Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fitowa ya tarar da Mufeeda ta saka mini Skirt da wata 'yar ƙaramar riga shara shara bata ƙarasa rufe mata cikin ta ba, tayi parking ɗin dogon gashin ta, ta saka hular hat tana rawa a falo tana juya jikin ta a hankali tana bin sautin waƙar dake tashi a talabijin ɗin dake falon, ba tsammani ta juyo taga Ammar a tsaye yana kallon ta, da Sauri ta ƙaraso inda yake tsaye tana faɗin
"Happy birthday to you Hubby"
Kallon ta kawai yake yi, ta riƙo hannun sa zuwa falon ya samu kujera ya zauna ta cire hular kanta ta dube shi tace
"barka da zagayowar ranar haihuwar ka Mijina Allah yayi wa rayuwar ka Albarka"
"Ya akayi kika san yaune ranar zagayowar haihuwa ta?"
"Barwa zuciya abunda take so Hubby, ina son yin wani abu daze faranta maka kawai na samu labarin wannan kwanan watanne na haihuwar ka, shiyasa na maka barka da zagayowar ranar haihuwar ka"

A hankali ya janyo ta jikin sa yana shafa gashin kanta da yasha gyara ya kwanta yana ta tashin ƙamshin mayuka, tunani yake akan saƙon da aka turo masa, yana cikin tunanin yaji muryar ta tace

"Abun sona naso mu kasance cikin farin ciki yau, Amma naga kamar baka walwala, Allah ya sa ba laifi nayi maka ba"?

Tai maganar jiki a sanyaye, Ajiyar zuciya yayi yace "muyi breakfast ko?"
Jinjina masa kai tayi, har suka kammala Mufeeda na kallon sa tana tunanin meke damun sa? Sosai kayan da ta saka suka karɓi jikin ta tayi kyau sosai, Amma tunanin da yake yaƙi barin sa ya kalleta sosai.

Ya shirya tsaf ze fita Mufeeda ta bishi
Cikin sanyi jiki tace

"Allah ya kiyaye hanya, Amma gaba ɗaya inajin babu daɗi da yanayin da kake yau, ban sani ba ko be kamata inji damuwar taka ba, Amma idan ni nayi maka laifin kayi haƙuri dan Allah"

Bece mata komai ba ya fice.

Gaba ɗaya Mufeeda haka ta wuni babu daɗi, ta shirya masa abubuwa da dama yau amma taga kaman baya cikin farin ciki, haka ta dake ta ci gaba da abunda ta shirya masa.

Ɓangaren Ammar ma yana tunanin wani irin Abu Mufeeda zata yi haka a bayan idon sa, wani sashe na zuciyar sa na ƙara yadda da matar sa akan babu wani abu da zata iya aikatawa na rashin gaskiya a bayan idon sa, a zaman da suka yi ya yadda da amanar ta.

Da daddare ya dawo gida a matuƙar gajiye, tunda ga falo yaga ta sauya tsarin falon, ta canza gurin zaman kujerun, ko ina se ƙamshi yake a gidan.

Fitowa tayi daga ɗakin ta tayi simple make up, yanzu ma English wears ne a jikin ta, murmushi tayi masa tace

"Birthday man sannu da zuwa, shine ka fita ka daɗe ko? Ko ka leƙo gida ai shikenan, zomu je ɗakina am having a surprise for you, na shiryawa wannan ranar sosai fa"

A ɗan hasale yace "Ke ni ki ƙyaleni, bana son duk wannan abubuwan shirmen naki, ki rabu dani"

Gaba ɗaya jikin ta yayi sanyi ƙwalla ta cika idon ta tace
"Yi haƙuri, Allah ya baka haƙuri, ban san baka so ba, dana san baka so da ba zanyi ba Insha Allah bazan sake ba, Allah ya huci zuciyar ka, Allah yabaka haƙuri" tai maganar muryar ta na rawa hawaye na bin Fuskar ta.
Da sauri ta juya ta koma ɗakin ta ta rufe ƙofa.
Jikin Ammar ne kuma yayi sanyi da abunda yayi matan, a hankali ya nufi ɗakin sa shima, yana buɗe ɗakin yaga shima tayi masa ado, ga zane zane na heart da tayi me ɗauke da sunan su a jiki da kalaman Soyayya dana fatan Alkhairi.
Ga balloons data hura ta ƙawata ɗakin se ƙamshi yake, gefe ga cake me fari da pink ta saka HAPPY BIRTHDAY HUBBY, ga lemuka da alawoyi data shirya, tausayin ta ne ya kama shi, besan adadin lokacin da tayi tana wannan shirin ba, be san adadin kuɗin da ta kashe akai ba dan kawai ta sashi farinciki, amma lokaci ɗaya ya Gwale ta.
Rage kayan jikin sa yayi ya shiga yai wanka yana ƙara kallon ɗakin yadda yai matukar kyau, fitowa yayi ya nufi ɗakin ta.
Yana zuwa yaga ta cire kayan adon da tayi, ta zauna a tsakiyar gado idon ta sharkaf da Hawaye ta hargitse gashin kanta tana kuka.
Ƙarasowa yayi ya kalle ta yace
"Taso muje a bani cake ɗin"
Ɗagowa tayi tana kallon sa hawaye na cigaba da bin idon ta,
"Taho mana"
yai maganar yana ƙara kallon ta, a hankali ta matsa inda yake zata sakko daga kan gadon, tausayin tane ya ƙara kama shi, bata iya fushi da shi, banda lokacin da tayi fushi harta fasa masa waya, bata iya fushi dashi ko tayi ma ita ke fara sakkowa ta bashi haƙuri.
Kafin ta sakko daga kan gadon yasa hannu ya ɗauke ta, kamar wata 'yar yarinya kuwa ta kwanta tai lamo a jikin sa.
Ɗakin sa ya nufa da ita, ya ajiye ta a bakin gado ya kalleta yace
"waye ya koya miki zane ne?"
"bakowa kawai iyawa nayi" jinjina kai yayi, kayan snacks ta gabatar masa, ai kuwa Ammar yaci sosai, shi irin wannan abubuwan basu dameshi ba shi dai kawai yaci Abinci ya dena jin Yunwa, wani abunma zama da Mufeeda yasa shi iya cin sa.
Ta yanka cake ɗin nan takai bakin sa, buɗewa yayi tasa masa, tunda Ammar yake be taɓa cin cake ɗin birthday ba, jin cream ɗin nan yayi har kansa dan daɗi.
"A ina kika siyo cake ɗin nan?"
"Ni nayi fa"
"A'a gayamin gaskiya dai"
Taso ta tsokane shi tace santi yake, amma ta tuna ze iya dena ci in tace haka dan haka ta ƙyaleshi, gaba ɗaya Ammar ya manta da abunda yake damun sa kuma yaji daɗin abunda ta shirya masa sosai, Amma kunsan halin mutumin bazece ya yaba ba.

Seda suka gama ciye ciyen su, Sannan Ammar ya nemi gurin kwanciya, har zata tafi ɗakin ta, ta fasa ta dawo ta hau kan gadon tace
"Yaya Ammar har yanzu baka gayamin laifin da nayi maka ba yau, gaba ɗaya yau haka na wuni raina babu daɗi ka gayamin dan Allah"
Juyowa yayi ya zuba mata ido ba tare da yace komai ba.
"Kayi Magana mana, kabarni a cikin damuwa fa"
Maimakon yace wani abu sema janyo ta da yayi jikin sa yace
"meyasa kika ɓata gyaran gashin da kika yi?"
"Ai cewa kayi baka so"
"Ni nace bana so? Bance bana so ba"
A hankali Ammar ya canza akalar hirar zuwa wani abu daban, tun tana jurewa harta fara kuka, A hankali ya ɗagota amma taƙi kallon sa, miƙewa yayi yaje yai wanka ya dawo yai kwanciyar sa a gefen ta, bata da zaɓi itama ta shiga banɗakin sa tai wankan, maimakon ta tafi ɗakin ta, seta haye gadon sa tai kwanciyar ta, seda ya tabbatar tayi bacci sannan ya juyo ya ƙara rungume ta a jikin sa yana fatan Allah yasa message ɗin da ake turo masa ƙarya ne.

Da Asuba da ya dawo daga salla seya kwanta a falo, Mufeeda kuwa da tayi sallar Asuba kwanciyar ta ta kuma yi a gadon sa tana bacci.

Seda gari yayi haske sosai sannan ta farka, tashi tayi ta fito ta tarar da shi yana bacci akan carfet, zuwa tayi kusa dashi ta kwanta tana ƙarewa fuskarsa kallo, A hankali ya buɗe idon sa ya kalle ta ya mayar ya lumshe.

A hankali ta ɗora hannun ta a ƙirjinsa dai dai inda zuciyar sa ke bugawa tace "Yallaɓai ina da saƙo ka bawa zuciyar ka"
Buɗe ido yai yana kallon ta
Mufeeda cikin salon muryar tausayi ko wanda ya karaya da wani abu ttace "ka gaya mata akwai zuciyar da take matuƙar begen ta ba dare ba rana, Akwai zuciyar da ke son kasancewa da ita har ƙarshen rayuwar ta, ta zama me yiwa wannan zuciya da take son ta afuwa, idan tayi ba dai dai ba tayi mata uzuri kasancewar wannan zuciya me rauni ce, kuma 'yar jaririyar zuciya ce dake girma yanzu, zuciya ce dake girma da soyayya ba zata iya ɗaukar tsatstsauran hukunci daga gurin ta ba, ina fatan saƙon zuciya ta ze isa ga zuciyar Abun so na, zuciya ta bata ganin kowa se kai, ban taɓa son wani ba in bakai ba akanka na fara, kuma daga kai na gama, ina roƙon ka kamar yadda kake min kallon yarinya Koma ince Jaririya ina fatan idan na maka laifi ka duba ƙanƙanta ta kamin hukuncin da Jaririyar zuciya ta zata iya ɗauka, ina fatan saƙona ze isa ga zuciyar ka kai tsaye nagode Hubby na" ta sumbaci fuskarsa ta miƙe.
Bayan ta yabi da kallo harta shige kitchen yana sake tunani daban daban a ransa.

**************
Wajen ƙarfe goma na dare dan har sun fara shirin kwanciya, dan Mufeeda har ta masa Sallama ta tafi ɗakin ta, aka fara buga musu gate, Ammar ne yaje buɗe ga mamakin sa yaga Faruk ne da yarinyar sa, se kuma Fa'iza abun ya bashi mamaki matuƙa ganin Faruk da Fa'iza a tare a wannan lokacin haka, amma ya ɓoye mamakin sa yace "kune kuke tafe yanzu?"
Yai musu iso har cikin gidan, zuwa falo
Faruk yace "Ai gani nai rashin kirkin nawa yayi yawa, dan haka naje har gida nace Fa'iza ta rakoni gidan ka dai inga Amarya har gida kafin in kawo Madam"

Ammar kallon tuhuma yakewa Fa'iza amma ya dake yace "Aikuwa ka kyauta bari in kira ta ku gaisa, dan harta kwanta"
Yaje ya taso Mufeeda suka taho tare, suka gaisa Fa'iza se wani mugun kallo take mata, hirar babu gaira babu dalili Faruk yake, gaba ɗaya Mufeeda ta tsani Faruk ɗin nan musamman irin kallon da yake mata.
Yarinyar da suka zo da itane Jawahir ta fara kuka, tausayin Yarinyar ya kama Mufeeda taje ta haɗo mata cornflakes tana bata.
Faruk yace
"Kai Amarya akwai san yara, ina fatan dai kun kusa kiran mu mu ɗau Baby"
Yai maganar yana mata wani irin kallo.
Fa'iza tace
"Ai ka tausaya mata tayi ƙanƙanta ace tayi ciki ai"
Wani mugun kallo Ammar yayi wa Fa'iza, Fa'iza tace
"Kinga dan Allah idan da cornflakes ɗin nan ɗan haɗamin dan nima Yunwa nake ji"
"Cornflakes Abincin yara ne, kamar Yadda kika faɗa Mufeeda Yarinya ce saboda ita nake ajiye irin wannan Abincin ba dan baƙi ba, da kunzo da wuri ne da se ko wani abun ta girka muku, Amma tunda kuka kai kamar wannan lokacin nasan kunci Abinci, Sannan Faruk gaskiya banji daɗin yadda ka ɗakko 'yar uwa ta kana yawo da ita a gari a wannan daren ba, raina ya ɓaci gaskiya kuma zanje in samu Mama se naji dalilin da yasa kika fito kika biyo shi a wannan daren, maza ka tashi ka gaggauta maida ita gida na gaya maka"

Fa"iza tace "Yanzu Yaya Ammar bani da Alfarmar da zanci wani abu a gidan ka? Har inzo amma ka koreni"

"Gidanki ne ko gida na? Ko kuma ya dace kizo min gida a irin wannan lokacin"

Faruk yace "Amma Ammar gaskiya.....

"Shut up get out from here please, kekuma zamu gauraya dake"

Haka ta tashi sum suma suka fice

Amin Afuwa abubuwa ne sunmin yawa sosai
Domin gyara, sharhi, ko Shawara
Ayshercool
0706306568
[14/07, 8:19 AM] Ayshercool: ✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

Please follow me on Wattpad, vote and Comment

https://www.wattpad.com/1096499534?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Ayshercool7724&wp_originator=NWkhlySuZ8Eug%2BopXFfcycv2JGS3axjaccC5%2FbUYT6YzeXAYV4ybw7FnTr8fHQDwo5ncF8TNfQfelSdeR5t0OZi0%2FKAiAcvwuLa561y0j%2BMpxBPI15z3EyzU4ZruY9KP

ELEGANT ONLINE WRITER'S

             

           

                  

                        Page 21

Bayan tafiyar su Faruk gaba ɗaya jikin Mufeeda yayi sanyi, ta kalli Ammar zatayi magana, Amma yai sauri yace "kar inji wata magana daga bakin ki, tafi ɗakin ki kije ki kwanta" haka tai shiru ta wuce ɗakin ta cike da Fargabar kar Fa'iza taje ta kunno mata wata wutar a gurin 'yan uwan Ammar.

Ammar tunani ya dingayi wace irin Alaƙa ce tsakanin Faruk da Fa'iza, da har zesa su dinga yawo a wannan daren su biyu se ƙaramar Yarinya, iyayen Fa' iza suna da tsauri akan tarbiyya amma me zesa abar Fa'iza ta fita a wannan daren? Meye alaƙar ta da Faruk? Da wannan tunanin yai bacci.

Da safe Mufeeda na ta kallon Ammar, tana so ta gaya masa abunda ke faruwa game da halin da take ciki da wanda yake kiran ta, Amma sam Ammar baya walwala ransa a matukar ɓace yake tun zuwan su Faruk jiya da daddare, babu alamar ze tsaya ya saurare ta be kamata ma ta tunkare shi da zancen ba ganin yadda yake cikin ɓacin rai, dan haka bata gaya masa ba ta lallaɓa yai breakfast ya fice.

*****************
Maƙotan Mufeeda' yan layin su suka shirya zasu tafi duba Maman Nur, suka biyo wa Mufeeda wai in zata je.
Mufeeda tace
"dan Allah kuyi haƙuri idan kunje kuyi mata sannu, baya nan ban tambayeshi ba kunga be kamata in fita ba"

Wata maƙociyar su tace  "ke yanzu dan dai dubiya muje yanzu mu dawo shine sekin wani tambayi miji, yanzu fa zamu dawo"

Mufeeda tace "A'a bekamata in fita be sani ba"

Maman Amir ta kwaɓe baki tace "Aikin banza sannu daɗi miji, dama seda nace muku karmu biyo mata, Yarinya 'yar ƙarama se girman kan tsiya da nuna tafi kowa tsoron Allah, tsoron Allah a baki, zuciya baƙi ƙirin"

Mufeeda binsu tayi da kallo suka gama surutan su suka fita suna mita.

Har suka je Asibitin nan Maman Amir Mita take, suka je suka tarar Maman Nur an gama sama ta jini, Jaririn data haifa ɗinma yana Nursery Unit saboda bashi da cikakkiyar lafiya.

Suka mata Sannu, Maman Nur tace "wai Maman Amir mitar me kike hakane?"
"Wannan banzar Yarinyar mana, muka biya mata tazo muzo duba ki amma taƙi wai bata tambayi mijin ta ba, 'ya se girman kai kamar wata matar gwamna, Da mijin nata wani shege me a ƙasar nan inaga da seta kore mu daga unguwar"

Wata Yayar Maman Nur me suna Hadiza tace "to ai da gaskiyar ta, ya zata fito bata tambayi mijin ta ba, ai tayi gaskiya"

Maman sadik tace "Anty hauwa bari kawai, ta fiye iyayi ne, ita fa ko ɗam shiga maƙotan nan a Saba da juna ba tayi ga rowar tsiya ta jaraba"

Anty Hauwa tace "Wallahi banga laifin ta ba hakane daidai, ta zauna inda mijin ta ya ajiye ta kuda kuga zaku iya yawo se kuyi tayi"

Maman Amir tace "wallahi Anty hauwa ba wani bin miji, to jiya Sa'idu me kayan miya ne ya gaya wa Baban Amir yace ganin idonsa ya ga tana zance da wannan Alhaji Idris ɗin na bayan layin mu da ranar Allah"

Maman Nur tace "ke dan Allah dagaske?"

"Wallahi tallahi dagaske, dan har Baban Amir yace ze tari mijin nata Amma ya fasa"

Nan suka salallami suna ƙara jagwalgwala maganar, Anty hauwa tace  "ban taɓa sanin munafuncin maza ya kai haka ba, kinga ku kiyayi wannan me kayan miyan, kuma wallahi in sharri kukayi mata se Allah ya tambaye ku"

Maman Sadik tace "ba wani sharri, nifa rashin lafiyar Maman Nur ma ina zargin ta, don in baku manta ba ranar da muka kai mata anko se cewa tayi, Ai maman Nur tayi Addu'ar Allah ya sauke ta lafiya yafi wannan ankon da take rabawa, Jama'a kunga Yadda Maman Nur ta ƙare a Asibiti, ta haihu lafiya amma kalli "

Maman Nur ta zare ido tace
"Wallahi hakane maman sadik, na haihu lafiya, Amma naita zubar da jini, nikam kar dai ace mayya ce"

Maman Amir tace "ai cire kamar ɗin, itace kawai se kowa ya kula da kansa, bayan bin maza hadda maita"

Nan suka haɗu suka saka gulmar Mufeeda suka dinga zagin ta gami da tsine mata bata san suna yi ba, laifin ta ɗaya taƙi yadda ta zama irin su, mata masu gantali da yawon kwararo kamar ba matan Aure ba, Matan da basu ɗauki sirrin mazajen su a komai ba duk inda suka zauna sesu tone shi.

****************

Mufeeda tana zaune tana karanta Al'qur'ani mai girma, cikin nutsuwa ji tayi ana mata wani irin mahaukacin bugu da seda yasa ta miƙe tsaye a tsorace, kasa matsawa tayi ta tsaya tana rarraba ido dan firgick, gashi dai Yamma ce amma bugun ya tsorata ta, kamar mara gaskiya haka ta fito tsakar gidan ta nufi gate cikin murya me cike da tsoro tace
"Waye?"
"Mune ko ba zaki buɗe ba?" babu ko tantama muryar Jidda ce, buɗe ƙofar tayi bata ko ƙarasa buɗe ƙofar ba Jidda ta danno ƙofar da ƙarfi ta shigo, ita da Fa'iza ne da wasu Yara, wanda 'ya' yan Anty Jidda ne.

Tun daga tsakar gidan ta fara faɗa tana masifa,
"Ke har kin isa wani daga dangin mu yazo gidan nan ki hanashi wani abu, ina ɗan uwan mune yake siya ya ajiye, 'yar ƙanƙanuwa dake se rashin mutunci"
Fa' iza tace

"wallahi Anty Jidda idan ba'a ɗau tsatstsauran mataki akan wannan yarinyar ba, wallahi se ta raba shi da kowa, baki ga zagin cin mutunci da yayi min saboda ita ba, akan shege cornflakes aka wulaƙanta ni, ta wani haɗe rai tace gaskiya ya sallameni za ta yi bacci "

" tunda da uban ta aka haɗa kuɗi aka gina gidan ai dole ta faɗi haka mana, ku shiga kowa ya ɗau abunda yake so, Ammar ne ya siya"

Mufeeda ta koma gefe ta zubawa sarautar Allah ido, kayan garar Mufeeda da suke ci yasa Ammar yake samun rararar kuɗi, ya ɗanyo siyayyar kayan buƙatu, Amma Fa'iza ta shiga kitchen ta ɗakko ƙaton kwano da cokula, tazo suka dinga zazzage cornflakes ɗin nan suna antaya Madara cike da mugun ta suna ci suna zubarwa, suka gama Fa'iza ta shiga kitchen ta buɗe mata fridge ta ɗebi abunda ranta yake so, suka wulaƙanta mata falo Abinci har kan kujerun ta, Mufeeda tayi tagumi ta zuba musi ido.

Anty Jidda tace "Wallahi duk ranar da wani namu ya kuma zuwa gidan nan kika masa wulaƙanci, ko kika saka Ammar ya wulaƙanta shi sekin koma inda kika fito, Yarinyar banza data wofi kawai"

Tabbas Anty Jidda ta haifi Mufeeda, kuma taci darajar Ya yar mijin ta ce, banda haka ba abunda ze hana Mufeeda ta sawa falo key da mata duka da muciya, sedai Hausawa suka ce Ana barin halak dan kunya.

Tana nan zaune Fa'iza ta shiga kitchen ta dafa Abinci fiye da yadda zasu iya cinyewa, ta ci kowa yaran nan kwano suka ci suka jagwalgwala sauran, 'Yar Anty Jidda Haseena wadda zata shekaru ɗaya da Mufeeda ita ce tace
"Amma Anty Fa' iza wannan almubazzaranci ne, Abincin nan yayi yawa, muma idan Abbnmu ya dawo yaga an wulaƙanta masa Abinci Faɗa yake mana"

Fa'iza tace "Rufemin baki ko in make ki, ji gulmamiya, wancan Abbanku ne yake siya wannan kuma uncle ɗinki ne ya siya, kici iya cinki ki bar sauran"

Suka yiwa Mufeeda kaca kaca da gida, ga zagi da cin mutunci da suka zazzage mata sannan suka tafi. Zama Mufeeda tayi tai shiru tana Hawaye, ta rasa me tayi wa bayin Allah nan suka tsane ta haka.

Wayar ta ce ta fara ringing, tasa hannu ɗaga ta kai kunnen ta.

"Amarya ba kya laifi shine kika yi blocking ɗina a what's App ko? To ai ba zaki taɓa gujemin ba, baze yuwu inta Azabtuwa da ƙaunar ki ni kaɗai ba, kuma idan ba kiyi wani abu a kai ba to ina tabattar miki dani zanyi, ki huta lafiya abar sona"

Ya katse wayar sa, Mufeeda ta kasa ko motsawa daga inda take ta rasa me ya kamata tayi, tayi tunanin ko ta gayawa Mama halin da take ciki, se kuma taga yayi wuri ace ta fara gayawa Mama ga matsalolin da take ciki, dama Abunda Maman taita jiye mata kenan, ina ma na bi abunda Mama ta faɗamin wataƙila da hakan bata faru ba, wata zuciyar tace ai duk daren daɗewa ai zanyi Auren kuma ƙaddara ta ba zata canza ba.

Tayi nisa sosai a cikin tunanin dan haka ba zato ba tsammani taji Ammar yana ƙoƙarin buɗe ƙofar falo, dan sam ba taji tsayuwar babur ɗinsa ba, zumbur ta miƙe da nufin tattare kayan da su Fa'iza sukayi kaca kaca da su, Amma Ammar ya riga ya shigo, turus yayi yana bin falon da kallo, Anyi kaca kaca da Madara a tsakiyar falon ga kwalin cornflakes da jarkokin lemo komai an zubar da shi a wulaƙance, da sauri ta ƙara so inda yake tana masa sannu da zuwa ta miƙa hannu da nufin karɓar kayan hannun sa ya kalle ta yace
"Meye haka a falon ki? Abincin Akayiwa haka?"
"A'a Yaya Ammar dama baƙi nayi shine....
" Shut up " ya mata tsawa.
" baƙi kikayi shine za'a wulaƙanta min Abinci haka, kalli falon nan fa ji almubazzaranci kuma kina kallo? Kin sani saboda ke nake ajiye wannan abubuwan ni ba damuna suka yi ba, Amma kika bari a ka wulaƙanta haka, kalli Abinci har a tsakar gida an ajiye shi fal a bakin tap, da yake baki san zafin nema ba ko shiyasa kike wulaƙanta wa, bazan ƙara siyo wa ba, zan ajiye Abinci ne kawai, in kinyi hankali na siyo a nan gaba amma ko Madara ba zan sake siya ba, sakarya kawai "  ya watsar da ledar da ya shigo da ita a falon ya wuce ɗaki Fuuuuu.

Jiki a sanyaye ta durƙusa ta shiga gyara inda ya ɓaci a gidan, gaba ɗaya ta rasa mafita akan lamuran nan, Allah ya temaki Mufeeda hankalin Fa'iza be kai kan Flask ɗin Abincin Ammar ba, dan haka seda ta gyara ko'ina sannan ta ɗau Abincin ta bishi ɗakin sa.

Ya kwanta yayi rigingine yana kallon ceiling da alama tunani yake yi, ta ajiye Kayan Abincin tace
"Yaya Ammar ga Abinci na kawo maka"
Banza yayi mata yaƙi kallon ta, cikin sanyin Jiki tace "dan Allah kayi haƙuri, zan kiyaye insha Allah dan Allah kayi haƙuri"
A fusace yace "ɗauke Abincin ki ki fitar min daga ɗaki"
"Dan Allah kay.....
"ki ɗauke Abincin ki nace na ƙoshi, idan baki fita ba ni zan bar miki ɗakin"
Cikin hanzari ta ɗauke Kwanukan ta fito.
Ɗakin ta ta koma ta kwanta, ta rasa me ke mata daɗi
"ya Allah idan abunda bayin nan naka sukemin da mugun ta sukemin Allah kayi musu abunda suka yi min" ta ƙarasa maganar hawaye na zubo mata,
"har zuwa yaushe zan cigaba da ɗaukar laifin da ba nawa ba, babu Amfani in gaya masa abunda sukemin dan ba abunda hakan ze haifar se wata rigimar da tashin hankali, Allah ka bani mafita"
Haka ta ci gaba da Hawaye tana surutai.
Kiraye kirayen sallar magariba ne yasa ta tashi taje ta ɗaura alwala ta daɗe akan sallaya har kusan ƙarfe sha ɗaya tana ta Addu'a tana kaiwa Allah kukan ta, kamar yadda taga Mama ta nayi a lokuta da dama.

Da gari ya waye farkawa kawai tayi taji ƙarar Napep ɗin Ammar yayi ficewarsa, ji tayi gaba ɗaya duniyar tayi mata zafi bata ƙaunar ganin ya share ta. Idan ya fice tun safe baya dawowa se sha ɗaya kuma yana dawowa ɗakin sa yake wucewa, ko kula ta baya yi balle ya ci Abincin ta, Ammar be iya fushi ba sam, gaba ɗaya idan yana fushi tsoro yake bata dan wani irin kwarjini yake mata, ko tunkarar sa bata son yi, dan idan ya mata tsawa ba ƙaramin firgita take ba.

Yau tana idar da sallar Asuba bata koma ba ta fito, ta shiga aikace aikace, aikuwa ƙarfe bakwai ya fito ze fice, tana kitchen ta fito da sauri tana kiran sunan sa, be saurare ta ba yayi gaba, cikin sauri ta bishi amma ta bige goshin ta da ƙofa da sauri ya tsaya ya juyo, ƙarar da

Please Login or Register in order to submit comment