Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hangen me kuɗi ne to bazan kalle ka ba, amma zuciya ta ta makance kai kaɗai nake gani, ni kaina ina ganin kaman na fiye zaƙewa, jiya da nake chatting daka tsaya munyi waya zanji daɗi a raina ɓacin ran abunda kamin da tunanin wane irin mutum Allah ya haɗa ni dashi zamuyi zaman aure ya hanani bacci na ɓige da chatting muna shirye2 biki da ƙawaye na, yanzu kuma ɗinki na kai unguwar su Anty murja ina tsoron hanya shiyasa mijin ta ya dawo dani gida, mahaifina mutum ne me matuƙar tsauri akan tarbiyya baze taɓa bari na inje unguwa inyi dare a kawoni a mota ba, kuma mijin yaya Aminar ma akwai ɗanta da yayi mana rakiya, Amma Allah ya baka haƙuri Allah ya huci zuciyar ka insha Allah zan kiyaye faruwar hakan a gaba"

Ta juya zata tafi ya kira sunan ta
"Mufeeda" banza tayi masa ta ƙara sauri hawaye na bin idon ta tana jinsa taƙi ko waiwayowa tayi gaba abunta.


Gaba ɗaya se jikin Ammar yayi sanyi tare da tunanin meyasa yayi mata faɗa haka gashi ya sata kuka
(🙄🙄🙄)





Kuma inba comment zan ajiye typing ɗin littafin nan
Domin sharhi, gyara ko shawara
Ayshercool
07063065680

[23/06, 10:48 PM] Ayshercool: ✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

     

ELEGANT ONLINE WRITER'S

             

                      Page 8




Ammar bashi da zaɓin daya wuce ya tafi, a zuciyar sa yana jin kaman be kyauta ba abunda yayiwa Mufeeda.

Ita kam data koma gida seda ta sha kuka tayi ya ishe ta sannan ta hau Addu'a "ya Allah kai ka jarabceni da son wannan bawan naka Allah ka kawomin mafita"

Seda ta idar da addu'ar ta ɗakko wayar ta, ta buɗe hoton Ammar ta ƙura masa ido sannan tace

"Yaya Ammar kenan faɗan kawai ka iya amma sam bazaka yi wahalar sarrafawa ba, kace baka iya soyayya ba amma ina ganin kishina ƙarara a idonka, ba a kishi idan babu soyayya, se ƙwaila ta baka mamaki"

Ammar yaji ya fara damuwa da abunda ya aikata tsaki yayi yace "toni ina ruwana ma meye zan damu kaina akan wannan ƙaramar yarinyar"

Shirye2 se nisa suke lokaci na ƙaratowa, ba tare da Ammar da Mufeeda sun samu wata kyakywar fahimtar juna ba.

Mufeeda ta shareshi ta dena kulashi, tana kallon sa online amma ba zata kula shi ba saƙonnin ma ta dena tura masa.

Dukda can ƙasar zuciyar sa seya dinga jin zafin shareshin nan da tayi amma shima ya ƙyaleta.

Mufeeda ta maida hankali akan Neco exams ɗin ta, duk ta ƙara ramewa ga pressure ɗin exams ga na shirye2 biki dukda tana ta shan gyara ta ƙara kyau hakan be hana ramar da tayi fitowa ba.

Tana kwance tana chatting tana kallon Ammar online taƙi kulashi ya turo mata saƙo

  "ki gayawa su Baba ranar Asabar insha Allah za'a kawo kayan lefe"

Zumbur ta miƙe zaune tana ƙara juya saƙon, maimakon taje ta gayawa Mama seda ta kira Yaya Amina ta fara gaya mata suka yi ta murna tare sannan taje ta sanar da Mama, Mama tace "to Allah ya kaimu"

Sam bata nuna ma taga saƙon ba balle tayi wa Ammar replying.

Mama tayi shirye2 tarbar masu kawo lefen aka yi sa'a mazane suka kawo, Akwatuna uku da kida ƙaramin buhun shinkafa da bagcco na takalma, aka basu tukuici suka ce ba zasu karɓa ba.


Mama tayi mamakin kayan da'aka zubowa Auta, dukda ko kaɗan basu kama ƙafar wanda aka kawowa 'yan uwan ta ba, amma ba laifi yayi ƙoƙari a matsayin sa name ƙaramin ƙarfi yayi ƙoƙari dan kayan ta ba masu arha bane.


Ammar shikaɗaine namiji gidan su, yayyen sa uku mata se biyu ƙannensa, suna ta tsokanar sa "Bana Allah yayi, Allah ze yaye masa gwauran taka, Allah yayi an samu wadda tayi nasarar shiga ran 'yan mazan umma" jinsu kawi yake yi, dan shi be ɗau wannan auren nasa wanu auren kirki ba kawai dai sunan zeyi aure ne.


Labari ya ishe  budurwar sa a da wato zainab wai Ammar zeyi Aure, ta shiga tashin hankali da damuwa dan ba ƙaramin so take masa ba dukda tana masifar tsoron sa saboda zafin kansa da izzarsa, amma tana matuƙar son Ammar, kasa jurewa tayi ta ɗau waya ta kira shi.

Akayi sa'a yana gida dan ya gama cin Abincin rana kenan ta kira shi bayan sun gama gaisawa tace
"Ammar dagaske aure zakayi?"

Ammar sam be san wani abu rarrashin mace ba se kace ba cikin mata ya taso ba dan haka yace mata "Eh aure zanyi, nima auren ne yazomin ba shiri Allah ya kawo auren"

"Amma Ammar duk son da nake maka, na sakankance sekamin haka"

"ke nima fa auren nan ba wai da son raina zanyi shi ba, kawai dai Allah ya nufi zanyi ne, ba yadda zanyi"

"Ammar bakamin adalci ba, ina nan na sakankance kawai se inji labarin zakayi aure, kuma ma wai ƙara mar yarinya, bayan ka gama cemin kai ba zaka auri yadinya ƙarama ba ashe dama duk yaudara ta kake yi?"

Ajiye wayar Ammar yayi dan bashi da lokacin cigaba da sauraren ta tana ɓata masa rai, ya gaya mata gaskiya amma tana ƙoƙarin kaishi bango.


Zainab ta taɓa aure shekarar ta biyu suka rabu da mijin, maƙwabciyar yayarsa ce Jidda, acan suka fara haɗuwa ta nuna tana sonsa, Jidda ta ƙara haɗasu ta ƙarfafa abun, shi dai Ammar kawai yayi niyyar auren Zainab ne saboda tana da shekaru a ganin sa itace tasan meye zaman aure, yanzu ma da aka kai kayan lefen nan Yayar sa Jidda se kushe abun take yi saboda yaƙi auren Zainab, dan ita zainab take so ya aura, koda taga kayan da Ammar ya haɗa ma se kushewa take tana "akace ƙwaila ce kuma a haɗa duk wannan kayan akai mata, naji cewa kayi kai ba son ta kake ba"
Ammar kam da baya son raini ya haɗe rai yace
"dan bana sonta bazan wulaƙanta musu yarinya ba, 'yar manyan mutane ce meye riba ta idan ankai musu kaya a tsiyace mutunci na ne ze zube, ba ruwanki da abunda zan kai"
Ummansa ce tai tayiwa Jidda faɗa akan sam abunda tayi be dace ba a matsayin ta na babba.


Mufeeda tayi murna mara misaltuwa ganin duk kayan nan nata ne, sam ba tayi tunanin wai yayyen ta an kawo musu da yawa ba, ita nan duniya gani take tamkar Ammar yafi kowane namiji bajinta.

Yayin da unguwar su ta ƙara ɗaukar gulma wai dan tsiya akwati uku aka kawo mata, dama ya za'ayi zaton wani kayan arziki a gurin ɗan keke Napep.

Mufeeda tuni ta manta da batun suyi faɗa da Ammar ta kira shi a waya, yana gaban umman sa a zaune da yaya Jidda da sauran 'yan uwa, yana ɗagawa ko gaishe shi ba tayi ba cikin murna ta fara magana

"Yaya Ammar ɗina naga kayan da aka kawomin nagode Sosai Allah yasaka da alkhairi, Allah ya ƙara maka buɗi ni ban san ma wane irin godiya zan yi maka ba nagode sosai"

Kana jin muryarta kasan yarinya ce sosai, Ammar yace "Ameen ki gaida mutan gidan" ya katse kiran, umma tace
"Haba Ammar be kamata kayi haka ba, kayan da aka kai ba wani na kirki bane amma se murna take tana godiya gaskiya yarinyar nan tana da hankali"

Halima tace "nikam Yaya Ammar ta burgeni wallahi se murna take yi"

Jidda kam taɓe baki tayi tace "wai Umma me kike so yace mata ma, dole tayi murna tunda ba sonta ake ba ta cusa kai"

Sam Ammar baya son irin wannan shirmen na mata dan haka ya tashi ya fice.


Mufeeda ta kammala jarrabawar ta lokacin saura sati uku biki, shirye2 sunyi nisa sosai kai ya fara ɗaukar caji, ƙannen Mama ne suka je suka gano gidan domin su san yanayin kayan da za a sai mata, gida ne ƙarami amma harda gate da matsakaicin tsakar gida, akwai wadataccen falo da ɗakuna guda biyu a ciki kowanne da banɗaki, se kitchen a falo, da ɗaki ɗaya a tsakar gida da toilet, ta gefe jikin bango kuma an shuka flowers, daidai gwargwado gidan yayi kyau ana ta jinjinawa ƙoƙarin Ammar.



Baba ya saiwa Mufeeda duk abunda ya kamata, yana matukar jin damuwar aurar da ita daze yi da ƙarancin shekaru amma yana mata addu'a Allah yasa haka shine mafi alkhairi.


Mufeeda kam se shan gyara take tayi fes da ita kaman ba ita ba, tana zaune a gida tana cikin ɗakin ta tana chatting ta jiyo ana gayawa Mama tsegumin ana tayi dasu a anguwa, ana kushe mijin Mufeeda ana zata auri talaka kuma har wadda take surutun abun a unguwa aka gayawa Mama, kuma abun takaicin makwabciyar su ce take yaya ta abun tana kushewa bayan ita 'yan mata huɗu ne a gaban ta babu wadda ta aurar.


Mama taji haushin abunda aka gaya mata ana faɗa akan auren autar tata, ai kafin mama tayi magana tuni mufeeda ta fito daga ɗaki fuskarta murtuk cikin ɓacin rai tace

"ita wadda take kushe min miji' ya'ya nawa ne a gaban ta? Nayi imani da Allah da yaran ta suka sami wanda be kai nawa ba so zata yi, yara daga me bleaching seme soya awara saboda rashin miji, kuma wallahi se naje har gidan ta na mata rashin mutunci tun......

"Ke rufemin baki" mama ta daka mata tsawa

"ki ƙyalesu suyita surutun mana ze fito a jikin kine? Kowa yayi nagari kansa meye na tada jiniyoyin wuya? Ke ko gajiya ba kyayi da faɗa"

"Amma Mama ina ruwan ta dani? Ni zan auri me a daidaita sahu nata mijin fa faskare yake yi da 'yan kame2, ni wallahi idan banje na zazzage mata ba zuciya ta ba zata yi sanyi ba"

Mama tace "to sekin dawo ina magana ki nayi, matar data haifeki ki ƙyalesu suyi tayi karki ɓata farincikin da kike ciki mana, wuce ki koma ɗaki"

Mufeeda ji tayi kaman zuciyar ta ta fashe, taso mama ta ƙyaleta taje taiwa matar nan rashin mutunci daga ita har 'ya' yan ta, dukda rashin kunyar mufeeda akan sa'anin ta ya ƙare amma yau kam taso mama ta ƙyaleta tayi wa matar  nan saukale.

Ta koma ɗaki tana ta ɓacin rai, tana ƙoƙarin gano meye aibun sana'ar Ammar da ake kushe mata shi, kuma ai ba dole ne dan yayyen ta na auren masu kuɗi ace itama seta auri me kuɗi ba.


Tana ta wannan tunanin Kiran Ammar ya shigo wayar ta, ɗaga wayar tayi tareda yin shiru, Ammar yace "ina waje" da yake indai yazo haka yake ce mata

Dukda ranta a ɓace yake taji daɗin zuwan nasa dan akwai abubuwan da take so su tattauna.

Ɗakin mama taje ta sanar mata zata fita Ammar yazo sannan ta wuce, tai masa iso ya shigo inda suka saba zama, duk lokacin daya zo fuskarta ɗauke da fara'a da shauƙin ganin sa yake ganin ta amma yau sam fuskarta a haɗe, tunanin sa ko tun akan saɓanin da suka samu ne ranar daya ganta a mota, da yake tun lokacin be ƙara zuwa ba se yau.

A hankali cikin turo baki ta furta
"ina wuni"
Seda ya ɗan tsura mata ido a ransa yace "ikon Allah a da ko a mafarki akace zan auri 'yar mitsitsiyar yarinya kaman wannan cewa zanyi ƙaryane, amma abun mamaki waini ammar ni zan auri wannan' yar ficikar" yai ajiyar zuciya sannan yace

"baki da lafiya ne?"
Girgiza masa kai tayi alamar A'a,
"to me akayi miki?"

Kaman ya taɓo abunda yake damunta tace

"ɓatamin rai akayi, 'yan unguwar nan ne suke cewa wai zan auri me a daidaita sahu, na cewa mama ta bari inje in rama ta hanani" ta ƙarasa maganar hawaye na zubo mata.

Tabbas akwai ƙuruciya a cikin maganar ta, haka nan seyaji ta bashi tausayi yace

"kinga matsalar ki ko? Daga tambaya se kuka meye hakane? Kinga da tun farko baki ce ni zaki aura ba babu memiki gorin zaki auri me a daidaita sahu, amma gayamin me yasa kike sona?"

Ɗan ɗagowa tayi ta kalle shi tace "nima ban sani ba"

"Akwai dalili ki gayamin"

"nifa ban sani ba"

"shikenan tunda haka kika ce, kin fi son a cigaba da yi miki gori kin auri talaka, kalli gidanku fa kalli motar Baba kalli suturar da kike sakawa, amma kince ke se talaka kaman Ammar kike so dole aita ɓata miki rai, baki dace da Auren talaka kaman Ammar ba, karatu ne ya dace dake idan kin gama ki samu wani haɗaɗɗen mutum me kuɗi ki aura, amma kinga Ammar talaka ne sosai kalli suturar da yake sawa, bashi da komai kinyi garajen zaɓarsa a matsayin miji"

Zuba masa ido tayi  kawai ta fashe da kuka cikin kuka tace 
"Niba kwaɗayayyiya bace, ni ba kuɗi nake so ba Yaya Ammar nake so, ban san Ya akayi na fara soyayya ba, ban san ya akayi nake sonka ba bayan ko damuwa bakayi dani ba, ni kuɗi basa gaba na"
Sosai take kuka hada sheshsheƙa, Ammar yayi ƙasa da murya yace

"at your age is too early ace kin fara soyayya zuciya ce kawai take ruɗarki, ni anya ba jumping aka yi miki a baya ba, dan kamata yayi ace kina Jss2 ko 3 yanzu"

A ranta tace " ka manta kamata yayi ace ina ciki ba a haifeni ba ƙarewar Jss3 "

A fili kuma tace " ni ba'aimin jumping ba shekara ta ɗaya aka sani a makaranta saboda mama tace ina surutu sosai "

Ammar seda ya ɗanyi murmushi dan komai na yara take yi yace

"No wonder you are still baby, bakifi a saka zani a goyaki ba amma kince ke aure zakiyi meyasa kika zaɓi yin aure yanzu akan karatu? Aure akwai challenges masu yawan gaske da ba lallai ki iya ɗauka ba a shekarun ki "

Ta zumɓura baki fuska duk hawaye tace
"tunda ni Baby ce seka dinga goyani ai"
"Waye ze goya kin?"
"Yaya Ammar ɗina"  girgiza kai kawai yayi yace
"baki gayamin meyasa kika zaɓi Aure akan karatu ba?"
"Nifa da nafi son in fara karatu, kawai na haɗu da kai naji tsoron kar wata ta rigani auren ka shikenan fa" tai maganar tana son ganin reaction ɗin sa

Ikon Allah ita abunda ke ranta kenan

Ammar yace "Amma bani da kuɗi fa kuma gani mummuna nayi miki girma"

"Nifa ko gurgu ne kai a haka nake sonka, ni duk mazan duniya da nagani babu me kyan Baba na da kuma Yaya Ammar ɗina, kuma ai Arziki na Allah ne, dama dai ni nasan ba sona kake ba"

Murmushi yayi tare da girgiza kai yace
"kinga goge ragowar hawayen nan kar wani yazo wucewa yace wani abun nayi miki"

Tasa hannu ta goge hawayen fuskarta, Ammar yace
"me kike shiryawa na bikin naki?"

"Bikinmu dai" ta mayar masa

"Waike ba kya jin kunya ne?"
Kallon sa tayi ta ɗan lumshe ido tace  "wai kunyar wa zanji? Aiba ƙarya nayi ba bikinmu ne nida Yaya Ammar"

Tunda take Ammar be taɓa zuwa gurin ta ya daɗe haka ba sunyi hira me tsawo, amma yau Ammar hada murmushi dan haka ta saki jiki take ta masa yarin ta, dan ta ƙudurce wa zuciyar ta da ƙuruciyar tata zata yi amfani ta mallake shi.

Ammar yasa hannu a Aljihunsa ya ɗakko kuɗi ya ajiye mata yace "ga wannan nasan ana party kokuma kamu na Amarya, sekuma yayi shiru daga baya yace" ke sam be kamata a kiraki wata amarya bama"

Ta kalleshi tace "to me za'a kirani? Ƙwaila ko?"

Kallon ta yayi bece komai ba ya cigaba da magana "gashi nan ki ɗauka ki ƙara kiyi wani abun"

Ya kuma sa hannun sa a Aljihu ya ɗakko wasu kuɗin yace "wannan Halima tace min ana bada kuɗin ƙunshi da sauransu dai ban san kan abunba gashi nan kiyi abunda ya kamata kuɗin ba yawa kin san ni talaka ne"

Ƙura masa ido ta ɗanyi sannan tace
"banda abunka Yaya Ammar kai da kake fama da hidima meye na bani wannan kuɗin haka? Ni angama shirya komai a gida ba abunda muke buƙata ka barsu kawai kayi wani abun dasu"

Haɗe rai yayi sosai sannan yace "kin raina ko?"

Da sauri ta girgiza kai tace "A'a ni ban raina ba"

"idan na kuma baki abu kikace Bazaki karɓa ba sena ɓata miki rai ai ba roƙa ta kikayi ba"

Mufeeda tace "to Allah ya bada haƙuri nagode Allah ya ƙara buɗi"

Ammar ya miƙe yace "zan tafi"

"Se yaushe?" ta tambaye shi

"se ranar ɗaurin aure" shi da yayi maganar ma kunya ce ta kama shi, waida wannan 'yar mitsitsiyar abar za' a ɗaura masa aure

Haɗe rai tayi tace
"bazaka zo kaga kwalliya ta ba na biki?"

Kwaɓe fuska yayi yace "ke in an miki kwalliyar ma ba kyau za kiyi ba"

Cikin shagwaɓa tace  "ni wallahi ba mummuna bace"

Ammar yace "Auke tunanin ki kyaune dake? To ban sani ba wataƙila nan gaba idan kika girma kika zama mace kiyi kyau amma a yanzu dai kam se a hankali"

Ji tayi kaman tayi dariya Ammar ya gama raina ta saboda wulaƙanci ma wato ba ta kai mace ba lallai zata bawa Ammar mamaki, amma ta maze tace

"to ni mece inba mace ba?"

"Aike ƙwaila ce"

"wai dan Allah Meye ƙwaila?"

"Ke kin isheni da surutu bana son yawan magana seda safe"

Mufeeda aran ta tace "bari in nunawa mutumin nan ƙwailar ma mace ce"

Ta kashe murya sosai ta kalle shi cikin shagwaba kaman 'yar yarinya tace

"Mijin Jaririya ban gaji da ganin ka bafa dan Allah ka tsaya in ƙara kallon ka"

Ya haɗe rai yace "ke bana son shirme fa"

"waini komai nayi shirme ne, muje in raka ka ni ban gaji da ganin ka ba"

Haka ta biyo shi wajen gate yace "koma gida rakiyar nagode haka"

"to My love, ka gaida gida ka gaishemin da Mama, ina sonka Yaya Ammar ɗina" ta kashe masa ido ɗaya ta koma gida.

Girgiza kai yayi ya nufi Napep ɗin sa, yana ƙara jinjinaa yarintar mufeeda.

Shi mamakin kansa ma ya dingayi yadda ya tsaya yana sauraren shirmen ta. Ammar ya dinga ji a ransa ina ma Mace ze aura, inama Auren kirki zeyi ba wannan auren shirirtar ba, Yarinyar da sam ba zaman Auren ne a gaban ta ba ita dai tace zata yi aure ne saboda tana sonsa, sam besa ran wani zaman Aure da Mufeeda ba kawai zeyi aurene ya ƙarasawa Mama raino.




Ɗakin Baba ta shiga da sallama ta tarar dashi zaune tare da Mama, Baba yace "Autar Baba kuma Amarya to be"

Murmushi Mufeeda tayi ta ƙarasa ta miƙawa Mama kuɗin da Ammar ya bata, Mama tace
"wannan kuma na menene?"
"Bani yayi wai inyi haƙuri bashi da kuɗi in ƙara inyi wani abu, sannan inyi kitso da ƙunshi a ciki"
Mama tace "roƙon sa kikayi kenan?"
"Ni kin san bana Roƙo shi yace sena karɓa"

Suna cikin maganar ne yaro yayi sallama ya kawo viva yace
"Ammar yace a bawa Mufeeda"


Mufeeda ta karɓo ta shigo ɗakin Baba
Kayane ɗinkakku shadda ce blue da leshi se takalmi da jaka na Amare, ita dai Mufeeda kasa magana tayi se kallon kayan take.

Baba yace "A jikina ina jin Insha Allah yaron nan ze kulamin da Auta, akwai shi da ƙoƙari, yanzu bayan kayan lefe hadda wata hidimar ta daban"

Mama tace  "lallai yaron nan akwai ƙarfin hali, bayan hidimar lefe da yayi hadda wata ɗawainiya daban, kuma gashi an riga an sai mata kayan da zata yi fitar biki"

Mufeeda tai farat tace "ni gaskiya na Yaya Ammar zan sa"

Mama tace tashi ki bar ɗakin nan mara kunya kawai, ban taɓa ganin mace mara kunya kamar ke ba, ana maganar aurenki kina tsoma baki shashasha kawai.



Hausawa sukace rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, kwanci tashi asarar rai satin bikin Mufeeda ƙwaila da Oga Ammar ya kama (😜😜😜)

Tunda satin biki ya kama jikin ta yayi sanyi komai a hankali take yi kaman kazar da ƙwai ya fashewa a ciki.

Yaya Amina da fati sune suka zama tamkar manyan ƙawayen ta.

Tasha lalle anmata gyaran kai tayi kyau matuƙa ga fatarta se sheƙi take yi, Mama daurewa kawai take yi dan har cikin zuciyar ta take jin rabuwa da Autar tata, dukda kullum cikin faɗa suke.


An kama mata gurin kamu, tayi shigar gargajiya anmata simple make up tayi kyau sosai, 'yan gulma se cewa suke wannan amarya' yar yarinya se kace auren ƙauye, hada masu Anya ba magana ta ɗaukowa iyayen ba shiyasa suke so su lallaɓa su aurar da ita ba, kowa da abunda yake faɗa, akayi kamu da sauran Al'adun gargajiya aka watse.



Abokan Ammar sunyi bajinta, suka haɗa kuɗi suka sai masa ƙaramin inji, suka sai masa dish suka bashi kuɗi naira dubu saba'in, da yake Shima Ammar meyi ne, duk wanda sha'anin sa ya tashi dukda bashi da shi sosai amma ze daki jikin sa yayiwa mutum alheri, gashi shi babu wani babban sha'ani daya taɓa taso masa balle suyi masa kara, shiyasa wannan karon suma suka jajirce suka yi masa wannan abun Alkhairin.

Ammar yaji daɗin kuɗin nan matuƙa, dan haka ya samu Abba ya nuna masa kayan da abokan sa suka bashi, Abba yaita murna yana samu su Albarka.

Ammar ya bawa Abba dubu hamsin yace
"ga sadakin sa nan da za'a bawa Mufeeda"
Abba yace "Madalla Allah yayi maka Albarka, Allah ya Sanya muku Alkhairi"

Yaya jidda na gidan Ammar ya bawa Abba kuɗin sadakin.

Ta dinga mita tana masifa "wannan 'yar mitsilar yarinyar za' a bawa sadaki har dubu hamsin saboda Almubazzaranci wallahi Ammar ni har ka fara bani kunya duk wannan izzar se kashewa ƙaramar yarinya kuɗin ka kake, wallahi zakayi dana sanin auren wannan abar dan banga abunda zaka samu a jikin ta ba, banda abun namiji ga mace kaman Zainab amma ka ɗakko wannan 'yar mitsilar abar"

Ammar yace "Komai girman ta komai ƙanƙantar ta tunda Auren ta zanyi dole in kashe mata kuɗi tunda itama 'yace mutane ne suka haife ta, tunda Auren ta zan yi kulawar ta dole ta dawo ƙarƙashina dole in nema in kashe mata tunda kema naki mijin yana nema yayi miki"

Umma tace "jidda karki ƙara shiga sabgar abunda Ammar zeyiwa Mufeeda, Allah ya riga ya ƙaddara baze auri Zainab ba Mufeeda ze aura"



Duk Events ɗin da akayi babu wanda Ammar ya halarta, Amma danginsa sunje, Amma Amarya dai2 gwargwado tayi kyau matuƙa, Mufeeda tana da kyau ba laifi
(Amma oga yace bata kai mace ba dan haka se a hankali, se anyi rainon ta😂).





Ayimin haƙuri may be zaku ɗan jini shiru kwana biyu

Share please
More Comments More typing
Ayshercool
07063065680
[23/06, 10:48 PM] Ayshercool: ✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

     

ELEGANT ONLINE WRITER'S

             



                      Page 9

Tunda aka fara bikin nan ko waya Mufeeda basu yi da Ammar ba, kan Mufeeda ya ɗau caji sosai, ana i gobe ɗaurin Aure Mufeeda ta fara kuka, ji take kaman tace ta fasa kuka sosai, Mama tun tana rarrashin ta harta bata haushi tace

"da Ubanwa yace kice ke Auren kike so, ki rufemin baki ko in zane miki jikinki"



Yaya Amina ce

Please Login or Register in order to submit comment