Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yabata kulawa tunda itama matarsa ce kawai yana mata hakane danta fahimci kuskuren ta amma yasan tana sansa,

" Ayya sannu ai da saiki faɗamin bawai kidinga kuka ba, yakarasa maganar yana mai kwantar da ita akan bed ɗin yaja mata bargo ya rufe mana jikinta yafito

Maryam tana ganin fitowar shi tasaki murmushi shima ya maida mata ya wuce ɗakinshi ya ɗakko maganin ciwan kai ya koma wajen Islam ya ɗauki ruwa mai dan sanyi ya tashe ta yabata maganin

Ya mike zai fita Islam ta rike hannun shi tana hawaye tace, " dan Allah yaya Raihan kayafe min duk abinda na maka nidai fatana kawai kasoni ka kula dani wlh nayi nadamar aikata hakan Please ka yafemin kuma itama Maryam ɗin zan bata hakuri insha Allah bazaka kuma samuna da wata matsala ba nayi maka alkhawari dama ɗaya kawai nakeso kabani

Raihan cikin jinzafin zuciya ya furzar da iska daga bakinshi yana tuna irin rashin imanin da suka aikatawa Maryam, rintse ido yayi yana kara tuno ba Islam bace kadai mai laifi babbar wadda ta haddasa abin ame Hauwa ce kuma yanzu idan yace bazai yafewa Islam ba zata iya chanza shawara ta kuma haɗa wani tuggun gara ya yafe mata komai yazo karshe

Cikin kasala yace, " okay babu damuwa Allah yasa hakan ne da gaske amma kisani idan har na kamaki da wani kuskuren zan sakeki kuma saina miki wulakancin da tunda kikazo duniya bakiga wanda akaiwa irinsa ba

Kuka tasa tana dafe kanta take daɗa jaddada masa da gaske ta tuba, dolace tasashi sakin fuska ya rungume ta jikinsa yana shaida mata ya yafe kuma lalle idan tanasan zama dashi ta zauna da Maryam lfy

Murmushin samun nasara tayi tanajin daɗin hakan ta fahimci zafin zuciya da nuna fishi bazai sa tayi nasara ba dole ta haɗa da kissa

Raihan kuwa yaso ya fita amma ya fasa ya biyewa Islam suka fara zuba romantic a zafafe dan dama shi a matse yake

Maryam tana palo shiru shuru Raihan bai fitoba sai ta tashi ta kai yaron ɗaki ta dawo tayi sashin Islam tana zuwa bakin ƙofa tafara jiyo nishi sama sama sai ta kasa kunne taji bil hakki da gaskiya shanawar su suke dan babu abinda kakeji sai sambatu

Lokaci ɗaya taji ranta ya baci zuciyar ta tana mata zafi kishi ne kawai yake damunta babu yadda zatai dole taja kafa dakyar ta koma ɗaki tana haɗa kai da guiwa, tunani take ashe dama so yake yayi sex shiyasa babu musu ya tashi ya tafi ashe da abinda yake so

Chan wata zuciyar taraya mata to ita menene nata aciki mata da mijine fa, duk yadda taso ta cire abin aranta ta kasa komawa tayi kan bed ta rungumi filo tana sauke ajiyar zuciya hawaye na zuba a fuskar ta tafara karanta addu,oi nasa sanyin zuciya idonta a lumshe zuwa yan mintina taji komai ya fara tafi mata arai tayi hamdala taroki Allah yasa hakan shine mafi alkhairi Allah ya haɗa kansu


Raihan saida yayi 2 Round yasamu cikekkiyar Satisfied Islam kuwa ta gurzu anji maza tasha kuka amma dan naci bata iya hanashi ba ji take tamkar ansa mata attaruhu a HQ nata duk ta haɗa gumi fuskar nan tayi gaje gaje gajikinta sai ɓari yake

Kallonta Raihan yayi cikin nuna kulawa yafara rarrashin ta yasan tayi kokari dan wannan karo na biyu kenan, saida yaji jikinta yadaina ɓari tukunna ya tashi ya faɗa toilet yayi wanka ya haɗa mata ruwan zafi yasa sinadarin kashe zafi aciki

Yana fitowa ya ɗauketa chak ya kaita yasata cikin ruwan ya tsaya saida ya tabbata ta gasu sannan ya fito yabar ta aciki tana wanka

Dubawa yayi yaɗau kaya yasa yaje bakin Mirror ya shafa mai yaduba babu turaren sa acikin saitin kayan ta kawai saiya fesa na Islam ya fice daga ɗakin

Yana fita yaɗau mukullin mota yana sauri zai fita ya leka ɗakin Maryam ya ganta tana bacci yana murmushi ya sunkuya kusa da ita yayi mata kiss a goshi ya shafi kanta ya matsa kusa da jaririnsa shima yamasa kiss yaja musu ƙofa ya fice

Maryam tanaji tamai shiru babban abin takaicin saida taji kamshin turaren Islam ajikinshi ta kara kufula tana tinanin yanzu shikkenan irin yadda Raihan yake rawar kafa akanta haka zaidinga yiwa Islam musamman ma yanzu da take bashi HQ nata yana ci ihmm kawai Maryam tace

Islam kuwa jitake komai yayi mata wasai aranta take raya inda Raihan zai dunga bata kulawa kamar haka to babu ruwan ta da wata kishiya dama haushin ta ɗaya akwace mata shi, cikin nishadi da annushuwa ta sheka kwalliya dan yau ma kwanan ta ne riga da siket tasa mai jan hankali sannan ta kimtsa ɗakin ta fito parlo tana ta wani yamutsa fuska ta zauna chan ta yanke shawarar ta kira Raihan taji Muryar sa ko hakan zai sashi yin tunanin ta

Tashi tayi taje ta dakko wayar tana dawowa taga Maryam a palo tayi murmushi tace, " sannu da hutawa ya baby, Maryam batayi mamakin jin Islam tayi mata magana ba tace lfy a takaice tacigaba da kwallon TV

Zama Islam tayi kusa da ita ta danna wayar takira Raihan,

Yana zaune cikin office dinsa yaga kiranta da kamar ya ɗauka har ta yanke

Islam ganin bai dauka ba yasata hakura cikin sanyin murya tace, " Maryam mekikeso adafa da rana? ,

" Ihmmmm kune amare ai Islam kidafa komai ma, " haba kufa masu gidane uwar gida ran gida ki manta da komai ki saki jikinki nima yanzu nagane gaskiya na zabi zama dake lfy dan na samu zuciyar mijina,

" Idan har da gaske kike zanfi kowa farin ciki da hakan Islam Allah yasa, tace Ameen



Bayan kwana hudu abubuwa sunyi sauki Islam ta haɗa hankalin ta waje ɗaya tunda ta fahimci mai Raihan yakeso ta zauna lfy yanzu kam kalau suke zaune Maryam ma tasaki jiki da ita sosai Raihan kuwa daɗin hakan yakeji

A ban garan papy kuwa yaje yagano amarya har ankai komai na biki tunda shi yace da gaggawa yakeso ya sakar musu bakin aljihu sai wadaka da kudi suke

Ame Hauwa duk tana sane da hidimar auren sosai ta shiga tashin hankali babu yadda zatai tayi bin bokayen amma babu wani ci gaba gashi batasan komai game da matar dazai aura ba bare tayi takansu papy saboda cin fuska agaban ta yake waya bako kunya haka ya dau Yasmin goɗai goɗai da ita yakaita ta kwana biyu a gidan su amarya ta dawo aka haɗa mata sha tara ta arziki

Yanzu gyaran gidan papy ake nera tayi kuka an warewa amarya part dinta a saman bene ƙarshen haduwa sashin amarya yayi aljannar duniya kenan



Suna yau yake saura kwana uku kuma ranar za,a daura auren papy kowa na gidan hidima yake dan babu ruwan su da wani nuna bakin ciki kodan gudun kar suyi bakin jini

Islam ma an gyara mata sabon gidanta da har zata koma papy yace kar a rabasu ya bawa Raihan sabon gida fil acikin family Hours sama da kasane ran tsatstse bedroom dinsu duk suna saman parlo kuma akasa kowa da parlon sa sai babba a tsakiya sannan akwai ɗakunan baki a kasan saman benan ma kowa yanada parlon acikin bedroom dinsa

Gida ya rantsu iya rantsuwa anzuba komai har sun koma yan,uwa sai murna suke Raihan ya saiwa Maryam da Islam motoci Sababbi masu tsada da kyau

Ya sakewa Maryam lefe dan an kwashe nata yayi mata mai guda goma goma har saiti uku akwai komai aciki ga sarkar Gold tundaga wuya har kasa

Yau takama saura kwana biyu suna Maryam ta fito daga wanka tana shafa mai daga ita sai towel ajikinta raihan ya shigo shida kanshi ya shafa mata Grease yana jadda da mata yadda yayi kewar ta danshi harga Allah bayajin daɗin Islam kamar yadda yake samun nutsuwa da ita, haɗata da Allah yasoma yi idan ta tsarkaka tabashi hakkin sa ba saitayi arba'in ba

Rufe baki tayi cikin tsoro ta tuna abinda tsohuwa tace mata indai ta yarda ta bashi kanta da danyen jego zai iya yagata ta hakura sai tayi arba'in, tuno hakanne yasata cewa

Ai ba lallai ma ya tsaya ba har arba'in din, cikin marai raice fuska ya roketa tace ai haka tsarin yake tunda kanada wata matar ka hakura har lokacin dan dole yabar zancen

Suka fita parlon ta tadda Amal tazo ita da Yasir bayan sun gaisa Raihan da Yasir suka zauna a parlo Maryam kuwa taja hannun Amal suka wuce ɗaki



Bayan sun gaisa ne suke hirar auren papy Amal tace, " yashirin biki wlh duk nayi bizi ga kuma suna na karatowa

" Nima haka wlh Amal danma yaya Raihan yana tayani kuma yanzu aiyukan gida Islam ce keyi wlh baki ganiba cikin kwanakin nan ta sauya har mamaki take bani kamar ba itaba rannan ma ita tayiwa baby wanka agaban Raihan,

Amal cikin nuna jindadi tace, " alhamdulillah haka akeso ashe zata ɗau shawara ai wlh da tayi wasa da yanzu tazama jawara, ta karasa maganar tana dariya

Hirarsu suka cigaba dayi cikin nishadi Amal tace, " yakamata idan kinyi arba'in kifara koyan mota kizo nizan koya miki koda yake nasan yaya bazai bari ba shizai koya miki da kansa anayi ana shan love

" Amal wlh kina ban dariya ai kamar kinsani yanzun ma ya aka kare sai fama nake dashi Allah yasoni ma akwai Islam shiyasa ma bazan taba bashi ba sai bayan nayi arba'in,

Rike baki Amal tayi tana zaro ido tace, " arba'in yayi yawa Maryam gaskiya ki bashi idan kin warke ai saiya takura da yawa,

" Bazaki ganeba Amal sonake nayi gyare gyare dukda gurin ya rufe amma ina bukatar hutu kinsan fa haihuwa ba wasa bace musamman ni danayi ta fari,

" To kumafa hakane amma gaskiya kifara gyaran ki tun wuri nan da sati biyu abashi hakkin sa akwai wajen wata mai magani da take haɗa amare lokacin bikina ita ta haɗa ni kuma anty laulam ma agurinta take siyan magani zan hadaku tabaki wlh sai kinjiki tamkar baki taba haihuwa ba kuma tana gyaran jiki fatar ki ta ƙara kyau da haske,

Rungume ta Maryam tayi tana murna tace, " gaskiya naji daɗi kawata Allah yabiya ki,

Islam ce tafito tun daga saman take hango Raihan da Yasir a parlon kasa suna hira, sakkowa tayi tana fadada fara,arta ta zauna tana cewa

" Barkan ku da hutawa Yasir ina yini, shima cikinfara a ya amsa mata dan yanzu yasan ta sauya,

Kitchen ta wuce ta ɗora gahwa bayan yan sakanni ta tafasa ta debo glass cup ta jero a tire ta kawo musu Raihan yana murmushi yayi mata sannu

Juyawa tayi zata tafi tace, " to Yasir agaida gida kace ina gaida Amal,

" ai tare mukazo tana dakin Maryam, okay tace ta wuce saman

Da sallama abakin ta tashiga dakin Maryam ta taddasu sunata hira tazauna suka gaisa tace, " ina bacci kuka shigo banji shigowar ki ba,

Murmushi Amal tayi tace, " ai dana jiki shiru nasan kina chan kina bacci, Yar dariya Maryam tayi tace, " Dole tayi bacci ke kuwa amarya cefa ko bakiga harta sauya ba

Dukansu sukai dariya Islam ta karasa kusa da jaririn ta ɗaukeshi dayake idonsa biyu ta duba jikinshi ko yayi tutu ta sake masa famfas amma baiyi ba,

Itakan Amal har cikin ranta taji dadin yadda taga Islam tana nannan da babyn Maryam acikin zuciyar ta take rokon Allah yasa ta ɗore da haka har abada,



★★


A bangaran su feras kuwa abu ya tafi yadda akeso bassuna ta sauka lafiya ta haifi yanbiyu masu kama da ubansu kuma duka maza har anyi suna

Kowa na gidan yana cikin farin ciki habawa kuɗi kuwa ankashesu ni kaina bansan adadinsu ba hmmm abu nasu maganin a kwabesu

Sheikh Ali da feras sun haɗe kansu gwanin sha,awa anyi bikin Aisha gazzal ma ankusa nata, yanzu ammensu ras takejin zuciyar ta batada wata damuwa kullum addu'a take musu baki ɗaya haɗi da yiwa Allah godiya daya bata sirikai na hakika wanda babu mugunta akansu sun ɗauketa tamkar mahaifiyar su basasan ɓachin ranta

Part ɗin feras na nufa tundaga matattakalar benan nakejin wani sassanyan kamshi mai ratsa zuciya yana tashi ina shiga parlon na hangi bassuna a zaune hannunta rike da kaya chan ta tashi ta shiga dasu bedroom ta bude wdrp tasasu tanufi toilet tana murda wa tajishi a buɗe tacusa kai tana murmushi ta sameshi yana wanka karɓar soson tayi tana watsa mishi kallon love ta soma cu ɗashi da kanta

Yana murmushin jin daɗi yasa hannu yajawota jikinshi yana shafa mata kumfar a jiki, zaro ido tayi cikin mamaki tace, " yanzufa nayi wanka kake kara batani

Kashe mata ido yayi yana cewa, " saida nace karkiyi kibari mukara one round kikayi gashi kuma kin kawomin kanki, yakarashe maganar yana cire mata rigar dake jikinta, bassuna kam hakan yamata dan tunda tayi arba'in ta fahimci sex yafi mata dadi yanzu sam bata gajiya dashi kamar yadda shima baya gajiya ko fita yayi wajen aiki bajimawa yake ba saboda ita da baby's ɗinta, haka ta tayashi suka gurji juna kowa ya gamsu sukai wanka suka fito tare suka shirya ita tasa masa kaya shima yasa mata cikin soyayyah da nunawa juna kulawa

Tare suka sakko zuwa part ɗin Ammy dan Twins suna wajen ta

Saida suka zauna aka sha hira dan achan suka tadda jawahir da babyn ta





✍🏻 ZAINAB ZEENARIYA
⛲⛲⛲⛲DAULATUL ARAB⛲⛲⛲⛲



By Zainab Ahmad Yusuf ZEENARIYA


The last page 1️⃣0️⃣0️⃣



Alhamdulillah Alhamdulillah dukkan godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki tsira da aminci su tabbata ga shugaba Annabi Muhammad ( S A W )


Nayi farinciki sosai dana samu dama da Aron lokaci narubuta wannan labari ina mai Rokon Allah yasa jama'a su amfana dashi kuskuren dayake ciki kuma Allah ya yafe min 🤲🏻 Ameen


INA MIƘO GAISUWA MAI TARIN YAWA ga ɗaukacin Al, ummar da suke bibiyar wannan labarin wanda nasansu da wandama ban saniba 🫶🏻🫶🏻🫶🏻 nasan dayawa sun fahimci sakon dana isar acikin wannan littafin 🥰🥰🥰🥰

Masu kirana kai tsaye da yimin fatan Alkhairi ta WhatsApp kuma ban mance dakuba ina godiya God bless us together and God bless us in our lives Ameen 🥰🥰🥰🫶🏻🫶🏻


Inayiwa makaranta na Albishir da sabon labari wanda zan fara fitar muku dashi nan kusa bada jimawa ba kudai karku bari A barku abaya danjin sabon salon dana zo muku dashi mai rikitar wa chakwakiya kai abindai sai mun haɗe🤓🤓🤓

Masu yimin magana akan matsalar rashin yin typing da wuri kusha kurumin ku wannan mushkila tazo karshe da yardar Allah idan nafara bazan dakata ba harsai nakai ƙarshen book 🥰🥰🥰 harda masu cemin idan kuɗi nakeso na maidashi na kuɗi nadinga typing kullum indaina yi musu jan aji 🤣🤣🤣 kuma naga sakonku to kusha kurumin ku badan kuɗi nake typing ba na godewa Allah da ni imar daya wadatani da ita ɗari biyar ɗinki ko dubu ɗaya bazata isheni koda saka data ba 🤨🤨🤨 dan Allah nake kuma dan masoya mabiya sannan dan kwaɗayin ladan dazan samu daga wajen Ubangiji 🧕🏻 Allah yasa mudace Ameen 🤲🏻🤲🏻







Bismillahir rahmanurrahim



Bayan tafiyar su Amal ne Islam ta karaso kusa da kujerar da Maryam take kai ta dabafa tana kallon ta tace

" Nikam Maryam akwai wata tambaya danakeso nayi miki ina fatan bazakiji babu daɗi ba ko kidauke ta dawata munufa,

Murmushi Maryam tayi tace, " babu komai wlh Islam yi tambayar ki Allah yasa nasan amsarta,

Ɗan nisawa Islam tayi tafara magana dacewa, " tunda nake A rayuwata banta ba gamo da mutum mai sa,a da nasara acikin rayuwar saba sai ke, kina yawan tsallaka sharrika da dama wanda duk wanda akaiwa su baya hayewa kaɗan daga cikin irin nasarorin ki da suka bani mamaki shine na Auren Raihan da kikayi shin kinada masani akan asirin da su ame Hauwa sukai masa na karyaga wata mace ta burgeshi ballanta na yayi aure har a mallaka masa tarin dukiya da Company's, amma lokaci ɗaya mukaji labarin yace zai aureki bayan ke bama jinsin sa bace duk da cewa kema Allah yayi miki kyau ta ko ina amma mata masu suna mata ba irinaba kuma ba irinkiba sun nemi soyayyar sa sau babu adadi amma basa samu koda fuskar dazasuyi magana dashi , to tambayata anan itace ya akai kika samu wannan nasarar kuma menene abinda kike takama dashi har Allah yabaki wannan damar,

Sai kuma ta kara nisawa tana kallon idon Maryam tace, " Allah yasa bazakiji zafin wannan tambayar ba Yar uwata amsa nake bukata dan kullum da tunanin hakan nake kwana nake tashi gashi ke dai nasan bakyabin boka bakyabin malam,

Maryam tunda Islam tafara magana take kallon ta tana murmushi har ta ida sannan tace

" Azkhar ne sirrin sai kuma tsoron Allah danasa acikin zuciya ta koda na riski mummunar shawara a al,amarina bana yarda da ita inayin amfani da abubuwan da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yazo mana dashi


Anan nakeso nadan ja hankalin mu mata gameda Azkhar 👂🏻👈🏻

Ƴar uwa shin kinayin azkhar ɗin safe da maraice kuwa ❓, koko aiki dasan kwanciya bacci ko saurin kunna data suna hanaki yi ❓, da kinsan falalar yinsu da ko kina gudun ceton rai zaki dinga yinsu in kuma kinsan falalar yinsu meyasa kike sanya ko mantawa dasu❓, Azkhar suna haskaka rayuwa suna sauya mummunan abu zuwa kyakkyawa , kariya ce daga sharrin kowane abu yana kawo arziki dajin daɗin rayuwa, yana gyara zuciya yana kusantar da mutum ga Ubangiji, yana kai mutum zuwa aljanna, shin mai zaisaki yin sanya dasu bayan gasunan dayawa masu sauƙin karantawa sai ɗinbin lada da falala , dan Allah murinka yin Azkhar kar muyi sanya dasu dan neman kusanci da kariya awajen Ubangiji, duk abinda mukeyi mudinga daurewa munayi koda acikin kitchen ne ko, a tafe ko a zaune, Allah yabamu iko yasa mu gyara Ameen


Kallon ta Islam tayi tana mamakin amsar data bata a takaice tayi tinani tabbas wani malamin su yataɓa faɗa musu falalar Azkhar kuma har farin jini yake sawa shiyasa Raihan duk ya gigice akanta bama ya tinanin saɓa mata sai abinda tace, kuma tabbas kowa yasan Maryam yasan bata wasa da ibada addu,oi bata sanya dasu dolane kuwa abuga da ita abarta

Muryar Maryam ce ta katsa mata tunani taji tace mata, " kinyi shiru Islam,

" Babu komai Maryam nagode da tinatar wa kuma nima insha Allah zan dage anjima ma zan yiwa yaya Raihan magana yasiyomin littafin Azkhar,

" La basaiya siyo miki ba inadasu bari nabaki, dan danan Maryam tamike tanajin daɗin yadda suke zama da Islam yanzu komai yayi kyau

Wata jaka Maryam ta ɗakko jakar da ɗan girmanta tana buɗewa tafara zaro littattafan addu, oi kala kala hadisan Manzon Allah ( s a w ) shi kanshi Azkhar ɗinma kala biyar ne da ita aciki dabawa Islam ɗaya da litattafan addu'a guda uku

Islam mamaki ya isheta tace, " ko sati bakiyi da dawowa ba ya akai kika samu litattafan nan haka,

" Abinda Raihan yasan inaso ne wlh dayaga banida su kuma shima nasa sun ɓata shine yasiyomin su,

Gaskiya kam hakan yayi kyau nima yanzu zan dage da addu'a Allah ya yafemin zunubai na, Maryam tace Ameen suka cigaba da hirar su har aka kira sallar magriba Islam tayi alwala a ɗakin Maryam tayi sallah itama Maryam ɗin wanka tayi ta cire najasar cikinta duk da bata tsarkaka ba amma idan taji kiran sallah tanayin wanka ta yi alwala ta ɗau charbi tayi ta addu,o,in ta

Bayan sun kammala gaba ɗaya suka sauka kasan bene Islam tayi kitchen zata girka musu abincin dare Maryam ma ta bita dukda tayi tayi tazauna amma taki tare sukayi komai sannan kowa ta wuce shashin ta bayan sun jere kayan abincin a dinning table

Maryam ruwa ta kara watsawa ta kimtsa cikin wata doguwar riga mai laushi kamar buba take amma shara shara ce komai na jikin mutum ana gani sai wata dake ciki ita kuma roba robace iya gwiwa mai siririn hannu turaruka ta shafa ajikinta masu kamshi na Arab sannan taɗan shafa hoda sama sama tasa man lebe kadan ta gyara dogon gashin kanta tasake shi ya kwanta a kafaɗunta shima sai kamshi yake zubawa

Kusa da ɗan jaririn ta koma ta sake mishi kaya ta fesa masa turaran jarirai ta zauna tana kallon baiwar kyau da Allah ya bawa yaron kamar shi ɗaya da Raihan gashin kansama irin nasane kawai dogwayen yatsun ta ya ɗaukko da siranta karsu sosai ɗan yagaji da kyau komai nasa abin burgewa ne gashi kamar ka taɓashi jini ya fito

Raihan yana dawowa daga masallaci ya zauna a parlon kasa Islam tanajin shigowar sa gidan ta fito cikin riga da wando fakistan sababbin shigowa marum kala tana ta zuba kamshi

Tana gama sakkowa daga benan ta zaune a kusa dashi tana watsa masa kallon love ta kwantar da kai a kirjinsa tana masa sannu da zuwa ,

Ya mutsa fuska yayi dan yunwa yakeji ya shafi kanta batare dayace mata komai ba , Islam tace masa , " Food is ready my choice, kallon saman benan yayi yace, " housewife ɗinfa ?

Islam tasaki murmushi duk da takan ɗan sosu idan taji yace ina matar gidan amma bata wani nuna damuwa dan lallabawa take ta zauna lfy, " bari na kirawo maka ita ai yau tare mukai abincin,

Kamin ta tashi ma Maryam ta fara sakkowa daga benan tundaga nesa Raihan yake kallon ta ji yake tamkar ya haɗiyeta Allah shi kaɗai yasan irin son da yake mata, har ta karasa ya kasa hakuri saida ya mike agaban Islam ya ɗauketa yana juyi da ita dukansu suna dariya sannan ya sauke ta yana duba irin haɗuwa datai dukda cewa bayau tasaba kwalliya ba amma kullum da kalar kyan da take masa mu samman yanzu data haihu takara kiba ga hasken jin daɗi da tayi fatar ta tayi luwai luwai abin sha,awa Allah yaga zuciyar sa idan yafita har sauri yake yazo ya zauna da ita

Cikin fara,a yace, " kingan kiko wannan fa tsokanoni kike kuma nasan baza, Aban ba, yakarashe maganar yana kaiwa bakinta kiss ya matseta ajikinshi sosai yana shakar daddaɗan kamshin ta sai lumshe ido yake kamar maijin bacci

Maryam ta kalli Islam dake gurin tasan babu daɗi agaban ta suna haka da ɗan hanzari ta zame jikinta tana murmushi gashi yaki sakar mata hannu haka dai tamai dabara tace suwuce suci abinci

Agurin cin abincin ma amanne suke yanata bata abaki tana masa shagwaɓa, wannan kuwa ba bako bane awajen Islam dan tunkan ta auri Raihan tanajin labarin yadda suke zuba soyayyah abinsu shiyasama koda taga wani abin baya mata bazata sai dai ɗan zafi dayake mata arai dan ita sam Raihan baya mata Abinda yakewa Maryam tsakanin shi da ita sai dai wajen sex anan ne idan ta lodi magun guna yaji daɗi zai ta haɗa mata Words of love ,


Bayan kwana biyu komai yana tafiya dai dai gobe suna dakuma ɗaurin Auren papy gida cike yake da baki musamman gidan mai jego mutane sunata hidima sai hira ƴan uwa da abokan arziki

Yasmin na hanga agadon Maryam tana ta bata labarin fatin da akai na papy da amaryar sa tana kuma nuna mata hotuna da videos Maryam kuwa akasan zuciyar ta daɗi takeji kamar ya kasheta afili kuma mamakin Yasmin take yadda duk tabi tazaku da auren nan

" Anty Maryam kinga yadda amaryar papy takeko wlh kyakkyawa ce ga ilimi ga kuma aiki da iliminta ta iya zama da mutane kuma kinsan wani abin mamaki daya faru awajen ?

Aa Yasmin sai kin faɗa, " mc ne yafito da amarya yace zaiga son da ƴaƴan ango suke mata kinsan kuwa yaya Raihan da yaya Yasir atake suka rubuta mata chak na 30 millions dan danan yan wajen biki suka haukace kowa yahau shewa duk irin mahaukatan kuɗin da aka kashe sun bani mamaki,

Maryam batai wani al,ajabi ba dan tasan sun mallaki kuɗin da sukafi karfin yin wannan kyautar, cikin raha tace, " chab gaskiya anyi bani bari Islam da Amal su dawa nasha labari

Dayake Maryam bataje wajen partyn ba Raihan da Islam ne sukaje sukasa kaya kala ɗaya sunyi kyau sosai Maryam ita tayi musu rakiya ma har bakin mota itama irin kayansu tasa saida sukasha hotuna suka tafi

Anty laulam ce ta shigo dakin dayake yanzu tana yawan zuwa sunkulle kamar da suna mu,a malar su abin gwanin sha,awa

Saida ta karaso ta zauna tana dariya tace matar sadik an zauna anata

Please Login or Register in order to submit comment