Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuba ko, kulle ido Yasmin tayi tana dariya Maryam tace wanene kuma sadiq,

Anty laulam ta gyara zama tace, " ke bari nabaki labari wani kanin abokin Abban Sultan ne yace yana sonta kuma harsun haɗu yau sun tattauna yayi mata ɗazu dazamu shiga wajen party naji Abban Sultan yana tambayar ta yayi mata tace masa eh

" Alhamdulillah lillah masha Allah su yaya Raihan zamuyi auren autar mu , amma Yasmin duk wannan labarin da kika bani baki gayan na saurayin ba,

Cikin raha tace, " wlh anty kunya nakeji wai nima yanzu Aure zanyi, takara sa maganar tana kyal kyalewa da dariya, suna cikin raha Amal da Islam suka shigo suma ko kwalliyar basu wanke ba bare kaya duk a toilet din Maryam sukai wanka kowa cewa yake a part ɗin Maryam zai kwana dayake wajen wadatacce ne

Islam ma ganin babu kowa a shashinta ne yasata zama aka dinga hidima da ita ana hira da ƴan uwa ana shewa

Misalin karfe sha biyun dare Raihan ya shigo gidan yaganshi makil so yake yaji ɗumin Maryam amma baki sun hana , yana shiga parlon kasa baki suka fara gaisawa dashi yaran ƴan uwa suna ta yi masa labarin wajen party da kuɗin da akai barinsu

Wata kaka awajenshi ce tattijuwa ta karaso kusa dashi tana zolayarsa tace, " kai ɗana mai kama da aljanu kaga yadda naji wasu ƴan mata sunata yabonka a bayana ashe haka kake tafiya da imanin yaran mutane to saika faɗan menene sirrin,

Dariya yayi yana dafata yace, " ai abun ajinin mu yake kema naji yadda ƴan samari suke yabanki awajen, cikin zolaya suka kwashe da dariya ya nufi sama kai tsaye part din Maryam ya numa yana shiga yaga mutane makil sai hira suke bayan an gaisa ya fice yayi ɗakinsa,

Wanka yayi yashafa mai dagashi zai towel ya jawo wayar sa ya dannawa Maryam kira, tana cikin mutane wayarta ta ɗau ruri ta duba taga shine tasan kwanan zanchan cewa zaiyi taje ya mammatse ta shiyasa ta mikawa Islam wayar tace ta ɗaga tace masa tana wanka

Islam ta tashi ta matsa wajen da ba hayani ya ta ɗaga , Raihan yanajin an ɗaga ya gyara kwanciya yace , " honey Queen kinbar mijinki da kewa rabona dajin ɗimin jikinki tun yamma awa kusan biyar kenan,

Wani abu Islam taji ya tsaya mata saitayi murmushi tasan cewa dolane mai mata biyu yafison ɗaya kuma ita Maryam kyawawan halayen tane ya jamata, itama yanzu indai tanason ta zama kamarta dole ta koyi ɗabi unta, cikin fara,a tace, " lah yayana nice bari na kawo maka abinci nasan yunwa kakeji,

Raihan yanajin Muryar Islam ya ɗanja karamin tsaki yace, " okay, a takaice kafin takuma cewa komai ya kashe wayar ji kake kittt,

Islam jiki a sanyaye ta wuce takai wayar Maryam tace "maiyace, " ihmmmm wai abinci yakeso bari nakai masa, tace to, ita kuma tawuce kitchen ta haɗa abinci akuloli ta wuce ɗakinta dasu saida ta kuma watsa ruwa tasa wata sheɗaniyar rigar bacci tashafa turare ta ɗora dogon hijabi akai ta wuce da kayan abincin part ɗin sa,

Da sallama ta tura Kofar ta ajiye kayan a karamin table ta karasa inda yake kwance ko kaya baisaba daga shi sai towel tayi murmushi taje ta cire hijabi tahau kan bed ɗin ta kwanta asaman kirjinsa tana shakar daddaɗan kamshin sa mai kwantar mata da hankali

Lumshe ido kawai Raihan yayi yanajin yadda islam take masa abubuwa chan daya fara hawa network ya mirgina ta ta koma kasa ya haye samanta, saida suka durji juna akasha soyayyah da sambatu harkowa ya gamsu, tare suka shege wanka ita ta cuɗashi shikam bai wani tsaya cuɗata ba ya fice, bayan ta fito tasa kaya dayake akwai kayanta a ɗakin sa sannan shima ta ganshi yayi shirinsa cikin kayan bacci ta zuba musu abinci sukaci dayake dare yayi tana ganin ya kashe kwai ya kwanta itama ta manne a jikinsa ta kwanta


Washe gari da asubah aka raɗawa Yaro suna bayan sun dawo daga masallaci Maryam ta kagu taji sunan da aka sama yaron dukda tasan bazai wuce sunan papy ba kodai wani sunan ɗan uwan nasa

Tanajin shigowar sa ta bishi ɗakinsa bayan sun gaisa tace, " ya sunan babyn nawa? , Murmushi yasakar mata yace ansa masa sunan yaya Abubakar, Maryam tanajin haka da sauri ta ɗago ta kalleshi murya na rawa idonta ya ciko da kwallah tace, " kana nufin sunan ɗan uwana aka saka masa?,

Kai ya gyaɗa mata yana mai jawota jikin sa , ita kuma tuni tafara hawayen farin ciki da tunawa da ɗan uwanta da mahaifiyar su, Raihan yanaganin haka yarungume ta yana cewa,

" A duk duniyar nan bani da abinda zan saka miki dashi Maryam ke haskece acikin rayuwa ta kin fuskanci kalubale da yawa adalilin zamana dake , shiyasa akoda yaushe nake kokarin nafaran ta miki yanzu da Allah zai baki ƴa mace to tabbas da sunan ummanki zan sa miki dan kidinga ganinsu kine rage raɗaɗin dayake damunki,

Maryam tana shashshekar kuka tace, " nice nafi kowa dace da nasarar samin adalin miji mijin marainiya idan ina tare dakai kana ɗebenin kewar kowa nawa saboda soyayyar da kake nunamin babu abinda zanyi na biyaka sai fatan Allah yayi maka sakamakon aljannah ta wannan hanyar,
Ameen ya amsa yakai mata kiss

Anata taron suna raguna kosassu takwas aka yanka shanu uku aka dinga sadaka da naman har masallatai saida aka karkasa naman aka bawa mutane

Gida ya shaki baki ankafa runfuna anata hidima abinci kuwa daga hotel akai other su kala kala anata wadaka da ciye ciye mata da maza ansha kwalliya, misalin karfe sha biyun rana dai dai aka daura auren papy da amaryar sa


Ame Hauwa tanajin labarin andaura ta shige ɗaki ta kulle kanta sai faman rusa uban kuka take abinda yakara bata takaici shine yadda kowa na gidan ya gujeta duk da sun ganta suna mata magana amma babu wanda yake shiga harkar ta kosu biye mata bare akullah wani abun, anata bidiri takasa fita konan dachan wata kawarta ce ɗaya tazo taketa rarrah shinta tana mai bata shawarar ta lallaba papy kafin lokacin iddar ta yayi tasamu ya maida ta idan yaso saita yaki amaryar tabar gidan

Wuni akai ana kaɗe kaɗe har dare aka kawo amarya anata buɗa papy agaban ƴaƴa da jikoki haka ya rike amaryar sa akai musu rakiya Maryam bata bari anbarta abaya ba saida taje

Kowa yana ta yaba yadda sashin papy ya tsaru anata yi musu fatan Alkhairi bayan an raka amarya papy ya fice yakoma gun abokansa kafin baki su gama tafiya ya samu sarari

Kowa sai zuwa yake yanayiwa amarya fatan Alkhairi Yasmin kuwa tana like da amarya chan amaryar ta yaficeta tace, " Yasmin ina Maryam matar yayanku naji labarin ta awajen papy dan Allah ki haɗani da ita inason ganinta ,

Dariya Yasmin tayi tace, " to anty amarya karki damu gobe zanzo miki da ita indai anty Maryam ce batada mushkila,

Misalin sha biyu da rabi na dare gida ya ɗaɗe babu kowa Yasmin ma bata kwana agidanba jan kawayen ta tayi suka kwana agidan Maryam , gida ya rage sai ame Hauwa da ƴan tsirarin baki, suna zaune a parlo suna hira kawar ame Hauwa tace, " ke tashi mutafi ganin amarya, yamutsa fuska tayi jiki asanyaye tace bazata ba dan kar idonta yagane mata kayan bakin ciki

Suna cikin tattaunawa ne papy yazo ya wucesu hannunsa ɗauke da ledodi niki niki ko kallon su baiyi ba yashige

Chan dai suka gaji da muna funce muna funcensu suka watse,

Asashin ango da amarya kuwa bayan sunyiwa Allah godiya suka cika cikinsu amarya sai shagwaba take zubawa papy shikuma jiki na rawa yake rarrashin ta har yasamu ya shoshale abinsa jiyayi tunda yazo duniya kamar baitaba jin daɗin maceba irin haka acikin ransa yake tuna mahaifiyar su Raihan itace matarsa ta farko tunda yarasa ta yarasa farinciki a shimfida ame Hauwa babu wani daɗi a tattare da ita sai yanzu ya fahimci illar dayawa kansa na zama da ame Hauwa,

Adaran kuwa tsabar jin daɗi saida ya kwana kan amaryar shi , basu runtsa ba kyaututtuka kuwa tasha su har ɗan mutum da uwarsa saida yace yabata, soyayyah kuwa ji suke kamar sucinye junansu

Washegari da safe amarya tana kwance ba lfy papy sai jera mata sannu yake ya fito kai tsaye yahau mota ya wuce gidan abinci mafi kusa ya kwaso musu kayan ciye ciye kala kala ahanya ma kasa hakuri yayi saida ya kirata ya tambaye ta ko dawani abun da take bukata tace masa aa sai magunguna da tafaɗa masa ya biya ya siyo mata


Bayan sati biyu da biki abubuwa da dama sun faru kowa yana cikin jin daɗin sa amma banda ame Hauwa jitake gidan yayi mata zafi kamar wuta kiri kiri papy yayi watsi da ita abin takaicin ma ƴar cikin ta bata ko sauraren inda take idan ta ganta saidai ta gaisheta kawai ta wuce

Amarya kuwa tayi kyan kai ta kame kowa na gidan hannu bibbiyu musamman ma Maryam dayake tana tausaya mata ta jata a jiki tunda tazo suka gaisa itama taje mata barka suka shaku kamar dama chan sunsan juna, gashi kullum sai sunyi waya Raihan ma yana matukar jin daɗin yadda amaryar take son iyalinsa hakan yasa kowa na gidan suke kiranta da babbar uwa yara da manya

Papy ma yasamu nutsuwa yamaida hankalin sa kan kasuwanci shida yaransa gashi babbar uwa ba macha ce ce maison barna ba tana tattalin dukiyar su yadda Yakamata

Yasmin ma har ansa Ranarta ita dasu shahida da safeeya abin gwanin sha awa




Bayan shekaru biyu wani kyakkyawan yaro na hanga ya fello da gudu cikin lambu yana kiran abbee abbee Raihan dayake chan gefe ya washe baki yana masa oyoyo da gudu yaron ya faɗa jikinsa yana dariya cikin harshen larabci ci yace, " mamy nace ta hanani biyoka wai, cikin gwaranci yake wannan maganar duk da yarone amma ana fahimta,

Chan na hangi Maryam ta fito da matashin ciki ajikin ta ta karaso tana dariya tace, " yayana ashe saida kabiyo abbeen naka, dayake yaron duka yaya suke kiransa

Raihan yana murmushi yace, " kyaleshi dama fita zanyi tunda ba nisa zanyi ba sai mutafi tare,

Islam tana daga saman bene ta hango su fuska babu fara,a ta haɗiyi wani mugun miyau idonta yayi raurau da kwallah ta zauna tana share hawaye tace, " Allah na rokeka ka kawomin ɗauki inada bukatar ganin nima na ajiye iri a doron duniya nasan na cuci kaina Allah na tuba bazan sakeba, tarusa wani kuka mai cin rai,

Chan Maryam ta shigo taji kukanta ta tura Kofar dakin nata ta tsugunna kusa da ita tafara magana da cewa, " Islam meyasa kike son takurawa kanki sam kinkasa hakuri da kaddara wannan kukan babu abinda zai jawo miki sai matsala,

Cikin sassauta murya tace, " Maryam nakasa yafewa kaina laifin danayi kina gani fa nasamu ciki saboda kawai biyewa sharrin kawaye suka zugani na zubar dashi dan kar nayi saurin tsufa gashi yanzu shekara biyu kenan babu haihuwa babu dalilinta kuma likitoci sunce bazan sake samun wani cikin ba banida ragowar kwayun haihuwa, yanzu ya zanyi kullum kara tsanar kaina nake,

Numfasawa Maryam tayi cike da tausayin Islam tace, " kiyi hakuri wannan kaddara ce Allah ya kaddara miki ki rungume ta kuma ni banga abinda zaisaki shiga damuwa ba tunda Raihan yace ya yafe miki duniya da lahira kuma ko a fuska baya nuna miki komai,

Nan dai ta rarrasheta tayi mata nasiha suka fito parlo sai janta da hira take duk da cikin jikinta ya tsufa hakan baya hana Maryam yin aiki ranar girkinta koma ba itakeda girkiba yi take haka ta tashi ta wuce kitchen tayi wanke wanke ta ɗora abinci

Chan Islam ta shigo da waya a hannun ta tace, " Maryam kinga hoton wannan motar yanzu na ganta a facebook ta wasan yarace mai kyau zan nunawa baby yasaiwa yayana,

Dariya Maryam tayi tace, " kedai Islam bakwa gajiya da tara kayan wasa keda abbakar duk kuncika mana gida da kaya niki niki ga Yasir ma indai ya siyowa amnah saiya siyo masa,

Islam tayi yake tace, " nidai wlh koma yane sai an siyo masa sabuwar shigowa ce, Maryam tace," sai kuyita yi, tana dariya cikin zuciyar ta tanajin daɗin yadda islam take nunawa ɗanta kauna tamkar ita ta haifeshi


Yasir ma Amal ta haihu sunsawa yarinyar sunan mahaifiyar su Raihan suna ce mata amnah yanzu amnah shekarar ta ɗaya da ƴan watanni, su Yasmin kuwa duk sunyi Aure sun haihu abinsu Yaron Yasmin ansa masa sunan papy

Amaryar papy ma ta haifi ƴa mace ansa mata sunan mahaifiyar ta yarinyar kamar ta ɗaya dasu Raihan kana ganinsu zakasan ƴan uwane, sosai gida yasamu haɗin kai kowa yana kaunar kowa suna nunawa junansu kulawa

Ame Hauwa kuwa tunda watanni ukunta suka kare ta tattara inata inata tabar gidan ita barin gidan ma daɗi ya mata dan ta gaji da kallon takaici kiri kiri papy da amarya ko kunya basaji suke soyewarsu agidannan kamar ba gobe

Bayan fitar ame Hauwa ne daga iddah ta samu wani dattijo mai mata uku ya aure ta taje a ta huɗi babu yadda zatai yanzu duk ta tsiyace abin tausayi babu kuɗinma da zatayi bin bokaye dole tasata hakura ta karbi kaddara kullum cikin nadama da danasanin abinda ta aikata take hakan yasa taje tanemi yafiyar su Maryam da Raihan da Yasir akan abinda ta musu tana kuka tabasu tausayi suka yafe mata sukai mata Alkhairi tabar gidan


Bayan wasu watanni Maryam ta haifi kyakkyawar ƴarta mace aka sa mata sunan ummanta daɗi kamar ya kashe Maryam don yadda take samun farinciki agidan mijinta


Bayan wata biyar ne Raihan da Maryam da yaransu suka hau jirgin Nigeria Alhamdulillah sun samu dangin su Maryam dukda cewa magabata sun mutu amma kannan uwarta da ubanta sunanan suna ganinta suka ganeta dan batada maraba da mahaifiyar ta ansha koke koke anyi murna mara adadi, Maryam tayi musu bayanin duk abin ya faru sukai kuka suka jinjina irin wahalar da tasha sukaiwa Allah godiya, anan ne suka bata labarin mahaifinta yadawo nemanta bai sameta ba har ciwo ya kamashi mai tsanani bayan doguwar jinya rai yayi halin sa kafin ya mutu kullum cikin kiran sunan ƴar sa yake da neman gafarar Ubangiji

Maryam najin haka ta rushe da matsanancin kuka tana rokon Allah yayi masa rahama tace ta yafe masa duniya da lahira


Sosai Raihan yaji daɗin samun dangin matarshi yayi musu shatara ta arziki dayake yanzu Maryam ta koya masa hausa raɗau yakejin yaran kamar ba balarabe ba kuma yaransa ma sunji Hausa

4 weeks su Raihan sukai a Nigeria suka koma kasar Dubai abinsu rayuwa ta cigaba da tafiya yadda yakamata cikin farin ciki da kaunar juna

Bayan wata biyu Raihan da Maryam suka koma Nigeria Raihan ya gina katafaran Company a Nigeria ya mallakawa family ɗin dattijo suka koma Daular su lokaci zuwa lokaci sukan kai ziyara





TAMMAT BIHAMDULLAH DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MAƊAUKAKIN SARKI TSIRA DA AMINCI SU TABBATA GA ANNABI MUHAMMADU SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA,

ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ANAN NA KAWO KARSHEN LITTAFIN DAULATUL ARAB INA FATAN ALLAH YASA SAKONA YAJE FIYE DA INDA NAKE TUNANI


KAFIN NA RUFE DOLANE NAYI MUKU GODIYA AL, UMMAR GROUP ƊIN DAULATUL ARAB KUN NUNAMIN KAUNA ALLAH YASAKA MUKU DA ALHERI ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️


Nice dai taku ɗinnan Zainab Ahmad Yusuf, wacce kukafi sani da Yar mutan Libya auuuu 🤭 na manta ansoke wannan sunan wai ni Yar Nigeria ce dole da sunan kasata zanyi amfani 😄😄 to dai nice taku Zainab ZEENARIYA 👋🏻👋🏻👋🏻👋🏻👋🏻

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment