Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mufeeda ta kwana huɗu a Asibiti, likita ya tabbatar musu typhoid da malaria ke damun ta, da yake Asibitin kuɗi ne, kusan duk seda likitoci da Nurses ɗin Asibitin suka santa, kullum cikin kuka take, ko ya taji ciwo se kuka, idan Mama ta takura ta taci Abinci se ta hau kuka, idan akazo Allura kuwa ba ƙaramin dambe ake sha da ita ba, ga rashin son magani taɓara daban2 kafin a sallame su, Baba ne ke lallaɓa abarsa Mama kam kusan dukan ta take yi.

Aka sallame su da sauran magungunan su suka tafi gida, Alluran da akai mata suna da ƙarfi saboda ta sha wahala, dan haka tun kan suje gida take cewa bacci take ji, suna zuwa gida ɗakin ta fes mama ta gyara.

Bata fara neman komai ba se wayar ta, ta kunna tana sa ran ganin saƙon Ammar kona ya jiki ne amma bata ga komai ba.
Haushi ne ya kamata kaman ta sa kuka, ji tayi kan ta kaman ze cigaba da ciwo ba shiri ta ajiye wayar ta kwanta domin ta samu bacci.

Hausawa suka ce sabo turken wawa. A kwana huɗun nan Ammar ya fara tunanin anya yarinyar nan ba dagaske take bata da lafiya ba? Last seen ɗin ta tun lokacin da ta tura masa message ɗin nan, Zuciyar sa na ta gaya masa abubuwa daban2.


Yaya Fadila tazo gida domin sake duba Mufeeda, taje ta tarar tana bacci amma duk ta rame sosai, Fadeela tace  "lallai Autar Baba an sha jiki, duk ta rame"
Mama tace

"Aikam ta sha jiki, kuma ta ƙarawa kanta wahala dan bata shan magani, ai zaman jinyar nan tata ba ƙaramin ɓata min rai yayi ba, ta fiye rakin tsiya kaman ba mace ba shiyasa bana so tayi rashin lafiya"

Suna cikin hirar wayar Mufeeda ta fara ringing a gefen pillow ɗin Mufeeda, A hankali Fadeela tasa hannu ta ɗakko wayar.

My Yaya Ammar

shine akan screen ɗin, dariya Fadeela tayi tace
"Mama sirikinki ne fa ya kira"
Tsaki Mama tayi tace
"sirikin Dr. Dai"

Fadeela tai murmushi ta ɗaga wayar tayi sallama
Ammar ya amsa ba tare da wata doguwar magana ba yace

"Ina me wayar?" ba ƙaramin mamaki Fadeela tayi ba saboda abune mawuyaci ka banbance muryoyin su in ba ka zauna da dukan su ba, Amma sallama kawai tayi yasan ba Mufeeda bace, gashi cikin gadar yake magana, Fadeela tace

"bata da lafiya bacci take"

be kuma cewa komai ba ya kashe wayar sa.

Fadeela tace "Ikon Allah yau ni naga isa da izza, kinji yadda yake magana kuwa Mama?"

Mama tai tsaki tace
"Ai se taje taita yi yaron da ko damuwa beyi da ita ba tun ranar ɗaurin Auren Amina wata na biyu kenan ban ganshi a gidan nan ba, ko dubiya bezo ba ni na kasa gane kan wannan shirirtar, ga baban ku ya goya mata baya yace zece ya fito, ko lokacin da yazo gidan nan ko ɗan murmushi babu a fuskar sa da ganin sa zeyi masifa "

Fadeela tace
"Mama yadda auta take da rawar kai da shagwaba ta auri gayen nan zata sha wahala, a muryar sa zaki gane yana da izza da isa, kuma Mama ya mata girma kalle shi fa ki kalli ƙirar jikin sa, ita kuma kalli ɗan nata jikin wallahi mama kiyi wani abu akan lamarin nan, kar ku biye wa haukan ta"

Cikin damuwa Mama tace  "Fadeela ya zanyi nayi2 babanku ya gane amma yaƙi, ya goyi bayan ta yace yadda take sonsa ɗin nan idan bamu goya mata baya ba zata iya shiga wani halin, nayi rarrashin nayi nasihar amma ina kin santa da kafiya musamman idan baban ku ya goyi bayan ta akan abu"

Haka suka ci gaba da tattaunawa akan lamarin.

Se kusan la'asar Mufeeda ta tashi daga baccin, tayi wanka ta ɗanci Abinci shima seda suka haura da Mama.

Fadeela tace "professor Auta wannan gardin ya kira ki fa"

A ya tsine Mufeeda ta kalli Fadeela "Waye kuma gardi?"

"Wannan Saurayin naki me fuskar shanu, wanda yazo bikin Amina"

Da farko Mufeeda bata yadda ba, ta harari Fadeela tace
"Mama ki gayawa Yaya Fadeela babu ruwan ta dani karta ƙara cewa Ammar ɗina gardi, sedai mijinki ne gardi"

Fadeela tace "Ashe har da zuwa ki ga yawa Baba ke Aure kike so ko? Hmm yarinya  ba dai Aure ba? ba zaki gane ba yanzu"

Share fadila tayi ta koma ɗakin ta, ta ɗakko wayar ta, da mamakin ta tana duba call log sega kiran Ammar, tsalle Mufeeda ta dinga yi a ɗaki tana murna.
Ta nemi guri ta zauna tana tunanin ko ta kira shi? Se kuma ta fasa tace se dare tasan maybe yanzu yana aiki.


Se bayan sallar isha'i kusan tara da rabi na dare sannan ta ɗakko wayar ta ta kira Ammar, Amma abun haushi be ɗaga ba, missed call biyu tayi masa amma ne ɗaga ba.
Haushi ne ya kamata ta ajiye wayar a gefen ta ta kwanta tana zumɓura baki kaman tana gaban sa.

Bacci ne ya fara ɗaukar ta, cikin baccin ta ji wayar ta na vibrating, Ammar ne seda ta saki murmushi sannan ta ɗaga wayar tasa a kunnenta sallama yayi mata
Seda ta ƙara ƙasa da muryar ta sosai kaman tana jin jiki sannan ta amsa masa Sallamar

  (tafa warke har faɗa suka kusa yi da Yaya Fadeela ɗazu saboda an ce masa gardi amma ya kira ta noƙe murya kaman yanzu take jin rashin lafiyar 🙄🙄🙄)

"Na kira ɗazu kina bacci ya jiki?"

Seda ta ƙara ƙasa da murya cikin shagwaba da wata irin sassanyar murya tace
"Ni banji sauƙi ba bani da lafiya har yanzu, banji sauƙi ba ji nake kaman zan mutu, Yaya Ammar ba zaka zo ka duba ni ba?"

Kaman an masa dole yace "meya same ki?"

"komai ma ya dameni zazzabi nake sosai, kwana na huɗu a Asibiti, dan Allah Yaya Ammar kazo in ganka kar in mutu bamu haɗu ba please"

Ji yayi gaba ɗaya wata kasala ta saukar masa yanayin yadda auta ke magana, seda ya numfasa sannan yace

"zuwana baze hana rashin lafiyar ki ba, sedai zan miki Addu'a Allah ya baki lafiya"

Kawai ta saka kuka babban abunda Ammar ya tsana a rayuwar sa kenan kuka
"nidai dan Allah kazo, idan na ganka zanji sauƙi, in kazo dubani zaka samu ladan gaida mara lafiya, kai na fara gayawa bani da lafiya amma bazaka zo ka dubani ba ko? Shikenan nagode dama ni na damu da kai in na mutu Baba ne kawai ze kewa ta"

Ta ajiye wayar ta ci gaba da kukan ta, da yake bata katse kiran ba Ammar yana jin sheshsheƙar kukan ta.

Katse kiran yayi tare da dafe kai yace "Ohh My God"

Mufeeda kam ta sha kuka, da surutai
"nikam wace irin ƙaddara ce na kama son wanda be damu da niba, Ni dama haka son yake? Wayyo Allah na"
Ji tai kanta ya fara nauyi dan haka ta lumshe idon ta tana jiran bacci ya ɗauke ta.


Ammar ya rasa yadda zeyi, haka nan idan ya tuna kukan da Mufeeda take a waya se yaji idan be je ya duba ta ba kaman be kyauta ba, Amma a matsayin wa zeje dubiyar? Baya son tambayar su Jabir shawara yanzu zasu raina masa hankali, dan haka kawai ya share.


Mama ta lura kaman jikin mufeeda ya dawo, dan wuni tayi a kwance ko Abinci ta kasa ci se complaint take da kanta.
Da ƙyar ta samu tayi sallar magariba shima a zaune tayi saboda ciwon kan da take ji sosai.

Yaro ne ya shigo yai Sallama ya tarar da Mama a tsakar gida ya gaishe ta da yake ɗan maƙotan su ne, yaron yace
"Wai Mufeeda taje inji Ammar"

Mama ta taɓe baki kaman tace baza ta zo ba, Amma ta fasa tace "kace tana zuwa"

Mufeeda kuwa dukda tana fama da kanta tana jin jiri amma haka ta miƙe ta ɗauki ɗankwalin Abayar ta ta yafa ta fito waje
Mama ta kalleta tace "yau naga tsiya kekina fama da kanki amma shine har kin fito, kai Allah yayi miki magani"

Mufeeda ba tace komai ba ta shiga ɗakin Mama ta ɗakko Babbar Dadduma tai waje abun ta, zuciyar ta cike da farinciki da ɗokin ganin Ammar.

A jikin gate ɗin su ta tsaya ta na kallo shi daga inda yake tsaye opposite ɗin gate ɗin yana danna wayarsa, ita dai a duk lokacin da ta ganshi ƙara yi mata kyau yake da kwarjini.

Ta tura masa message

"Ka shigo gareji, Yanzu Baba ze dawo, ya ganni a waje ze min faɗa"

Ɗaga kansa yayi ya hango ta, ya taka a hankali ya shiga gate ɗin gidan su, har ta shimfiɗa daddumar ta zauna, da yake da wuta ko ina da haske. kana kallon ta zaka gane bata da lafiya, dan ta rame sosai ta ƙara haske.

Ƙamshin turaren sa ya kashe mata jiki tare da ƙara masa kwarjini a idon ta gaba ɗaya ta kasa ɗaga kai ta kalle shi ta sunkuyar da kanta ƙasa.

Sema da ya zauna akan daddumar ya zama na yana daf da ita, suna jin Ƙamshin turaren juna, taji gaba ɗaya kamar yau ta fara ganin sa.
kaman kullum yauma fuskar sa babu wata fara'a

A hankali tace "ina wuni?"
Ya kalle ta yace "lafiya Ashe ma kin warke?"

Ai kaman ya taɓa mata inda yake mata ƙaiƙayi ta tura baki kawai ta fara share hawaye.

Ya tsuke fuska yace
"Meye kuma abun kukan? Kince inzo in duba ki nazo kuma seki dinga min kuka? Wannan se ace wani abun nayi miki ai" yai maganar in very serious tone

Maimakon ta shiga taitayin ta sema wasu hawayen dake kuma bin fuskarta wannan karon hadda sauti, cikin shagwaba ta fara magana

"Ni wallahi ban warke ba, ko sauƙi banji ba, yau ma a kwance na wuni, Yanzu Yaya Ammar ba dan na roƙe ka ba ba zaka zo ka duba ni ba ko? Cikin dare rashin lafiya ta kamani ba wanda ya sani kai na fara gayawa a sume aka kaini Asibiti, Amma kaƙi zuwa duba ni, ni ka tsane ni kuma ban san me nayi maka ba"

Ta ci gaba da kukan ta cike da shagwaɓa kaman wata 'yar yarinya ƙarama hawaye wani na bin wani.

Ammar yai ƙarfin halin cewa "look ko ki dena wannan kukan, ko kuma in tashi in tafi"

"to zan dena"

"ba cewa zakiyi zaki dena ba, kidena kawai, goge wannan hawayen"

Ta ɗan lumshe ido sannan tace "Niba handkerchief a gurina sedai ka bani naka in goge"

Kallon ta yayi galala ya haɗe rai yace "goge da mayafin ki"
Noƙe kafaɗa tayi
"A'a ni da handkerchief ɗin ka nake so zan goge, nasan yana Ƙamshin turaren ka"

"naga Alamar kin warke, Allah ya ƙara afuwa" yai maganar yana ƙoƙarin miƙewa

Ta kwantar da kai tare da kwantar da murya tace "dan Allah da manzon sa karka tafi yanzu"

"Ni wannan abubuwan da kike ne bana so, shi yasa bana son zuwa inda kike, ina sauri ne ana jira na ai nazo na duba ki"

"Yanzu tafiya za ka yi?"

Shiru yayi mata ya durƙusa ya ɗau mukullin babur ɗin sa da wayar sa, ya tsaya yana gyara links ɗin hannun rigar sa itama ta miƙe tsaye, Amma abunka da mara lafiya jiki ba ƙwari tana tashi taga duhu a idon ta duniyar tana juya mata, dafe kanta tayi data ji ya sara mata.
Yuuuuu ta tafi zata faɗi, Cikin zafin nama Ammar ya riƙo ta.

Da ƙarfi zuciyar Ammar ta buga, gaba ɗaya jikin sa yayi sanyi, be taɓa riƙe macen da ba maharramarsa ba yana sane se yanzu, jikin ta rau yake da Zazzabi me zafin gaske.

"Wash Allah kaina ze fashe"

Tsoro da fargaba ne suka kama Ammar, kar wani yazo ya ganta a jikin sa, ga kuma jikin ta zafin daya ɗauka.
Jingina ta yayi a jikin bango yace "zaki iya tafiya ko inyi magana cikin gida a zo a shiga dake?"
Girgiza masa kai tayi tace
"na rage jin jirin zan iya shiga gida da kaina"
"Sannu ɗan ƙara hutawa seki shiga"
Ta jinjina masa kai



Baba ne ya dawo ya tarar da Ammar yana shirin tafiya, mufeeda kuma zata koma cikin gida, Ammar ya tsaya ya gaida Baba, yai masa ya me jiki.

Baba ya amsa masa cikin mutunci ya kalli Mufeeda yace "Auta na ya jikin naki"
"Da sauƙi Baba"
"Masha Allah" Baba ya dawo da kallon sa kan Ammar yace
"Ammar ko?"
Ammar ya jinjina kai yace "Eh hakane"
Baba yace "Yawwa dama ina son ganin ka, biyo ni"

Galala Ammar yayi yana fatan "Allah yasa ba riƙe Mufeeda da yayi ya gani ba yai zafon wani abun"

Murmushi Mufeeda tayi tare da yin gaba abunta ba tare da ta kuma waiwayo ba



More Comments More typing

Domin sharhi, gyara ko shawara
Ayshercool
07063065680
✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''






Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]



*ELEGANT ONLINE WTITERS*




                            Page 5

Cikin gida mufeeda ta koma tana me farinciki tare da roƙon Allah yasa Ammar ya amince.

Har falon Baba Ammar ya shiga suka ƙara gaisawa da baba, Baba ya dube shi yace
"Ammar a wace unguwa kake sannan menene sana'ar ka?"
Ammar yaji gaban sa ya fadi tare da mamakin wannan tambayar amma ya dake ya bawa Baba amsar tambayar sa, Baba ya cigaba da yi masa tambayoyi game da shi yana bashi amsa.

Baba ya nisa yaxe "to dama abunda yasa na kira ka kuna nayi maka wanna tambayoyi ba komai bane face auta tazo ta sameni da maganar ka,  kuma yanayi ya nunamin kanada hankali da nutsuwa, to nidai gaskiya mutum me son abunda yaran sa suke so matuƙar be saɓawa shari'a ba, da farko Auta karatu take sonyi amma katsam ta sauya tunani, kuma bana tauye abunda yarona yake so ince lallai se yabi nawa abunda nake so, tunda harta furta ta zabi Aure akan karatu nace bari inyi maka magana idan ka shirya ka turo magabatanka, ina so abun ya zamana anyi shi anan kusa, sedai ina son bayan auren ka barta ta ci gaba da karatun ta"

Ras! Ras!! Ras!!! Gaban Ammar ya faɗi, ya ɗago ya kalli mahaifin Mufeeda da nufin ya sanar da shi shi babu wata alaƙa ta soyayya a tsakanin sa da Mufeeda, Amma ya ga dattijon ya masa matuƙar kwarjinin da baze iya kallon sa ya gaya masa hakan ba, nan da nan gumi ya dinga tsatstsafo masa ta ko ina.

"baka ce komai ba"

"To Baba nagode insha Allah zanyi magana da magabata na"

Baba yace  "yayi kyau, Allah ya Sanya Alkhairi a tsakanin ku"

Da ƙyar Ammar ya baro gidan nan zuciyar sa na bugun uku uku, shi dai gaskiyar magana Mufeeda tayi masa ƙanƙanta a aure, ta ina zeyi zaman Aure da wannan jaririyar yarinyar? Shi sam babu wani abu makamancin son ta da yake ji a ransa, shi be taɓa jin yana son wata ba balle yace ga yadda akeji, ita kanta budurwar sa zainab bawai dan yana jin yana sonta yake niyyar auren ta ba, se dan tana da irin shekarun da yake son mace ta kai kafin ya aure ta, gashi tsoron sa da take ji da kwarjinin sa baya bata damar nuna masa soyayya, dan sam Ammar kallon shiririta yake wa wannan abubuwan na soyayya.

Allah ne ya kai Ammar gida lafiya, ba dan yasan a yadda yake tuƙin ba.
Yana zuwa gida ba wanda ya kula ya shige ɗakinsa ya rufe ƙofa ya samu guri ya zauna yayi shiru

"Waima yaushe nace wa yarinyar nan ina sonta da har za tayi min haka?"

Wayarsa ya lalubo a fusace ya nemo lambar ta ya danna kira.
Tana daga kwance ta janyo wayar tasa a kunnen ta, ai tana ɗagawa Ammar ya fara masifa

"ubanwa yace miki ina sonki? Me yasa zaki je ki gayawa mahaifinki ni kike so? Ni sa'anki ne ko sa'an Auren ki ne ni? Kina jarirya da ke har kin san wani menene aure wata ƙwaila da ke, ni bani da ra'ayin auren ƙwailar mace mara aji kamar ki dan haka tun wuri ki koma ki gayawa mahaifinki kin fasa"

Sosai Mufeeda taji zafin maganganun Da Ammar ya gaya mata, jaririya! Ƙwaila! Mara aji! Dakewa tayi ta kwantar da murya tace

"Wash Allah kaina, har yanzu fa ban warke ba yaya Ammar a kwance nake, ka bari idan na warke seka gayamin abunda kake son gayamin, idan kuma na mutu shikenan ka huta"

Jikin sa ne kuma yayi sanyi, dan ya manta ɗazu a yanayin da ya barta, tsaki yayi ya katse kiran ta ajiye wayar tace

"hmm Ammar kenan wannan izzar da ta kemin ɗawainiya da kai sena sauke maka ita, nice Jaririya kuma ƙwaila sena nuna maka WATA KISSAR.. Se Mata, zaka ga ƙwaila ganin idon ka"

Ta gyara kwanciyar ta, ta kwanta ta ja bargo ta rufe jikin ta.

******************

Kusan kwana uku Ammar ya kasa gayawa kowa abunda ke faruwa duk a takure yake ya rasa meke masa daɗi

Yau Da safe Ammar ya tashi sam babu walwala ya shiga ya gaida Umman sa fuskar sa a haɗe alamar bayan rashin fara'a akwai damuwa a tare da shi.

Halima ta kawo masa kayan karin kumallo ya zauna ya ɗan cakali kaɗan ya miƙe ze fita, umman sa tace
"Ammar zauna za muyi magana" ba musu ya nemi guri ya zauna

"Ammar me yake damunka ne? Kwana biyu naga sam baka walwala, ko Abincin kirki baka ci, gayamin meke faruwa ne?"

Kaman ya ƙi gaya mata, amma yaga idan yai shiru be gayawa mahaifiyar sa ba waze gayawa?
Dan haka ya zauna ya warware mata komai tunda ga hɗuwar sa da Mufeeda zuwa yau, murmushi tayi tace

"Masha Allah a ina ne gidan su yarinyar? "

Ammar yace "Umma ba fa sonta nake ba, yarinya ce me ƙarancin shekaru da rawar kai, tayi min yarinta da yawa ni bazan iya auren ta ba"

Umma tace
"kaga dakata, ai Addini be hana aure tsakanin ku ba, kuma ƙarancin shekaru ba'a nan zaman aure yake ba, dan haka zamu ci gaba da Addu'a, dan dama na gaji da yawan saɓani da kake samu da mahaifin ka akan rashin auren nan"

Ammar yace "haba Umma kinfi kowa sanin bana son in auri yarinya tazo ta dingamin hauka, ta rainani yarinyar nan da kaɗan tafi yayayyiya fa, nifa bana son auren yarinya ƙarama tazo ta dingamin shirme"

Kallon sa Umma tayi tare da yin murmushi tace  "yaro man kaza, kana raina ta kana ce mata jaririya se kaga jaririyar ta baka mamaki, ai duk mace mace ce komai ƙanƙantarta, da kasan baka sonta ai tun a lokacin seka gayawa mahaifin ta, ko kuwa se yanzu daka Gaya masa unguwar da kake da gidan ku sannan zaka ce baka son ta in kayi haka baka kyauta ba"

"Umma ni dai dan Allah ki sama mun mafita amma gaskiya bana son ta"

Umma tace "karka kuma cewa baka son ta, ko da wasa karka kuskura ka kalli idon mutumin da yace yana sonka ka gaya masa baka sonsa, ba'a haka kaima Allah ze iya jarabtar ka wataran, tashi kaje seka dawo ma cigaba da maganar"

Umma ta sallami Ammar ya tashi ya tafi yana ƙara zullumi da tunanin wannan lamari a ransa.

Da magariba Ammar ya dawo gida dan yana jin yunwa, bayan yaci Abincin dare, yai sallar isha'i a gida, dan ya rasa jam'i, kuma yana son ya ɗan zaga ya ɗau fasinjan dare, ya gama abunda zeyi ze fita Baban sa ya shigo ya tsaya ya gaida Abban sa, ya kalle shi yace
"fita zaka kuma yine Ammar?"

"Eh Abba zani na ɗan zaga in samu fasinjan dare"

Abba yace "ɗan tsaya kafin ka fita ɗakko min tabarma a ɗaki"
Ammar yaje ya ɗakko tabarma ya shimfiɗa wa Abban sa ya zauna.
Abba yace "kaima zauna"

Ammar ya cire takalmansa ya samu guri ya zauna

Abba ya kalle shi yace

"Ammar mahaifiyarka tayi min bayanin abunda yake faruwa, ance ka fito, nayi farinciki da jin hakan ƙwarai, yanzu abunda nake so da kai zuwa rana ita yau kaje banki ka ɗakko abunda ya samu da kake tarawa zanyi wa kawunka magana, Insha Allah zamuje akai maka kuɗin Aure"

Ƙuuuuuu cikin Ammar ya bada wata irin ƙara ya kalli mahaifin sa yace  "Abba wallahi ba sonta nake ba"

Abba yace "mu muna son ta, aini duk wanda yake ƙaunar ku Ammar nima ina ƙaunar sa"

"Abba wallahi yarinya ce sosai, bata fi ayi rainon ta ba"

"Ammar duk yarinyar data nuna tana sonka a yadda kake ɗin nan, ga fushi da saurin zuciya ga jinkai, kai ba kuɗi ba kai ba mulki ba amma tace tana sonka, harta ga yawa mahaifin ta a irin yadda da yawan 'yan matan zamanin nan masu son abun duniya tace taji ta gani tana sonka, wallahi Ammar ka bari yarinyar nan ta suɓuce maka zakayi babbar asara, ina me tabbatar maka zata iya zama da kai a halin akwai ko babu"

"Abba ya za' ayi in zauna da macen da bana so, kuma fa akwai wadda nake zuwa gurin ta fa"

"Ammar ni tunda muke baka taɓa cemin kana da wadda kake zuwa gurin ta ba, dan haka kayi haƙuri Allah yasa haka shine mafi alkhairi"

Gaba ɗaya Ammar be taɓa tunanin abubuwa zasu hargitse masa haka ba, wannan wace irin jaraba ce, daga haɗuwa da yarinya ta zame masa gum
(glue inji bebi 😂) shi sam beta ɓa kawo batun aure a nan kusa ba mussman auren ƙaramar yarinya amma lokaci ɗaya al'amura na ƙoƙarin sauya masa.

*******************

Kwana biyu Mufeeda ta warware harta koma makaranta, Baba be gayawa Mufeeda yadda suka yi da Ammar ba, Sannan ya yanke shawarar a aji biyar na sikandire Mufeeda zata zana jarrabawar kammala sikandire ya aurar da ita.

Ammar be kuma bi takan ya jikin Mufeeda ba, itakam mufeeda addu'a take idan Auren Amma ze zame mata alkhairi Allah ya tabattar idan kuna babu alkhairi Allah ya zaɓa mata mafi Alkhairi amma tabbas zuciyar ta na matukar son Ammar.

Sati ya zagayo cif Ammar be kuma yiwa mahaifin sa batun maganar kai kuɗi ba, ranar kwana na goma da maganar, Ammar yana kwance yana bacci da safe Abba yazo yana buga masa ƙofa, da sauri Ammar ya tashi yazo ya buɗe ƙofar.

Abba yace "Ammar idan kai baka gudun magana toni baza ka maidani ƙaramin mutum ba, ka amsawa mutane zaka tura magabatanka yau kwana goma dayi maka maganar ka kawo abunda yake hannun ka amma kayi biris dani, ban isa in gaya maka magana kaji ba ko Ammar?"

"Abba bahaka bane, nifa kuɗin da nake da su basu fi dubu talatin ba, kuma ni...

Abba ya katse shi ta hanyar cewa
"Sa kayanka kaje ka ciro su ni akwai dubu ashirin a gurina, gobe insha Allah zamuje mu kai"

"Amma Abba kaga"

"nagama magana Ammar, in na isa da kai kayi abunda nace in ban isa ba kuma shikenan"

Abba ya juya ya fice, Ammar ya zauna akan katifarsa ya dafe kai.

Ya fara tunanin Anya aka kai dubu hamsin baza su raina ba? Mahaifin Mufeeda yana da rufin Asiri kuma yayyen ta suna auran masu kuɗi anya baza'a wulaƙanta shiba, dan shi babban abunda ya tsana kenan a rayuwar sa wulaƙanci, waima yanzu ba abun kunya bane ace kaman shi da shekarunsa ya gama cika baki amma ya auri Mufeeda, yasan Idan ya auri Mufeeda dashi da wanda bashi da aure duk ɗaya dan wannan yarinyar bata isa komai a gurin sa ba.

A fili yace "Allah yasa su raina kuɗin suce baza su karɓa ba"

Hakanan jiki babu ƙwari ya miƙe ya tafi banki ya ciro kuɗi.

***************

Mufeeda ta dawo daga makarantar boko a matuƙar gajiye, data dawo tayi mamakin ganin Mahaifinta a gida a wannan lokacin, taci Abinci tai shirin ta tsaf ta tafi Islamiyya.

Bayan ta dawo da daddare Baban ta yasa akai

Please Login or Register in order to submit comment