Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƴan uwanka masu kaunarka sannan kuma yanzu zan kasheka , tana gama faɗin haka yaji motar tayi wani cijewa ta daki gefen ginin kan kadar ai kuwa nan take ginin ya rushe daga motar har FERAS ɗin dake cikinta suka faɗa wannan babban taikun da ko jirgin samane yafaɗa yagama yawo nutsewa zaiyi bare kuma motar






Please comment and share fisabibullah 🤝





✍🏻
ZAINAB AHMED YUSUF HAƊAJA
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲





AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA







By
ZAINAB AHMED YUSUF HAƊAJA
MRS Abzee






PAGE 3️⃣7️⃣⏮️3️⃣8️⃣

Bismillah






Faɗawar motar keda wuya ta nutse cikin babban tekun babu shiri FERAS yafara kokarin fita daga cikin motar amma ina yakasa duk yadda yaso ya gwada kokarinsa ya gagara har ruwa yacika motar taf dukda mai tsadace hakannema yasa ruwan jinkirin cikata amma yanzu tayi makil

FERAS yafara ɗuɗɗukar ruwa har ya wuce minti ishirin sannan a hankali kyawawan idanunsa sukafara lumshewa alamun komai yazo karshe alokacin da tunaninsa yazo taki babu abinda yake tunawa sai Ammeen sa da kannansa mata da shaikh Ali ,da wannan tunanin FERAS ya wula duniyar dazaka iya kiranta da mutuwa dan gaba ɗaya komai nasa ya saki gashi acen kasan teku kuma acikin mota


Gidansu FERAS kuwa da magriba bayan shaikh ali yadawo daga masallaci Ammeen su take tammabaya ina FERAS , cike da damuwa shaikh ali yanemi guri yazauna kusa da mahaifiyar tasu sannan yace ,

" Ammee karki damu kanki ai tunɗazu FERAS ya haɗe abinda yake bukata yabar gidannan amma karkiji komai nasan idan ya huce zai dawo , cike da damuwa Ammee ta girgiza kai tana cewa , " inaji ajikina kamar da matsala tun ɗazu gabana yake faɗuwa kuma kasan halin FERAS da zuciya karyaje ya aikatawa kansa wani abun , kasanfa wannan tafiyar ta musamman ce tunda nida kaina na koreshi bawai shiya tafida kansa ba

" Ammee duk kidaina tunanin haka insha Allah babu wata matsala amma tunda kin damu bari nakirashi a waya nasan zai ɗaga kodan yaji kince kin hakura kin yafe masa , nan shaikh ali yacuro wayarsa ya dannawa FERAS kira amma wayarsa a kashe , dama da layuka uku yake amfani amma duk layin da aka kira a kashe yake sosai hankalin Ammee ya daɗa tashi cikin kiɗima da nadama, tasa akira wani daga cikin abokansa , nan kuwa aka kirashi shima abokin nasa ya shaida musu bai ganshiba ,

Shaikh ali ya dage sai rarrashin Ammee yake a haka su aisha da gazzal suka tadda su suma suka zauna suna tayashi rarrashi , aisha ce tace , " Ammee kiyi hakuri kinsanfa halin yaya FERAS maibima kunyace ta isheshi ya kashe wayoyin dan yasan bai kyautaba , gazzal kuma ta kara da faɗin , " Ammee kinsan yaya FERAS da mako wallahi nasan duk inda yake bazai wuce kwana ukuba zai kiraki a waya yabaki hakuri kokuma kigama yazo dakansa ,

A hakadai suka lallaba Ammee ta hakura amma badan ranta yasoba dan ita kadai tasan yadda zuciyarta take luguda akan FERAS da wasu wasin ko wani abunne ya faru dashi





★★★ Raihan rungume yake da maryam yana rarrashinta yana bata hakuri dan shi yama fita jin zafin abinda yafaru har Allah Allah yake yagama lallabata ya koma wajan YASIR dan wallahi bazai hakura da wannan cin mutumcinba , dan iskanci yabiyo matarsa hargida ya karya koffa yashiga yana naiman yimata fyaɗe wannan ai raininema ,

Cikin sassanyar murya ta sigar rarrashi yafara yiwa maryam magana da cewa ,

" dan Allah maryam kiyi hakuri nasan baa kyauta mikiba amma insha Allah daga yau YASIR bazai kara wannan kuskuranba kinsan abinka da ɗan shaye shaye maibi yashawone amma koma mai yasha namiki Al,khawarin ko kallon banza YASIR bazai sakeyimikiba ballantana yayi sha,awar taba jikinki

Maryam cikin muryar kuka tace , " yaya nifa bansan cewa banida gataba sai akan abinda YASIR yakemin kaduba ka gani kai shaidane tunkafin nayi aure yake bibiyata gashi haryau bai hakura ba , please idan da hali kacenza mana gidannan saboda wallahi ina tsoran watarana karya kuma dawowa kasanshi da taurin kai baya hakuri da duk abinda ya kwallafa rai

" maryam kenan kawaidai kintsoratane amma kizuba ido kisha kallo nidai ina fata bai yimiki komaiba ko ?, Raihan ya jefo mata tambaya haɗi da kafeta da ido yana tsoran kartace YASIR yayi mata wani abun , itama kafeshi tayi da idanuwa sannan ta girgiza masa kai alamar aa , sai yaji wani daɗi a ransa dan da hakan tafaru da baisan halin dazai shigaba

Afili kuwa saiyace , " kitashi kije kiwatsa ruwa kihuta ni natafi wajen papy dan musamu mu yankewa wancen bunsurun hukunci tunda yafara shiga gidajen mutane , yafaɗa yana mai kashe mata ido duk dan yaga tayi murmushi , amma saita kuma cure fuska ta zumbura baki tawuce dakinta



Raihan yana shiga gidansu yasamu papy da kannan sa su uku wato abu sultan mijin anty Laulam da abu Amal da abu shahida, sai YASIR da sukasa a tsakiya ,

Da sallamah Raihan ya karasa wajen yana zuwa ya zauna a kasa yana gaida iyayen nasa, cikin mutum tawa kowa ya amsa masa , jim kadan wajen yayi sannan Abu shahida ya fara magana da cewa , " wato Raihan munji shashancin da ɗan,uwanka YASIR yaje yana kokarin aikatawa a gidanka kuma munyi Allah wadai dajin wannan dan babu abin kunyar daya wuce wannan sannan munyanke masa tsatstsauran hukunci akan hakan tunda bashida mutumci

Raihan yanajin haka ya gyada kai yace " komai kuka yanke Abba daidaine dama na dade inaso muzauna Akan YASIR mu tattauna shikaɗai a gidannan yabuwayi kowa sai jawo mana zagi yake ,

Abu sultan ne ya numfasa yace ," kontar da hankalin ka Raihan ai komai yazo karshe dole yanzu yanutsu tunda bashi yakeda kansaba akwai magabatan sa bari kaji kukuncin da muka yanke masa

Abuna farko zai daina shigar banza ta yan iskan yara kuma mun hanashi shan giya duk wanda yaganshi da giya yasanar damu mukuma zamusa kayi masa dukan kawo wuka kuma daga yau yadaina yawon banza kasuwa zai dinga zuwa sannan sallah tadaina wuceshi dan duk inda mukasa kafa saiya sa , bayan wadanan hukunce hukuncen da muka yanke masa munyanke shawarar yimasa aure dan tunda kaga yafara rikiɗewa yakoma bunsuru aure yakeso duba da hakane yasa muka yanke shawarar haɗashi aure da Amal

Raihan yanajin haka yace , " Abba Amal kuma taya za,ayi a haɗa nutsatstsiyar yarinya da wannan tantirin ɗan iskan sanin kan kune duk cikin ƴan matan gidanan babu yarinya mai ladabi da biyayya ga nutsuwa kamar Amal , ni gaskiya a ganina wannan haɗin bayyiba idan aka hadasu wallahi cutarta zai dingayi

Abu Amal yanajin haka ya jinjina kai yayi gyaran murya yace , " gaskiyane maganar ka Raihan amma mu a hangenmu babu wadda ta dace a haɗasu aure sai Amal ɗin tunda itace mai kamala hadi da addini mebi tazama silar shir yuwarshi , dan kuwa idan har mukace zamu haɗashi da islam ko shahida ko safeeya duk kanwar jace maimakon gyara saidai a bata , idan kuma mukace zamu fita waje munema masa matar aure to babu wani uba dazai yarda ya haɗa auren ƴarsa da YASIR dan kuwa duk garinnan babu wanda baisan halinsuba shida wannan tantirin uban gidan nasa FERAS

Jinjina kai Raihan yayi alamar hakane sannan ya juya ganinsa ga YASIR yakara koramasa kashedi da cewa , " kai kaji duk abinda aka kafa maka kuma wallahi ko mutuwa zakayi saika bisu sannan duk ranar dana kara ganinka da abokin danasan mashayine ma wallahi saina saba maka kamanni gidana kuma ko gobe ka koma kasan dukan dana maka yau kuma kai ko jakine akace amai maita maka shi bazaka yardaba , daga haka yayiwa iyayen nasa sallama yawuce gidansa


A daran kowani magidanci ya kaiwa matarsa labarin haɗin auren YASIR da Amal wasu suce Allah wadai wasu suce Allah ya kyauta , haka shima Abu Amal yaje yatara iyalansa ya shaida musu abinda aka yanke ommu Amal tanajin haka tahau surfa ruwan bala,i wai wallahi baa isa an cuci rayuwar ƴartaba an haɗata aure da bunsuri mai bin gidajen matan aure ba, ita kuwa Amal tanajin wannan zancen taji duk duniya tamata zafi danko hayaniyarma bata sanji hakan yasata shiga ɗakinta ta kullo kofar tafashe da wani wahalallan kuka tana cewa

" nashiga uku ni Amal yazanyi nikuma maizanyi da YASIR a matsayin miji kwata kwata bai dace daniba bazan iya yarda da wannan auren ba yazama dole nima na nemi ƴan cina nafaɗawa kowa ni yaya Raihan nakeso na huta ko asamu mai fuskantar lamarina akawo karshen damuwata



Nikam nace Allah sarki Amal kiyi hakuri wallahi duk wanda Allah ya jarabta to tabbas ɗan baiwane Allah yana sanshi shiyasa yake samasa jarabawa acikin rayuwarsa




Raihan bai koma gidaba saida akayi sallar isha , da sallamah a bakinsa yashiga gidan yana zuwa yaga gimbiyar bata parlor hakan yasashi nufar dining kai tsaye yaci abincin data shiryamasa sannan ya wuce ɗakinsa yayi wanka ya kwanta cen wajen karfe goma yaji yakasa bacci yanason yaje yaga halin da maryam take ciki baiji ko motsinta a parlor ba akasin kowani lokaci dayake jin zirga zirgarta

Da sallamah ya tura Kofar ɗakin nata yana shiga ya ganta cen karshen bed ɗinta ta cukuikuye jikinta da makeken bargo amma duk da haka rawar sanyi take da sauri yakarasa yana kiran " subhanallahi maryam lafiya kuwa na ganki haka

Maryam kuwa tana karkarwa ta fashe da kuka mai narkar da zuciyar mai sauraro , cen kusa da ita Raihan ya karasa ya rungumota jikinsa yana shafa kanta yana rarrashi yaji jikinta zafi rau zazzabine ya kamata

" gaskiya maryam kedai raguwace yanzu zazzabin kikewa kuka haka menene abin kukan a zazzabi , maryam kuwa gallah masa harara tayi tana kara sautin kukanta , cike da mamaki yake rarrashinta danshi baitaba ganin shagwaba irinta maryam ba wadda shi kansa yasan shikaɗai akeyiwa kuma hakan yana burgeshi sosai

Cendai yagaji yace , " to shikkenan kitashi kiwatsa ruwa kisha maganin zazzabin inadashi bari na ɗakkomiki maza tashi ki shiga toilet, yamutsa fuska tayi tana wani haɗagirar sama data kasa tashiga toilet ta watsoruwan zafi aikuwa tana fitowa taji sanyi yarufeta bakinta sai rawa yake

Ahaka Raihan yazo ya taddata daga ita sai rigar wanka, sosai taburgeshi ganinta haka amma saiyawani basar yamurtuke fuska yace ," dalla malama menene hakan zakizo kiwani zaunamin tsirara acikin gida kuma saina dankeki kice na lalata miki rayuwa kina matsayin budurwa ko ? ,

Wani wawan kallo maryam tayi masa sannan ta gyara zama tace , " towaikai yaya mai ruwanka karfa ka manta ɗakina kashigo bawai ninaje nasameka ba amma ba komai ba laifinka bane tuzuranci ne yake damunka dan haka kasamu kayi aure ka huta kai ko acikin yaran gidannan ne kasamu abaka ɗaya gasu islam da Amal ,

maryam tafaɗa tana mai kashemasa ido dan tafaɗi su islam da Amal ne dantaji ya matsayinsu yake a wajenta

Shafa kai Raihan yayi sannan yace , " lallai ma maryam kin rainani wato ninema tuzuru to kike maganar nayi aure bayan wanda nayi ai inada aure kokin manta na tuna miki harda wani cewa wai ga islam da Amal yarandana rukesu suna jarirai kumama dan kin rainamin hankali kiwanice na aure su gwarama ke zan iya zama dake a matsayin abokiyar rayuwa tunda banrikeki a zanin jarirantaka ba amma sukam ko aka bansaba ni ba sa,ar yarinya bace kema saa kikaci ,, yafaɗa yana kashe mata ido ɗaya

Wani sanyi maryam taji a ranta sannan tace , nikuwa ya kukayi da YASIR ina fatadai anbimin hakkina , dariya Raihan yayi yace , " sosai makuwa ai hukuncin da aka yankewa YASIR yayi tsauri dayawa amma kinsan ni menene baiyimin daɗiba waidanaji sunce zaa haɗa YASIR aure da Amal,

ruke baki maryam tayi a lamar mamaki tace , " nabani nikuwa ina Amal ina YASIR ai baa haɗa wuta da ruwa yanzu ya Amal zatayi dannasan wallahi ko akafa aka ɗaura mata YASIR zata kunce ta gudu saboda mugun halinsa ,

" hmm kedai bari maryam wannan abun nima ya tabamin zuciya idan akaiwa yarinyar nan haka sam baa kyauta wa rayuwarta ba amma dai nibanida tacewa mebi kiga Amal ɗin ta amence dan YASIR kyakkyawane gashi yaro

" lallai kam ba irinkaba tsohoko , " haba yarinya ina tsufan yake kinaso kina kaiwa kasuwa ai yanzu ƴan mata irinmu sukeso dan a cewarsu munfi iya kiwo ,

" lallai saikace da gaske ni banga abin so anan ba ,

" hakaɗai kikace kibadakai bori yahau kiga ruwan kauna ,

" hmm yaya Raihan kafarako to nagode da wannan ziyarar tunda ka kawomin maganin kama hanyarka konayi maka ihun kwarto yanzu ,

" ihm lallai yarinya a darannan aji kina ihu ai sai ace daɗi kika kwasa tundadai ansan mata da miji ne a gidannan kuma wallahi kika kara cewa kala saikinsha tumurmusau yanzunnan tunda naga ke da anfara wasa da dariya dake saikin faɗawa mutane magana mara daɗi mara kunya kawai mitswwww , yaja tsaki yafice ita kuwa maryam tana dariya tayimasa gwalo








Please comment and share fisabibullah 🤝






✍🏻
Zee ƴar mutan libya ce
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲






AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA




By
ZAINAB AHMED YUSUF HAƊAJA
MRS Abxee






PAGE 3️⃣9️⃣⏮️4️⃣0️⃣

Bismillah





.....kamar wanda aka mintsina haka FERAS ya zabura yamiki sai yaganshi awani waje maikamada lambu wajen ya kayata da kayan itatuwa na ciye ciye gashi anyiwa wajen fasalin ɗaki amma ba ɗakibane saidai hadda wani kaya taccen gado mai bala,in kyau

Abinda yadada bawa FERAS mamaki shine wasu mata daya gani kyawawa farare marasa kiba susu shida duk kayansu kala ɗayane sannan kuma kunnuwansu ba irin na mutane bane irinna berayene a tsaye kai kana ganinsu jikinka zai baka ba irin jinsunmu bane

Cen yasa kafafuwansa ya sakko daga kayataccen gadon da aka kwantar dashi ga mamakinsa yana taka kasan ciyawar yaga wajen kamar glass acikin ruwa suke amma inda suke babu ko ɗugon ruwa saiwani dimima da kamshi wajen yakeyi , gashi yana hango kifaye kala kala ta glass ɗin da aka yimusu katanga da waje , azuciyarsa ya raya duk yadda akai wadanan ba mutane bane aljanun ruwane

Yana cikin tunaninne yaji daya daga cikin ƴan matan tace , " lah kunga bil,adam yatashi muje mufaɗawa sarauniya , biyu daga cikin matanne suka tafi faɗowa sarauniyar sukuma sauran suka kawo masa wani irin abinci wanda ko dabba bazata iya ciba bale dan adam shidai FERAS baice uffanba kawai tunani yake kala kala da kuma tsoro daya kamashi musamman idan ya tuna al washin aljana RUBBAH na kashe shi wanda shi a kankin kansa baisan abinda yayi mataba

Yana cikin wannan tunanin yaga wasu maza katti guda biyu masu irin kunnuwan matannan sunzo sun tafi dashi , duk da acikin ruwa suke amma duk inda suka wuce babu ruwa ko ɗugo dayake taba jikinsu , ahaka sukakai wata babbar fada mai cike da kayan kawa wanda gaba ɗayansu na zinarene sannan mutanan dake cikin fadarma sun banbanta dan kalar shigarsu ta alfarma da kuma kayan kawa da sukayi kalliya dashi na ɗanyen zinare irin na kasan ruwa ,

Cen suna tafiya aka kaishi wajen wani iyakar labule kato suka durkusar dashi yana durkusawa kafa fara bushe bushe da raye raye nan take labulen ya sauka kasa , FERAS yayi arba da wata haɗaɗɗiyar matashiyar budurwa mai bala,in kyau sufarta bata misaltuwa
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲





AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA






By
ZAINAB AHMED YUSUF HAƊAJA
MRS Abzee





PAGE 4️⃣1️⃣⏮️4️⃣2️⃣

Bismillah





...FERAS yana ɗaga kai ya kalli sarauniyar aljanun nan sai yaji gabansa yayi mummunar faɗuwa lokaci ɗaya jikinshi yaɗau rawa , murmushin da sarauniyar tayimasane yasashi jin dama dama lokaci daya wajen yayi tsit dukda tarin mutanan da suke rusune a wajen

Cen sarauniya ta buɗi baki da zazzakar muryar ta tace , " yakai bil,adam kozamu iya sanin kadan daga cikin labarinka dan kuwa munriga mungano abubuwa da dama a tattare dakai ,
FERAS yanajin haka ya ɗago kai sukai ido biyu da ita saiyaga idonta sak na mage , cikin sanyin jiki FERAS yace , " zan faɗa miki komai amma saikin fara faɗamin dalilin dayasa kuka ceceni ,

Murmushin bangirma irin nasu na sarauta tayi sannan tace , " munga kana bukatar rayuwane shiyasa muka ceceka har muka buɗe maka ido kasamu nasarar shigowa cikin daularmu ,

" to masha Allah, nidai bil,adamane kuma ba komaine ya kawoni ruwannan ba sanadin wata aljanace mai suna RUBBAH , nan FERAS ya kwashe duk labarin haɗuwarsa da aljana RUBBAH dakuma azabtar dashin data dingayi bugu da kari hatta tarwatsa masa Ahali datayi tacusa musu kiyayyarsa har mahaifiyarsa ta koreshi , saida yafaɗawa sarauniya


Sarauniyarnan tanajin labarin FERAS ta mike tsaye tayiwa kanta kirari da kakkausar murya sannan tace , " ni sarauniya UBAIDATU ƴar sarki HAYATUL,NASRIM nayimaka Alkawarin cetonka daga hannun waccen bakar Azzalumar kuma nida kaina zan muku shari,a da ita a wannan fadar da yardar ubangiji maɗaukakin sarki ,

sarauniya ubaidatu tana gama faɗin haka ta ɗaga hannunta sama nandanan saiga hayaki golding yana fita nan danan wasu manya manyan mutane guda huɗu suka bayyana , cikin fushi sarauniya tabada umarni aje a kawo mata ,Aljana RUBBAH, yanzu da azama dakaru suka kunna nutso izuwa neman RUBBAH duk inda take a faɗin duniya




★★★ Ana wata ga wata gidansu Raihan ya kachame kowa cewa yake auren YASIR da Amal bai daceba sukuma iyaye maza sunce wallahi aure babu fashi tunda ƴaƴansune

Amal kuwa tarasa inda zatasa kanta ko abinci bata iyaci kullum batada aiki sai kuka itabawai bakincikin auren YASIR takeba kawai tana takaicin zata rabu da soyayyar Raihan, dan tasan indai ta auri YASIR to babu ita babu saran zama mallakin yayanta Raihan gashi kuma tarasa tawace hanya zata sanar da wani damuwarta musamman yadda taga omminta dukta birkice akan auren wai ita adole baza,a aurawa jininsu Raihan ƴaƴantaba saboda ta tsanesu ko mutuwa za ayi bazata haɗa zuri,a dasuba

Shikuma Abu Amal yace aure babu fashi kuma idan ommu Amal ta matsa masa to abakin auren ta ,

YASIR kuwa tundaga lokacin da aka kafa masa dokoki yakebi sauda kafa dan gudun kar takuma gamasu da Raihan ya nakastashi a banza ,


Yaune iyayen YASIR suka bashi umarni dayaje ya gana da Amal su fahimci juna kafin afara shirye shiryen bika , haka itama Amal da magariba abbanta yakirata yasanar mata YASIR zaizo zance ta saukeshi a parlorn baki , Amal tanajin haka taji zuciyar ta kamar an kwara mata ruwan zafi cikin sanyin jiki murya na rawa ta amsawa abban nata dato dan babu yadda zatayi bazata iya bijirewa umarnin abbanta ba tabashi kunya

Shima karan kansa abu Amal yana matukar san ƴarsa dakuma tausayinta amma yafiyimata sha,awar auren YASIR dan wannan jahadine babbah kuma yasan ƴarsa da biyayyah bazata taba bijirewa umarnin mijintaba

Misalin karfe shida da rabi na magribah YASIR yaturo kanin Amal wai yakira masa ita , alokacin Amal tana kwance a ɗaki yaron ya shigo ya yashaida mata , saitaji gabanta ya faɗi idonta yaciko da kwallah amma gudun kar yaron ya fahimta saita wayance tace yaje yace tana zuwa ,

Amal koda da tashi shiri bawani kwalliya tayiba kawai hijabi ta zunduma har kasa taɗan fesa turare sama sama taɗau karamin charbinta tarike a hannu ɗaya hannun kuma wayarta , koda Amal tafito tayi saa bata samu kowaba bare su hanata , haka ta nufi parlorn baki dake hanyar get ɗin part ɗinsu , tana zuwa bakin kofar taji kamshin turaran YASIR ta dade kafin ta shiga da sallamah a bakinta kanta yana kallon kasa ta karasa ,

bayabo ba fallasa YASIR ya amsa sallamar ita kuma ganin haka yasa bata gaisheshiba dan zuciyarta cike take da tsanar YASIR

Jim sukayi acikinsu babu wanda yace uffan har nawani Ɗan lokaci sannan YASIR yayi gyaran murya yace ," nasandai kinriga kinji abinda iyayenmu sukace basaina miki karin bayaniba , kai kawai Amal ta gyada masa alamar eh sannan yakara da cewa ,

" Amal kinsan niba mutumin kirki bane to tun wuri kirufawa kanki asiri kije kice bakya sona bazaki aureniba idan bahakaba wallahi kece masha wuya danni babu ruwana abinda yasa nake baki wannan shawarar naga kinada hankali duk ƴan matan gidannan kinfisu nutsuwa to banason abinda zai jawo miki dana sani gara kisamawa kanki mufita danni dakike ganina babu abinda ya shafeni idan tayi ruwa rijiya idan bataiba masai ina fatan kingane abinda nake nufi ????,

Amal tananin haka ta share kwallar data gangaro mata tace , " tabbas hakane yaya YASIR nima bana sanka ko kaɗan kuma bana fatan rayuwa dakai a matsayin mijin aure , amma hakan bazai taba sawa nabijirewa umarnin abbanaba koda kuwa hakan zaiyi sular rasa rayuwata , amma ni ina ganin kaida kake namiki zaifi kyau ace kaje kasanar dasu baka sona bazaka aureniba kaga tunda ba ayiwa namiji dole maibi kaga sunfasa ,

Da sauri YASIR ya daka mata tsawa yana wuci ya mike yace ,

" daga baki shawara saiki wani gayamin magana to bari kiji wallahi kitabbata indai kika shigo gidana kin kare rayuwar farinciki da kanki zaki gudu , dan bakisan wanene YASIR ba kawai kina kallonane , ke inbanda dole ubanme zanyi dake yarinyar data taso a gabanmu tun kafin kisan kanki muka sanki harkikazo kikafara irgar dangi , sai yanzu dankinga kinzama mutum zakiyiwa mutane gwallin banza wani darene jemage bai ganiba harda wani zindimo hijabi kegamai tsarkakekken jiki , mitsuwwww

Yaja mata wani wawan tsaki , itakamdai Amal shuru tayi tana hawaye dan bataga maganar data faɗa masa mai zafiba da har zaimata wannan cin mutumcin , shikuwa YASIR yana gama yimata ruwan masifar yafice , durkushewa Amal tayi tana kuka take cewa , " nashiga uku ni Amal ta ina zan iya rayuwar aure da wanda sam baisan darajar ƴa maceba , rasa maibata amsane yasata tashi tana zubar hawaye ta wuce gida abinta



★★ ban garan su maryam kuwa yauma kamar kullum yadda ta saba haka ta shiryawa mijinta abinci ta gyara musu ko ina , misalin karfe takwas na dare Raihan ya dawo lokacin maryam tana parlor tana kallo tayi masa sannu da zuwa ya amsa , kai tsaye ya wuce bedroom ɗinsa yayi wanka

Harkusan karfe tara maryam tana zura ido kozataga Raihan yazo yaci abinci amma shiru hakan yasata shiga ɗakin tana zuwa taganshi kwance a bed ɗinsa yaɗaga kansa sama kamar mai bacci , da sallamah takarasa bakin bed ɗin ta zauna a gefe tace ,

" sannu da zuwa yaya Raihan, na shirya maka abinci kuma naga baka fito kaciba , Raihan yanajin haka yaɗanja karamin tsaki yace , " banida lfy yau banajin zan iya cin abincin saidai ki kawomin shayi da lemon tsami nasha

To kawai maryam tace ta tashi ta kawo masa abinda ya bukata sannan ta zauna a kan bed ɗin tana kallonsa , da alama koma me yake damunsa yanajin zafin ciwan duba da ganin yadda yake kankance ido yana cije lebe haɗi da shafar gashin kansa hakan yasa ta cewa , " nikam yaya inane yake maka ciwone naduba ko munada maganin na ɗakko maka ,

Raihan yanajin tambayar datayi masa yajuyo yawani wallo mata kallon zaki gane kuranki yace , " yauwa maryam nace ba kozakiyimin wani aikin kuɗi ne yanzu na biyaki ko nawa kike bukata , maryam tanajin haka tace " da gaske to aidama ni zaman kuɗi nake agidannan komai kasani indai zaka biya zanyi , Raihan yaɗago yawani sakar mata murmushi yace , " aikin bawani mai wuya bane sonake ki kwana a ɗakinnan yau kwana ɗaya tak nikuma zan baki dubu ɗari biyu kash hannu da hannu ,

Haɗe rai maryam tayi lokaci daya sannan tace " wow kuma kudin da tsoka to amma tsoran ɗakin kakejine dazakace natayaka kwana , murmushi yayi yace , " to ai kinsan mara lafiya kawai inaso ki kula danine kafin gari ya waye inyaso kinga idan nayi tashin dare dakko waccen miko wancen duk saikiyimin kafin gari ya

Please Login or Register in order to submit comment