Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mana wai taga dangin miji"

Fa' iza tace "ba wannan ba anty jidda, data bamu Abinci baki ga kaji a ciki ba manya manyan yanka, nace Allah sarki su Abba su basu ci ba amma daga aure ya saiwa matarsa kaji fal, banda na kitchen wanda ba'a soya ba"

Anty Jidda ta jinjina kai tace
"hmmm Allah sarki, se anyi magana yace shi bashi dashi sana'rsa ba wata babbar sana'a bace, Amma har ya iya saiwa matarsa kaji iyayen sa ko oho, wallahi ze gamu dani ai zanje gidan"

Nasreen tace "ai gara dai kije wallahi Anty Jidda dan in ba'a ɗau mataki akai ba ana mata kallon ƙaramar yarinya gaida su Abban ma seya dena zuwa balle ya basu wani abu"

(Abunka da mata, wanda mune maƙiyan junan mu) haka suka dinga ziga jidda suna gaya mata abunda akayi da wanda ba'ayi ba, seda suka tabbatar sun kunna ta ta hau sosai sannan suka bar gidan.

*****************

Yau Ammar da Yamma ya dawo be kai dare ba kaman yadda ya saba, yana komawa yaga Mufeeda da wasu shigar dukda be gaya mata ze dawo ba, kayane Pakistan a jikin ta kanta ba ɗankwali, Mufeeda tayi murnar dawowarsa, sedai kaman kullum yauma a gajiye yake, ta jera masa sannu ba a dadi, kafin taje ta kawo masa Abinci ya zare rigar jikin sa ya bar vest da dogon wando. kafin Mufeeda ta dawo iskar fanka dake busa shi har ya jingina da kujera ya fara gyangyaɗi.

Mufeeda na fitowa daga kitchen taga Ammar yana bacci, bata taɓa ganin sa da vest ba, kodai yasa shirt ko kuma Jallabiya.

Ganin sa haka yasa ta ga yaƙara mata wani uban kwarjini, da ka ganshi kaga ƙaƙƙarfan namiji, ga gashi kwance a ƙirjinsa bacci kawai yake abunsa
Mufeeda na matuƙar Tausayin Ammar, neman halak akwai wahala, hartazo ta ajiye Abincin be buɗe ido ba.

A hankali cikin fargaba da tsoro taje kusa da shi, a hankali ta riƙo hannun sa cikin nata tace
"Yaya Ammar ka tashi kar wuyan ka yayi ciwo fa, ga Abincin na kawo maka"
Ɗan buɗe idon sa yayi ya mayar ya lumshe, ƙurawa fuskarsa ido tayi, sannan ta kai hannun ta zata taɓa masa gemu caraf ya riƙe hannun ta yace

"ai ina kallon ki" dariya tayi me cike da ɗaukar hankali tace
"kana jina amma kaƙi kulani seda zan taɓa gemun ka ko? Ka bari in taɓa sau ɗaya mana"

Ya ɗan kalle ta yace "A'a ba yanzu ba"

A shagwaɓe tace "se yaushe?"

"Sekin girma" ya bata amsa

Tura baki tayi tana ɗan harararsa
"ni wallahi na girma tunda baka taɓa goyani ba, ko Abinci ma da kaina nake ci ba kai kake bani a baki ba"

"Ke yanzu na baki Abinci a baki seki ci?"

"Au meze hana? Kaima fa rannan na baka a bakin nan kaci"
Tayi ƙasa da muryar ta daidai kunnen sa tace
"Kuma da'akaci ba'ayi min Comment ba, Yayi daɗi ko akwai abunda zan gyara a Abincin ba'a gayamin ba"

Ammar ya ɗanyi murmushi yace "Aini har yanzu ina tunanin anya ke kika dafa? Saboda ci kawai nake saboda ina jin Yunwa amma ba daɗi"

Yau ba ƙaramin mamaki Mufeeda take ba, Ammar yana mata hira kaman a mafarki, Mufeeda ta riga ta gama gano Ammar a ɗan zaman su ta gano abubuwan da yake matuƙar so, dukda magana seya ga dama yake yi amma actions ɗin sa in tayi wani abu yasa take gane abubuwan da suke birge shi.

Mufeeda tace "to ko zamu shiga kitchen ɗin tare?"

"kin isheni da surutu fa, kuma ni bacci nake ji"

"yanzu la'asar fa tayi zakayi bacci"

"eh kwanciya zan in huta"

"Abincin fa?"

"Se an jima zanci, ɗakko min pillow guda biyu a ɗaki" ba musu ta miƙe taje ta kawo masa pillow, ya jere pillows ɗin ya kalle ta yace 

"oya ga naki nan kwanta"

"Aini bana jin bacci"

"eh kwanta, nasan muddin na kwanta bazaki bari inyi baccin ba damuna zakiyi"

Kallon sa take yi, sekace wata yarinya 'yar shekara biyar ɗin nan.

"ni gaskiya Yaya Ammar wanki ne dani, zan wanke kaya na da bedsheets, na haɗasu  a ɗaki se kuma inyi bacci? Bayan ina da aiki"

Ya kalleta yace "kece zaki wanke kaya su fita? kiyi jiƙa jiƙa dai, ba fita za suyi ba"

Zata kuma magana, ya janyo ta ya kwantar da ita akan pillow yace

"kar in ƙara jin bakin ki" dan yasan Mufeeda bazata taɓa bari yana bacci ita kuma idon ta biyu ba, wannan bakin nata ma ya isa ya hana shi bacci.

Haka ta kwanta tayi shiru, shima ya kwanta a nasa pillow, babu daɗewa Mufeeda ta fara ajiyar zuciya bacci ya ɗauke ta, shi kuma ya kasa baccin ƙamshin man gashin ta da tuararen jikin ta suka kashe masa jiki amma ya kasa bacci, baƙin gashin ta ya zubawa ido da yake ta sheƙi.

Jin ta fara sauke numfashi ne alamun bacci ya sashi a hankali ya kai hannun sa kanta, ya taɓa gashin nata.

Sam bata san yana yi ba, haka ya dinga shafa gashin nata a hankali na wani lokaci, a hankali Ammar ya miƙe daga inda yake kwance ya shiga ɗakin ta, ko ina tsaf dashi a ɗakin nata.

Drower ɗinta ya buɗe yaga kayan data naɗe na wanki, yasa hannu ya ɗauka ya wuce ta a falo ya fita tsakar gida.

A zamansu da Mufeeda na ɗan lokacin nan, akwai halayen ta da suke matukar burgeshi, duk rikicin ta da shagwaɓarta tana matuƙar bashi girma, dama Ammar mutum ne me matukar son girma, komai ya bata komai ƙanƙantar sa ta dinga godiya kenan tana masa addu'a shida iyayen sa, dukda shi in tayi abu baya yabawa, amma yana jin daɗin addu'ar da take masa, da nuna tausaya masa da take yi.

Se magariba ta buɗe ido, ta juya taga babu Ammar a gurin, ta miƙe ta duba taga ya fita beci Abincin ba, tana fitowa tsakar gida taga ya haɗa kayan sa da nata ya wanke, ya wanke napep ɗinsa a tsakar gida, mamaki ne ya cika Mufeeda, taje tai alwala tayi sallar magariba sannan Ammar ya shigo gida.

Falo ta fito ta sameshi ya zuba Abincin sa ya fara ci.
"Mijina wanki fa naga kayi min" shiru yayi mata yana danna remort, tare da tauna Abincin sa.

"Yaya Ammar ka wankemin kayana, yanzu idan akazo aka tarar kamin wanki ace matarka bata da imani, ka fita ka nemo Abinci sannan ka dawo kamin wanki"

Ya ajiye spoon din yace "ni za'acewa bani da Imani na bar wannan 'yar Yarinyar tana wanke kayan ta, hadda abun shimfiɗa ta"

"Amma Yaya Ammar...
" Ke Yimin shiru, kin isheni da surutu, ga leda can ki ɗauka naki ne" yai maganar ransa a haɗe dan karta kuma magana, ta ɗakko ledar ta duba popcorn ne a ciki da tarkacen chocolate.

Murmushi tayi tace 'Nagode Baby"
Harararta yayi tai saurin cewa "yi haƙuri ashe fa nice babyn, mijin baby, babyn ka ta gode Allah ya ƙara maka buɗi na alkhairi"

"Ameen" ya amsa.

Seda ya gama cin Abincin tace "Yaya Ammar dan Allah ka dinga dawowa da rana kana cin Abinci, ka dena wuni a rana".

Kaman baze magana ba se kuma yace "Idan ban wuni a rana na nemo ba, me zan baki? Me zan kaiwa su Abba?"

"Allah sarki Minjna, gobe insha Allah za'a kawo mana gara se a ɗebarwa su Umma, muma mu samu seka ɗan huta na kwana biyu"

"Gara kuma? Me yasa za'a kawo gara?"

"ai duk wanda aka aurar a gidan mu Baba yana masa gara"

"ya bani 'ya, ya rangwantamin kayan aure, Sannan kuma ya bani gara abun yayi yawa ai, zan iya baki Abinci dai dai ƙarfina amma baza' a ɗora masa ɗawainiya ba, hakan tamkar na gaza ne"

Taje jikin Ammar ta kwanta a hannun sa tace  "tabbas Yaya Ammar ko ƙasa kake ɗauka ka bani zan karɓa inci ba tare da nayi ƙorafi ba, saboda nasan abunda kake da shi zaka bani, ba gazawa ce tasa Baba yake bamu gara ba, sedan sanin cewa maza kuna kashe kuɗi lokacin Aure, dan Allah yaya Ammar karka ce A'a bazaka karɓa ba"

Shiru yayi bace mata komai ba, wayarsa ce ta fara ringing, Jidda ne ke yawo akan screen ɗin wayar sa, ɗagawa yayi tare da yin sallama.

Suka gaisa sama sama, shi izza da rashin son raini, ita kuma jidda a fusace take da shi.
Jidda tace
"idan baka komai ina son ganinka gobe in Allah ya kaimu"

Ammar yace "zan duba inda lokacin zanzo" daga nan ya kashe wayar sa.

"Yaya Ammar wacece wannan"?
"kin fiye tambaya fa"

"Yaya Ammar kenan yanzu laifi ne dan na tambaya?"

"Yaya tace" ya bata amsa a taƙaice.

"Amma baka bani mun gaisa ba?" tai maganar tana saka popcorn a bakin ta

"zaku gaisa wataran"

"Hmm wacece kuma Fa'iza?"

"ƙanwa ta ce, cousin ɗina ce"

Ta gyara kwanciyar ta a jikin sa tace "Wadda ta kira ka rannan fa da daddare?"

"Ke ɗagani ban sani ba, kin fiye tambaya"
Murmushi tayi masa tace "Yaya Ammar kenan, daka san abunda mace take ji idan taga mijin ta da wata mace daban, da baka ce na fiye tambaya ba"

Kare mata kallo yayi cike da rainin
hankali yace
"wace ce macen?"

Wani irin kallo tayi masa, ta miƙe tsaye har zata wuce ɗakin ta ta dawo ta bayansa ta sunkuyo da kanta kunnen sa 
"kowace mace, mace ce komai girman ta komai ƙanƙantar ta, tunda ɗaurin kallabin wata yarinyar yana iya zaunar mata da mutum a gida, ai nima na kai acemin mace baby na, kishin ka ne yasani nake abunda nake"

tayi kissing ɗin sa a goshin sa tace
"I love you baby"

Ta juya ta tafi ɗakin ta, Yayin da Ammar yabi bayan Mufeeda da kallo.

Wannan yarinyar me take nufi ne? Ɗaurin kallabin ta yake zaunar mata da mutum a gida, to wata ke nufi kenan.
Miƙewa yayi ya tafi ɗakin sa kaman wanda ƙwai ya fashewa a ciki, yai shirin bacci ya kwanta, amma ya kasa bacci, haka kurum yau yake jin Nishaɗi, wanda ya rasa na menene, gaba ɗaya duk inda ya juya ƙamshin turaren mufeeda ne ke tashi a jikin sa, lumshe ido yayi yana tuna yadda ya farka ya ganta a ɗakin sa, da yadda ya dinga shafa gashin ta kaman kar ya dena.

Sosai Ammar ya kasa bacci, ya dinga juyi akan gadon, Seda ya fito ya sha tea sannan ya koma ya iya bacci.

*******************

Yauma yana baccin safen sa tazo ta tashe shi,

"Mijin baby ka tashi zanyi wanka"

Ya buɗe ido yace "dan zakiyi wanka se kinzo kin tasheni?"

"kaifa kace in zanyi wanka in maka magana ka kaimin ruwan, kace kar in sake shigar maka toilet, toilet dina ba ruwa"

Tsaki yayi ya miƙe, ya fita tsakar gida ya ɗebo ruwa a bucket ya kaimata toilet, harze fita taje gaban sa ta juya masa bayan ta
"Yawwa mijina ɗan aljanna, Allah ya barmin kai saura ka zugemin riga ta"

Ƙara tsuke fuska yayi, da kamar ya share ta, amma a ransa yace
"bari in zuge mata karta zaci wani abu a ranta"

Cikin fushi Ya kama zip ɗin da nufin ya zuge mata da sauri ya fita, tana sane ta ƙwala ihu wai ya haɗa da fatar ta, kuma ƙarya take, ɗan Riki cewa yayi yace

"Subhanallah, tsaya in gani ban sani ba na haɗa da jikin ki"

Ƙin tsayawa tayi ya duba, ta dinga tsalle tana kuka wai ita bayan ta zafi, Ammar yace
"yi haƙuri zo in ƙara sa zuge miki, ba ina sane na haɗa da jikin ki ba"

Fuskarta harta fara hawaye, gaba ɗaya Ammar yaji ba daɗi, zata ga kaman yana sane yai mata

"A'a ni bana so, dama tunda naga ka haɗe rai baso kake ba ka zugemin da baya na, ni ƙyaleni in ƙarasa abuna".

Tafara kici kicin cire rigar ta, ai ba shiri ya juya ya bar mata ɗakin, yana fita ta zauna ta sha dariyar ta sannan ta shiga tai wankan.

Da ta fito falo taƙi kulashi wai ita lallai haushin sa take ji, ko hirar ma yau ƙin yi masa tayi tai zamanta a kujera tana tura baki.

Haka ya gama karyawa yana yi yana kallon ta, da sassafen nan maimakon ta karya chocolate take sha, kaman yayi magana amma ya ƙyaleta.

Ya gama karyawa ya kalle ta yace
"zan tafi"

Ta kalleshi tace "adawo lafiya" ta ci gaba da cin popcorn ɗin ta, sabon da Ammar yayi in ze fita seta raka shi tana masa rangwaɗa tare da addu'a, yau da bata yi ba seya ji babu daɗi, yana fita kafin ya kunna babur ɗin sa ta tura masa

"I love you my soul, Allah ya tsaremin kai ya albarkaci neman ka, ya wadata mu da halal"

Ɗan murmushi yayi ya tura mata "bana so, ai kina kallo har na fita kika ƙi kulani"

Tana ganin message ɗinsa ta miƙe tana murna, tare da faɗin Yaya Ammar kazo hannun ƙwaila.

******************

Kai tsaye gidan Anty Jidda ya nufa don yaje yaji kiran me take masa haka, yai sa'a tana nan, haje suka gaisa se wani haɗe rai take Ammar yace
"kince kina nema na Allah yasa lafiya"

Jidda tace "hmm Ammar kenan ina fa lafiya, tun yanzu daga yin auren naka beje ko'ina ba, za'a fara wulaƙanta mana dangi"

"kamar yaya ban gane me kike nufi ba"

"Ahh dama ai bazaka gane ba, yanzu tsakani da Allah ace su Nasreen suje gidanka amma a wulaƙanta su"

Nan ta dinga zazzagewa Ammar, wai ya fara wulaƙanta iyayen sa da 'yan uwan sa akan wannan' yar ficikar yarinyar mara mutunci, wadda bata san darajar manya ba.

Sosai suka yi faɗa da Jidda, yace "karta ƙara zagin Mufeeda baya tunanin mufeeda zata aikata abunda ta faɗa"

Ya tashi yai tafiyar sa, wunin ranar gashi nan ne dai kawai, yana tunanin anya Mufeeda zata aikata haka? Wani sashin na zuciyar sa yana gaya masa Mufeeda tana da tsiwa, kuma ba'a shedar mutum.

Mufeeda tana ta murna ta gyara gida ko ina fes ta sha kwalliya, tun da rana taiwa Halima waya cewar taje, da Halima taje ta bata Abinci cikin flask ya sha nama wanda Yaya Amina ta kawo mata a miya, tace wa Halima ta kaiwa Su Umma, amma sam bata gayawa Ammar tayi hakan ba.


Har wajen tara Ammar be dawo ba, har Mufeeda ta fara shiga damuwa akan ina Ammar ya tsaya haka be dawo ba?

Se wajen tara da Rabi sannan ya dawo, tana jin ya shigo da babur ɗin sa ta fita da sauri tana "Mijin baby yau ina aka tsaya ne, tun ɗazu na kasa nutsuwa ban san inda ka shiga ba, na kira ka bata shiga"
Banza yayi mata ya wuce ɗakin sa, tsayawa tayi tana tunanin me akayiwa Ammar haka ya sashi yin fushi haka, bata karaya ba tabi bayan sa zuwa ɗakin sa, ta tarar yana cire agogon hannun sa, ta tsaya a gaban sa tace
"Yaya Ammar wai meya faru ne?"
Har yanzu bece mata komai ba ya nemi guri ya zauna akan gadon sa, gefen sa ta koma ta zauna ta riƙo hannun sa tace
"Yaya Ammar dan Allah ka gayamin meya faru?"

Tureta yayi daga jikin sa yace
"karki ƙara kwanciya a jikina, saboda wulaƙanci 'yan uwa na suzo gidan nan amma ki musu wulaƙanci, me suka yi miki? To bari kiji in gaya miki wani abu, dan ina aurenki baze yuwu ki wulaƙantamin' yan uwa ba, ni bana son rigima kinsa sunje sun gayawa Yata kin musu wulaƙanci se faman jaraba take min, ni bana son tashin hankali na gaya miki, tashi ki barmin ɗaki na"

Tunda Ammar ya fara maganar Mufeeda ta sunkuyar da kanta ƙasa, yaita banbamin sa ya gama ba tace masa uffan ba, seda yayi ya gama sannan ta ɗago ta kalle shi, ta kuma riƙe hannun sa tace

"Kayi haƙuri dan Allah, Insha Allah bazan sake aikata makamancin hakan ba, Sannan suma ka basu haƙuri akan laifin da suka ce na musu, bisa kuskure ne ni ban san nayi musu ba, Insha Allah zan kiyaye"
Ta ƙarasa maganar hawaye na bin fuskarta, ta miƙe zata bar ɗakin, har zata fita ta waigo tace masa
"Ga Abincin ka can a falo, sannan na dafa maka tea ɗinka, akwai ruwan wanka a ɗaya flask ɗin. Daga nan ta juya ta bar ɗakin da sauri tana sheshsheƙar kuka.





Ayshercool
07063065680
✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

     

ELEGANT ONLINE WRITER'S

             

           

                  

                        Page 13



Mufeeda tana komawa ɗaki ta kwanta akan gadon ta tana zubar da hawaye

"ashe wannan ƙalubalen Mama take jiye min tace nayi ƙanƙa ta da fara fuskanta, Allah ka bani ikon cin wannan jarrabawa" haka Mufeeda ta cigaba da zubda Hawaye.

Ammar kam ya ɗanji babu daɗi kukan daya ga tana yi, amma tunda har take bada haƙuri to tabbas tayi ne, kuma ze nuna mata kuskuren ta, 'yan uwan sa nada mahimmanci a gurin sa, baze taɓa bari ta wulaƙanta suba.

Haka yai kwanciyar sa beci Abincin ba, da safe haka ta tarar da Abincin yadda ta ajiye masa, haka ta ɗauka ta kai fridge tai masa girkin safe ta gyara ko ina kaman yadda ta saba.

Fuskarta harta ɗan ɗaga saboda tayi kuka sosai, ƙarfe takwas Ammar ya fito har ta kammala komai.

Tana ganin sa tace
"Yaya Ammar ina kwana"

Kallon ta yayi ya ɗauke kai, yana ƙoƙarin fita, taje ta sha gaban sa tace

"Yaya Ammar dan Allah kayi haƙuri, kazo muje kaci Abincin, karka zauna da yunwa"

"bazanci ba na ƙoshi" ya faɗa a hasale yai waje, falo ta koma ta zauna ta haɗa kai da gwiwa ta dinga kuka kasa cin Abincin tayi itama.

Can da Rana tana kwance abun duniya duk ya dame ta, taji ana buga gate haka ta miƙe jiki babu ƙwari taje ta buɗe, kamanin matan da Ammar ne yasa ta gane 'yan uwan sa ne, murmushinta ta faɗaɗa ta musu barka da zuwa, Maryam ce da Amina Yayyen Ammar, Mufeeda tana ta ɗan ɗari ɗari karta yi wani abun da za' a ƙara zuwa a cewa Ammar tayi, amma se taga su sam bahaka bane, suna ta mata hira kaman ƙanwarsu, a hankali ta ɗan saki jiki dasu suna hira.

Suma tayi musu girkin Abinci, suka zauna suna hirar duniya da yanayin rayuwa, cikin hirar Maryam ta dinga yiwa Mufeeda nasiha tace
"Mufeeda naji daɗin yadda na ganki 'yar gayu dake ga tsabta, kaman kin san Ɗan uwan namu akwai son gayu"

Murmushi Mufeeda tayi ta sunkuyar da kai, Amina tace "Amma halin sa sekin haɗa da haƙuri, mutum ne me sauƙin kai se dai yana da wahalar sha' ani wani lokacin, kiyi hakuri"

Maryam tace "maybe mune yake nunawa wahalar sha'anin ita ba haka ake mata ba"

Ita dai Mufeeda sedai tayi murmushi tana sunkuyar da kai.

Maryam ta kuma cewa "Kiyi haƙuri Mufeeda da yanayin Rayuwar kinji, babu Auren da bashi da ƙalubale, amma kiyi hakuri ki fuskanci mijinki, sannan karki kuskura wani yasan sirrin auren ki kinji?"

Mufeeda tace "Insha Allah Anty nagode sosai"

Mufeeda taji daɗin zuwan su, sun ɗebe mata kewa sosai dukda ƙasan zuciyar ta a cunkushe yake, se bayan la'asar suka yi mata sallama suka tafi.



Koda Ammar ya dawo bebi takan ta ba balle ta gaya masa 'yan uwan sa sunzo.

Kusan kwanaki biyu kenan Ammar baya shiga sabgarta, duk wani abu da ya shafi cin Girkin ta, ko zaman falo ya dena, gaba ɗaya a takure take.

Tana kwance akan gado tana ta tunani, 'nikuma kalar tawa ƙaddarar kena  dangi miji su dinga haɗamin makirci a gurin miji, dan ta Ammar wannan me sauƙi ne, amma duk namijin da yasan ciwon kansa baze taɓa bari matarsa ta ci zarafin' yan uwan sa ba, shiyasa bata ganin laifin Ammar, ita burin ta a yanzu ya dena fushi da ita, Amma ya zama dole ta ci gaba da rarrashin sa harta shawo kansa.

*********************

Shi kansa Ammar baya jin daɗin yadda ya share ta, yayi missing ɗin fitinar ta da kuma Addu'oin da take masa, amma baze nuna mata karaya da wuri ba seta gane tayi kuskure tukuna seya tabattar mata da 'yan uwan sa ba abun wulaƙantawa bane.

Yana zaune a falo da daddare yazo da Abincin sa daga waje yana ci, Mufeeda bata gaji ba tazo da plate ɗauke da Abinci akai tazo gaban sa ta ajiye tace

"dan Allah Yaya Ammar kayi haƙuri kaci Abincin dana dafa"
Shiru yayi mata ya ci gaba da Cin Abinci,
"Yaya Ammar dan Allah ka gayamin mezan maka wanda zesa ka huce, ni ko cewa kayi inje in basu haƙuri zanje, indai zaka haƙura please"

Ammar baya son ɗaga ido ya kalleta, amma hawayen da take zubarwa har cikin ransa yake jin kukan nata babu daɗi.

Kasa jurewa tayi ta faɗa jikin sa ta ci gaba da kuka, jikin ta wani irin ƙamshi yake fitarwa, gaba ɗaya yaji jikin sa yayi sanyi, yadda ta ruƙunƙume shi da hannayen ta ya saukar masa da kasala, zuciyarsa nata harbawa sannan tana ta raya masa abubuwa daban daban, ji yayi kaman ya ƙara rungume ta a jikin sa, amma yin hakan yana nufin wani abun daban kenan, dan haka yasa hannu ya ture ta yace
"kin san bana son kuka ko? Karki ƙara kwanciya a jikina" ya tashi ya bar mata falon.

Kukan ma yanzu kasawa tayi, wace irin zuciya ce da Ammar haka wanda baya jin magiya? Haka taja jiki ta koma ɗakin ta gwanin ban tausayi.

Ammar kam ya shiga yanayi me wuyar fassara, wannan rungumar da Mufeeda tayi masa.

Da safe kafin ta tashi ya fice ya bar gidan, sam Mufeeda ko Abinci bata iya ci saboda damuwa.

Kai tsaye ya wuce unguwar su domin yaje ya gaida su Abba, A soro ya haɗu da Abba yana shirin fita, ya tsaya suka gaisa suka ɗanyi hira, Ammar ya ciro dubu biyu a aljihun sa ya miƙawa Abba, Amma Abba yace

"Ammar ka bar kuɗin ka, nauyin iyaline yanzu akan ka, bakomai ni ina da kuɗi a jikina" Yadda Ammar yake da kafiya haka Abban sa yake se haƙura yayi ya ƙyale shi ya shiga cikin gida.

Guri ya samu ya zauna suka sha hira da Umma, Yace a bashi Abincin safe yaci
Umma tace  "ka baro gidan ka sannan mu kazo ka cinye mana Abinci, maimakon ka taho mana dana Amarya"

Ɗan murmushin yaƙe yayi yace "Umma kenan yau naku nake son ci"

"A'a kodai akwai matsala ne?"
"A'a babu wata matsala Umma"

Umma tace "Halima ɗakko masa fulasan Mufeeda ya tafi dasu"

Ammar ya kalli Umma sororo yace "flasan Mufeeda kuma?"

Halima tace "Eh mana Yaya Ammar, sau biyu tana kirana a waya na karɓo mana Abinci, wallahi ta iya girki sosai, ran da mukaje gidan ka baka nan, Su Yaya fa'iza suna ta mata wulaƙanci wai matar ka 'yar Yarinya amma tana zubo mana Abinci tsit kake ji"

Shiru Ammar yayi bece komai ba, ya karya a gida, daze tafi ya bawa Umma kuɗin da yayi niyyar bata dana gurin Abba yai musu Sallama ze tafi yace "Halima biyo ni da Kwanukan nan"

Umma tace "to Ammar kace ina gaida 'yata, ya kamata kuma ka kawo mana ita, ko seta haihu munje barka"

Da sauri ya kalli umma, a ransa yace "ji umma da wani zance, wai seta haihu aka ga wannan' yar yarinyar da ciki ai naji kunya"

A fili yace "zan kawo tane, na tafi"

"to shikenan ka gaishe ta dan Allah, kace mata nagode sosai, Allah yayi albarka, Su Maryam ma da sukaje shekaranjiya suna ta ƙara yaba Sirikartawa, ka gaishe ta dan Allah, Allah yayi muku Albarka"
"Ameen" ya amsa

Tunani daban daban ne suka ziyarci zuciyar sa, ya akayi aka samu banbanci da abunda Anty Jidda ta gaya masa?

Halima tabi bayan sa da flasai, seda suka fita suka je gurin a daidaita sahunsa Ammar ya kalleta

Please Login or Register in order to submit comment