Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da wuyanta suka shige ɗaki

Bayen sun zauna jawahir tace musu," aisha gazzal kufaɗamin wanene wannan ɗin kuma akanme yake magana dahar yake alwashin kasheni a gidan mijina , gyara zama aisha tayi sannan tace

" anty jawahir dafaridai zanbaki hakuri akan abinda yafaru,, shi wannan dakike gani shine babban yayenmu daga shi sai mijinki shaikh ali ,, duk gidannan shine mai gudanar da komai kuma uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya dashi tarbiya ɗaya aka bamu amma FERAS yafuta zakkah aduk garinnan ma kowa yasanshi kuma duk mutumin kirki baya haɗa sahu dashi wannan shine babban dalilin dayasa duk namijin auren dayazo mana yake guduwa , amma mun ɗauki wannan amatsayin kaddara saboda muna matukar kaunar ɗan,uwan mu, wannan abinda kikaga yayi miki mebi yashawo abinda yafi karfinsane amma kiyi hakuri tunda munfaɗa masa ke wacece bazai kumaba ,

Jinjina kai jawahir tayi cike da al ajabi take tunanin wannan lamari gashi dai shine babban amma yafita zakkah yan,uwansa masu mutumci da kaunar juna shikuma yana jawo musu bakin jini

" naji aisha shikkenan Allah ya shirya mana shi kuma insha Allah ko Ali bazaiji wannan maganarba kuma karku faɗawa Ammee kunji ,to suka amsa sunajin daɗin yadda halin jawahir yake babu ruwanta




★★★



Ame hauwa ce zaune ta hakimce , ita kuma ommu Amal tanata kai komo a ɗakin cen naji taja doguwar ajiyar zuciya tafara magana

" yanzu munyi yunkuri na farko wato bari damukai aka ɗaura wannan auren saura yunkuri nabiyu wannan karamin lamarine Ame hauwa cikin sauki zamu datse wannan auren amma saimunsaka kullalliyar da dole a kwace compani daga wajen Raihan sannan a koreshi daga cikin wannan gidan

" to yanzu ya kike gani ommu Amal zamuyimusu tsafine kokuwa dai yazamuyi ?,
" yawanci sihiri bayakama wanda yarike ibada baya wasa da salloli kuma baya rabuwa da azkar kinga kuma wannan sana,ar Raihan ce da matarsa, idan mukace zamuyi haka bata kuɗinmu zamuyi a banza bukata bata biyaba ,

" to yanzu ommu Amal taya zamu bullo musu , " zamubisu da makirci bita da kulli duk wani hanya dazamu bi wajen lalata auren nan zamu biya sharruka kala kala ba tsaiko , amma saimun shiga jikin maryam sosai ta fuskar kauna zamu san ya yanayin zaman auren nasu yake sannan wace hanya ce zatai mana saukin bi wajen rusa auren dakuma haɗa babbar tarzomar da sai kowa ya tsani Raihan a gidanan

Hannu Ame hauwa taba aminiyar tata suka tafa da murnar samin mufeta



... Raihan yafara zuwa compani akowani lokaci forgiveness yake fita baya dawowa sai karfe huɗu wani lokacin sai magaruba idan kuma yabiya tagidan mustapha abokinsa sai wajen sha daya yake shigowa

Yau kusan kwana uku kenan tsakanin maryam da Raihan babu wanda yaga wani kullum tana ɗaki batawani damu dashiba shima kuma yayi overlooking akanta , yadaiyi saa yana samun favor ɗin girki daga gareta

Yauma kamar kullum tana zaune a parlor misalin karfe uku na yamma taji duk gidan yayi mata zafi kamar hadin baki babu wanda yake zuwarmata tunda akai na ɗoki dakumadai tsoran yaya Raihan yasa kowa yaja jikinsa dan idan kafiye zakewa da zuwa kullum yana ganinka yanzu zai taka maka burki , tashi tai ta saka abaya mai duwatsu akan wasu matsatstsun wando da riga datasa ta yafa ɗan mayafi ta fice

Gidansu Amal tafara shiga dan nanne na kusa da ita saida tazauna suka kwashi hira wajen awaɗaya sannan ta wuce gidan anty Laulam tana zuwa ta kwanta anty Laulam sai tsokanarta take tanace cewa ," aa gaskiya Raihan ya iya kiwo kinga yadda kikai kyaukuwa kinyi wani luwai luwai dake kwana uku kawai da aure haka wato jin dadi ya boyeki ko ankiraki a wayama baa samunki

" anty Laulam bahaka bane kawaidai dan nasamu nutsuwane yanzu bana fita ko ina kuma bana aikin wahala ni inaga wannan shiyadan cenzani,, cikin zolaya anty Laulam tace ," um um maryam fadi gaskiya aure ba wasa bane naji yake sultan yana cewa papy sai murna yake ganin yadda Raihan yasamu Tranquility yanzu duk ya cenza kamar ba shiba

Nan suka cigaba da hirarsu ta duniya cen wajen karfe biyar anty Laulam ta tashi tashiga bedroom saigata da ledodi guda biyu cike da magunguna tana zuwa tacewa maryam," ga waɗannan maganin na musamman nasa aka kawo miki dama su baa shansu sai an kwanbiyu da aure kan sannan kinsan daɗin abin , karkiyi wasa da wannan maganin maryam na mallakane wallahi indai kikasha yau inaga Raihan sai yayi miki kyautar DAULATUL ARAB gaba ɗayanta saboda daɗi ,, gabaɗaya maryam jitayi babu dadi daganin maganin nan take abubuwan da suka faru tsakaninta da Raihan suka shiga dawo mata yanzu ita wane tsau tsayine zai kaita kuma shan magani ,, ganin anty Laulam ta kureta da idanune yasata cewa ," kai amma anty naji daɗin maganinnan amma bazansha yanzuba kibani idan naje gida zansha ,, " ah haba maryam magaruba takawo kai indai ba bakida lafiya ba kawai kisha yanzu yau a kwana ana buga soyayya danni nafison kusama mana baby haf,kas ,

" nasani anty aibazai yafaɗamin yau bazai samu dawowa da wuriba sai wajen karfe goma saboda zaibiya wajen bikin abokinsa, jinjina kai anty Laulam tayi sannan tace ," eh gaskiya yayi wuri yanzu kinsan maganin namu ojan ojanne kibari sai karfe goma tayi tukunna kisha saboda kisamu sararin kula dashi

Hira tayi daɗi wasa wasa karfe takwas tayi hargari yayi duhu tukunna maryam ta tashi ta nufi gidanta , tana zuwa tadau mukulli tabuɗe ta shiga abinta

Tunkan ta karasa parlor tacire abayar jikinta tana tafe tana juya kyawawan ɗuwaiwukan ta harta karasa tsakiyar parlorn ga mamakinta taga Raihan a zaune yanashan gahuwa taji tsoran ganin yadda ya haɗe fuska batace kalaba tajuya tana tafiya gabaɗaya kananan kayen datasa sun bayyana kyawun halittar da takedashi ta wutsiyar ido yake kare mata kallo a wani bangaran nazuciyarsa yana mamakin sauyawar maryam wato iskancin nata yakai tafara fita batare data sanar dashiba ji yayi bazai iya hakuriba dole zaije yasameta

Da karfi ya banka kofar ɗakin nata maryam dake shirin sa leda a drawer tai saurin waigowa tana kallonshi , saida ya tako daf da ita tukunna yace ," ke wato iskancin naki yakai da kidinga fita tun farar safiya kina bingidajen unguwa har dare saboda kijawomin zagi ko ? ,






Comment and share fisabibullah 🤝






✍🏻
ZAINAB AHMED YUSUF HAƊAJA
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲





AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA




By
ZAINAB AHMED YUSUF HAƊAJA
MRS Abzee





PAGE 2️⃣7️⃣⏮️2️⃣8️⃣

Bismillah




Maryam buɗe baki tai zatai magana , wata tsawa Raihan yadaka mata wadda tasa jikinta tsuma nan take tsoro da fargaba suka kamata shikuma cikin faɗa yake cewa

" karki sake naji bakinki anan mara kunya fitsararriya kawai yanzu zamusa kafar wando ɗaya dake tunda na fuskanci bakyason musamu peace a gidannan to yanzu zamu fara wasan babu ruwana da Treaty dake tsakanina dake

Ledar hannunta datake kokarin sawa a drawer ya fuzga yana dubawa ɗaya bayen ɗaya dankuwa duk ya ganesu tunda da sunayensu ajiki da kuma mannannun fastar mata da miji irin na maganin mata

" eyeee lallai maryam lamarinki yafara girmama rannan nakamaki kina waya yau kuma gaki da tarin magungunan mata to ina zaki kaisu wai ubanme kike nema ajikin ɗa namiji ne ? eye jara babbiya

Shiru maryam takuma yimasa tana matsar hawaye dan Allah Allah take karya taba lafiyar jikinta , " ba magana nake mikiba mezaki da wannan waye yabaki , cikin muryar kuka tace ," danaje gidan anty laulam ne tabani ,

" aikinsan da cewa ba mijine dakeba tsabar kinibibi da jaraba kika karbo maganin mata salon kizo ki mamayeni wato kinji daɗi a wancen lokacin shine kike neman kari a kwakuleki hankalinki ya kwanta to ahirr ɗinki nafi karfinki wallahi, harija mayyar maza kawai mitswww , yaja tsaki yafice haɗi da jamata ƙofar garam

Yana fita ta tsugunna a bakin gado tafara raira kukan takaici babu abinda yafi mata ciwo irin taji Raihan yana ce mata harija mayyar maza , wannan kalmar ba karamin kona matarai takeba wai ace kamar ita a matsayinta na wadda bama tasan wanene namijiba yadinga jifanta da waɗannan kazaman kalaman


Dan takaici yau maryam ko abincin dare bataciba tanajin motsinsa a parlor hattaji shigarsa ɗaki da alama ya kwanta itama bacci barawo batasan lokacin dayayi awan gaba da itaba

Kiran asuba na farko ta tashi tasakarwa kanta ruwan ɗumi tayi alwala bayan ta idar da sallah ta shirya cikin wasu riga da wando masu yanayin nasanyi amma basuda nauyi , kitchen ta nufa dama komai nata a kimtse yake shayi ta hada ta wace ɗakinta bayen ta shane tasoma gyara ko ina nagidan dukda babu datti amma maryam bata bariba , wani haɗaɗɗen turaren kamshi ta kunnawa gidan hatta ɗakin Raihan bata bariba saida ta kimtsashi , gari na gama wayewa taji shigowar Raihan da sallamarsa amma tai burus a ɗaki dukda taji sarai saima gyara kwanciyarta tayi nan da nan bacci ya ɗauketa

A bangaran Raihan kuwa yaji matukar daɗi ganin yadda maryam take tsafta fiye da tunani danshi a rayuwarsa bayasan kazanta kuma baya haɗa sahu da kazami , misalin karfe shabiyu ya shiga ɗakin maryam kwance yaganta ta dunkule waje ɗaya tana bacci zama yayi abakin gadon yana karewa ɗakin kallo sosai yake yaba tsaftarta ko ina kalkal sai kamshi yake , yajima yana kallon jikinta yana auna yanayin kowane girman sassan jikinta a zuciyarsa yace lallai wannan yarinyar zatai kwaliti

Yana cikin kallon natane yayi karo da wani yanka a hannunta maikama da yankan wuka kuma da ɗan girmansa zaiyi tsayin karamin ɗan yatsa , mamakine ya ishi Raihan wanene yajimata ciwo haka kuma ko dinki babu ahaka gurin ya warke ,, take Raihan yaji tausayinta yakamashi Allah sarki rayuwa kenan yarinya karama kamar wannan haka take rayuwa babu wani nata batada kowa sai Allah dududu bazata wuce sha takwas bah ,, kiran wayarshi ne ya dakatar masa da tunaninsa bayan ya ɗaga ya kashe wayar yasa hannu yana tashin maryam , kemai mai taki tashi saima ruko hannunshi datayi tana rungumewa a kirji kam , wani shok yaji danjin hannunsa a luntsuma luntsuman nonuwanta , da sauri yajanye hannunsa dan da alama bacci take haikam bama tasan menene yake faruwaba , jiyayi kamar ya kyaleta amma sai yakuma sa hannu yana jijjigata da karfinsa aikuwa babu shiri ta bude ido tayi matukar tsorata da ganinshi yau har saman gadonta a tunaninta ko dukanta zai saita wani marai raice hadda gaisheshi

Murya ciki ciki ya amsa sannan yace , " kitashi kiyi wanka kisa kaya masu kyau abokina mustapha yace zaizo da iyalinsa yau suganki kitashi kiɗora girki

To kawai tace mishi sannan ta shiga toilet ta goge baki ta shige kitchen abinci mai rai da lafiya ta girka irinna ARAB kusan kala huɗu tayi dandanan ko ina nagidan yadau daddaɗan kamshi , bayen tagama komai takuma kimtsa parlor dukda babu abinda yayi ta fesheshi da turare shidai Raihan yana zaune yana kallon ikon Allah dayake jumaa ce babu aiki yau a gida zai wuni

Ita kuwa maryam wanka takuma yi saida ta tsane jikinta sannan ta ɗakko mayuka masu kyau da kamshi na gyaran fata tashafe jikinta dasu , ƴar kwalliya tayi mara yawa sannan ta ɗakko wata sabuwar Abaya ruwan madara mai bala,in kyau buba mara nauyi duk jikinta duwatsune sai kyalli suke ta baza feshe jikinta tayi da turarurruka masu kamshi tukunna ta nemi bakin gado ta zauna tana gemes a wayarta , cen wajen minti goma taji haya niya alamar shigowar baki , jitayi kamar tafita saikuma tayi burus, cen saiga Raihan ya turo kofa yana zuwa yace mata sunzo ga mamakin maryam saitaga shima yaɗanyi kwalliya , rike hannunta yayi suka fita

Suna isa fatima matar mustapha ta rungume maryam bayan sun gaisa ne aka fara hira da Raihan da Abokinsa, mustapha ne yake cewa , " o ikon Allah kenan abokina bayen lokaci mai tsaho daka ɗauka bakai aure ba saigashi Allah ya haɗaka da mata tagari yarinya kyakkyawa , murmushi Raihan yayi ya rungumo maryam jikinsa hadi da yi mata kiss a goshi yana cewa ," eh mana abokina dama zazzafan rabon auren wannan sarauniyar matanne ya hanani aure har nafara girma amma yanzu babu komai tunda nasameta bakaga sai ɗanyacewa nakeba , dariya gaba dayansu suka saki sannan fatima tace ," gaskiya ne wannan Raihan kayi saar mata Allah yabada zuria ta gari Allah ya daidaita yakuma bata hakurin zama dakai dan kaida mustapha saidai addua , cikin raha fatima take magana itakuwa maryam shiru tayi musu dan batasan su daɗe a gidan ganin yadda Raihan yaketa makale mata yana wani rungumeta a gabansu saikace irin da gaske matarsace

Kemaimai maryam taki cewa komai sai sunkuyar da kanta kasa tayi tana wasa da yatsunta , har baki sukaci abinci sunata yabawa maryam bata wani saki fuskaba hakan ya matukar konawa Raihan rai saiya faki idansu ya galla mata harara hadi da yimata kallon zakici ubanki , sarai tasan ya kufula amma sai tanuna ko a jikin ta





★★★ FERAS ne ɗaure da Tarwul yafito daga toilet yaji wayarsa tayi kara yana dubawa yaga kiran YASIR kin ɗagawa yayi shikuma YASIR yaki daina kira cendai yagaji yaɗaga batare dayace komaiba

" hello FERAS fatan kana lafiya ya kwana da yawa kajini shiruko wallahi bana kasarne ,, shiru feras yayi masa nanma baice komaiba , shikuwa yasir dama yayi tsammanin haka daga wajen abokin nasa hakan yasashi karayin magana cikin marai raicewa yace " please uban gidana kayi hakuri nasan haryanzu haushina kakeji kayimin afuwa yarintace banida mai sharemin kukana sai kai oga FERAS

Murya ciki ciki feras yace " mai kake bukata ?, " ina cikin tashin hankali feras duk duniya bantaba ganin yarinyar dana jarabtu da zazzafar sha,awartaba kamar maryam ina cikin matsala duk lokacin dana shirya makirci a kanta sai Raihan yayimin cikas saina yanke shawarar zan aureta duk masifa da bala,in da zaifaru bazan hakuraba saina huce abinda nake zulama bayan nagama wulakantata sai na saketa , kwatsam naji labari wai yaya Raihan ya aure ta bayan yasan ina muradinta , " karamin tsaki FERAS yaja sannan yace ," Raihan ya fika bukatar yarinyar shiyasa yayi maka wayo ," to yanzu ta wace hanya kake ganin zamu bullowa lamarin ?, " aa yasir nasha faɗa maka babu ruwana da wannan lamarin , kasandai ina yawan goya maka baya akan kowace harkallah amma banda ta mata to yanzuma hakan take babu abinda zance maka saidai kayi hakuri kabar batun yarinyar nan dan ba rabonka bace

Babu yadda yasir ya iya dolece tasashi amsawa da to dan bayaja da maganar FERAS amma badan ya hakura ba, shikuwa feras kashe wayar yayi yasa jallabiya ya fesa turare haɗi da kunna sigari kamar yadda yasaba babu wani batun sallah bare neman tsari daga shaiɗanu

Sakkowa matattakalar benan yayi dan yunwa yakeji, kitchen yawuce dan yahaɗa shayi amma ga mamakinsa yana shiga yaga jawahir tana girki dayake babban kitchen ɗin gidan ɗayane a kasa komai akwai aciki , jawahir kuwa tana ganinshi taji gabanta ya faɗi fuskarnan tashi ba faraa jikina bari ta rusuna tana gaisheshi , baice komaiba ya karasa gaban famfon kitchen ɗin dake kan kanta ya sa kofi ya kunna bangaran tafa shashshen ruwa saida kofinsa yacika yaɗaga ruwan zafin ya kwarawa jawahir a jiki , jawahir cikin azaba ta shiga kurma ihu tana sassosa jikin ta , shikuwa FERAS ko a jikinsa ganin ɗanyen aikin dayayi mata , a sukwane Ammee da shaikh ali suka fito danjin uban ihunda jawahir take







Please comment and share fisabibullah 🤝





✍🏻
ZAINAB AHMED YUSUF HAƊAJA
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲





AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA





By ✍🏻
ZAINAB AHMED YUSUF HAƊAJA
MRS Abxee

Marubuciyar

Sangartacciya
Harzen da hurzen
Majnun
Banida gata
Morat ne kaddara ta
Gwarzon namiji
Mur atussaliha
MUFAJI,A AND DAULATUL ARAB




SADAUKARWA
WANNAN PAGE GABA ƊAYENSA SADAUKAR WA NE A GAREKU MASOYANA NA KASASHE DABAN DABAN MAZA DA MATA INA GANIN SAKONNIN FATAN AL,HERINKU KUMA INA GODIYA ALLAH YABAR KAUNA 🤝🥰🥰 AMEEN


________________________________





PAGE 2️⃣9️⃣⏮️3️⃣0️⃣
Bismillah





.... Gaba ɗayan su Ammee da shaikh Ali wajen jawahir suka nufa wadda saman kirjinta har yafara sabulewa , aruɗe suke tambayar garin yaya shikuwa gogon yaja baya ya naɗe hannayen sa da kuma sigari a bakinsa yana kallonsu

Cikin radaɗi da tsananin azaba jawahir take nuna FERAS da hannu tana cewa " shine shiya konani , Ammee cikin fusata ta tashi daga gaban jawahir takarasa kusa da feras cikin bacin rai tace ," mai tai maka ka konata FERAS ?, shiru yayimata dayacire sigarin daya zuka mai makon yayi magana saiya busawa Ammee hayakin sigarin a fuskarta

Take idanun Ammee suka ciko da hawaye zuciyar ta tasoma tafasa harshenta har ɗaci yake cikin matukar hassala ta ɗaga hannu ji kake tass tass ta shararawa FERAS zafafan maruka guda biyu a kuncinsa saita fashe da kuka ta cukumi kwalarsa tana cewa ,

" nayi nadamar haihuwarka a rayuwata FERAS ni uwace amma ina Allah wadai da samunka FERAS Allah ya tsi..... , bata karasa furta kalmarba shaikh ali yayi saurin zaburowa ya rufe mata baki yana hawaye yake cewa, " lah Ammee karkiyi haka Ammeena na rokeki kada ki furta haka , wani makwallaton bakin ciki Ammee ta haɗiya tanajin kanta yayi mata nauyi kuka takuma rushewa dashi tayi saurin fita daga kitchen ɗin ta nufi ɗakinta ta kulle ta faɗa kan bed ɗin tana raira kuka cikin tashin hankali da bakin ciki

Shaikh ali kuwa yana ganin Ammee ta fita ya maida kallonsa ga FERAS yace ,

" anya kuwa kanaso kagama da duniya lfy ? kasan irin bala,in da ka ɗibarwa kanka kuwa nasa mahaifiyarmu cikin tashin hankali ? , a fusace shaikh ali yake magana hakan yasa jikin FERAS yin sanyi dan shi kanshi baizata ran Ammee zai baci hakaba , batare dayace komaiba ya fice daga kitchen din mukullin mota ya ɗauka yabar gidan yana tunanin halin da Ammeen sa take ciki

Shikuwa shaikh ali rintsa ido yayi yana fidda wasu zafafan hawaye ya karasa kusa da matarsa ya kama hannun ta haɗi da ɗorawa kan kirjinsa yace ," iskut ya habibty mahalesh , ( ishiru masoyiyata kiyi hakuri ) gyaɗa masa kai kawai tayi alamar ta hakura sannan ya ɗauketa ya kaita ɗaki ta sauya kaya suka tafi mutaishfa ( Asibiti ) ,

Suna tafe acikin mota amma jawahir bata daina kukaba bawai kunar takewa kukaba tunani take yanzu haka zatayi rayuwar auren ta cikin barazana da yayan mijinta yake mata , shaikh ali ne ya kalleta yace," jawahir ina mai kara baki hakuri wlh banji daɗin abinda yafaruba na auroki daga gidan mutumci gidan tarbiya kuma manyan mutane sannan adinga wulakantamin ke inaji ina gani , wallahi sam bantaba kawowa a kainaba wai zaku samu matsala da FERAS tun da nasanshi babu ruwansa da mata , waima menene ya haɗakune harya konamin ke ? , murmushin takaici jawahir tayi tace ," Ali nifa banma san wannan yayan nakaba , haka rannan babu kowa agidannan daga ni saisu aisha da gazzal, yazo yadinga cewa zai kasheni daker su aisha suka kwacene ,

" amma jawahir maiyasa baki sanar danibah ? , "wallahi Ali banaso ran Ammee yabacine inasonta tamkar mahaifiyata , " Allah sarki jawahir karki damu insha Allah zamuyiwa tufkar hanci koma daga ina matsalar take zamu ganota , " Allah yabada iko , ameen ya amsa mata suka cigaba da tafiya acikin mota,

Cen shaikh ali yaji wayarsa tana ruru yana dubawa yaga FERAS da sallama abakinsa ya ɗaga wayar , aban garan FERAS kuwa yana ganin yadaga yafara cewa ,

" Ali zaifi maka sauki kasaki wannan tsinanniyar idan kanaso muzauna lafiya idan kuma tagama tsafaceka bazaka iya sakintaba to karka sake ka kara kawo mana ita cikin gida kaje cen kanemi gida kasata idan ba hakaba wallahi sainayi ajalinta idan yaso koma mai zai faru ya faru ,

Shaikh ali yanajin haka yaja burkin motar jikake kiiiiiiii , sannan yafara magana ," FERAS kasan mai kake cewa kuwa zaka kashetafa kace akan me metayi maka laifine dannayi aure wato kai a rayuwarka bazaka taba zama garkuwa ga ahalinkaba saidai kazama barazana a garemu kuma wai a hakan kaine a matsayin babbah,

ya isa haka Ali, FERAS yadaka masa tsawa wadda tasa shaikh ali yin shiru shikuma FERAS yakara da faɗin ,

" izinin ubanwa ka nema da zakayi auren kuma ma da kuɗin ubanwa kaje ka auro wannan hankakar tauraruwa mai wutsiya , " ya isa FERAS bazan iya jure waɗannan kalaman nakaba kudin ubana naɗiba yadda kake takama da komai na gidan haka nima nake takama dashi tunda nima ɗane kuma yadda za a raba abaka naka haka nima zaa bani nawa duk da kaine babba amma bazaka fini da komaiba, ka sani kawai ina yimaka karane da kuma biyayyah dan baka girmanka amma bawai dan tsoranka ba FERAS, kuma wallahi tunda akazo wannan matakin a wannan karon bazan zuba maka idoba dole na nuna maka iya karka dama saboda Ammee nake jurewa to amma tunda itama baka ɗauketa a bakin komaiba so kake ka kashemana ita bazan taba raga maka ba , mitswwwww yaja tsaki ya kashe wayar


A ban garan FERAS kuwa yana kokarin maida martani yaji shaikh ali ya yanke wayar cikin zafin zuciya yana huci ya shiga kiran ali amma ya kashe wayarsa cikin bacin rai yayi jifah da tamfatsetsiyar wayar tasa a kwalta kuma yasa tayar mota yabi takanta ko layinsa bai tsaya ɗaukaba dan tsan tsar bacin rai duk tsadar wayarnan haka ya lahantata wadda da kudin marayu yan uwansa yasiya wai dan ya fita daban cikin gayu ,



Ni kuwa yar mutan libya nace Allah yarabamu da bakar zuciya irinta FERAS 🙆♀️ bari kuma na tattara kayana izuwa gidansu Raihan 🚶🏼♀️




★★★ jikin baki yayi sanyi ba yabo ba fallasa suka ce tafiya zasuyi Raihan kuwa kunya tagama mamayeshi yayi musu rakiya bakin mota sai abokin nasa yace " nikam Raihan lfy naga gaba ɗaya madam bata wal wala kodai batajin daɗin jikintane , murmushi Raihan yayi yace, " eh da wannan ma dan jiya saida na kaita sandiliya ( kyamis ) bata jin dadin jikinta

" ah haba shiyasa naga yanayin to kodai kodai har mun samu baby ne ? , dariya Raihan yayi a wannan karon yace ," ah haba saikace wani ayu daga yin auran ko sati bamu rufaba zaa samu baby, mustapha yakuma cewa " to nasan ya karfin injinka yake ai abun rabone

" to naji amma dai wannan ba abinda kake nufi bane , nan Raihan yayi musu sallama suka tafi hadi dabawa fatima kudi mai tsoka yana mata godiya


Suna tafiya ya nufo gidan a fusace tunkan ya karasa yake naɗe hannun riga dan yariga ya kufula da tozartashin da tayi ,

Maryam tana zaune a parlor taga shigowar Raihan a fusace da gudu tayi bedroom dinta yabi bayanta tana kokarin dannawa kofa key yatura sai kuwa tai baya da gudu kuryar makeken bed dinta tana kuka

Shikuwa Raihan baiko cire takalmin kafarsaba ya haye gado ya cebkota , mikar da ita yafara yi a kwance saman bed ɗin sannan ya wanka mata mari har sau huɗu saida taga wuta duk da hakan bai kyaletaba ya cire rigarsa take faffadan kirjinsa ya bayyana saiya faɗa kanta ya sakarmata duk wani nauyinshi yana mammatsata tamkar mai kwabin fulawar gurasa da hannu

Maryam kuwa ihu take kurmawa tana magiya ya ɗagata dan tsabar nauyinshi jitake har numfashinta yana cijewa ga kuma matsar dayakewa jikinta duk da bashi da kiba amma akwai jikin maza madaka gakuma nauyi , maryam datayi ihu zai doke bakin haka datasa hannunta tana tureshi zai murde hannun ,, yau kamdai maryam taga horo na rashin imani dan kanta tagaji da kwatar kanta ta kyaleshi yagama yimata duk wata izaya saida yagaji dan kansa ya ɗagata yasa riga yafice

Yana fita ta rushe da wani sabon kukan a zuciyar ta tace daga yarjejeniya yana nema ya lahantani wallahi bazaiyuba dole a war ware yarjejeniyar nan , da kyar ta

Please Login or Register in order to submit comment