Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gani duk P. A din zaka dauka shike Kawo maka su please kadena irin wannan tunanin kaji my boo" Kai ya d'aga yace "Abiey next week zan wuce KOREA" kallonshi kurum Abiey yake almost 30secs kafin yace "Kodai kaji haushi nane" da sauri ya girgiza Kai yace "Subhanallah ni awa? Ai ban Isa ba Abieyna me gareni wayeni dazan yi fushi dakai ah ah Allah ni banyi ba" murmushi Jin dad'i Abiey yayi suka wuce sama shida Ummee,



Yana nan zaune Sega PRINCESS SHUWAIBA ta shigo hannunta rik'e da wayarta tana ta fama da alkyabba, wani uban tsalle ta daka tare dayin kanshi, dasauri ya mik'e yana fad'in "what kind of nonsense is this Shuwaiba" zumb'uro baki tayi tare da cewa "am happy to see you dear" d'an had'e rai yayi yace "to thanks" Kai ta gyad'a tana me k'ara Jin wani dad'i a zuciyarta shysa take k'ara k'aunar Prince d'inta domin Sam bayada wulaqanci, kallon shi tayi tace "guest what?" ya girgiza Mata Kai tace "ka k'ara kyau sosai" tab'e baki kurum yayi Don Inda Sabo ya saba, Yana mik'ewa yace "fatan Abbu na yana lafiya" "lafiya lau" ta amsa tana cire alkyabbar ta, kafin tace "brother wae yaushe ne auranmu eyeh??" filon dake Saman kujerar gefen shi ya d'auka ya jefo mata, dariya kurum tayi Don tasan baxe tanka ba, shima girgiza Kai kurum yayi ya wuce sama dan besan doguwar magana.



*Hajja Neenah palace*

"Wai khaleesat lafiyar ki kuwa na lura cikin y'an Kwana kinnan duk kin canza ki gayamin Mike faruwa tun kafin uwar ki ta sani tazo nan ta tada hankalin kowa" Neenah ta k'arashe maganar cike da nuna damuwa, Hajja Mubina tace "gaya mata gaskiya dai Neenah gwara muyi maganin matsalar nan da kanmu kafin Abun ya kaima waccan gantalalliyar uwar taki" khaleesat ta k'ara fashewa da kuka tace "ni Babu wani Abu dazaku iya yimin gwara kurum na sanar da MY nasan ita bazata bari na kuma yin kuka ba wallahi" Hajja Jumaima tace "haba khaleesat keda kanki kinsani koni uwar ki bata ragamin dana haifeta balle kuma mutanen gidan Dan Allah kiwa Allah karki sanar mata ki gaya mana in sha Allah zamuyi miki maganin ko miye kinji" khaleesat na kallonsu tace " sanin kanku ne ina mutuk'ar k'aunar Prince Shureim amma kowa yayi burus da lamarin nan kudubi waccan balbelar harta kwaso jiki tazo daga Jin ya dawo kuma kunsan itama ZUWAIRA tana nan zuwa ko gaskiya ni bazan iya ba Haka kawai bak'in ciki ya kasheni gwara na sanar da MY kurum "ta k'arashe tana danna wayarta, da sauri Hajja Jumaima ta amshe wayar tace" daman Wai Akan tsinannan yaron nanne Kai amma Shureim anyi asarar haihuwa ki barni dashi dan ubanshi dakanshi ze nemeki " Hajja Neenah da Hajja Mubina duk tab'e baki sukai suka kama kansu.


*QUWAIZ GARDEN JIDDA*


Samarine guda biyar a zaune a Saman k'ayatattun kujeri ancika teburin gaban su da abubuwa kamar juice, giya, fruit, nama dadai sauran su kowa da abunda yake ci, gaba d'ayan su bazasu wuce 27 a shekaru ba da kagansu kaga y'an gata da kud'i suka ratsa, NABIL shine wanda ya fara magana, yace "ammmm JAMEEL kuna ganin kuwa yarinyar nan y'ar Korea zatayi mana aiki yanda muke so" wanda aka Kira da Jameel yace "oho Kadai ga yanda aiki ya kasance mund'auko yar kashmir, India, Kuwait, Ghana, Congo, Jamaica, America, Ukraine duk basuyi aiki ba kud'in mu nata tafiya a banza wasu sonshi suke farawa wasu kuma suce ai mutumin kirkine bazasu cutar dashi ba wasu kuma ya koresu, ni wallahi jikina duk yayi Sanyi gani Nike kamar itama y'ar Korean nan kawai mu hak'ura koba Haka ba guys" FAWAZ yace "Nadai inace Anan har shawara na Baku Akan mud'auko y'ar NIGERIA itace kurum zatayi mana Aikin nan daidai gwargwado amma Babu wanda ya goyi bayana hasalima kai Nabil ai cewa kayi sud'in basu San komaiba se rayuwar wahala, to Allah matan k'asarnan y'an ta addane zamu samu komai a gurin su " JABEER yace" wannan Haka yake Fawax gaskiya abunda yadace muyi kenan koya kuka gani " se sannan Khameel yace" hmm kubari mugani Idan ta Korean nan batayi komai ba harnan da sati uku aise muje Nigeria mugani ko da gaske Fawax yake "haka duk sukayi Na'am da wannan shawarar, suka cigaba da party su.

*Muhammad Shureim palace*


Labari kurum take bashi da nune (yaren kurame) shima kuma ya maida hankali sosai kamar me d'aukar darasi, seda ta Kai ayah sannan take cemishi" yau kamar yanayinka yad'an sauya yayana " murmushi kurum yayi Mata Yana Mata nuni da" karta damu lafiyar shi k'alau " haka suka cigaba da fira har zuwa sanda Ummee tazo suka d'aura da'ita,
Cike da nishadi suke firar har duka yaran nata sukayi barci daga bisani ta raka Shubai'a d'akinta ta dawo tayima d'an nata addua ta wuce makwancinta.
Safiya ta gari gimbiya da Yarima.......




*KATSINA*


"wash Allah sannu Ummah Kinga nagama tuyar wainannan da kyar Allah" Ummah tace "uhmm ai kina k'ok'arima kwanannan kinga tunda na fara rashin lafiyar nan fa ke keyin komai ai gaskiya Nagode" Sarauta tayi murmushi tace "Ummah ta kenan ki kwantar da hankalin ki kwanannan zamuyi kud'i muma kema ki huta kurum gaba d'aya" Ummah tayi murmushi Don indai shirmen Sarauta ne AKAN KUDI Babu wanda bata sani ba tace "to Allah dai yanunamin kafin na mutu" Sarauta tace "tab Lallai toke ummah waye yace Zaki mutu ma ai kwanannan zamu koma billionaires" Ummah tayi murmushi tana k'ara jinjina ma shirmen Sarauta tace "to Kedai kidage ki cika ma mahaifin ki burinshi na ganin kinyi karatu kinji" zumb'uro baki tayi kafin tayi magana wani yaro ya shigo yace "Ance wae Sarauta taje Inji Deen" Sarauta ta had'e rai tace "Bana nan" yaron ya juya ze fita Ummah tace "Kai kace tana zuwa" Kai yaron ya gyad'a ya fice, Ummah takalleta tace " bakidai dena wulak'anta mutane ba ko Sarauta Wai Dan...." dasauri Sarauta ta katse ta da cewa "ke nifa ba gurina akazo ba shams ne saurayin Maryam yanzu haka fad'a sukayi shysa kikaga yazo ni wallahi ko kad'an bana son soyayyar nan tasu Allah mtsww" ta k'arashe da dogon tsaki, mik'ewa tayi ta d'auki Hijab d'inta ta fita.

Yana jingine a jikin motar ta k'araso, ba yabo ba fallasa suka gaisa, kafin ya Sosa k'eyarshi yace "ammmmm dan Allah kawarmu temakona nike son kiyi wallahi k'auye mukaje nida alhaji to ranar da muka tafi bamuyi waya da Maryam ba kuma kinga k'auyen ba nepa haka naita fama da rashin charge kwananmu biyu a can d'in, to kinga yaud'in nan muka dawo naje gidan su na aika ankirata tana fitowa taga nine kurum seta koma kuma nakira tak'i d'auka " Sarauta tayi murmushi tace" toni yanzu me zanmaka? " yace " kinga ita bata San da wannan bayanin ba please shi Zaki temakamin kiyi Mata atayani neman afuwa " ajiyar zuciya tayi tace " Tohm shikenan zan Mata magana Nagode se anjima " daga haka ta koma gida

Sarauta nasa baki a maganar kamae yakoma normal.

Haka rayuwa tacigaba da tafiya Sarauta Nayi y'an k'ananan abubuwa domin samun kud'i kamar yin note, assignments, Sato questions paper, tracking, dadai sauran su, duk intasamu kud'i cema Ummah take ai tare suka samu da Maryam, ita kuma Maryam ta'iya kare k'awarta........


KARKU MANTA AKAN KUDI K'IRK'IRARREN LABARI DA NAYI SHI DOMIN FAD'AKARWA DAKUMA NISHAD'ANTARWA TAKUCE DAI ME NISHAD'ANTAR DAKU KULLUM DA KO YAUSHE

@ *SHERNTEE GHAYU* 🥰🥰





@07064706167


💵 💴 *AKAN KUDI* 💵 💴

(A poor lady story)

.......... 25th April, 2023

*Story & writing*
*By*

@ *sherntee ghayu*🥰🥰

*Na sadaukar da wannan page d'in xuwa ga jaruma ta me k'arfafani a Koda yaushe, Ina mik'o sakon gaisuwata a gareki LATEEFAT*


🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* 📚

🅿........ 005 & 006


*Bayan wata hud'u*

*JIDDA*

**Yarima palace**


Tsaye take a gabanshi idanunta jawur tana hawaye tana bayani cikin harshen(yare) turanci, kallonta yayi kafin yace "ki zab'a kodai kiyi kukan ko kuma kiyi shuru kiyi min bayanin komai" hawayenta ta fara gogewa tana cewa "wallahi ko sau d'aya banyi abunda ze cutar da kaiba kuma Koda sukace duk sirrin kasuwancin ka suke son sani Babu abunda na tab'a sanar dasu hasalima ni Ina fara ganinka Naji soyayyarka a raina taya zan cutar da abunda Nike so dan Allah sir kayi hak'uri karka sanar musu wallahi kasheni zasuyi, sunce muddin aka samu matsala zanga abunda ze faru kamin a fuwa " ajiyar zuciya yayi ya kalleta fuskar shi cike da annuri kamar Koda yaushe yace" nawa suka baki " tana share hawayenta yace" Caro 5 " yayi ajiyar numfashi yace" zan baki Caro 10 kije na koreki Idan kin sanar musu nasan komai ruwanki Idan ma baki sanar musu ba ruwanki " Yana kaiwa nan ya juya da nufin tafiya, da sauri ta rik'e k'afarshi tana fadin" ah ah please karka koreni Ina son ka inason zama dakai please " juyowa yayi yace" please Dam-bi stopped it " daga Haka ya juya ya fita, Anan Dam-bi tasa kuka, a k'ofar falon ya had'u da Shubai'a, kallon shi take tana lek'en Dam-bi, da hannu tayi mai tambayar me akaima Dam-bi, murmushi yayi yai mata side hug yace" karki damu muje na baki labari " ya k'arashe Yana juyawa da'ita, juyowa tayi ta kuma kallon Dam-bi zatayi magana yace" muje yau farfesun kifi Princess zatayi min" daga haka ya jata suka sauka, (Dama d'abi'ar shice duk Idan Yana da P. A Toh ko Ina tare suke tafiya har gida tare suke zuwa, Shubai'a itace ke zama abokiyar firar su Idan bata had'u da yar wulaqanci, shiyyasa kowa na gidan ke sanin P. A)

Hak'ik'a ran su Jameel ba k'aramin b'aci yayi ba, sunyi mata tambayar duniya Akan metayi mishi ya koreta kodai ta sanar mishi da gaskiya ne, amma Sam tak'i cewa komai cewa tayi Haka kurum ya koreta, ba yanda zasuyi shysa suka kyaleta ta koma k'asarta.

*Waye Yarima Muhammad Shureim*


*SARKI JUNAID MALEEK* ya kasance shine sarkin masarautar JIDDA, matan shi hud'u, a lokacin daya auri matar shi ta farko Wato MARYAM dasuke Kira da MAMU Sam Sarki beyi niyar k'ara aure ba amma kasantuwar shekarunsu shidda da aure basu haihu ba yasa aka takuramai Akan seya k'ara aure, Anan ya auri matar shi ta biyu Wato ANEENAH dasuke Kira da NEENAH, Sam Neenah batazo da fitina ba zaman lafiya suke ita da Mamu, bazaka tab'a cewa kishi suke ba, Sarauniya Mamu ta d'auki Neenah tamkar k'anwarta. Haka rayuwar ta cigaba da tafiya itama Neenah har lokacin bata haihuba, hakan ba k'aramin tada hankalin sarki JUNAID yayi ba, shysa yasa aka samo mishi Mata biyu, a lokaci d'aya ya auresu, HAJJA MUBEENA DA HAJJA JUMAIMA suma shekarar su biyu Babu wacce ta haihu, a wannan lokacin ba iya sarki ba har matan shi hankalin su ya tashi anfara tunanin ko shine be haihuwa, Awata ranar alhamis ne matan sarki suka tashi da ciwo da farko hankalin sarki ya tashi amma daga baya da aka sanar mishi da su Duka hud'un ciki garesu ba k'aramin murna yayi ba gaba d'aya masarautar Sunyi murna sosai.

Mamu itace ta fara haihuwa d'anta namiji kyaklyawan gaske aranar suna yaci Sunan MUHAMMAD LADTEEF suna kiranshi da Zabvier, daga nan se Neenah ta haihu d'iya mace ta Haifa, tsabar son da takema Mamu yasa tasa ma yarinyar sunanta Aslam suke kiranta dashi, HAJJA MUBEENA DA HAJJA JUMAIMA kuwa gaba d'aya y'ay'ansu Babu me rai a ciki Haka yasa musu bakin ciki a ransu Dama su tun fil azal basa shiri da Mamu domin sun tsaneta, ita kuwa tun zuwan su gidan ma ba lafiya gareta ba amma duk da Haka tana basu kulawa daidai gwargwado, dama Neenah itake tare Mata wani lokacin Dan basuba har sarki Yana d'an shakkarta domin bata da kyau shysa su Hajja Mubeena ke shakkarta sosai.


Haka har bayan wani lokaci Allah ya bama Hajja jumaima haihuwa, d'iya mace ta Haifa wacce taci Sunan SIRAYYA, tun Sirayya na yarinya bataji, Akan abunda take so bata d'aga k'afa ko Hajja jumaima bata d'aga ma k'afa balle sauran matan gidan, amma a Haka kowa ke nuna Mata soyayya musamman Zabvier dake mutik'ar k'aunarta duk da rashin kunyar da take mishi, a cikin y'an kwanakin ne Aslam ta mutu, Neenah tayi kuka sosai a Kan mutuwar d'iyar tata.
Bayan wani d'an lokaci Allah ya bata wani cikin, tayi murna sosai ba d'an kad'an ba, bayan wata tara ta Haifi kyakkyawar d'iyarta me suna MADINATUL MUNAWWARA suna kiranta da NUR tunda aka Haifi Nur Zabvier yaji yayi k'anwa, kullum suna tare kusan ma shiyake rainonta.

Ganin sarki bashi da y'ay'a maza yasa k'anin sa yabashi d'anshi MUHAMMAD SHUREIM suna kiranki da SARAUTA, soyayya da k'auna ce me girma ta shiga tsakanin Zabvier da Sarauta, son juna suke sosai yanda kasan y'an biyu Haka suka zama, sosai Sarauta ke nuna ma Nur kulawa domin ba k'aramin k'aunarta yake ba Yana matuk'ar sonta.

A ta d'ayan bangaren kuma su Hajja Mubeena sunata shirin yanda zasuyi suga bayan Sarauta saboda suna ganin very soon ze fisu matsayi a gurin sarki, gashi kuma Sirayya tana matuk'ar k'aunar shi amma shi Sam hakan baya gaban shi domin Nur ita Kadai ce farin cikin shi kuma gimbiyar shi hakan ba k'aramin bak'anta ma Sirayya yake ba, shysa mahaifiyarta tad'au aniyar gwara kowa ya rasa da d'iyarta ta rasa hakan shysa suka had'a k'arfi da k'arfe gurin ganin sun samar ma kansu mafita,
TA kanas suka shirya sukaje gurin wata bokanya Anan Abu Dhabi, kurciya suka sa a kayima Sarauta, Aiko ko Kwana biyu ba ak'ara ba aka nemi Sarauta aka rasa wanda hakan shine silar fara gaba tsakanin sarki da d'an uwanshi Omar sarki Kuwait.

*Bayan wasu shekaru*

Yaran sarki junaid shidda, Mamu nada d'a d'aya LADTEEF, se Hajja jumaima yara biyu SIRAYYA, YUSUF, se Hajja Neenah guda biyu, NUR da NI'IMATU se Hajja MUBEENA SAFIYATU.

Tuni Hajja Neenah ta Bama Mamu kyautar Nur, saboda Nur yarinya ce me sanyin Hali da kwallafa rai Akan Abu, itako Neenah Sam bata son Haka shysa ta d'au keta kacokam taba Ladteef da mamun shi ita, Aiko a hannun Ladteef ta tashi shine cinta shanta kula da ita kukanta dariyarta da komai nata domin ita Mamu ma batada lafiya tun bayan haihuwar Zabvier, Safiyatu ta kasance y'ar so kuma y'ar lelen mamanta domin duk wani buri na Neenah Akan safiyatu yake,

Hakan take ma a b'angaren jumaima se abunda y'ay'anta ke so take musu, juyata Sirayya take kamar itace uwar, Dan Dama ita Babu me shiga harkarta yanzu seta tada hankalin kowa, Yusuf kuwa babu ruwanshi ko ayi ko kar ayi duk d'aya yake a gurin shi,

Bayan wani lokacine sarki Omar Yazoo ma da sarki Ladteef da buk'atar shi Akan ya had'a yarshi Nur da d'anshi TAHEER aure, ganin hakan kamar shine ze kawo maslaha tsakanin su yasashi amuncewa, Ladteef ya samu da maganar, shima Ladteef yayi murna sosai dan Dama yanama Taheer kallon amininshi Sarauta, yaje yasamu abar k'aunar shi kuma k'anwarshi da maganar a zahiri ta amince kuma ta nuna Babu yanda za'a yi ta guji d'an uwan Sarauta amma a bad'ini ta Kasa amuncewa da abunda yake fad'i, bata son Taheer Sarauta take so, to Akan me ne za'a takuramata aurenshi, gaskiya yaya kayi hak'uri amma bazan iya auren Taheer ba,

Sanda Neenah tasamu labari fatan alkhairi kurum tayi musu tunda ba tagaban goshinta bace.
Cike da murna aka soma shirye²n bikinsu, ranar d'aurin aure kurum aka nemi amarya aka rasa hankali ya tashi kowa ya rud'e amma saka makon ganin wasik'ar da amarya ta Bari yasa kowa ya kwantar da hankalin shi, wasik'a ce kamar haka:
Yayana ka yafemin kayi mini komai na rayuwar duniyar nan Kaine uwata kuma Kaine ubana banson k'in amincewa ne saboda gudun fushin ka amma kayi hakuri na tafi Idan da rabon mu gana zan dawo, ka yafemin yayana Ina k'aunar ka)

Tundaga wannan lokacin Ladteef yad'auki gaba, tsana, da kuma fushi ya d'aura Akan Nur.
Shikuma Taheer tun daga ranar yake ciwo kuma yace Babu shi Babu aure har k'arashen rayuwar shi, Neenah taji ciwon guduwar d'iyarta amma ya zatayi Babu shysa ta hak'ura.

*Bayan wasu shekaru*

Allah yayima sarki junaid rasuwa inda d'anshi Ladteef yaci gaba da mulkar k'asar JIDDA, gaba d'aya k'annanshi Sunyi aure kuma kowa ta haihu, Sirayya nada y'ay'a biyu, mijin ta na farko da taso kamar ranta anan JIDDA yake da zama, haihuwar su d'aya Allah yayi mishi rasuwa tayi kuka kamar ta mutu, shysa ta d'auki soyayyar duniya ta d'aura ma d'iyar shi khaleesat wanda a hannun kakarta jumaima ta tashi duk wanda ya tab'a khaleesat tofa ranar bashi da baccin lafiya, Haka har Allah ya fiddo Mata miji tayi aure, dakyar a kasamu tabar khaleesat Anan tabi mijin ta Faris, acan ta Haifi d'anta Nabil wanda shima yana tare da y'an uwanshi Anan JIDDA.
Se Yusuf daya rasu bayan ya Haifi d'anshi Khameel, wannan dalilin ne yasa sarki Ladteef yad'auki soyayyar duniya ya d'aura ma Khameel domin Yana matuk'ar son Yusuf.
Se NI'IMATU yaranta uku, jameel, Shuwaiba da JABEER
Se safiyatu yara biyu, zuwaira da fawaz.

Se sarki Ladteef wanda seda matar shi tayi wabi(matattu) guda uku wanda duk sharrin su Hajja ne ke kashe Yaran, tun Muhammad Shureim na ciki suka so ganin bayanshi amma Ina seda Allah ya kawoshi duniya, Babu irin wahalar da be shaba ahannun y'an uwan mahaifin shi da kakan ninshi amma saboda yaro ne me sirri shysa Babu wanda ya tab'a sanar mawa, a hakan aka Haifi k'anwarshi, dakyar sarki ya amince aka saka Mata Sunan k'anwarshi shima seda Ummee ta dage sosai sannan MADINATUL MUNAWWARA SUNA KIRANTA DA SHUBAI'A, Shubai'a yarinya ce me d'an banzan surutu gason y'an uwanta, bata da wata na Kasa,
Wata rana taje b'angaren su Hajja Mubeena taji suna fira da jikokin su Akan yanda suka Kora Sarauta Haka xasu Kora Shureim kuma sesun kwace gaba d'aya dukiyar daya tara, Shubai'a taji tsoro sosai hankalin ta ya tashi tsabar rud'ewa ce tasata fashewa da kuka ta wuce b'angaren su, tsaf suka ganta hakan ne yasa sukaje gurin bokanyar su sukasa ta tura aljani ya danne ma Shubai'a harshe kuma ya goge Mata tunani, duk randa a sirin nan ya karye zata tuna komai da komai, sarki da Shureim sun nemi magani Amman a Banza Haka suka gaji suka hak'ura.

Shureim babban likita ne, kuma sannan business man, mutum ne me neman na kanshi tun Yana yaro danshi Sam be yarda da wata Sarauta ba, Sam ba a gaban iyayen shi ya tashi ba a k'arashen turai ya tashi.
Khaleesat, shuwaiba, zuwaira duk jirgi d'aya ya kwasosu gaba d'ayansu Shureim suke so, dasuka fahimci hakan se suka Dena ma juna magana kallon Banza kurum ke had'asu gashi kuma kowa Kakarshi tamai alkawarin seya samu.
Mamu nanan a Raye tun bayan rasuwar sarkinta ciwon paralysis ya kamata komai yimata ake, tana can k'arshen masarautar a wani sashe na daban, da farko sarki Ladteef da ahalinshi sune ke kula da'ita kafin tunanin su ya gushe Akan ta ko sunanta basa fad'a balle kuma ita. Tana can amintacciyar baiwarta ke d'awainiya da ita.

Fawax, Khameel, jameel, Nabil, jabeer Babu abunda suke hari face narkakkun kud'in Yarima Shureim ba wanda shi kanshi besan adadin su ba, companies, hospitals, industries, banks, dadai sauransu, wannan shine abunda suke hari akoda yaushe.

Wannan shine tak'aitaccen labarin Yarima Muhammad Shureim

*cigaban labarin*.....

KARKU MANTA LABARIN AKAN KUDI K'IRK'IRARREN LABARI NE DANAYI SHI DOMIN NISHAD'ANTARWA, TUNATARWA DAKUMA FAD'AKARWA NICE TAKU ME NISHAD'ANTAR DAKU A KULLUM DA KO YAUSHE

@ *SHERNTEE GHAYU* 🥰🥰

@07064706167


💵 💴 **AKAN KUDI**💵 💴

(A poor lady story)

....... 25th April, 2023

Story & writing
By

@**Sherntee Ghayu**


🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* 📚


👑 J. W. A. 👑

🅿..... 007 & 008

~Cigaban labari~

*King's Ladteef palace*

Had'e rai sosai sarki yayi Yana kallon shi, rai a d'an b'ace yace "yanzu abunda kayi ka kyauta kenan dubi duk ka fad'a Anya ma kana cin abinci kuwa?" ya k'arashe yana tab'a wuyanshi, Khameel ya kuma Had'e rai yace "Abieyna wallahi banason karatun nan duk ya bi ya isheni da anfara exam hankali na ke tashi Allah banaso" Abiey yayi murmushi yace "my son kenan Toh yanzu fad'a min inba kayi karatu ba me zakayi kodai k'asar Moroccon ce baka so" k'ara shagwab'e fuska yayi yace "Allah Abiey Bana so ni kawai a barni" Abiey yace " to a Barka hakanan kake nufi kome" Khameel yace "ahh ahh, to Wae base mutafi tare da Prince ba Koda a companies d'inshi se in dunga temaka mishi ko" Abiey yayi murmushi yace "my son kana son yayan nan naka da yawa fa kaidai baka son ya wahala ko kad'an ko" Khameel yace "ai dole nane na so d'an uwana kuma na tausaya mishi, Toh amma shi baya gani kullum k'ara nisanta kanshi dani yake yi, Abiey yafa k'ara korar P. A d'inshi, zanmai alfarma d'aya ne kurum zan kuma Nemo mishi wata amma da zarar ya koreta fa to sedai Wahala ta kasheshi babu ruwana" Abiey yace "what itama ya koreta kake nufi, my son Dallah ka rabu dashi waye shi d'in me kake nema a gurinshi shi baze tab'a ganin ka kyauta mishi ba, hmm ka rabu dashi kurum shi ya sani Aikin wofi kurum" Khameel yace "Abiey na kar ranka ya b'aci mana, shifa d'an uwana ne baxan so wahalar Shiba, zan kuma Nemo mishi me hankalin dazata iya zama dashi kuma ma kaga Nima zan dunga temaka mishi ta b'angaren companies d'inshi tunda Dai kaga ni ba likita bane ko" Abiey ya shafa kanshi yace "Allah ya albarkaci rayuwar ka

Please Login or Register in order to submit comment