Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karɓa? Nawane bakya so ko?"
Gaba ɗaya Jidda ta tsani yarinyar nan, duk wani salon bariki ta iya.
Umma tai murmushi irin na manya tace  "Aishi wannan ƙyale shi, suyi ta nemowa suna bamu muna cinyewa"
Ammar yace "yau dai na ganku a rana keda Umman"
Mufeeda tace  "Dan Allah Umma karfa yayi mana dariya, Anty Maryam kisa baki mana"
Anty Maryam tace  "Gaskiya Umma kar kisa Yayi mata dariya mana"
Da ƙyar Umma ta karɓa, tana ta mata Addu'a dasa Albarka kamar ta bata duniya, suka yi Sallama suka tafi.
Seda suka shiga Ammar ya nuna mata dabbobin ta, suna ta hayayyafa gwanin sha'awa, Sannan suka tafi.

Bayan fitar su Mufeeda Anty Maryam ta bawa Umma labarin abunda su Fa'iza suka yi wa Mufeeda, da yadda ta zauna a gurin ta bayan sun samu Saɓani, Abun ya daki zuciyar umma, tayi tayiwa Ammar faɗa idan Fa'iza tazo tace ya mata wulaƙanci.

Maryam tace  "Wallahi Jidda ba kowace mace bace zata iya abunda Mufeeda tayi ba, na haƙuri da Ɗan uwan mu, Muddin kikayi dalilin kashe masa Aure wallahi kin cuce shi, kuma baze manta ba, nan ma Umma tai kan Jidda da faɗa, da taga alamun babu me goya mata baya, ta miƙe tai haramar tafiya, ranta a ɓace.

Ammar yaji daɗin Abunda Mufeeda tayi, dan be san zata basu ba, suna tafe a hanya yace
"Mufeeda Nagode sosai, Amma kuɗin da kika bawa su Umma yayi yawa, karki kwashe jarin naki fa"

Wata uwar harara tai masa wanda hakan ya shashi yin shiru, suka tari abun hawa zuwa unguwar su Mufeeda.

Suna yin Sallama ta tarar da Baba ze fita, ai da gudu ta tafi ta rungume shi, seda Ammar yaji tsoron karta jiwa kanta rauni, ko nauyin cikin bata jiba take wannan tsallen.

"Autar Baba naga kin zama ƙatuwa, Ammar me kake bata ne? Ta cinye maka tuwo ko?"

Murmushi Ammar yayi suka gaisa da Baba, Baba yace
"tunda 'ya' ya na sunzo bari in zauna muyi hira"
Ammar yabi Baba ɗakin sa, Mufeeda ta ƙarasa gurin Mama, Ta tarar da Yaya Fadeela, Yaya Fadeela ta hangame baki tana bin Mufeeda da kallo, Mufeeda ta rungume Mama tana Shagwaɓa.

"Mamana ina Missing ɗinki sosai"

Fadeela tace  "Auta wannan ƙiba haka? Ke kuwa me kike ci haka?"

"Abunda kike ci mana"

Hira suka shiga yi, Fadeela tace  "Auta a cire hijjabin mana, kowani salon ne kuma haka?"

"bazan cire ba ɗin"

"Autar Baba kodai kodai"

Hararta Mufeeda tayi tace  "Kodai me?"

Ammar yai sallama a falon Mama suka gaisa, sannan yace ze tafi bayan la'asar zezo su tafi.
Mufeeda ta tashi ta tafi rakashi, suna fita Fadeela tace
"Mama kinga abunda nagani kuwa?"
Mama tace  "A ina?"
"Kamar ciki ne da Yarinyar nan fa"
"Hmm Fadeela kenan, nagani mana se fatan Allah ya raba lafiya"

Mufeeda ta dawo falon suka cigaba da hira, tunda Mufeeda ta cire hijjabin ta Fadeela taga cikin Mufeeda har ya fito, ta dinga tsokanar ta.

"Mufeeda ni zan miki wankan Jego fa in kin haihu"

"Allah ya kiyaye, wallahi ba zaki minba"

"Ohh ni Fadeela, wai Mufeeda da ciki"

"Eh ya ranki? Shiyasa nake raina ki takuramin kike"

Haka Mufeeda suka wuni suna hira, Fadeela tana ta tsokanar ta, duk lokacin da Mufeeda tazo gida idan tana hira Mama tana fuskantar Mufeeda na cikin kwanciyar hankali, Ammar ya isa da gidan sa, ta dinga tuna lokacin da take ƙoƙarin hana Auren nan, yadda mazan yanzu suke se a hankali samun kamar Ammar se an tona.

**********************

Wata ɗaya da sakin Saima Jabir yana ta shirin Aurensa, Saura Sati biyu a fara biki, Amma Ammar, da Aminu sam basa goyon bayan Auren Jabir, dan haka sam besa su shirgin Auren sa ba.

Saima kam tana murmurewa, ta siyo form ɗin makaranta ta cike zata koma, dama tayi N. C. E, ta sai D. E Form zata koma Jami'a, ta tura aka kwaso mata kayan ta tsaf daga gidan Jabir, dukda gwaggonta ba wata me ƙarfi bace, Amma sam bata tsangwamar Saima, Saima ta iya ɗinki dan haka ta cigaba da sana'ar ta, suna rufawa juna Asiri, nan da nan ta fara dawo da ƙibarta kamar ba ita ba.

Sa'idu me kayan miya aka yanke masa hukunci zaman shekara uku a gidan yari ƙarƙashin wata kotun Addinin musulunci, tunda Abun nan ya faru layin su Mufeeda suka zauna lafiya, ba gantali ba tashin hankali kowacce tana gidan ta, idan suka haɗu da Hajara a hanya har guduwa suke su ɓuya

Ammar ya dage sosai da zuwa kasuwar nan, da safe ya sauke kaya a biya shi, ya siyo wani abun ya fito bakin kasuwa ya siyar, ɓangaren Mufeeda ma likkafa ta cigaba, yanzu har manyan kuloli take cikawa da kayan sanyi, Almajirai suzo su ɗauka sukai mata kasuwa
Da yake Mufeeda tasu ta ɗanzo ɗaya da Hajara, ta bata shawarar ta dinga haɗawa da snacks za tayi ciniki, dan sune Abincin shaf shaf mussman ga ma tafiya, Aikuwa Mufeeda ta shawarci Ammar ya bata goyon baya, a hankali ta fara haɗawa da snacks ɗin.
Wataran se Ammar ya dawo da daddare yake temaka mata ta haɗa kayan siyarwar, saboda cikin ta ya tsufa.
Duk abun nan Sam Ammar besa mata ido akan abunda take samu ba, ba ruwan sa sannan babu abunda ya fasa yi na hidimar gidan sa.

*********************
Satin bikin Jabir ya kama akai biki aka sha shagali, aka yi ɓarnar dukiya, kamar yadda akayiwa Jabir Alƙawari aka bashi gida da mota, aka sake masa Aiki a kamfanin Mahaifin Fatiyya.
Sedai tun a ranar farko da ta tare Jabir ya gane Fatiyya tasan Maza, Amma ba shi da ikon magana ko dan wannan daular da'aka sa shi a ciki, haka nan ya haƙura bece komai ba.



Ammar sun gama sauke kaya a kasuwa, yana shirin tafiya Wani hamshaƙin Alhaji da suka gama sauke masa kaya, yasa aka kira masa Ammar,Ammar yazo suka gaisa.
Ammar a nutse yake sam baya wannan rawar jikin da sauran suke idan sunga Alhajin, Alhajin yace
"Dan Allah in ba zaka damu ba kuɗi nake so ka kaimin banki"
Ɗan zare ido Ammar yayi, shi dai yasan ba ma'aikacin Kamfanin Alhajin bane, kawai aikin sa idan ya shigo kasuwar za'a sauke kaya ya sauke a biya shi, Amma me yasa yace masa ya kai masa kuɗi banki?

Alhajin yace  "Dan Allah ka temaka, in bazaka damu ba, na yaba da hankalin ka ne, depositing kawai zakayi min, ga kuɗin can a mota, me kaimin ne baya nan, million biyar ne"

Kallon rashin yadda Ammar yake wa Alhajin, Alhajin ya miƙa masa mukullin motar, jiki a saluɓe Ammar ya karɓa yakasa cewa komai, Ya rubuta masa Account details ɗin ya bashi. Hakanan Ammar ya tsinci kansa da kasa musawa Alhajin saboda dattijantakar sa.

Ammar ya kai kuɗin ya karɓo receipt ya dawo kasuwa Amma Alhajin baya nan ya fita amma ze dawo.
Ammar ya zauna ya jira ko gurin tasa sana'ar beje ba, se bayan la'asar sannan Alhajin ya dawo, yana zuwa ya tarar da Ammar, yace
"Yi haƙuri Ammar, na zaunar da kai, da kasani ka tafi, ka kawomin  receipt ɗin daga baya"
Ammar yace  "A'a gara dai dana jira, gashi, kuɗin million bakwai ne ba biyar ba"
Ya miƙa masa receipt, yasa hannu ya karɓa ya dinga juya receipt ɗin yana kallon Ammar, yana nazarinsa, yace
"Nagode sosai Ammar, na ɗauka " ya zura hannu a Aljihu ya ɗakko bandir ɗin kuɗi naira dubu ɗari ya bawa Ammar.

"A'a bazan karɓa ba, ba seka biyani ba"

"Ammar ba biyan ka nayi ba, kyauta ce fa"

Girgiza kai Ammar yayi yace "Nagode, Amma ka barsu" daga nan ya juya ya tafi.





Jabir ya fara gane kuskurensa, dan satin Fatiyya biyu bata girki sedai suci takeaway, ga yawo kamar masifa, bashi da ikon ya tambaye ta ina taje? Ko ina zata? Data raya mata seta fice abun ta, sekuma ya ganta, be isa tayi abu yayi magana ba seta balbale shi da masifa, ga rashin kunya da ƙazanta, zata gyara jikin ta Amma banda mahallinta, ga gayyar ƙawaye kowa ƙawar ta ce, Abun duniya ya fara damun Jabir, da yana ganin Saima bata iya komai ba, se gashi Fatiyya kamar rainon gaɓaye jaka take, ko magana bata iya ba, ga rashin kintsi.



A hankali Alhaji Haruna yake karantar Ammar, Ammar ba ruwan sa da kowa, da yaje kasuwa abunda ya kaishi kawai yake yi, dan ko Abokai bashi da su.

Alhaji Haruna duk lokacin da ya tashi Aiken kuɗi seya aiki Ammar, kuɗi bana wasa ba maƙudan kuɗi masu nauyin gaske.

************* *********

Ammar kafin ya fita se yayiwa Mufeeda aikin gida, da daddare ma idan ya dawo haka, wataran kuma ya kira Halima a waya yace tazo ta taya
Mufeeda aiki, Ammar yace idan cikin ya cika wata tara ze maida ita gida koda Naƙuda zata tashi baya nan.

Ranar data shiga wata na tara, Cikin dare kusan ƙarfe biyun dare labor ya kama Mufeeda, tashin Ammar tayi a gigice tana jin ciwon har cikin kanta.

Gaba ɗaya Ammar ya ruɗe, tausayinta ya kama shi, kamar ze kuka yace  "Sannu Mufeeda, bari in fita inga inda zan samo abun hawa"
Riƙe shi tayi gam ta hana shi fita ko ina, se salati take, vest ɗin Ammar kuwa da ta riƙe ta seda ta tale har cikin sa.
Ta dinga sintiri a ɗakin, Ammar ya kasa fita, gani yake daya fita wani abun ze sa meta, se Addu'a yake Allah ya raba ta da cikin lafiya, tun tana iya tafiya harta durƙushe tana ambaton Allah.
Waya Ammar ya ɗakko a gigice yana ƙoƙarin kiran waya, kawai yaji kukan Jariri yana ɗaga kai yaga Mufeeda ta haihu yaro Jariri yana ta tsala kuka.

Jifa yayi da wayar ya taho kanta da sauri, ya riƙo hannun ta yace
"Sannu Mufeeda" murmushi tayi masa tare da gyaɗa kanta, ta nuna masa Akwatin da ta shirya kayan haihuwar ta, kamar yadda Mama ta gaya mata, ta nunawa Ammar yadda ze yanke cibi da komai.
A ƙarshe dai Ammar ne ya gyara komai, hatta kayan jinin data ɓata da ɗakin shi ya zage ya gyara su tsaf.
Dama Mama ta koyawa Mufeeda komai, in case haihuwa zata ka mata babu wani a kusa.

Kamar ba Mufeeda ce tayi labor ba, ya dafa mata ruwa tayi wanka ta kintsa jikin ta, Jaririn ƙato dashi se kuka yake yi.

Haka Ammar ya rungume Mufeeda da Jaririn yana godiya ga Allah, wai Yau ƙwailarsa ce ta haifa masa Jariri, waze maka wannan kyauta inba Allah ba, Ga mace ta gari ga ɗa.

Da safe duk wanda suka kira suka ce Mufeeda ta haihu se yaita mamaki, Mussman idan akace ita kaɗai ta haihu, kafin kowa yazo gidan Ammar ya share ko ina ya dafa Abinci taci.

Da Mama taje gidan tayi mamaki taga ko ina tsaf, Mama tace
"Auta dan Allah ke kaɗai kika haihu?"
"Hajiya Mama kenan, wallahi da gani se Yaya Ammar, Allah ya bani da sauƙi ko ciwon mara da kikace banji ba lokaci ɗaya ciwon ya taso min cikin dare"
"Sannu Autar Mama, ga farfesu nan na taho miki dashi ki samu kici"
"A ajiye se an jima, Yaya Ammar ya dafa Abinci naci"
"Ikon Allah, lallai Allah yasaka wa yaron nan da Alkhairi"

Kwana uku da haihuwa Ammar ya shigo da wata ƙatuwar Akwati, wanda suke ɗakin Mufeeda suka fito suka basu guri.
Ammar ya kalle ta yace "Ƙwaila ta Ammar"
Ta tura baki tace
"Ai wallahi na zama mace, tunda na haifi wannan me kukan"
Murmushi yayi yana jan hancin ta, ya turo mata Akwatin gaban ta, ya karɓi yaron ya kwantar da shi, Sega Ammar yana ɗaukar Jariri, da baya ɗauka dan gani yake yayi ɗan mitsitsi dayawa.

Cikin Mamaki ta buɗe Akwatin, kayan Jariri ne, duk abunda ake buƙata kayan wanka diapers ba abunda babu, itama ga sabon kaya kala uku da turaruka da sabon takalmi da Jaka.

"Kayan robobin kuma suna ɗakin tsakar gida, na siyo fulawa da shinkafa, abun hakika kuma Abba ya bayar, sannan kuɗin da muke tarawa na bar miki nawa da nakin, seki haɗa ayi hidimar suna"

"Yaya Ammar, ina ka samu kuɗi haka muna fama da kanmu? Yaya Ammar meyasa ka takura kanka"

"ba takura bace, haƙƙina ne inyi, kuma na daɗe ina tara kayan, Anty Maryam nake bawa kuɗin ta siyo, fatana Allah ya barmin ke, sannan ya raya mana Ibrahim Khalil a tafarki madaidaici ina Alfahari dake Mufeeda"

Rungume Ammar tayi tana kuka tace
"Allah ya ƙara Arziki Mijina, Allah ya baka abunda kake nema duniya da lahira, mungode, mungode, we loves you Abu Khalil"

"Mentioned it not sweetheart, ni yakamata inyi godiya"

Ta tattare kayan ta kira Mama tace "Mama ku tayani godiya, kinga siyayyar da Yaya Ammar yayi mana"

Nan ma Mama taita Addu'a da saka Albarka.

Yaya Fadeela tace  "Mufeeda gaskiya ki bani sirrin wannan soyayya haka, Allah sarki nan muka dinga surutan kinyi ƙanƙanta da Aure yayi miki girma, kawai se mu gaki da ɗa, ohh Auta manya"

Mufeeda tace  "kyaji dashi dai"

********************

Abun duniya ya ishi Jabir, Fatiyya tasa shi gaba da rashin mutunci ga gori na masifa, gashi ba damar ya kai ƙararta gidan su, ba akaiwa iyayen ta ƙara ɗan su, gantali ga
Almubazzaranci, daga iyayen sa har 'yan uwan sa basu isheta kallo ba.


Ɗaure take da towel ta fito daga cikin banɗakin dake cikin ɗakin hotel ɗin, ta kalli mutumin dake kwance akan gado yayi ɗaiɗai, ta ɗan yamutsa fuska tace
"Alhaji ka tashi kayi wanka ka maida ni inda ka ɗakko ni, bana jin daɗi"
Washe baki yayi yana shafa cikin sa yace
"Fatiyya manyan mata, nifa banƙi mu kwana anan tare ba"
Haɗe rai tayi tace "Kafiye wasa, dan Allah ka tashi jini nake zubarwa fa"
Zaro ido yayi yace
"jini kuma? meya haɗa ki da zubar da jini?"
"Inaga ciki ne dani fa, kamar ɓari zanyi"
Alhaji Idris yace "ke se kace ba wayayyiya ba, tun abaya da muke tare da ke baki yi ciki ba se yanzu? Daga yin Auren seki bari kiyi ciki"
"Kaga nifa ban san da cikin nan, dan Allah kayi ka maidani, dan banzo da mota bane da bazan tsaya jiran ka ba"
"Kai Amma ban gama shagali na ba kin katsemin jin daɗi"
"Koma meye ai kaine ka janyo shi, dan Allah Alhaji Idris kayi sauri"

Haka ya tashi ya shiga yayi wanka, sedai me yana fitowa ya tarar da ita a kwance kamar ba rai a jikin ta jini ya malale a gurin.

A gigice ya zaro ido, ya dinga jijjigata yana kiran sunan ta Amma shiru, bata Amsa ba, da gudu yasa rigar sa ya fice, fitar tasa tayi dai2 da kawo Abincin da suka yi order, yaga Alhaji Idris ya fice da sauri, da sauri ma'aikacin yabi bayan Alhaji Idris yaga ya shige mota ya, aikuwa ya haddace lambar motar sa.
Ya koma ɗakin ya tarar da Saima a kwance cikin jini male male.



Ranar suna Jariri yaci suna Ibrahim Khalil, Dai2 gwargwado anci ansha, Ammar yayi bajinta daidai ƙarfin sa.
Mufeeda ta samu Alheri sosai.
Anty Murja ce ta zaunawa Mufeeda saboda jego, Sam Ammar da Mufeeda basa jin kunyar Anty Murja, su barta da rainon ɗa su shige ɗaki suyi ta cin dariyar soyayyar su, Anty Murja tayi mamakin yadda Ammar yake barkwanci da dariya haka, yadda yake haɗe rai da miskilanci idan za'ace yana magana ma seka Musa, Amma wataran a falo suke soyayyar su shida Mufeeda, ba ruwan su da idon Anty Murja.

Ranar da Ammar ya koma kasuwa Alhaji Haruna yasa aka kira masa shi, Ammar yaje suka gaisa.
Alhaji Haruna yace  "Ammar kwana biyu baka shigowa kasuwa lafiya kuwa?"
"lafiya ƙalau, me ɗakina ce ta haihu shiyasa"
"Masha Allah, Amma babu Labari, Allah ya raya abunda aka samu, Amma gaskiya zanzo har gida in ga Jariri"

Ammar yace "to Nagode sosai, Allah ya kawo ka"


Bayan Alhaji Idris ya bar hotel ɗin nan ya gudu ya bar gari, yana ta shirye2 barin ƙasar aka kira shi a waya aka sanar masa hukumar custom sun kama kayan da yayi order, Nigeria bata buƙatar irin wannan kayan, gaba ɗaya ya gigice ya rasa abunyi, gaba ɗaya dukiyarsa ya narka akan kayan nan Amma wai custom sun kama kayan.
yana ƙoƙarin kiran abokin
kasuwancinsa 'yan sand suka zo suka kama shi a gurin.

Jabir ya shiga tashin hankali jin A hotel aka ga matarsa tayi ɓari, kuma abokin iskancin nata ya gudu, Jabir yayi kuka, dan yasan Alhakin Saima ne ya kama shi.

Ya shirya ya tafi gidan Gwaggon Saima, yasa aka yi masa Sallama da ita, ba tasan ko waye ba ta fito, tana ganin Jabir ta haɗe rai tace
"malam me kake mana a ƙofar gida?"

Jabir ya fashe da kuka yace
"dan Allah Saima kiyi haƙuri ki yafemin, Alhaji kine yake ɗawainiya dani, dan Allah kizo mu koma mucigaba da rayuwar mu, wallahi na canza hali"

"Allah sarki, kuma gashi ka makara, dan ko baka makara ba babu ni babu komawa gidan ka, sedai ina maka Albishir ranar Asabar za'a ɗauramin Aure, zan Auri sirikin ka wato mahaifin Saima, sedai ni ba Auren Jari zanyi ba"

Ta juya ta shige ta bar Jabir a tsaye, abun takaici yana komawa gida ya tarar da Saima yai mata rashin mutunci yace tabar masa gidan sa tace sedai ya bar gidan, dan gidan uban ta ne bana uban sa ba. Jabir yai mata saki uku sannan ya bar gidan.

Baban Fatiyya ya shigar da ƙarar Alhaji Idris akan ya sace masa 'ya yai mata Fyaɗe, aka hana shi kare kansa yanaji yana gani aka kulle shi.

Bayan ya Auri Saima haka Fatiyya ta koma gida, duk yadda babarta take juya mahaifin ta ƙarshe' yan kallo suka zama dan se abunda Saima take so akeyi.

Alhaji Haruna yaje gidan Ammar yaga Jariri yayi masa Addu'a sannan yace
"Ammar babban dalilin zuwa na gidanka shine, A baya na jarrabaka gurare daban daban, Na lura kana da Amana sannan ka birgeni saboda rashin girman kanka da Amanarka, wadda tayi ƙaranci a yanzu, shi ne nace Akwai branch da zan buɗe na saida kayan masarufi da nake yi, zan zuba kayan million Ashirin, ka riƙe gurin ka ɗau ma'aikata ku riƙe gurin, idan shekara tayi zaka dinga raba riba biyu kana biya na, a hankali har shagon ya zama mallakinka"

Zare ido Ammar yayi yace  "Aini ban taɓa kasuwanci ba, ta yaya zan iya juya dukiya me yawa haka?"

"zaka iya Ammar, ina so in taimake kane, dan a rayuwa ta ina son inga na temaki na ƙasa dani shima ya tsaya da ƙafar sa, na jinjina maka dan har unguwar nan nazo nayi bincike akan ka naji daɗin yabon da naji ana maka"

Ammar yayi shiru yace  "to zamuyi shawara da Madam, abun da muka yanke shikenan"

Alhaji Haruna yayi murmushi yace  "Kai wannan Madam ana ji da ita, ko dai in baka 'yane, naga ka iya riƙe gida"

Ammar yace "daga ita ba ƙari ai"

"shikenan Ammar, da wasa nake maka, sena jika"

Mufeeda tayi farinciki da jin labarin, tace
"Yaya Ammar mahaƙurci mawadaci, wataƙila da sana' ar A daidaita sahu kake ba lallai ka samu wannan Ni'imar ba, Ammar da yake Allah me hikima ne, seya raba ka da Napep ya maida kai kasuwa, yanzu dai muyi ta istikhara tukuna inda Alkhairi Allah ya tabattar, sannan kayi shawara dasu Abba "

Haka kuwa akayi, bayan yin Addu'oi da Neman shawara, Ammar ya Amince ya karɓi shagon, Allah yasanya masa Albarka ya dinga ciniki, nan da nan Ammar ya zama hamshaƙi.

Da Khalil ya isa yaye, ya kaiwa Umma shi ya nemo wa Mufeeda Admission, ta shiga makaranta, seda Ammar ya cika Alƙawarin da yayi wa Baba akan karatun Mufeeda.

A hankali Ammar ya gama biyan Alhaji Haruna kuɗin sa, shagon ya zama mallakin sa, ya canza gida ya sai mota, kullum cikin neman taimako ake a gidan Ammar, duk me wata buƙata in dai ya biyo ta gurin Uwargidan Ammar anyi ta an gama, dan Mufeeda bata taɓa cewa abu yaƙi, 'yan uwa da abokan Arziki babu wanda baya morar Arziƙin Ammar.

Faruk ya haɗu da ciwon sugar, gaɓoɓin jikin sa suka dinga gutsurewa suna zubar da ruwa.
Fa'iza kuwa har shekara talatin babu wanda ya Aure ta.

Ammar ya zama hamshaƙin ɗan kasuwa, ya buɗewa Mufeeda Ƙaton gidan gona, aka ci gaba da yi mata kiwo, ta zama wata uwar mata.

A duk lokacin da aka tashi yin interview da Ammar, idan aka tambaye shi meye matakin Nasarar ka a rayuwa? Waye wanda kake kwaikwayo, waye ya baka ƙarfin gwiwa akan harkar kasuwanci? Amsar ɗaya ce yake bayarwa
"Mata tace"

Duk lokacin da ya zauna zeyi misali se ya bada misali da Mufeeda, ya kance "A baya ina raina Mata, ina ganin babu macen da zata iya sauyamin ra'ayi, seda na Auri Mufeeda na gane 'WATA KISSAR SE MATA' Allah yayi musu baiwa da hikima, na sarrafa zukatan maza, idan Allah ya baka mace tagari kamar Mufeeda ka gode Allah, dan Mufeeda 'yar Aljanna ce Insha Allah "

Mufeeda ta haifawa Ammar yara huɗu, seda ta zama professor akan harkar sadarwa, mata da yawa sukanzo mata da matsololinsu ta basu shawara, mussman take gabatar da shirye2 a kafafen watsa labarai, sannan ta mallaki personal blog ɗinta da take wayar da kan mata akan sha'anin zamantakewa.

Kullum a kamata tambaya ko zata bada misali da Ammar take bayarwa
"Mijina ɗan Aljanna ne Insha Allah, da dukkanin maza zasu sauke haƙƙoƙin dake kansu, su kuma mata suyi biyayya da tabbas mutuwar Aure zata ragu, kuyi koyi da hali irin na Alhaji Ammar"

Ire iren wannan hirarrakin nasu yana matuƙar burge mutane.



Tammat bihamdillah, Masha Allah, Alhamdilillah, Rabbigfir zanbi kullahu, diƙƙahu, wa jillahu, sirrahu, wa alaniyatuhu.


ANAN NA KAWO ƘARSHEN WANNAN GAJEREN LABARIN ME SUNA WATA KISSAR... SAI MATA, INA FATAN AN AMFANA DA DARUSAN DAKE CIKI.
ABUNDA NA RUBUTA NA DAIDAI DAGA ALLAH NE, AKASIN HAKA KUMA DAGA NINE INA FATAN ALLAH YA YAFEMIN.

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

Haɗaɗen littafin nan dana fara kawo muku na dakata da kuka daɗe kuna jira me suna AƘIDA TA insha Allah yana nan tafe a watan September, ku kasance tare da Alƙalamina domin jin me littafin ke ɗauke dashi, idan kina daga cikin wanda basu karanta littafin ABDUL JALAL ba kuwa, to ki garzaya ki nemi naki, domin jin cakwakiyar dake cikin sa, Insha Allah bayan AƘIDA TA, Akwai sauran daɗaɗan litattafan da suke daf da isowa gareku domin faɗakarwa, da nishaɗantar da ma'abota fahimtar wannan harshe namu na Hausa.


Karku manta link ɗin voting na zaɓen gasar dana shiga yana nan tafe, ina fatan zakumin kara in lokaci yayi ku zaɓi labari BAƘIN TABO gajeren labarin gasa



Ina buƙatar jin ra'ayoyinku akan wannan littafi dana kammala, domin gyara, sharhi, ko kuma shawara, kai tsaye a tuntuɓeni ta wannan lambar

Ayshercool
07063065680


Ku asancni a cikin sabon littafina da zd e zo muku a 1st september insha Allah mai suna AƘIDA TA



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it

Please Login or Register in order to submit comment