Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

naki tabbas suɗin ƴan babban family ne kuma masu matukar kuɗi a wannan Daula tamu sunada kamfanoni masu tarin yawa dan haka ki kwantar da hankalinki zamu kaiki wajen mijinki bari maigidana yadawo

Wani farin ciki ne yamamaye Maryam ta rungume matar tana kuka tai mata godiya sosai

Dayamma bayan dattijon yadawo ya tarda abin mamaki Maryam ta farfaɗo haka shima akai masa bayanin abinda yafaru tsohon nan yayi shiru nadan wasu lokuta sannan yace ,

" Maryam naji dukkanin zaluncin da aka miki amma wani hanzari ba guduba bai kamata kije gidan nan da wannan cikin ba tunda kina gab da haihuwa kibari ki haihu saimukai ki , Maryam tanajin abinda tsoho yace ta durkusa harkasa tana kuka tace ,

" Dan Allah baba kataimaka min banki ta takaba amma bazan iya jira saina haihuba ina bukatar sanin halin da mijina yake sun kashemin shine kokuwa

" Allah Sarki yarinya ba damuwa tunda kina san zuwa zamu kaiki Allah yasa hakan shiyafi alkhairi




★★★

A fusace ame hauwa ta nufi dakin yasmin tana huci ta tsaya a kanta , yasmin datake karatun Alqur'ani ta dago kai cikin mamaki ta kalli Maman tata tace , " Ame lafiya naganki haka ,

" Ban sani ba uban menene haɗin ki da yasir da akacemin an ganku a wajen shan shayi tare faɗamin menene shirin ki da hakan , murmushi yasmin tayi tace ,

" Haba Ame hauwa menene na dogon bincike haka kibari lokaci kadan nake jira zakiji duk abinda yake wakana karki damu ai ni nabiyo duk wani halinki ,

Ajiyar zuciya Ame hauwa tasauke tana zama a gefan gado tace , " nifa hankalina bazai kwanta ba sainaji menene kike shiryawa,

Dariya yasmin ta kyal kyale tana tafa hannaye tace , " Ame kenan alokacin da kukai taku kullah kullar ai ban sani ba kawai sai jinayi Maryam ta gudu Islam ta auri yaya Raihan kuma wallahi nasan shirinkune,

" Ke yasmin banasan maganar banza mu babu wani shiri da mukai akai kawai Allah ne ya shirya hakan ai da har Islam ta hakura dan tace bazata iya yin ciki ba ,

" Eh lallai kam Ame kun fauwalawa Allah komai ba karya

Dukan bayanta Ame hauwa tayi tana dariya tace " ke bansan iskancin banza





Tunda gari ya waye yau Islam take kukan takaici Saida tayi mai isarta sannan tafito parlor a zaune ta tadda Raihan yana kallon TV bata ko kalli inda yakeba ta zauna a kujera ɗaga kanta dazatai kenan taga hotunan Maryam sunkai guda ashirin manya da kanana akafe a bangon , da sauri Islam tazabura ta mike tsaye tana waige waige a ruɗe tamkar mahaukaciya ta kalleshi shima kallonta yake yana murmushi dajin daɗin yadda ta sauya yanani


Kallon kallo Suke ita dashi tashi Raihan yayi ganin takasa cewa ya jawo ta jikinsa yana murmushi yace, " yadai amarsu hotunan sunyi kyau ko

Islam bata iya bashi amsaba danjin yadda yake yawo da hannunsa a jikinta yana murmushin mugunta ya kama hannunta yana cewa zo muje kiga wani abu, baijira jinta bakintaba ya figeta izuwa ɗakinsa

Suna shiga idanunta sukai mata tozali da wani tafkeken hoton Maryam da Raihan sunsa Kayan bacci anyi musu ɗaukarnan da ake cewa romantic picture , wani wahalallen yawu Islam ta hadiya makwat Nan danan hawaye suka fara kwarara a fuskar ta Raihan yayi kamar bai ganiba yace , " ai ina baki labari wannan hotunan dakike gani na wayatane dama tun jiya nabada a wankomin to Sai yau aka kawo shine na kakkafa duba kiga wannan baima jimaba lokacin cikinta yafito mukayi ai bama iya nan nasa hotonba harda toilet da kitchen duk nasa,

Islam bata saurareshi ba tajuya dagudu tanufi ɗakinta jikake garam ta doka ƙofa tafaɗa kan makeken gadonta tana kuka chan tajawo wayar ta tashiga latse latse ta danno numbar ame hauwa tana dagawa Islam tarushe da kuka


A bangaran ame hauwa kuwa tanajin muryar islam tana kuka tayi wani kayataccen murmushin jin dadi aranta tace ya guma mata kenan a fili kuma tace " aa aa Islam lafiya innalillahi Allah yasa ba dukanki yayiba,

" Ame bagara dukaba yarasa abinda zaimin sai wannan wai,

" To maiya faru fadamin menene kidaina wannan kukan haka ,

" ame dole nayi kuka tunda ya aureni yake azabtar da zuciyata jiyace ranar dayafara sunnar aure dani amma wallahi bakiga wula kanciba koda yatashi kawowa zare jikinsa yayi daga nawa ya zubda ruwan akasa kinga baya bukatar hada Zuri,a dani kuma yau ina tashi da safe sai gani nayi ya kakkafa hotunan waccen tsinanniyar matar tasa ame hatta toilet da kitchen saida ya kafa hotonta

" La la la dan hauka mai yake damun Raihan ne subhanallah wallahi yayi kadan yace zai ki hada jini dake kinga manta dashi sukuma hotunan da zarar yafita ki kwashe kaf ki kona babu abinda zai iya wannan ai cin fuskane

Islam tanajin haka takara harzuka lallai ame hauwa takawo shawara









✍🏻 Zee ƴar mutan Libya
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲







AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA





✍🏻
By
ZAINAB Ahmad Yusuf



WhatsApp number 0917586263




Page 9️⃣4️⃣

Bismillahir rahmanurrahim








Islam tana katse wayar tafara kai komo a ɗakin tana Allah Allah yafita ta kone duk wani hoton Maryam dake gidan



A bangaren Maryam kuwa tunda garin Allah yawaye takejin ciwan mara tun yanamata a hankali haryafara yawaita amma sam taki faɗawa tsohuwar saboda yauce ranar dazasu kaita gidan Raihan kuma indai sukasan tafara nakuda bazasu kaitaba

Haka maryam tajure ciwan dayake yunkuro mata yana karuwa a hankali babu abinda bakinta yake sai lazumi gabanta yana tsawaita faɗuwa tsoranta daya kada tamutu bataga Raihan ba dan batada tabbacin zata haihu kokuwa

Tsohuwar ce taturo ƙofar ɗakin da kaya a hannun ta tanemu guri tazauna ta dafa kafadar Maryam tace, " ƴata kisa wannan dogon hijabin da nikabi babanki yashirya yanzu zamu tafi dan mu isa da wuri

Kai kawai maryam tasamu damar gyada mata Sannan takarbi hijabin tasa ta daura nikab suka gama shirinsu tsab suka dau mota suka hau hanyar zuwa gidansu raihan




Islam tana ganin Raihan yatafi masallaci taji sam bazata iya jure ganin hotunan nan ba tafara aikin yayewa tana fita dasu harabar gidan

Saida tagama kwashesu tsab sannan ta kunna musu wuta tana tsaye suna konewa Amal tafito daga gidansu ta hangota

Karasowa tayi inda take tana cewa, " Islam menene haka kike ƙonawa,

Murmushi Islam tayi tana cewa, " meruwanki kafar yawo daga ina kuke naganki keda ommina, " wlh kinga hospitel mukaje, " waye bashida lafiya, " nice mana,

" Kuma naganki garau meyake damunki hartakai gazuwa asibiti, " hmm Islam kenan cikine to dani kuma likitoci sunce mace zanhaifa, saurin kallon ta Islam tayi tana washe baki tarungumeta, " kai amma Amal ina miki murna wayyo dadi su Ame Hauwa zasuyi jika,

" ai kuwa sai atayamu da addu,a Allah yaraba lafiya, ameen ta amsa mata cen daga nesa sukaga Raihan ya shigo

Yana karasowa kusa dasu Islam tawani haɗe rai Amal kuwa har kasa ta durkusa ta gaidashi cikin sakin fuska ya amsa mata sannan yashige gida

Yana shiga yaga babu hotan Maryam ko daya babu shakka suta ƙona aikuwa afusace yafito yana kwaɗa mata kira

Islam da Amal duk saida suka tsorata daganin yadda Raihan yafito yana karasowa gaban Islam yace mata," ina hotunan matata, Islam bako kunya tace, " naƙonasu, kanta yi auye ya wanka mata mari saida tafaɗi shikuma yashiga tumur musar ta yana takata dakafa da sauri Amal tarikeshi tana kuka take bashi hakuri

Ihun Islam ne yasa su yasmin da shahida da safeeya futowa dagudu dan ganin meke faruwa aikuwa cikin tashin hankali suka shiga bashi hakuri har sukai sa,a yarabu da dukan islam amma ga mamakin su Islam zagin Raihan take

Ana haka yasir yajiyo hayaniya yana zuwa ya tadda Abinda yake faruwa da sauri ya rike hannun Raihan yana bashi hakuri cikin ɓacin rai Raihan yake cewa, " kacikani yasir kanaji fa zagina take yau saina nuna mata niwanene dan na aureta bayana nufin nazama kaskantacce bane dole tagane kuranta

Ame hauwa ne suka karaso wajen ita da anty Laulam suna bashi hakuri labarin yaje musu chan kasan zuciyar su kuwa daɗi sukeji koba komai Islam da Raihan sun raba abin faɗa a family hause ɗin, dakewa Ame hauwa tayi tafara zazzaga masifa tanai wa raihan faɗa da kakkausar murya take cewa,

" Amma Raihan kabani mamaki da girmanka da hankalin ka kadinga dukan matarka a tsakiyar mutane cikin kannanta da yayyenta wannan ai shashanci ne dan bakasanta saikadin ga yimata haka to wallahi bari nakira papynka ai yana gida kai Ammar maza jeka kirashi yazo yaga yadda yayiwa yarinyar nan yanzu idan ubanta yagani yaya zaiji,

Magan ganun Ame hauwa sun tsuma kowa a wajen Amal ce ta iya cewa, " amma hotunan sufa Islam ta kona aga bana ya tambaye ta babu ladabi babu ɗa,a tafaɗa masa magana zagi babu irin wanda batai masaba kitambayi su yasmin

Ana haka saiga papy sun jero da abbu Amal suna tambayar meyake faruwa islam ce da jikinya yayi kacha kacha da kasa takaraso da gudu tarungume abu Amal wato babanta tana kuka tace, " abbana dan Allah katafi dani wallahi bazan iya zama da Raihan ba kaga sbinda yamin yanzu kawai dan kun aura masani

Abu Amal baice komaiba amma fuskarsa tanuna tsantsar bacin rai da wula kancin da a kaiwa ƴarsa, papy kuwa fuskar nan tamkar baitabayin dariya ba ya tsaya karewa Raihan kallo jiyake tamkar ya koreshi daga gidan ya huta danya fuskanci soyake yaraba musu kan zumunci

A dai dai wajen wata bakar mota tayi parking take kowa yabi motar da kallo wasu tsofaffine suka fito mata da miji chan kuma sai ga wata tafito sanye da bakin hijab da nikab , Raihan yana ganin matar yaji gabansa yafaɗi bugun zuciyar sa ya karu

Tsohon ne yabawa su papy hannu suka gaisa Sannan yakalli Maryam dake tsaye yace mata, " ƴata karaso ki gabatar musu da kanki

Maryam tunda tanufo gun take kallon Raihan idonta akansa bugun zuciyar ta yana tsananta ga nakuda dafara karfi yanzu duk jikinta ya haɗa gumi hawayene kawai suke zuba a idonta harta karasa takowa wajen ta cire likaf ɗin fuskarta

Da sauri kowa yazaro ido aka shiga kallon kallo tsakanin Ame hauwa da Laulam da Islam, Raihan kuwa da sauri yakarasa inda take yanaji tamkar a mafarki ya rungumeta yana kuka tamkar karamin yaro yake cewa,

" Ina kika shiga meyasa zaki tafi kibarni kece rayuwata kece duniya ta Maryam, kukane mai karfi yakwace musu duka su biyun, Maryam takasa magana ciwan nakuda bawasa jikintane yafara kar karwa ta rike kafaɗarsa tana durkushewa

Da sauri ya riketa yana tambayar meke faruwa cikin rawar murya tace masa haihuwa zatai dasauri yace yasir kawomin mota mukaita hospitel haihuwa zatai

Tsohuwar da sauri takama maryam suka sata amota yasir ne yaja motar Raihan da tsohuwa huna rike da Maryam Amal kuma tana gaban motar suka ja suka tafi

Papy ne yakalli dattijon cike da al,ajabi yace, " nakasa gane wannan lamari bawan Allah ina kuka samu yarinyar nan??, Murmushi tsohon yayi sannan yace, " labarine mai tsayi wanda zaifi maka daɗi kaji daga bakin maryam fatanmu Allah yasauketa lafiya gaskiya yarinyar nan tana matukar san zama da mutanan gidannan ashe muna tafe a mota nakuda take bata bari mungane ba duk dan ta haɗu da mijin ta

Jijjiga kai papy yayi yana cewa, " bakomai Allah yasauketa lafiya, yana gama faɗin haka yajuya yashige gida


Hmmm Ame hauwa tunda sukaga Maryam batirunsu yayi matukar yin sanyi Islam ce tace, " Ame dan Allah mushiga daga ciki inaso zamuyi magana, bamusu sukabiya itada anty Laulam izuwa gidan Islam

Suna shiga Islam tafara magana cike da tashin hankali , " ame mene hakan yake shirin faruwa munfa kasheta ya akai tarayu wallahi indai ta fadawa Raihan abinda yafaru tofa tamu tagama karewa a gidannan , ame hauwa ce taja dogon nishi tanajin bugun zuciyar ta ya tsananta, anty laulam kuwa zama tayi a kujera tanacewa, " gawata shawara tunda babu hujjar mu mukai mata haka tobasaimu musaba muce bamusan zancen ba zatagane batada wayo kuma dole mukashe yarinyar nan koba yanzuba tarusa mana komai wallahi nasan datuni papy ya koreshi ,

Yasmin ce taja dabaya tana kallonsu ta windo tayi murmushi tai wucewarta



Koda su Raihan sukaje hospital tuni Maryam nakudarta tayi nisa Raihan kuwa duk ya susuce yarasa indazaisa kansa dan danan aka shiga da ita ɗakin haihuwa likitoci sunyi sunyi raihan yatsaya daga waje amma yaki dole tasa aka shiga dashi yana manne da hannunta sai zufa yake yanda maryam take kuka shima haka yake tamkar shine mai nakudar azahirin gaskiya jiyake tamkar shiyakejin zafin nakudar a zuciyar sa babban burinshi tahaihu lafiya itada babyn dake cikinta dan dune rayuwar sa


Sukuma su Amal da Yasir da tsofaffin nan duk suna daga waje suna kaikomo kowa hankalinsa a tashe daga nesa suka hango su ame hauwa da anty laulam da islam da Yasmin abun baiwani bawa Amal mamakiba shikuwa yasir suna hada ido da yasmin suka sakarwa juna murmushi

Suna karasowa ame hauwa tarike hannun yasir cike da nuna damuwa tace yajikin Yar tawa tasauka kokuwa ansamu matsala, shiru Yasir yayi Amal ce ta iya bata amsa da suna ciki basu fitoba


Cikin minti talatin maryam ta haifi sontalelen saurayin danta ammafa tasha wuya dankoda dan yazo fadowa saida tasuma ɗan yana fadowa kuma tafita hayyacinta jini ya balle Raihan kwata kwata bawai ta ɗan yakeba yana kan matarsa likitoci kuma sai kaikawo suke akanta cikin mintuna 33 sukai nasara Maryam tadawo daidai kwata kwata bata wani karuba wajen haihuwa shiyasama tasha wuya sosai

Tana farfadowa Raihan ya rungumeta yanawa Allah godiya sai,a wannan lokacin duka su biyun suka tuna da abinda aka haife Maryam kai ta daga mishi alamar tambayar ina ɗan, nuna mata gefe raihan yayi inda wata likita take gogema yaran jiki yanata tsala ihu, murmushi Maryam tasaki guntun hawaye yana sulalowa daga fuskar ta, hannu Raihan yasa yana share mata sannan yayi kissing ɗin goshinta sudai likitoci kallon ikon Allah suke wata dattijuwa mai fara,a wadda bazata wuce shekara 47 bace tayi murmushi tana dafa kan maryam tace,

" Gaskiya ƴata kigodewa Allah dayabaki miji nagari kamar wannan bawan Allahn tunda muke karbar haihuwa bantaba ganin namijin daya tsaya akan matarshi hakaba harta haihu gaskiya kunburge ni Allah yasawa rayuwar ku albarka, ameen duka suka amsa dashi sannan suka shiga gyarawa maryam jiki aka kaita ɗakin hutu


Raihan futowa yayi yasanarwa da mutanen waje maryam ta haihu saiyaga su Ame hauwa abinda ya bashi mamaki ganin islam dayayi dan sam baiyi zaton zatazoba cikin fusata yakarasa yana daga murya yacewa Islam, " uban waye yakawoki nan mekikazo yi babu ke babu iyalina daga yau matata da ɗana basa bukatar ganinki, gaban Ame Hauwa ne yabada rasssss dan atunanin ta Maryam ta faɗa masa,

YASIR ne yarike hannun Raihan yana rarrashinshi yace, " yanzu duk ba wannan ba ya maryam ɗin take ta saukane, " eh tahaifi ɗa namiji , duk gurinne suka kwashe da Alhamdulillah amma banda Ame hauwa da Islam da anty Laulam,

Amal ce tace, " to yaya ina maryam ɗin take zamu iya shiga muganta, eh kawai yace sannan yaja hannun yasir yace zomuje kanti musiyo musu kayan dasuke bukata,


Maryam kuwa tana kwance agadon jinya ta kurawa babynta ido dake kusa da ita tana irga duk wani fitan numfashin sa dukda damuwar da take ranta hakan bai hanata jin wata zazzafar kaunar yaron nashiga rantaba , sallamar mutane taji saita ɗaga kai tana amsawa kirjintane yayi wani irin bugu ganinsu Ame hauwa wani yawun bakin ciki ta hadiya mukutt sannan ta amsa sallamar Amal ce tayi saurin karasowa ta rungume maryam tanai mata barka da sauka sannan ta koma wajen babyn ta daukeshi tana murna tace ,

" lah kunga ɗanmu kamarshi ɗaya da yaya Raihan tamkar an tsaga kara

Ame hauwa ce tayi murmushi tana karasowa tace " muga ɗan jikan nawa mai kama da ubansa, Amal takai hannu zata mika mata kenan Maryam tayi magana cike da tsawa ta mike zaune tana nuna Amal tace, " Amal karki bata ɗana karki sake kibata dana nace miki,

Kallon kallo aka shiga yi sai tsohuwar nan ta karbi babyn tabawa Maryam sannan ta zauna kusa da ita tana shafa kanta tace, " yata ansamu kai lafiya, murmushi Maryam tayi tana kwantar dakai a kafadar tsohuwar tace, " inna gaskiya Allah yayimuku albarka da kuka haifemu ashe haka haihuwa take nasha wuya tamkar bazanyi raiba , rungume ta tsohuwa tayi tana cewa, " hakane yarinya ta Allah yasa masu biyayyane Allah ya albarkaci rayuwar yaronnan ya tsone idon makiya akansa




Raihan da yasir sundawo daga siyayyah yasir ne yake tuki sai Raihan ya kalleshi yace, " yasir ashe dama matsala zata iya tasowa iyalina katsaya akai amatsayin ka na ɗan uwans ya akai ka sauya haka yaushe kafara tunani mai kyau,,

" Yaya Raihan Allah ne sula kuma Amal ce sula tasauyamin duk ɗabi,una ita tanunamin Kai babban masoyinane kuma banida kamarka tabbas yanzu na yarda mace ta gari bawai iya yara take koyawa tarbiyya ba hatta mijinta tana koya masa yanzu Maryam kanwa na dauketa ina matukar dana sani aduk lokacin dana tuna irin rashin adalcin dana mata shiyasa yazamemin dole na nemi yafiyar ta

, " To Alhamdulillah Yasir haka akeso Allah yakarbi tubanka kuma yayiwa Amal albarka da irin juriyar datai dakai kuma insha Allah nima zan lallasar maka maryam tanada saukin kai zata yafe maka,

" Yauwa yayanmu gaskiya yau kayi matukar burgeni yadda naga kunshiga ɗakin haihuwa an haihu a gabanka, dariya Raihan yayi yana cewa, " ahto saika kwaikwaya idan matarka tasamu ciki kai mata amma saika danne zuciyar ka idan bahaka ba tausayi zaisa zuciyar ka bugawa,

" Ai yaya karka damu muma muna hanya kanwar taka tasamu itama, " ah haba to Alhamdulillah Allah yaraba lafiya saika dage da kulawa da matarka kar asamu wata matsala,

Suna tafe suna hirarsu har suka karaso hospitel ɗin suna shiga inda maryam take suka tadda kowa a ɗakin Raihan ne yafara haɗawa maryam shayi mai zafi yabata amma saitaki karba yanata lallabata itakuma ta haɗe rai cike da damuwa tace masa, " yaya inason nasanar maka abinda yafaru dani, tsohuwar ce tayi saurin toshe mata baki tana cewa, " aa yarinya kibari bayanzu ba tukun kihuya kusamu nutsuwa wannan maganar batanan bace

Haka kuwa maryam tadau shawarar tsohuwa nan aka shiga shira yasir yasiyowa kowa abinci zuwa yamma aka sallamesu dan komai lafiya hatta ɗan


Koda suka karasa gida tsohuwar nance rike da jaririn shikuma Raihan rungume da maryam dan dakyar take takawa saita rikeshi

Ame hauwa ce tabukaci a kawo maryam part ɗin ta amma Raihan yace aa gidansu zasu anty Laulam kuwa kunyar Maryam yahanata magana

Maryam tana shiga gidan nata taga komai ya chanza ansake sababbun kaya masu tsada ɗakin Raihan ɗin yashiga da ita sannan aka shigo da tulumin kayan jaririn da suka siyo maryam dai kwanciya tayi a gado tana mai karbe danta

Islam suna shiga gidan tawuce ɗakinta ita kuma Amal da tsohuwa suka shiga toilet dan hadawa Maryam ruwan wanka aikuwa mai zafi suka samata sannan suka zuba magun gunan da aka basu a hospitel suka saka maryam ta shiga ruwan tadade tana gasa jikinta sannan taji dama dama

Tana fitowa daga wankan akai wa jariri nasa yanata tsala ihun yunwa,










Comments and share 🤝🤝
⛲⛲⛲⛲ DAULATUL ARAB ⛲⛲⛲⛲








AREWA WRITERS ASSOCIATION OF NIGERIA






✍🏻 By zee ƴar mutan Libya



🪀🥏 My Number +218917586263




Page 9️⃣5️⃣

Bismillahir rahmanurrahim








Cikin kan kanin lokaci gida yafara cika da ƴan barka anata shige da fice Raihan kuwa yana kataryar matarsa baije ko inaba idanma ana bukatar wani abun yasir yake aike

Amal ma har dare bata tafi gidaba hakama tsohuwar nan shikuwa dattijo yawuce gida abinsa dan maryam ce ta roki tsohuwar tazauna mata kafin suna,

Islam kuwa tunda tashige ɗaki bata fitoba tanaji har ommin ta tazo barka amma ko tari tama sawa dakin ta kye kar a dameta acikinma idan banda kuka babu abinda take tanaji tana gani gashi ta auri Raihan dinma har gara batai auren ba Allah ne kaɗai yasan kalar wulakanci da Raihan zasuyi mata musamman yanzu dayasamu haihuwa da matar dayafi so


Dare yasomayi Amal ce tace, " Maryam yakamata kidaɗa watsa ruwa kanki kwanta kinga yanzu karfe goma tayi, eh kumafa hakane maryam tabata amsa sannan tamike ta nufi toilet shikuma Raihan yafice tsohuwa kuwa tuni tayi bacci a ɗakin saukar baki

Amal tashi tayi takuma gyarawa maryam gadon sannan tabawa baby ruwa dan taga yanata mutsu mutsu yafarka daga baci bayan tagama tasamu turaren wuta mai dadda ɗan kamshi ta turara a ɗakin Maryam tana fitowa ɗaure da Tarwul ajikinta taga ko ina tsab zama tayi tana dariya tace, " nagode kawata wlh da mace na haifa sunanki zansa mata, dariya itama Amal ɗin tayi tana cewa, " kedai nasan zaki iya amma yayanmu sunan Ammeen sa zaisa data rasu saidai idan kun haifi tabiyu

" Kumafa hakane to ata biyun zamuyi muki takwara samun irinki a dangi ai babban arzikine, " ke maryam banasan tsokana, suka kuma kwashewa da dariya, kiran wayane yashigo wayar amal murmushi tayi ta daga cikin salo da shagwaba tace, " hello baby na, aɗaya bangaran yasir yayi murmushi yana cewa, " to masu jego ataho gida haka dare yayi,

" Uhm uhm ni ni gaskiya anan zan kwana, " aa wlh hakan bazata sabuba hubby na kizo nasiyo miki chocolate, " aa wayo zakamin ƴar mu yanzu bata san chocolate , " okay haka zakice to ganinan zuwa gidan zan kamaki ne kice su sama mana ɗakin kwana dan niyau gaskiya bazan iya hakura ba sonake nima baby girl dinmu tazo duniya cikin koshin lafiya, " bakada dama baby to kazo mutafi amma da sassafe zan dawo, " ok ganinan,

Maryam mutuwar tsaye tayi dayake tana jin abinda Yasir yake cewa Amal tana gama wayar maryam ta kwashe da buda harda tafi take cewa, " mutuniya ta wai yasir ne haka kuke kwasar love kuma ashe cikine dake bani labari ya akai kika tankwaro wannan bawan Allah haka, " hmm kedai kawata kijira gobe akwai labari, to Allah yakaimu naji ana kwan kwasowa inaga yazo kije saida safe

Nan sukai sallama Amal ta tafi


Raihan ne ya shigo gida yaga ba kowa a parlorn da alama baki sun gama tafiya ajiye ledodi biyu yayi a dining table sannan yatafi da ɗaya dakin Islam yana turawa yaji ƙofar a buɗe kwance ya sameta tayi ruf da ciki akan gado da alama kuka take dan sai shash sheka take kanaji zaka samu ta jima tana kukan,murmushin takaici Raihan yayi sannan ya haɗe rai yace mata, " kekuma kukan me kike mekuma akai miki banasan iskanci fa Islam ki shiga tai tayinki,

Ɗago kai tayi fuskar nan tayi jajir abinka da balarabi ya baki na rawa tace, " meyasa bazanyi kukaba kwata kwata baka sona baka kaunata yanzu ga matarka ta dawo ninasan bakin cikine zai kasheni a gidanka wlh ita ka iya kwantar dakai ko agaban wane ka nuna mata soyayyah amma nikuwa sai dukama dakamin agaban kanwata yan gidannan babu wanda bai ganiba hatta mahaifina, murmushin takaici yakuma yi dan shi sai yanzuma ya tuna laifin data masa hadda zaginsa dan danan yakuma jin tsanarta ta nunku a zuciyar sa cikin bachin rai yace,

" Ita Wadda nake nunawa soyayyar tanada tarbiyar da ko dukanta nayi ataron al,umma bazata zageniba kekuma fa wanne irin zagine bakimin ba kinga banida lokacin wannan ga abinci kici ni natafi saida safe, da sauri ta mike tsaye tana cewa, " amma dai yau kasan kwana nane ko kuwa dame jegon zakaje ka kwana nidai wallahi idan aka tauyemin hakkina koda sau dayane bazan taba yafe makuba,

Raihan yanaji yayi banza da ita yafice daga ɗakin bedroom ɗinsa yanufa inda maryam take ya taddata tana shafa mai zama yayi kusa da babyn yasa hannu ya ɗaukeshi yana kallonsa
, Maryam talura da yadda Raihan yashigo gidan ransa a bace hakan yasata cewa, " yana ganka haka waya bata maka rai daga ina kake,

" Hmm daga ɗakin Islam nake wlh duk ta takuramin kwata kwata bana ko kaunar ganinta, Maryam tanajin haka ta ɗago kai tana cewa, " to kaima banda abinka mai yakai ka shiga harkar islam kaima kasan bakunya ce da itaba,

Kallon ta Raihan yayi sai yanzu ya tuna ashefa Maryam batasan

Please Login or Register in order to submit comment