Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sakan yakasa hakuri matarsa kawai yake tunani gashi yakira wayarta ba,a ɗagawa cen saiyaji an kashe wayar

Karfe biyar ɗin kuwa tanayi ya haɗe kayensa ya hau mota ko gida bai biyaba ya wuce gidan hajiya babbah , bayan yayi parking yafito ya tadda gidan makil da jama,a anata gai sawa wasu ƴan matane sukace masa , " yaya ina anty maryam bakazo da ita bane ,

Tambayar dayaran sukai masace tabashi mamaki sai yayi zaton ko basu gantaba karamar cikin yaran ya ɗaga sama yana mata wasa yace , " antyn ku tazo tun safe saidai idan baku gantaba bari nashiga daga ciki bai jira jinta bakinsu ba ya wuce , yana shiga parlorn suka gaisa da mutane sai ware ido yake ko zaiga maryam amma bai gantaba ,

Ame hauwa ce ta fito rike da kofin shayi a hannunta tace , " ahh maraba lale da manyen baki ko kai ka kawo su Laulam ɗin kaga tun safe basuzoba , fuskar Raihan ce ta chanza lokaci ɗaya hakan ya bawa Ame hauwa tsoron kaddai ya gano amma da yake macece mai dakewar zuciya saita basar tanajiran jin ta bakinsa

" Ame ni ba tare nake dasuba tunsafe rabondanaji maryam a waya kuma ko lokacin data shirya zata fitoma saida mukai sallamah tace ga Laulam na kwan kwasa kofa , " to kodai motar tasuce ta lalace nima ɗazu na kira Laulam amma bata ɗaga wayarba Allah dai yasa lfy , " aikuwa Ame bari yanxu na koma gida na dubasu dan bazai yu ace nan da gidaba fafiyar minti ishirin su wuniba " gaskiya kam kaje ka duba ko zuwan suka fasayi nima yanzu zamu taho dan yamma tayi angama taro

Raihan bai bata amsaba ya juya ya tafi zuciyar sa sai tufka take tana war wara hankalinsa ya kasa kwanciya haka yake fafara gudu a kwalta haryakai bakin get aka buɗe masa ya shiga , yana zuwa bakin part ɗinsa sai yaga motar Laulam a kofar gidansa hakan ya kara sawa yaji nutsuwa shiga gidan nasa yayi amma me zai gani tun daga parlor anyi watsi da kayensa gabansane ya yenke ya faɗi daya duba jikin bangon ɗakin duk babu poton maryam ko ɗaya an cire sai nasa dakuma wanda sukai tare da ita na bikinsu ansa jar maka an kansile jikin fuskar maryam

Tashi yayi ya nufi bedroom ɗinta yana kwala mata kira amma sai yaga wayem duk kofofin sif a abuɗe maryam ta kwashe kayenta tsab kayan jariran dasuka siya na haihuwa kuwa duk a watsa su tsakiyar ɗakin

Da sauri ya yiɗakinsa yana kiranta nanma wayam ankuma hargitsashi zama yayi a kasa dabaro yana tunanin mai hakan yake nufi

Tashi yayi ya nufi gidan Laulam yana zuwa yaga kofar gidan a buɗe tundaga soro yake kwaɗawa Laulam kira

Da sauri ta fito fuskarnan taci kuka ta godewa Allah duk ta kumbura ta ce masa , " Raihan maryam ta gudu ta ta tafi ta kwashe komai nata daga gidanka ta tafi daularsu wai dama ba sanka takeba babu yaddah banyi da ita ta tsayaba kodan cikin jikinta amma haka ina gani tasa wasu bakaken mutane suka sa mata kayenta a mota ta tafi

Luuuu Raihan yayi zai faɗi da sauri anty Laulam ta rukoshi
















✍🏻 ZAINAB AHMED YUSIF
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲






AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA






✍🏻 ZAINAB AHMED YUSIF






PAGE 8️⃣9️⃣⏮️9️⃣0️⃣

Bismillahir rahmanurrahim









Duk da anty Laulam ta rike Raihan saida yakai kasa yana dafe kansa cikin tashin hankali


Bango ya dafa ya mike jikinsa yana rawa yace , " taya zakicemin matata ta gudu bayen ko da kikazo kina kwankwasa kofa video call muke da ita kuma ni nasan halin maryam tana sona bazata iya rayuwa babu niba bazata gujeni ba dole akwai abinda ya faru ?, yakarasa maganar yana kafeta da kallon tuhuma

Rushewa tayi da kuka hadda majina tana cewa , " Raihan kasan inasan maryam na ɗauketa kanwata bazan taba jin daɗi ta nisanceka ba yau maryam ta bani mamaki dan karara ta bayyanamin bakai takeso ba kuɗi takeso kuma tunda ta samu ta tattare kuɗin da kayan kuɗi ta shaidamin babu mu babu ita har abada nasan zakaji babu daɗi saboda kana kaunarta amma Allah zai shiga lamarin ,

Maganar Laulam ta sake sashi cikin tunani hakan yasa ya juya ya tafi ba tare dayayi mata wata magana ba , kai tsaye wajen mai gadi ya wuce yana huci yace masa , " kaga lokacin da matata ta fita kuma da wa tabar gidannan

" eh yallabai Raihan nagani lokacin da taketa kwashe kaya tana fito dasu sai wata motar bakaken mutane tayi parking a kofar gida naki buɗe musu saida hajiya maryam tazo tace mutanan tane na buɗe ina gani ta loda kayanta hajiya Laulam tanata yi mata magana tayi hakuri ta zauna amma magan ganun da hajiya maryam take fɗa sun bani mamaki

Raihan jirin da yakeji ne yakara karuwar masa cikin tashin hankali ya juya ko ganin gabansa bayayi sosai ya wuce gida , kuma dubawa ko ina yayi yagani babu maryam babu dalilinta kamar yadda suka shaida masa batabar komai nataba inda yake ajiye makudan kuɗinsa yaje ya duba yaga wayem ja dabaya yayi ya dafe kansa yana furta innalillahi wa inna,ilaihir raju,un hakan na nufin saboda kuɗi ta yaudareshi ta gudu kenan haryanzu zuciyar sa ta kasa yadda ya tabbatar da maryam tana masa sahihiyar kaunar da bazata gujeshiba wani irin ihu yayi ya daki mudubin dake gabansa take hannunsa ya yanke yana tsiyayar jini bai bi kota kan hannunba ya ɗau mukullin mota ya ja ya fice a sukwane

Gudu yake tsalawa a titin yana tafe jini duk ya fatamasa jiki shi kansa baisan inda yanufa ba babu abinda yake sakawa sai matarsa da cikin dake jikinta wasu zafafan hawayene suka gangaro masa zuciyar sa tamkar ta fito waniraɗaɗi da zugi yakeji aransa

Kofar gidan mustapha babban amininsa yayi parking yana fitowa daga motar ya fara buga masa Ƙofa bugu biyu aka buɗe mustapha cikin mamakin yanayin dayaga Raihan ya dafa kafadunshi cikin ruɗewa yace

" Raihan lfy mai yake faruwa kagafa hannunka yana zubda jini menene , Raihan yarfe hannayensa yayi ya dafa kansa dayake ciwo tamkar ya tsage yace , " narasa ta nasara matata da cikin dake jikinta bansan ina zan nemotaba mustapha mutuwa zanyi idan banga maryam ba ,

" subhanallah Raihan garin yaya ina maryam ɗin tashiga ,

kuka Raihan ya fashe dashi shikuma mustapha cikin al,ajabi da tsananin tashin hankali ya kama hannun Raihan suka shiga gida kayan wankin ciwo yaɗakko ya gyara masa hannun sannan ya zauna a gefansa ya kuma tambayarsa meke faruwa , anan Raihan ya zaiyane masa duk abinda ya faru hatta zaman lfiyar da suke da matarsa saida yafaɗa masa ,

Hura iska mustapha yayi daga bakinsa yace , " abinnan akwai bukatar muyi kwakkwaran bincike kai ka tabbatar min da bakada wata matsala da matarka to akan me kenan zata tafi kuma kace min kataba sakinta meyasa lokacin daka saketa batabar gidan nakaba saiyanzu da kuka fahimci juna dole akwai abinda yafaru ko yake shirin faruwa ,

" mustapha maryam ta taba faɗamin dan kuɗi take zaune dani mai yuwar hakanne ta tafine saboda tasamu abinda take bukata ina kokonto akanta , kallonsa mustapha yayi yace " wacce hujjah kakeda ita da zakace kana shakku akan matarka , " tunda nake da ita bata taba faɗamin wacece itaba kuma daga ina take nidai kawai nasan ƴar kasar NIGERIA ce aduk lokacin danace tabani labarinta sai ta chanza fuska izuwa bacin rai tai ta rokona karna sake tambayar ta ahalinta to ka faɗamin idan ba taso tarabu daniba mai yasa takasa faɗamin wacece ita nidai kawai nasan ina matukar santa kuma yadda da itane yasani na zauna da ita ba tare danayi kwakkwaran bincikeba ,

" Raihan karka dogara da wannan hujjar ka kullaci matarka dole akwai wani abun tunda har ta iya faɗawa Laulam zata rabu dakai mai yasa kai bazata sanar makaba karfa kamanta kaji daga bakin mai gadine da Laulam amma bakaji daga bakin maryam ba , " ai tasan zan samu sakontane shiyasa ta sanar musu , " bazaka fahimtaba Raihan amma kajira lokaci zai bayyana komai kuma ka tsananta addu,a Allah zai war waremaka abinda ka kasa hanga idanma ta gudunne da gaske zaka samu kwakkwarar hujja koda sakone a waya zata tura maka kaga daga nan saika tabbatar da abinda nake faɗa maka

Shidai Raihan har kamo wannan lokacin yana kila wa kalane amma baisan menene gaskiyar lamariba , sosai suka tattauna da mustapha yanata rarrashinsa da kyar ya yarda yaci abinci sannan yabashi maganin ciwankai yasha ,

Koda Raihan zai tafi mustapha ne ya rakashi ya tukasu har gida sannan ya karbi mukullin motar yatafi da ita gidansa


Raihan koda ya shiga gidansa kasa zama yayi yaji gaba ɗaya ya tsani kansa da komai na gidan fitowa yayi harabar part ɗin nasa ya jingina kansa da bango yana kuka mara sauti shiyasan rayuwarsa ta gama lalacewa tunda ya rasata da abinda yake cikinta

Zuwa karfe takwas na dare kuwa labari ya karaɗe duk gidan cewa maryam tasaci kuɗaɗe ta gudu kowa da abinda yake faɗa ita kuwa Amal labari yana samunta tarushe da kukan takaici dan tasan wannan kitumurmura aka shiryawa yarinyar da batajiba bata ganiba tinanine ya shiga kai kawo a kwakwalwar Amal fatanta ɗaya Allah yasa ba kashe maryam sukaiba dan babu yadda za,ai ace ta gudu tabar mijinta yadda take tsananin kyaunarsa

Amal saida ta kira ommin ta a waya tasanar mata ta bata dama yau tace ta tonawa Ame hauwa asiri da irin kitimurmurar da take shiryawa amma omminta ta hanata tace mata basuda wata hujjah tabari suga abinda Allah zaiyi dan babu inda zalunci ya tabayin nasara

Adole Amal ta hakura tabi shawarar omminta amma tana cikin tsananin damuwa tausayin Raihan da maryam ne yake nukurkusar zuciyar ta



Papy ma kiran kannan sa yayi su uku aka zauna sukasa Raihan a gaba sai yimata faɗa da Allah wadai da halin maryam suke shikuwa Raihan bai tanka musuba hawayene kawai yake kwarara a idonsa tunda ya zauna ya sunkuyar dakai kasa baiko ɗagoba har suka gama masa wankin babban bargo akarshe papy yace ,

" Raihan idan har ka haifu cikin iyayenka ka manta da yarinyar nan , dago kai Raihan yayi ya zubawa papy jajayen idonsa yanayi masa kallon mamaki da ker ya iya buda baki yace

" har yanzu maryam matatace kuma akwai ɗana dake cikinta dan haka bazan taba iya mantawa da itaba koda kuwa na tabbata da gaske bata sona ta gujenine dan haka kayi hakuri papy bazan iyaba ,

Girgiza kai yayi cike da hassala yana cewa , " wannan kai tashafa Raihan nagama maka komai tunda na yarda ka aureta banyi gaddama ba gashi asannu kuskuran da kayi na yarda da ita yana bibiyarka dan haka karnaji karna gani banaso wannan abin ya shafi lafiyarka daga yau ina mai umartarka kacire komai daga zuciyar ka kacigaba da harkokin ka koda fashin office ne bana bukatar kayi mukuma nan nida ƴan uwana zamu tattauna abinda muka yanke zamu sanar maka tashi kaje Allah yayi maka albarka ,

Raihan bashida tacewa papy yagama magana hakan yasashi tashi jiki babu kwari ya bar parlorn

Ba gidansa Raihan ya wuceba masallacin dake family hause ɗinsu ya wuce yaje yayi alwala yayi sallah yajima yana rakon Allah akan neman mifita sannan yayi karatun alqur,ani ya kwanta dukda ba baccin yakeba amma yafada duniyar tunanin matarsa idonsa kuwa babu abinda suke zubarwa sai hawaye







***

Koda su rasta suka ɗauki gawar maryam da suke tsammani ta mutu basu birnetaba zuwa sukai tsakiyar wani babban titi dake cikin jeji sukai suka shimfiɗeta dayake sunsan hanyar manyan motocice dole wata motar tabi ta kanta taniketa yadda ko fallanta baza,a samuba

Bayan tafiyarsune babu jimawa wata babbar mota ta doso wajen tundaga nesa tsohon dayake tuki ya hango kamar mutum a gabansu a kwace hakan yasashi danna hon ba kakkau tawa amma anki tashi , matarshi da take gefece tace masa sukarasa ya haska musu sugani aikuwa suna karasawa ya haske sukaga machace kwance cikin jini kyakkyawar matashiyar budurwa ,

Dukansa salati suka rafka jiki na rawa suka fito tsohuwar ta dudduba jikin maryam da farko ta ɗauka ta mutu amma data taba gefan zuciyar ta sai taji tana bugu , cikin firgici tacewa mijin nata , " wannan yarinyar fa tanada rai cike take da bukatar taimako abin tausayi ga kuma ciki a jikinta ya kamata mutaimaka mata , mijin bai mata musuba suka kama maryam suka sata amota suka wuce gidansu da ita

Koda suka karasa gida basu wani yinkurin kaita asibitiba saboda su masu karamin karfine , tsohuwarce ta dafa ruwan zafi ta cirewa maryam kayan jikinta sannan tafara goggoge mata jikin tana dubawa kozata ga wani tabo da zai iya shaida musi abinda ya faru da ita amma babu wani tabo saina kanta daya fashe hakanne yasasu gano dukane aka yajaza mata doguwar suma , iya kokari tsofaffinnan sukai wajen ganin maryam ta far faɗo amma ina shiru

Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah yau wata ɗaya da tsintar maryam amma bata farfadoba saidai sun samu nasarar dawowar numfashinta daidai kuma cikin jikintama alamu sun nuna bai mutuba dan yana motsi




***

A tsawan kwanaki talatin na rashin maryam sam Raihan yakasa sukuni yana cikin tashin hankali amma dan rashin adalci irinna iyayensa basu bashi wata damar samun nutsuwaba nunawa suke tamkar wani abu bai faruba rayuwarsu sukebabu wani tunanin abinda yafaru dashi abincima sai mustapha yazo ya sashi a gaba tukunna yake ci gashi yayi wata uwar rama fatarsa tayi duhu

Yau da daddare papy ya kirashi ya haɗa ƴan uwansa kamar yadda suka saba tattaunawa bayan ya gaishesu papy yace , " Raihan zuwa wannan lokacin nasan ka samu nutsuwa narashin matarka shiyasa muka yanke shawarar kayi wani auren dan yanzu kai ba yaro bane hakan zai rage maka raɗaɗin rashin matarka harka manta da komai ,

Rasss Raihan yaji gabansa ya faɗi tunani yake taya zai iyayin rayuwar aure da wacce ba maryam ba , shirun da Raihan yayi yaki cewa komaine yasa papy cewa , " kayi shiru ina sauraranka

" papy da dai anyi hakuri ku karamin lokaci inanan ina addu,a nasan matata zata dawo gareni , " rufemin baki shashasha mara hankali ina kaji a na yin haka matar data gudu ta barka ita zaka tsaya zaman jira to bari kaji aure zakayi kuma basai kasha wuyar neman matar aureba abbu Amal yabaka auren kanwarka islam nan da kwana biyi za,a ɗaura muku aure wannan umarnine bawai shawararka mukebi ba dan haka tashi kabamu waje mitswww, papy yaja tsaki cike da bacin rai

Raihan afusace yatashi dan yanzu yagama tabbatarwa kansa babu wanda yake kaunarsa a gidan kowa kansa yasani babu wanda ya damu da damuwar sa , yana fita ya shiga gidansa ya zube akasa yana kuka tamkar karamin yaro wai shine yau papy yakewa faɗa da girmansa yana tilasta masa aure

Shiru yayi saka makon tuna sunan wacce papy yace masa zai aura cikin sauri ya nanata islam wani katutun bakin cikine ya tsaye masa ji yake tamkar ya kashekansa dan gaba ɗaya zaman duniyar ya isheshi taya zasuce ya auri islam kamar daman jira suke hakan tafaru dashi



Washe gari da safe aka sanar wa mutan gida gobe da safe za,a daura auren islam da Raihan, kowa na gidan yaji matukar mamaki islam kuwa kamar ta kashe kanta dan daɗi ita kuwa ommu Amal bata wani nuna farincikinta ba dan haryanzu zarginsu take dasa hannunsu a abinda yafaru da matar Raihan amma lokaci yananan zai nuna kansa

Islam ko kunya babu haka ta shiga gidan Ame hauwa tana murna ta rungumeta hadda kukan farinciki tana godiya ita kuwa yasmin wani kallon banza take watsa mata cike da takaici tace ,

" amma kedai islam anji kunya yanzu fa nan gidan sirikanki ne shine kikazo kina mana murna wai zaki auri Raihan, dariya suka kashe da ita sannan Ame hauwa ta shaidawa islam suje wajen kawarta da take gyaran jiki mai kyau na gaggawa a haɗata kafin gobe dan su papy sunce aranar zata tare

Wani farin cikine ya kuma lullube islam kamar ta zuba ruwa a kasa tasha ,


Wani abin mamakin aranar papy ya ɗebo ma aikata suka sake gyara gidan Raihan aka fidda tsofaffin kayan gado da kujeru aka zuba sababbi hadda kayansu labulaye kayan kitchen sabo aka sa wanda sukafi na maryam haɗuwa da yake harkar ta kuɗice aranar aka gama komai

Shikam Raihan dan takai ci bai ko kwana agidanba kayan da yake gani yake tuna maryam duk an zubar jiyake kamar yayi hauka

Mustapha ne yaketa rarrashinsa yana tausarsa akan ya danne zuciyar sa yayiwa iyaye biyayya wata kila ganin biyayyar dayayi musu hakan yasa Allah ya dawo masa da matarsa , hakan yayi matukar tasiri a zuciyar Raihan dan yasan Allah yana da ɗaɗawa mai da ɗaɗawa iyayen sa badan yasoba ya cigaba da danne zuciyar sa har zuwa ranar da aka ɗaura auren sa da islam


Tundaga wajen ɗaurin auren Raihan ko poto bai tsaya an musuba yaja motarsa ya fice daga gidan bashida inda zashi hakan yasashi yin parking a wani babban masallaci ya shige yayi zamansa yanata jan charbi



Gidan biki ya cika makil anata tsammanin ganin ango ko da sau ɗaya babu wanda yaga giftawarsa

Islam da ita da kawayenta suna gidan Amal ana shan hira sunata tattaunawa dayimata murna nasamun haɗaɗɗen namiji kamar Raihan, Amal kuwa babu abinda ya shafeta ta fito daga bedroom ɗinta sanye da zundumemen hijab har kasa fuskarnan tata jajir taci kuka , kwallo ɗaya islam tayi mata ta tuntsire da dariya babu kunya acikin mutane tace ,

" ya akaine matar kangararre kukan me kike ko watsatstsan mijin nakine ya lakada miki duka uhm koda yake nasan hakannema hakuri zaki kinga yadda rayuwa take keda kika amsa sunan nutsatstsiyar gashi kin kare da watsatste nikuma mara mutuncin mara kunyar Allah yabani ɗaya tamkar dubu acikin maza, ai kuwa sai gurin ya dau shewar kawayen islam suna dariya hadda tafa mata







ZAINAB AHMED YUSIF
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲





AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA






By zee ƴar mutan libya






PAGE 9️⃣1️⃣

Bismillahir rahmanurrahim









Take Amal taji ranta ya matukar baci bakinta har ɗaci yake cikin fusata tace , " Alhamdulillah ni nagode wa Allah daya zabarmin YASIR amatsayin kaddarata kuma naji daɗin hakan dan nasan alkhairi ne to amma kuma kefa himm koda yake bazan tsaya ina sa insa da ke acikin wadan nan taron ƴan Allah yabaku musamunba nabarki da halinki duk abinda kika shuka shi zaki girba ni kinga tafiyata idan kungama abinda zakuyi ku kullemin gidana

Tafaɗa tawuce tabasu waje , dariya suka sake shekewa da ita


Agidan Ame hauwa kuwa zaune take cikin manyan abokan sheɗancin ta wato yayah babbah da Laulam suna tattaunawa Ame hauwa ce tace ,

" yanzu shirinmu na biyu zai fara aiki inaso kowannen mu yadaina nunawa Raihan rashin so da kwaɗayin dukiyar sa agaban islam kunsan son da take masa zata iya rusa mana lissafi ,

Hajiya babbace tace , " hmm nifa wallahi banaso ko kadan naga Raihan yaji daɗin rayuwa nafi bukatar ganinsa haka batare da yayi aureba , " kwantar da hankalin ki yayah babbah wannan auren ai jeka nayika ne wallahi islam saita gwammaci mutuwa da zama gidan Raihan dan ko maryam ɗin dayakeso bai hanashi gasa mata aya a hannuba bare kuma ita matar cushe kudai kuzuba ido kusha kallo , cewar anty Laulam kenan ,

Dariya Ame hauwa ta kwashe da ita tace , " ai ni kadai nasan da lilina na kullah wannan auren munanan daku kamar yadda nayi alkawarin wulakanta ƴaƴan ommu Amal to sai sun wulakanta babu fashi , " gaskiya kam Ame hauwa tuggunki ya hau layi ai wallahi zama da YASIR sai yafiyewa islam daɗi akan zama da Raihan dan yadda yake dan wulakancin nan nasan sai tayi dana sanin zuwa duniya,




Misalin karfe bakwai na dare gidan biki anyi haramar raka amarya da ango cikin gidansu amma babu Raihan babu da lilinsa ran islam ba karamin baci yayiba abin kunyane acikin ƴan uwa da kawaye ace abinda akeyi abikin kowacce amarya na al,adar DAULATUL ARAB amma ita ba,ai mata shiba ,

Sukuwa ƴan biki ganin dare nayi yasa aka raka amarya ita kaɗai babu ango dan danan gida yaɗau tsaigumu ran ommu Amal ya bachi dan jin kunnan ta taji ana gulmarsu ana zaginsu wai angon basan amaryar yakeba amma sai ommu Amal ta danne dan duk tsuntsun dayaja ruwa shi ruwa kan duka


Gidan Raihan kuwa islam ce zaune amakeken gadonta ita dasu yasmin da shahida gaba ɗaya ran islam yagama baci duk tarin farin cikin da take ciki na auren sa hakan bai hanata gani n laifinsaba dan tasan yana sane yayi mata wannan wulakancin

Yasmin ce ta kalli islam da taketa kumbure kumbure idonnan ya kada yayi jajir tace , " yadai amarsu ta yaya Raihan sai aje a cire kayen tunda angon baizoba naga kayen sun miki nauyi abisa al,ada angone a wannan lokacin yake cirewa amaryarsa kaya cike da soyayyah amma tunda ke naki angon baya bukata ki tashi mutayaki cirewa kan mutafi ,

Wani kululun bakin cikine ya tokari zuciyar islam takasa buda baki tayi magana tsabar bacin rai kwafa tayi tana girgiza kai tace , " hmmm yasmin kenan wannan ai ba,abin gori bane a sannu zakuga yadda zan sauya yayanki na cusamasa soyayyah ta ai anyi mewuyar tunda aka daura aure ,

" uhm inda ba kasa nan ake gardamar kokawa mugani akasa ba cika bakiba mrs Raihan, cewar shahida kenan tana yamutsa fuska takara da cewa , " yasmin darefa yayi kizo mubar gidanan yanzu karfe tara kar yaya Raihan yashigo ya ganmu yazaci zigata muke , " to kugaida gida saida safe dan Allah karku shigo da wuri inaso nasamu cikekken lokaci nida mijina , dariya suka kwashe da ita sukai mata sallamah suka fice


Koda yasmin ta koma gida tasamu papy a parlorn sa yana cin abinci ga Ame hauwa a kusa dashi , har kasa ta tsugunnah ta gaishe da mahaifin nata

" lafiya kalau amara kirjin biki tun dazu ina kika shigane , " wallahi papy ina gidan ya Raihan tunda akakai islam har dare yafarayi bai zoba haka muka tafi muka barta ita kaɗai

Papy ruwa zaisha amma saiya ajiye cof ɗin ruwan ranshi abace ya ɗau waya ya kira Raihan yana ɗagawa yace , " Raihan nagode da wulakanta nin dakai an kaimaka yarinya salan kaja mana zagi tunsafe baka leko gidannan ba kanunawa duniya ban isa da kaiba to wallahi bari kaji ƴaƴan wasuma bana sawa kara su ketare bare kai dana haifa dan haka duk inda kake kuma ko mai kake ka wuce gidanka yanzu kuma gobe da safe kazo ka sameni inasan ganinka

Tunda papy ya fara zazzaga masifa Raihan yayi shiru yana rike da wayar a hannunsa babu abinda yake ji sai zafin zuciya da raɗaɗi amma saiya danne ya sassauta muryar sa yace , " papy dan Allah kayi hakuri yanzu zan tafi insha Allah, papy bai bashi amsaba ya kashe wayar , Raihan jiki babu kwari ya tashi daga masallacin ya hau motarsa ya nufi hanyar gida


Koda ya karasa gidan karfe goma tayi na dare haka yayi parking ya sa mukulli ya buɗe gidan yana sallamah ciki ciki

Bai saurari ko inaba duk da yasan islam tana ɗakinta yayi wucewarsa ɗakinsa , wanka yayi yasa kayan bacci yayi kwanci yarsa bayan ya kashe kwai mai haske yabar mai duhun duk da ba bacci yakeba amma idonsa arufe yake yana aikin daya saba tsawan kowane lokaci wato tunanin matarsa ,

Islam tana daga ɗaki taji shigowar sa itace hadda kara gyara jiki tana fesa turare cike da tsammanin zai shigo dakinta amma shiru kamar baisan da itaba a gidan hakan yayi mutukar kona mata rai tana zaune ita kaɗai kamar mayya wai sunan wannan shine daran farkonta a gidan miji , takaici ne ya isheta tafara rai ra kuka cikin tsananin bacin rai

Raihan yana daga ɗaki sarai yajiyo kukanta kusan minti

Please Login or Register in order to submit comment