Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amince ya auri y'ata kurum, Khaleesat tace "kuma fa shima Yana sona My" Sirayya tace "nasani nasani y'ar marainiyar Allah yi hak'uri Dena kuka kinji" Shuwaiba ta wani fashe da matsanancin kuka tana fad'in "dama ai nasani kowa Anan tsoronta yake ji dubi ta yanke hukunci kuma kowa yayi shuru, nidama nasani ummmaaah baki sona, ita jibi abunda tayi Akan y'arta ni kawai zanbi duniya Babu wanda ze k'ara ganina gwara na mutu kowama ya huta kawai" Ni'imatu ta rik'ota tana cewa "Aifa sedai ayi duk wacce za'ayi amma Shureim Shuwaiba kad'ai ze aura kuma Hakan za'ayi" Hajja Neenah tace "kwarai ma kuwa Idan ba haka ba kuma ni nasan Mize faru" wata irin k'ara Juwaira tasa wanda seda kowa ya dod'e kunnenahi tace "ni kawai mutuwa zanyi kashe kaina xanyi Nida bani da gata ba'a d'auke ni Amatsayin mutum ba gwara kawai na mutu kowama ya huta" Safiyatu tace "Aiko dana shiga uku ki mutu kuma dako anyi mace² d'anshi kanshi Shureim d'in seya bak'unci lahira Aiko bazan Bari Hakanma ta faru ba gwara ayi me yiyuwa wallahi" Hajja Mubeena tace "kwarai ma kuwa" Sirayya tace "Naga ubanda zesashi ya auresu" Safiyatu tace "ke bafa tsoronki ake ba neman zaman lafiya ake amma awannan gabar kuma dole kowa yayi ta kanshi dan sama ma farin cikin shi farin ciki" Ni'imatu tace "wannan Haka ne ma kuwa" nanfa fad'a da cacar baki ta b'arke har ana k'ok'arin Kai bugu, falon ya gama hargitsewa, "ya'isa!!!!!!!!!" ya furta cikin tsawa, lokaci d'aya falon yayi tsit, "dukkan su zan auresu" shine kurum abunda yace ya mik'e yabar gurin nanfa aka fara Kallon Kallo, kafin kowa yaja y'arshi ya wuce ciki Ummee ma ta kama Shubai'a suka wuce ciki. Duk wannan hatsaniyar da akai Sam Sarauta batasan meyake Faruwa ba saboda tana d'aki tana Rama barcin ta da batayi ba jiya.





"baka da hankali ne Shureim dazaka amince wa auren mahaukatan yaran can" Abiey ya fad'a Yana fuskarta Ummee, itama ta tab'e baki tace "Nima Abun bak'aramin mamaki yabani ba meyasa zaka aikata hakan Shureim" Shureim yayi ajiyar zuciya yace "Ina buk'atar zaman lafiya ne" sarki yace "Aida ka Bari sun gama regime su sun hak'ura kawai nasani xasu hak'ura basuda hatsaniya amma kaga waccan shed'aniyar Sirayya se addua koma ya akayi mijin ta ke iya rayuwa da'ita" Shureim yace "Abiey inason gobe a d'aura auren sannan su tare a gidana sabon da aka gina dama part 5 ne gidan" Abiey ya kalli d'an nashi cike da tausayi yace "amma Shureim" Shureim yace "amma me Abiey hakan shine mafita mu hak'ura kawai seda safenku" daga Haka ya fice a d'akin, Ummee kuwa batasan Sanda kukan tausayin d'annata ya kwace Mata ba, haka sarki yayita lallashi harta hak'ura.




"hello Maryam kin kirani Ina barci" Maryam tace "barci kuma Keda baki barcin rana lafiya Dai ko" Sarauta tace "kawai zazzab'ine ke damuna shysa" Maryam tace "Subhanallah Meya faru ko anmiki wani Abun ne" Sarauta tace "ah ah kawai kaina ke ciwo karki damu Babu abunda ya faru" Maryam tace "kin tabbatar" Sam yau Dai Sarauta batason yawan magana indai ba ne mahimmanci bace shysa tace "karki damu yanzu Ina wani Abu Idan na gama zan kiraki" daga haka Sarauta ta yanke wayar.





"what Shureim are you out of your sense baka da hankali ne zaka aikata hakan Akan me zaka amince eye" Shureim yad'an kauda wayar daga kunnenshi saboda k'arar tayi yawa yace "please Hisham zan kiraka Ina wani Abu" cikin b'acin rai Hisham yace "Idan ka yanke wayar nan semun samu gagarumar matsala, dole na dawo na Hana faruwar auren nan" Shureim yace "kaga Hisham Nina amince zan auresu kuma dukkan su Ina sonsu karka shiga rayuwa ta data iyalina dan Allah kadena magana irin Haka banaso kaina ciwo yake a halin yanzu zan nemi magani nasha I will call you later" daga Haka ya yanke wayar ya kwanta.





"wannan wace irin magana ce Haka kikeyi My nafasa fa kika ce to wallahi ko mu d'ari ze aura zan amince na aureshi balle mu hud'u " Sirayya tace" duk yanda kike so Haka za'ayi y'arnan ki kwantar da hankalin ki Zaki zauna dashi ke Kad'ai kinji" Khaleesat ta Matsa jikin mahaifiyartata ta kwanta tana fad'in "Ina sonshi My shidin kyakyawan gaske ne inason shi sosai" Sirayya tace "karki damu akai kiyi barcin ki me dad'i amaryar y'ata" duk dariya sukayi





"ummmaaah shid'in fa me kud'i ne sosai yakike gani Idan na aureshi zan huta sosai fa" Ni'imatu tace "hakane y'arnaan Nima Ina miki wannan tunanin, kuma kinajina nasan duk y'an uwannan naki planning zasuyi Kedai karki kuskura kiyi hakan ki sakar mishi jiki har Allah ya baki ciki ki Haifa mana magajin wannan dukiyar" Shuwaiba tayi dariya tace "hakan ma za'ayi ummmaaah na Kedai kawai ki kwantar da hankalin ki Aini Sam bani da kishin indai zan haihu" Ni'imatu tace "Aiko Babu wacce zan Bari ta haihu a cikinsu ke kad'ai ce matar shi" Shuwaiba tace "Ina sonki ummmaaah na" Ni'imatu tace "Nima Ina sonki y'ar nan.





" Wai Dan Allah Juwaira mekika gani ajikin wannan yaron da kika mak'ale mishi Haka har Zaki aureshi kufa hud'u" Juwaira tace "uwata kenan Shureim fa cikakken namiji ne wanda ko wacce macce ke fatan samun irin shi, amma babu inda bazan iya shiga dashiba, bikin kawayena, party's Babu inda bazanje dashiba ga kud'i ga ilimi shid'infa ya had'u sosai" Safiyatu tace "to ai yayi kin burge ni kaina ma ciwo yake banason yawan hayaniya Allah gashi kuma yau munyi" Juwaira tace "Allah ya baki lafiya ammata" Safiyatu tace "Ameen Dai kema maza ki kwanta kinga gobe akwai Hidima ko dan tamu seta fi tasu" Juwaira tayi dariya ta kwanta





"Wai ku kuwa kuna ganin abunda mutanen nan suka yanke hakan yayi daidai kenan" fawaz ya fad'a Yana Kallon sauran y'an uwanshi, jabeer yace "humm kaima Dai kafada nifa kasa magana ma Nayi Abun ya ban mamaki da Prince ya amince" Khameel yace "mu ai hakan gaba ta kaimu zamu dunga zuwa gidan akai² domin ganin abunda ke faruwa ko" Nabil yace "wannan Haka ne kuwa Allah Dai ya kaimu goben" fawaz yace "Ameen Dai ni kunga Bari naje na duba littafai na next week zanje makaranta Inada exams" Nabil yace "waishi wannan har yanzu be yarda karatun nan ba" jabeer yace "kabar d'an anacin yaje yayi tayi Aikin Banza" fawaz yayi murmushi ya fice, Khameel yace "Allah ya tsayar maka d'an wahala kawai" haka suka cigaba da fira.





"Shubai'a karki damu kinji ki kwanta kiyi barci dare yayi kinji" Ummee ta fad'a tana kwantar da'ita, Shubai'a ta kwace tana nuni da "Ummee ba'a yima yayana adalciba dubi halin dasuka saka shi" Ummee tayi ajiyar zuciya tace "karki damu Allah na tare dashi kwantar da hankalin ki kinji autar Ummee kwanta" dakyar ta samu ta lallasheta har tayi barci Sannan ta tashi ta tafi d'akin ta takwanta cike da zullumi.




*WASHE GARI*



A yau d'aruruwan mutane suka shaida d'aurin auren Yarima Shureim da amaren shi, Shuwaiba, Juwaira, da Khaleesat, wanda hakan ba k'aramin Bama mutane mamaki yayi ba, aranar Yarima ya aikama kowa da Key d'in part d'inta, ta b'angaren kowacce kuwa murna kawai ake Abun ba'a magana.





"what aure har Mata uku kuma" Ummee tace "Sarauta ki kwantar da hankalin ki Babu abunda ze faru" Sarauta tayi mu tace "kawai abunne ya bani mamaki sosai amma ai Babu komai Haka Allah ya rubuta karku damu" Shubai'a tayi Mata nuni da "ki kwantar da hankalin ki kuma kiyi hak'uri yaya be aikata hakan dawani nufi ba" Sarauta tayi murmushi ta girgiza Kai tace "Allah Babu komai Allah yasa hakan shine alkhairi karku damu, Bari in shiga ciki in d'anyi wanka" daga Haka Sarauta ta wuce ciki, Shubai'a ta kalli Ummee tana Mata nuni da "kamar bataji dad'i ba" Ummee tace "karki damu hakan na faruwa bawani Abu bane ba Sabo muje ciki kema ki shirya" Sam Ummee da Shubai'a basu ji dad'in lamarin nan ba ko kad'an.





Sarauta na shiga d'aki ta jingina da k'ofa tareda lumshe ido, ajiyar zuciya kurum take yi tad'au tsawon minti uku agurin kafin ta bud'e ido, cak ta tsaya tana Kallon shi kafin tace "Kai kuma, mekakeyi Anan".........



*Hmmmm ikon Allah kenan wannan rayuwa, Allah sarki Shureim kamar Nayi Mai kuka, amare kuma Ina tayaku murna, Allah sarki sarautar mu Kowanne Hali kike ciki a yanzu Abun Babu dad'i wallah* 😭😭😭😭.





*karku manta AKAN KUDI kirkirarren labari ne danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa dakuma tunatarwa nice taku me nishad'antar daku akullum da ko yaushe*




@ *sherntee Ghayu* 😍 😍






@07064706167

💵 💴 *AKAN KUDI* 💴 💵

(A poor lady story)

........ 16th May, 2023

*Story & writing*
*By*

@⁨Ummu Khamees �⁩ *Uwar baba wannan naki ne Keda duk d'auka kin masoyan Sarauta* 🤣🤣🤣💪🏼


🅿....... *025 & 026*




........... Ajiyar zuciya yayi ya k'araso tare da kama hannun ta ya zaunar da'ita a bakin gadon, kafin shima ya zauna, shuru na d'an lokaci kafin yace "yau aka d'auramin aure da y'an uwana" in I don't care mood d'innan tace "and then, nace seme, nifa auren contract ne kawai dana gama aikina zan kama kaina sukuma ai y'an uwanka ne ko" Shureim yayi ajiyar zuciya yace "dama nasanar dake ne Don karki ga kamar an cutar dake" Sarauta tayi murmushi tace "please can you leave" mik'ewa yayi yace "why not" tace "you can go" Kai kurum ya d'aga ya fice. Ajiyar zuciya tayi tanajin wasu irin zafafan hawaye na gangaro Mata, saurin gogesu tayi tana d'auko wayarta, number Maryam tayi dialing, seda ta kusa tsinkewa sannan aka d'aga, Maryam na d'agawa tace "Yawwa besty dama ke Nike jira ki Kira, ummah nason yin magana dake inama gidan yanzu Bari inje in kai...." kasa k'arasawa tayi sakamakon Jin Sarauta ta fashe da kuka, afili Maryam ke fad'in "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Sarauta ah ah, ah ah wannan ba halinki bane ked'in ba mace bace me rauni kar ki gayamin kinzama raguwa, akullum Kece ke k'ara k'arfafani amma a yau kuma Naji kinayin abunda baki tab'a yi ba, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Sarauta Meya faru wani Abun yayi miki ne dan Allah ki sanar min" Sarauta na sheshshekar kuka tace "Maryam yaufa da safe ya auri Mata uku Idan dani hud'u fa kenan Maryam you know ni mace ce me matuk'ar kishi bansan yanda zanyi ba, Maryam bazan iya zama dashi da wa'incan wulak'antattun y'an uwan nashi ba Maryam I can't" ta k'arashe tana fashewa da kuka, Maryam tayi shuru kafin tace "kina sonsa ne??" dasauri Sarauta ta goge hawayen ta tace "me, kinsan abunda kike fad'a kuwa kinsan Mekike cewa, gaskiya Maryam Kinsha wani Abu, kawai dan yana kyakyawa sena so shi, Bana sonshi banason shi kuma bazan tab'a sonshi ba har abada" Maryam tace "Idan kuma kika soshi fa" Sarauta tayi murmushi tace " *daga ranar zan koma Akan soyayya ba Akan kud'i ba, I mean bani Babu burina har abada*" Maryam tace "fine Naji wannan kuma zan tuna miki, Toh amma meyasa ki kuka akai bayan ba sonshi kike ba" Sarauta tace "Ina tunanin bazan iya zama dasu a Dan wallahi cima ba d'aya ba se'in karairaya su abanza" Maryam tayi murmushi tace "kinajina k'awata karki sake kisama ranki ke matar shice ah ah kisama ranki ke P.A d'inshi ce kawai zakiyi aiki dashine kawai nad'an lokaci, besty ked'in fa jaruma ce ba jahila ba akullum da ko yaushe sonike jarumtar ki tafi ta kullum k'awata kiyi abunda yakaiki kurum ki dawo gida, ked'in P.A ce kawai kisa haka a ranki "Sarauta tayi murmushin jindadi tace" wannan haka ne Maryam niba matar sa bace, kuma banida had'i dasaura matan shi zan zauna a matsayina na P.A "Maryam tace" Yawwa kawata karki Bari wani Abu ya k'ara b'ata miki rai harya kaiki ga kuka hawayen ki nada matuk'ar mahimmanci" Sarauta tace "Maryam Kece k'awa d'aya tamkar da dubu Ina alfahari dake" Maryam tayi dariya tace "Kedai kika sani" nanfa fira ta b'arke a tsakanin su Sega Sarauta nata dariya suna fira.





*WASHE GARI*



Ankai amare, guri yayi kyau sosai, dukkansu aguri d'aya aka ajesu sedai kowa da b'angaren shi, amma duk wacce tasauko falo zata had'u dasauran y'an uwanta abokan zaman ta, Babu wacce aka kawo dakomai domin akwai komai a gidan, komai iri d'aya akayi musu Kala ce kawai ta banbanta se b'angaren Shureim dashine Babba kuma me Kaya Kala daban, guri fa se masha Allah Dan ya had'u, kowacce daga cikin amaren murna kurum take ta auri zab'in ranta.



*At 10:00am*



Zaune yake a main parlorn Yana danna iPad d'in dake hannun shi, maroon suit ne ajikinshi, gashin kannan yasha gyara sosai, yasauko ya rufe rabin fuskar shi, Idan ma yaduk'a baka iya hango komai na fuskar shi face kyakyawan lips dinshi, Juwaira ce ke saukowa daga upstairs d'in, sanye take cikin kayan alfarma ta d'aura Alitalia me bala'in kyau da tsada a sama, ba laifi amma se masha Allah dan tayi kyau, tana hango shi ta saki k'ayataccen murmushi, 3seater ta zauna tana fad'in "Barka da safiya my nisful hayat" d'an yak'e yayi Mata yace "kin tashi lafiya" tana wani tank'warra murya tace "fatan Dai mijin juwairiyya ya tashi cikin k'oshin lafiya" murmushi kurum yayi Mata, kafin wani ya kuma magana Sega Khaleesat tasauko, itama tayi shiga ta alfarma Tasha alkyabba me D'an Karan tsada ba'a cewa komai tayi kyau, kusa da Juwaira ta zauna tana nad'e alkyabbar ta tace "fatan me kyau ya tashi Lpy" murmushi yayi yace "kin tashi lafiya" tayi ajiyar zuciya tace "kwanan ka lafiya shine nawa, Ina matuk'ar k'ara godema Allah daya hadani da miji me kyau kamar Kai, Ina matuk'ar k'aunar kyakkyawan mijina" itama murmushi yayi Mata kafin yace "Nagode kema you look cute" wani k'ayataccen murmushi tayi, kafin tayi magana Sega Shuwaiba ta shigo falon, tana sanye da k'ananan Kaya inda ta d'ora wata fitinanniyar alkyabba a sama se uban k'amshi take ta k'araso ta zauna a gefen shi Kan 1seater, tayi murmushi ta daga mishi hannu tace "Hii my husband" Shureim yace "Hii kin tashi lafiya" tayi murmushi tace "am fine what of my billionaire husband" yayi murmushi yace "fine" tace "jiya nasha mafarkin ka" be cemata komai ba ya cigaba da Aikin shi, sund'au ak'alla 15mins a gurin kowa Yana danna wayar shi, kafin Shuwaiba tace "my billionaire husband muje muyi breakfast mana" be d'ago ya kalleta ba yace "can't you wait for her..." Juwaira tace "who?" yace "my first wife" duk Kallon juna sukayi, kafin wani yayi yunk'urin yin magana sukaji takun takalmin ta, kusan lokaci d'aya duk suka d'aga Kai suka kalleta, cike da tak'ama da Sarauta take saukowa daga Saman stairs d'in, sanye take cikin blue black suit ba k'aramin kyau tayi ba, tad'aura after dress sky blue me kyau a sama, ta d'aura Vail d'in jallabiyar asaman kanta amma duk da Hakan be Hana kyakkyawan gashin kanta bayyana ba ta baya, fuskar ta Babu yabo Babu fallasa ta k'araso falon, kusa dashi taje ta tsaya, hannun ta rik'e da files dakuma iPad, tayi murmushi takalli mutanen falon tace "barkan ku" Babu wacce ta amsa Mata saboda duk haushinta sukeji sakamakon ganin ta fisu kyau duk da bawata shiga me kyau tayi ba, tab'e baki Sarauta tayi ta juya ta kalli Shureim tace "morning Sir" Yana aje iPad d'inshi yace "morning" tace "ga files d'in nagama dubawa" ta kalli agogon hannun ta tace "munada meeting 11:30am to 1:00pm zuwa k'arfe 4 kuma zamuje asibiti domin duba wasu ayyukan na daban by 6 kuma zamuje banki" ta k'arashe tana mik'a Mai files d'in, madadin ya bata amsa se cewa yayi "kin tashi lafiya" Kallon shi tad'anyi kafin tace "Alhmdll" Shureim yace "muje muyi break fast" tad'an d'aure fuska tace "na k'oshi muje kawai" yakalleta yace "dakika ci me..." tace "Aidai cikina ne ko" tab'e baki yayi ya kalli sauran yace musu "se mun dawo" be jira amsar kowa daga cikin suba ya d'auki top d'inshi ya fice.




Khaleesat tace "tab waiko kunga abunda na gani koni kad'ai na gani" Juwaira tace "Nagani wallahi Wato waccan k'ask'antattar tafimu yake nufi komiye" Shuwaiba ta mik'e tana fad'in "muje muyi breakfast daga baya se muyi maganar ni kunsan matsala ta da girki" Khaleesat da Juwaira suka tab'e baki, Haka sukaje sukayi breakfast d'in kowa da abunda yake sak'awa a ranshi, Shuwaiba ce tafara yin ajiyar zuciya tace "dolene muci uban yarinyar nan fa" Juwaira tace "ku barni da shegiya seta gwammaci bata sanshi ba Arayuwar ta" Khaleesat tace "aimu mungama more Mata tunda munsan Wacece ita d'in" Shuwaiba tace "kunsan itad'in Wacece" Juwaira tace "kwarai ma kuwa brother Nabil da Khameel sun sanar damu komai akanta" Shuwaiba tace "to meyasa ta aure mana miji" Khaleesat tace "basu sanar mana ba cewa sukayi Wai soyayya suke" Shuwaiba tace "tirk'ashi yanzu Dai kubani labarin Wacece ita" Khaleesat tace "muje bedroom d'inki saboda tsaro" duk dariya sukayi kafin suka tashi suka tafi.




"Yawwa kinga nan yafi sirri kina Jina, itad'in y'ar NIGERIA ce, batada Baba ga tsinannen son kud'i, ke atak'aice dai da kyanta kawai take tak'ama" Shuwaiba tayi ajiyar zuciya tace "hummmnn atak'aice dai shegiya ce kenan" Khaleesat tace "kwarai ma kuwa" Shuwaiba ta tuntsire da dariya tace "ikon Allah kenan Humm" Juwaira tace "lafiya " Shuwaiba tace "lafiya Lau" haka suka cigaba da fira. Amma Kash kowa akwai abunda yake sak'awa a ranshi na yanda ze cutar da d'an uwanshi.





Zaune suke a office d'in kowa Aikin shi ya keyi, Babu me Kallon wani balle magana, zuwa can ya mik'e ya nufi k'ofar fita yana fad'in "ki taso muje" mik'ewa tayi tana d'aukar wayarta da iPad d'in Aikin ta, tabishi.


Direct wani tank'amemen gida suka nufa, tun daga waje taga escorts nata Sara musu, dagudu suka biyo su suka bud'e musu k'ofa, ko fuskarta ka kalla zaka tabbatar da gidan yayi Mata, murmushi kurum tayi tana Kallon flowers d'in gidan, ajiyar zuciya tayi ta bishi abaya, a main falon suka zauna, se kalle² take saboda Babu k'arya falon ya had'u duk da rabin kwalliyar falon flowers ne kamar Dai a office d'in shi, wannan dalilin ne yasa Sam bata gajiya da zama a office d'in, kuma duk wani office dinshi ma Haka yake, ajiyar zuciya tayi tana shak'ar daddad'an k'amshin falon, gani tayi ya tashi ya nufi wata hanya, minti kad'an segashi ya dawo hannun shi rik'e da tea cup yana sha, kusa da'ita ya koma ya k'ara zama, had'e rai tayi dan ita yunwa ma kad'ai ta isheta, dan rabonta da abinci tun jiya da rana, kallon shi tayi tace "Wai nan Ina ne" KO Kallon ta beba balle ya bata amsa, zuwa can wasu kyawawan couples suka shigo falon, mijin na rik'e da matar tashi dake fama da tsohon ciki, dukkan su fuskar su d'auke da murmushi, kusa da juna suka zauna kafin, mijin matar ya mik'ama Shureim hannu suka gaisa Yana fad'in "Barka da zuwa Yarima, ammafa Naji dad'in ganinka" Shureim yayi murmushi kafin yayi magana, matar ta sunkuya ta tab'a k'afarshi (irin d'abi'ar Indiawan nan) tace "kasamin albarka" Shureim ya dafa kanta Yana Kallon mijin cikin yaren turanci yace "Wai ita har yanzu bata dena wannan d'abi'ar ba" mijin yace "kasan Abun da wuya ta barshi da wuri, kamar yanda kaima bazaka canza Hali ba" Shureim ya nuna Sarauta yace "my first wife" sannan ya kalli Sarauta yace "wannan Abu-nawwas kenan abokina ne wannan kuma matar shice Angelina ba'india ce but know she's a Muslim" Sarauta ta kalli Angelina tayi murmushi tace "Barkanki ya jiki" Angelina tace "mukuma yanzu ai jiki dasauki saura kuma ku" Sarauta tad'anyi murmushi, nanfa aka fara had'a musu abinci na alfarma, tashi Shureim yayi shida Abu-nawwas suka fita lambu, sukuma suka barsu, Aikuwa Sarauta taji dad'in hakan sosai dan dama yunwa takeji, Aiko taci ta k'oshi, Angelina tace "mijin ki mutumin kirki ne shine yayi silar aurena da Nawwas" Sarauta tace "Uhmm" Angelina tace "bazamu manta dashi ba na iya rayuwarmu kinga ma Idan na Haifi namiji to sunansa zamu saka, Idan kuma mace ce shine ze zab'amana" Sarauta ta kalleta tana tunanin me Sir Shureim yayima mutanen nan Haka ne, kafin ta tambaya Sega su sun dawo, ya kalli Angelina yace "Kindai cika Mata ciki ko" Angelina tace "Uhmm ba laifi amma bata wani ci meyawa ba" Abu-nawwas yace "Kai Mrs. M.S yafa dace ace kin cinye komai da komai danke fa akai" tayi murmushi tace "Allah naci" Abu-nawwas yace "Mudai ah ah gaskiya kid'an k'ara" Angelina tace "ki k'ara ko kad'an ne" Shureim yaja kujerar ta yace "key tashi mutafi karsu kashemin ke da abinci" Sarauta tayi murmushi ta mik'e sukayi sallama da Angelina sannan ta tafi, Tasha turaruka a gurin Angelina, lokaci d'aya tashiga ranta, kunsan yanda kyauta tawa take.



Suna tafe a motar tace mishi "gaskiya matar nan tanada kirki sosai" Shureim yace "Angelina kenan watansu 10 da aure" Sarauta tace "Allah sarki Idan ta haihu kuwa xanje Mata" wani Kallon bada aurena yayi Mata ba ya juya, itama bata k'ara magana ba harsuka k'arasa gida, seda suka fito tace "kaga na baro files d'innan da zanyi aiki dasu gobe, bansan gida zamu zo ba" be kalleta ba yace "jeki gida" tab'e baki tayi ta juya ta nufi ciki. Wayar shi dake ringing tun d'azu ya d'auko ya d'aga.





Ta cikin wayar wata daddad'ar murya tace "Inata Kira baka d'agawa" yayi ajiyar zuciya yace "Muna tare da'ita ne shysa kuma banason ta tsargu da wani Abu" ta cikin wayar akace "uh ai bansani ba kayi hak'uri kaji" Shureim yayi murmushi yace "Laa Babu komai yakike" tace "lafiya klau, inason ganinka fa Allah duk na damu sosai" yace "karki damu *DIAMOND* inanan zuwa kinji" tace "to shikenan *GOLD* zanta jiranka Anan" yayi murmushi yace "nak'osa muyi rayuwa a tare" tayi ajiyar zuciya tace "dan yanzu hakan baze yiyuba, amma kasata ta gane kurenta kayi Mata abunda zatayi ladama mafi muni a rayuwar ta" Shureim yace "amma Diamond.." katseshi tayi dacewa "dole ne hakan ta faru bawani maganar Amma dole ne hakan ta faru dole tayi nadamar aikata komai" Shureim yace "indai zakiyi farin ciki zan aikata hakan" tace "that's my Diamond *kafin Shureim yayi magana yaji motsi a bayan shi, dasauri ya juya, a tsaye ya ganta, rass yaji gaban shi ya fad'i kardai taji abunda yace, saurin yanke wayar yayi yana cewa" ammmm lafiya... " Sarauta tace.........




*Tohfa wata

Please Login or Register in order to submit comment