Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya auri Islam ba chab babbar magana to ta ina zaifara yimata bayani

" Am baki fahimce niba ai itaɗin yanzu kanwarki ce kuma yar uwarkice,ya karashe maganar yana kallon idonta yaga tayi murmushi tace , " eh mana ai kanwatace tunda yayanta nake aure amma banaso kana shiga hurumin yarannan karsu rainaka,

" Baki ganeba har yanzu ina nufin islam tana gidannan itaɗin matata ce na aureta,

Kamar daga sama maryam taji wannan maganar hakan yasa turaren da yake hannun ta yafaɗi kasa jikake tasss yafashe tuni hawaye suka fara sauka a idonta cikin muryar kuka tace, " me kunnena suke shirin jiyemin Raihan ka auri Islam fa kake cewa,

" Kwarai maryam nasan hakan bazai miki daɗi ba amma ke kinsa bayin kaina bane bazan tabai miki kishiya dasan rainaba dan kinsan babu wata ƴa mace da take burgeni idan bakeba ,

Shiru kawai maryam tayi masa tana kwashe kwalbar turaren tana jinsa yana mata bayanin yadda akai auren tasan gaskiya ya faɗa dan dama su Ame hauwa sunce mata zasusa Raihan ya auri Islam

" Please maryam naji kinyi shiru Allah yasa karkiyi fishi dani akan hakan kinsan ba laifina bane kuma da ace biki tafi kinbarni ba da tuni hakan bata faruba,

," Bakomai yayana Allah yasa gaskiya ta bayyana amma ancutar dani kuma anzalince ni babu abinda zance da dangin nan naka saidai Allah yayi mana saka mako

Busar da iska yayi daga bakinsa sannan yakaraso kusa da ita yakama hannunta yana cewa, " Please kiyi hakuri kinga yanzu mu iyayene baikamata kidinga irin wannan magan ganun akan danginaba yanzu idan yaronnan ya girma yaji kina faɗin haka akansu ai bazai daukesu da kimaba Please my wife Rayuwa mai kyau nakeso mugina da iyalina kuma dole saida hadin kanki ki amince ki manta da wani batunsu ki rikesu tsakani da Allah kinga Islam papy ne yabani aurenta badama nasaki wallahi idan nasaketa tsinemin zaiyi yace na lalata musu zumunci amma idan har kinasan hakan saina saketa na daukeki da yaronmu mubar musu kasar gaba daya amma kisani zanyi rayuwane tamkar mara galihu kuma mara asali Please banasan haka ta kasance inasan zama cikin dangina,

Maryam jitayi gaba ɗaya jikinta yayi sanyi badan tsohuwa tayi mata magana akan karta tona zancen nan yanzu ba tabbas yau zata war warewa mijinta komai, " shikkenan my husband karka damu insha Allah zan zauna da Islam lfy amatsayin abokiyar zama kuma zan zauna da danginka lfy amma akwai wata muhimmiyar magana dayakama ta kasani kuma zaka sani idan lokaci yayi, " wacce maganace wannan, " karka damu akwai lokaci, " ko to taso muje nabaki abinci yana dining, " ehh baby ni bazan iya fitaba kohar kamanta mejegoce ni, " ayya sorry bari nakawo miki amma kisa kaya tukun,

Yana fita wasu zafafan hawaye suka sakkowa maryam ta share cike da takaici ashe Raihan zai iyayi mata kishiya koda yake balaifinsa bane amma gaskiya yakamata ta rama abinda sukai mata, wani tunani ne yazo mata ƙwaƙwalwa hakan yasata tayi murmushin takaici a fili tace, " dayar Nigeria kuke magana zasukan wacece Maryam dole narama abinda kukaimin ta hanyar cusamuku bakin ciki da tsoro kafin natona muku asiri

Cikin sif dinta ta duba inda take ajiye kaya abin mamaki babu komai nata, Raihan ne yashigo ɗauke da faranti yajero abinci ya ganta tsaye ta rike kugu , " yadai Maryam lfy, " wai yayah ina kayanane,

" A'a bakin kwashesu dazaki tafiba ai bakibar komaiba, " what ni na kwashe kayan nawa, " aa to wazai ɗauka??, Maryam tanajin haka takara fusata fuuu ta fice daga dakin tanufi ɗakin Islam Raihan yabi bayanta

Tana zuwa ta banka ƙofar saita tadda ɗakin abude ta cusa kai cikin hassala ta hangi Islam a tsaye ta shaki wuyanta sosai tana cewa, " kifaɗa min ubanme yasa kukaimin haka wato bayan kun nemi kasheni har sharri kuka bini dashi to bari ni nafara kasheki kafin ku hallakani tsinanniya azzaluma aiga mijin nan saikiji daɗin zama dashi mugani, Islam harzatayi magana taga shigowar Raihan cikin sauri tafara tari tana ihun wuyanta dasauri Raihan ya karaso ya jenye hannun Maryam duk da tanata fusge fusgen kwacewa yaki sakinta ita kuma Islam sai kuka take,

" Raihan ka cikani nakashe tsinanniyar yarinyar nan na huta akanme wato dama sun shiryamin hakanne dan ta aureka,

Raihan cikin tsawa yace, " kiyi shiru mana wai yakikeso nayine mesukai miki kiyayyafa ba hauka bace meyasa bakyasan nazauna lfy ne

, " Maganar gaskiya Raihan banice bana san zaman lafiyar kaba barikaji abinda yafaru dani har kaneman karasa a wacen ranar muna video Call dakai Laulam tashigo mukai sallama dakai akan cewa muntafi gidan yaya babbah saranar ƴar ta,,,, Anan nemaryam takwashe labarin duk abinda yafaru tafaɗawa Raihan,

Maganar tamatukar tsorata Raihan dan danan idanunsa suka kaɗa sukai jajir cikin tashin hankali ya kalli Islam yana nunata yana naɗe hannun riga jikinsa har rawa yake kamar mai shirin dambe yace, " Islam ki faɗamin gaskiya akan wannan maganar idan bahaka ba wallahi zan iya kasheki a wannan daren gara kigayan yadda akai kihuta,

Islam jiki na rawa tafara matsawa baya dan danan kukan da take na karya ya koma na gaske tasoma cewa, " wa wa wallahi bansan wannan zancen ba karka yarda ka aikata aikin dana sani taya zamu kasheta kuma idan harni bana kaunarta to anty Laulam fa da Ame Hauwa ke kuma Maryam kiji tsoron Allah wai mai mukai mikine haka kike nemanmu da sharri wato har anty laulam ɗin ma da irin sakaiyar dazaki mata kenan,

Islam tana kaiwa nan a Maganar ta durkushe tana sakin wani marayan kuka maryam mamakine ya isheta ganin yadda jikin Raihan yayi sanyi hakan yasata fusata ta wuce ɗakin ta

Raihan bin bayan maryam yayi ya taddata tahada kai da bango tana kuka cikin tsananin damuwa yakarasa inda take yafara magana,

" Maryam inaso ki faɗamin gaskiya nakasa gane kan wannan lamari tayaya za,ai ƴan uwana suce zasu kasheki dama ita islam da Ame hauwa nasan ba sansu kike ba to ita kuma Laulam menene nata aciki meyasa kikeso kiyi musu sharri, saikuma ya numfasa cike da damuwa yakuma cewa,

" Kinga Maryam nine mijinki kuma nine gatanki uban ƴaƴan ki inaso kumanta daduk waɗan nan kana nan magan ganun wannan zancen da kike cewa sunyi yinkurin kasheki idan har kinsan karyane kibarshi idan bahakaba wallahi zakisani cikin matsala,

Sai a wannan lokacin maryam ta juyo tana kuka tace, " bazaka ganeba Raihan bazaka ganeba tayaya zan musu sharri mai sukamin inaso ka sani duk duniyar nan idan har baka gasgatani ba babu wanda zai yarda dani kuma katambayi su inna zasu faɗa maka sune wanda suka tsinceni saida nayi watanni kafin na farko,

" Gaskiya abinnan daban mamaki amma yanzu kisamu ki kwanta kinga bakyajin daɗi idan gari yawaye zamu karasa maganar, Nan Raihan yasamu yalalla bata har tayi bacci shikuma ya wuce parlor ya kwanta daya rintsa kadan maganar Maryam ce take masa yawo aka tabbas yakamata ya gasgatata dan bata taba masa karyaba to amma taya zai yarda su Ame hauwa zasu iya yin haka, da wannan tunanin yakwana har gari yawaye






★★★


Alhamdulillah dukkan nin wani buri na FERAS sai cika yake rayuwa mai tsafta suke gudanar wa da BASSUNA a gidan auren su soyayyah kuwa ba,a magana

Yanzu haka feras da Shaikh Ali sun zama manyan ƴan kasuwa gidan dasuke cikima ankara kawatashi , kannan feras kuwa anyi bikin aisha da yaya mu,aruf wato yayansu jawahir da BASSUNA gazzal kuma ansa mata rana dan har bikin ya kusa

BASSUNA na hanga zaune a parlorn Amme hannun ta dauke da jariri wanda bai huce ɗan wata huɗu ba tana masa wasa, Ammen ce ta idar da Sallah cikin fara,a tace, " wai mijinnan nawa ba cewa nayi ku karbo masa madara ba meyasa jawahir takemin wasa da miji haka bata bashi abinci,

Dariya bassuna tayi cike da zolaya tace, " wlh Abby ɗinne baya koshi koɗazu agabana gazzal ta dinga ɗura mishi madara, dariya suka kwashe da ita sai sukaji sallamar su feras sun shigo

Amsawa sukai cike da fara,a feras ba ko kunya yazo jikin matarshi yazauna yana cewa , " kai abbyna haka ka zaunamin a cinyar mata saika tumurmushe mana ƴan biyu,

" Allah ya shiryeka feras kamaidamin mijina tamkar kakan ka to nawa yaron yake dahar nauyinsa zai tumurmushe cikin yan biyu, Shaikh Ali yana dariya yace,

" Ammee kemafa kinsan halin mutumin kawai bazai iya kawaici ba soyake yanuna miki tsantsar san da yakewa kanwata da yanbiyun mu, " yes kwarai kuwa bro faɗa musu dai

Nan hira ta barke har Jawahir ta sakko akasha hira da ita a kitchen ɗin ammee sukai girkin dare sukaci cikin soda nunawa juna kulawa family sun hada kansu masha Allah







∆∆∆∆

Islam gari nawayewa tanufi gidan ame hauwa dama tun dare ta kirata a waya sun tsara yadda zasuyi


Da sallama Islam ta karaso ta tadda papy a falo da ame hauwa, tana zuwa ta faɗa jikin ame hauwa tana kuka tamkar wadda akaiwa mutuwa

Cikin tashin hankali papy da ame suke tambayar lfy dakyar ta buɗe baki tana cewa,

" Nashiga uku papy dan Allah kayiwa Yaya Raihan magana yasakeni bazan iya wannan zaman auren ba so suke su kasheni da raina wallahi papy Raihan bayasona daga zuwan matarshi jiya jiya bakaga irin sharrin data mana ba kuma ya yarda hakan yasashi yimin dukan kawo wuka kamar ya kasheni

Papy yanajin haka yafusata cikin bacin rai yace, " yau zankawo karshan Wannan iskancin dole Raihan ya karbi mummunan hukunci, papy yana gama faɗin haka yanufi hanyar fita a fusace cikin sauri ame hauwa tasha gabanshi tana cewa,

" Haba papyn yara ba,a yanke hukunci cikin fishi kazauna akira maka Raihan ɗin yafi kaje bamusan mezai faruba dan Allah kasanyaya zuciyar ka, da kyar ta rarrashi papy yadawo yazauna sannan ya ɗau wayarsa yakira Raihan ko amsa gaisuwar sa baiyiba yace yazo yanasan ganinsa

Bajimawa Raihan yashigo yana ganin Islam yaji gabansa ya faɗi bashakka kararsa takawo

Ame hauwa ce kawai ta iya amsa sallamar amma papy shiru yayi,

" Aduk cikin yarana bantaba tunanin kaine zakadinga kawomin matsalaba Raihan maiyasa kakeso karaba kan gidannan da girmanka da hankalin mun baka auren yarinya saboda baka maidani wata tsiyaba sai wulakan tata kake Kana jamin zagi,

Cikin nuna damuwa Raihan yace, " babu abinda zance maka papy sai kayi hakuri wlh duk abinda kaga yana faruwa halin islam ne meyasa Amal da aka ɗaura mata Aure da Yasin bata taba kawo kararsa ba kuma kowa yasan wanene yasir kuma nima alokacin dana auri Maryam bata taba kawo muku karataba saboda muna zaune lfy,

Ame hauwa ce tayi saurin cewa, " kai Raihan har yanzu baka gane matsalar kaba Wannan matar takace takeda gagarumar matsala batasan zama Damu, papy kuwa yanajin haka yace,

" Tunda hakane kawai Raihan kaje kasamar mata wani gidan awaje kasiya kasata inyaso saikadin ga zuwa ni bana bukatar ta acikin Wannan gidan ka kiramin ita nafaɗa mata da kaina,

" Dan Allah papy kayi hakuri kasan Maryam yarinyace kuma gashi tanada jego yanzu sai nake ganin kamar idan ka ce na chanza mata gida banmata adalci ba,

" Rufemin baki shashasha ke Yasmin zokije ki kirawomin Maryam tazo yanzu,

Harga Allah Raihan baiso aka matsa sai ankira Maryam ba yanaji yanagani yasmin ta tafi kiran



Yasmin tana shiga gidan taga Maryam da tsohuwa a zaune suna hira ta gaishesu bayan sun amsa tace, " maryam kizo inji papy yanzu, Maryam tanajin haka tace to tabawa tsohuwa jaririn ta tashi,

Suna shigowa parlon taga laulam taga yasir taga mijin anty laulam da baban islam da Raihan ga Islam ame hauwa kowa yataru

Gaishesu Maryam tayi Sannan tarakube a gefe Yasmin kuma ta wuce ɗakinta

Gyaran murya papy yayi yace, " Maryam abinda yasa muka tara mutane anan muka kiraki saboda mugano inda matsalar gidannan take kifaɗa min meyasa kikeson rabamin kan family,

Idon maryam ne ya cuccuko da kwallah cikin takaici dajin Abin da papy yace tafara magana da cewa,

" Papy banida kowa anan sai ku sai mijina alokacin da mukai aure dashi banida wani kudiri akan kowa na gidannan saina zaman lafiya kwanci tashi babu wuya har nafara gano akwai matsala wallahi bazan musu sharriba gasunan da ame hauwa da yayah babba da anty laulam da islam kasheni sukeson yi shine sukazo gida sukamin sharri waina kwashe kaya na gudu

Salaty gurin ya ɗauka mijin anty laulam ya nuna islam da yatsa yana huci yace, " ke ashe bakida mutumci agidan ubanwa suka nemi kasheki bamasan iskancin banza anan, abu Islam kuwa gyara zama yayi dayake shi mai hankaline kuma ummu Amal tana yawan ce masa bata yarda da guduwar matar Raihan ba akwai wata a kasa, hakanne yasashi cewa,

" Kinga yarinya ki nutsu kiyi mana bayanin abinda yafaru zamu bincika mu tabbatar da gaskiyar ki babu cuta babu tutar wa, Maryam tanajin Abin da babansu Islam yace yasata jin dan dama dama a zuciyar ta sannan ta kwashe labarin abinda yafaru tsaf ta faɗa musu

Maryam tana gama kaiwa karshen maganar ta anty laulam tasaka kuka cikin tashin hankali tace, " nashiga uku sharrin dazakimin kenan menayi miki kowa agidannan yasan na nuna miki kauna amma abinda zaki sakamin dashi kenan

Ame hauwa kuwa cewa tayi, " lallai nayarda yaro man kazane yanzu ke maryam ina kikataba ganin anyi haka kawai ni yanzu nagama yarda yarinyar nan sotake tarusa mana haɗin kan gida

Kowadai awajen yanata tofa albarkacin bakinshi na Allah wadai da Maryam, papy ne yace

, " Toke yarinya kinga duk kowa nan bamu yadda da abinda kikace ba saboda haka yanzu kibamu hujja,

" Papy inada shaida nafarko a tambayi mai gadi yaushe nazo gidannan na kwashe kayana nabiyu akwai tsofaffin da suka tsinceni suma shaidane,

Papy yana jin haka yakuma cewa, " maigadin dakansa yaba mu shaidar yaga kina kwashe kaya sannan kuma Wanda kikecewa sun tsunceki ai bazamu yadda da shaidar suba tunda tare kuke,

" Papy wallahi banida riba idan nayiwa yan gidannan sharri amma aduba maganata, shiru wajen yayi na yan lokuta kowa da abinda yake sakawa katsam Yasir yamike tsaye yafar magana

" Ninasan duk abinda yafaru kuma mu zamu kawo shaida dama wannan lokacin nake jira ranar da za,a kawo duk wani karshen zalunci a gidannan, kallon kallo su ame hauwa sukashigayi cikin tsoro

Sannan Yasir yawuce bdakin Yasmin bajimawa sai gasu tare yafar magana

, " Yasmin yauce ranar da gaskiya zatai halinta inaso kinunawa kowa anan Wannan Vidio,

Yasmin jikintane yafara tsima dan itama kanta wannan lokacin take jira cikin sauri tafara magana da cewa, " papy maganar Maryam tabbas gaskiyace

Raihan ne yamike tsaye cike da dimuwa da mamaki yacewa yasmin, " kina nufin gaskiya Maryam tafaɗa sunyi kokarin kasheta,

" Eh kwarai kuwa yaya Raihan tabbas dagaske ne sunyi kokarin kashe maka mata hatta aurenka da islam shirinsu ne kuma papy idan baka mantaba ame hauwace tabaka shawara kahaɗa auren islam da raihan to tayi hakane dan cimma munifa sannan ita take kunna duk wata wuta a tsakanin Islam da Raihan ta hanyar kitsawa islam mugayan abubuwa

Wallafi papy babban abinda zai daga muku hankali sai kun kalli wannan bidiyon anan zakuga yadda suke tattaunawa, Yasmin tana faɗin haka ta kunna bidiyon taje gaban makekiyar TV dake falon tasa USB a wayarda tajona dan danan video ya bayyana acikin tv aka fara kallo ame hauwa da anty laulam da islam ne suke tattauna yanda zasu bullowa Maryam harsuka yanke shawarar sukashe ta gefe kuma waya suke da yayyah babbah tana tsara musu abinda zasu aikata


Babban abin daya daɗa tadawa kowa hankali saida sukaji cewa ashe ame hauwace ta yiwa Yasir asiri tun yana karami ya lalace shikuma raihan ta hanashi aure haryafar manyan ta sannan itakuma Maryam tazo ta aureshi suka kasa samun galaba akansa shine dalilin dayasa suka shirya kasheta

Video yana karewa kowa yahau kallon kowa cike da mamaki Maryam kuwa kuka kawai take Raihan kam jiyayi shiyama tsani zaman gidan cikin bacin rai yace,

" Na ɗaukeki mahaifiya ko daidai da rana ɗaya bantaba nunawa bake kika haifeni ba meyasa kika zabi rusa mana rayuwa menene ribarki kin lalatamin rayuwar ɗan uwa kuma ahakan kina tare da mahaifinmu abun kunya ƴar ki ta cikinki itace taga rashin imanin naki yayi yawa ta tona miki asiri wallahi tirrr da wannan halin naki,

Abu sultan ya kalli matarshi cikin fishi yace, " laulam inaso kisani wallahi abu dayane zai hanani sakinki yanzu saboda yaranki ne ammaduk da haka zan sanar miki babu ni babu ke natsawan shekara biyu zaman ƴaƴan ki kawai zakiyi nikuma zan kara aure, Laulam tanajin haka tafashe da kuka tana dafa kafarsa tace,

" Dan Allah abu Sultan kayafemin wallahi sharrin shaidan ne dakuma ame hauwa data jani cikin wannan mummunar harkar,

Ame hauwa kuwa tarasa bakin magana sunkuyar da kai kawai tayi gumu sai ɗuga yake tata tagama karewa









Comments and share 🤝🤝🤝
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲








AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA








✍🏻 By zaynab Ahmed Yusuf





🪀 WhatsApp number +2180917586263





Page 9️⃣6️⃣

Bismillahir rahmanurrahim






Papy kam kasa magana yayi gaba ɗaya ƙwaƙwalwar sa ta birkice idonsa ya kaɗa yayi jajir shi jiyake inama yafarka yaga mafarki yake matar daya aminta da ita shekara da shekaru yabata yarda da amana ashe itace take rusa masa dukkan nin wani gini dazai gina nazaman lafiya

Raihan ma kana ganin yadda yasunkuyar dakai zakasan kuka yake shima kansa abin yayi masa bazata, yasir kuwa mikewa tsaye yayi yana bin dukkan su da kallo yace,

" nifa bazanyi wani mamaki da abinda suka aikata ba dama rayuwa tagaji haka san zuciyar sune yaja musu amma ni abunda yafi bani takaici Islam dasuke amfani da ita suna aikata duk wata ta,asarsu to bari kiji ingaya miki Islam zakiyi dana sanin wannan abu danke daga ganin wannan idon naki dama chan na futsara ne kuma babu alamar nadama a tattare dake,
Yasir yana gama faɗin haka yafice daga gidan, Maryam ma tashi tayi zata tafi papy yace mata, " dakata ƴata ninarasa dawacce kalma zanyi amfani wajen neman yafiyarki dan Allah Maryam kiyafemin narashin fahimtarki danayi wallahi banyi tsammanin haka abun yakeba harnadin ga zarginki,

" Wlh papy karkaji komai ninayafe maka dama ban kullaceka ba ubah nadaukeka har abada bazan sauya wannan matsayinba, Maryam tana gama faɗin haka tajuya zata fice taji anrike mata ƙafa tana juyowa taga anty Laulam ta dafa kafarta hannu bibbiyu tana kuka tace,

" Dan Allah kiyafemin kitaimaka kiyimin aikin gafara wallahi sharrin sheɗanne kuma nasan idan baki yafeminba bazan taba samun sukuni ba, abu Sultan ne yayi saurin cewa, " ke Maryam karki yafe musu wallahi kibari kowa yagirbi abinda ya shuka lokacin da suka aikata sun manta da Allah sai yanzu

Girgiza kai maryam tayi tana cewa, " karka damu abu Sultan Allah ma munai masa laifi ya yafemana dan haka nayafe miki Allah ya yafe mana gaba ɗaya, tana kaiwa nan tafice, papy ne ya busar da iska daga bakinsa yana cewa, yarinya ƴar aljanna,

Raihan ma mikewa yayi idon nan nasa sunyi jajir yace, " papy nima zan wuce sai anjima, " ok to idan anjima zan kiraka akwai zama dazamuyi, " to papy nagode,


Gurine yarage babu kowa sai papy da abu Amal da ame hauwa da Islam dama su anty Laulam sun tafi

Ba tsammani saijin duka kake abu Amal yarufe Islam da duka kota ina harda taka mata ruwan ciki, papy ne yarikeshi yana faɗa yace, " kayi haukane kake mata irin wannan dukan kasheta zakai,

" gara nakasheta na huta da irin wannan masifar data jawo min yarinya sa,ar kanwarki batajiba bata ganiba kina neman kasheta saboda Raihan to wallahi Islam ki saurara kiji yau zansa Raihan ya sakeki kuma baza kiyimin zawarci agidaba chan dangin uwarki zaki tafi tunda dama duk gaiyar muna fukance nayi nadamar haihuwar ki wallahi haka kikaga Amal ta tafi darayuwar ta saike ishashshiya

" Haba Abu Amal meyasa kake furtawa yarinyarka wannan kalaman kabari zuwa jimawa zamuyi tunani akan hukuncin daya dace muyi musu amma duka bashida amfani, shidai abu Amal baice komai ba yafice daga gidan afusace

Islam ce ta tsugunna gaban papy tana kuka tace, " papy dan Allah kuyi hakuri karka bari Raihan yasakeni inason mijina wlh bazan iya rayuwa babu shiba, jijjiga kai kawai papy yayi baice mata komaiba yatashi yabar musu parlon daga ita sai ame hauwa

Islam tana kuka tajuyo da ganinta kan ame hauwa tace, " me kikayi kenan kin yaudareni kinyi amfani dani wajan cika buri kanki gashi yanzu kin jawomin tsana wajen mijina da iyayena nashiga uku wallahi bazan yafe mikiba Allah zai bimin hakkina

" Ke Islam karkimin rashin kunya wallahi zan gaggaura miki mari ke wacce iriyar shasha sha ce, tana faɗin haka saikuma tayi shiru ta matso kusa da Islam tafara magana cikin raɗa take cewa,

" Kinga abu ɗaya zakiyi idan kinaso Raihan yakasa sakinki kice kinada cikin sati biyu kuma juyin duniya karki bari likita su dubaki idan aka matsa kice zaki zubda cikin wallahi nasan dole hankalin Raihan yadawo kanki kuma duk Wannan maganar take zata mutu,

Wani irin kallo Islam tabi ame hauwa dashi cikin fusata tamike tsaye tana cewa, " wallahi baki isaba na kara bin irin wannan muguwar shawarar taki kikuma jefani cikin wahala dabakin jini, tana gama faɗin haka taja tsaki ta tashi tafice daga gidan

Kai tsaye gidan Raihan ta nufa dan tasan idan taje gidan iyayen ta bazasu barta tazauna ba, Islam tana karasawa gidan tayi sa,a babu kowa a parlon hakan yabata damar shiga ɗakinta ta kulle tana tunanin wani irin mataki Raihan zai ɗauka akanta ,


A bangaren abu Amal kuwa yana zuwa ya faɗawa ommu Amal duk abinda yafaru sosai hankalinta ya tashi cikin takaici tarushe dakuka tana cewa Ame hauwa ta cuceta data bata mata yarinya

Abu Amal kuwa murmushin takaici yayi yace, " wallahi babu ruwana kanku kuka cuta aida aminiyarki ce dakikaga uwar bari gaiyar ta watse gashi tasamiki ƴa a wahala nidai kullum ina daɗa godewa Allah dabaisa Amal cikin wannan masifar ba




A bangaren Raihan kuwa suna ɗaki shida matarsa Maryam yayi iya bakin kokarin sa ya rarrasheta yabata hakuri cikin nuna rashin damuwa tace,

" Babu komai wlh Raihan Allah yanasan mai yafiya nina yafe musu amma yanzu kayarda da abinda nadaɗe ina faɗa maka ko cewa ame hauwa basanku takeba,

" Wlh na yarda Maryam abunne kamar almara yacce nake ɗaukar ta tamkar mahaifiyata gani nake kamar bazata taba cutar damuba dan bata nuna hakan afiliba

" Dama haka mugu yake wallahi tunkan muyi aure daman nake ganin kamar da matsala saida maganar aurenmu ya bullo nagama tabbatar wa wacece ita,

Dogon numfashi raihan yaja ya kwantar dakansa akan cinyar maryam yana cewa , " kinga lokuta da dama takan nunawa Yasir soyayyah fiye dani hartasa papyma yake masa haka sautari idan na tam bayesu meyasa tayi haka saitace wanda yalalace shi ake nunawa soyayyah dajansa ajiki gudun karya dauwama cikin wannan halin to ashema gaba ɗaya ita tajefashi halin dayake ciki gaskiya matarnan shaidaniya ce Nagode wa Allah nagode miki Maryam,

" Bani zaka godewa ba dan dana gaya maka baka yardaba Yasmin da Yasir zaka godewa susuka tabbatar da zancena,

" Karki damu matata ni nakine kuma kema kinsan nayarda dake ɗari bisa ɗari, Maryam tabuɗa baki zatai magana kenan taji babynta nakuka hakan yasata cewa,

" Yayah mikomin shi, dasauri Raihan yamike jikinsa har rawa yake yadau yaron dasauri Maryam ta karbeshi tajawo fidar da madara aciki zata bashi Raihan ya kwace fidar,

Kallonshi Maryam tayi cikin mamaki tace, " yaya meyasa baza,a bashiba ??,

" Maryam daga yau baza,a kuma bawa yaronnan madaraba saboda ni a ra,ayina inaso ƴaƴana susha nonon mahaifiyar su hakan zai taimakawa lafiyarsu da imaninsu gaba ɗaya duk yaron da bai sha nonon mahaifiyar saba to zai tashi bayajin tausayinta kuma bazai taba kyautata mata yadda yakamata ba saidai idan irin lalurace tasa ba a bashi nononba kokuma rasuwa tayi ,

Murmushi Maryam tayi dan tagamsu da bayanin mijin nata tace, " shikkenan mijina insha Allah naji kuma naɗauka yanzu ka koyamin yadda ake bawa jaririn nono, Maryam takarashe maganar tana mai rufe idanunta,

Dariya Raihan yasaki yana karasowa kusa da ita ya zauna inda take yana curo breast ɗin nata yana bawa yaron

Please Login or Register in order to submit comment