Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hanna yensa waje ɗaya






Comment and share
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲






By ZAINAB AHMED YUSUF






AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA







PAGE 8️⃣1️⃣⏮️8️⃣2️⃣

Bismillahir rahmanurrahim











Wanke wanke take a kitchen amma gaba ɗaya hankalinta baya kan aikin da take tunanine kala kala acikin kwakwalwar ta shin wai ita menene ma abinda takewa Raihan dayakesa su suna yawan samun sabani idan ada babu soyayyah ai yanzu sun tabbatarwa da junansu su masoyane na hakika

Jinjina kai tayi afili tace lallai akwai lauje cikin naɗi wannan al amarin ba banzaba gara ta tsaya tasan metake tunda taga mutanan nan suna haka to tabbas akwai abinda Ame hauwa take buri dangane da Raihan da YASIR hakan yasa itama tasu ta shafeta

Watakil dukiyarsu ce to kuma idan duniya ce ai Ame hauwa tanada Kuɗi ko duba da yanayin yadda kowa na family hause ɗinnan ke wadaka da kuɗi babu yaro babu babbah

Maryam jitai kanta ya fara yi mata ciwo dan ta gaji da zancen zuci , karamin tsaki taja tace gara na fuskanci abinda yake gabana

Ta noke kafaɗa tana cigaba da aikinta




***


Ommu Amal tasa islam agaba cikin bacin rai da bal balin masifa take cewa " mekuke kullawa keda Ame hauwa wane shiri kuke dan nayi imanin wannan amintar taku bata banzaba ???,

Shiru islam tayi tana latsa latsen wayarta hakan ya fisata ommu Amal jitai zuciyar ta kamar ta buga dan bacin rai ,islam batai auneba taji omminta ta fizgi wayar tata tabuga da bango ta taka , dan danan waya tayi kwatsa kwatsa

Mikewa islam tayi cikin hayayya kowa tace , " akan me zaki fasamin wayata ?, ta faɗa tana zazzarowa uwar tata ido da sukai jajir dan bakin cikin tarwatsa mata waya

Mamaki ne ya ishi ommu Amal ai kuwa ta ɗauke islam da kyawawan maruka guda biyu a jere , dafe kunci islam tayi tana gunjin kuka ta fice daga gidan

Kai tsaye gidan Ame hauwa ta nufa tana zuwa ta faɗa jikin ta tana gursheken kuka

Cike da mamaki Ame hauwa ta ɗago kan islam taga shatun yatsu sunyi jajir cikin fusata da bacin rai na gan gan tace , " waya mareki haka ji yadda gurin yayi jajir yatsu sun futo ?,

Cikin muryar kuka islam ta labarta mata abunda yafaru , wani sanyine da farin ciki ya mamaye zuciyar Ame hauwa afili kuma saitace , " wai ni kam mai yake damun ommu Amal ne kahaifi ɗa acikinka amma kana masa bakin ciki da abinda yakeso ai kuwa indai nice bazan daina baki gudummuwa wajen cikar burinkiba dole ta hakura tabarki kiyi yadda kikeso ,

Nan tashiga rarrashinta yasmin tana kallonsu a gefe tana mamakin shu,omanci irinna Ame hauwa, saida islam ta daina kukan sannan Ame hauwa ta fara magana

" yauwa ya ake ciki da zancen Raihan wace nasara muka samu ,

" kamar yadda muka tsara komai ya tafi adai dai a wancen ranar naje har office ɗinsa nasa akaimin izinin ganinsa yasha mamaki dayaga naje har kanfanin su ni kuma sainai amfani da kissata ta mata kamar dai yadda kikaimin bayani cikin rarrashi da ladabi da biyayyah haka na bashi hakuri akan abinda yafaru tsakanina da shi na cewa danayi ina sansa abinda yafi bani mamaki wlh sai naga duk yanzu ya rage zafin rai bai wani nuna fushiba yace ya hakuri shine yake tambayata meyasa bazan bashi hakurin agidaba saina zo office anan ne nake cemasa motatace ta lalace shine na biyo idan zai tafi gida ya tafi tani

Yana jin haka yace naje waje najira su tashi haka naita jira har yamma sannan yazo muka tafi a hanyane kuma nake masa karyar nasamu mijin aure dan ya daɗa gamsuwa da yanzu bana sansa ,, hmmm nan islam ta numfasa ta kara da faɗin " in takaice miki zance Ame daga haka nasamu damar danasan yadda nayi nake karya kullum inna fita da sunan banida mota nake tsayawa a hanyarsa yana ragomin hanya har sau uku kuma nasan matarsa zata ganmu dan rannan da asuba na kirashi bayan naga futarsa masallaci shine shegiyar ta ɗaga na gaggaya mata magana


Wata dariyar farin ciki Ame hauwa tayi tana tafa hannu tace " aikinki yayi kyau da irinku nakesan har kalla sam islam bakida weak a lamuran ki good mun samu babbar opportunity Abandoned life Raihan and wife
Sai kuma shiri na gaba ya ake ciki akan maganar cikin da zakiyi ,

Sunkuyar da kai islam tayi tana tunani cen ta ɗago tana kallon Ame hauwa tace , " akwai wani mutum mai kuɗi dattijo da muka haɗu dashi a facebook shima balarabene yacemun nashirya mana haɗuwa konawane zai biyani to amma , sai tayi shiru da zancen a zahirin gaskiya islam tana kokarin kare mutumcinta bata taba sex da kowaba tunda take a rayuwarta tana jin tsoran hakan batare da aureba ... Keee taji Ame hauwa ta daga mata tsawa saida hanjin cikinta ya kaɗa

" yanzufa nake yabanki kuma sai kinuna tsoro mai kike nufi to bari kije idan har kika kasa samo cikin shegennan babu yadda zaki ki mallaki Raihan gashi mun fara wining tun yanzu kinanena ki rusawa kanki lissafi yanzu a kadamin da ake a gidannan kowa ya shaida ya ganki da Raihan a mota kuna dawowa dan haka babu yadda za ai idan kince yamiki ciki suki yarda tunda sungani duk ƴan matan gidannan da ke yake yawa

Wani kwarin gyaiwa islam ta kara samu tace , " ai kuwa yau ɗinnan zamu haɗu da mutumimnan bari naje gida na ɗau layina nasa akaramar wayata dama inada number sa na kirasa , " yauwa kaji ƴar gari kokefa



***


A wajen su FERAS kuwa tafiyar aisha keda wuya yaja matarsa jikinsa yana lallashi

Cikin muryar raɗa yace mata , " jiya mai yasa baki bari nasamu ladan gyaraki da kainaba sai kika gudu kika nunawa su shaikh wlh dana gansu naji kunya sosai , ɗan ya tsuna fuska tayi dan bataso taji ya riketa batace masa komai ba wasa kawai take da yatsun hannun ta

" yakamata kafin ki tafi kizo na nuna miki part ɗinki dakuma irin abinda aka tanadar miki , " aa basaina ganiba gara idan ankawoni nashiga gaba ɗaya hakan zaifimin basaina koma gidaba nazo ina tunanin gidana , " hakanma yayi to amma ke kina ganin yaushe su yaya mu,aruf zasu gama fishin su kawomin matata dan wlh ba karamar cutuwa nakeba , " ai kaine bakaje ka basu hakuriba

Katseta yayi da cewa , " waya faɗa miki banjeba ai naje harna gaji da ban hakuri sai dai acemin wai sunyi binkike toni narasa maizasu buncuko wanda ya wuce abinda suka gani , yakarashe maganar yana mai rike hannun datake wasa dashi yashiga shafa tattausar fatar hannunta yanajin wani irin yanayi a jikinsa tundaga saman kansa har kasan kafarsa

Itama bassu idantane yafara kaɗawa take ta buɗe baki zatai magana sai taji kasala ta saukar mata muryar tatama da wani salo mai cike da sauyin yanayi tafita , " ahhh hannu nah , ɗago manyan idonsa yayi dasuka chanza ya sakar mata tattausan murmushin da yake kara futo da asalin kyau da haɗuwarsa cikekkiyar gashin girarsa yaɗaga mata yana mai langabe kai ya kai bakinsa daidai kunnan ta yana cewa , " baby kibari muhuta kansudawo,

Ayanayin yadda iskar bakinshi ta shiga kunnanta yasata jin wani zarrrrr yarrrrrr da sauri ta dunkule hannunta , kissing ɗinta yafarayi tundaga saman goshinta da kuma tunta saida yazo daidai labban ta sannan ya tsaya ta yadda suke shakar numfashin juna cike da kauna a hankali ya karasa haɗe labban nasu

Dan sanyi sanyi taji alebansa wanda hakan yakuma sata shiga wani sabon salon dayasata ɗora hannunta a faffaɗan kirjinsa shikuma ya zura harshensa yana mata wani irin shu,umin kiss mai matukar gigitarwa

Numfashinta taji yafara sama sama tana janshi da kyar dan sha,awace ta taso mata ka in da na in

Nan tabiye masa suka dunga wasanni da junansu karshema ya ɗauketa chak suka shige ɗakin saukar baki dake cikin part din shaikh

Ayacce bassu takejin daɗin romantic ɗin dayake mata shaf saita manta dazafin sex ta buɗe masa kafa sosai saida ya soma aikawa tagane shayi ruwane shikam ba tausayi saida yabiya bukatarsa da kansa yayi musu wanka ya gasa matarsa sosai sannan sukai sallah ita ta kwanta shikuma yafice daga part ɗin

Bayan sallar magriba su jawahir suka dawo sunata kwala kira amma bassu taki fitowa tana daga bakin kofar ɗaki daga nan take musu sannu da zuwa

Karasawa kusa da ita jawahir tayi tace , " yauwa sister zubomana abinci yau munyi yawa sosai wlh , to tace taja kafarta a hankali take takawa tanajin wani zugi da radaɗi na baibayeta harta haɗo kayan abincin ta fara jerawa

Shaikh yatafi masallaci jawahir ce kawai ta kurawa kanwar tata ido saida ta gama kawo abuncin tazauna sannan jawahir ta lura da gashin kan BASSUNA a jike yake dan danan zarginta ya tabbata taɗan yi murmushi tace , " yau gogan yazo ne , saurin kallonta bassuna tayi tace , " wa kenan

" ƴar rainin waye waye zaizo daya wuce mijinki gaskiya FERAS anyi ɗan naci sannu zakisham mafa wlh haka suke , ta karasa maganar tana tuntsirewa da dariya ta kai jus bakinta tanasha

Kasa magana BASSUNA tayi dan kunya da kanta ta jawo musu wata hirar dan abar wannan zancen



***
Gidan Amal

Zaune YASIR yake yana kallo a parlor cikin kwanciyar hankali abinsa

Fitowa Amal tayi daga bedroom sanye da wasu kananan kaya riga da wando wadda rigar a iya hakarkarinta ta tsaya cibiya a waje wando kuwa ko rabin cinyarta bai kaiba ta ware kyakkyawan gashin kanta ya sauka agadon bayanta ga kamshi dayacika gurin na daddaɗan turare mai jan hankali

Sakin baki YASIR yayi galala yana kwallonta cikin wani salo take taku wanda yasa jikinta yake rawa habawa YASIR mikewa tsaye yayi yana murmushi, tana karasowa ta faɗa jikinsa ta rungumeshi

Lumshe ido yayi yana shafar bayenta tunani yake a zuciyar sa gaskiya indai haka aure yake akwai daɗi yanzu sam bama yasan fita mashaya ko wajen matan banza dan duk abinda yakeso yana samu awajen Amal hakan ne yasashi yanzu ya rage shan giya indai yana gida hakura yake da ita yaja matarshi jiki yayi abinda yakeso dan ta musamman ce

YASIR zama yayi a kan kujerar Amal ma ta zauna akan cinyarsa tana murmushi, hannu yasa ya zakayo da hanna yensa ta kugunta ya riketa gam ajikinsa yana shakar daddaɗan kamshinta yana sauke sassanyar ajiyar zuciya

Murmushin samun nasara Amal tayi azuciyarta tana daɗa yiwa Allah godiya daya cika mata burinta yanzu mijinta baya wani hantarar ta dukda bai dai na abinda yakeba amma ya rage dan har hira suke hakan yasa tafara jinshi a zuciyarta takanji farin ciki a duk lokacin dayake tare da ita kuma takan shiga damuwa alokacin dayayi nesa da gida

ajiyar zuciya tasauke cikin kasa lalliyar murya tace , " yayah na yau kaine kake kallo baka jirani nazo munyiba ??, ta karasa maganar tata tana langabar da kai ta sigar rarrashi da shagwaba , wani murmushi yasakar mata yana shafa kirjinta yace , " sorry baby ai nayi zatan wani aikin kikene shiyasa amma fa gaskiya baby na kinyi kyau kinganki kuwa kamar wata baturiya , rufe fiskarta tayi da tafin hannunta alamar taji kunya

" Allah da gaske nake baby ni yau bama zanje ko inaba wlh saboda wannan wanka ina matukat so naga mace da wannan shigar sai kuma naga da kikayi kin kere ko wacce mace kyau a duniya , sai kuma yayi kasa da murya cikin raɗa yace , " kin hadu baby taciki da waje ke mai kyauce kuma ta musamman inajin daɗin zamah dake ,

Haba wani farincikine ya lullube Amal tayi wani farrrrr da ido shikuwa wani abu yaji akasan zuciyar sa na kaunarta yanzu komai nata burgeshi yake gashi uwa uba yanzu ta kware wajen iya sarrafa banana tasashi yaji tamkar ya kwala ihu








Comment
And share
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲





AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA






STORY AND WRITING by ZAINAB AHMED YUSUF








PAGE 8️⃣3️⃣⏮️8️⃣4️⃣

Bismillahir rahmanurrahim










Zaune take a saman lallausar cinyarsa tana wasa da gashin gyemunsa tahanyar kwatan ta yimasa kitso

Shikuma yana shafa cikinta hirar soyayyah mai daɗi suke a tsakaninsu cike da kaunar juna a gefe guda kuma sautin kiɗane ke tashi saffah saffa inda sukasa wakar soyayyah ta turanci wanda haɗakar shahararrun mawakan NIGERIA suka yita ( Camidoh sugarcane )

Wanni irin kallon kauna sukewa junansu cikin shagwaba maryam tace , " hubby sonake katashi kamin rawa , kiss yayi mata akumatu yace saidai kitashi muyi , baijira tacewarta ba ya mike tsaye ya mikar da ita suka sarkafe hannu irin na turawa sukafara rawa cike da nishaɗi ita da ɗan kyakkyawan mijinta

Sun jima a haka kowanne murmushi yake sun shagala da kallon junansu su

yasmin ce ta shigo parlorn ,abinda tagani ne yasata saranda wani malolon bakincikine ya tokare mata awuya ta kalli yayan nata ta kalli maryam da bamasu san da zuwantaba kwafa tayi tana karajin wutar kiyayyar maryam azuciyarta na karuwa ita abun mamaki yake bata komai yayanta yagani a wannan bakar fatar ya like mata har ta chanjashi haka daga zaki mara fara,a izuwa dan soyayyah

Gyaran muryar yasmin tayi fuskar nan babu yabo babu fallasa tana karemusu kallo ga mamakinta sai gani tayi sun juyo sun kalleta ba tare da sundaina rawar kaunar ba saima wani shishshigewa jikinsa da maryam take karayi shikuma cikin sakin fuska ya rungumeta a jikinsa yana cewa, " yasmin meyasa idan zakizo gidannan bakyasan sallamah kawai saiki faɗo mana

" yaya dama papy ne yace a kirawoka yaji wayarka a kashe wai kazo yanzu , ok kawai yace mata yana wasa da gashin kan maryam

Fuuuu yasmin ta fice tana dana sanin zuwanta gidan dan babu abinda ta tsana irin taga maryam da yayanta suna soyayyah dan ita jitake da Raihan ya zauna da maryam amatsayin mata gara ya mutu babu aure


A wajensu maryam kuwa yasmin tana fita ta zame jikinta daga na Raihan ta sa remot takashe kiɗan sannan ta faɗaɗa murmushin ta tace , " hubby kaje kiran papy naji ance yanzu yakesan ganinka ," ok to shirya muje ki rakani kinga saiki gaida Ame hauwa

Kallon fuskarsa tayi taga bada wasa yakeba da ita zai tafi hakan yasa batai masa musuba taje ɗaki ta ɗakko wata bakar abaya da yelon mayafi ta feshesu da turare tasa sosai rigar ta amsheta sai ɗan cikinta daya bayyan cikin rigar

Tana futowa ya faɗa ɗa fara,arsa ya ware mata hannu ta faɗo jikinsa yana shakar daddaɗan kanshinta dabaya gajiya dashi yakama hannunta suka kulle gidan suka tafi

Yaran gidan suna ganin yayansu da matarsa yasasu suka dunga zubewa suna kwasar gaisuwa , daidai gidan ommu Amal suga gamu da rukunin yan matan gidan wato islam da shahida da yasmin

Islam tana hango Raihan da maryam ta haɗiyi wani yawan bakin ciki mai kauri take idonta suka cicciko da kwallah amma saita dake tana sunkuyar dakai kamar bata gansuba , yasmin ce ta katse mata tunani da cewa, " kunga abinda nake faɗa muku wlh haka na taddasu a gidan ta maidashi tamkar karamin yaro tasashi agaba suna rawa wannan abin bakaramin tsayamin yayiba , shahida ce ta sheke da dariya tana cewa , " wace macece ce zata samu namiji kamar yaya Raihan ɗin mu tayi wasa da damarta ga kyau ga kuɗi ga iya soyayyah ga kyan tsari jiki mai kyau iya kwalliya ke komai na rayuwarsa abin birgewa ne uwa ubah kyan hali , wata muguwar harara islam ta watsa mata hakan yasata kame bakinta suna kallon hanyar da su Raihan suka wuce har suka kure musu


Da sallamah dauke a bakinsu suka shiga parlorn papy ya amsa musu cike da fara,a yana musu maraba haɗi da basu wajen zama cikin ladabi suka gaida papy shima ya amsa yanaiwa maryam ya jiki tace da sauki , Ame hauwa ce ta fito rike da tire da ruwa da lemuka tajere a tebel ɗin gabansu tana faɗaɗa fara,arta suka gaisa

Bayan sun gama gaisawa Ame hauwa tace to ƴata tashi mushiga daga ciki mubarsu su tattauna

Jiki babu kwari maryam ta bi bayanta dan iya gaba ɗaya yanzu Ame hauwa tsoro take bata , ɗaya parlorn Ame hauwa takai maryam kamar wata bakuwa haka akai mata masauki cike da kissa haka Ame hauwa take jengwalar maryam da hira mai kama da tambaya , " o, maryam tunda kikai aure babu wani naki daya tako yazo gidannan da sunan sunzo ganin ƴarsu gashi ko waliyin nakima bamu kara ganin kafarsaba to kuma idan kin haihu shi ɗan ace ina dangin uwarsa suke

Rasss maryam taji gabanta ya faɗi da tambayar Ame hauwa idan maryam ne sukai rau rau hawayene yake kokarin zubomata amma saita dake ta sunkuyar da kanta

" kinyi shiru kenake saurare , murmushin takaici maryam tayi tace , " muna gaisawa da ƴan uwana ta waya kuma ma idan na haihu mijina yace zamu tafi ganin gida ,

" uhm wannan abu yayi kyau yakamata kam kuje yagansu yasan asalinki dan mu a ka idarmu ma ko bare bama aure saina dangi haka al,adunmu suke sai gashi yau Raihan yasa kafa ya shure duk wannan al,adun ya auro wacce bama jinsin saba amma karki damu fa duk da haka muna sanki kuma zaki karbi kyakkyawan sakamako daga wajenmu zakiji dadin rayuwar DAULATUL ARAB fiye da tunaninki kedai kawai kijira lokaci kiga yadda al amura zasu jujjuya miki , takarashe maganar tana wani irin murmushi haɗi da bin maryam da kallo mai cike da tsan tsan tsana wadda ko a kwayar idon Ame hauwa kana iya hangota karara

Gaban maryam ne yakuma tsananta faɗuwa dajin magan ganin Ame hauwa tabbas wannan magan ganun da take da biyu to metake nufi kenan Allah yafisu maryam ta fada azuciyar ta



zaune yake kusa da papy yana jira yagama wayar yaji kiran da yake masa

Papy yana ajiye wayar ya kalli Raihan cikin tsanaki yafara magana , " Raihan magana nakeso nayi dakai mai matukar mahimmanci ,

gyara zama Raihan yayi ya daidai ta nutsuwarsa cikin ladabi yace , " naam papy ina jinka

" wato Raihan na yaddah dakai fiye da tunani wannan ne yasa na dan kamaka ragamar manya manyan wasu daga cikin kadarorina kake tafiyar dasu amma ga mamakina acikin watan daya wuce anyimin asarar kudaɗen da nikaina bansan adadinsu ba kuma bansan ina aka kaisuba kai hattah wannan babban company da aka cikashi da kayan dukiya kayansun kare kuma babu wani kuɗi da suka fito yanzudai atakaice inasan sanin ina kuɗi na suka shiga me akai dasu mai yasamesu ?,

Tunda dady yafara jerowa Raihan tambayoyi yaji gabansa ya faɗi kansa yasara a duniya babu abinda Raihan ya tsana sama da atuhumeshi akan abinda shi kansa baisan inda sukeba tabbas jagorancin kayan mutane masifa ne , cije lebe Raihan yayi cikin rashin kuzari yace ,

" papy sanin kankane tun ina yaro bana taba ɗaukan abinda nasan ba nawa bane har kamo yau danake 40 year wallahi papy bansan yadda akai wannan kuɗin suka bataba , yakarashe maganar cikin damuwa

Girgiza kai papy yayi yace , " ninasan dalilin batan dukiyata , dasauri Raihan ya ɗago ya kalli papy cike da neman karin bayani , kai dadi ya ɗaga masa alamar eh yace , " kuɗina sun batane ta dalilin matarka da take nunawa duniya ta isa da kai take hanaka kaje ka kulamin da dukiyata wadda gaba kuzaku moreta nasha sakawa lamuranka ido ina tunanin kai mutumne mai hankali da gidanka bazaifi karfinkaba sai gashi yarinya sa,ar kanwarka tana kokarin rusa maka lissafin rayuwa a wannan shekarun naka Raihan bai dace ace sai wani ya ankarar dakai barna zaka ganeba ina sane da bakabawa aikin dana baka mahimmanci ba saikayi 2 weeks baka leka koda company ba to inaso kasa aranka ba kowane lokacine na iyaliba dole akan fita tsawan kowane wuni dan anemo musu abinda zasuci idan ka fusatani na kwace kasuwancina wallahi abincin da zakucima wuya zai muka dan kasaba da kuɗi ta yadda ba kowane aikine zai kawo maka kudin da kakesoba sai nawan dole

Gumine yafara kwarara a jikin Raihan gaba ɗaya ya shiga da muwa shi a rayuwarsa bayasan yaji iyayensa suna ganin lefin matarsa cikin sanyin jiki yace," papy a gafarceni wlh balaifin maryam bane lokacin batada lafiya shine nake kula da ita kantaji sauki ,

Murmushi papy yayi irin nasu na manya yace , " ai nima bawai naga laifinta bane kawaidai na ankarar da kaine dannasan idan ba uzurin iyalinkaba babu abinda zaisa kayimun sakaci da kasuwanci na har asamu asara mai yauwa, " yauwa nagode papy insha Allah zan kiyaye , " yauwa haka akeso bakomai Allah yayi maka albarka , ya amsa masa da ameen sukai sallamah ya wuce inda maryam suke tare da Ame hauwa yace sutaso su tafi


Har bakin get Ame hauwa ta rakasu bayan sun tafi ta shigo cikin gida ta zauna a gefan papy tana tayashi kwashe tarin takaddun da yake gabansa tace , " papyn yara ya kukai da ɗan nawa Allah yasadai bakai masa faɗaba dan naga ka fusata da batan kuɗinnan?,
Sauke ajiyar zuciya papy yayi yace

" ban masa faɗaba ai dama bawai na kirashi dan na masa faɗa bane wannan dukiyar dama tasace kawai inaso na ɗorashi ahanyar da zai koyi tattalin ta da kula da ita shiyasa tunda yanzu kinga shi kadai ne babbah acikin su ukun da Allah ya ban , Ame hauwa tanajin haka taji wani bakin ciki ya doketa zuciyar ta naraya mata batai nasaraba lallai papy wato bai karbe komai daga hannun Raihan ba kenan , kallonta papy yake cike da tambayoyi yace , " tunanin me kike , kokarin saita nutsuwarta tayi tana yaken dole tace , " eh kwarai hakane kam gara da ka tunatar dashi amma wasa da dukiya bashida amfani tunda Raihan ba yaro bane , eh kawai papy ya ce mata sannan yamike ya wuce toilet yayi alwala ya fita izuwa masallaci



Islam ce zaune a ɗakinta tagama shirinta tsab na fita unguwa turare ta ɗauka ta feshe jikinta dashi sannan ta zuba kuɗi ajaka da ƴan tsurarin kayan kwalliyarta tasa sabuwar wayar datasiya aciki tadau karamar jajar ta rike a hannun sannan ta fito

Ommu Amal tana kitchen tana girki taji kamshin turaren islam duk yacike gidan da alama fita zatai aikuwa da hanzari ommu Amal ta fito ta shagabanta tana kare mata kallo tace , " ina zaki haka da ranan nan ?, kallon fuskar uwar tata tayi taga babu alamar wasa hakan yasata yin murmushi tace , " zani gidansu kawata lailah ne ,

Wani irin kallo ommu Amal ta mata , " shikkenan idan kinje ki haɗani da lailan ta waya zamuyi magana da ita , to tabata amsa tawuce


Tunda islam ta shigo ɗakin hotel ɗin gabanta yake faɗuwa zama tayi a gefen gadon tanajin karar ruwa abanɗaki tasan yana ciki







Comment
and share⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲





AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA






By
zee ƴar mutan libya






PAGE 8️⃣5️⃣⏮️8️⃣6️⃣


Bismillahir rahmanurrahim









Kasa nutsuwa islam tayi gaba ɗaya jitake gabanta yana tsananta faɗuwa kamar bazata iya aikata abinda take shirin aikatawa ba kai komo take kamar maijin fitsari acikin ɗakin tana yarfe hannaye bakinta ne ke furta innalillahi wa inna ilaihir raju,un

Ahankali tafara tunanin fecewa kallon kofar toilet ɗin tayi aikuwa cikin sanɗa ta ɗau jakarta ta fice , ba wata wata taje moto park taja motarta tabar hotel ɗin

Tanata tsala guɗu a titi tana tunanin meye mufita takasa aikata abinda takeso tsoran makomarta ya rinjayi burinta tadawo bashirin , wata iska mai zafi ta hurar daga bakinta tana dukan sitiyari da hannun ta tuni hawaye masu zafi suka shiga gan garo mata ahankali bakinta yake furta Alhamdulillah ya Allah Alhamdulillah hatta karasa get ɗin gidansu

Tanayin parking ta wuce gida babu kowa a parlor hakan yabata damar wucewa ɗakinta tana shiga ta rage kayen jikinta ta faɗa kan gado tana raira wani irin kuka mai ban tausayi zazzafar soyayyar Raihan ce take azazzalarta gashi tanaji tana gani tarasa yadda zatai tasamu mufita





Shirye take cikin fararen riga da wando na bacci masu azabar kyau da ɗaukan hankali wani sihirtaccen kamshi ne ke fita

Please Login or Register in order to submit comment