Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duniya tsakanin miji da mata


Raihan yana shiga ɗakinsa ya kwanta yana tunanin wai shimai ruwansama da duk abinda yasir zaiyiwa maryam menene nasa aciki dagirmansa zai dinga jawa kansa raini ,rasa mai bashi amsane yasashi jan tsaki yaɗau wayarsa yana latsawa


A bangaran maryam kuwa gaba ɗaya takasa sukuni azaba ta isheta ga gajiyar aiki gamatsar datasha awajen yasir wasu hawayene suka shiga sakkomata afili tace "Allah yajikanku iyayena inda kuna raye babu abinda zai kawoni DAULATUL ARAB nafuskanci tangarɗa dayawa a rayuwata amma duk da haka bazan taba gazawaba harsaina cimma burina indai ina numfashi Allah ka tsareni daga sharrin waɗanan mutanan kada su illatamin rayuwata


★★★

FERAS Awane dalili zaka je ka kwashe wannan kuɗin na kane nafa fara gajiya da wannan iskancin naka wai mai kake so a rayuwarka ne agida baka shuka alkairiba a wajema haka

" Ammee nifa nafara gajiya da titsiyan nan haba babana yamutu yabarmin tarin dukiyar da harjikokin mu bazasu iya cinyeshiba to kifaɗamin idan banje nakasheba mai zamuyi dasu ?

" lallai feras rashin hankalin naka yakai babu abinda zance maka sai Allah ya shiryeka ya ganar dakai kuma kuɗi dakake cewa babanka ya mutu yabar maka gado ai ba kaikaɗai bane ga shaikh Ali ga Aisha da Gazzal sukuma nasu hakkinfa kasandai Allah bazai kyalekaba


FERAS yanajin haka baikara cewa Ammee komaiba yafice daga parlorn harabar gidan nasu yanufa yazauna awani kayataccen wurin hutawa

Dama da karamar mp yake tafe bajira ya kunna kiɗansa kamar yadda yasaba amma dayake gidan babbane sam ba,ajin kiɗan awaje wayarsa ce tafara ruru yana ganin mai kiran yawashe baki ya ɗaga yana faɗin

" wainak turolli tunjiya najika mukful ?

"Kaidai bari FERAS jiya nakusa gwangwajewa da babban muradina amma kash bankaida ciki burinaba Raihan yayimin katsa landan

" gaskiya yasir kai mish koyins ne wani lokacin nafaɗa maka kadaina wannan banzar harkar matan kaki

" hmm feras bazaka taba ganewa bane aduk lokacin daka taba snx zaka tabbatar da abinda nake faɗamaka

" yasir kainedai bazaka ganeba toni wallahi da,a bani mace kwara abani ɗan sigari guda ɗaya kasandai shine abu mafi araha amma kai duk kaje ka lalata kanka abanza bakada aiki saiyawan bin mata yau kana wajan ƴar turkiya gobe kana wajan ƴar isra,ila

" hhh jibi kuma ina wajan ƴar NIGERIA ba

"Hakadai zaka kare kaga ni bama wannan ba anjima akwai fitafa na ɗebo kuɗinnan zamuje ayi damu dolane ƴau mununa arzikin da muke dashi nasa aimana baboom na musamman

" kai feras amma naji daɗin wannan albishir ɗin kace yauzamu bada wuta

Nan suka cigaba da hirarsu ta kwararrun tantirai


★★★


Numfasawa tsoho baban fahda yayi yace " kana jina yaro duk duniya babu uban dazaiso ƴarsa ta lalace nima danbabu yadda zanyi da itane tariga tafi karfina kumama daɗin daɗawar lalacewarta sanadin wasu kawayenta ne ƴan sudan duk susuka firgitata

"Gaskiya baba natayaka jimami Allah ya yafe mana gaba ɗaya dan dukanmu munada laifi awajan Allah wannan uzurin naka baikai kaje ka nemoya ƴarka wanda zai biya mata bukata ba saboda haka ni babu abinda zance saidai Allah ya sauwake

" Ameen yaro ,tsoho yafaɗa suka wuce abunsu


★★★

Gaba ɗaya Raihan yakasa rintsawa daya rufe ido tunanin yanayin dayaga maryam da yasir yake

Tashi yayi daga kwanciyar dayake yazauna saman gadonsa ya haɗa tagumi gaba ɗaya yarasa menene ma anar wannan tunanin menene yake shirin faruwa dashi haka shidai yasan a rayuwarsa baitaba san wata ƴa maceba bare kuma ya kasa bacci saboda ita

Rasa abinyi ne yasashi mikewa yafice daga kayataccen ɗakin nasa

Yana fita harabar gidan yaga wata bakuwar mota ta shigo musu hargida kamar karyaje amma kuma sai yakasa hakuri dan shi baisan wani ɗan gidan mai irin wannan motarba

Yana zuwa ya kwankwasa glass ɗin motar, ga mamakinsa yaga tabuɗe babu kojin kunya





✍🏻
ZAINAB AHMED YUSUF HAƊAJA
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲




AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA



STORY AND WRITING ZAINAB AHMED YUSUF HAƊAJA
MRS
Abdussalam


WhatsApp number
+218917586263




PAGE 7️⃣⏮️8️⃣

Bismillah


..... Shahida kece wato karuwancin naki yakai kidinga kawomana ƴan,iska gidako


Wacce aka kira da shahida tai saurin zame bakinta daga na saurayinta cikin razana tafara inda inda tana cewa

" ka ka kayi hakuri yaya Raihan ɗan makarantarmu ne yazo mu gaisa

Cikin zafin nama Raihan ya wanka mata mari kankace kwabo yazagaya mazaunin drever yajawo saurayin nata yana duka

Ihu shahida take hakanne ya ankarar da mutanan gidan suka firfito matansu da mazansu guri yaciki makil

Papy mahaifin Raihan yayi saurin jenye Raihan cikin ruwan masifa yake cewa " wai Raihan mekakeso kazamane agidannan gaba ɗaya zafin zuciya yarikita maka kwakwalwa abu kaɗan saika rufe mutum da duka mai sukamaka


Raihan kallo yabi yan wajan dashi kafin yacewa kannan ubansa da mahaifinsa yanason magana dasu ta sirri ,Nan da nan aka kori kowa dayake wajan shahida harzata tafi Raihan yace badda ita

Bayan sun zazzaunane Raihan yafara bayani cikin nutsuwa da girmamawa

" papy sanin kowane acikin ku munada yawa a wannan hause ɗin kuma duk yaran gidannan mazan su da matansu mune manyansu daga AISHA
Sai ni , abinda nakewa yaran gidannan samarinsu da ƴan,matansu sai adinga gani kamar nacika mugunta ina cutarsu ku iyayanmu ne kuna cen wajan neman kuɗinku bakusan mai yake faruwaba idan yarinya ɗaya taja mana abin kunya tamkar tajawa duk wani ɗan family dinmune

nafito daga cikin gida naga shahida a motar wannan ɗan iskan suna iskancinsu wannan shine dalilin dayasa na daketa shima saurayin na dakeshi

Baban shahida yanajin haka yarufeta da duka dasauri papyn Raihan ya rikeshi yana faɗin

" haba yazaka kama yarinya da duka katabbata hakan akayi nifa sam yanzu nadaina yarda da maganar Raihan muguntarsa tafi karfinsa haka ɗazu yakama YASIR da duka agabana tamkar Allah ya turoshi

Baban shahida yana jin haka yaɗago yana huci yace " haba yaya yazaka din ga fadin haka kafi kowa sanin duk ƴaƴan gidannan babu nutsatstsan yaro kamar Raihan koda sigari baya sha babu ruwansa daduk wannan kazantar rayuwar ,wannan yarinyar kowa ya shaida tazama karuwa yasir ma kuma kowa yasan halinsa agidannan maganar gaskiya yaya ni naji daɗin hukuncin da Raihan ya yanke ina daɗa baka umarni Raihan acikin yaran gidannan duk wanda yayi badaidai ba kahukun tashi nina saka

Gaba ɗaya sauran kannan uban sukace gaskiya ne wannan muma mun goyi da bayan Raihan

Dolece tasa baban Raihan yin shiru

Nansuka juya kan saurayin shahida sukace yaɗau motarsa yabar musu gida kuma karsu kara ganin shi

Shidai Raihan baice komai ba dan yayi kudiri duk wanda yayi badaidai ba saiya tsawatar masa saidai duk abinda zasuyi suyi

Kanin papyn sane yadafashi yace " yarona dama inaso muyi muhimmiyar magana dakai da sauran iyayen ka kuma gashi anyi sa,a yaukowa yananan duk mun haɗun

Dai daita nutsuwarsa raihan yayi dan yasan kowace magana ce wannan tanada matukar mahimman ci ,cikin ladabi yace "ina jinka Abba

" Raihan nasan kai bayaro bane tunda Alalace zakai shekara 40 yakamata ka alkinta rayuwarka kazama cikekken namiji kaima duk sa anninka magidan tane da auran su amma narasa mai yasa bakason ko zancen aure Raihan,mu iyayenkane wannan halin da kakeciki ba karamin bakanta mana rai yakeba koba komai kayi aurennan dan gujewa daga faɗawa halaka

Cikin damuwa da tausayawa kanin mahaifin nasa yake wannan maganar

Raihan kuwa yanajin haka yasauke ajiyar zuciya dama yasan wannan ce maganar akoda yaushe basuda magana saita yayi aure , kakalo murmushi yayi a fuskar sa yace

" indai wannan ne karku damu insha Allah dana samu yarinyar data dace dani zanyi aure

Papyn sane ya katseshi da cewa " hakadai kullum kake cewa da anmaka maganar aure saikace baka samu wadda ta daceba saboda kana gani kanada kyau to abanza zaka tsufa duk wannan kyan dakake takama dashi yakare saidai ƴaƴan kannanka sudinga kiranka da kawu

Dariya kowa awajen yayi amma banda Raihan daya tafi duniyar tunani hakika shima yana san aure amma yarasa menene da lili duk da abukace yake abu ya faskara shikaɗai yasan azabtuwar dayake sperm yana nema yakaishi lahira amma dayake namijin gaskene baitaba nunawa wani damuwarsa ba sai likitansa , ƴan gidansu suna tunanin ko al,janace ta aureshi wasu kuma suna cewa yawan iskancin shi yake shiyasa aure bai dameshiba

" kayi shiru Raihan, maganar abba ta dawo dashi hayya cinsa yayi saurin cewa ," karka damu abba insha Allah khair zanyi ne

Bai bari sunkara cewa komaiba ya tashi yanufi cikin gida , yana zuwa ɗakinsa ya zube akan gado wasu zafafan hawayene suka shiga sakko masa a hankali yabude baki yana cewa ," papy bakasan halin danake ciki bane dakun tausayamin inabukatar taimako narasa mai yake faruwa acikin lamarina

Gani yayi kuka bazai masaba hakan yasashi tashi yanufi ɗaki yaɗaura alwala yayi sallar nafila haɗi da rokon Allah yakawo masa mufita cikin rayuwarsa




Gaba ɗayansu yan mata huɗun suna zazzaune safeeya ce tace " ni kuwa shahida mai yahaɗaki da zakin gidannan haryatara miki mutane ? ," himm lallaima safeeya kinriga kinsan halin ya Raihan kawai muna cikin mota nida saurayina yazo yafara mana tijara ni wallahi garama yayi aure yabar mana gida

Islam najin haka tayi wani murmushi tace " karku damu insha Allah yaya Raihan zai aureni zamu tafi mubar muku gidanku kuhuta

Dariya suka kwashe da ita amma banda Amal datake jin zuciyarta kamar ta tsage aduk lokacin da ƴar uwarta ta furta tanason Raihan,, safeeya tai saurin cewa " gaskiya islam kina bani mamaki kinsan fa irin tsanar da mamanki taiwa Raihan amma koda yaushe burinki kice kinason Raihan,

" hmm rabu da ita wawiya inbanda shashanci irinna islam ƴar karamar budurwa dake maizaisa ki dinga haɗa kanki da tsaho ɗan shekara 40
indama Raihan ɗin yasan kinayi da sauki amma idan kika kuskura yasan kina haɗa kansa da ke kashinki yagama bushewa wallahi kowa agidannan saiya tausaya miki,,, cewar shahida kenan

Itadai Amal batacemusu komaiba tafada duniyar tunani tabbas soyayyar da takewa ɗan uwannata ta gaskiya ce duk da tasan akwai rikice rikice kala kala nafarko ƴar,uwarta islam tanasan Raihan sonda haryakasa boyuwa acikin zuciyarta nabiyu mahaifiyar su ta tsani Raihan don abune da kowa yariga yasani agidan babban tashin hankalinta shine Raihan baisan tanayiba babu wanda yafahimci soyayyar datake wa Raihan kasancewar ta mai nutsuwa da zurfin ciki sam batada yawan surutu bare kafuskanci wani abun game da ita ,, nannauyar ajiyar zuciya Amal tasaki afili wadda tasa duka ƴan,matan suka kalleta ,, mazewa tayi tana cewa " wainikam duk aname zaku zauna kunata tattauna magana ɗaya haka gara muyi hirardazata fishshemu ,

Islam ce tace " gaskiya kam Amal dan nima banaso naji koda yaushe ana magana akan Raihan

Nan suka cigaba da hirarsu ta duniya cikin nishaɗi da kaunar junansu



★★★ wai meyake damunkane yasir meyasa kafiya damuwa akan yarinyar dama jinsumma bace ?

" hmm FERAS bazaka ganeba nikaɗai na hango hutun dazan samu ajikin yarinyar nan zatai daɗin dabaka tunani kaga idan zaka taimakamin wajan satota kafaɗamin idan kuma bazaka taimaka minba shikkenan

" wai na tambayeka yasir mai yasa kakeso nasa asato maka yarinyar ?

" dalilina shine inaso nasaceta saboda narama abinda Raihan yayi mini yanata wani rawar jiki akanta idan nasaceta sainaga yazaiyi nabiyukuma inaso nahuce haushin jikinta danakeji saina la,antata da SNX yanda bazata kara moruwaba

" gaskiya yasir bazan iya bada goyen bayan wannan barnarba ni wallahi yarinyar nan tausayi take bani dududu nawa take ayacce naganta bazata wuce shekara sha 18 ba kuma kasan dokar DAULATUL ARAB duk wanda yaci mutumcin karamar yarinya kasheshi ake


Cikin mamaki dajin kalaman FERAS,yasir yace masa " lallai FERAS yaushe kafara tausayi da harkake cemin tausayinta kakeji kuma dakake maganar wani idan anci zarafinta hukuma zatai hukunci ina taga mai tsaya mata yarinyar da batada kowa ko kasheta nayi babu wanda zai tuhumeni bare kuma da bawani izaya zan mata sosai ba tunda nima inasonta

Lokaci ɗaya bacin ran FERAS yanunku cikin hassala yace yasir ka kama hanya kai tafiyarka idan harkasan wannan maganarce zata kawoka wajena karka kara zuwa inda nake ,mitsiiiiiii yaja tsaki yahuce gida

Yasir kasa motsin kirki yayi yadda yaga FERAS yabirkice akan maganar maryam duk rashin imani na feras wai yau shiyake tausayawa yarinyar dama jinsun suba lallai akwai kura




👍🏻
Zee ƴar mutan libya
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲




AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA



STORY AND WRITING ZAINAB AHMED YUSUF HAƊAJA
MRS
Abdussalam



GARGAƊI
Wannan labari kirkiratane wallahi tallahi mace ko namiji duk wanda yayi karambanin juyamin labari ta wata sigar Allah ya isa kuma da yardar ubangiji saimunyi shari,a da mutum agaban Allah 👂🏻"daku nake ƴan gani ba kyalewa waɗanda basa ramun kansu sai wani yayi sushige 😎



________________________________


PAGE 9️⃣⏮️🔟



FERAS yarasa mai yasa yayiwa amininsa zazzagar kifin gongoni Akan yarinyar da tunda yake saubiyu ya taba ganinta ,tabbas bai kyautawa aminin nasaba amma dole yadaure yadinga fidda kansa daga wannan kazamar harka gaba ɗaya arayuwarsa ya tsani harkar mata da mai yinta

Yana cikin wannan tunanin yaji sallamar shaikh Ali ,bayabo ba fallasa yaɗaga kai yana tambayar sa lafiya ? ,zama shaikh Ali yayi yana faɗaɗa fara,arsa yace

" a gaskiya ɗan uwana naji daɗin yadda naga yau ka tsallake tarkon sheɗan wanda dawuya mutane su gane basuda saurin ruftawa

Shishar dayake zuka yacire daga bakinsa yace " kai nifa bangane mai kake nufiba wane sharri na tsallake ?

Gyara zama shaikh ali yayi yana cewa " ya ɗan uwana naji dukkan tayin da YASIR yazo maka dashi ada nayi tunanin zaka amsa amma ga mamakina sainaga Allah ya taimakeka ka haye daba karamin kuskure zaku aikataba wanda sanadinsa zai iya sawa ku tabe duniya da lahira

Tunda shaikh Allah yafara magana FERAS yazuba masa ido saida yakai aya tukunna feras ya cebki kwalarsa cikin zafin rai da hargagi haɗi da ɗaga murya yace

" rainin naka haryakai kazo kanamin labe da ranar Allah ko kunya bakaji Ali kafita daga idona ina ganin kimarka amatsayinka na limamin babban ma sallaci wallahi idan ba hakaba da sainaima rashin mutuncin dabaka tunani wawa dakiki kawai harzakazo kana cewa zan tabe kaine tababbe wanda babu abinda ka iya kullum kana hanyar masallaci (DIN UMMAK ZAKUMOK ) mitswww yaja tsaki ya sakeshi fuuuu yabar wajan tamkar wanda ake kaɗa masa gangi haka yake tsuma

Shikuwa shaikh ali baidamuba idan da sabo yasaba da halin yayan nasa ,hannu yaɗaga sama yana rokon Allah ya kara shirya yayan nasa



★★★
A tsaye take akanta tasata tsugunno hadda ɗaga hannaye sama

Ita kuwa maryam babu abinda take sai zubda hawaye gaciwon da mararta take mata amma ina bayadda zatai dole ta karbi hukuncin yasmin wanda inda sabo tasaba azabtar da ita


Tundaga nesa yake cije baki Allah Allah yake yakaraso wajansu dan hannunsa har kaikayi yake ,yasmin tana hangoshi tayi tsuru tsuru tamkar munafuka kuma tasan idan ta gudu wata masifarce hakan yasata juyowa kan maryam dake durkushe tace mata ta tashi tsaye

Yana zuwa bai ko kalli yasmin ba ya harɗe hannuwansa a faffaɗan kirjinsa yace " maryam mai yake faruwa anan ? ," tasani wankine banyiba saboda banida lafiya shine take hukuntani , takarasa maganar tana fashewa da kuka mara sauti

A fusace yajuya ganinsa ga yasmin cikin harshen su na larabci yace " dama maryam baiwace da harkike da zarrar hukuntata akan batai miki gassala ba ?

Cikin in ina tace " ya Raihan dan Allah kayi hakuri nadaina daga yau , shiru yayi yana ɗaga hannu alamar babu matsala sannan yace " shikkenan matsa cen kema ki karbi hukuncina ki durkusa ki ɗaga hannayenki sama karki sauke harsaina baki izini idan bahaka ba kuma kinsan sauran

Bashiri yasmin tabi umarni dan tasan halin ɗan uwanta , yaran dake wasan ball a harabar gidan suna ganin anty yasmin ta tsugunna alamar karbar horo sukai sum sum suka shige gida dan kar tashafesu sun san duk duniya babu wanda yasmin take tsoro sai Raihan

Zama yayi a ɗaya daga cikin kujerun da aka tanada nawajen shakatawar gidan ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya yana murmushi cikin tattausar muryarsa mai cike da tausayawa yacewa maryam " daga yau karki karaiwa yasmin kowane aiki ninasaki umarninane kinji , kai a sunkuye ta amsamai da to tanata faman zufa ita kaɗai ganin yadda Raihan ya kura mata ido tamkar maisan gano wani abu

" lafiya mai yake damunki ne naga duk kinwani rikice ? , baki na rawa tace " ba ba ba babu komai , nuni kawai yayi mata da hannu alamar ta shiga gida

Tana shiga kai tsaye part ɗin kanin mai gidan tanufa wajan Amal dama tasan inda zata sameta kai tsaye ta faɗa ɗakin Amal tana huci dafe da mararta

Amal dake kwance saman gadonta tana tunani taga faɗowar maryam tamkar anjefota tace " aa maryam lafiya ? ,amsa tabata da marartace take ciwo dan danan Amal ta ɗakko magani da ruwa mai sanyi tabawa maryam tasha sannan ta ɗakko mata audukar mata mai tarin yawa ta bata sannan tace tazo ta kwanta tahuta maganin ya tsirga

Maryam tana jin daɗin yadda Amal take sakar mata fuska tana kula da ita sosai dukda ta girme mata zatai shekara 22 amma hakan baisa ta kyamacetaba ta ɗauketa tamkar kawa



Ta saman windo shahida ta hangi duk abinda yake faruwa tundaga sanda yasmin ta hukunta maryam ƴar aiki har sanda ya Raihan yazo yake hukuntata hakanne yasa tai saurin kiran safeeya da islam suzo su gani safeeya tana gani taja tsaki tace sunfi kusa ai kanwarsa ce kuma ma Allah shikara dama yasmin haushi take bani da girman ta ta tsaya takirawa ƴar aiki aigara daya mata haka a gaban kannanta koba komai taji kunya

Dariya islam tayi tace " yauwa gadama ta tasamu bari na cenza kaya yanzu na haɗo coffee nakaiwa ya Raihan ila nasamu dama muyi hira yau dashi , kawayen nata suna jin haka suka haɗa baki cikin shewa suna cewa wannan shawara ce mai kyau taje

Haka kuwa akai islam ta shirya cikin riga da wando masu jan hankali abunka da balarabiya saitai kyau tamkar wata hurul aini

Rike take da wani haɗaɗɗen kofin gless mai ƴaƴa tunda ta doso wajen Raihan gabanta yake faɗuwa duk da tasan ba kallon ta yakeba hankalin sa yana kan littafin gabansa gefe kuma yasmin ce durkishe tana ta faman matsar kwalla

Da sallama a bakinta ta karasa , amsamata yayi batare daya ɗago kaiba , cikin ladabi da kwantar da murya islam ta gaisheshi ya amsa shima bai ɗago kai ya kalletaba bare yasan ya shigarta take kuma mai take tafe dashi duk da kanshin turarenta ya buɗe wajan

Cikin sanyin jiki tace " ya Raihan ga coffee na kawo maka , sai a lokacin ya ɗaga kai ya kalleta sama da kasa sannan yace " nace miki ina bukatar ki kawominne ?, aa ya Raihan,

" ok shikkenan inasu shahida?, suna cikin gida ," to kirawomin su yanzu kuzo ku share ko ina na gidannan

To kawai islam tabashi amsa jiki na rawa ta wuce wajan ƴan matan da duk suna kallo ta windo amma basujin mai ake cewa , tana faɗa musu yadda akai shahida tace " haba islam yazaki mana haka gashi kinsa yasamu shara da girmanmu muba yaraba , safeeya ce ta amshe da cewa " um nidai babu ruwana da sababin yaya Raihan wallahi gara tun wuri kuzo muje muyi sharan nan idan ba hakaba kowa yasan ragowar , gaskiya to aje akira Amal itama dole ayi da ita

Suna zuwa ɗakin Amal suka taddata ita da maryam sunata kwasar hira abinsu basu wani damu da ganin maryam a ɗakinba dan dama sun san mutuniyar Amal ce ,kai tsaye suka isar mata da sakon Raihan azuciyar Amal taji matukar daɗin jin wannan sakon dan koba komai zataga masoyinta rabon data sashi a ido ƴau kwana uku kenan

Bayabo ba fallasa a fuskar Amal ta tashi taɗau wata doguwar riga mai ɗan hijab tasa taɗauki tsintsiya suka wuce

Gaba ɗayansu durkusawa sukayi suna kwasar gaisuwa ba wata wata suka fara share sharen wajen


Wasu ƴan samarine guda biyu naga sun shigo gidan da alama ƴan gidanne dan naga yana yinsu ɗaya, suna karasowa da fara,arsu suka fara kwasar gaisuwa a wajen yayan nasu ,bayan sun gaisa Raihan yace suɗauki coffee ɗinda islam ta kawo masa su shanye ,hakan bakaramin sosaran islam yayiba amma saita haɗiye dan tasan dama bazaisha ba

" kai Ammar kaga yadda ya Raihan yake hora ƴan matan gidannan ko ?," eh nagani shiyasa wallahi nake matukar farin ciki da yadda ya Raihan yake ladabtar da kowa agidannan kai harfa yaya YASIR bai kyaleba ," ai yayi min daidai dama shine maganin yara da iyayensu gashi mu Allah bai ɗoramu a sahun aikin yauba dan har kyautar coffee yayi mana

Nan ƴan samarin suka kwashe da dariya

Saida ƴan shara suka gama tukunna Raihan ya bawa yasmin izinin tafiya daker take ɗaga kafa dan izayar dataji kowace gaba tana mata , tana shiga gida tafaɗa jikin Ame hauwa tana kuka mara sauti cikin tsananin azaba , arikice Ame hauwa take tambayar ƴar tata lafiya , cikin muryar kuka tace " ya Raihan ne yasani tsugunno da mike hannayena harna tsawon awanni kawai saboda maryam ƴar,aiki ," kan ubancen lallaima raihan ya shahara to wallahi bazai yuba ƴar tawa guda ɗaya tamkar tsoka ɗaya amiya zai azabtar akan waccen yarinyar dabama jinsummuba






✍🏻
ZAINAB AHMED YUSUF HAƊAJA
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲




AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA



STORY AND WRITING ZAINAB AHMED YUSUF HAƊAJA
MRS
Abdussalam




PAGE 1️⃣1️⃣⏮️1️⃣2️⃣

Bismillah


Tashi Ame hauwa tayi a fusace zataje inda Raihan yake , da sauri yasmin tariko hannun uwar tata tana zubda hawaye tace ," dan Allah Ame hauwa karkije wallahi idan kikamasa faɗa nashiga uku a gidannan azaba zai kuma ganamin datafi waccen

" habawa aikuwa daya riski bacinran dabaya tunani dama ance idan mutum yadaɗe baiyi aure ba mahaukaci yake komawa todai gashi magana ta tabbata Raihan yakoma majnun tuburan yau ya daki wannan gobe ya azabtar da wance dan haka kibarni inje inkarta masa rashin mutunci yacce ko kallon banza bazai kuma yimiki bah

Ame hauwa nagama fadin haka ta fusgi hannun ta tafice wajen Raihan


Babban wajen hutawar gidan ta nufa wanda tasan indai yamma tayi anan zakaga Raihan yana karatun littafi ko kuma mujalla ,gamamakin ta tana isa taga bayanan cikin hassala ta shiga dube duben gidan amma ko ina taduba ba Raihan babu dalilinsa watakila yafita tafaɗa azuciyarta

Ame hauwa bata koma part ɗintaba sai tai part ɗinsu ommu Amal dayake kawartace duk acikin faccalolinta dake gidan babu wadda sukafi shakuwa da ita kamar ommu Amal

Tana shiga gidan ta tadda faccalar tata da ƴaƴan ta a babban parlor suna hira , gaba ɗaya yaran suna ganin Ame hauwa suka fara gaida ita ciki kuwa badda islam da tashima tai tabar wajen dan batasan mu,amular Ammeen ta da Ame hauwa

Ommu Amal tana ganin aminiyar tata tarungume ta cikin kulawa take mata sannu da zuwa , bayan sun gaisa ommu Amal tace su shiga daga ciki saboda yara dan tanaso suyi maganar sirri da ita

Haka kuwa akai suka tashi suka koma cen kuryar bedroom suka haye gado , Ame hauwa ce tafara magana da matukar damuwa a fuskarta take cewa ,

" ommu Amal ina cikin tashin hankali sama da shekara goma sha uku nake faman neman hanyar dazanga na tarwatsa rayuwar ƴaƴan kishiyata Raihan da YASIR amma abun yaki yuwuwa shidai yasir nayi nasara yagama lalacewa amma haryanzu uban bai tsaneshiba matukar kwaunar ɗansa yake shikuma Raihan haryanzu nakasa samun nasara akansa duk wani kulla kulla danake kema kina tayani babu riba babban bakin cikina ma koƴar sigarin nan da samari sukesha tanuna sunfara lalacewa Raihan baitaba shaba nida nakeso yazama mashayi kuma kasurgumin barawo sannan yazama manemin mata daduk wata halaiya dazata sa mutum a halaka amma abu yakici yaki cinyewa

Ajiyar zuciya ommu Amal tasaki tana cewa

" nima kaina wannan abu yana matukar ɗagamin hankali kidubafa kigani bakin tsafi akai akan yarannan Raihan amma shiru kikeji ammafa kar wannan yaɗaga miki hankali Ame hauwa munada nasara kwaya ɗaya akan Raihan shine takinyin aure gashi da mukai masa bakin tsafi haryau aure ya gagareshi

" hmm ommu Amal kenan to yanzu menene ribar kinyin auran nasa munyi hakanefa saboda ya balage yadinga bin matan banza saigashi babu ko ɗaya

Please Login or Register in order to submit comment