Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

DOGON PAGE AMMA BANYI EDITING BA.

MASHA ALLAH, INA ME FARINCIKIN MIƘA SAƘON BARKA DA SALLA GA ƊAUKA AL'UMMAR I NA DUNIYA, FATAN ALLAH YA MAIMAITA MANA.

WANDA SUKA KIRANI DA WANDA SUKA TURAMIN SAƘON BARKA DA SALLA NA GANI INA GODIYA, ALLAH YA BAR ƘAUNA

In an karanta a tayani share please

Don't forget to
Follow
Vote and Comment

Ayshercool
07063065680✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨

( *Sai Mata* )

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

Please follow me on Wattpad, vote and Comment

ELEGANT ONLINE WRITER'S

     NOT EDITED   

                        Page 26

Ƙoƙarin ci gaba da kwantarwa da Mufeeda hankali Ammar ya cigaba dayi, Amma kuka take Sosai tana nanata "Innalillahi wa and raji'un"

Ammar yace  "Mufeeda, Saima fa ba mutuwa tayi ba, likitoci suna ƙoƙarin ceto ranta ne, ki dena kukan nan"

"da kunne na fa naji ance Jabir ya kashe ta"

"Ai bashi ya kashe ta ba, bata da lafiya ne kawai, ki bari gobe Insha Allah zanje Asibitin in ga abunda yake faruwa"

Da ƙyar ya dinga rarrashin ta, ya samu ta sassauta kukan da take yi, bacci ne ya fara ɗaukan ta, ba zato ba tsammani suka ji ana buga ƙofar falo da ƙarfi ana masifa, se yanzu Ammar ya tuna ne rufe ƙofar gida ba, da sauri ya miƙe yaje yaga wani mara hankalin ne yake musu wannan bugun?
Yana buɗewa yaga Maman Nur tana bala'i
"Waye uban ta a garin nan da har za tace zata dakarmin ɗa? Ita ta haifa min shi ko tare muka haife shi, wallahi in yarinyar nan ba tayi wasa ba sena mata dukan tsiya a layin nan"

Kallon da Ammar yayi mata ne yasa ta nutsu tana kame kame, cikin ɓacin rai Ammar yace 
"tinkiyar inace ke zaki shigo min gida ƙarfe goma na dare kina zaki daki mata ta? Me tayi miki?"
"Am... Ammm... Dama yarona tace zata daka nazo inji ba'asin me yayi mata zata dakarmin ɗa"
"shine za kizo kinamin hayaniya kamar tashin duniya bama ta daki ɗan naki ba zaki zo kina ɗagawa mutane murya kamar ba matar Aure ba, Wallahi na kuma ganin ki a gidana sena ɓata miki rai, fice ki barmin gida mahaukaciya kawai"
Yanayin Yadda Ammar yake maganar ne ya tabattarwa da Maman Nur ya ƙulu matuƙa dan haka sum sum ta fice.
Ɗakin Mufeeda ya koma, ya tarar da ita a zaune, bugun ƙofar da'akayi yasa ta tashi, ya ƙaraso ya zauna kusa da ita yace
"wai dan Allah meye haɗin ki da matar nan ne?"
Mufeeda tace "wallahi babu wani abu tsakanina da ita, kawai ta tsane ni ne, tun ranar da tace in bata Madara na hana ta, ta sakani gaba a layin nan wallahi badan darajar Aure na ba, wallahi da sena koya mata hankali, bana son biye mata ne kawai, sabon Aurena shine mutunci na, da zarar na biye mata mun raba abun faɗa mutunci na da naka ze zube a idon mutane "

Mufeeda kenan dukda tarin ƙuruciyar ta akwai kaifin tunani.

Ammar yace " Shikenan, ki cigaba da haƙuri ba ruwan ki da ita, duk abunda tayi miki na ba dai dai ba ki gayamin, idan ba tayi wasa ba sena kaita gurin 'yan sanda, mahaukaciyar banza kawai "

" A' a Yaya Ammar base ka kaita gurin 'yan sanda ba, aishi maƙoci haƙuri ake dashi, Allah ya shirya ta kawai, ni yanzu hankali na yana kan Anty Saima"

"Ki kwantar da hankalin ki, Insha Allah zata warware".

********************

Da Safe Ammar ya shirya yace zeje Asibiti yaga halin da Saima take ciki, Mufeeda tace seta bishi, yayi yayi ta zauna a gida tace ba zata iya zama ba binsa zata yi,
"Kinga kiyi haƙuri bekamata in tafi dake ba yanzu, ki bari inje inga halin da take ciki se inzo muje ki duba ta kinji Jaririya ta"
"Shikenan Allah yasa tana raye ya bata lafiya, muje in raka ka"
Ammar ya wuce gaba tana binsa a baya, suna fitowa tsakar gida ta shaƙi ƙamshin ɗumamen miyar kuka, ta kalli Ammar tace "Yaya Ammar ba kaji ƙamshin miya ba?"
"Naji mana, meyafaru?"
"Kaman daga gidan Anty Hajara nake jin ƙamshin"
Ammar yace "Maybe"
Marairaice Fuska tayi tace "dan Allah Yaya Ammar in baka kwano kace ta sanmin ko loma biyu ne?"
Wani irin kallo Ammar yayi mata yace  "Idan tuwon kike so ki dafa mana, kawai se inje da kwano ince a baki tuwo se kace bana baki Abinci, naga ma dai ba shiri kike da maƙotan nan ba, kawai se inje in fara roƙon Abinci"
"Dan Allah Yaya Ammar, ita wannan da zaka karɓo min a gurin ta ba irin su bace, niko loma ɗaya ta bani"
Ammar ya fara ƙuluwa, haushi ya cika shi yaja babur ɗinsa yai waje ya barta a gurin, ɗaki Mufeeda ta koma tana kuka ji take kamar taci babu, ji take inba tuwon nan ba ba zata iya cin komai ba.

*****************

Ammar yana tashi gidan Aminu ya fara zuwa suka tafi Asibitin tare, bayan sun gaisa Ammar yace  "Aminu wai dan Allah meyafaru ne? Jiya hankali na ya tashi sosai da abunda ka faɗa, kuma Mufeeda taji gaba ɗaya ta birki cemin da koke koke"

Aminu yace  "Hmm Ammar ni nama rasa ta inda zan fara, wallahi duk Faɗan da muka yi wa Jabir sam baya ji, Jinin ta ne ya hau taita Jijjiga. jiya dai har na baro Asibitin likitocin basu ce komai ba, yanzu da Safen nan kuma na kira shi bata shiga"

Ammar yace "Allah ya kyauta, bari muje muji"

Koda suka je Asibiti suka tarar da Jabir a zaune a reception duk yayi wani iri, suka gaisa suka yi masa yame jiki?.

Ammar yace "Jabir wai ya akayi haka ta faru meyasa meta ne?"

Jabir yace  "Wallahi da zan fita ne ta cemin kanta na ciwo, na ɗauka kawai rakine irin nata shiyasa ban kula ba na fita, kawai ina komawa gida na tara da duk jikin ta jini"

Wata Nurse dake reception ɗin tana cike files ta ɗago ta kalle su tace  "Eh ai da yake ba 'yarka bace dole kace haka mana, kudinga girmama larurar mace me ciki koda kuwa tana da raki, da yake cikin ba' a jikinka ba yake ba dole kace tana da raki ai, ai gashi nan ta kusa rasa ranta, ko Awo bata zuwa ga jinin ta yayi mummunan hawa, bata shan magunguna da'ake rubutawa masu ciki, dan Allah ku dinga girmama larurar mata masu juna biyu komai ƙanƙantar ta ko kuma buƙatun su"

Aminu yace  "Ayi haƙuri ranki ya daɗe yanzu wani hali take ciki?"

Nurse ɗin tace  "ku jira likitan safe yazo tukuna, Amma tana ICU kuma a rubutun da likitoci suka yi a file ɗin ta, Jinin ta ya hau batasan ma waye a akanta ba sakamakon jijjigar da tayi, an rubuta muku hoton ƙwaƙwalwa zakuje ku biya, masu kula da ɓangaren zasu zo suyi mata, sannan likitoci zasu ranar daza'ayi mata aiki, dan ba zata iya haihuwa da kanta ba"

Aminu yace  "Jabir kayi wauta wallahi, bekamata ace haka ta faru da Saima saboda kai ba"

Ajiyar zuciya Jabir yayi ya kasa cewa komai, haka suka dinga sintiri zuwa wajen biyan kuɗaɗe da'aka nema, 'yan dubiya suka dinga zuwa amma babu damar ganin Saima saboda tana ƙarƙashin kulawa ta musamman.

*******************

Rashin samun tuwon nan ba ƙaramin ɓatawa Mufeeda rai yayi ba dan seda tayi kuka tukuna, kuma taƙi cin komai ita kanta wannan abubuwan suna damun ta sosai, ga tunanin ko wane hali Saima take ciki daya dame ta, waya ta ɗakko ta kira layin Ammar, kafin ta tsinke ya ɗaga yasa a kunnen sa
"Yaya Ammar ya jikin Anty Saiman"
Ammar yace  "Jikin ta da sauƙi Alhamdilillah, dan yanzu haka ma bacci take"
Ajiyar zuciya Mufeeda tayi tace  "Masha Allah, Allah ya bata lafiya"
"Ameen, nima yanzu nake sa ran in taho, me zan taho miki dashi"
Zumɓura baki tayi kamar yana kallon ta tace  "Ni bana san komai, dama dana samu tuwon nan ne da se inci, tunda ban samu ba na sha ruwa kawai"

"Ke wato tunda na fito baki ci Abinci bako? Keba kya tausayin kanki"

"Nima ban san me yasa nake haka ba, Amma ni wallahi tuwon nan nake so"

"to ni karkiyi min kuka, ko tea ki haɗa Kisha, zan san yadda za'ayi kafin in dawo"

Ammar ya dage yana rarrashi a waya, gaba ɗaya ya manta da Aminu a gurin, Aminu yace
"Kaga mijin ƙwaila an dage ana rarrashi da alama an gamu kenan?"
"Aka gamu dame?"
"Ban sani ba, gaskiya wannan ƙwailar she deserves to be saluted, Kai Ammar ka wani kwantar da murya kana rarrashi, kai da kace raino zakayi ya akai ka haɗa ta da raino kuma?"

Ɗan Murmushi Ammar yayi yace 
"ba zaka gane ba that girl is so funny and romantic, ban san yadda akai komai ya canza ba"
Dariya Sosai Aminu yake yana tsonakanarsa.
Suka ƙara yiwa Jabir jaje suka bar Asibitin.

******************

Maman Nur suna zaune suna tafe ita da Maman Amir suna hira suka je gurin Sa'idu me kayan miya, nan suka tsaya suna munafuncin nasu da suka saba, Munafuncin Maman Sadiq suke yi, wai mijin maman Sadiq ke son ƙanwar Maman Nur, ita maman Sadiw ɗin bata sani ba, ya saiwa ƙanwar Maman Nur wayar dubu tamanin ya bar maman Sadiq da wayar dubu uku me fasashshen screen, Nan Maman Nur ta dinga zuba tana faɗar irin hidimar da yake musu, Sa'idu se zigata yake, suna cikin hirar Hajara tazo yin cefane, ko kallon su ba tayi ba ta gama cefanen tayi gaba. Tana tafiya Sa'idu yace
"Wai ita wannan 'yar waye girman kai kamar matar me A daidaita sahu, kuma kamar ita kaɗai take zaune a gidan"

Maman Nur tace  "Nifa banga alamar tana da miji ba, kamar zaman kanta take"

Sa' idu yace  "zaman kanta take to se ku killace yaran ku, dan kar ƙarti su fara muku sintiri a layi"

Nan suka yi ta gulmace gulmacen su sannan suka tafi.

*****************

Fa'iza ta shirya ta tafi gidan su Ammar, tayi sa'a kuwa Umman tana nan, Umma na ganin tace
"Fa'iza yau kece a gari haka?"
"wallahi kuwa Umma, ina Halima ne?"
Umma tace "Halima ta tafi Makaranta"
Fa'iza tace
"Umma naje gidan Yaya Ammar fa"
"Allah sarki ya kika baro su? Mufeeda har ta gaji da mitar banje ba, ina jin kunyar zuwa gidan Ammar, bana son ka dinga zarya a gidan yara, karka takura musu"
Kwaɓe baki Fa'iza tayi tace  "Nifa Umma ƙara na kawo miki"
"to ƙarar wa kuma?"
"Ranar da naje gidan Yaya Ammar wallahi a waje ya barni wai Mufeeda tana bacci bazan shiga a tashe ta ba, wallahi a waje yaimin korar kare"
Shiru Umma tayi tace  "Ammar ɗin ne yayi miki haka?"
"Wallahi haka yayi min, ranar ma munje da daddare amma baki ga korar karen da yayi min ba, tunda Mufeeda ta nuna bata sona yake min wulaƙanci"
Shiru Umma tayi sannan tace  "Amma basu kyauta ba, kiyi haƙuri Insha Allah zan musu magana, Amma Mufeeda mutuniyar kirki ce"
"Hmm kudai take wa kirki ni ban san me nayi mata ba, kuma goyon bayan ta yake, yafi sonta akan mu 'yan uwansa"
Umma tace "Haka naji Jidda tana ƙorafi akai, Amma ni dai ba tayi min nagani ba, Amma Insha Allah zan masa magana, kiyi haƙuri"

"bakomai Umma na dai gaya miki ne dan kisan me' ake ciki"

Haka Fa'iza ta ci gaba da ɓata Mufeeda a gurin Umman Ammar, Sannan tai mata sallama ta tafi.

Ammar yana ta sauri ya koma gida, se kuma yayi tunanin bari yaje gida ko ze samu Umma tayi tuwo ta bashi ya kaiwa Mufeeda.
Sedai yana zuwa ya tarar kamar ran Umma a ɓace, Umma tace 
"Yawwa Ammar naji daɗin zuwan ka, dama ina son ganin ka"
Ammar yace  "to Umma Allah yasa lafiya"
"Ammar ɗazun nan Fa'iza ta bar gidan nan, ta kawomin ƙararka akan abunda kayi mata, tazo gidan ka amma kaƙi bari ta shiga gidan ka, wannan wane irin haline? Bekamata ka dinga fifita Matar ka akan 'yan uwanka ba, bance karkaso Matar ka ba amma dai ka kula da' yan uwan ka"

Ammar yaso yayi ƙoƙarin kare kansa, Amma wani abu daya koya a gurin Mufeeda shine, muddin lokacin da babba yake maka magana kayi ƙoƙarin yin magana da niyyar kare kanka, to hakan na iya tunzira mutum, dan haka Ammar yayi shiru Umma ta gama faɗan ta, sannan ya ɗago kai yace
"to Umma Allah ya baki haƙuri, Insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba"
Umma tace "Yawwa ina Mufeedan tana lafiya?"
Ammar yace  "lafiya ƙalau tana gaishe ki, bari in koma in Abba yazo kice ina gaishe shi"
"to tsaya ina da gyaɗa me gishiri da aka kawomin bari in baka ka kai mata, sannan ka gaya mata akuyar ta ta haifi yara uku"
Bece komai ba se shiru da yayi zuciyar sa na tafasa, yana tunanin wane hukunci zeyiwa Fa'iza ya huce

Ɓacin ran da Ammar ya tarar ya hana shi gayawa Umma batun tuwo da rashin lafiyar Saima ba, ya karɓi gyaɗa harda tsintsiyar laushi ya tafi.

Ransa a ɓace sosai ya fito daga gidan ze tafi, Halima ce ta dawo daga Islamiyya taga Ammar yana ƙoƙarin tafiya
"Yaya Ammar Ashe kazo? Ina Anty Mufeeda?"
"tana lafiya" Ammar ya bata amsa ya shige A daidaita sahunsa ya tafi. Halima tayi mamakin ganin Ammar ya fito daga gida ransa a haɗe haka, ta ƙarasa ta shiga gidan.

"Umma wai me kikayiwa Uncle ne? Na ganshi da zan shigo kamar ransa a ɓace"

"me kuwa zanyi masa? Na dai yi masa faɗa ne Fa'iza da Jidda suna yawan kawo ƙorafi akan yana fifita matarsa akan 'yan uwansa, kin san duk abunda Baki yayi yawa, ɗazuma
Fa' iza tazo ta kawomin ƙarar sa shine na ɗan Ja masa kunne dai shine yake fushi"

"Umma kenan kuma a ce duk yawan Family ɗin mu su biyu kawai yakewa haka? Sudai suna da wata manufa a ransu amma wallahi Yaya Ammar baya nuna banbanci, kuma ita Anty Jidda ina itama nata mijin se abunda take so yake yiwa 'yan uwan sa"

Umma tace  "to nidai ban zaɓi ɓangare ba kawai dai nayi masa magana ne"

****************

Fa' iza seda ta gama gantalin gidan ƙawaye sannan ta tafi gida, tana zuwa ta tarar da motar Faruk a ƙofar gidan su, tsaki tayi zata shiga gida Faruk ya fito da sauri yace 
"Ke kina ganina amma kika wani basar zaki wuce, lambar yarinyar nan fa ta dena shiga idan na na kira dole ki samo mana wata"

A fusace Fa'iza tace  "toni ina ruwana? Ba na gaya maka kowa yayi ta kansa ba, na gaji da shirirtar da kake babu wani kyakkyawan result, dan haka kowa yayi ta kansa"

"Ke kin isa mu fara abu tare yanzu ki zame, ai ta inda aka hau ta nan ake sauka, Yadda muka fara tare haka zamu ci gaba"

"Baza'a sauka ta inda aka hau ɗinba, dalla ja jiki ka bani guri in wuce, niko uban me ya kaini ma haɗa kai da kai tun farko oho"

Faruk yace  "Hmm wallahi baki isa ki zame ba, in ba haka ba in watsa komai"

"inka fasa shege ne kai, ka tsaya ka jira in nayi nasara na fidda ita daga gidan kaje  ta ƙare muku can, Amma a yanzu kowa yayi ta kansa"

"Ni kike gayawa haka?"

"An gayamaka waye kai? Banda banza wofi"

Tas, Faruk ya ɗauke ta da mari, kallon sa tayi idonta fal Hawaye tace  "Nika mara?"

"Na mareki ɗin, kin isa ki cemin banza wofi in ƙyale ki"

"Wallahi baka isa ba, zaka gane baka da wayo sena ɗaura maka sharrin da baka isa ka kwance ba, bunsuru me bin matan mutane kawai"

"inkin Fasa min sharrin keba 'yar halak bace, munafuka koma meye dawa mu keyi inba tare ba"

Hankalin mutane ne ya dawo kansu, mutane suka fara taruwa.

Fuuu Fa'iza ta shige cikin gida tana kuka, tana zuwa ba tayi tunanin komai ba ta gayawa Mahaifiyar ta cewar wani ne ya mareta a waje.

"Mari kuma? Waye ya marekin?"

"wani Faruk ne abokin Yaya Ammar"
Se kuma da ta faɗa tayi wani tunani.

Mahaifiyar ta tace  "lallai to ke me kika yi masa daze mareki akan me? To wallahi baze yuwu ba, bari Yayanki yazo gurin 'yan sanda zan kai ƙarar sa, ko kuma shi Ammar ɗin in nemeshi ya gayamin dalilin da yasa Abokin sa ya mareki"

Fa'iza tace  "A' a Umma ki ƙyaleshi kawai nasan matakin da zan ɗauka"

Umma tace "Saboda me zan ƙyale shi, baze yuwu ba"

**************
Ammar a zuciye ya koma gida, gaba ɗaya ransa a ɓace yake, Mufeeda tana ta jira Ammar ya dawo taji ya jikin Saima, Amma yanayin sa ya nuna mata ransa a ɓace yake.

Ya dire mata gyaɗa da tsintsiyar laushi, murmushi tayi tace "da gani ba tambaya wannan saƙon Umma ne, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi"
Shiru yayi be amsa ba se ƙara haɗe rai da yake yi
"Mijina ya na ganka a hakane? Kodai Jikin Anty Saiman ne?"
"A'a jikin ta da sauƙi"
"to kowani abun aka kuma cewa nayi?"
Kallon ta yayi kamar ya gaya mata kawai ya fasa yace  "A'a bakomai"
Ƙyaleshi Mufeeda tayi ta zubo masa Abinci, ya kalle ta yace  "A haka kika yi girkin?"
"Naji zan iyane shiyasa na girka maka"
Ammar yace  "ke kuma me kikaci?"
"bakomai amma ga Gyaɗa nan da Umma ta bani se inci, amma Allah yau da baka karɓo min tuwo ba seda nayi kuka"
Hararta yayi yace  "kawai se in ɗau kwano in tafi maƙota roƙon Abinci kamar Almajiri"
"Allah ya baka haƙuri, ci Abincin ka"
Haka ya maze ya ci Abincin sa, Amma ransa babu daɗi.
Sallar isha'i ma a gida yayi, Mufeeda tana lura dashi, ya kwanta a falo yayi shiru abubuwa da yawa suna damun sa a rai.
Mufeeda tazo ta zauna a kusa dashi, ta kwantar da kanta akan ƙirjinsa tace
"Abun so na, dukda nasan nayi yarinta daka gaya min abunda ke damunka amma ganin ka a wannan mood ɗin yana sani a damuwa"
Shafa gashin kanta yayi yace  "Waye yace miki ina cikin damuwa?"
"Hmm ai kallo ɗaya nake maka in san a wani yanayi kake, farinciki baƙin ciki ko makamancin hakan duk ina iya ganewa"
Ɗan murmushi yayi yace "kinmin wayo da yawa, ya akayi na bari duk kika gane ni haka?"
"Yaya Ammar gobe in Allah ya kaimu zaka kaini inga jikin Anty Saiman?"
"Ai ko kinje ba zaki ganta ba, likitoci ne kawai suke shiga inda take, amma insha Allah sunce gobe in Allah ya kaimu zuwa jibi idan jinin ta ya sauka za'a cire mata abunda ke cikin nata"
"to Allah ya raba su lafiya, Amma fa harna tsorata da haihuwa"
"Ai komai na Allah ne, kuma Insha Allah ina ta Addu'a ki rabu da cikin nan lafiya"

Ƙasa ya kuma yi da muryar sa yace "kefa Jaruma ce, tsoro ba naki bane tunda 'yar Jaririya dake  kike ɗauke da Jaririn Ammar a jikin ki" yai maganar ya shafa cikin nata da kaikace ko kayan ciki babu a ciki.

"Kaga cikani inje in kwanta inajin Bacci ne"
"zomuje ɗakina mu kwana a can, kinji ƙwailata"
Zaro ido tayi kaman zata yi kuka tace "taɓ gaskiya ni A'a wallahi"
"meyasa ba zaki ba?"
"Nifa Yarinya ce dan Allah ka ƙyaleni wallahi hanani bacci ka keyi"
Sosai ta bawa Ammar dariya,
"you are ready for it, that's why you choose marriage"
Zumɓura baki tayi tace "ba wani ni kawai dan ina sonka ne"
ɗaga ta yayi yana dariya tafi da ita ɗakin nasa.

***************

Da sassafe Ammar yana ta shirin fita Maman Fa'iza ta kira shi a waya, ya ɗauka itama mitar zata yi masa, dan haka ya amsa cike da basarwa bayan sun gaisa tace
"Ammar a cikin abokan ka wani ya mari Fa'iza waishi Faruk, yanzu hakan na kai maganar gurin 'yan sanda, dan Allah in ba zaka damu ba ƙarfe goma kaje police station ɗin ayi maganar"
Ammar yace  "gaskiya Anty kiyi haƙuri, kinga ina da aiki da yawa, ita tasan meya haɗo su kuje can ku warware abun a station ɗin" Ya katse wayarsa ya fice.

****************

Rana tayi sosai Mufeeda tana tsaka da wani bacci me daɗin gaske, dan kwanan nan Mufeeda tana fama da kasala da yawan bacci, tana cikin baccin taji ana hayaniya a waje kamar ana yaƙi a gigice ta miƙe ta saka hijjabi ta leƙa ƙofar gida, tana leƙawa taga su maman Nur ne suke ta Masifa suna faɗa a bakin layi, Maman Sadiq taje ta gayawa maman Amir cewar Mijin ta na soyayya da ƙanwar maman Nur, nan suka dinga tonewa juna Asiri, dambe ne ya kaure a tsakiyar layi aka yagawa Maman Nur riga ko vest babu a jikin ta aka danna kanta a kwata.
Da sauri Mufeeda ta mayar da ƙofarta ta rufe, ta koma cikin gida dan ita abun kunya ne a gareta a zo wucewa ace anganta tana kallo ana dambe a layi, gaba ɗaya matan layin nan suka firfito suka dinga tonawa juna asiri kuma wani abun in aka gangaro daga gurin Sa'idu me kayan miya magana ta fito.

Hajara ce ta fito itama jin Hayaniya tayi yawa, taje tana ƙoƙarin rabawa.
Maman Amir ta juyo kanta zata daka, Hajara tace "Wallahi kika taɓani sena karya ki gida biyar na bawa karnuka, nafiki rashin mutunci"
Maman Amir tace  "Aikin banza keda a gurin sa'idu me kayan miya ake bada labarin baki da miji zaman kanki kikeyi, karuwa kawai"

Hajara tace  "Yawwa dama irin wannan ranar nake jira da zaku taɓoni, zan nuna muku wace Hajara yau 'yan unguwar nan babu me rintsawa wallahi, zaku ga tsiya

Tofa!!!

Share please

Domin sharhi gyara ko shawara
Ayshercool
07063065680.✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨

( *Sai Mata* )

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

Please follow me on Wattpad, vote and Comment

ELEGANT ONLINE WRITER'S

     NOT EDITED   

         

              Page 27

Sun ɗauka Hajara ƙarya take, Maman Amir tace 
"ke ɗin banza ki hanamu bacci, uwarmu ce ke? Ko kuma halittar mu kikayi?"
Maman Nur kam gida ta shiga ta sako wasu kayan ta nufi gurin Sa'idu me kayan miya tana ruwan Ashar, Hajara tace "tunda kuka ce zaman kaina nake wallahi sena nuna muku zaman kaina nake, A bariki aka haifeni kuma a bariki na girma"
Gurin Sa'idu me kayan miya Hajara ta fara tafiya, tana zuwa ta tarar da wasu matan daya haɗawa munafunci suna ta zagin sa, ko a jikinsa yana siyarwa da wasu kayan miya ya maida su kamar wasu banzaye.
Hajara na zuwa tafara fatali da kayan miyar nasa, ya kalleta a fusace yace  "ke mahaukaciyar ina ce meye haka?"
"Mahaukaciyar gidan ubanka ce, kai ni zakayiwa munafunci, kace ina zaman kaina, baka da aiki se tara matan mutane suma jakuna su biye maka, kaita haɗa gulma kuna zagin mutane daga yau in ance ka sake ba zaka kuma ba"
Ta cigaba da fatali da kayan Sa'idau, nan aka saka wawa, har ɗan cinikin nasa na ranar, wannan matar tace yace kaza waccan ma haka guri ya hargitse da hayaniya.

Mufeeda kam Amai ne hana ta sakat, gashi cikin ta ba komai ga amai se taso mata yake, jin layin nasu yayi tsit ne yasa ta ɗauka sun watse dan haka tasa hijjabin ta, tafi ta ko guava ta samu ta siya.

Aikuwa tana fitowa bakin layi inda Sa'idu me kayan miya ke siyar da kayan miya ta tarar da mata sunyi dandazo a gurin, ga wasu kayan miyan na iyo a kwata, wasu an tattake.
mata sun sashi a tsakiya suna zagin sa tare da tsine masa har zata wuce Maman Nur tace 
"Yawwa Mufeeda gara da

Please Login or Register in order to submit comment