Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuciyar tace "kai aikuwa daka faɗo wannan 'yar Yarinyar zaka bawa haƙuri, ita fa tayi maka laifi"
Wata zuciyar kuma tace masa "But at least ya kamata kasan halin da take ciki" haka yaita saƙe2 a ransa.

Seda yayi Sallar isha, har ya zauna ze ci Abincin ya fasa ya miƙe ya nufi ɗakin ta, ya tarar da ita tana zaune a tsakiyar gado tana wasa da gashin kanta data tsefe, yai Sallama ta amsa ba tare da ta kalle shi ba, tunda ya shigo ɗakin yaji yana tashin wani sasanyan ƙashi me daɗin gaske.
Ya tako a hankali ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita, yayin da ta maze ta basar dashi kaman yadda yake mata a wasu lokutan idan yana fushi da ita.

"Wai Fushin me kike yi hakane?"
"Bakomai" ta bashi Amsa
"Kin min laifi kin koma kina fushi, Allah ya shiryeki, tashi muje kici Abinci"
"Ni na ƙoshi"
Haɗe rai yayi ya ƙura mata ido, juyawa tayi ta sakko daga kan gadon tana tura baki, ta fice falo.
ɗan girgiza kai yayi yabi bayan ta.

Ammar ya takura ta ta dinga cin Abincin nan badan ranta yana so ba dan har ƙwalla tayi, yace idan tai masa kuka ze ɓata mata rai sosai.

Suna cikin haka Wayar sa ta fara ringing, Idonta ya sauka akan Sunan Fa'iza da ke screen ɗin ƙaramar wayar sa, miƙewa Yayi ya tafi ɗakin sa Amsa wayar.

A ɗan hasale ya ɗaga wayar yace
"Ke lafiya kike kirana yanzu? Meye hakan kikayi?"
"Bakomai Yaya Ammar bugowa nayi in kwashi gaisuwa kawai, Sannan kwana biyu baka zo gidan mu ba"
"Abunda zaki gayamin kenan ya hana ki kirani tun rana?"
"to ai nasan lokacin kana aiki"
"Yanzu kuma ina hutawa ne, karki ƙaramin haka na gaya miki" yayi tsaki tare da kashe wayar sa yace
"Wannan wace irin takura ce? Mutum yayi Auren ma be huta ba? Da suke damuna da kira ni ina naga halin kuma Auren wata macen? Yanzun ma inji da rigimar wadda nake tare da ita mana" yai ta mita ya fito falo

Koda ya dawo falon ya tarar bata nan, Kwanukan yadda ya tashi ya barsu haka itama ta barsu a gurin, shi ya tattare Kwanukan ya kai kitchen, ya tsaya yana wankewa dan ya lura bata barin ko cokali ya kwana bata wanke ba.

Yana kammala wanke wanken akan ɗauke wuta, harze wuce ɗakin sa ya ƙyaleta ya jiyo sheshsheƙar kukan ta ta Window.

Ƙofar ɗakin ta ya tura ya shiga, ya kunna fitilar ƙaramar wayar sa ya haske ta, duk tayi jifa da fulullukan dake kan gadon ta, ta baje gashin kanta se sheshsheƙar kuka take, haushi ne ya kama shi, daze balbaleta da Masifa se ya tuna tunda suke bata taɓa masa makamancin haka ba, idan har ya ƙyaleta a haka be kyauta ba gata Yarinya ƙarama.

(Gareku Maza, ya kamata a dinga yiwa Mata Uzuri a wasu lokutan, idan har ya kasance mace tana kaman ta kyautatawa, wani lokacin ta birki ce saboda ɓacin rai ayi haƙuri a kai zuciya nesa, kar kace zaka hau ka ƙara mata tension, ka danne taka damuwar hankalin ta ya kwanta tukuna)

Ammar yaje ya kwaso fulullukan da tayi watsi dasu a ƙasa ya mayar da su kan gadon sannan ya hau gadon.
zuba mata idanu Yayi yana haskata yama rasa ta ina ze fara.
Gajiya tai da kallon da yake mata, ta zame ta kwanta ta juya masa baya, kashe fitilar wayar Yayi shima ya kwanta ya matsa kusa da ita dai dai Kunnen ta Yace
"Waike wace irin rigimammiya ce haka? Kinmin laifi baki bani haƙuri ba, kika fasa min waya bayan baki san da wa nake waya ba"

Gaba ɗaya jinta tayi wani iri Yadda suke kwance a guri ɗaya yake mata magana.

Ta dake tace
"Nasani mana, da 'yan mata kake waya"
"Shine kike fushi dan nayi Waya da
'yan Mata? Ai bani na kira su ba, su suka kirani fa"
Banza tayi masa ta ƙara matsawa gaba.
Aikuwa Ammar ya ƙulu yasa hannu ya fizgota yace
"Ni kike wa wulaƙanci dan ina lallaɓa ki, ranar da nake Waya da Maryam nake magana, kije kiyi abunda kika ga dama"
Jiki a sanyaye ta riƙe Hannun sa

"Yaya Ammar ɗina, Nasan nayi maka laifi amma ban san a wannan karon me yasa na kasa haƙuri in karɓi laifina ba, Yaya Ammar ina shiga damuwa idan naga wata ta raɓeka, ina iya jure komai amma banda wannan, dan Allah kayi haƙuri bazan ƙara ba, Wayar ka ma dana Fasa kayi haƙuri please, ka karɓi tawa kasa layin ka seka bani ƙaramar in riƙe, kayi haƙuri kaji "

" bana son wayar ki, ai bani na sai miki ba"

"Eh nidai naji ka karɓi tawa please"
Shiru Yayi bece mata komai ba yama rufe idon sa, miƙewa Zaune tayi tace

"Dan Allah Yaya Ammar badan halina ba, kayi haƙuri Insha Allah ko dawa zakayi waya bazan ƙara maka haka ba, yanzun ma sharrin sheɗan ne"

tai maganar tana riƙe hannun sa, ɗisar Hawayen ta yaji a hannun sa ya ɗan kalleta, dukda a duhu ne tayi kalar tausayi, tayi regretting har zuciyar ta.

A hankali ya janyo ta jikin sa yana taɓa gashin kanta dake matuƙar birge shi, amma bece mata komai ba.

"Yaya Ammar ka haƙura?"
Shiru ya kuma yi mata.
Cikin Muryar Shagwaba me cike da Yarin ta tace
"Dan Allah kace ka haƙura"
Still bece uffan ba, shiru tayi bata kuma cewa komai ba, ji tayi gaba ɗaya ta takura da yadda suke ɗin nan, Yanayin ya mata wani iri banbarakwai, dan haka ta Yunƙura zata miƙe taji ya riƙe ta gam, a hankali taji yace
"Turaren wa kika shafa?"
"Turare na ne"
"Hmm ba irin wannan kike sawa ba" Yai maganar a hankali tare da Ajiyar zuciya
Ɗan tura baki tayi tace 
"Yaya Amina ce ta bani ranar da ka kaini gida"
Jinjina mata kai Yayi.
Cikin shagwaba tace "Yaya Ammar bacci nake ji"
"to yi mana ai ba hanaki nayi ba"
"to ka cikani mana ka tafi ɗakin ka"

Ɗan Murmushi yayi yace
"Ni kike kora? To ai gida nane a inda nake so anan zan zauna"

Ammar yana jin yadda zuciyar ta ke harbawa da sauri sosai, gaba ɗaya ya takura ta.

Gajiya tayi da ƙoƙarin barin jikin sa tai shiru, amma ta kasa bacci tana jin Yadda yake sauke Numfashi ta ɗauka bacci yayi.
A hankali ta kai hannun ta ta taɓa gemun sa dake matuƙar birge ta, ji tayi ya riƙe hannun ta, ɗan zaro ido tayi tace
"dama idonka biyu wai?" bece komai ba se ɗan murmushi da yayi yace "Yau hankalin ki ya kwanta ko? Gobe zan aske shi"
"Idan ka aske ko hmm ni nasan me zan maka".

A hankali bacci me nauyi ya ɗauki Mufeeda, bugun zuciyar ta ya koma normal, Tunda Ammar ya shiga ɗakin ta zuciyar sa ke saƙawa tana warwarewa, ya rasa abunyi gaba ɗaya, wani gefen na zuciyar sa yace "Yarinya ce tayi ƙanƙanta"
Amma Cikin bacci Mufeeda taji abunda bata saba ba dan haka da ɗan ƙarfi tace
"Yaya Ammar meye haka ne? Nifa bacci nake ji, dan Allah ka koma ɗakin ka"
Ƙarshe Ammar be gama yanke shawara ba, se bayan da komai ya lafa ya dawo hankalinsa, dafe kai Yayi tare da faɗin
"Subhanallah, what the Fucking shit i did"
Yama rasa me ya kamata Yayi, ya dafe kansa yai shiru, Yayin da kukan Mufeeda ke fita ƙasa2, ta shi Yayi a hankali ya kunna fitilar wayar sa ta dunƙule a cikin bedsheet tana kuka, gaba ɗaya tausayin ta da haushin kansa suka kama shi, wai yau shi ne ya kasance da wannan 'yar mitsilar Yarinyar da yake wa kallon me ƙuruciya.

Ya miƙe ya fita, yaje ya kunna gas ya ɗora ruwa, Allah ya temake shi aka dawo da wuta, ɗakin ya dawo ya same ta yadda ya barta, yama rasa me zece mata.

A hankali yace "Can I help you? Ga ruwa can na kai miki toilet"

Sanin Halinsa yasa ta ɗan juyo ta tashi zaune tace masa
"bakomai zan iya kula da kaina"

Ta sakko daga kan gadon ta nufi toilet tana taka wa a sannu a hankali ya riƙe ta har ƙofar toilet,

Ammar yace
"but do you know how to take the ritual bath?"

Juyowa tayi ta Harare shi a ranta tace "Sekace da shi yake min?" Amma a fili tace
"An ko yamana a Islamiyya"

Seda ta shiga toilet Sannan Ammar ya canza mata zanin Gado ya fita da wancan.

Bayan yayi wanka yayi shirin kwanciya yaji kamar ya koma ya kuma duba ta, kuma se yayi tunanin karta raina shi, wani kallo zata yi masa idan ya koma?
( Yo Yaya Ammar raini na nawa kuma? 🤔🤔 bayan..... 😜)

Ya nemi guri ya kwanta.

Wani irin farinciki ne ke ratsa Ammar wanda ya rasa na mene ne? A zahiri yana matukar raina Mufeeda yana ganin ƙanƙantar ta amma ta bashi mamaki fiye da yadda yake zato matuƙa, lokaci lokaci se ya ɗanyi murmushi wani lokacin kuma yayi tsaki a hankali zazzaɓi ya dinga rufe shi, tare da wani bacci me daɗi yayi gaba da shi.

Da ƙyar Mufeeda ta iya bacci, dan har bacci ya ɗauke ta kuka take tana kiran wayyo Mama a hankali.

***************
Da safe wata uwar makara yayi, dan bayan Yayi sallar Asuba har goma da rabi bacci yake, a hankali ya buɗe idon sa da suka yi masa nauyi ga kansa na sarawa, Ya miƙe ya shiga toilet ya wanke bakin sa ya fito.
tunani yake idan ya fito ta ina ze fara haɗa ido da ƙanƙanuwar Yarinyar da ya kasa controlling ɗin kansa a kanta.
Ita kuwa Mufeeda gajiya tayi da kwanciyar, dukda Jikin ta babu ƙwari tashi tayi ta sake wanka ta sha kwalliya ta shiga kitchen.

Ga mamakin Ammar yana fitowa yaji ƙamshin Abinci, tana kitchen tana aikin ta, lallai Yarinyar nan wani lokacin akwai ƙarfin hali sannan ya jinjinawa juriyar ta, a hankali ya taka zuwa ƙofar kitchen ɗin, ta bawa kitchen ɗin baya dan haka bata san yazo ba.
Ƙura mata ido Yayi yana kallon ta.
Waya take yi da Yaya Amina, tasa wayar a hansfree ta ajiye tana waya.

Mufeeda tace "Yaya Amina wai dan Allah wani irin turare kika bani ne?"

"Turare ne kawai Amma meya faru?"

"A'a bakomai tambayar ki kawai nake"

Dariya Yaya Amina tayi tace
"Kai Auta ki labarta min mana"

"Uban me zan labarta miki? Keda Allah kawai Yaya Amina"

Dariya sosai Yaya Amina take, suka yi sallama ta ci gaba da aikin ta.

Seda Ammar yayi dariya mara Sauti da yaji tace wa Yaya Amina ita da Allah.

babu tsammani ta juyo taga Ammar ta ɗan razana ta ce
"Haba Yaya Ammar ni gaskiya ka bani tsoro, ban san kazo ba fa"
Ya wani maze yace
"Kingama girkin ne? Na makara zan fita"
"yi haƙuri saura kaɗan" ya jinjina mata kai ya koma falo, dama ita tasan za'ayi haka, mazewa ze tayi kamar be komai ba.

Har Yanzu da ta taho kawo masa kayan breakfast a hankali take tafiya tana yamutsa Fuska, wani irin tausayin ta ne ya kama shi, amma shi sam gani yake idan ya buɗe baki yai mata magana akan abunda ya faru koya mata sannu zata raina shi.

Yana lura da ita Abincin ma bata ci ba Sosai, kaɗan taci ta barshi, seda ya gama ta miƙe zata kwashe kwanukan Kaman an masa dole cikin basarwa yace
"Yi zaman ki kawai"
Da yake yasan yayi aika aika, duk wani aiki na gidan shi yayi, amma ya buɗe baki Yace mata Sannu ya gode ne baze iya ba.

Har Mamaki Halayen Ammar suke bata wani lokacin Yana dai ta kula da dukkanin Moves ɗin ta.
Mufeeda ma kuwa ta nuna masa kaman babu abunda ya faru tunda haka yake so, har wani respect na musamman ta shiga bashi ko da wasa bata nuna masa sauyi saboda abunda ya faru jiyan ba.

Wuni yayi a gida beje ko ina ba, Duk shi ya dinga ayyukan gidan, duk da shima baya jin daɗi, Mufeeda kam bakin ta yau mutuwa yayi, wuni sukayi kaman kurame, kusan akan kujera ta wuni gaba ɗaya jikin ta babu daɗi ciwo yake mata, Amma sedai Ammar ya kalleta ya ƙi ce mata komai.

Daddare tea ya dafa mata ya sha Madara da Milo ya kawo mata, ɗan yamutsa Fuska tayi za tayi magana ya haɗe rai yace
"ki karɓa ki ci Abinci kawai"
Tana tura baki taci Abincin seda ya tabattar ta ƙoshi sannan ya sata a gaba ta tafi ɗakin ta ta kwanta, shima ya tafi nasa.

Wayar ta ta ɗauka ta tura masa saƙo
"Yaya Ammar bani da lafiya fa"
"Meke damunki?" yai mata reply

Emoji ɗin kuka ta tura masa tace
"Ai kafini sanin meke damuna"

"Ai ba jikin mu ɗaya ba da zan san meke damunki, ki gayamin mene ne, idan ya kama muje Asibiti semu tafi"

"Shikenan tunda haka kace, Seda Safe have a nice dream Hubby, I love you"

Juya message ɗin nata yaita yi, wani irin tausayin ta ne ya kama shi, tabbas yasan yayi mata ba daidai ba, dan shi kansa ya yabawa dauriyar ta, dan ta bashi mamaki, Amma baze iya zuwa yace mata wani abu ba, to idan yaje meze ce mata?

Mufeeda harta rufe data zata kwanta aka kira ta a waya, ganin dare beyi sosai ba ta ɗaga, muryar Namiji taji suka gaisa tace
"ban gane me magana ba"

"Muffy beb, nasan bazaki gane waye ba, Amma me ƙaunarki ne, mezan samu ne daze sani nishaɗi"

"Dalla Malam Saurara, ina da Aure meyasa zaka dinga kirana, ko so kake ka kashemin Aure?"

"ƙwarai kuwa nasan ke Matar Aure ce, Amma kyakywar mace kamar ki baki dace da zama da Ammar ba, meze hana ki Auri wanda zaki huta kaman sauran 'yan uwanki?, zan baki zaɓi guda biyu ne, ko dai ki kashe Auren ki ki Aureni, ko kuma ki Amince mu dinga Soyayya muna hutawa ko kuma nida kaina ina kashe Auren, zaɓi ya rage naki"

Mufeeda ta tashi zaune tace "Allah ya shiga tskanina da kai, yayi min maganin ka, Kuma koma waye kai Na barka da Allah ya nuna maka ikon sa, Kuma nida Ammar Mutu ka raba"

Ta kashe Wayar ta, tayi blocking ɗin lambar, what's App ta koma taga Yaya Amina a online, nan ta gaya mata abunda ya faru da wanda ya kira ta yanzu da wanda ya biyo ta ɗazu.

Amina tace "Anya Mufeeda ba duk mutum ɗaya bane, inaga wanda ya biyo ki ɗin nan ne, kuma da ƙyar in be sanki koya san Ammar ba, Abunda ya kamata shine ki gaya masa"

Mufeeda tace "Kai Yaya Amina nasan halin abina, ƙyaleshi kawai idan, nayi blocking ɗin lambar sa"

"Amma kina ganin babu matsala idan baki gaya masa ba?"

"Zan gaya masa amma ba yanzu ba".


Ɓangaren Ammar har ya kwanta yaji saƙo ya shigo wayarsa, da sauri ya ɗakko ya duba yayi zaton Mufeeda ce


"KASA IDO SOSAI AKAN MATAR KA, DAN TANA AIKATA WANI ABU A BAYAN IDON KA, DAGA ME ƘAUNAR KA!!!




In an karanta amin share zuwa wasu groups ɗin dan Allah

Ayimin afuwa ba Editing

Domin sharhi gyara ko Shawara
Ayshercool 07063065680
[11/07, 8:43 PM] Ayshercool: ..✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

Please follow me on Wattpad, vote and Comment

https://www.wattpad.com/1096499534?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Ayshercool7724&wp_originator=NWkhlySuZ8Eug%2BopXFfcycv2JGS3axjaccC5%2FbUYT6YzeXAYV4ybw7FnTr8fHQDwo5ncF8TNfQfelSdeR5t0OZi0%2FKAiAcvwuLa561y0j%2BMpxBPI15z3EyzU4ZruY9KP

ELEGANT ONLINE WRITER'S

             

           

                  

                        Page 20



Shiru Ammar yayi yana sake juya message ɗin, tsaki Yayi ya ajiye tare da sawa ransa wrong Number ne kawai.

Ya ajiye Wayar da niyyar yayi bacci amma ya dinga tunanin Message ɗin, Halayen Mufeeda ya dinga tunawa na kirki, dan haka ya ƙara tabattar wa da kansa cewar wrong Number ne, tunanin daren su na jiya ya tsaye masa a rai, yana tuno wasu abubuwan da suka kasance tsakanin su, ɗan murmushi Ya dinga yi tare da rungume filon sa, Tunani yaita yi a ransa ko ya jikin ta? Me ya kamata yayi mata ko ya bata wanda zesa taji daɗi, yana wannan Tunanin wani nannauyan bacci ya ɗauke shi.

Da safe ma fitowa Yayi ya tarar tana ta aikace aikacen ta ya kalleta ko rigar bacci bata canza ba tana mopping

"Sannu agogo sarkin aiki, ki dinga sassautawa kanki da wannan aikin mana"

Ɗagowa tayi tare da yin murmushi ta ɗan risina tace "Ina kwana Yallaɓai"

"Lafiya ƙalau, kin tashi lafiya?"

"Alhamdilillah"

"masha Allah"
Yaje ya nemi guri yana zauna, ta kammala aikin ta, ta kalle shi tace
"in kawo Abinci ne ko se an jima, ina so inje in wanka ne"
"Je kiyi ki fito semu ci"
Ta kalle shi ta lanƙwasa kai tace
"za'a bani a baki?"
"Je kiyi wankan ki dawo dai"

Taje tai wanka ta canza kaya, sannan ta fito ta gabatar da kayan breakfast din, kaman Yadda ta buƙata Ammar ke bata Abincin a baki, yana ci yana bata.
Mufeeda ta so tayi masa zancen wanda ya kira ta amma se taga Ammar yayi mata kwarjini bata san a ya ze kalli abun ba.
Ɓangaren Ammar kuma tausayinta yake ji Sosai, yana son ya tambaye ta ya jikin ta? amma Izzar sa ta hanashi ji yake yin hakan tamkar ya faɗo ne a idon matar tasa.

Se da suka kammala yana ƙoƙarin tashi yaje ya shirya, tazo ta kwanta a jikin sa.
Ammar yace
"Ya haka? Fita fa zanyi rana ta fara yi"
"Nifa bana gajiya da ganin ka, ka bari in ƙara ganin ka mana"
"Kinga ɗagani ina sauri"
"Me kake so in girka maka kafin ka dawo?"
"Kome kika dafa zanci"
"Shikenan bari in jira ka anan ka shirya semu yi Sallama"
"Zo muje ki tayani in shirya"

Zumbur ta miƙe daga jikin sa ta koma gefe tare da tura baki

"A'a ina nan ka shirya seka fito"

Ammar ji yayi kaman yayi dariya amma ya basar ya shige ɗakin sa.

Tana nan zaune a falo ya fito ya shirya tsaf ze fita, wani murmushi tayi masa daya sa Ammar ƙura mata ido, ta tafi inda yake tsaye tace

"Kayi kyau sosai babban mutum, Allah ya kiyaye min kai ya ƙara mana Arziki, Allah yai maka jagoranci Namijin duniya"

Ɗan murmushin gefen baki Ammar yayi yace "Ameen" sannan ya fice.

**************
Mufeeda na zaune na aikace aikacen ta, yaro yayi sallama tai masa izinin ya shiga dan gidan Maman Nur ne ya gaishe ta ta amsa cikin sakin fuska, Yaron yace
"Wai cewa akayi inzo in gaya miki umman mu ta haihu"
Mufeeda tace
"masha Allah, kace ina mata barka kafin in shigo" tai masa kyautar sweet sannan ta Sallame shi ya tafi.

***********************
Nasreen zaune suna hira da Fa'iza , Nasreen tace
"Fa'iza wai ya ake ciki da mutumin ne? Ina fatan zuwa yanzu dai kinyi wani ƙoƙari?"
"bari kawai, ina ta up and down a gidan Anty Jidda ina kushe ta ina ƙara tura mata tsanar ta, in gaya miki anan naga wata guzuma wai ita ce tsohuwar budurwar Ammar wadda ze aura da, na maze in gaya miki ban nuna musu komai ba, Amma itama zata gane kuskuren ta, yanzu ba ta tata nake ba, ina nan ina shiryawa matar Ammar tarkon da ba zata fita ba se Auren nan ya mutu "

Nasreen tace
"Shikenan Allah ya taimaka, amma dai abi komai a sannu dan wallahi Fa'iza yarinyar ta fara bani tausayi, Yarinya ce ƙarama ga Sanyin Hali"

Tsaki Fa'iza tayi tace
"ki koma bayan ta kenan?"
"A'a nina isa in koma bayan ta in bar 'yar uwa ta, bata isa ba ina bayan ki har yanzu"
"In dai kina bayana to ki cigaba da goyan baya"
"Karki wani damu ana mugun tare"
Suka yi shewa tare da tafawa.

********************

Mufeeda ta kira Ammar a waya ta gaya masa anyi haihuwa zata shiga barka yace mata to.

Da Yamma Ta shirya ta fita da niyyar yiwa Maman Nur barka, amma tana zuwa aka ce mata ai, an tafi da ita Asibiti tana ta zubar da jini Jaririn ma kaman bashi da lafiya.

Mufeeda ta Jajanta musu ta fito, akwai surprise ɗin da take shiryawa Ammar dan haka ta miƙe ta tafi titi shagon da take son yin siyayyar da take buƙata.

Seda tai siyayyar ta ta gama ta kama hanyar komawa gida.
shan gaban ta akayi da Napep taji ance
"Ke 'yan mata daga ina?"
Ɗagowa tayi a fusace zata yi magana seta ga Ammar ne, Murmushi tayi tace
"Nice' yan matan? To ɗan Saurayi siyayya na fito"

Ammar yace
"kin cemin zaki shiga maƙota barka amma in ganki anan, me kike yi?"

"Allah ya bada haƙuri, Siyayya na ƙaraso titi nayi, kuma nayi niyyar gaya maka dama"
"Shikenan shigo mu tafi"
Ta ɗan kashe masa ido tace "Nawa zan biya?"
Ɗan murmushi yayi saboda haɗuwar su ta farko ya tuna.


Shiga tayi yaja babur ɗin, maimakon su tafi gida kai tsaye seda yayi zagaye da ita sannan suka nufi gida, a hanyar su ta komawa gida Mufeeda tace

"Yaya Ammar zan sai Kayan miya a gurin me kayan miyan kan layi"

Ammar ya jinjina mata kai, Kafin su ƙarasa bakin layin taga motar wannan mutumin da ya biyo ta ranar a ƙofar wani katafaren gida.
Tunani ta fara yi a ranta
"Kenan mutumin nan a unguwar nan yake kenan?"
Ammar ya kalle ta ta mirror yace
"ya dai? Akwai magana ne?"
Saurin girgiza masa kai tayi alamar A'a.

Suka tsaya gurin Sa'idu me kayan miya, suka sai kayan miya sannan suka yi gaba.

Mijin Maman Amir na gurin me kayan miyan shima yaje siyayya, Sa'idu me kayan miya yace 

"Taɓɗijan Iska na wahalar dame kayan kara"
Mijin Maman Amir yace "kamar yaya?"
"Hmm ai Matan yanzu se Addu'a, wannan maƙocin naku me A daidaita sahun nan, baka ga Yadda yakewa gidan sa hidima ba, kusan kullum cikin cefane yake, ko ya shiga shagon Sunusi me kanti siyan madara, ƙwai bredi, kusan duk ɗan cinikin nasa a haka yake tafiya, Amma rannan da tsakar rana ba kunya na ganta ita matar tasa tana zance da wani Alhaji me mota, seda na ƙura ido naga ashe Wannan Alhajin ne na bayan layin nan, Alhaji Idris "

Buɗe baki Baban Amire Yayi yace
" Kai haba dai? "
" Wallahi dagaske nake, Allah ya nunamin Annabi kamar yadda na gansu "
"Taɓɗijan amma wannan anyi sakaryar mata, To Allah ya tona mata Asiri, shegiya da idon ta kamar an soya Aya, ashe munafuka ce, ai shiyasa mutum ya zama tsayayye a gidan sa, ni mata ta isa taimin wannan shirmen? A haka kalle shi kamar namijin gaske sakarai ni har ya ban haushi"

Haka Baban Amir ya ci gaba da zazzga tare da zage zage shikuma me kayan miya yana ziga shi.

Seda baban Amir ya tafi Sa'idu yace

"Aikin banza ji yadda yake wani cika baki waishi ya isa da gidan sa, Kamar ba nan matar tasa take yawo kwararo kwararo tana fallasa Asirin sa ba, anan gurin nan suke zama take zazzage sirrin sa ba waishi ke ya isa da gidan sa, aikin banza, ni ina nan gefe ayi dai mu gani"

********************

Da safe Ammar ya tashi daga bacci ze fito ya ɗakko wayarsa ya kunna, saƙo ne ya shigo wayar sa yana dubawa saƙon Mufeeda ne na birthday wishes ya shigo wayar sa, saƙon cike yake da nuna fatan Alkhairi da kuma tsantsar Soyayya a ciki, Murmushi yayi ya ajiye wayar har ya miƙe wani saƙon ya shigo wayar sa

"KA SA IDO AKAN MATARKA, TANA AIKATA RASHIN GASKIYA A BAYAN IDON KA"

Mamaki ne ya kama Ammar shiru yayi yana tunani, yana sake juya saƙon, wani irin rashin gaskiya ne Mufeeda zata aikata a bayan idonsa? Tunani yake akan Yadda take masa biyayya iya yinta, taya za'ace tana aikata wani abu a bayan idon sa? Amma zeso yasan wanda yake ya turo masa wannan saƙonnin.
A hankali ya ajiye wayar ya miƙe jiki a sanyaye ya fito falon.
Yana

Please Login or Register in order to submit comment