Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ajikinta tamkar sabuwar amarya gashin kanta yasha gyara shima kanshi kamshi

Zaune yake yagama shirinsa na bacci tsab yana danne danne a computer yaji daddaɗan kamshinta mai sanyaya zuciya lumshe ido yayi yazare siririn gilas ɗin dayake idonsa ya ɗago fuskarsa cike da fara a yace ," maman boy zonan tawan , hararar wasa ta watsa masa sannan ta faɗa jikinsa cikin sigar shagwaba take cewa , " hubby kasanfa banasan kana danne dannen computer nan da dare saboda wannan lokacinane bana office ba, dariya yayi yana wasa da yatsunta yace , " afuwan ai yau ruwan soyayyar da kika shayar dani agidannan ce ta mantar dani abubuwa da dama ciki kuwa haddani kaina babu abinda nake tunawa sai ke da kuma tsantsar soyayyar da nake miki shaf na manta inada wasu bayanai da zan tura sai yanzu na tuna ,

" ok to shikkenan na huce ai kai shalelene baka laifi, ta faɗa tana rufe computer ta ajiye a gefe , kwanciya tayi ganin haka shima yasa ya kwanta ya kan kameta a jikinsa sosai yana wasa da gashin kanta

Maryam tunda suka dawo ɗazu take jujjuya magan ganun da Ame hauwa ta faɗa mata tabbas yakama tayi taka tsan tsan idan ba hakaba akwai matsala babbah , tana cikin wannan tunanin ne taji wasan da Raihan yake mata da sauri ta ɗaga kai ta kalleshi tana cewa , " hubby nifa gaskiya nagaji kabarni na huta haka idan na biye maka kai ba gajiya kake da wannan lamarinba, tafaɗa tana turo baki

Dariya mara sauti yayi yace , " ai ko ana gajiya awannan bangaran ni bazan taba gajiya dakeba hubbah amma tunda kince kin gaji ba matsala ki huta abinki masoyiyata nasan zaki bani anjima ai ko , yafaɗa yana kashe mata ido ɗaya , kai kawai ta gyaɗamasa ta kwanta

Tsakiyar dare maryam ta farka cikin firgici tsoratar da tayi ne yasa tayi kara tana jujjuya kanta tana rirrike zanin gadon da sauri Raihan ya farka yana salati ya kunna fitila ya jata jikinsa yana jijjigata haɗi dayimata addu,a yana kwala mata kira

Cikin gigita take cewa , " zasu kasheni zasu rabani da ɗana zasu rabani da mijina wannan wace iriyar kiyayyah kuke masa mai yayi muku naga ɗan uwankune , Raihan ya rasa yadda zaiyi da maryam ya tsorata hakan yasashi haɗe bakinsa da nata yana mata kiss ta wannan hanyar ne kawai zatai shiru

Aikuwa lub tayi sai wani dogon numfashi da take ja yana iya juyo bugu zuciyar ta buɗe idon da tayi tana kallonsa ne yasashi cire bakinsa daga nata cike da tausayi yake shafa kanta ,

Ruwan sanyi tasha dukda haka tana jikin Raihan gaba ɗaya jikinta kar karwar tsoro take bataso tako tuna irin tuggun da taga an haɗawa mijinta amafarki , rintsa ido tayi tana furta , " Allah na gode maka dakasa mafarki nake ba gaskiya bane , tafada tana mai kwantar da kanta a faffaɗan kirjin Raihan hawayene suka shiga gangaro mata adai dai lokacin da ɗan cikin ta yayi zullo dan shima yasha wuyar fizge fizgen data dinga yi

Cikin sanyin murya Raihan yace mata , " me yake faruwane maryam tunanin me kikasa a ranki da harkike mafarkinsa haka ??, yafaɗa yana kafeta da idanuwa , " babu babu komai Raihan babu komai , kawai abinda tace kenan ta mike tashiga toilet ta ɗauro alwala ta duba agogo karfe uku na dare doguwar riga har kasa tasa ta ɗora hijabi ta tada sallah

Raihan bai gamsu da amsar data bashiba dan danan yashiga nazarin mai yake faruwane haka tabbas idan bai mantaba tana yawan nuna masa ƴan uwansa basasan zamanta dashi tokodai sune suke mata wani abun da har tsoransu yasa take mafarkinsu, ya tambayi kansa sai kuma ya jijjiga kai yana tunanin irin soyayyar da ƴan gidan suke nuna mata musamman ma iyayen sa Ame hauwa tana matukar nuna mata kauna kamar yacce zata nunawa yasmin tanasan jan maryam ajiki sai dai ita maryam ɗin dataki bata haɗinkai , tuna hakan ya kara tabbatar masa da bawata mishkilah



Washe gari da safe bayan sun kammala breakfast Raihan ya shirya tsab zai wuce office har bakin mota ta rakashi saida ya shiga yana kokarin tada motar yace , " sorry my wife yau zakiyi wunin gida ke kaɗai , karamin murmushi tayi tace, " inda sabo ai nasaba , " ok idan kingaba abinda kake zaki iya fita gidan Laulam kutafi gidan yayah aisha babbar yayarmu ta gidannan ana sa ranar, ƴarta kuma kowa da kowa na gidannan zaije , " wow daman kamar kasan ina marmarin fita naga gari bari zan kira anty laulam ɗin awaya naji time ɗin daza,aje

Nan sukai sallamah yatafi ita kuma ta wuce gida tana shiga taji wayarta tanata ruri dasauri ta ɗaga tana murmushi

" hello habibty yakikatashi , " lfy kalau sahibaty ina kika shiga ina kira shiru ko kina wajen yayan namune , " kamar kin sani wlh natafi rakashi zai fita office ne nabar wayar agida

" ayya shiyasa naita kira shiru yauwa dama kiranki nayi naji zakije gidan yayah aisha ana baikon ƴarta , " eh zani my husband yasanar min karfe nawa za,a , " zanzo gidanki anjima saimu wuce wajen anty Laulam mutafi baki ɗaya , " ok to sai anjiman , suka ɗan taba hira ta kashe wayar




****



Bassuna cikin fara,a da annushuwa take taya yayyanta girke girken taryar abbansu ,anty shafa ce tace , " gaskiya zuwan abbah yayi bazata wlh daker abban bilal yabarni nazo wai cewa yake asatinnan daya kama kullum ina hanyar gida , anty sana ce tayi dariya tana cewa , " aike kinsan zuwan abba saudiya sam baya amfani da waya gashi idan ya tafi saiyayi zamansa sai ana gobe zaizo zai kira waya yace zaitaho yasamu kimtsar dole

Itadai BASSUNA tana jinsu batasa bakiba Allah Allah take yadawo asanar masa da lamarin aurenta tanada yakini abbanta zaisa su kaita ɗakin masoyinta


Misalin karfe biyar na yamma jirgin abba ya sauka bayan an taryoshi cikin farinciki da annu shuwa kowa ya hallara a babban parlor har yayyansu maza anata hira

Abba ne yakalli bassu yana lura da tayi shiru bata fiya sa baki a hirar ba sai anyi abin dariya ta kyal kyale da dariya , " aa auta ta amarya bak i bani labarin yadda lamarin biki ya wakana ba kuma kunyi shiru baku nunamin hotunan bikinba

Dukansu gurin yayi tsit suka shiga yin kallon kallo anty jawahir tace , " ai abba dayake ita amaryar bata tareba

Da sauri abba ya ɗago yana kallon jawahir soyake ya gasgata abinda take cewa maida ganinsa yayi ga mamansu yace mata , " maiya faru an ɗaura aure bakukai yarinya ba ??,

Yayah ma,aruf ne yace , " abba matsala aka samune mijin bashida tarbiya munsamu wani video nasa dayake aikata abin Allah wadai a yayin da ake shirin kai masa matarsa , " kamar yaya bashida tarbiya kuma wace hujjace da ku ta hana miji matarsa ina bukatar ku fahimtar dani , abba ya karasa faɗar maganar yana bin kowannen su da kallo cikin zuciyar sa kuwa ransa ba karamin baci yayiba dajin wannan zancen

Mahaifiyarsu ce ta karantawa abba duk abinda yafaru , sosai ran abba ya baci cikin fishi yake cewa

" wannan wane irin sha shancine ma,aruf da girmanka zaka aikata ko wanene wannan yaro kuma komai ya aikata bakada hurumin rike masa mata kace wai bashida tarbiya bayan kasan daga gidan daya fito banji mamakiba amma kun zubarmin da mutumci da kima saikace bakusan yakamata ba da girmanku kuma kema maman yara kina ji kina gani aka aikata hakan meruwan ku da wani video wanda duk yadda akai makiyane suka shirya masa hakan a daren auransa dan su bata masa suna ku kuma kuka basu damar nasara

Sosai abba yayi musu wankin babban bargo sannan yabawa ma,aruf umarnin ya kira masa FERAS a waya yace yazo yana san ganinsa gobe da safe



Haka kuwa akai da safe misalin karfe goma FERAS yazo gidan BASSUNA sai murna take takasa boye farincikin ta bayan sungai sane akai masa iso ya shiga parlorn da abba yake

Dauke da sallamah abakinsa abba yana kishingiɗe akan kujera yana ɗaga kai sukai ido huɗu da FERAS

Wata iriyar zabura FERAS yayi cike da firgici bakinsa yana rawa yace , " kaine abban BASSUNA, abba shima cikin mamaki yake jijjiga kai cike da al,ajabi yace

" nutsu yaro kazauna kadaina wata fargaba magana zamuyi dakai , hawayene yafara kwarara a fuskar FERAS yana jinjina ikon Allah yake cewa , " inata nemanka na nemi gafarar ka babbah amma bansan inda zan samekaba hakika na aikata babban kuskure a rawuwata na wula kanta ka danayi ni nasan ba zaka taba yarda ƴarka ta zauna dani ba amma babah wallahi yanzu nagyaru sosai rayuwa ta koyar dani darusa da dama

" murmushi abba yayi irin nasu na manya yace , " banji mamakiba na ganin ka danayi a matsayin sirikina kuma kada kayi tunanin abinda kamin a baya zaisa na chanza ra,ayina na baka ƴata ,

FERAS yanajin haka ya karasa inda abba yake ya dafa kafafunsa yana hawaye yace , " nagode abba nagode wallahi inasan matata Allah ne kadai yasan halin dana shiga a lokacin da suka hanani ita bazan taba yafewa kainaba idan har baku yafemin ba ,

" bakomai yaro amma yanzu kaje gida inaso zanyi nazari dan tabbatar da maganarka na cewa kagyaru duk da naga hakan a tattare da kai amma ina bukatar kwakkwarar hujjah

Hannu FERAS yasa ya rufe fuskarsa da tafin hannunsa yana kuka zuciyar sa ce ke masa radaɗi da azaba gakuma tarun nadamomi da yake fuskanta a rayuwarsa lallai duk wanda bai ji tsoran Allah ba ya shiga uku

" bakomai abba ina sauraran ka fatana Allah ya tabbatar mana da mafificin alkhairi kuma na gode maka sosai daka fahimceni , " bakomai yaro Allah ne abin godiya

Nan FERAS yatashi jiki babu kwari idanunsa sunyi jajawur saboda kuka farar fuskarnan dukta dame kallo ɗaya zakai masa ka hangi tashin hankali a tattare dashi

Yana fitowa harabar gidan BASSUNA ta karaso itama fuskarta duk babu fara,a ta tsaya agabansa cikin sanyin jiki tace , " mijina mai yake faruwane duk yadda akai baku daidaita da abba ba kuma naga fuskarka babu wal wala gashi har zaka tafi bamuyi sallamah ba

Sun kuyar dakai yayi yanaso ya boye mata hawayensa yace , " kiyi hakuri bassu bana tunanin abbanki zai amince na zauna dake saboda akwai wani mummunan abu daya faru a tsakanina dashi abaya ,

Cikin sauri ta ɗago kai ta kalleshe cike da tsoro tace , " wani abune wannan haka , tafaɗa tana kafeshi da idanuwa , nisawa yayi yace , " kinsan komai game da rayuwata tabaya kafin Allah ya shiryeni nayi abubuwa da yawa kuma na wulakanta mutane marasa adadi ciki kuwa harda abbanki
Akwai wata rana da muka fita yawo nida abokina YASIR a wani babban titi muna gudu a mota duk wanda ya ganbu bamu hanya yake danni kaina shaidane mutane suna tsorona to sai aka samu akasi abba yana cikin wata jar mota yana tafiya ahankali nikuma ganin bai kaucemin ba yasa nadaki bayan motarsa kuma nayi parking cikin mutane naci masa mutumci namareshi kuma nasa ya lalata motarsa mai tsada saboda ina ganin na fishi arziki , FERAS bai iya karasa maganarba kuka ya kwace masa tamkar wani karamin yaro ,

Itama BASSUNA kuka take tana furta innalillahi wa inna ilaihir raju,un kamari babana fa kace kamareshi acikin bainar jama,a kaci masa mutumci , ta girgiza kai tana hawaye tajuya zata shige gida , da sauri ya rike mata hannu yana bata hakuri ta fusge hannunta cike da hassala da bacinre tace , " kai ba mutumin kirki bane yanzu na tabbata kuma karka kara kirana da sunan matarka na tsaneka tunda ka wulakanta min ubah , tana kaiwa nan a maganarta ta juya ta rufo kofar shiga gidan nasu ji kake garam

FERAS kafafunsa kasa ɗaukan sa sukai dan azabtuwar da zuciyar sa take masa ya daɗe a kofar gidan yana tsugunne kozaiga fitowar BASSUNA yabata hakuri amma babu wanda ya fito hakan yasashi ɗaukar motarsa yabar gidan

A bakin get ɗin gidansu yayi parking baiko kashe motarba ya shiga gida yana zuwa ya tadda Ammee azaune a parlor tana jan charbi karasawa yayi gaban ta yana hawaye ya kwantar da kansa akan cinyarta shshshekar kukansa kawai kakeji tamkar wani karamin yaro

Hankalin Ammee ba karamin tashi yayi ba da sauri ta ɗago kansa cike da fargana tace , " maiya ke faruwa ne ya kukai da iyayen nata , " Ammee nayi nadama kuma nayi kuskure nan ya kwashe labarin abinda ya faru yasanar mata sosai ta jinjina lamarin cike da damuwa tace , " karka damu FERAS Allah yasani kashiryu kuma insha Allah bazaka kara aikata kuskuran daka aikata ba ba komai insha Allah bazasu hanaka matarkaba zasu baka abarka da yaddar ubangiji ni mahaifiyarka ina tayaka da addu,ar samun nasara a rayuwarka

" Ammee babbar damuwata BASSUNA tace bata sona ina mata magana ko saurarena bataiba kuma wallahi inasan matata idan har na rasata mutuwa zanyi bazan taba rayuwaba zuciyata bugawa zatai






Comment and share
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲





AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA






✍🏻 by zee ƴar mutan libya






PAGE 8️⃣7️⃣⏮️8️⃣8️⃣

Bismillahir rahmanurrahim










Maryam tagama shirinta tsab cikin wata ha ɗaɗɗiyar liffaya mai duwatsu kalar gold sosai ta amshi jikinta ta mata kyau matuka

Bawata kwalliya ta ciki a fuskarta ba fauda kawai ta shafa tasa man lebe tafeshe jikinta da turare bayan ta zizara kwalli dayake matukar fitomata da asalin kyanta , wayar tace ta hau ruri tana ganin mai kiran ta saki wata fara,a ta katse kiran ta kunnah data ta hau WhatsApp, wani murmushin ta kuma saki sakamakon ganinshi online da tayi da sauri ta danna mishi video call

Daga bangaran Raihan kuwa yana ganin ta kirashi video call ya saki wani kayataccen murmushi ya shafi gyemunsa ya ɗaga ,

Maryam tanayin tozali da kyakkyawar fuskar mijinta ta saki wani irin murmushi mai ɗauke da ɗunbin soyayyah tace , " Assalamu Alaika ya zaujee , " wa,alaikumussalam ya hubbah ykk yagidan ya baby na , " lfy kalau ya aikin danna ganka zaune a office nasan yanzu hakama bazai wuce kana nan kana latsa latsen computer ba kona chanka ,

Dariya yayi ya haska mata kan tebul ɗin dake gabansa yace , " kin chanka kuwa dai dai hubbah kingani wlh yanzuma haka aikin nake kika kira amma gaskiya ganinki danayi hakannan sai yasani naji duk na kwaɗai tu yamma tayi na tashi nazo wajen iyalina dan wannan kwalliyar ta fusgoni wlh , dariya mai sauti maryam tayi cikin jin daɗin maganarsa tace , " haba habibina kabari lokaciyayi dan nasan zaka iya tahowa yanzu kuma ba lallai ka taddamu ba unguwa zamu gidan babbar yayah ,

" anya kuwa hubbah bazaki fasa zuwa unguwarnan ba nazo kawai muyi huta warmu , " hmm kai dai wallahi mijina na kasa gane maka tamkar wani ayuuu haka kake baka gajiya da soyayyah, tafaɗi maganar cike da zolaya , " hhhhh lallai yarinya ke kuma aikinfi ayu dan jarabarki tawuce musali gaki ƴar kan kanuwa dake amma lafiyarki har mamaki take ban tubarkallah masha Allah nasamu dai dai danine dole na koma ayuuu mu bawa juna kulawa , " hhhhh hakane mijina to Allah ya barmu tare nima ina matukar al fahari da samun nagartaccen namiji irinka ina sanka hubbina Allah yabar mu tare , tafaɗa tana kashe masa ido haɗi da yimai kiss yana kallonta

Wata kasalace ta saukar masa dan ya tabbata da yana kusa da abin zaifi armashi , " ameen summa ameen zaujati na amma me kuke jira har yanzu baku tafi gidan baikon ba , " eh wlh kaga da Amal nake jira sai kuma tace min YASIR ya hanata zuwa gashi kowa na gidannan ya tafi hatta anty Laulam ta tafi danace mata tare da Amal zamu zo to amma yanzu na kira anty Laulam ɗin na fada mata Amal bazata ba to tace gatanan zata dawo ta ɗaukeni tunda bai kamata ace kowa yaje amma banda ni ,

Jim kadan Raihan yayi yana kallonta kamar yace tafasa sai kuma yace , " to ba damuwa Allah ya dawomin da iyalina lfy amma kar ayi dare koda yake zanzo in ɗaukeki anjima karfe biyar na yammah daganan sai na ɗan zagaya gari dake na kaiki gurare ki huta kafin dare yayi na kaiki gidanki na shimfiɗe ki a gado kiyi kyakkyawan hutu kinsanfa inaji da wannan ƴar ficiciyar matar tawa , " nima inaji da wannan ɗan tsohon mijin nawa shiyasa nake fatan kare rayuwata dashi koba komai nasan idan ina tare da shi nasamu al,jannar duniya kuma inada yakinin zama dashi zaimin silar samun ta lahirah , " insha Allah zaujati Allah yayi miki Albarka keda baby , " Ameen hubbina bari naje naji ana buga kofa inaga antyn tazo , " ok to ki kulamin da kanki sai kin dawo

Yauwa ta amsa masa ta kashe wayar ta ɗau jakarta tasa takalmi ta nufi kofa , anty Laulam ce tsaye tace , " yauwa maryam kinshirya to zo mutafi ke nake jira an taru sosai dangin ango har sunzo , nan suka shiga mota ba kowa a kwatas ɗin hatta mai gadi ma bayanan get a wangale sukai ficewar su

Suna tafe a hanya maryam tanata zubawa anty Laulam labari amma shiru kakeji bata wani amsa mata duk ta sauya mata fuska sai wani murmushi da take saki lokaci zuwa lokaci ga gudu da suke shararawa tamkar zasu tashi sama

Wajen awa guda suna tsala gudu sannan suka isa wani guri mara mutane ko abin hawa babu a wannan titin shima saida suka shanye tafiyar kusan rabin awa sannan suka fara nutsa tsawa cikin wani jeji jeji , maryam kam duk ta kosa su sauka dan ita yanayin da taga anty Laulam ta sauya maya yasa duk taji wani iri gani tayi sunyi parking a wani karamin gida da kuma wasu motoci guda biyu a gidan abinda yabawa maryam mamaki gidan shikadai ne tallin tal acikin jejin babu wani maha luki , itadai maryam bata kawo komai a rantaba ta fito daga motar tana mamakin yadda duk kuɗi irin nasu hajiya babbah take zaune a wannan karamin gidan kuma jeji

Fitowa anty Laulam tayi tace , " to matar Raihan sai afitoko ga gidan muje , kai kawai maryam ta gyada mata tabi bayen ta

Suna shiga falan maryam tayi turusss ganin babu kowa a gidan sai yayah babbah da Ame hauwa da islam ,

" maraba lale da zuwa maryam ga guri zauna dan yau munada tattaunawa mai tsanani a tsakanin mu kafin mu aiwatar da kudirin mu , gaban maryam ne ya yenke ya faɗi dajin furicin hajiya babbah kenan hakan yana nufin sun hada bakine suka kawota nan , muryar anty Laulam ce ta katse mata tunanin ta da cewa , " to gashidai yau na tabuka abin arziki acikin wannan tafiyar dama Ame hauwa kullum kinamin gorin na kasa aiwatar da komai akan yarinyar nan yau gashi na kawo muku ita na tabbatar muku danibama ba koma baya bace a cikin wannan group ɗin naku

Wani sarawa maryam taji kanta yayi dajin maganar anty Laulam tabbas ta tabbatar cin amanarta tayi wato dama itama makiyarta ce bata taba nuna mataba , dafe kai maryam tayi tanajin yawun bakinta na neman kafewa yanayinta ya yi wani mugun sauyawa naganin abinda batai tsammani ba take hawaye suka fara kwararo mata cikin shakar kiyar murya tace , " menayi muke anty Laulam dama kema ba kaunata kikeba bakinku ɗaya , " eh maryam ni ban taba sankiba kuma bazan sokiba nashiga jikin kine danna ɗauke miki hankali daga gano kullalliyar da take cikin gidannan dukanmu da kike ganinmu nan bakinmu ɗaya kuma duk wani tuggu da munafurci mu muke shiryashi dan har kisan kai munyi kwatsam munanan muna filan dinmu akan yadda zamuyi mu kwace dukiyar dake hannin mahaifin Raihan murabe a tsakanin mu sai kikawani faɗo mana cikin rayuwa kika auri Raihan wanda sanadin auren ne ya rusa mana duk wani shiri da yanzu wannan dukiyar tazama tamu amma kin karya duk wani alkhadari asirin da mukaiwa Raihan na shekara sama da ishirin akan karyayi aure rana tsaka kika rusa mana shi shiyasa yanzu zaki karbi hukunci dai dai da yadda kika aikata hadda wani sakin jiki ki kwashi ciki kinga ko ba komai kya kwashi gado

Ame hauwa ce tace , " ita ta isa taci sile daga dukiyar da mukai shekara da shekaru muna harin yo ke dolamafa yarinyar nan ta karbi wannan mummunan hukuncin dan ni tunda nake bantaba ganin mutumin da nakeyin aiki ya tsarwatsamin ba irin wannan tsintacciyar bakar magen da bansan uban wane ne asalintaba , tafa hannuwa islam tayi ta tashi ta karaso gaban maryam tana watsa mata wata iriyar harara tafara magana da cewa ,

" bana faɗa mikiba dole na auri Raihan ba to ganasara ta nan tafara samuwa kinga daga wannan gurin babu wanda zai kuma jin labarinki har gaba da abada kuma zamuyi amfani da wannan damar bayan mun kasheki mucewa Raihan kin koma daularku kinsace masa kuɗaɗe kin kwashe kayanki kintafi kuma dama baisan ke wacece ba kuma baisan daga ina kika fitoba dan dama mu munji labarin cewa waliyinki na karyane karshedai Raihan zai tsaneki zai tsani wannan tsinannan cikin naki dan dukan ku zaku mutune nikuma naje nayi rayuwa dashi ni kaɗai , takarasa maganar tana shekewa da dariya

Yayah babbace itama ta taso ta karaso gaban maryam da tayi mutuwar tsaye itama kanta batasan yanayin da take cikiba zabga mata marin da taji anyine yasata ɗagowa a furgice sukai ido huɗu da yayah babbah ta kuma wanka mata wani marin da saida maryam tajishi har kwaryar kanta dake barazanar tarwatsewa saboda yanayin yadda takejin sa idanunta sunyi jajir takasa ko ɗaga baki tayi magana hawayene ke fita a idonta wani nabin wani

" maryam kinsan waya shirya duk wannan tuggun to nicenan hajiya babbarsu ni nafi kowa tsanarki maryam shiyasa nayi amfani da ranar baikon ƴata danna kawo karshen ki Allah sarki gaki yarinya karama amma kinshigo DAULATUL ARAB daular da babu wani mahaluki daya isa yazo yayi mana abinda kekikai mana bama karbar asara bama karbar faɗuwa amma ke kina rusa mana shiri faɗamin meyasa hankalin Raihan ya karkata gareki har muka kasa cin nasara a kansa meyasa kika zurfafa bincike akanmu gashi kin gano mutuwarki

Sai a wannan karon maryam ta ɗago jajayen idonta dasuke zubar da hawaye fuskarnan rure da wutar kiyayyah da ɗaukar fansa tace , " saboda soyayyah ce nace miki soyayyah ce yasa na rusamuku duk wani bakin tsafinki batare dana sani ba soyayyah ce tasani saka ido a al,amuran mijina harna gano kuɗin macutane musamman ke Ame hauwa , maryam ta maida ganinta ga Ame hauwa cikin ɗaga muryar ta cigaba da cewa

" kin cuci kanki kinyi asarar duniya da lahira ɗan daya ɗaukeki uwa shizaki tarwatsawa rayuwa ɗanda bashida buri daya wuce na ganin farin cikinki shizaki rusawa nasa farincikin , sai kuma ta maida ganinta ga anty Laulam tana nunata da yatsa tace , " Allah ya isa bazan yafe mikiba Laulam kin cuci yardar da take tsakanina dake kuma insha Allah kona mutu sai kunnuwana sun jiyemin labarin wulakantar ki acikin wannan duniyar ke kuma islam har yanzu bakida maraba da dabba kamar yadda na sanar miki wancen lokacin bazan taba baki satar amsaba akan waɗannan miyagun mutanan amma zakigani gaki ga duniyarna

Kan marwan ta rufe baki ji kake kwalllll sautin wani katan karfe da hajiya babbah ta daki kan maryam dashi , zubewa maryam tayi kasa sharaf tuni jini yafara zuba daga kanta

Murmushi Ame hauwa tayi tace kinmin daidai hajiya yayah kuma babbah gashi ta mutu abanza ko shurawa bata karaba yanzu abinda za,ai ku kira rasta ya ɗaukemana ita ya kaita waje mai nisa ya binne





*****
Misalin karfe uku na yamma Raihan yana office amma duk ya rasa nutsuwarsa gabansane yake faɗuwa duk

Please Login or Register in order to submit comment