Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kanta a mudubi tundaga sama har kasa sai chan tayi murmushi tayi kwafa cikin kasan zuciyar ta take tunanin meyasa Raihan baya sonta duk da kyau da sura mai kyau da Allah yayi mata, rashin mai bata amsane yasata sakin zanchan ta tashi ta wuce kitchen abin mamaki sai taga wannan ƴar dattijuwar dasukazo da Maryam ce take girki aciki

Ƴar tsohuwa kuwa tana ganin Islam cikin fara arta ta gaishe ta, da han zari Islam ta ɗaga mata hannu rai a bache tace,

" Dakata malama banason gaisuwar ki wane yabaki izinin shigomin kitchen uban me kike nema anan ko bakida labarin nan gidanane bana waccan mayyar ba oya maza maza kifice min dagani tunkan nasa hannu na fitar dake,

Sakin baki tsohuwa tayi galala tana kallon ikon Allah ba shakka wannan itace Wadda aka haɗa baki da ita aka kori Maryam dan ta aure mata miji cikin nuna rashin damuwa tsohuwa tace,

" Ba shakka ai zaki aikata fiye da hakama indai kece Islam to amma fa kisani ita duniyar nan faɗine da ita wanda baizo bama jiransa take bare wanda yazo yana cikinta, tsohuwa tana gama maganar ta tafice tabar mata kitchen ɗin

Dogon tsaki Islam taja sannan tafara shirye shiryen dafa breakfast ,



Maryam ce tafito parlo sanye da kana nan kaya wanda sukai matukar karbar jikinta saboda tayi kiba masha Allah kota ina kamshi take bazawa zama tayi a parlo tanajin gidan yadda yake tashin kamshin abinci a zatonta tsohuwa ce take girkin chan saitaga tsohuwar ta fito daga ɗakinta

Bayan ta karaso Maryam ta tsugunna har kasa ta gaishe ta cikin jin daɗi tsohuwa ta amsa tana tam bayar jikin nata,

" Jiki da sauki alhamdulillah , " to masha Allah ina jikan nawa, " yana ciki ai har na shirya shi ma ya koma bacci,

" Mekike dafa manane tunda safe haka, murmushi tsohuwa tayi tace, " bani nake girkin ba abokiyar zamanki ce,

Maryam tana jin haka ta fahimci Islam ce wani murmushi tayi akan fuska wanda baikai zuciyar ta ba wato ansamu nutsuwa saboda Raihan ya kwana a ɗakin ta har wani breakfast take girka masa wani irin baƙin ciki Maryam taji ya tsaya mata arai wato shi kishi duk inda yake kishine

Maryam bata kara jin wani takaici ba saida taga yadda Islam ta ɗame taci kwalliya sai wani baza gashi take tana yanga,

Misalin karfe bakwai Raihan ya shigo dauke da sallahma abakinsa kallo ɗaya Maryam tayi masa ta kauda kai dan gani tayi yaci kwalliya harda sauya jallabiyarsa dan yana ɗakin Islam,

Shikuwa Raihan yana ganin Maryam a parlo wani irin daɗi yaji da sauri ya karaso ya zauna a kusa da ita yana faɗaɗa fara arsa yace, " hajiya ta anfito ne

Murmushin dole Maryam tayi dan karya gane kuncin dake kasan ranta cikin sakin fuska tace, " eh wlh dama naji shiru baka shigo bane, ina masallaci ya bata amsa yana shigewa bedroom ɗin ta

Jim kadan Maryam tayi sannan ta tashi tabi bayansa zaune ta taddashi ya dauki jaririn yana masa addu,o,i

Zama tayi kusa dashi tana cewa, " hubby dama inaso muyi wata magana, kai kawai ya gyada mata alamar yana sauraron ta, ita kuma ta cigaba da faɗin

" Ya kamata ka gyarawa Islam sabon gidannan naka nakusa da gidan papy azuba mata kaya ta koma tunda itace amarya kaga gidannan bazai mana ba mu biyu,

" Kwarai kuwa kinyi magana mai kyau amma ni har yanzu hankali na bai kwanta da Islam ba ina samata idone nagani ya zaman zai kasance idan ta sake tayi yunkurin rusa mana farinciki to zan ture duk wani mutun tawa dake tsakanina da ita nasake ta kowa ya huta,

" Hmm kaidai baka raboda maganar saki jiran kiris kawai kake, Maryam ta faɗa tana yar dariya,

" Kece bakisan halin mutanan nan ba sun wuce inda kike tunani,

" To ai shikke nan Allah yasa mu dace sai kuma magana ta biyu inai maka albishir da yau zan baka labarin rayuwata da sanar dakai koni wacece

Raihan yanajin haka ya ɗago kai da sauri ya kalle ta cikin mamaki ya ajiye jaririn a gadon yara ya kama hannun ta cike da zumuɗi yace, " da gaske kike yau zaki sanar dani abinda na daɗe ina burin ji

Gyada masa kai tayi tana murmushi shi kuma ya rungume ta sai da suka dauki sakanni sannan ya sake ta ya kalleta ido cikin ido yace, " ina sauraron ki,

Cikin sassanyar murya tace

Sunana Maryam sunan babana Alhaji Al,Hassan Adam datti sunan mamana samera yusuf datti

Mamana da babana yan uwan junane duk danwa da dan kani suke a babban family na Alhaji uba dattijo dake Nigeria jahar Gombe

Babana ɗan kasuwa ne sosai tun yana matashi yake soyayya da umma amma mahaifin mamana baya son alakar su saboda babana mashayin giyane anyi anyi ya daina yaki ita kuma maman ahaka take sonshi

Dama kowa yasan suna soyayyah sai wata rana baban yafito yace yanaso abashi auren ummah na amma sai duk Yan family din dattijo suka nuna rashin goyan bayansu

Hakan ne ya fusata baba da mama suka yanke shawarar guduwa suyi aure, hakance kuwa ta faru suka tattare yan kuɗin da suke dasu suka gudu garin kano

Anan ne suka sauka cikin wani kauye da ake ce masa daka tsalle anan suka sauka gidan wani liman aka daura musu aure aka basu daki suka zauna

Babana yafara kasuwan cin saida kaji da kudin daya zo dasu yasai abin hawa na babur yana siyan kaji a kaushe yakai burni ya siyar ahaka suke rufawa kansu a siri amma duk da haka baibar shan giya ba

Bayan shekara daya da aurenne suka samu haihuwar da namiji mai kama da babana aka sa mishi suna Abbakar, bayan shekara uku aka haifeni daga nan mama bata kuma samun haihuwa ba

Nida yaya Abbakar munyi karatu amakaran ta mai kyau saboda baba Allah yayi masa rufin asiri da yar sana,arsa har gidan gona ya bude yanzu harka ta zama baba yabar kauye ya koma cikin gari a unguwar rijiyar zaki ya gina gida amma babban gidan gonar sa yana kauyen daka tsalle

Alokacin danakai shekara 15 ne nagama makaran tar Sakandire yayana kuma yana ja mi,a yana karatu ɓan garan likita

Kwatsan ummah tasamu wani cikin munata murna nida yaya Abbakar duk da lokacin munsan babban mu kwararran mashayi ne amma hakan yazame mana jiki a gabanmu ma sha yake giya kuwa babu inda bazaka ganta ba agidanmu

Bayan cikin mama ya tsufane wata ranar lahadi da bazan taba mantawa da itaba daren kaddara ta daren daya zama silar rushewar farincikina daren dayasa nazama mara komai da kowa acikin wannan duniyar,......

Kuka Maryam tarushe dashi mai cinrai tana rintse ido tana juya kai hannun ta ɗaya akan kirjinta alamar damuwa da abinda ta tuna, Raihan cikin tashin hankali yace,

" Subhanallah nafahim ci yadda kike ji idan har tunowa da wannan zai tada miki hankali bana bukatar ji dukda inason ganin ta hanyar dazan taimaka miki,

Maryam tajima tana kukan sannan tayi shiru tamai da ganinta ga Raihan tace

A wannan ranar ne da daddare bayan munyi sallar Isha, nida mama sai tace min idan inajin yunwa nazuba abinci naci ita bazata iya ciba tun safe takejin gabanta yana faduwa, shiru nayi ina marai raice fuska naturo baki ina cewa,

" Aa ni gaskiya mama idan har bazaki ciba nima bazan ciba, murmushi tayi taja hancina tace haba yarinya ta ai kinsan jikin mai ciki yau bana sha,awar komai,

Ana haka sai ga yaya Abbakar ya shigo ya zauna shima yana tsokana ta munata raha har naci abincin sannan nayi kallo danaji bacci kuma na shige ɗakina na kwanta yaya ma afalo ya kwanta yana karatu Haɗi da duba litattafai dan yace jiran dawowar baba yake komai dare zasuyi magana akan kuɗin jarabawa,



Chan cikin baccina najiyo Muryar Ummu sama sama tana kuka take cewa, " Abbakar baban naka zaka daka nashiga uku dan Allah Al, Hassan ka ajiye wukar nan ɗan naka zaka kashe,

Hayaniya naji sosai Muryar baba da ya Abbakar kamar ana damme dagu du na zabura ina kwance sai ganina nayi a tsaye nakarasa parlon ina kuka nake kiran ummah ummah a yadda nagansu ne ya tadamin hankali Ummu tarike baba kam tana kuka ga wata wuka a hannun sa shikuma yaya Abbakar yana tsaye da farar jallabiyar sa fuskar sa duk jini baba ya yankeshi, dasauri na karasa na rike yaya Abbakar ina kuka nake cewa,

" Yaya jini a fuskar ka ka gudu kar ka mutu nashiga uku baba dan Allah kayi hakuri wayyo ummana zan mutu jama,a kutai maka mana, yaya baice komai
Ba sai huci yake baba kuma yana faɗin

Samera ki cikani na kashe yarannan na huta, shikuma yaya yanajin haka
Yace " ka kashe ni mana sai me kashawo giyar ka kawai zan bari ka dakar min mahaifiyata wlh sai dai kadau Raina,

Baba yanajin haka ya ya fuzge daga rukon da ummah tai masa yazo asukwane ya faɗa kan yaya Abbakar ina kwallo a gabana ya dinga chaka masa wuka har ya daina motsi

Ummana kuwa tunda tayi ihun farko ta dafe kirji ta fadi bata kara shurawa ba nikam kasa kuka nayi na kame a tsaye ina binsu da kallo bugun kofar gidan mu da akai ne yasa babana ya ɗago arazane ya dubi ummah ya dagata yana jijjigata ahaka makota suka shigo suka tatda wannan mummunan tashin hankali mazan kuwa rike babana sukai kam yana kuka yake cewa Abbakar ka tashi karka mutu unmanka taki far faɗowa

A daren Yan sanda suka zo aka tafi da Abbakar da maman hospital Abbakar tunkan aje Asibitin yariga rai yayi halin sa ummah kuma ana kanta tun dare har gari ya waye babana kuma yana gurin yan sanda

Jama,ar unguwa ne sukai ma yaya Abbakar sutura aka kaishi inata kuka tamkar nabishi haka nakeji ya'ya Abbakar yana sona yana jidani yau gashi mummunar mutuwa ta riskeshi

Gidan mu ya cika da jama,a wasu ma badan gaisuwa suka zoba kawai dan sunji cewa ubane ya kashe dansa da yamma misalin karfe 4:26 motar Yan sanda ta kawo gawar ummah na daga asibiti wai daga ita har ɗan dake cikin sun mutu zuciyar ta ce tabuga, inajin haka nima nafada doguwar suma akai asibiti dani ban samu ganin jana izar ummana ba

Kwanana biyu bansan inda kaina yake ba a hospitel ana ukun na farfaɗo

Abinda na tarar yayi matukar dagamin hankali buɗe idona keda wuya na taddani a wani daki docton dake dubani ne yake kokarin yimin fyade kiri kiri naganshi tsirara akaina yana kokarin kwanciya dani

Da sauri na mike ina ihu duk da jirin dake dibana hakan bai hanani tureshi na tsinke ruwan da aka jonamin na take dagudu nafita daga asibitin ina fita titi na ga ashe yar karamar rigar masu jinya ce ajikina iya gyaiwa da sauri nahau adai daita nace yakaini rijiyar zaki dama banisa da unguwar mu yana saukene na shige makota wajen baba lantana ina kuka na rungume ta

Nakasa cewa komai ta nata tambaya ta jikina sai rawa yake mai a dai daita yayi sallamah aka bashi kudinsa, ruwan wanka lantana tasamin nayi wanka har wannan lokacin kuka nake shikke nan ummah na da yaya Abbakar sun mutu sun barni ni kadai gashi tunkan aje ko ina nafara haɗuwa da miyagun cikin duniya

Baba lanta na ce ta dinga rarrashi na tana min nasihar nayi hakuri da kaddara haka Allah ya tsaramin kwanci tashi babu wuya wata uku da faruwar wannan Al'amarin ga gidan mu nan bana iya zama saidai na dau kaya na fita kullum gidan lantana nake kwana batada ya mace mijinta ya mutu danta yana kaduna me kudine achan yake aiki da iyalansa yaransa biyu kanana yana kawowa lantana ziyara kuma yana mata aiken kudi sunan sa yaya abbah nasaba dashi dan har waya yake min yace idan ina bukatar kuɗi nasanar masa nikuma sai nace aa dan duk abinda nakeso lantana tana min

Kwatsan aka saki babana daga gidan yari wai angama Shari,a ance yanada tabin hankali , nidai ban yarda da hakanba shiyasa koda babana yazo yace inzo mukoma kauyen daka tsalle naki yarda dashi ya gaji da magiya kosan ganinsa banayi harya tafi

Idan aka samu wata yana zuwa ya dubani amma bana yarda dashi dan gani nake kasheni zaiyi


Ahaka rayuwa ta cigaba da tafiyar min ina yawan tunawa da ummata da yayana saidai nayita kuka kawata Aisha ita take rarrashi na yanzu kam alhamdulillahi nafara zuwa makaranta yaya Abba ya biyamin komai har islamiya ma nayi sauka daman tun iyaye na suna nan ina karatun arabi,

Yaya Abba ya bukaci nakoma gidansa da zama idinga kula da kananan yaransa dan matarsa aiki take zuwa dagasu sai yar aiki agidan, nima naso zuwa amma lantana ta hana wai bazata iya zama ita kadai ba saboda tsufa

Hakadai zancen tafiya ya watse kwatsam wata safiyar juma,a lantana ta tafi biki nikuma ina wanke wanke yaya Abba ya shigo yatsaya muka gaisa sannan ya shige daki chan naji ya kwalamin kira natashi naje

Ina zuwa naganshi zaune a parlor yacemin inzuba masa abinci nazuba masa nabashi nakai masa ruwa da lemo yanata kallona yace, " kanwata nifa hira nakeso kimin,

Ban kawo komai a raina ba na zauna dama nagama wanke wanken muka fara hira chan yace min, " maryam kingirma fa tubar kallah aure yakama ta amiki,
Rufe fuska nayi cikin jin kunya nace aa banaso sai naji yacemin, " daga ganin wannan kyakkyawar surar taki mai tada hankali ansan zaki dadı kuma kema akaran kanki nasan kina Sha,awar aure ko samun saurayin dazai dinga debe miki kewa

Cike da mamaki na sauya fuska dan naji maganar tasa wata iriya shiru nayi na takure ina tunani meyake nufi chan naji ya matso kusa dani ya rike hannu na da sauri na kalleshi cike da tsoro abin da bai taba min ba ganin na tsarota yasashi cewa

" Karki damu kanwa ta nasan baki fahim ceni ba ina nufin ni zan zame miki wannan saurayin dazan jiyar dake duk wata ni ima dajin dadın rayuwa abinda nake bukata kawai ki yarda dani, yafada yana mai damka min rafar yan dari dari na dubu ashirin a hannu na

Da sauri na yadda kudin idona yacika da kwallah chan banyi aune ba naji hannun sa a kirji na cikin tashin hankali na zabura ina kuka na mike tsaye shime tashin yayi ya rike hannuna yana cewa, " dan Allah karki fishi wallahi na dade ina Sha,awar ki idan ma bazakiyi hakan ba to kiyarda na aureki

Nikam kin saurarar sa nayi ina kuka nasa hijabi na gudu gidansu Aisha kawata ina zuwa na tadda batanan asoran gidansu na zauna dan bazan iya zama aciki ba mamanta ta mutu kishiyar mamanta kuma masifaffiya ce

Saida naci kuka na gode Allah idona yayi jajir Aisha ta taddani juyin duniya nakasa gaya mata abinda yafaru hakadai taɗan lallabani har magariba ta rakani gidah sannan yaya abbah ya tafi na tadda ya ajemin wannan kuɗin kuma yarubuta min wasika ta ban hakuri

Hakadai nan ma rayuwa ta cigaba da tafiya gaba daya na tsani yaya Abba koyazo bana sakar masa fuska idan kuwa lantana taje unguwa nima gidansu Aisha nake zuwa


Bayan wata shida Allah yayiwa lantana rasuwa alokacin shekarata 18 nayi kuka mara adadi na shiga damuwa anyi zaman makoki an watse yaya Abba ya kirani yace idan na amince ya aureni tunda yanzu banida kowa sai su haka nan ma na kuma ki da maganarsa danni ko kadan bansan so ba

Ganin babu inda Za,a barni ne yasa matar yaya Abba tace nabisu can gidansu na zauna tunda nagama karatu kafin nasamu mijin aure

Zamana agidan naji dadin sa dan yaya Abba baya shiga harkata matarsa tana sona nasaba da ƴaƴansa kullum zasu tafi aikinsu yarankuma suje makaranta daga ni sai jummai mai aiki


Cikin yan watanni lissafin yaya Abba yakuma dawowa kaina ya matsamin da zanchan lalata har takai takawo tsakiyar dare zaina shigowa ɗakina sai nayi kuka namasa magiya sannan zaice wai na rungume shi idan inaso yatafi babu yadda na iya dole hakan nake masa dan gudun karya tabamin mutumci na

Wata rana kamar yadda yasaba ya shigomin ɗaki yasa na rungume shi matarsa ta ganmu ina kuka zan karasa kusa da ita da sauri ta turani tana cewa

" Dakata munafuka dama yacemin kina bibiyar sa ashe da gaskene, dasauri na kalleshi ina kuka nace yaya Abba dan Allah kafada mata babu ruwana kanna rufe baki naji ya wankan Mari yana cewa,

" Matsa daga nan muna fuka naga tsakiyar dare kike tashi kizo ki kirani wai saina kwanta dake kinsaba da maza bakya iya bacci idan batare da namiji ba haka zanta baki hakuri kiki hakura yau shine hadda rungume ni ai gashi ta ganki

Mamaki ne ya hanani magana kirikiri yayi min sharri

Gari na wayewo suka koreni daga gidan babu yadda na iya haka na komo Kano kauyen daka tsalle nan wajen babana yayi farin ciki da zuwa na

Abinda ya bani haushi baba duk ya tsiyace saboda shan giya duk ya karar da dukiyar sa hatta gidan gonar ya siyar ya cinye kudin babu yadda na iya da kaddara haka na zauna


Wata rana babana yace na shirya naraka shi unguwa nashur ya azatona gidan Yan uwan sa zai kaini dan dama bansan kowa nasaba

Haka nabishi chan wani gari dabansan sunan sa ba inaji ina gani babana ya kaini gurin wasu mutane ashe gidan karuwai ne ya Saidani aka bashi giya da kudi

Aranar nayi kuka mara adadi suka kulleni a daki wata mata mara imani ita ta siyeni ta bawa wasu hajiyoyi mata ni wai ayi lezbiyan dani

Aka kaini gidan wata mata suka dunga bani abinci da magani wai wata hajıya aka ajewa ni tace macen da bata taba sanin kowaba take so hakan yahana matan wajen sumin komai abinci mai lfy akeban ga gyaran jiki kamar wata amarya har zuwa lolacin da hajiya tazo ta daukeni ta kama mana hotel wai anan zamuyi daran farko

Dare nayi hajıya tasa hannu zata ciremin kaya ai kuwa nasamu kwalbar lemo na fashe mata uku akai ta suma na gudu daga hotel din bansan inda na nufaba haka na kwana a tashar jirgin kasa dama na kwashi kudi washe gari da safe na fati kano nakoma tsohuwar unguwar mu rijiyar zaki kwana na biyu achan gidansu Aisha dama nafada mata duk abinda yafaru dani

Ai kuwa tace min kamata yayi nabar kasar gaba daya natafi neman kudi dan idan nazauna babu mai rikeni banida kowa sai Allah anan tayi min hanya wajen kanwan mamanta mai kai mutane daular larabawa yin aiki

Wannan shine da lilin zuwana daulatul arab wato kasar Dubai


Raihan shima yayi kuka dajin tarihin rayuwar Maryam soyayyar ta ce dakuma tausayin ta suka kuma nunkuwa a ransa tabbas babu wanda ya isa yarabashi da matarsa Allah ne kawai yasan munufarsa ta kullah wannan soyayyar

Raihan sosai ya rungume ta a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya yace, " gaskiya kinsha wuya kuma kinga jarabta a rayuwar ki namiki alkhawari zan share miki hawaye har karshen rayuwata bazaki kara shiga damuwa ba ina sonki kuma ina kaunar ki ke tamkar rayuwata ce wallahi wallahi babu abinda zan tauye miki matukar ina numfashi adoran duniya

Kwatar da kanta tayi a kafadar sa tana hawaye tace, " tunkan muyi aure zuciyata ta gamsu kai garkuwane a gareni inai maka so mara misali kuma ina alfahari dakai dan bada ban kai ba bansan ya rayuwata zata kasance ba

.... Bayan nazo daular Dubai na hadu da babbancin rayuwa akwai wata mata hajiya ake cema itace mai saukar mata ta nema musu aiki ce gidan ta matane burjik

Anan ne aka samomin aiki agidan wata tsohuwa babu abinda nake mata saidai idan zata fita shan iska nakamata muzagaye gidan kuma ina tayata hira sosai nasaba da balarabiyar nan sunada mutumci shekara ta biyu a wajensu nakware dajin larabci sosai kwatsam Allah yayiwa tsohuwa rasuwa

Ananne aikina yakare nakoma gidan hajiya da zama dadi ba dadi haka nake hakuri duk rabin matan gidan karuwanci suke da larabawa da bakake inada kawa sunanta mayah kyakkyawa ce Amma ta girmeni yar kasar fakistan ce tana sana,ar lalle sosai take sona

Mayah budurwar Yasir kaninka ce ya yaudare ta yace zai aureta inda tabi daɗin bakinsa ta biye masa suka tafi ya kama mata hotel harna wata biyu suke rayuwa tamkar ma,aurata mayah bata taba sanin ɗa namiji ba a rayuwarta sai akan Yasir amma hakan bai hanashi butulce mata ba yayi mata ciki ya gudu yabar ta ta dawo gidan hajiya

Hajiya tayi tayi mayah tazubar da cikin amma taki hakadai muka hakura ashe mayah abun yana damunta kwatsam wata rana da dare muna kwance sai na jita tana wani irin tari ina zuwa inda take naga tasha guba tasha tana gabda mutuwa tace nayi mata alkhawarin daukar fansa akan Yasir saida na dau mata alkhawarin Allah yayi mata cikawa

Nayi kukan rashin mayah nayi bakin ciki bayan wasu yan kwanaki aka kawoni aiki gidanku ina sane na nuna banajin yaranku na dinga bincike akan Yasir ina bibiyar sa sau biyu ina samasa guba a abinci baya ci saidai nazubar

Shikuma Yasir ganin nafiya sa ido akansa ne yaja hankalin sa kaina ya dinga kaimin farmaki yana so ya batamin rayuwata da taimakon Allah da tai makonka na kubuta daga hannun Yasir

Daga Raihan har Maryam ajiyar zuciya suka sauke Maryam tace wannan shine labari na bana kaunar tunashi saboda tashin hankalin da suka faru a ciki

Narasa kowa har yanzu ban karajin labarin mahaifina ba yana nan ko ya mutu nidai nasan asalin mu yan kano ne a Gombe A family din Alhaji uba dattijo wanda akafi sani da tatti

Har yau bansan ta inda zan fara nemansu ba,

Raihan jijjiga kai yayi yace, " karki damu kinada ni zan taimaka miki wajen nemo ahalinki namiki alkhawari amma kibari yaronmu ya kara wayo ta yadda idan munje zaiyi magana dasu

Murmushin jin dadi tayi ta rungume shi cike da soyayyah




To masu bibiyar wannan littafi kundai ji wacece Maryam kuma kunji labarin ta muhaɗu a page nagaba danjin mezai faru




✍🏻 ZAINAB Ahmad Yusuf ce
DAULATUL ARAB

By Zainab Ahmad Yusuf


PAGE 9️⃣9️⃣





Kaiwa da koma Islam take acikin ɗaki abin duniya yayi mata zafi tarasa ta yadda zata sarrafa kanta zuciyar ta wani zugi da raɗaɗi take mata jitake kamar zata fito meyake faruwa ne kodai alhakin Maryam ne yake bibiyar ta

Cikin mawuyacin hali ta faɗa kan bed tana sakin kuka mai tsuma zuciya tunanin ta ɗaya yanzu haka zata cigaba da rayuwar gidan Raihan tana matar sa amma babu koda sakin fuska ina gaskiya da sake

Tashi tayi ta ɗauki wayarta tana latsawa ko zataji sassauci chan taji Muryar Raihan da Maryam suna hira a palo cikin ni shadi, wani kukan ta sake rushewa dashi tana dafe kanta daya fara mata ciwo

Maryam dake zaune a palo tajiyo sautin kuka kasa kasa sai ta kalli Raihan tanason ganin yanayin sa dan tasa Islam ce ke kuka, shikam ko ajikinsa ya cigaba da yiwa babynsa wasa

Ajiyar zuciya ta sauke ta kalleshi cikin lankwasa harshe tace, " meyake faruwa yaya ko wani abun kamata take kuka,

Noke kafaɗa yayi alamar baisan komai ba, Maryam cikin nuna rashin jin dadi tace, " pls kaje kaji meyake damunta wata kila batajin daɗi,

Raihan kawai mamakin zuciya irin ta Maryam yake bayaso taji babu daɗi hakan yasashi mikewa ya mika mata babyn yawuce ɗakin Islam

Tura kofa yayi ya karasa har bakin bed ɗin da take kwance ya harɗe hannuwa yana kallonta batare dayace komai ba

Islam dake kwance tayi ruf da ciki sai sauke nannauyar ajiyar zuciya take, kamshin turaren shi ya daki hancin ta hakan ne yasanar mata zuwan sa duk da haushin shi takeji hakan bai hanata jin daɗin zuwan da yayi ba ashe dai ya damu da ita

Tsawan sakanni aka kwashe yana tsaye baice mata uffan ba itama bata ɗagoba chan dai ya gaji yasa hannu ya jawota jikinshi yarungume yana shafa bayanta alamar rarrashi murya kasa kasa yace, " meyasa kike kuka me akai miki?,

Islam mamaki ne ya isheta kodai mafarki take chab gaskiya tayi mamaki cikin rawar murya tace, " kai na kemin ciwo, tafaɗa tana kara shigewa kirjin sa babu abinda kake ji sai sautin ajiyar zuciyar ta

Raihan kuwa acikin zuciyar shi tausayi take bashi shima kanshi yasan abinda yayi mata bai kyauta ba amma babu yadda zaiyi dole ya daure zuciyar shi

Please Login or Register in order to submit comment