana y'ar uwa ki barta taji da gajiyar ta" Safiyatu tace "gaskiya Kam ki d'aga mana y'ar uwa" Ummah tayi dariya tanajin wani sabon farin ciki na ganin ahalinta na k'ara lullub'e ta tace "ahahh fa ku kyaleta ta kwanta, dabana nan ai bata kwanta ba" Shuwaiba tace "kwarai ma kuwa, kuma wallahi ummah bakisan wani Abu ba yau d'innan akwai d'a'amum kinji yanda wani k'amshi na musamman yake tashi kuwa" jabber yace "Aifa su Shuwaiba mala'ikun tauna, wallahi ni nasani da za'ayi common 4hours ace ba'a bama Shuwaiba abinci ba to da inaga hankalin kowa ya tashi" Khameel yace "to ai Kai kama kaita da nisa awa2 kawai zatayi bataci ba duk duniya se sun sani" Nabil yace "ai yaya ba k'aramin k'ok'ari yake ba wallahi" Shureim yace "kunga ku kiyaye mu Tohm, Ina ruwanku ne ma, ba matata bace Idan ma naciyar da'ita ai don su Nike nema" Shuwaiba na komawa kusa dashi tace "that's my Mr billionaire" kowa a falon yayi dariya, Khameel datun d'azu yake Kallon khairy datayi shuru bata cewa komai yace "kewai bakya magana ne" tayi murmushi tace "inayi mana" yace "Ainasha ma kurma ce saboda Naga tuntuni ake magana ke baki ce komai ba" khairy ta had'e gira tace "towai Kai inama ruwanka danine eye, mtsww nifa banason shishshigi" kowa yayi dariya, ummah ta kalli Hisham dayake danna waya Yana dariya tace "amm Hisham ya Maryam" ya d'ago kanshi Yana sosawa yace "tana ciki" Aunty Sirayya tace "kaga Mara abunyi shine zaka baro y'ar baiwar Allah Haka baka ganin bak'uwa ce" Hisham yace "itafa tace min tana buk'atar hutu" Aunty Safiyatu tace "Aida yake Haka ake hutu da yunwa ko" Aunty Rama tace "kubar mahaukacin ai seda na Bari ya fito sannan na shiga nakai Mata snacks da pure milk Tasha sannan tayi wanka ta kwanta amma fa shida Haka ya barota ko Oho, ni inaganin wannan rayuwa" Hisham yace "Uhm kaji uwa ta gari sedai kuma kiyi hak'uri fa ba'a nan zamu zauna ba balle ki fara sangarta min ita Haka" Aunty Rama tace "gidan ubanwa zaka kaita" yace "k'asar zamu Bari mana, amma fa se inda ta zab'amana amma ni nafi son Rasha ko Russia saboda kasuwanci na yafi k'arfi acan" jameelerh tace "Aikuwa yanda matar ka take me kyau d'innan k'asar Rasha zata Dace da'ita" ya harari yah jameelerh yace "na kawota inda kike ki b'ata min ita da yawo" jameelerh ta jefeshi da filow, Ummee da shigowarta kenan ta kalli aminiyar ta tace "kinga k'anwar mijina tashi ki shiga ciki ki huta Idan kika biye ta wa'innan shashashun Babu abunda zakiyi" Ummah tace "to matar yayana Bari naje Nayi wanka kawai na dawo gurin yarana, Aina maji kamar sanwa ta sauka ko" Shuwaiba tayi zumbur tace "Yawwa uwa ta gari kiyi sauri ki fito muci abincin dan Babu wanda zan Bari yaci koni ma d'and'ano kawai zanyi" ta k'arashe suna tafawa da Ummah wacce lokaci d'aya suka saba.






B'angaren Sarauta kuma, tunda suka je d'akin Abiey take kuka, dakyar ya samu ya lallab'e ta, Koda ya tambaye ta shin da gaske ita d'iyar Nur ce, eh kurum tace mishi, kuma daya tambaye ta da gaske Sarauta shine mahaifin ta cewa tayi ita bata saniba saboda batasan ma waye baban nata ba, Jin hakan yasa sarki shiga wata duniyar tunanin ta daban, Haka ya tashi ya fita domin kanshi yadau xafi, itakuwa Sarauta tana nan zaune cike da kunya da kuma mamakin ganin ummah da Maryam, "Meya kawo su tabbas akwai wani Babba wanda yake dasa hannu acikin duk wannan, wanene kenan" tunani kalakala haka Sarauta ta keyi inda ta rufe kanta a d'aki tama kasa fitowa saboda tsabar kunyar ummah data Kamata.






Dukkan su zaune suke a dining room d'in banda Shureim da yake zaune a falo yanata yima ummah signal Alamar ta taso su tafi, ita kuwa firar da ahalin ta keyi Mata ma ta hanata tashi, kowa da abunda yake cewa kuma duk ummah suke Bama labari, suna cikin firar ne kamar daga sama sukaji muryar Abiey Yana cewa "Maryama Wai taron miye ne akeyi Anan gurin" kowa seda ya nabba'a kafin Ummee ta juya cikin in..ina tace "Uhm dama Wai kawai dinner mukeyi, eh dinner ce kawai mukeyi" Abiey ya kuma d'aure face yace "to dare yayi kowa ya wuce yaje ya kwanta sekace wani sabon Abu duk kunbi kun ishi mutane da hayaniya mtsww" ya k'arashe Yana hayewa Saman benen Yana kuma cewa "karna sauko na iske d'aya daga cikin ku anan" daga Haka ya Haye Saman benen, ummah ta kalli Ni'imatu tace "yayah Ni'imatu duk saboda ni yake Haka ko" Ummee tace "Laaa Sam Bahaka bane kawai Dai Kwana biyu Haka yake ko magna bayason yi ki kwantar da hankalin ki kinji komai ze wuce" Ummah tace "karki wani kare shi nasan duk Danni yake hakanan" fawaz yace "tab ashe kuwa haushi ze kwantar da mutum dan munan har taron murnar dawowar Uwammu se munyi" Shuwaiba tace "Dagaske Kam ni zanma bada gudummawar dajaja" Shubai'a ta tuntsire da dariya tace "wallahi dama nasan abunda xaki fad'a kenan" Fawax ya kalli abar sonsa yace "wasuma dasun San yanda dariya take yimusu kyau da basu dunga ciccin face ba" Khameel yace "Aiko kaima kasan bazaka gayawa Lil sis d'ina dariya ba" Fawax yace "WA... Wai wannan d'in tab, kullum fuska a d'aure kamar dodo" Shubai'a ta fusata ta tashi ta bishi inda shikuma ya shiga zagaye dining d'in. Kowa agurin dariya yake yi da wannan damar ummah tayi amfani ta faki idonsu ta fita, suna fita daga part d'in Shureim yace "amma fa kin dad'e" ta kama kunnen ta tace "ayima Umma afuwa mah golden boo" yayi Mata murmushi kurum suka cigaba da tafiya, gani Nayi sun zagaaya ta d'ayan part d'in tsayawa yayi tare da cewa "ni zan tsaya Anan ma diamond ki shiga ciki sekin fito" tana goge hawayen ta tace "kawai ka tafi gobe da safe muyi waya" ya girgiza Mata Kai yace "dan Allah kiyi sauri ki fito mu tafi goben kin dawo ni nama tabbatar da yanzu anacan ana Cigiyar ki karkisa Abieyna ya kashe ni mana" tayi murmushi tace "inajin Idan Naga Mamuna bazan iya barin ta ba" yayi murmushi yana zama Saman wani guri yace "nizan jiranki Anan kiyi sauri" ta girgiza Kai tasan baze tab'a barinta ba, ta juya ta shiga ciki.






"Nidai maganar gaskiya na Gaya muku, kunsan tsakanin mu Babu b'oye² nagaya muku iya gaskiyata wallahi Babu abunda zan iya, saboda gaba d'aya shugabar malamai ta duniyar aljanu tana jikin ta kuma duk wani hatsabibin aljani dake aduniyar aljanu tofa Yana shakkarta dan ita kisa take har lahira yanzu Bahusba Yana nan bashi moruwar komai yazama kamar photo Allah kad'ai yasan me tayi mishi ni nama rasa yanda zanyi" Hajja Mubeena ta kalli Hajja jumaima suka goge gumin su kafin Hajja Mubeena tace "wallahi Mama unana yarinyar nan duk tana son tono komai" Mama unana ta fashe da dariya tace "Waiku da kund'auka da wasa nake, ai shirin Allah yafi namu kuma muma munsan hakan seda yardar shima muke yin komai, kuma dama aina fad'a muku yarinyar nan itace mabud'in komai ku tashi kawai ku tafi Banida Abun yi" Hajja jumaima ta ta tashi tare da fincikar hannun Hajja Mubeena ta kalli mama unana tace "Idan ke baxaki iya aikata komai akai ba muzamu iya, ai duk laifinmu ne damuka mik'a akalar yardamu agurin ki zakiga abunda muma da kanmu zamu iya ai *in this Nowadays d'an Adam yafi aljani iskanci yafi shed'ani shed'anci infact shima shed'anin Kansa ne* dan haka kijira abunda zamuyi ki zuba ido kawai kiyi Kallo" daga haka suka fice kamar iska, mama unana kuma se uwar dariya take musu.






Tun bayan data dawo d'aki Babu abunda ta iya aikatawa still har lokacin a zaune take ko sallah yau bata iya tashi tayi ba balle kuma wanka dacin abinci, yanzu ma tana zaune ko motsin kirki batayi Ummee ta turo k'ofar tashi go, kusa da Sarauta ta zauna tare da kamo Duka hannuwan ta, Sarauta na d'agowa ta fashe da kuka tare da fad'awa jikin Ummee kuka takeyi sosai kamar ranta ze fita Ummee ta goge hawayen ta tasoma lallashin Sarauta tana cewa "calm down daughter in-law ki Dena kuka kefa jaruma ce, jaruma ce ke sosai kuka Sam be dace dake ba, farin ciki ya Kamata kiyi ba kuka ba" Sarauta ta kalli Ummee cikin kuka take cewa "Wai meyasa kuke min hakan nan ne, niba jaruma bace meyasa zaku hanani yin kuka, *kuka fa ba ragwanci bane wani yarene na zuciya wanda wannan hawayen su kad'ai suke iya bayyana yaren* kubar ni Nayi kukana mana ku barni" ta k'arashe tana k'ara fashewa da kuka, a wannan lokacin Ummee batayi yunk'urin hanata ba seda ta Bari tayi me isarta kafin ta cigaba da lallashin ta harta samu ta nutsu tayi shuru, ita ta temaka Mata tayi wanka sannan ta Rama sallolinta before tagama Ummee ta had'o Mata abinci, dakyar ta samu taci d'an kad'an tana cikin ci amai ya kwace Mata before ta Gama Aman kuma zazab'i ya rufe ta, hankali tashe Ummee ta kwantar da'ita kafin ta fita neman Shureim domin yazo ya temaka Mata Koda allura ne.






Sanda ta shiga b'angaren ba iya Mamu ba harta y'an biyu Sunyi mamakin ganin ta, na ta zauna sukasha kukan su inda ta kwashe tas labarin rayuwar ta bayan barin gida ta sanar dasu, kuka kuwa sunsha shi, ganin Shureim ya isheta da waya ne yasa tayi musu sallama tare da sanar musu da cewa su shirya gobe da safe zata dawo ta d'auki Mamu su fita daga b'angaren, Aikuwa Mamu tayi matuk'ar murna sosai domin a wannan lokacin Babu abunda take buk'ata sama dataga d'anta d'aya tilo, Zabvier.






"Wai kana Ina ne, to koma a Ina kake kazo ka duba matar ka bata da lafiya wannan ai wulaqanci ne tun yinin yau ka kasa tsaye ka kasa zaune sekace sabon ango to kayi maza ka dawo na Gaya maka" hak'uri kurum ya bata yace Mata Yana zuwa, seda suka sha firar su da Ummah Akan hanya sannan suka k'araso d'akin data zab'a ya rakata kafin ya tafi, dan Sam be sanar da'ita cewa Wai Sarauta bata da lafiya ba.





"sorry mah daughter in-law kiyi hak'uri da wannan kukan dan Allah ki tashi Koda madara ce Kisha kinji" Aunty Rama ta k'arashe tana tallafo Maryam dake kuka, Hisham ya dawo gefen su ya zauna Yana cewa "wallahi Aunty kinganta nan tuntuni Nike fama da'ita amma tak'i sanar min komai kuma nasan duk wannan d'in baze wuce Akan Mrs M.S Sarauta bane, Nidai wannan surukar tawa tana bani wahala" Aunty Rama tace "banason kukan kinji ni, tashi Kisha madarar nan sannan kici abinci kinji" Maryam na share hawayen ta tace "na k'oshi" khairy tace "Kai Aunty miye ne haka dan Allah ki saki jikin ki kici abinci mana yanzu fa we're one family dan Allah" jameelerh tace "hakane Kam kisaki jikin ki kinji duk da mijin ki ya rainani amma Aike k'anwa tace ko" Maryam tayi murmushi ganin yanda Aunty jameelerh take aikama Hisham Harara shima Yana Ramawa, Haka suka shammace ta batasan ma Sanda ta saki Jiki dasu ba seda suka sha firar su gaba d'aya harda Aunty Rama wacce bata d'auki duniya da zafi ba.






Suna zaune a bakin gadon bayan ya Gama dubata har ruwa ya samata, hannun shi Sarauta ta rik'o tanajin sonsa kamar ze b'ula zuciyar ta ya fito tace "Mr wanene wanda ya kawo ummah nan" ya kalleta cikin halin ko inkula yace "nine Nayi hakan" tace "kuma Kaine ka Gayamata komai" ya d'aga Mata gira kafin yace "ki kwanta ki huta yawan tambayoyin basa da amfani" tayi Mai murmushi dan tsakani da Allah ko kad'an bataji haushin abunda yayi ba, tabbas so Hana ganin laifi (Niko nace

Please Login or Register in order to submit comment