Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni banga wata alama dazata nuna Raihan yana bin mataba

" karkice haka Ame hauwa watakila yana bin matan banzan a waje kiduba kiga lafiyayyen namiji kamar Raihan ace zai zauna haka tsawan shekara 40 babu aure aikuwa daya mutu dan ubansa , kuma sannan hanashi auranma ai babbar dabarace kefa kina duk wannanne dan karsu ci gadan babansu idan yamutu bazaki samu komaiba tunda ƴa ɗayace dake yasmin kinga kuwa Raihan da yasir suzasu kwashe komai

" kemadai kyafaɗa ommu Amal ,yanzudai yazamu bullowa wannan lamarin ?

Gyara zama ommu Amal tayi tana gyaɗa kai tace ," tasigar munafurci da manakisa zamu biyomusu akaji da uwar yarama bare yaran dole subar gidan yadda bazasu kara amsa sunan ubansuba ,kinsan masu iya magana sunce karfar baka tafi ta kasa aiki , kuma ata bangarena zanbaki babbar gudumuwar datafi kowacce dan nima da tamu da Raihan yarainani nikuma natsani mutumin da bazai biniba zakiga yadda zamuyi dasu shidaman yasir mungama da babunsa abunda yarage kawai babanshi yadaina masa kaunar dayake nunamai

Dariya suka kwashe da ita gaba ɗaya sannan ommu Amal ta matsa kusa da Ame hauwa taraɗa mata wata magana wadda nima kaina bansan abinda taceba


Bayan sungama kulla kullar Ame hauwa tafito ranta fes babu wata sauran damuwa tawuce sashinta

Tana shiga ta tadda maryam tana goge gogen kujeru ,kusa da ita tamatsa tana magana cikin harshensu na larabci tunawa tayi maryam batajin komai sai turanci itakuma ba iya turancin tai ba , hakanne yasata gallawa maryam harara tana jen tsaki alamar akwai wata akasa

Maryam taji zagin data mata amma saita danne dantazaci fiye dahaka Allah ma yataimake ta



★★★ bacci yake mai matukar daɗi a makeken gadonsa na alfarma wanda yaji bedshit mai matukar laushi babu abinda kakeji a ɗakin sai sassanyan kamshi haɗi da sanyin mukaiyub

A hankali ya buɗe kyawawan idanunsa ya na mika alamar gajiya da sauri ya maida kallonsa gefe yana murza ido saka makon wata kyakkyawar matashiyar budurwa daya gani akwance a gefensa farace sol ko,a jinsin larabawan ma kana ganinta zakasan ta musammance wasu sheiɗanun kayan baccine ajikinta waɗanda suka bayyana kyau da tsarin halittarta bata da kiba siririyace doguwa ammafa akwai kyakkyawan diri madaidaici

Afusace ya shaki wuyanta yana cewa ," ke ƴar iska tsinanniya karuwa ubanwanene ya kawoki harcikin ɗakina anfaɗa miki ni ina harkar matane wallahi saikin gane shayi ruwane

maruka ya wanka mata harsaubiyu yana daɗa kai mata shaka ya haɗata da bango babu abinda take sai kakari shikuma kamar wani zararre yake ruwan bala,i da zage zage wanda yakaraɗe duk faɗin gidan cikin ruwan masifa yake faɗin ," nasan babu wanda zaimin wannan rainin hankalin sai YASIR wato nacemasa banason hurɗa da mata shine yaturomin wannan maikama da goɗiyar to wallahi daga ke har yasir ɗin sainaci kutumar ubanku kazaman banza kazaman hofi

Banko ƙofar ɗakinnasa yaji anyi da sauri yajuya dan ganin wanda yashigo

Zare ido shaikh Ali yayi cikin mamaki yace ," ya ɗan uwana lafiya naga kanata faman ihu da maganganu kai kaɗai tamkar faɗa kuke da wata

Cikin rashin fahimta da hassala FERAS yace ," baka ganine baka gantaba ƴar,iska karuwa waini za a yaudara uban wanenema yabata izinin shigowa gidan nan kuma ya akai tasan ɗakina ?

" wace ce kenan ? nifa wallahi banga kowaba

Da sauri feras yajuya yana faɗin gatanan na shaketa , baigama karasa maganarba yaja da baya yana dafe kirji saka makon gani dayayi babu kowa a ɗakin sai shida shaikh ali

Dafe kai FERAS yayi yana tunani wannan abunda yafaru kamar almara

Shuru shaikh ali yayi dan yaga ɗan uwan nasa duk ya dubibice da sassanyar murya yace ," yakai ɗan uwana yanzu ka yarda babu kowa a ɗakinnan kai kaɗai kawai kakeyi watakila mafarkine

" aa shaikh ali wannan ba mafarki bane gaskene ido da ido naganta a kwance kusadani ni nazaci yasir ne yaturota saboda su yaudareni amma gashi ta bace babu ita babu dalilinta gaskiya wannan abu yamatukar bani mamaki

" indai ba mafarki kayiba FERAS to yazama dole karage shan giyar dakake watakila itace takesaka gane gane, irin wannan muke gudu shiyasa nida Ammee muke yawan yimaka magana akan karage shaye shayennan haka


Da sauri FERAS ya ɗaga masa hannu yace " dallah malam kazo kamin rashin kunyane kadinga cimun fuska to bazan daina shaye shayenba duk abinda zakuyi kuyi kuma ka gaggauta ficemin daga ɗaki shashasha kawai

Ba musu shaikh ali yaja kafarshi yabar masa ɗakin

A bangaran FERAS kuwa ali yana fita yaja ƙofar ɗakinsa ya rufe , wanka yayi ya taje gashinsa babu wata maganar sallah tunda mashayin giyane ko dadduma babu aɗakinsa bare Al,gur,ani ko azkar

bakin wando yasa iyaka gyaiwa mai bala,in kyau harda sarkoki ajikinsa sannan yaɗau wata riga mara nauyi yasa wadda kana gani zakasan mahaɗin rigarce sarkokinsa na wuya dana hannu yaɗauka yasa wanda duk rabin cikin su na ɗanyen gwal ne saina tagullah

Turaruka masu kamshi ya feshe jikinsa dasu daga bisani yasa kwamemen ta kalminsa kwambos mai bala,in kyau wanda yasaje da dress ɗin

Freezer ya buɗe cikin jerin kwalaben giyarsa yaɗau kwalba uku masu sanyi tun a ɗakin ya buɗe ɗaya yana sha ya karasa shiryawa yaɗau wayarsa da mukullum motarsa yawuce abinsa


Dreaving yake amma kwata kwata hankalinsa baya jikinsa tunanin yarinyar dayagani a ɗakin sa yake abun kamar al,mara kwalbar giyar dake kusa dashi yasake ɗagawa tafi rabi amma saida ya shanyeta tas kozai daina tunaninta amma ina duk kifta idon dazaiyi saiyaga wannan yarinyar

Parking yayi a tsakiyar titi ya karkata motar ta yadda babu wani mai mota dazai iya hucewa harsaiya matsa ,futowa yayi daga cikin motar ya kwanta asaman tsaftacecciyar motarsa mai tsada yana daga kwancen yaɗau bakin gless yasa sannan ya kunna sigari ɗaya hannun kuma kwalbar giya ga kiɗan daya kure a sifikun motar ,duk murfin motar guda huɗun a wangale suku

Cikin muntina kalilan tatin yacika da ababen hawa babu hanyar wucewa kowa daya dososhi wajen zaiyi magana saiyaja burki yayi shiru dan kana ganin motarsa ma zakasan bakaramin mai kuɗi bane bare kuma ka kalli shi kanshi FERAS ɗin duk tsagerantar ka saika saurara masa saboda kwarjinin dayake dashi







✍🏻
ZAINAB AHMED YUSUF HAƊAJA
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲




AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA




STORY AND WRITING ZAINAB AHMED YUSUF HAƊAJA
MRS
Abdussalam




PAGE 1️⃣3️⃣⏮️1️⃣4️⃣

Bismillah




Ɗaga kansa sama yayi yana tunani kala kala lumshe kyawawan idonsa yayi jim kaɗan yaji hayaniya ta yawaita gakuma karar hon ɗin ababen hawan mutane

A fusace yadiro daga motar yana huci yake zazzaga ruwan bala,i

" ku mutsiyata ƴaƴan wahala kowa yaɗauki tsinanniyar saiyararshi yabar wajennan tunkafin na tozarta mutum in banda kun rainamin hankali ni FERAS saboda nakashe titi guda ɗaya na ƴan muntina zakuzo ku isheni da hon


A zahirin gaskiya masifa bataiwa FERAS kyau amma mafaɗacine na bugawa a jarida baya ɗaukar raini kokadan kafin kaga dariyar FERAS sauɗaya kaga faɗanshi sau goma

Tsit mutanan wajen sukai gaba ɗayensu , nacen baya baya sun samu hanyar komawa amma nagaba inaaa sama da mota talatince a cunkushe babu yadda zasu matsa daga wurin dole sai FERAS yajenye motarshi

A bangaran feras kuwa gani yayi babu wanda ya tanka masa hakan yasashi koma kan motarsa ya ɗane yana duba kwalaben giyar yaga babu ko ɗaya aciki bayan yarage kwalba ɗaya hakan bakaramin mamaki yabashiba yanaji yana gani abu kamar al mara yarage kwalba ɗaya cike fal da giya amma ya tadda babu komai

Cije yatsa yake cike da takaici fuskarnan kamar dare shikadai yasan zafin dayakeji azuciyarsa wannan dalilinne yasashi shiga cikin mota ya wuce abinsa

Yana jen motarsa mutane suka fara hamdala suna wuce wa


Kai tsaye FERAS wajen abokansa ya wuce dayake dukansu sojojine abokannasa yana zuwa ya taddasu cikin kaki da alama daga wajen aiki suke shine suka yada zango a babban gidan hutawar da FERAS ne ma mallakinshi ,hannu suka fara bashi suna tafawa ɗaya daga cikin abokan nasu yace yadai oga FERAS naga gabaɗaya ranka a bace ko wanine ya bata maka rai yanzu muje mu aikata shi ?

Shuru FERAS yayi sannan ya shafi lallausan gashin kansa yace babu komai karku damu yanzudai abani giya nasha tukunna , dariya abokin nasa yayi yace oga kacedai mutuniyar ce bakada ita shiyasa ka haɗe rai

" oga FERAS wallahi babu irin wadda kake sha anan wallahi tunda yasir yadaina zuwa kwana biyu shikkenan babu wanda yakara kawo irinta dama kukaɗaine masu shan mai tsada

Gyaɗamasa kai kawai FERAS yayi yafice daga gidan



★★★ Raihan ne da mahaifinsa zaune a parlor kai kana ganin yanayin kasan muhimmiyar magana suke tattaunawa , papy ne yafara magana da cewa

" Raihan inaso kasancewa babu wani mahaluki dazaiso ganin ɗansa cikin wannan halin ,aduk lokacin danaga abokanka ko kannanka da yaransu nakanji bakinciki mara musaltuwa harnakan godewa Allah dayasa mahaifiyarka bataga wannan bakincikin ba

Ni nayi maka magana abokaina da kanne kowa yayi maka magana akan aure amma amsa ɗaya kake bayarwa wai lokacine bai ba toyanzu anzo karshe inaso kajawo lokacinnan yazo kusa dan nagaji

Kasani Raihan ayanzu banida wani magaji dayawuce kai dama ku uku Allah yabani kai da yasir da kanwarku yasmin , yanzu ga waɗannan takardun karbi kaduba


Hannu Raihan yasa yafara karantawa cen yawashe baki da fara, arsa yace ," papy yanzu wannan tamfatsetsan kanfanin daka daɗe kana ginawa angamashi

Dariya papy yayi yace ," eh ankammala amma fa yaci kuɗi Raihan dan harkayama ansiya babban kanfanine shiyasa naga babu wanda yadace yaja ragamar wannan companin saikai Raihan inaso kasharemin kukana kafiddani kunya kayi aure nan da ranar bikin buɗe compani yazama na mun tashi da farinciki biyu

Waro ido Raihan yayi cikin mamaki yananata aurefa kace papy ," eh Raihan idan ma bakada wadda zaka aura ni zan nemomaka ,, da sauri Raihan yace aa papy amma adan karamin lokaci

" lallai Raihan abin naka ya ta azzara to wallahi karkaga ina maka sako sako kayi tunanin zan rangwan tamaka idanma baka nemo matar aurenba nizan ɗauramaka aure dakoma wacece kuma aranar dana sa babu fashi gara kashirya tunda kace kanada budurwa kafaɗa mana iyayenta muje ayi magana

Dafe kai Raihan yayi cikin tsantsar damuwa yace ," to papy abani nanda kwana biyu zanyimaka magana ," aa Raihan kwana biyu yayi yawa saidai kwana ɗaya kaje kagama duk wani nazarinka idan yaso saika faɗa mana iyayen yarinyar muje musamesu ," to papy nagode


Raihan yana fita daga sashen papy yanufi ɗakinsa yanata kai kawo gaba ɗaya tunani ya cika masa kwakwalwa shi wallahi bayasan aure daza a barshi zai iya gama rayuwarsa shikaɗai gashi papy ya ballomasa ruwa dama irin wannan ranar yake jira kuma yasan dole tazo gashikuwa tazo

Shiru naga Raihan yayi nakusan awa ɗaya yanata faman zagaye ɗakinsa cen yazauna abakin gado da alama ya gama tunanin dayake , shiga banɗaki yayi yawatso ruwa dayake dare yayi sannan yayi sallar nafula ya karanta azkar ya kwanta



Washegari da sanyin safiya maryam ta tashi tafara aikinta babu abinda kakeji sai sautin share sharen da maryam takeyi babu kowa a babban parlor sai ita kaɗe

Raihan ne yafito sanye da jallabiya cikin girmamawa ta gaisheshi ya amsa har yafita yadawo yace tasameshi a gaydin zasuyi magana , ba musu tabashi amsa da to dan tayi matukar yarda da Raihan bazai taba cutar da itaba

Ko minti uku baiyi da zuwaba saiga maryam tana zuwa ta tsugunna har kasa ta sunkuyar da kai tace ," gani yaya Raihan

Doguwar ajiyar zuciya Raihan yasaki kana yafara magana da cewa ," maryam inaso zanyi muhimmiyar magana dake wacce sirrice daga ni sai ke saikuma Allah dayake kallonmu bayanmu kada kibari wani yaji abinda zan sanarmiki , amma kafin nafara faɗamiki inaso ki amsamin tambayar dazan miki

Inaso nasan kewacece kuma ina iyayenki amatsayinki na yarinya karama menene dalilin daya kawoki DAULATUL ARAB ?

wasu zafafan hawayene suka biyo kuncin maryam cikin sanyin jiki tafara bashi amsa ," banason tuno koni wacece babu komai acikin labarina sai bakinciki da takaici dan Allah yaya Raihan narokeka kada kamatsamin akan sanin koni wacece bawai bazan iya baka labarina bane ,kawaidai banason tuno da munanan abubuwan da suka faru da rayuwata idan natuna haka nakan shiga bacinrai da damuwa wanda warwaruwar hakan yakanyimin wahala ,,, kukane ya kwacemata mara sauti

Shiru Raihan yayi yana mamakin maryam azuciyarsa yace tabbas yarin yarnan akwai babban abun dayake ruɗata arayuwarta amma dayardar uban giji shizai mata maganin matsalarta kuma sai yasan yadda yayi yaji labarinta

" bazan matsamiki ba maryam dama ance mai ɗaki shiyasan inda yake masa yoyo kai tsaye zanfaɗa miki dalilin dayasa nakiraki inaso kitaimakamin za,a ɗaura mana aure dake wanda a zahirin gaskiya aurene na sunna kuma na gaskiya iyayena zasu ɗaurashi amma kuma a tsakanina dake babu wata auratayya yarjejeniyace zan dinga biyanki albashi duk wata harna tsawan wata biyar dazarar komai yalafa zan sakeki

Rasss rassss maryam taji gabanta ya faɗi ɗago kai tayi tana kallonshi shima kallonta yake ya kureta da idanuwa murya na rawa tace ," menene dalilinka nayin hakan yaya Raihan ?

" yauwa tambaya mai kyau dalilina nayin wannan shirin bawai danni kaɗaiba hardake maryam kina cikin babbar matsala zamanki agidannan akwai abubuwa dayawa wanda suke faruwa koke baki saniba yau kwana uku kenan nakama wasu yara a kofar gidannan sunzo da bakar mota dama na jima a ƴan kwanakinnan ina ganin wannan motar sai na musu target suka shigo hannu dasukaci duka a wajen sojoji sai cewa sukai wai anturosu su sace ƴar aikin gidanmu nayi matukar mamaki dan banyi zaton hakanba dana sake bincikawa sainagane ashe YASIR ne kanina yasa su satoki

ban cewa YASIR komaiba dan banaso kowa yasan zancen agidannan kingakuwa kina cikin hatsari nasan halin YASIR bashida hakuri idan yaso yin abu babu makawa saiya aikata , abu ɗayane zai fiddaki daga sharrin YASIR shine wannan auren duk da nasan zaki fuskanci kalubale da dama amma hakan mafitace agareki ,nikuma zan samu saukin matsin lammar da mutane sukemin akan aure


Gaba ɗaya tsoro yacika maryam afile take cewa "Allah nagode maka daka tsareni daga sharrin YASIR " yaya Raihan na amince da maganar aurennan amma abisa sharaɗi guda ɗaya

" inajinki maryam faɗi sharaɗinki ," kayimin Alkawarin duk da auren gaskiya ne babu abinda zai shiga tsakanina dakai kawai zamu dinga amsa sunan ma auratane ?

" eh nima ai abinda nace kenan ki kwantar da hankalinki babu komai indai wannan ne namiki alkawari kuma sannan daga yau zamu dinga amsa sunan masoya a gidannan kada kiji kunya duk wanda ya tambayeki kifaɗa masa dama muna soyayya tun tuni kuma kina sona

" insha Allah zanyi hakan

" yauwa yanzu kishiga gida idan anjima komai ake ciki zanyimiki bayani




Papy ne da Ame hauwa zaune a bedroom misalin karfe goma nasafiya suna tattaunawa

" haba juddu yazakamin haka bayan munyi dakai cewa idan aka gama companin nan nice wadda zaa bawa dan duk cikin ƴaƴan ka babu wanda ya cen cenci ɗaukar nauyin compani daga ɗan shaye shaye sai maibin mata tuzuru

" hauwa yaukece kike cewa Raihan maibin mata tuzuru saboda bakece kika haifeshiba nayi tunanin ko kowazai kushemin ɗa kebardake ashe hardake wajen zagin Raihan to naji na gode amma karki manta ana barin halak dan kunya ,kuma companine bazan bayarba ɗana zan bawaduk abinda zakiyi kiyi sannan aure Raihan zaiyi aure nan bada jimawaba idan mutuwa zakuyi saidai kumutu sha sha sha kawai


Papy yaja zaki ya fice daga ɗakin nata rai a bace yanufi ɗakin Raihan yasamu Raihan yana karyawa ya zauna kusa dashi bayan ɗan nasa ya gaisheshi yace masa

" Raihan wajenka nazo ya maganarmu da bari zanyi sai yamma amma wallahi nakasa hakuri Raihan namatsu ka tsayarmin da magana ɗaya

Gyara zama Raihan yayi cikin murmushin samun mufita yace ," papy nidama nadaɗe da samun matar dazan aura ina sonta tanasona amma tsoran kin amincewar ku yasa naki bayyana soyayyata ,,, sai yadakata da maganar tasa yarike hannu papyn nasa yace papy maryam ce wadda nakeson aure

" maryam Raihan maryam dai wadda nasani ƴar,aikin gidannan ? ," eh papy ita ," haba dama nasani tunda naga kana rikicewa akanta duk wanda yatabata kake ɗaukar mataki nasan akwai soyayya,to shikkenan Raihan ni nayi farinciki da wannan haɗin kuma insha Allah za,ayi aurennan amma wani hanzari ba guduba ina iyayenta ?

Da sauri Raihan yace ai papy tanada magabata a DAULATUL ARAB akwai kannan mahaifinta sunanan anan su zasu wakilceta





CHAKWA KIYA ANYA WANNAN AUREN MAKIYA ZASU BARI YAKASANCE KUWA ❓






✍🏻
Zee ƴar mutan libya ce
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲





AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA





STORY AND WRITING ZAINAB AHMED YUSUF HAƊAJA
MRS
Abdussalam





PAGE 1️⃣5️⃣⏮️1️⃣6️⃣

Bismillah




" To masha Allah Raihan kaga komai yazo da sauki sai kafaɗa mata tayiwa magabatan nata magana zamuje musamesu

" yauwa papy nagode da fahimta ," bakomai Raihan ka kwantar da hankalinka kaje kafara shirye shiryenka nima zan kirawo kawunnan ka mutattauna


Nan Raihan ya amsa masa da to sannan papy yafice bayan yafita shima Raihan ɗin yashirya yaɗau motarsa yafice


Juddu mahaifin Raihan na hanga da kannan sa suna tattaunawa mai biye wa papy ne yace ," nidai ta bangarena babu wata matsala na amince da aurenan tunda dama abunda muka daɗe muna jirane yazo


Babansu islam da Amal ne yace ," eh wannan abu yayi matukar yi Allah yasanya al,kairi sai mujawa Raihan kunne duk da nasan ba yaro bane karyaga yarinya ba jinsinsaba yadinga cutar da ita kuma gashi batajin larabci dan madai shima Raihan ɗin ya iya yaran datakeji wato turanci

Kowa yagama tofa albarkacin bakinsa amma banda jameel wanda shine auta acikinsu , ganin hakan yasa suka tambayeshi lafiya saida ya numfasa tukunna yace ," nifa a ganina gaskiya wannan auren bai wani yiba kota ina basu daceba kwata kwata banyarda da tarbiyar yarinyar ba taya zaace yarinya karama ta ɗau kafa tundaga afurka tazo DAULATUL ARAB babu uwa babu ubah bamu san asalintaba wacece ita duk bamu saniba kawai dan munason ɗanmu yayi aure sai mubari ya aure ta yana matsayin jinsin larabawa ita kuma tana jinsin bakake

Haydar ne yace haba jameel yazakace haka karka manta addinin muslunci bai haramta mana auran kafuraima bare kuma ita da take musulma kana maganar jinsi mutane dubu nawa nasani daga cikin DAULATUL ARAB sun auri jinsin bakake kuma acikinmu larabawan ma ai akwai bakake , karfa kamanta ba dole akaiwa kowadaga cikinsuba susukace sunasan junan su dan haka bamuda wani zabi daya wuce ayi aurannan

Duka gurin suka amsa da eh hakane shidai jameel babu abinda yakara cewa sai Allah yasanya alkhairi



20:00 PM narana labari yakaraɗe ko ina nacikin gidan cewa maryam ƴar aiki da Raihan soyayya suke har anyi maganar aure

Amal tana samun wannan bakin labarin ta shige ɗaki ta kulle kanta tanata faman kuka na fitar hayyaci cikin tashin hankali duk da batabari kowa ya fuskanci damuwarta ba kukan ma babu sauti takeyinsa

Islam kuwa kai tsaye wajen Ammeen ta tawuce tayi mata zaman ƴan bori tana ta kuka tana faɗin ," dan Allah Ammee na kitaimaka min wallahi zan iya mutuwa inason yaya Raihan kamar raina Ammee kiyimin adalci bazan iya yin aureba sai yaya Raihan

Tun da Ammee taji abinda islam take faɗa zuciya ta kwasota batasan sanda tayo kan ƴar tata da dukaba tana faɗin ," tsabar kin rainani nizakizo kina faɗawa wai kinason Raihan kinsan tsakanina da Raihan babu mutumci na tsaneshi kamar mutuwata

Jin ihun islam Amal dake kwance a ɗaki tayi sai cen taji Ammeen tasu tana ta ruwan masifa da alama dukan islam take ,da gudu Amal tafito daga ɗakin nata tana karasawa ta tsugunna a gaban Ammee tana bata hakuri dan batasan tashin hankali

Ammee taki saurarar Amal dukan islam take babu kakkautawa ,wata kara sukaji Amal ta saki tafaɗi kasa yiff suna ganin haka duk su biyun sukai kanta suka shiga jijjigata wani shure shure Amal take ga wata farar kunfa datake fita daga bakinta

" Ammee kingani ko zamu jawo Amal tamutu a banza kinsan batasan tashin hankali yanzu sai mutanan ta su tashi ,,, Ammeen bata kula islam ba ta rungume ƴarta ajiki tana zubda hawaye dan ta tsani ganin Amal cikin wannan yanayin

Islam ce ta tashi ta ɗakko turaren hayakin da akewa Amal idan hakan tafaru nan danan aka turara mata kan kace kwabo tayi wata atishawa sai bacci , gyara mata jiki Ammee tayi sannan suka kwantar da ita a bedroom ɗin Ammee

Bayan komai yalafa Ammee ta kalli islam da kakkausar murya tace ," islam indai kin haifu ƴar halak datafito daga cikina amatsayina na uwarki ina mai shawartarki kibi umarnina karna sake jin maganar Raihan abakinki karki bari kowa yaji wannan maganar kibar min komai a hannuna

Tasowa islam tayi ta tsugunna kusa da uwar tata tace ," Ammee naji bazan kara maganar yaya Raihan ba amma dan Allah kiyimin rai ki taimakamin ya aureni ,

" karkiji komai islam aike ƴatace dole naso abinda kikeso dan haka tunda nace kibarmin komai a hannuna kawai kibarmin




A bangaran Ammee hauwa kuwa sunajin bakin labari na auren Raihan da maryam komai ya dagulewa kwakwalwar Ame hauwa cikin fishi taje tasamu maryam tana ta zaginta ta uwa ta uba wai karyane ba soyayya sukeba lalatarsu suke munafukan banza

Maryam kuwa hakan bai dametaba sai ta nuna batasan komai ba dama basaja take musu akan batajin yaransu ,dan kanta Ame hauwa tagaji tabar wajen


Matar kanin mahaifin Raihan wato anty Laulam tanajin wannan zancen farinciki ya kamata dama kullum addu,arta Allah yasa Raihan yasamu matar aure yahuta ,duk da mijin anty Laulam yanuna rashin jin daɗin auren maryam da Raihan zaiyi matar tasa tayi iya bakin kokarinta wajen nunamasa rashin aibun hakan kuma yafahimta

Da yamma anty laula tasa aka kirawomata maryam bayan sun gaisa take cewa maryam " amarya kitashi kizauna akan kujera aike yanzu kinzama ƴar gida tunda matar da Raihan zai aurace

Cikin kunya da sunkuyar da kai maryam tamike tazauna akan kujera

" kisaki jikinki ki kwantar da hankalinki maryam ɗazu Raihan yakirani awaya yake faɗamin kuma abban sultanma yabani labari , naɗau nauyin duk wani abu dakike bukata maryam ki ɗaukeni tamkar yayarki nizan kula dake a yadda Raihan yake bayyanamin yana matukar sonki kuma yanasan kasancewa dake

Murmushi kawai maryam take azuciyarta tace ooo ni maryoma ina ganin rainin hankali irin na yaya Raihan duk ya kiɗimasu damasu son auren da masu ki sai bayyana suke

" bakice komaiba maryam kodai kunyata kikeji ? ,, " aa anty Laulam nagode da kulawa Allah yasaka da alkhairi

" ameen maryam to yanzudai kitashi akwai wasu kaya da zan baki kisa Raihan yacemin zamu fita dake anjima za afara siyan kaya dan bikin saura kwana biyar ,,,, rassss maryam taji gabanta yafaɗi tsoranta ya bayyana kwana biyar anya kuwa wannan yarjejeniyar zatayu

Dafata anty Laulam tayi tana kara cewa " karkiji komai kanwata babu wani abu indai ina tare dake ,Raihan mutumin kirkine kuma wayayyen mutumne bakida wata matsala dashi nasan zai kula dake tamkar kanwarsa dan yanada tausayi

Da kyar maryam ta kakalo murmushin dole tace " hakane antyna Allah yayi mana jagora ,tabata amsa da ameen suka shige ɗaki ta haɗawa maryam sha tara ta arziki hadda turarurruka masu bala in kanshi irin nasu na ARAB

Agidan maryam tayi wanka tasa sababbun kayan da anty Laulam tabata farar abaya tass mai madaidaitan ado , masha Allah maryam tayi kyau duk da bakace amma ajin farkoce wajen kyau ga gashi dayake asalinsu fulanine ga siririn madai daicin hancinta ga ɗan karamin baki mai saurin gigita mayun kiss diri kuwa ba a magana dai dai da jikintane bai yi yawaba kuma baiyi kaɗanba ,karshen haduwa maryam takai shiyasa YASIR ya gigice akanta


Misalin karfe biyar na yamma Raihan yakirawo wayar anty Laulam yace mata gashi a bakin get sufito suwuce wajen siyayyar

Dan danan anty Laulam tasa hannunta ajaka taɗakko wani turare tace maryam tafesa ,maryam na fesa turarenan kamshi yabaɗe ko ina suka fice ,, ajingine jikin motarsa suka tadda shi cen ɗaya wajen bangaran kuwa Ame hauwa ce da ommu Amal da sauran ƴan matan gidan sunyi rukuni awata katuwar tabarma kana ganin fuskokinsu zakasan akwai zazzafar kiyayyah

Please Login or Register in order to submit comment