Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ishirin tanayi jin batai shiru bane yasashi tashi yana tsaki ya sakko daga bed ɗin ya futo

Yana zuwa bakin ƙofar ɗakin nata yatura , cen kuryar gado ya hangi islam ko kwalliyar amaren bata cireba ta boye kanta a tsakanin cinyoyinta tana ta aikin kuka , ranshine yaji yabaci dan baisan da lilin da zatazo ta cika masa kunneba cikin hassala yace ,

" ke lafiya da daddarannan zaki zo ki cikawa mutane kunne ki hanani bacci , ɗago kai islam tayi cike da mamaki lallai Raihan wato madadin yazo ya rarrasheta hanasa baccima tayi , wani sabon kuka ta kuma fashewa dashi cike da kissa da shagwaba tace

" ni tsoran gidannan nakeji gurin ommina zani bazan iya kwana ni kadai ba , haushin tane ya kuma kamashi kamar wata jaririya zatace tsoro takeji lallai yarinyar nan aikuwa zai gwada mata shi waye , cikin rashin nuna damuwa ya nuna mata hanyar fita yace , " ok fito ki tafi tunda kinsan bazaki iya wannan rayuwar ba kika yadda da auren,

Gaban islam ne ya faɗi dajin zancen Raihan chab lallai akwai aiki a daran farkon ka ango yace ka tafi gidanku , wata sabuwar dabarar ce ta kuma shugowa islam cikin matukar damuwa da sunkuyar dakai tace , " nifa ba san aurenka nakeba kawai abbanane da papy suka yenke hakan amma ni inada wanda nakeso kuma tun wancen lokacin nace na manta dakai , " ok to aike mace ce yanzun idan kinje gidan saiki sanar musu kinada wanda kikeso su warware yadda suka ɗaura , yana gama faɗin haka yayi ficewarsa daga dakin yana jen tsaki ya koma dakinsa ya kwanta

Jijjiga kai islam tayi a zuciyar ta tace bakasan wacece islam ba wallahi dole kasaurareni amatsayin mata zuciya ta bazata jure wannan wulakancin ba , kayanta ta shiga cirewa tayi wanka ta saka kayen bacci ta duba agogo taga karfe sha biyu na dare turare ta ɗauka mai dadin kamshi ta feshe jikinta dashi sannan ta kalli kanta amadubi ba karya ita kanta tasan ta haɗu kuma kowane namijine ya ganta cikin wannan kayen dole ya tsunduma kogin sha,awarta

Fitowa tayi ta tsaya bakin kofar dakinsa bawani neman izini kawai ta tura tana shiga ta kunna kwai mai haske da sauri Raihan ya ɗago kai ya kalleta wata uwar harara ya daka mata yana cewa ,

" meya kawoki nan , " uhm uhm nifa yunwa nakeji tunsafe banci komaiba kuma ai hakkin ciyar dani akan ka yake ,

Kallon mamaki ya bita dashi lallai ba karya auran nan ya jamasa zubewar daraja da raini a wajen islam, tashi yayi ya karaso inda take yace , " ficemin daga ɗaki karna sake ganin kafarki a ɗakin nan idan ba hakaba wallahi sainayi kasa kasa dake nafada miki , “ wallahi bazan tafiba idan kuwa kaga nabar ɗakin nan saidai na fita daga gidannan gaba ɗaya

" ok haka kikace to fita dama ai bani na kawokiba shashasha mara hankali jaka mara tarbiya , yakarasa maganar yana figar hannunta saida ya kaita kofar gida ya turata saida ta fadi sannan ya danna key,

Kallon kanta tayi taga a yadda ya wullota waje cikin bakin ciki da bacin rai tasa kuka babu ko takalmi a kafarta ta wuce part ɗin su Ame hauwa,

Tana zuwa tayi sa a Ame hauwa ta fito daga kitchen cikin kuka islam ta karasa ta fada jikinta tana kuka

Cikin mamaki Ame hauwa tace , " lafiya ko dukanki yayi nidaman nasan Raihan bazai bari kuzauna kalauba , " Ame hauwa korata fa yayi cikin darannan ya wulloni waje wai bazan kwanar masa a gidaba , " lahhh ha ila wannan yaron wana irin mara mutumcine akai masa amaryar yau dinnan ya koroki aikuwa bari naje na samu papy ke ki wuce dakin yasmin tabaki hijab kisa zai gane kuransa ,

Ame hauwa tana shiga ta laburtawa papy ai kuwa cikin hassala ya futo yasa islam agaba suka tafi Ame hauwa na biye dasu a baya

Bugu papy yakeyi ba kakkautawa Raihan yana bude ƙofar yaga papy saida gabansa ya faɗi baiyi auneba jikake tasss tasss papy ya wanke Raihan da mari

" mutumin banza mutumin hofi naga ladan haihuwa na gode wallahi Raihan idan kayi wasa akan auren nan zan iya tsine maka albarka , da sauri Ame hauwa ta shiga tsakani tana salati tafara bawa papy hakuri sannan ta umarci islam ta wuce ciki

Raihan kuwa har kasa ya durkusa yana bawa papy hakuri amma bai kulashiba ya wuce , jiki babu kwari ya maida kofa ya rufe yana shiga ɗakin ya ganta tayi kane kane a kan gadonsa tana kukan muna furci

Raihan dan bacinrai ji yake kamar yayiwa islam dukan mutuwa yarinya karama ta hadashi da mahaifin sa , cikin takaici yace , " kin kyauta kinje kin haɗani da babana ,

" ba laifina bane kai kace natafi nikuma naga yanzu ba iyayenane sukeda iko akainaba shiyasa na tafi gidanku ,

Kai kawai ya gyada mata ya wuce ciki ya ɗau turaren maryam ya feshe ko ina na dakin dashi sannan ya yayi ƙatan bedshit ya shimfiɗa a kasa ya ɗora filo ya kwanta ,

Babu yadda islam zatai dashi haka ta hakuri ta kwanta a sama shi akasa amma ranta ba haka yasoba ,






✍🏻 ZAINAB AHMED YUSIF
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲





AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA





By ZAINAB AHMED YUSIF





PAGE 9️⃣2️⃣

Bismillahir rahmanurrahim






Kiran farko na asuba Raihan ya buɗe ido saiyaji mutum a kwance a bayensa yana juyawa yayi aran gama da islam ta wani kan kameshi tana ta shararar baci

Ransane ya kara baci ya tashi ya shige toilet yana tunanin ta hanyar dazai hukunta islam yadda papy bazai masa faɗaba danya fahimci yarinyar rainin hankalinta yakai makura

Bayan ya fito daga toilet dinne ya wuce masallaci , bayan yadawo daga masallacinne ya shigo ɗakin ya tadda yadda yabar islam a kwance haka ya taddata , murmushin mugunta yayi yaje ya bude Freezer ya ɗakko ruwa mai kan kara kankara ya daidaici dai dai fuskarta da kuma kirjinta ya soma tuttula mata ruwan sanyin

A zabure ta mike tamatukar gigicewa ihu kawai take amma Raihan bai daina tuttula mata ruwanba saida yakare tass yayi mata jangaf jikinta har tiriri yake cikin muryar kuka ta kalleshi tace,

" anya kuwa yaya Raihan kana tsoran Allah nifa matarkace , murmushin gefan fuska yayi mata sannan ya karaso daf da ita yana karewa jikinta kallo tundaga sama har kasa sannan yace , " bakikai matsayin dazanyi rayuwar aure dakeba ke matar dasu papy suka auro suka kawo gidannan ce dan haka kibude kunnan ki ki saurari abinda zan faɗa miki ,

Islam taso ta karacewa wani abun amma ganin yadda Raihan ya tamke fuska babu alamar wasa aciki yasata kame baki tayi shiru shikuma yacigaba dacewa ,

" daga yau karki kara yadda na dawo daga sallar asuba na taddaki kina bacci idan ba hakaba da ruwan kankara zan tasheki kuma duk wani aikin gidannan ki tabbata kinyishi danku malalata ne bakusan komaiba sai kuci ku kwanta nan ba gidan hutu bane wallahi kika sake gidana ya kazance jikinki ne zaiyi tsami sannan ki tashi kiyi sallah ki shiga kitchen kiyimun breakfast abu na gaba kuma wanda shiyafi mahimmanci islam zan miki gargaɗi na karshe kada ki sake kuskuran zuwa gidanmu kikai ƙarata idan ba hakaba wallahi saina azabtar dake yadda da kanki zaki zabi barin gidannan , mitswwww

" Allah Allah wallahi bazanyi ba aini ba baiwarka bace , Raihan harya fice yaji muryarta kasa kasa tana magana dawowa yayi a fusace yace , " mekikece wa , da sauri ta rike bakinta tana kuka ta girgiza masa kai ,


****


Yau ta kasance ranar asabar da farar safiya mahaifin BASSUNA yakira FERAS a waya yace yazo yana bukatar ganin sa , FERAS baiwani bata lokaciba ya shirya yaje

Cikin fara,a aka tarfeshi abinda yakara bawa FERAS mamaki ganin yadda yaya ma,aruf yasakar masa fuska sosai har hira suka ɗan taba aharabar gidan kafin amai iso ya karasa parlorn babansu BASSUNA,

Cikin ladabi da biyayya ya durkusa har kasa ya kwashi gaisuwa , shima baban bassu cikin sakin fuska ya amsa sannan yayi gyaran murya yafara da cewa ,

" wato FERAS Alhamdulillah bincike ya kammala mun tambayi dattawan unguwarku agame da halaiyarka sun shaidamana duk abinda yafaru dakai ada kuma sun tabbatar mana da ko ada ɗinma bakai biye biyen mataba sannan nasamu zama da ɗan,uwanka shaikh ali mun tattauna dashi yayimin bayani akanka sosai wanda ni na tabbata shaikh ali bazaimin karyaba kuma duba da yanzu kadai na duk wani shaye shaye dabin abokan banza ina mai farincikin sanar dakai ni na amince da tarewar matarka ɗari bisa ɗari ina fatan Allah yabaku zaman lfy kuma sannan inaso yau basai gobeba ka tafi da matarka ,

FERAS yanajin haka habawa kuzo kuyi kallon farin ciki tsabar murna sai da yayi hawaye babu abinda yake sai godiya , nan aka haɗawa BASSUNA kayenta nasawa a cikin mota nan bassuna tafito cikin kayatacciyar shigarta tayi kyau sosai duk ƴan uwanta sun rakota har bakin mota anatai mata addu,a dafatan zama lfy ,

Ba wata wata FERAS ya danna hancin motarsa kan titi yahau kwalta yafara sharara gudu , suna tafe yana satar kallonta itakuma ta sunkuyar dakai tana wasa da yatsunta , lura tayi yana kallonta hakan yasata ɗagokai da zazzakar muryar ta tace , " habibina dan Allah kayafemin namaka laifi , " amarya ai bata laifi hasalima nine mai laifi amarya ta karki damu wannan mijin naki babu ruwansa farincikin ki shine nasa , " nagode sosai habibina Allah ya kara haɗa kanmu yabamu zaman lfy , ameen ya amsa mata daidai lokacin da sukai parking a kofar gida

Saida yafito sannan ya karaso ya buɗe mata murfin motar ta fito yakama hannun ta suka shiga gida , a parlor suka tadda Ammee dasu aisha suna hira ,

Suna yin sallamah guri yaɗau shewar aisha da gazzal da sauri suka karaso suka rungume BASSUNA,
Ammee da take gefe tana dariya tace , " kubi a hankali karku kadata ,

Bayan sun zazzauna Ammee tayi farinciki sosai tanata jan bassu ajiki tasa aka kirawo jawahir da shaikh sukazo aka hadu akai musu nasiha sosai sannan akai ciye ciye aka shafa addu,a

Jawahir ce tace , " Ammee inaganin bassu ta zauna a wajenki kafin magariba tayi murakasu part ɗinsu ni kuma nidasu gazzal sai muje mudaɗa gyara mata part ɗin musa mata turaruka , " eh hakan yayi sosai ,


Haka kuwa akai bayan sallar magriba Ammee ta haɗawa BASSUNA ruwan wankan magani tashiga tayi wanka sannan aka haɗa mata na turaruka shima tayi , bayen tagama shiryawane aka rakasu ɗakinta ita da ango jawahir har video tayi musu yayin rakasu ɗakin nasu ta turawa ƴan uwanta sugani ,

Bayan an rakasu kowa ya tafine FERAS sukai alwala sukai sallar isha,i bayan sun idar sukai nafila sukai addu,oi sannan suka cika cikinsu da abinci suka fito parlor suna kallo suna hira

Misalin sha ɗaya na dare BASSUNA har tayi bacci a parlor dayake ita bamai kaiwa dare bace , FERAS yana ganin haka yaɗau abarsa tamkar ƴar tsana yaje ya shimfiɗeta a gado dama tunda sukaci abinci sukayi wanka suka shirya cikin kayan bacci dan haka baya bukatar wani shiri

Batare da bata lokaciba ya kashe kwai yajewa matarsa dan raya sunna , ya lallaba abarsa cikin salama ya sauke farali batare data sha wuyaba bai bartaba hassaida ya ɗan ɗanawa BASSUNA daɗin dake cikin sex suka more daran su kowa cikin farin ciki ,




*****

Bayen sati ɗaya da auren Raihan abubuwa da dama sun faru islam tana gasuwa awajensa yadda yakamata gashi bata iya shiru da bakinta duk rashin mutumcin daya mata saita sanarwa su Ame hauwa

Yau misalin karfe shida na yamma papy ya kirashi yayi masa zazzagar kifin gon goni sannan yayi masa nasiha mai ratsa zuciya haɗi da tunatar dashi kar dan bayasan islam ya cutar da ita ya tuna Allah yana kallonsa kuma Allah baya yafe hakkin wani dan wani yaji daɗi koda kuwa tsakanin uwa da ɗane bare kuma mata da miji ,

Raihan ya fahimci papy sosai hakan yasa yaɗanji sanyi har yazauna sukasha hira haɗi dayiwa papy alkhawarin zai sauke duk wani nauyi nasa bazai kara kuntata mataba , sosai shima papy yaji daɗin hakan dan shi babban burinsa bai wuce na ganin kwanciyar hankalim ƴaƴansa bah ,


Raihan yau da ƴar fara,a ya dawo gidansa babu murtikewar fuska hakan yasa islam sakin jiki anata iyayi aka jere masa abinci a dining table amma bai saurari abincinba saida yayi wanka yafito daga shi sai boxer yana shafa mai saiga islam ta shigo

A yadda ta ganshi ne yasata jin kasala dan islam macha ce mai matukar saurin sha,a wa musamman akan Raihan lokuta da dama ko kyakkyawar fuskarsa ta kallah tana shiga sabon yanayi bare kuma yanzu datai tolazi da faffaɗan kirjinsa wanda take mafarki da kulaficin kwanciya akai ,

wani yawu ta haɗiya makot wanda yasa Raihan juyowa ya kalleta

Murmushi tasaki ta karaso kusa dashi sosai tana cewa , " ahh mijina madadin kabari na zo na shafa maka man da kaina , bata bari yayi maganaba ta tsiyayi man tafara shafa masa a lallausar fatarsa mai kama da audiga ,

Ɗan tsaki yaja yana kau da kai bayaso ya tanka mata chan baiyi aune ba sai yaji ta zura hannunta a boxer ɗin sa da sauri ya turata baya saida tafaɗi kasa

Yace , " islam yaushe kika zama haka bansaniba waya nuna miki sa hannu a boxer faɗamin kina matsayin budurwa wacce batasan ɗa namijiba uban me kike nema a wandona ?, ya faɗa yana nufota yana zare ido cike da tuhuma ,

Kuka islam tasa tace , " yaya yanzu laifine dan na maka haka aikai mijinane banda wani laifi ayin hakan , " karya kike islam ni nama fara kokonto akanki anya kuwa bakya bin maza dan babu yadda za,ai yarinya budurwa babu gaira ba dalili ta zurawa miji hannu a wando batare da yakai mata tayiba ,

" ni wallahi ban taba sanin wani ɗa namiji a rayuwata ba nidai nasan kawai ina da tsananin sha,awa shiyasa bana yarda na shiga cikin maza sai gashi nayi aure yau tsawan sati guda mijina bai taba ko rike hannunaba da sunan soyayya to faɗa min ya kakeso nayi wallahi Raihan kaji tsoran Allah idan ba hakaba duk halin dana shiga kai kaja min ,

Shiru Raihan yayi yana tunani hakika zanchanta gaskiya ne koba komai yakamata ya sauke wannan nauyin karyaje yayi laifi a wajen ubangijinsa ita mace raunine da ita ba kowacce mace bace takeda juriya ba , ajiyar zuciya ya sauke ahankali ya karasa inda take zaune tana kuka ya kama hannunta cikin sassauta murya yace , "calm down shikkenan komai ya wuce tunda hakkinki kike so za,a baki , ya shafa kanta sannan ya mike ya fice

Islam wani sanyi taji aranta take tasaki murmushin samun nasara

Raihan kuwa yana fita parlor ya zauna a dining table yafara cin abincin , chan saiga islam ta fito taja kujera ta zauna a kusa dashi tace , " au dama ba fita kayiba , kai kawai ya gyaɗa mata yacigaba dacin abincinsa badan yanajin daɗin abincin ba saidan yanajin yunwa kuma shiba gwanin siyan abinci bane saita kama dole ,

Koda ya gama cin abincin suka zauna a parlor islam surutu ta dinga masa tamkar charbi ya tsinke take cewa , " ya kasan me wallahi yawo nakesan mufita muzaga gari kuma inaso mujejje gidansu ƴan, uwan ommina su ganka , ko kallon inda take baiba yana daga zaune yana danne dannen wayarsa , kallonsa tayi taga gabaɗaya hankalinsa ba,a kanta yakeba

" yaya magana fa nake maka " inajin kiki ba kunne ne yake jiba , " nace yaushe zamuje unguwar , " su family ɗin ommin naki basu sanni bane naga tunkan a haifeki suke zuwa gidannan sun sanni nasansu to mekuma zani namusu , " amma yaya ai yakamata , bata karasa maganar ba ya katseta da cewa ,

" karki dameni ya kamata dame kinga banason wannan surutin naki ina bukatar nutsuwa tashi kiban guri dan Allah , ya faɗa cikin haɗe fuska, tashi tayi jiki babu kwari tanufi hanyar ɗakinta saita tsaya ta bayensa ta kalli wayar dan ganin abinda ya ɗauke masa hankali yaki saurarenta hotan maryam ta gani ashe tun ɗazu hotunan matarsa yake gani shiyasa yayi mata haka , kwafa tayi ta wuce a zuciyar ta tana Allah wadai da maryam ta mutummah amma yakasa mantawa da ita


Da akai kiran sallar isha Raihan fita yayi yaje masallaci daga nan ya tada mota ya nufi gidan mustapha sun dade suna hira mustapha yaji daɗin ganin yadda Raihan yadan saki jikinsa yafara komawa daidai Allah yasa masa hakuri da dangana Alhamdulillah,

Raihan bashi yabaro gidan mustapha ba sai karfe sha ɗaya nadare sannan ya dawo gida koda ya shigo parlor sai ya tadda islam a zaune tana jiransa gidan yaɗau kamshin turare mara daɗi mai hawa ka , islam tana ganin shigowar Raihan ta tashi da ɗan gudu ta faɗa jikinsa tana masa sannu da zuwa cikin iyayi da kisisina sai wani karya jiki take ita ba kyan suraba gashi tasa wasu fitu nannun kayan bacci duk da haka tayi kyau sosai cikin kayen da yake ba laifi akwai ken fuska

Kallo ɗaya Raihan yayi mata ya kauda kai ya wuce bedroom ɗinsa ta bi bayensa tana kallo yana cire kaya ya shiga wanka dan yagaji bacci yakeso yayi

Islam tana zaune a bakin gado haryayi wanka ya fito tana kallonsa ya shafa mai sai taga ya ɗakko turare ya faffesa ajikinsa da ɗakin baki ɗaya mamaki ne ya ishi islam dan tasan wannan kamshin turaren ba nasa bane na maryam ne

wani irin bakin cikine ya tsaya mata cikin rashin nuna jin daɗi a fuskarta tace , " yaya Raihan ya nasa turare mai kamshi mai tsada zaka fesa wannan ɗan titin wanda kaskan tattun mutanene mara gata kawai suke amfani dashi ,

Ɗagowa Raihan yayi ya kalleta tabbas ya gane dawa take wato turaren maryam ne na kaskan tattu murmushi yasaki yace , " kinsan kowa da abinda ya dameshi ni bana ra ayin abubuwa masu tsada dan basuda wani daraja amma abu mai araha yanada wani sirrina daban da bakowane ya sanshiba dan haka ni wannan ne zabina idan kinga zaki iya shaka to idan kinga bazaki iyaba ɗakuna sunada yawa a gidannan zaki iya tafiya , kauda kai kawai islam tayi tasan yagane mai take nufi saita basar ta ɗau rumot ta chanza tasha ta haye gadon tana kallon katuwar shashar dake kallon fuskar gadon ,

Shima yana gama shirinsa ya kashe kwan ɗakin ya haye gadon daga nesa da ita yayi kwanciyarsa , matsowa kusa dashi tayi ta rungumeshi tanajin faɗuwar gaba dan batasan yadda zata kaya a wannan daren ba tsakanin ta da Raihan

Raihan jin ta manne jikinta da nasane yasashi tur sasa zuciyarsa ya sauke nauyin da yake kansa duk da zuciyar sa cike take da tsanar islam amma babu yadda ya iya haka dai yaɗanyi wasanni da ita ya rikitata da salonsa saida ya tabbatar ta kwaɗaitu tukunna ya shigeta tuni islam tafara bare baki anji maza shikam gogan hadda mugunta ya kara dan abinda zuciyar ka takeso shi kake lallabawa

Raihan yayi yayi yasamu gamsuwa da islam amma ina duk batada wata wadatacciyar ni,ima ba kamar maryam ba da koda iya jikinta yayi wasa kawowa yake bare kuma aje ga sex, tuna hakanne yasa ran Raihan matukar baci gashi ta cika masa kunne da kuka gashi sha,awarsa ta tashi kuma ya kasa samun biyan bukata haka ya tashi jiki babu kwari ya shige toilet ya sakarwa kansa ruwan sanyi yana tunanin matarsa ɗaya tamkar dubu acikin mata hawayene suka shiga sakko masa gashi mararsa har ta fara ciwo a zuciyar sa yake tunanin duk duniya bazai taba samun mace kamar maryam ba gashi duk da islam yasameta budurwa baiwarta bata kai ta maryam ba gashi batada wani daɗi ta ko ina shi batai masaba

Tausayin kansane ya kamashi afili ya furta , " ya Allah ka dawomin da matata ubangiji ka kawo karshen kukana ka karkato da hankalin maryam kaina aduk inda take kuma ka karemin ita da abinda yake cikinta










✍🏻ZAINAB AHMED YUSIF
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲







AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA






By ZAINAB AHMED YUSIF






PAGE 9️⃣3️⃣

Bismillahir rahmanurrahim







Wanka yayi yafito daure da Tarwul ajikinsa kallo ɗaya yayiwa Islam dake kwance akan gado yayi ya kauda kai

Yanaji tana kuka amma baikoyi tariba yashafa mai yasa jallabiya yafice parlor, shayi yasamu mai zafi yasha sannan ya kashe kwan parlorn ya kwanta a doguwar kujera yalumshe idonsa yana tunanin dare ɗaya tamkar dubu daren dabayajin zai kuma samun irinsa a rayuwarsa daren da yarinya karama ta maidashi cikekken mutum wato daren farkonsu da maryam

Islam tayi zatan Raihan zaizo yataimaka mata wajen wanka amma shiru hakan bakaramin kona matarai yayiba jiki babu daɗi ta tashi tashiga toilet tana kuka wannan karan ba kukan ciwan da jikinta yakemata takeba kukan rashin soyayyar Raihan gareta take wannan zaman dashi gara babu namiji ko dutsene idan akazo fannin sex yana nunawa mace soyayya amma ita bata samu wannan ba dukda yasamu budurcinta jiyake tamkar dole akai masa

Bayen tafito daga wankanne tasake kaya tafito parlor , akwance ta taddashi kwan dakin ta kunna ta karasa kusa dashi ta tsaya zuciyar cunkushe da damuwa tafara magana,

" Me kake anan dazaka baroni kazo ka kwanta kai kaɗai??, Shiru yayi mata baice komaiba danshi sam bamayason kallon fuskarta , " nagane Raihan nasan duk abinda kake nufi akaina bazan iya wannan rayuwar ba nifa matarkace ina bukatar soyayyar ka kullum da bakincikin da kake tusamin amatsayina na wadda namaka dakon budurcina nakawomaka gidanka kagama amfani dani ba godi bare nagode to wallahi kasani idanma tunanin waccen ƴar iskar matar takace nafita saboda nayi imanin ba budurwa kasametaba ,

Sai a wannan lokacin Raihan yabuɗe idanunsa da suka rine sukai jajir ya wanka mata mari ya nunata da yatsa yana cewa, " ki dinga dai daita kalamanki akanta idan ba hakaba zakisha wuya niban miki doleba har yanzu kinada dama idan bazaki iya zamaba zansawake miki kije kiyi rayuwar ki nisan bana bukatar ki, yana karashe maganar ya wuce bedroom ɗin sa yasa key , durkushewa Islam tayi tana kuka tace nashiga uku meyasa bazai soniba meyasa burina yaki cika har yanzu nakasa samun yadda nakeso

Nikuwa ƴar mutan Libya nace mugun halinkine yaja miki Islam dama haka Allah yake lamarinsa muje zuwa bakiga komai ba





★★★


Gurine daya kayatu da furanni masu matukar kyauda kamshi gudu take acikin wajen tanaso takai ga mutumin da bayensa kawai take hanga dukda tsohon cikin dake jikinta hakan bai hanata gudinba tana kuka take cewa " kataimaka min zan mutu taimako katsaya taimako wayyo Raihan raihan kada katafi,

Azahiri kuwa tsohuwar dake kula da maryam ce taji tana surutai da sauri ta shigo ɗakin taga Maryam sai mimmika take tana surutai tana kiran sunan Raihan hawaye na zuba a idonta Chan kuma saita zabura ta farka a sukwane jikinta na bari

Rirriketa tsohuwar tayi tana tofa mata addu,oi cen Maryam ta dawo hayyacinta tana dafe kai take abubuwan da suka faru da ita suka dawo mata kwallon dattijuwar da ta riketa tayi sannan ta karewa gidan kallo chan tafashe da kuka tana rike hannun tsohuwar tace, " kitaimaka min ki kaini wajen mijina inasan ganinsa yasu kashemun shi sun rabani dashi sunnasan raba soyayyar mu sunraba shi da cikin dayafi kauna aduk duniya, rarrashinta tsohuwar tafarayi danta fahimci tanacikin bakinciki da takaici,

Saida tabawa maryam ruwa tasha sannan tace ,

" Yarinya nibansan komai game dakeba nima tsintarki mukai nida mijina akan titi amma inaso na taimakeki dan duk yadda akai kina cikin damuwa ki faɗan wanene Raihan ɗin saimu nemomiki shi, hawaye Maryam tashare tace,

" Nagode muku sosai kun taimakeni shiɗin Raihan mijinane damukai aure dashi, nan Maryam ta kwashe labarinta tsab tabawa tsohuwar sosai tsohuwar ta tausaya mata duka kuka suke anrasa mai rarrahin wani chan tsohuwar tace,

" Maryam nasan mijin

Please Login or Register in order to submit comment