Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register




Allah sarki maryam sunkuyar da kai tai danwani wulakantaccen kallo taga sunayimata , ga mamakin mutanan gurin sukaga cikin farinciki Raihan ya rungumo maryam jikinsa yana mata sannu da futowa

Hakan yayi matukar basu mamaki dan kowa yana gani yasan akwai so da kauna, da kansa ya buɗe mata murfin gaban mota tashige ita kuwa anty Laulam sai dariya take tana farincikin yadda taga Raihan yana nunawa matar dazai aura kulawa da soyayya

Ita kam maryam kallon mamaki tadinga bin Raihan dashi a zuciyarta tana tunanin kodai Raihan ɗan iskane saiwani rungumarta yake yana kashe mata ido haɗi da kalaman soyayya bayan basu sa da haka a yarjejeniyar suba , kwafa tayi a hankali tana kudire bara su kebance zata fada masa karya sake yimata irin haka ita ba ƴar iska bace


Tankamemen wajen siyayya na zamani Raihan ya kaisu a zatan maryam bawasu kayan kirki za,a siyaba amma ga mamakinta sai taga anty Laulam ta je wajen wasu ran tsatstsun Akwatuna ƴan turkiya sun zabi mai guda goma kamar saitin samira babbarce akasa sai mai biye mata haka bida bi har ɗan kit da jaka ,mamaki bai gama cika maryam ba saida taga mahaukatan abayoyin da anty Laulam take zabarmata ga jakun kuna da takalma masu bala in kyau kayan kwalliya kala kala da kayan shafa da turarurruka su kansu kusan kaloli goma aka kwasa sar koki kuwa ba a magana

Sune harkarfe takwas na dare suna siyayya abban sultan ne ya takurawa anty Laulam da kira wai su sultan sai kuka suke hakan yasa yaya Raihan yace mutafi gifa inyaso abubuwan da baa gama siyaba adawo a karasa ,hohoho ni maryam tunda nake bantaba ganin kaya masu kyau da tsadaba irin na lefan Raihan Allah Allah nake musamu kebewa naji wai dagaske kayanane kokuwadai idan lokacin yarjejeniyar mu yacika zai karbi kayansa




A bangaran su Ame hauwa tunda su Raihan suka fita ommu Amal taja Ame hauwa cikin gida dansu samu sararin tattaunawa

" Ame hauwa kinsan matsalar data kunnomin gidana kuwa game da auren Raihan ?

" nima kaina ina cikin matsalar ommu Amal Juddu yace min yafasa bani companin nan wai Raihan zai bawa shine sukaje akai kullah kullah za ayi auren da maryam dama nasan duk ranar da Raihan zaiyi aure kashina yabushe dan Juddu tattara masa komai zaiyi yabashi

" gaskiya kam Ame hauwa yakamata munemo mufita kuma gashi lokaci yakure mana Abu islam yace min cikin wannan satin zaa ɗaura auran kuma islam ta tuburemin akan maganar wai Raihan takeso wallahi bakiga budurin da akasha ba harsaida mutanan Amal suka tashi haryanzu tana kwance babu lafiya danaga faɗa da ƴaƴana bazai yuwuba saina yiwa islam dabara nace zan shiga na fita nasan yadda zan hana auren amma karta faɗawa kowa cewa Raihan takeso


" o ni hauwa kiji sabuwar jaraba yanzu ace inbanda rashin sanin ciwankai na islam menene hadinta da Raihan mezatai da tsoho koba komai taduba irin abinda yake tsakaninki da Raihan mana bayasan ganinki bakya san ganin sa totaya aure zaiyu ahaka kuma shi ashe muna masa kallon haka zai kare babu aure saiga maganar maryam

" hmmm babu komai Ame hauwa ita islam ai nagama da babunta na kifeta akan zanyi shige da fice nasa Raihan ya aure ta ,yanzu kawai matsalar dake gabanmu zamu kallah maganar aurannan data kanfani dole musan abinyi

" to yanzu wace hanya kike gani yadace mubi ommu Amal ," hanya ɗayace shine mubari auren yakasance idan akai auren shine zamu samu damar ɗaukan mataki akan maganar compani kawo kunnanki kiji ,, nan naga taraɗa mata wani abu wanda su kaɗai suka san mesuke cewa



Lokacin da Raihan yayi parking a harabar gidan babu kowa saboda darene hakan yabasu damar sawa mai gadi ya shiga da kayan lefan part ɗin anty Laulam batare da kowa ya ankara ba

Sallama maryam tayiwa anty Laulam hadi da godiya sannan anty Laulam tace gobe da safe maryam tazo tana neman ta

Cikin gidansu Ame hauwa maryam tashiga dama nanne inda take aiki tana shiga taga babu kowa a falo sai ta shige ɗakinda dan dama batasan haɗuwa da kowa a gidan gudun karsu cimata mutunci

Ga mamakin maryam tana shiga ɗakin nata tagansu a zazzaune suna zaman jiranta yasmin da islam da shahida

Islam ce ta taso kusa da inda maryam take tsaye kan kace kwabo jikake tass karar marin da islam ta wankawa maryam sannan tafara magana

" ke wulakantacci ya karya bakar kunama kirasa dawa zakija sai ni wai kawai bamusan hawaba sai muji sauka zaki auremin Raihan to wallahi kin ɗebo ruwan dafa kanki kifara tunanin makomarki dan kinkusa mutuwa nayi alkawarin ganin bayan duk wata ƴamace datace zata shiga tsakanina da Raihan

Tasss tasss kan islam tarufe baki taji an wanka mata kyawawan mari guda biyu ba iya islam ba hatta su yasmin sunyi mamakin ganin yadda maryam ta zage tamari islam

Cikin isa da izza maryam ta nuna islam da yatsa tana cewa " duk da kingirmeni amma yakamata na nuna miki ban bancina dake karki manta nice budurwar babban yayanku wadda zai aura ko banci darajar komaiba ada yanzu naci darajarsa nafi karfinki islam babu yadda zaki dani aurene nida Raihan kusa aranku tamkar an ɗaurashi babu fashi







✍🏻
Zee ƴar mutan libya ce
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲




AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA




STORY AND WRITING ZAINAB AHMED YUSUF HAƊAJA
MRS
Abzee





PAGE 1️⃣7️⃣⏮️1️⃣8️⃣

Bismillah




Mamakine ya ishi yan matan wajan wai yau maryam mai aikin gidansuce takeda zarrar marin islam ceb akwai kura ,ita kuwa islam kasa magana tayi dafe da kuncinta tana tunanin yau ko duniya zata tashi sai ta nunawa maryam ruwa ba sa an kondo bane

Kallon kallo gaba ɗayansu suke wajen yayi tsit kowa yana kissima abubuwa kala kala , basu fargaba suka tsinkayi muryar Raihan yana shigowa , maryam tana ganin haka ta fasa wata shegiyar kara tayi waje dagudu tana kururuwa

Bata tsaya ko inaba sai bayan Raihan tana kuka ta durkushe a bayensa , a kiɗime Raihan ya tsugunna yana tambayarta lafiya cikin muryar kuka take faɗin ," nashiga uku Raihan zasu kasheni tunda kace zaka aureni nashiga tashin hankali yanzuma babu abinda namusu ina zuwa islam tafara dukana

Raihan baigama jin mai takecewa ba ya tashi daga gurin hadi da jan hannun maryam sukai ɗakin , atsaye ya taddasu curkwai curkwai yana huci yake kiran ," metai muku kuka daketa wanene ya tabata

Gaba daya su islam sun ɗimauce dan sunga makircin da basuyi tsammaniba daga maryam ,yasmin ce tayi saurin cewa ," wallahi yaya bamu muka daketaba islam ce tamareta

" what mari matar tawa zaki mara islam kinada hankali kuwa , bai tsaya jin tabakin islam ba ya wanka mata maruka masu zafi guda biyu wanda saida suka sata kifewa kasa

Duk da haka Raihan bai kyale islam ba saida yasa ta tsugunna har kasa tabawa maryam hakuri sannan yace duka su zazzauna yanason magana da su bayan sun zauna yafara magana cikin sanyin muryar tamkar bashine yagama zazzaga masifa bah

" yasmin islam shahida safeeya abinda nakeso daku kunutsu ku kama kanku guri guda kowacce tasani yanzufa maryam ta sauka daga ƴar aikinku takoma matata tunda nan da kwana biyar zaa ɗaura mana aure , kuma ma ni a tunanina abin farincikine a wajenku ace yayanku zaiyi aure kuma yarinyar da zai aura kunsanta kunsan halinta ,ashe ku ba haka kuke ba menene abin assada aciki idan iyayankunema suke ɗoraku a wannan layin wallahi tun wuri kusauka , saboda rashin tunaninku da girmanku kuba yara kanana ba kudinga haddasa fitina haka kukaga Amal tanayi baiwar Allah babu ruwanta da shiga irin wadannan shirgin

To wallahi ku kiyayeni idan kunaso musa kafar wando ɗaya dakune karku fasa abanza zan karya yarinya wallahi nadai faɗa muku kuma dole kuyiwa maryam biyayya daga yanzu har gaban abadan indai tana matsayin matata kunji na faɗamuku ,yakare maganar da daka musu tsawa

Ko wacce acikinsu ta amsa da munji yaya Raihan kuma insha Allah zamu kiyaye , dahaka yabasu izinin ficewa daga ɗakin

Suna fita maryam takuma fashewa da wani sabon kukan wanda wannan karan tabbas ba kukan muna furci bane nagaskene ita kadai tasan kalubalan dazata fuskanta a auren Raihan sai tayi da gaske zata cimma galaba ,, batayi auneba ta tsinkayi muryar Raihan yana rarrashin ta

" kiyi hakuri maryam nasan zaki fuskanci abubuwa da dama agidannan amma abinda nakeso dake ki toshe kunnuwanki karkiji karki gani kuma daganan zuwa ranar da zaa daura auren banaso ki ɗauke ko tsinke a gidannan ke idanma kinga zaman nan bazai yuba ki koma wajen Laulam tabaki ɗaki kafin a ɗaura auren

" yaya Raihan ashe dama kowa baya sanka agidannan ? , cikin mamaki Raihan yace ," waye baya sona kuma meyasa kikace haka ?, " nafahimci babu wanda yake farinciki da auren nan sai papy da anty Laulam sauran kuwa tunda sukaji zancen kowa ya burkice babban abinda yafi ɗauremin kai acikinsu harda mahaifiyarka Ame hauwa

Haɗe rai Raihan yayi lokaci ɗaya sai maryam taga yakoma mata fuskarshi ta asali wadda tasani baya fara a cikin bacinrai yafara yimata magana ," maryam karna kuma jin wannan maganar daga bakinki ki tsaya iya matsayinki karki manta auren yarjejeniya fa zamuyi bana gaskeba to ki iya takunki kada zakewar tayi yawa kuma karna sake ji kinyi min zancen Ame hauwa duk tsiya ai uwatace bazata cutar danibah

Yana gama faɗin haka bai jira jin tabakin maryam ba yafice daga ɗakin , ita kuwa tashi tayi tana tunanin mai ma yakaita wannan zakewar salon yazo yana mata faɗa maganinta kenan gashi ya shata mata layi



★★★ shikaɗai a kyakkyawan waje mai cike da furanni kala kala ga wasu manya manyan duwatsu masu shararar ruwa ta cikinsu babu abinda kakeji a wajen sai ku kan tsuntsaye mai daɗi

Wani sanyin daɗine yake tashi a wajen haɗi da kanshin furanni ,gabaɗaya FERAS ya shagalta da kallon wannan kayataccen wajen cike da nishaɗi ya ɗaga kansa sama ,wow ya furta a fili saka makon ganin yadda sama tai wasai sharshar

Cikin nutsuwa ya fara taka kafarsa da ko takalmi babu yana jin yadda yake taka lausassun ciyayin waje ga wani ɗan danshin ruwa dayake taba masa kafa , yaɗanyi doguwar tafiya tukanna yafara hango alamar mutum daga cen nesa da sauri yakarasa wajen yana zuwa yayi arba da ita ,wannan karan shigarta ta mutumci ce dan kuwa fararan kaya tasa

Lokaci ɗaya ranshi ya baci cikin fusata yace ," wacece ke meyasa kike bibiyata me kike bukata a wajena bakida labarin ni ba mabiyin mata bane to koma wacece sainaga bayanki zakiyi danasanin shigowa rayuwata

Dajin wannan maganar wannan matashiyar budurwar ta hassala tai wata kururuwa da dukkan ilahirin wajen ya amsa take fuskarta ta cenza launi izubaka kirin idonta ya koma jajawur wasu hakora marasa kyan gani suka fito mata ,FERAS bai kara firgitaba saida yaga dukkan kayan jikinta ya koma bakake wannan furannin sun kone bakikkirin sararin samaniya tayi jajawur komai nawajen take yasauta tamkar yana masarrafar dalma hatta duwatsun nan sun koma aman wuta tsuntsaye duk sun mutu , muryarta ya tsunkaya cikin dodon kunnansa tana faɗin

" nice bakar kaddararka mafi muni sunana ALJANA RUBBAH inada bakin iko mafifici acikin yan uwana jinnu nazabi nazama bakar kaddararkane saboda wasu manya manyan dalilai kuma dole saina ai watar da kudirina akan ka FERAS

Tana gama faɗin haka ta ware hannayenta take wani bakin hayaki ya mamaye feras sama hayakin yafarayi dashi ,FERAS yayi matukar razana cikin tashin hankali yafara kokarin yin addu,a amma ina gam yaji bakinsa ya rufe wani kasurgumin aljani yagani mai mummunan siffah bakikkirin yazo da kachar wuta zai ɗaureshi gashi babu damar gudu yana saman wannan bakin hayakin ya mamayeshi , kara kusantoshi aljanin yake shikuma FERAS tsoransa yana daɗa karuwa harya karaso ya ɗaga wannan katuwar kacer wuta ya zabgawa FERAS a kafaɗa ,

wata mahaukaciyar kara feras yasaki da duk saida ilahirin gidan nasu ya amsa a razane ya farka daga baccin dayake ,wata ajiyar zuciya yasaki yana hamdala da Allah yasa mafarki yake tashi yayi yaje gaban mudubi yafara dudduba jikinshi kozaiga inda aljanin nan ya zabga masa kacha , Alhamdulillah ya furta ganin babu wani abu daya sameshi amma haryanzu a tsorace yake ,, jiyayi anturo ƙofar dakin da sauri ya daga kansa dan ganin mai shigowa Ammeen sace tazo jiki a sanyaye ita da kannansa guda biyu aisha da gazzal

Ganin hakanne yasa yaji zuciyarsa tadan yimasa sanyi ,, zama sukayi Ammee tace " FERAS lafiya mai yake faruwa nakasa gane maka a waɗanan kwanakin rannan shaikh ali yafaɗamin yazo ya taddaka kana ta faɗa kai kaɗai azuwan wata kake gani yau kuma kacika giddannan da ihu mai yake faruwane ?

Shafa kanshi yayi jiki a sanyaye yace "babu komai Ammee mafarki nayi kuma banyi tunanin ihunma ya fitaba

" hmm FERAS kenan dama nasan zurfin cikinka ba lallai kafaɗa minba amma inaso kasani komai yayi zafi maganinsa Allah wallahi duk wanda ya manta da bautar ubangiji yadinga shiga tashin hankali kenan karfa kamanta FERAS kaine babbah acikin yan uwanka mahaifinku baya raye kaine madafar kowa acikinmu dakai muke al fahari babu yadda za ai muso kasamu wata matsala arayuwar ka abinda nakeso dakai ka kula FERAS ka kula ka koma ga Allah

Murmushi feras kawai yayi yace karsu damu babu komai





★★★
Yau saura kwana biyu a ɗaura aure Raihan da maryam abu yayi abu yan gida sai shige da fice suke baki sunata hallara itadai maryam tasha mamakin irin makudan kudin dataga an kashe babu abinda baa siyaba Raihan kuwa sai wani nuna mata madarar soyayya yake amma idan agaban mutanene gaba ɗaya abunma ita ganinshi take tamkar Games


Allah sarki Amal baiwar Allah cikin kwana biyu tayi wani ba la,in rama tarage shiga cikin mutane bata magana da kowa sai dole mamanta tayi tayi da ita tafada mata damuwarta amma taki saitace babu komai

Allah shikaɗai yasan irin wahalar da zuciyar Amal takesha akan soyayyar yaya Raihan da babu wandama yasan tanayi ,, islam kuwa duk ta ruɗe ummanta tana ta yaudararta akan tana nan tana haɗa makircin da Raihan zai aureta


Allah ne kadai yasan shirin da Ame hauwa sukai itada ommu Amal dan kuwa tundaga ranar da suka tattauna babu wanda yakuma nuna bakinciki akan auren saidai babu ruwansu da maryam ko kallo bata ishesuba


Zaune suke yan samarin gidan su huɗu suna hira da yammaci sai kira yashigo wayar Ammar yana dagawa yayi sallamah baa ko amsa masaba yaji mai kiran yana cewa

" kai Ammar ɗan jeka kaduba ɗakina akwai wata bakar jaka a karkashin gadona ka ɗakko zan turo abokina samin ya karbah

" to bari yaya Raihan ya dawo idan na ganshi zan karbi mukullin ɗakin naka ,
" au dama mukullin nawa a hannun Raihan yake ?,

" eh shi ne ya karbi mukullin dan daima yanzu baya zamane yashiga rububin biki da yanzu zan dakko maka jakar ,
" ya shiga rububun biki kuma ? Bikin wa ake agidan

" au natinafa yaya YASIR ka daɗe baka gida bakasan da zancen auren yaya Raihan ba ,

" kacedai tsoho yasamu kasuwa bana wacce mara sa arce zata aureshi ?,

" kai yaya YASIR kanada abin dariya wlh wai wannan maryam ɗince zai aura ƴar aikin gidanan






Please comment and share fisabibullah 🤝




✍🏻
Zee ƴar mutan libya ce
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲





AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA





STORY AND WRITING ZAINAB AHMED YUSUF HAƊAJA
MRS
Abzee




WANNAN PAGE SADAUKARWA NE AGAREKI KAWATA KUMA ƳAR UWATA ❤️❤️ NUSAIBA YAHAYA IBRAHIM ( MAMAN AJRAM ( 💃🏼💃🏼💃🏼


_______________________________



PAGE 1️⃣9️⃣⏮️2️⃣0️⃣

Bismillah




Wata muguwar ashar YASIR ya kutum tuma wadda saida tasa Ammar mikewa tsaye tamkar yana ganin yasir a gabansa yace ," lafiya yaya yasir naji kayi wannan zagin koda matsalane ?

" babbar matsalama kuwa niza ayiwa haka wallahi wannan auren bazai taba kasancewa ba saidai idan bana raye yarinyar dana jima ina hari duk wani shiri danake akanta Raihan yazo yarusamin ,

Cikin mamaki dajin maganar yasir Ammar yace ," yaya kana nufin kai kakeson maryam shine yaya Raihan zai aure ta ?

Kwafa yasir yaja yanajin zuciyarsa tamkar ana zuba masa wuta maganama yakasa tsaki kawai ya iyaja ya kashe wayar

Ammar cikin mamaki yajuyo ya kalli marwan dake kusa dashi yace ," ceb ana wata ga wata ashe yarinyar da yaya Raihan zai aura budurwar yasirce ?

Murmushi marwan yayi yace " hmm aukaida baka saniba duk gutsuri tsomar da ake agidannan baizo kunnankaba to bari kaji ayadda labari yasameni wai maryam ɗin ansha kamata da yasir suna iskanci kuma saigashi kwatsam yayansa Raihan yace zai aureta soyayyar dabamusan da itaba kawai zancen aure mukaji nan da kwana biyu

" ceb lallai akwai babban bala,i dayake shirin faruwa agidannan dan kasan halin yaya yasir duk inda tantiri yake yakai kaf garinnan sara musu ake shida uban gidanshi FERAS

" gaskiya kam hakane to Allah dai ya tabbatar musu da alkhairi ya kaɗe hau da fitina ,, ameen dai Ammar




Maryam ce zaune a parlorn anty Laulam tana kallo ga sultan a gefanta yana wasa ƙofa taji an kwan kwaso a zatanta anty Laulam ce tunda dama batanan ta tafi makaranta dayake malamace


Maryam na buɗewa taga Raihan da sauri ta sunkuyar da kanta kasa tana gaishe shi ,, batare da wani abuba ya amsa mata yana tambayar ta Laulam bata dawoba ,i tabashi amsa sannan ya shige parlon ya zauna daga gani yaɗebo gajiya wasu ba kaken ledodi ne a hannunsa guda biyu madaidaita ,

maryam dake rabe a bakin kofar taki karasawa yakira tana zuwa ta tsugunna ledar dake gabansa ya tura mata tana karba ta buɗe taci karo da wata tamfatsetsiyar waya mai bala in kyau wadda kuɗinta bazai wuce dubu ɗariba layi yazaro yamiki mata

Sosai maryam taji daɗi tafara yimasa godiya yace babu komai akwai number sa yasa mata alayin duk abinda take bukata ta kirashi tafaɗa masa


" yauwa maryam ansamo wasu mutane guda biyu ƴan kasar NIGERIA mazauna DAULATUL ARAB dazasuyi basaja amatsayin kannan mahaifinki wato magabatan ki

" to babu matsala yaya Raihan duk abunda kayi daidaine yauwa

Kai kawai Raihan ya ɗaga mata yagyara zamanshi akan kujera 3ster ya kwanta dan yayi matukar gajiya itakamdai maryam kunyace ta isheta ganin babban mutun kamar Raihan wanda yake mata matukar kwarjini yazo ya kwanta tana kare masa kallo ta dau sultan suka fice daga gidan


Gidansu Amal ta nufa tana shiga ta tadda ommu Amal a parlor har kasa ta tsugunna ta gaidata babu wani yanayi a fuskar ommu Amal da fara arta ta amshi gaisuwar tana tsokanarta da amaryar kwana biyu

murmushi maryam tayi tana sunkuyar da kai tace Amal tana nan ,eh tabata amsa da tana ɗakinta

da sallamah ta tura kofar ɗakin a kwance ta tadda Amal a kan dadduma da alama batadaɗe da idar da sallah ba

" wslm maryam shigo , bayan ta shigo sun gaisa maryam tace " Amal kwanabiyu shiru kebaki zoba nibanzo ba da harnayi fushi dake sainaga yakamata nazo naji dalilin rashin nemana bayan kinsan bikina za ayi kuma duk gidanan banida wadda tafiki

Yaken dole Amal tayi wanda ake cewa yafi kuka ciwo cikin karfin hali tayi kokarin boye bakincikin ta dan harga Allah bazata iya ganin lefin maryam ba amma kuma zuciyarta bazata jure jin zancen auran masoyinta da wataba abun yana matukar kona mata rai

" ayya kawata kiyi hakuri nima ina dan wani uzurine shiyasa baki ganniba

" himm to shikkenan dama zuwa nayi na fada miki anty Laulam tace gobe za ayi gagarumar walima wadda daman al adar DAULATUL ARAB ce indai zakuyi biki ango da amarya zasu haɗa zazzafar walima a tara ƴan uwa da abokan arziki shine nazo nafada miki danni banida wata kawa kuma aminiya data wuce ke

" eh hakane gobe za ai walimar jibi aɗaura aure naji abbanmu yana faɗa ɗazu da safe dan har bakima sun fara zuwa

" eh wallahi nima nagansu kinga wayar da nurul khalb ya kawomin

Amal tanaji maryam takira Raihan da hasken zuciyarta taji tamkar ta mutu dan bakin ciki ga wani abu dayazo ya tsaya mata awuya bakinta har ɗaci yake ciwan kanta yakaru daker ta iya buɗe baki tace ," maryam nikuwa inaso na tambayeki a iya sanina dake a gidanan babu wata soyayya dake tsakaninku da yaya Raihan amma kuma yanzu kun bayyanata kuma da gaske kina sonshi zaki zauna dashi zaman aure

Maryam jitayi gabanta ya faɗi dan tambayar ta shiga jikinta take ta tuna da maganar Raihan dayake cewa duk wanda ya tambayeta tana son shi tace eh kuma sunjima suna soyayya ,, kakalo murmushi maryam tayi tafara magana da cewa

" Amal hakika nima kaina bansan irin adadin soyayyar da nakewa yaya Raihan ba ina masa so mara musali kuma na shirya rayuwa dashi ta har abada babu ruwana da shekarunsa ko zancen mutane zan farantawa mijina ta yadda zaiyi alfahari dani zan shayar dashi madarar soyayyar da babu wata ƴamace da zai kara tunaninta a duniya bayan ni

Amal tanajin haka hawayen da suke barazanar sakko mata suka zubo take kuka marasauti ya kwace mata ta sa kanta akan cinyar maryam tana wani kuka mai bala in ɗaga hankalin mai sauraro

Cikin razana maryam tace " lafiya Amal mai yake faruwa haka dan Allah kifaɗamin ko nayi miki wani laifine

Kokarin tsaida kukan Amal tayi tukunna tafara magana cikin matukar sanyaye

" maryam zan bayyana miki sirrin zuciyata danayiwa kaina alkawarin babu wani wanda ya isa yaji amma yanzu bazan iyaba yazama dole kisani, idan ba hakaba zaki iya sani a sahun makiyan auranku duk da amintar da take tsakanina dake

" haryanzu ban ganeba Amal mai yake damunki kifaɗa min ko menene nayi miki al kawarin babu wanda zaiji

Share hawayen dake fuskarta Amal tayi sannan tace " shekarata 22 aduniya acikin waɗan nan shekarun nawa bantaba sa wani ɗa namiji a rainaba bare ayi batun soyayya saboda inada wanda nakeso wanda tunbansan kainaba nake kyaunarsa tare da soyayyarsa na girma nasan koni wacece wannan wanda nakeso ɗin ba kowa bane face yaya Raihan banida wani buri daya wuce naga na mallakeshi yasoni fiye da yadda nakeson sa amma kash baima son inayiba tsawan wadanan shekarun bantaba wasan faɗawa waniba bare a taimaka min gashi ƴar uwata uwa ɗaya uba ɗaya tana matukar yimasa soyayyar da bata iya boyewa ni yazanyi nasan wallahi mutuwa zanyi idan har bansamu Raihan a matsayin miji ba please dan Allah maryam ki tausayamin karki kara sani acikin zancen auren ku idan ba hakaba zuciyata zata iya bugawa nasan kuna san junanku babu yadda zaayi nayi muku kutse acikin soyayyarku na rungumi wannan a matsayin kaddarata idan nacinyeta shikkenan idan kuma zuciyata ta buga namutu shikkenan ,takarasa maganar tana fashewa da kuka


Tunda Amal tafara magana maryam take hawaye cike da al ajabi dan tayi matukar tausaya mata Allah sarki duniya kenan

acikin zuciyar maryam take tunanin toko tafaɗa wa Amal gaskiyar lamari auren yarjejeniya suka shirya yi da Raihan wata zuciyar kuma tace karta faɗa idan tayi haka tamkar ta karya al kawarin da suka kullane kuma idan ta rushe yarjejeniyar tasan zamanta agidan yakare Allah ne kaɗai yasan irin tashin hankalin dazata fuskanta koga YASIR ma daya ɗau aniyar wula kanta mata rayuwa





Please my panc comment and share fisabibullah 🤝





✍🏻
Zee ƴar mutan libya ce
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲






AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA





STORY AND WRITING by ZAINAB AHMED YUSUF HAƊAJA
MRS Abzee






PAGE 2️⃣1️⃣⏮️2️⃣2️⃣

Bismillah




" Amal nayi matukar tausaya miki bantaba ganin mace mai juriya wajen soyayya kamar keba amma Amal ni ina ganin mai zai hana kifaɗawa yaya Raihan kina sansa karki damu da ganin ni matarsa ce wallahi indai ya amince miki banida matsala zamuyi zaman lafiya abinmu

" maryam kenan bakisan wanene ne yaya Raihan ba kawai jin sunansa kike, shi a rayuwarsa bayasan maganar aure shekararsa 40 amma baya damuwa da rashin iyali anyi tunanin kobashida lafiyane amma ga dukkan alamu lau yake kamar kowani namiji mai lafiya,abinda nakeso maryam ki manta da maganata aurena da yaya Raihan bazai taba yuwaba kawai abu ɗaya zakiyimin maryam kijajirce wajen saka ido acikin wannan

Please Login or Register in order to submit comment