Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kanta babu ɗankwali se bakin ta da take shan sweet.

Ammar yace "Ya haka?"

"Na kasa bacci, kuma naji kana kallo shi yasa na fito"

Ammar kaman ze kuka yace
"kinga ɗagani banyi shafa'i da wuturi ba"

"in muka gama kallon base kayi ba"

"waike baki san yanzu lokacin sanyi bane? Ba'a son yawan taɓa ruwa ba?"

"to ba se in dafa maka ruwan alwala ba"

A ransa yace "wannan 'yar yarinyar in banyi dagaske ba yauma seta hanani bacci"

Dan haka ya haɗe rai yace
"Malama ki ɗaga ni"

Maimakon ta ɗaga shi, sema ta gyara zaman ta ta miƙe ƙafafuwan ta akan nasa, kaman yadda yayi ta jingina bayan ta a ƙirjinsa ta ci gaba shan alawarta da zuwa yanzu bakin ta ya zama ja jawurrr saboda kalar alewar.

Daskarewa yayi a gurin ya kasa magana balle ya motsa, lallai yau ya ƙara tabbatar da tsagwaron yarinta akan Mufeeda, Ammar yayi ƙam dashi kaman gunki, sun kusa mimtuna goma a haka, ko a jikin ta kallon ta kawai tame.

Ta fara taune alawar nan a bakinta, sekuma ta janye ƙafafuwan ta ta juyo ta kalle shi tace
"Au naman ta ban maka bismillar alewa ta ba gashi na taune ta, bari in tafi dan na fara jin bacci"
Ta miƙe da nufin ta tafi amma ba zato ba tsammani Ammar ya janyo ta.

Abunda yayi ne yai matuƙar bata mamaki, dan ko a mafarki batayi zaton hakan ba.

Seda Ammar yasa baki ya shanye alawar da ta tauna a cikin bakin ta tsaf, sannan ya cika ta ya miƙe kamar beyi komai ba ya wani maze ya haɗe rai yai tafiyar sa ɗakin sa

(🙄🙄 to su Yaya Ammar manya)





Ashe dai kuna son littafin nan haka? Ai ban sani ba seda nayi tsallaken update na rana ɗaya nasha tambaya.
To yaseen in ba Comments posting se Allah ya kaimu Monday.
Ina godiya masoya da addu'oinku da kuma shawarwari.

Domin gyara, sharhi ko shawara ƙofata a buɗe take
Ayshercool
07063065680
✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

     

ELEGANT ONLINE WRITER'S

             

           

                  

                        Page 17



Binsa tayi da kallo har ya shige ɗakin sa, tashi tai ta koma ɗakin ta, tana ƙara mamakin abunda Ammar yayi mata.

Da safe harta tashi ta gama breakfast be fito ba, tana ƙarasa gyara gida ne ya fito yana wani basarwa, Mufeeda ta kalle shi tace
"barka da Safiya Babban Mutum"

Be amsa ba se jinjina mata kai da yayi, ya nemi guri ya zauna, ya fara breakfast ɗin sa yana wani mazewa, murmushi take yi tasan abunda ya faru jiya ne yasa yake ta wannan basarwar.

Seda ya gama ta koma kusa dashi tace "Hubby kalli lalle na yayi kyau kuwa?"
Kallon hannun yayi da zuwa yanzu ya fara zama maroon, ya gyaɗa mata kai, amma bece komai ba.

Ta kawo masa breakfast ɗinsa ya fara yi, yanayi yana wani mazewa gaban sa taje ta zauna ta zuba masa ido ya ɗago idon sa ya sauke a nata yace

" Se kinsa na ƙware kike min wannan kallon haka?"
"A'a bazaka ƙware ba, kallon Soyayya ne sedai ka ƙara jin daɗin Abincin, A bani a baki mana duk randa ka ciyar da ni da hannayen ka masu tarin Alkhairan nan nafi ƙoshi fa"

Hararar ta yayi yaci gaba da antaya loma, tayi ƙasa da murya tace
"haba Autan Abba mijin Autar Baba, ba dan halina bafa kaga ni Yarinya ce zanyi maka kuka fa"

"ga guri nan maza zauna kiyi kukan, tunda ke a rayuwar ki Kuka kamar jin daɗin sa kike yi"

Tura baki tayi ta riƙe hannun sa

"dan Allah baby ka bani a baki, nice fa Jaririyarka ce seka barni da yunwa?"

Kallon ta yake yadda take ta zuba taɓara.

Ammar ya haɗe rai yace
"kinga idan baki bari ba zan tashi yanzun nan in bar miki gidan"

"Allah in baka bani ba zanƙi cin Abincin yau"

"to karki ci mana cikina ko naki?"

"cikina ne, Amma ni bazan iya zama ina kallon abun ƙauna ta beci Abinci ba, dama nasan baka sona"

"Dama na taɓa cewa ina sonki ne?"

"Baka taɓa cewa kana sona ba, Amma nasan ana sona ko ba a gayamin ba na riga na sani"

Kallon ta yayi ta ɗago itama ta kalle shi tare da kashe masa ido.

"Ni dai bance ina so ba, saboda a yanzu dai raino kawai nake yi, ni banga abun so a gurin ƙwaila ba, banda rawar kai da Yarinta babu abunda kika iya"

Ta gyaɗa kai tace "Shikenan nagode, Nikam har zuciya ta idan nace ina sonka, to ina nufin abunda na faɗa"

Ta miƙe ta koma kan Kujera tai shiru, ƙarshe ma ta kwanta ta rufe idon ta, Yanayin yadda yaga ta yine ta ɗan bashi tausayi, Amma dai bece mata komai ba ya kammala breakfast dinsa, kaman ya miƙe yaje yai haramar Fita, se yaga be kamata ya tafi ya barta tana fushi ba duba da Yadda take shiga damuwa idan taga baya walwala.

Hannunsa ya Miƙa ya ɗan ja yatsan ƙafar ta, a hankali ta buɗe ido ta kalle shi,
"Sakko in baki Abincin, kar inje kice bana baki Abinci"

Ba tace komai ba ta Sakko tazo gaban sa ta zauna, Yanayin Fuskarta ya nuna ƙirirs take jira tayi kuka, dan ba ƙaramin haushin abunda Ammar ya faɗa taji ba.

Ya haɗa mata abun karyawa ya kalleta yace "dawo nan" ya nuna mata inda zata zauna daf dashi, ta matsa ta zauna ya fara bata Abincin a baki tana ci.

Ya ɗan girgiza kai yace "Rigumammiya kawai se kace 'yar Yaye"

Tura baki tayi tana sosa gefen fuskarta, tamkar irin shagwaɓaɓɓun Yaran nan.

"Na ƙoshi fa"

"kin ƙoshi wa kike nufi ya cinye ragowar ki?"

"To ai na ƙoshi cikina ya cika"

"ɗan wannan Abincin ne kika ƙoshi, oya buɗe bakinki ki cinye sauran"

"Allah in kace se naci zan iya yin Amai"

Haɗe rai Yayi yace "kenan ɗan wannan Abincin kikeci shiyasa ba kya ƙiba, sekin cinye"

Hannu tasa ta ɗaga rigarta tace "kalli fa cikina ya cika sosai"

"Nagani rufe" ta sauke rigar ya ɗan ƙura mata ido sannan yace
"Allah ya shirye ki"

"Mekuma nayi?"

"A'a bakomai Addu'a kawai nayi miki"

Ƙarshe Ammar ne ya tattare Kwanukan, dan yau rikici take ji sosai.

Yana shirin fita ne yaro yayi Sallama da yake yau gidan a buɗe yake, Mufeeda ta amsa ta fito tsakar gida, ta kalli yaron tace

"Ya akayi ne?"

Ya miƙo mata kofi yace "wai gashi inji Umman mu wai dan Allah ki ɗan zuba mata madara da milo zata sha tea, idan kina da Butter ki ɗan san mata taci bredi"

Mufeeda tace "ayya ka koma kace mata dan Allah tayi haƙuri, bani nake siyan kayan ba, me gidan ne yake siya kuma bana bayar da abu seda izinin sa"

Yaron yace "to" ya juya ya tafi.

Ta koma falo tana tsaki,Ammar da yaji yadda suka yi da Yaron yace

"Meyasa baki basu ba? Kefa kikace abunda ka bayar shine rabon ka"

"hmm Yaya Ammar kenan, ina sane na hanasu, kai baka san wannan rainin hankalin na wasu matan ba, ranar suka shigo nan suka nemi su rainamin hankali dan sun ganni ƙarama, Yanzu dana basu shikenan sun Sami gurin zuwa, duk abunda ka siyo tare zamu yi amfani da shi, duk nasan irin wannan abubuwan tun a unguwar mu"

Ammar yace "Kinga kowa rainaki yake saboda ke Baby ce, kowa yana miki kallon Yarinya, waini gayamin ma me yasa kika ce kina son Aure ne a shekarun nan naki?"

"Saboda nima Mutum ce, kuma ina son kasancewa da abunda nake so, zuciya ta ta makance bata ganin kowa a wannan lokacin in ba kai ba, ni dai nasan ina sonka sosai, kuma bazan iya cewa ga dalilin da yasa nake son naka  ba, koda yake na maka ƙanƙanta kuma baka sona amma shi so babu ruwan sa, karka makara rana ta fara yi fa, Adawo lafiya "

Ta juya ta koma ɗakin ta, Shiru Ammar yayi na wani ɗan lokaci daga baya ya miƙe ya fita sam beji daɗin yadda sallamar su ta kasance yau ba duk se yaji babu daɗi.

Koda yaro ya koma ya gayawa Maman sa Saƙon Mufeeda take bala'i
"Jimin 'Yar matsiyata babu a house anzo gidan miji an samu shine zata yiwa Mutane Iskanci, bata san mune masu unguwar ba, in ba tayi wasa ba sena sauke mata wannan wulaƙancin da take ji dashi se zaman unguwar nan ya gagare ta" haka ta zauna ta dinga mita tana Masifa.

Daga ƙarshe dai haka ta saka Mayafin ta ta fita yin cefane, gurin me kayan miya taje ta tarar da mutane sosai a gurin ta samu guri ta zauna. Seda ya ɗan sallami Mutane sannan ya kalleta yace
"uwar biyu me za'a zubo miki ne?"

Ta gaya masa abunda ze haɗa mata, sunayi suna hira da Sa'idu me kayan miya.

Sa'idu Yace "Amma Maman Nur wannan ne watan haihuwar ki naga da ƙyar kike tafiya"

"Wallahi kuwa sa'idu a wannan watan nake sa ran haihuwa duk na gaji da cikin nan wallahi"

"Ai se haƙuri tunda kin kusa saukewa, mudai fatan mu ki haihu Asha suna muci shinkafa"

"Hmm Anya shinkafar nan kuwa, ai abun se Addu'a kasan Baban Nur da wulaƙanci wani lokacin, yaci basussuka sun masa Yawa, muna ta rigima da shi akan abunda ze bani na taro waishi bashi da kuɗi, ni ko ba abunda ya dameni so nake in fita kunya, kaga su Maman Amir ɗin nan ba ƙananan munafukai bane, Alla Alla suke in haihu suga abunda zanyi kallon su kawai nake, ina zan bari suga walle na"

Sa'idu yace "gaskiya kam be kamata ba"

Yana cikin haɗa mata kayan miyan ne sega Maman Amir itama tazo yin cefanen.

Suka gaisa ta kalli Maman Nur tace "Maman Nur ina su Nur ɗin kika fito cefane da kanki?"

"wallahi suna makaranta, ga gidan ba kowa kin ganni ko karyawa banyi ba na fito kafin kayan miyan su ƙare"

Maman Amir tace "maman Nur kidena zama da yunwa fa, kina ɗauke da ciki kina wasa da Abinci"

Me kayan miya yace "gaya mata dai"

"Hmm kin san me maƙwaciya ta tayi min? Wai na aika ta sanmin Milo in sha tea, amma ta hanani"

"Haba dai ke dama seda na gaya miki Yarinyar nan ba Mutunci za tayi ba"

Me kayan miya yace  "Wai wace Yarinyar ce ne?"

Maman Nur tace "wata 'yar mitsilar Yarinya ta jikin gida na, matar wannan me a daidaita sahun, banza bata saba sha a gida ba, anzo birni ana iskanci"

Suka haɗu suka dingayi da Mufeeda suka zage ta tsaf a teburin me kayan miya
(Mata kenan Allah ya shirya)

*********************

Yau Ammar be dawo da azahar ba, se bayan sallar isha'i ya dawo, ya ɗauka ze dawo ya tarar da ita yadda ya barta amma yana dawowa ta ɗan tsuke fuska cikin shagwaba tace
"shine se yanzu ko? Ina ka tsaya yau baka dawo da wuri ba?"

"inda kika aikeni" ya bata amsa

Tayi murmushi tare da duƙar da kanta tace
"Allah ya bada haƙuri, Allah ya huci zuciyar Manya"
Ɗan Murmushi yayi yace
"ban Abinci, tunda na fita banci komai ba"

"Bana hana zama da yunwa ba?". Tai ƙasa da muryar ta tace "idan aka ƙara se nayiwa mutum abunda baya so"

Ya kalleta yace "Mene bana son?"

"Idan ka kuma zanyi ka gani, ko in maka tausa ne? Naga ka gaji da yawa"

Da sauri yace "A'a bana so"

"Tausar tawa ce baka so? Zaka rage jin gajiyar"

"A'a nagode kawomin Abinci inci, ina so mu ɗan fitane zaki rakani unguwa"

Ta kawo masa Abinci shima ta nayi tana damun sa.

"Yaya Ammar naga kaman gemun ka ya ragu fa"

"Eh na rage sumar kaina ne, akamin gyaran fuska"

"to kuma se a rage maka gemu?"

Ɗan tittiraza ƙafa tayi tace "Ni gaskiya dan Allah kar a ƙara rage wa, haba dan Allah ni ina son gemun fa"

" zanje kuwa a aske shi gaba ɗaya"

"da bazan ƙara kallon ka ba se ya fito" tai maganar tana miƙewa.
Seda ya kammala cin Abincin sa sannan suka shirya zasu fita ya kalleta yace
"Idan anyiwa mutum haihuwa me ake bashi?"
"Waye ya haihu?" ta tambayeshi

"Matar Aminu ce ta haihu har anyi suna ma, ni namanta ya gayamin"

Mufeeda ta jinjina kai tace "zaka iya sai musu rigar Baby, Amma riga tana tsada sosai indai me kyau kake son basu, amma kaman ka basu kuɗin kawai ina da turaren wuta, se in bata nima"

Ammar ya jinjina kai sannan suka gama shiri sannan suka fita.

Kaman haɗin baki suna zuwa suka tarar da Saima da Jabir a gidan.

Saima na ganin Ammar tare da Mufeeda tace
"Gaskiya munji kunya, kamar in gudu yau gani ga Amaryar Ammar ban taɓa zuwa ba"
Fiddausi tace "Ai nidai zatamin uzuri saboda nayi nauyi ne lokacin"

Mufeeda dai ba tace komai ba se Murmushi da take yi ta zauna suka gaisa da su Aminu da Matansu.

Aminu yace "Ammar se yau zaka zo kaga Jaririyar ko? Yau kwana tara da haihuwa"

Ammar yace "to komu koma ne? Ai badan Fiddausi ba ba zanzo ba, kai kaje gida nane?"

Aminu yai murmushi yace "Allah ya bada haƙuri"

Tunda suka zo Jaririyar take kuka, aka miƙawa Ammar Jaririyar, Amma sam be iya ɗaukar Yara ba, yanayin yadda ya riƙe yarinyar kasan be iya ba.

Mufeeda taje kusa da shi tace "Yaya Ammar ai ba zata yi shiru a haka ba, kalli yadda ka ɗauke ta fa, kawo ta ka gani" tasa hannu ta karɓeta, tana jijjiga yarinyar amma ba ta dena kuka ba, wuyan Yarinyar yayi ƙananan ƙuraje saboda zafi kuma yarinyar nada jiki, Mufeeda tace
"Maman Baby dole taita kuka fa, zafi take ji"

Mufeeda ta cirewa Yarinyar kayan jikin ta, ta shafe ta da Hoda sannan ta ki fata akan cinyar ta tana shafa bayan ta tareda jijiya yarinyar, shiru Yarinyar tayi dukda ba bacci take ba, Jabir yace

"Ikon Allah, To ke Fiddausi ya akayi baki iya raino ba, Mufeeda karki yadda ko koya masa yadda ake raino in bahaka ba idan naku Babyn yazo kudinga yi tare"

Saima tace
"Mufeeda kina son Yara Allah yasa nan da 'yan watanni muzo mu ɗau naki"

"Taɓɗijan nima Yarinya ce har yanzu rainona ake, ban isa inyi raino ba"

Tai maganar kaman' yar Yarinyar, Ammar ya Harare ta, ita kuma tai masa Murmushi, Jabir yace
"Babbar magana"

Aminu yaja su Ammar suka koma part ɗinsa suna hira, suka bar su Mufeeda a tare.

Ammar yace "Jabir ya batun matsalar ka da Saima kuwa? Ina fatan yanzu komai ya daidaita"

Jabir yace "ba dai komai ba, Amma da ɗan sauƙi"

Aminu yace "Jabir kenan, ai kamata yayi komai ya daidaita ka dena wayar da 'yan matan kokuwa?"

"A' a fa inayi amma na dena yi a gida sosai, zamana nake a waje insha wayata sannan in dawo, dukda haka shima be mata ba ƙorafi take"

Nasihar dai suka ci gaba da yiwa Jabir.

Mufeeda ta ɗan saki jiki da su Saima suna hira Sama sama, Saima tace
"Nima Allah ya nuna min na rabu da nawa cikin lafiya, amma ina jin tsoron haihuwa"

Fiddausi tace "Wallahi da wahala, amma in har kika kwantar da hankalin ki, kika kula da cimarki da shan magani zaki rabu da shi lafiya insha Allah"

Saima tace "Ai abunda yake bani tsoron be wuce duk lokacin da naje Awo se a cemin jinina ya hau ba, harfa sun ɗorani akan maganin hawan jini"

Mufeeda tace "Subhanallah, Allah ya sawwake kuma ba'a son hakan, Allah ya baki lafiya"

Fiddausi tace "Amma meyasa jinin ki yake hawa?"

Saima tace "to ya zanyi Fiddausi, nifa ba dan anyi test na gano da cikin nan ba to da sena kashe auren nan, nayi haƙuri ne saboda bana son Abunda zan haifa yayi irin rayuwar wahalar da nayi saboda rashin uwa a gidan, to yanzu ga hawan jini ina tunanin ko zanyi rai idan nazo haihuwar oho"tai maganar kamar za tayi kuka

Mufeeda tace "Amma Anty Saima meyasa zaki kashe auren ki? Naga Yaya Ammar yace min saura watanni bikin mu akayi naku"

Ajiyar zuciya Saima tayi tace "Bari Mufeeda babu komai a rayuwar Auren da nayi se nadama, Unguwar mu ciki harda mijin ki babu wanda be san soyayyar mu da Jabir ba ciki hadda mijinki, mutane na ganin tsaurin Ammar sosai duk cikin su ukun nan babu me sauƙin kan Jabir, ina ta murna nayi dacen Mijin Aure wanda ze sharen kuka na, Amma me bayan Auren mu komai ya canza, har ƙarfe biyu seya kai yana chatting, ko yaya nayi masa laifi se zagi da ashar yana cin mutuncin iyayena na rasa me nayi masa tun ina haƙuri na fara ramawa, ga gori wai ni 'yar matsiya ta ba akwoni da abun kirki ba, bayan Jabir yasan halin da nake ciki a gidan mu, a hannun kishiyar uwa na tashi kuma mahaifina bame ƙarfi bane, ya zama bani da mutunci a idon sa se dare yayi yana buƙata ta, na kasa jure cin mutunci da wulaƙanci da yake min na fara ramawa, na dena saurarasa na dena masa duk wani abu na biyayya kona kyautatawa baya jin ko ɗar ya wulaƙantani ko a gaban waye nima bana jin komai nake ramawa" ta ƙarasa maganar tana hawaye

Gaba ɗaya jikin Mufeeda yayi sanyi, tace "Anty Saima be kamata ki dinga biye masa ba, tunda kika riga kika yi Aure, idan kika kashe Auren kika koma gida baki da wata makoma a gida, idan har kukayi faɗa kika biye masa kikace sekin rama to tabbas kece zaki sha haushi, shi ze fita ya sha iska ya manta kunyi, amma ke kina gida ke zaki cigaba da shan takaici, kuma ƙin kula dashi zesa 'yan matan su cigaba da jansa a jiki, amma kiyi ƙoƙarin kwantar da hankalin ki kodan lafiyar ki"

Fiddausi tace "ni na rasa ma abun cewa"

Saima ta goge Hawayen ta tace"zan Jarraba Mufeeda, Amma abun babu sauƙi fa"

Suna cikin hirar ne Aminu ya shigo yace "Mufeeda Ammar yace ki fito ku tafi dare yayi"

Seda Mufeeda ta sake ƙanƙame Jaririyar kaman kar ta bayar, sannan tabawa Fiddausi ita, ta bata abunda zata bata na barka, sukayi Sallama Mufeeda ta fito.

Jabir yace "Gaskiya Ammar Amaryar nan tana son Yara, yakamata kuyi zuciya fa"

Banza Ammar yayi masa yace "Mukam seda safenku"

Sukayi Sallama suka fito, Ammar ya lura gaba ɗaya Mufeeda bata walwala dan tunda suka kama hanyar gida ko uffan bata cewa har sukaje, ya ɗauka kawai ta gaji ne tana jin bacci amma idan ya kalleta ta mirror se yaga kaman tunani take.

Haka suka koma gida gaba ɗaya bata walwala, suna komawa tace masa seda safe ta tafi ɗakin ta, gaba ɗaya halin da saima ke ciki ne ya hana ta sukuni, ta kwanta da nufin tayi bacci amma baccin ya gagara zuwa, ƙishirwa take ji dan haka ta fito dan ta sha ruwa, Ammar yana falo har wannan lokacin, kusan sha biyun dare ko me yake oho?

Bata kulashi ba, Seda taje ta sha ruwan ta dawo zata koma ɗakin ta, taji yace
"Zo ina son ganin ki"

Juyowa tayi jiki a sanyaye ta zo gaban sa ta zauna tare da sunkuyar da kai.

Ya kalleta yace
"Meke damunki ne?"

Girgiza masa kai tayi tace "bakomai"

"Kalleni, Bana son ƙarya, naga tunda muka taho mood dinki ya canza"

cikin sanyi jiki tace "Yaya Ammar I give up"

"you give up on what?"

"Duk yadda ake gayamin akwai ƙalubale a Aure ban zaci ya kai haka ba se yau da Anty Saima ta bani labarin Auren ta, ita da tai Auren Soyayya kenan, ni meye tawa makomar da ya kasance ni kaɗai nake son mijina, ina tunanin ni wani irin ƙalubale zan fuskanta, na karaya sosai har na fara tunanin dama banyi Auren ba"

Ta riƙo hannun Ammar tace "dan Allah Yaya Ammar idan saɓani yazo tsakani na da kai karkamin irin hukuncin da Jabir yakewa Anty Saima, bazan iya jure zagi ko in ganka kana mu'amala da wasu 'yan matan daba Auren su zakai ba"

Kallon ta yake yadda take sharɓar Hawaye sosai hadda sheshsheƙa.

Ajiyar zuciya yayi dan ba ƙaramin tausayi ta bashi ba, janyo ta yayi jikin sa, ta kwanta sosai akan ƙirjinsa tana ci gaba da kuka, a hankali yace

"Sunan sa Jabir, ni kuma Ammar dan haka ba lallai halin mu ɗaya ba, kinyi ƙanƙanta da fara damuwa ko tunani, ki sha chocolate ɗinki kiyi wasanki kiyi bacci kawai shi ya daxe dake a yanzu ba tunani ba"

Sam Ammar be ɗauki abunda take faɗa so serious ba

Cigaba tayi da kukan ta, Ammar yace "kiyi shiru, zan baki chocolate ai kina so ko?"

"A'a Yaya Ammar let's be serious please"

"kinga dare yayi, maza yi bacci"
Noƙe masa kafaɗa tayi ta cigaba da kuka.

"zamuyi faɗa fa, ki dena kuka ko kina so muyi faɗa?"

Ta girgiza masa kai

"to Yimin shiru, kowa ya aikeki shiga cikin manya oho, gobe kikuma shiga zancen manya sekin jiyo abunda ze hana ki bacci"

"Ai nima babbar ce tunda ina da Aure ai"

Ammar ya kalleta yace
"Au haba? Ashe matar Aure ce, yaushe kika zama matar Aure?"

"ranar daka bada Sadaki aka ɗaura mana Aure"

Ammar yace "Amma ai baki biya sadakin da kika ci ba "

Sarai ta gane inda zancen sa ya daosa amma tace
"Dama in anci sadakin biya ake? Ni ban taɓa jiba"

Hannu yasa ya ɗago haɓarta suna kallon juna yace "Hmm baki taɓa ji bako? Idan na kuma cewa ke Yarinya ce kikamin Musu sekin biyani Sadaki na"

"Se inje ince Baba ya biya ka, amma ni ban taɓa ji ba se yau a gurin ka"

"Ke kika ci dan haka ke zaki biya"

Shiru tayi masa ta lumshe ido ta ƙara shigewa ta kwanta a jikin sa.

A hankali yake shafa gashin kanta, zuwa jimawa ta fara sauke ajiyar zuciya alamar tayi bacci.

Ammar a ransa yace "Allah karkasa na zama daga cikin Azzalumin maza"

Dukda yana mata kallon Yarinya, Amma she's so Simple gata da Biyayya sedai rikicin ƙuruciya.




Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
.✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

     

ELEGANT ONLINE WRITER'S

             

           

                  

                        Page 18



Baccin ta take hankali kwance a jikin Ammar, yasa hannu ya ɗago nata hannun, lallen hannun ta ya ƙara dark sosai gwanin sha'awa, a hankali ya kai hannun ta hancin sa ya shaƙi ƙamshin lallen, haka ya dinga wasa da da yatsun hannun ta, bacci yake ji sosai amma kasalar da yake ji ta hana shi motsawa dan haka ya zame ya kwanta a kan carfet da Mufeeda a jikin sa bacci yayi awon gaba dashi.

Se Asuba sannan ya farka, yaje yayo alwala sannan ya tashe ta, ba ƙaramin mamaki tayi ba kenan a falo ta kwana.

Miƙe wa itama tayi taje tayi salla ta koma baccin ta.
Bata farka ba se wajen ƙarfe goma na safe, da sauri ta miƙe ta shiga tai brush ta fito a gurguje bata san ya akayi tayi bacci haka ba.

Ammar baya falo ta nufi kitchen da sauri ta tarar, ya dafa tea ya zuba a flask ya shirya komai kaman yadda

Please Login or Register in order to submit comment