Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah ya kawo ki, ga munafukin da yaje yana yamaɗiɗi a unguwa wai ya ganki kina zance da wani, har mijin ki aka tara aka gayawa, lokacin da kika tafi gida ba lafiya yace auren ki ne ya mutu"

Mufeeda tace "to ni ina ruwana? Me kike so ince ko zan manta yadda ni kika sani a gaba da sharri da cin mutunci a layin nan, a fakaice har maita kika ɗoramin yanzu da ta kwaɓe muku zaki dinga gayamin, kuje Allah ne ya kama ku"

Mufeeda tai wucewarta ta tafi gurin me guava, tana tsaye tana cinikin guava, sega Alhaji Idris yayi parking a motar sa, Sam Mufeeda bata ganshi ba seda me guava yace mata "Hajiya ana magana" tana juyawa Alhaji Idris yace  "me guava zubawa babyn nan ko ta nawa take so in biya"
Banza tayi masa tace 
"me guava ban ta iya kuɗina"
Me guava Ya zuba mata kamar yadda tace ya bata ta nufi hanyar gida, aikuwa Alhaji Idris ya biyo ta, ta ratse tabi ta lunguna dan ta guje masa, Amma yayi parking ɗin motar sa ya bita.

Sosai Mufeeda tasa gudu yana binta yana ta tsaya taji, da ƙyar ta kai gida tana zuwa ta buɗe ta shige ta rufe ƙofar ta, a tsakar gida ta zube tana ta haki, ya daɗe a gurin yana buga gate ɗinta wai ta fito suyi magana ko nawa take so ze bata, hawaye ne ya fara bin idon ta, wannan wace irin masifa ce daga yin Auren ta zuwa yanzu ta haɗu da ƙalubale daban daban wanda bata san iyakar sa bama, wani irin zamanine wannan ace dattijo kamar Alhaji Idris yana bin yarinyar da yayi jika da ita kuma yasan matar Aure ce.

Tana cikin wannan tunanin taji ƙarar harbin bindiga, ai da gudu ta shige ɗaki ta ƙule a gado jikin ta na cigaba da tsuma.

Hajara ce tayi waya ta kira sojoji, Ashe baban ta babban General ne na Sojoji, mijin ta ma babban soja ne tunda aka haife ta a barrack take, aka turo mijin ta aiki kano tace ta gaji da zaman barrack tana so yakama mata gida ta zauna a wajen barrack, suna shirye2 dawowa kanon aka tura shi yaƙi Maiduguri, dan haka se yasa abokin sa ya kama mata gidan ta dawo ta zauna, dan haka tai waya aka zo hadda Sojoji mata aka tattare mata su Sa'idu da su Maman Nur da suka yi wa juna jina jina saboda duka, dan har jaririn da Maman Nur take goyo aka fasawa kai saboda dambe.

*********************
Maman Fa'iza taji hasuhin abunda Ammar yayi matuƙa da yace babu ruwan sa akan lamarin, ita kanta Fa'iza taji daɗi da yace ba ruwan sa dan tana tsoron Asirin su ya tonu.

Faruk yana gurin aikin sa 'yan sanda sukazo suka tafi da shi, Yayan Fa' iza Abubakar shi ya kai ƙarar sa gurin 'yan sanda akan marin da yayi wa Fa' iza.

Maman Fa'iza ta kira Maman Ammar a waya ta gaya mata abunda ya faru da yadda suka yi da Ammar, Umma ta bata haƙuri tace za tayi masa magana

Umma ta kama mita tana "Nikam na rasa wannan hali irin na Ammar, meye a ciki dan yaje ya taimakawa 'yar uwarsa, kawai yaje station aji
ba' asin meyasa ya mareta ayi musu tsakani tunda Abokin sane shine baze iya ba, kai Allah ya shirya Ammar.

Abba yace " Banga laifin sa ba, tunda bashi yayi marin ba kuma ba shi yace ayi ba, da alaƙar kirki ce tsakanin ta da Shi Farukun da baze mareta ba, babu yarinyar da zata kama kanta wani ya mare ta a banza"

Umma tace "dukda haka dai, tunda har Maifiyar Fa'iza ce ta nemi yaje ai se yaje, inda mutunci ai itama uwarsa ce"

Abba yace  "hakane"

Umma ta kira Ammar a waya, yana tsaka da tuƙi sega kiran umma, Yayi parking ya ɗaga wayar, bayan ya gaishe ta umma tace
"Ammar kai duk maganar da za'a gaya maka sedai ta shiga ta dama ta fita ta hagu ko? Yanzu abunda kayiwa Maman Fa'iza ya dace? Meye laifi dan kaje police station anji ba'asin da yasa ze mareta? Aiba raguwa zakayi ba"

"Umma kenan, Allah ya baki haƙuri, amma ni dai nasan Faruk abokina ne, Amma bansan wace irin Alƙace a tsakanin su da har yasa ya mareta ba"

Umma tace  "koma dai wace iri ce, kaje kaji kodan Mahaifiyar ta"

"shikenan zani Insha Allah"

"Ai ba zaka ba kaje yanzu suna police station ɗin unguwar su Fa'iza na nan babban titi"

"to Umma"

Ya katse wayar, ita dai Umma indai akan lamarin 'yan uwane setaita cusashi, abunda ya shafe shi da wanda be shafe shi ba.

Ya ajiye wayar kenan ya nufi unguwar su Fa' iza aka kira shi da baƙuwar lamba, ya kuma tsayawa ya ɗaga, ko gaisawa basu yi ba balle yasan wake magana yaji ance
"Kai maza ka koma gidan ka, Sojoji sunzo unguwa suna ta kwashe matan mutane suna tafiya da su" aka katse wayar

Ai a gigice Ammar yabi lambar amma shiru, ya kira Umma yace
"Umma dan Allah kiyi haƙuri ba zan samu zuwa station ɗin nan ba, yanzu aka kirani wai sojoji sunje suna kwashe matan mutane a unguwa"

Umma tace  "Subhanallah,ƙ Allah yasa lafiya shikenan Allah ya kiyaye kai maza ka koma, zanyiwa maman Fa'izan bayani"

Ammar ya kashe wayar ya tafi, aikuwa yana zuwa ya tarar unguwar tasu tun daga titi kamar anyi ɗan ƙaramin yaƙi kowa ya kulle a gida ss hayaƙi unguwar take.

Har yaje ƙofar gidansa bega kowa ba, yasa key ya buɗe gidan ya shiga da sauri ya shiga yana ƙwalawa Mufeeda kira, ya nufi ɗakin ta da sauri yana zuwa ya tarar da ita ta ƙule akan gado tana kuka, a gigice ya ƙarasa kan gadon nata ya ɗagota yace
"Mufeeda lafiya meyafaru? An kirani a waya wai Sojoji na kwashe matan mutane a unguwar nan meyafaru?"

Mufeeda ta gaya masa duk abunda ya faru gaba ɗaya a unghwar na dambe da tons tonen Asiri da suka yi hadda zubarwa da juna jini, shiru Ammar yayi yace
"Alhamdilillah da Allah yasa baki zama daga irin su ba Mufeeda, da yau bansan wani baƙin ciki zanyi ba ace anyi dambe da mata ta a layi, dambe na tashanci hadda keta sutura kuma ace sojoji sun tafi dasu Allah kaɗai yasan meze faru, Allah yayi miki Albarka"

Mufeeda ta goge Hawayen ta tace  "Yaya Ammar wai ashe me kayan miya ne yaita cewa ya ganni ina zance da wani, har akazo aka tare ka aka gaya maka?"

Ammar yace "bansan waye ya fara zancen ba, amma maƙocinmu ne ya tareni bayan sallar asuba ya gayamin"

"shikenan ai koba komai Allah ya sakamin yanzu"

"hakane kam, kiyi haƙuri ki dena kuka kinji, ni mema yasamin ke kuka haka?"

Nan ta kwashe abunda ya faru tsakanin ta da Alhaji Idris ta gaya masa data fita ɗazu, nan da nan Annurin fuskar Ammar ya ɗauke, wani irin gumi ya shiga tsatstsafo masa, gaba ɗaya gashin jikin sa ya miƙe.

" meyasa baki gayamin tun tuni ba? "

"saboda ina gudun ɓacin ranka"

"Wannan ba hujja bace" ya faɗa a ɗan hasale.

"Allah ya baka haƙuri, Yaya Ammar nasan halinka fiye da yadda kai kasani, na ɗauka ze dena bina amma yau kam da gudu ma ya biyo ni har ƙofar gidan nan"

A hankali ya raba Mufeeda da jikin sa ya miƙe, cikin zafin nama ta riƙe shi tace 
"Yaya Ammar kabi komai a sannu, mutumin nan yana da kuɗi sosai kar yasa ayi maka wani abun"

Ammar ya ƙwace hannun sa ya fita da sauri, yana fita ya tarar Mazajen wanda aka kwashe sun daddawo suna salallami, babu wanda yasan inda aka tafi da matan nasu, gashi Hajara bayan an tafi dasu ta rufe gidan ta ta ƙara gaba.

**********************

Faruk yana police station a bayan kanta yana rarraba ido, tun safe Su Fa'iza basu je ba se bayan la'asar da suna jiran Ammar kuma beje ba.

Lokacin da suka je suka yi sa'a D. P. O yana nan, aka buɗe file ɗin da aka rubuta ƙorafin da su Fa'iza suka shigar, aka kalli Faruk akace  "Kai me wannan baiwar Allah tayi maka ka mareta?"

Faruk yace  "Yallaɓai saɓani ne muka samu, amma dan Allah ayi haƙuri hakan ba zata sake faruwa ba"

Abubakar yace "Yallaɓai ba wani ayi haƙuri ya faɗi wani irin saɓani ne yasa har ze mari ƙanwa ta?"

D. P. O yace  "waima tsaya meye a tsakanin ka da ita?"

Faruk yace "ƙanwar Abokina ce"

"ina Abokin naka?"

Nan Maman Fa'iza ta faɗi dalilin rashin zuwan Ammar, D. P. O yace
"yanzu dai sulhu ya kamata ayi, tunda shi sulhu duk inda yake Alkhairi ne"

Zumɓura baki Fa'iza tayi tace  "bawani sulhu kawai a fitar min da haƙƙina dan baze mari banza ba"

"
D. P. O  yace " ke nutsu, idan kika yi min rashin kunya zan saka a saki bayan kanta kema, waima meye dalilin Yin marin ne, dan ba yadda za'ayi da mutuncin ki, abokin Yayanki ya mareki"

Faruk yace  "Yallaɓai zagina tayi"

"to zagi yana fitowa a jiki ne? Banda shashanci da nusaranci meya kaika dukan mace banda ragwanci"

Nan maman Fa'iza suka zage akan lallai se an fitarwa da Fa'iza haƙƙin ta basu yadda da sulhu ba, ganin da Faruk yayi ze kwana a ciki dan sunyi masa taron dangi, ya kwashe abunda ya faru tsaf tsakanin sa da Fa'iza ya gaya musu.

D. P. O yace "to Hajiya kinji, kina ta zaƙewa a Bima ta haƙƙin ta da kin haƙura anyi sulhu da haka bata faru ba, kinga yanzu dole mu haɗa da ita saboda abunda suka yi babban laifi ne kuma dole a hukunta su tare"

Maman Fa'iza tace  "Fa'iza abunda kikayi kin kyautatawa kanki kenan, duk yadda na rarrashe ki akan ki haƙura da batun Ammar baki haƙura ba shine zaki kashe masa Aure, Yarinyar da babu ruwan ta baiwar Allah tsakanin ta mutane girmamawa, shikenan kije dan kanki, duk hukuncin daya dace ai mata ayi mata officer "

Abubakar yace " A'a Mama be kamata a barta a nan ba tunda mace ce, abamu belin ta amma dole Ammar yazo gurin nan ku gaya masa abunda kukayi, wallahi kaji kunya Faruk kaci Amanar Ammar "

****************

Ammar daya fita, gidan Alhaji Idris ya wuce yasa aka yi masa sallama dashi,
Koda Alhaji Idris ya fito yaga Ammar ya wani yatsine fuska, Ammar be kula da yadda Alhaji Idris ke masa kallon ƙyama ba yace
" Dama nazo ne muyi magana ta fahimta da kai, na samu labarin kana bibiyar mata ta wai kana sonta, kuma ta gaya maka matar Aure ce ita, da farko naso in kaika hukuma kai tsaye amma naga gara inzo muyi magana nida kai, a matsayin ka na dattijo be kamata inyi maka haka ba, shiyasa nazo da kaina gurin ka dan Allah ka fita harkar mata ta, nine mijin ta tana da Aure dan Allah ka fita harkar ta"

Wata irin dariyar ƙet irin na riƙaƙƙun 'yan duniya Alhaji Idris yayi, sannan yace
"hmm yaro man kaza, ai ita duniya faɗi ne da ita meye a ciki dan naga matar da bata dace da kai ba nace ina so? Ai ba wani abu dan tafi da cewa dani dan.....

" Rufemin baki tsohon banza dana wofi, nazo maka da niyyar muyi magana ta kirki amma kaƙi i will show you what am capable of doing, Wallahi badan da hukuma ba da da kaina zan illa taka, an gaya maka mata ta irin sakarkarun matan banzan da karnuka irin ka suke bine? Wallahi inba Allah daya bani ita ba babu me iya rabani da ita, kuma bari kaga hukuma ce zata rabani da kai"

Alhaji Idris yace  " Nikuma zan nuna maka tasiri, da kuma ƙarfin da dukiya take dashi, zanyi Amfani da hukumar da dukiya ta in wulaƙanta ka, kana kallo matar da kake taƙama da ita talauci seya sa ta tsere ta barka, ba dai ni kazo ƙofar gidana kana ɗagawa murya ba, zaka gani sena jefa ka cikin talaucin da babu me ciro ka"

"ƙarya kake munafuki, Allah baya barin zalunci kuma idan taƙamar ka dukiya wanda yayi ka ya baka dukiyar shize maganin ka" Ammar ya juya ya bar gurin cikin zafin nama da tafasar zuciya.

Wasa2 har ƙarfe takwas na dare, babu labarin Inda aka kai su Maman Nur, mazajen su na ta yawo gidajen radio suna sanar da sojoji sun kwashe musu mata basu san inda aka kaisu ba, wadda tasa aka kwashe su an nemeta an rasa shikenan anyi kidnapping ɗin matan su.

Se wajen sha ɗaya na dare aka bada sanarwar cewa, ba wanda ya sace su Sojoji da suka zo suka tafi dasu State CID, sashen kula da manyan laifuka, ana zarginsu da tada tarzoma a unguwa da yunƙurin yin kisan kai ta hanyar dambe da illata junan su da suka yi harda karya ƙafar Jariri da dasa masa kai.
Haka mazajen su da 'yan uwan su suka ɗunguma suka tafi State CID amma aka hana su shiga akace su koma dare yayi.

Inda aka kaisu Maman Sadiq kamar kabari, ga matsi ga sauro na Jaraba a gurin nan ko juyi ba zaka iya yi a ciki ba, ga gurin se tsami yake yana wari, ko Abinci babu wadda taci haka suka dinga kuka a gurin nan, Sa'idu kuwa Hajara tace a kai shi barrack a koya masa discipline idan ya kwana bakwai a miƙawa 'yan sanda shi suyi binkice a kai shi kotu a tuhume shi akan haɗa fitina da bibiyar matan mutane.
Aikuwa Sa' idu yaga masifa, dan ba ƙaramin tumurmusa yasha a hannun sojoji ba, gashi gaba ɗaya cinikin sa an kwashe a gurin dambe, an watsar masa da kayan miya, ɗan babur ɗinsa na can, ga duka daya sha gashi an sashi tsallen kwaɗo ko iya tashi ba yayi.

Ammar Yana zuwa gida ɗakin sa ya wuce ba tare da ya kula Mufeeda ba, tana ganin haka tasan a zuciye yake, seda ta bari kamar awa ɗaya da dawowarsa sannan ta tafi ɗakin nasa bakin ta ɗauke da Addu'oi.

Ya ƙule akan gado zuciyar sa tana ta tafasa, wai shi wannan tsohon banzan ze kalli tsabar idonsa yace wai yana son matar sa, matarsa ta Aure

(ba dai kace ƙwaila bace? Ai wani ƙwailar yake so 🤭🤭🤭)

Kan gadon sa ta hau cikin murya me sanyi tace 
"Mijina koba ka faɗamin ba nasan a cikin damuwa kake, shiyasa tun a baya na kasa gaya maka abunda ke faruwa, idan ina ganin damuwa a fuskar ka ji nake tamkar zuciya ta tayi bindiga"
Ta matsa kusa da shi ta rungume shi ta fara shafa sumar kansa, kaman me raɗa tace  "dan Allah ka kwantar da hankalin ka, karka sani cikin damuwa dan ina kana fushi gani nake kamar a duniya nika ɗai aka tsana, kayi haƙuri Mijina Allah yana tare damu, kayi haƙuri, Allah yana son bawan sa me haƙuri kuma baya barin zalunci nasan baze wuce gurin wannan mutumin kaje ya ɓata maka rai ba, sam mutumin nan babu Allah a ransa"

Ƙara rungume Mufeeda yayi a jikin sa kamar wani ze ƙwace masa ita, ya dinga shaƙar ƙamshin turaren ta kamar me koyar magana yace
"Mufeeda kina sona?"
"Surely, with all my heart, karka manta Soyayya ce tasa na Aure ka a lokacin da bana zaton kai kana sona"
"Mufeeda" ya kuma kiran sunan ta
"Na'am abun sona" ta amsa masaz
"zaki iya rabuwa dani?"
"Babu wani dalili bayan mutuwa da ze rabani da kai, in ba da ƙwaƙwarar dokar Addini ba"
Ya ƙara rungume ta yace  "Mufeeda ban taɓa Soyayya ba se akanki, ban taɓa sanin haka Soyayya take ba, Mufeeda"
"Na'am My Ammar"
"Ban san meye kishi ba seda na zauna dake, ke kika koyamin Soyayya, seda na fuskanci meye Soyayya sannan na gane na fara sonki ne ranar da na fara ganin ki, na ɗakko ku a babur ɗina, Salon ki na daban ne, na riga na saba da komai naki, bana tunanin akwai wanda ze iya jurewa zama dani kamar ki, na saba da ƙuruciyar ki, Nishaɗinki, haƙurin ki, ladabin ki, da kuma kawaici bana tunanin akwai macen data haɗa dukkanin abunda kika haɗa, ko akwai ta nike kawai nasani, Mufeeda komai naki yana burgeni, komai kikayi looks beautiful to me"

Shiru Yayi yana sauke ajiyar zuciya, yayin da hannayen Mufeeda ke
cigaba da shafa sumar kansa tare da mamakin jin wannan kalamai da suke fitowa daga bakin Ammar, ko wane lokaci tayi abu dan ta birge shi baya kulawa, Ashe yana jin daɗin abubuwan da take masa tankawa ne baze ba se yau data ciyo shi.
Tana cikin tunanin ne ya sake kiran sunan ta, bata gaji ba ta sake amsa masa
Ammar ya ɗora da cewa "Rayuwar Ammar ba zata cika ba idan babu ke, Mufeeda ban san haka kishi yake ba, wanda na nuna a baya ashe shirme ne, seda wani ya tsaya a gaba na yana gayamin wai yana son abunda yake mallaki na, sannan na gane menene kishi, wallahi zuciya ta kamar tayi bindiga, badan ina tsoron abunda ze biyo baya ba da sena illa tashi sedai kome ze faru ya faru"
Tana jin yadda jijiyoyin kansa suka miƙe, jikin sa ya ɗau zafi ga bugun zuciyar sa dake fita da sauri saboda ɓacin rai.

"Mufeeda takace kai kaɗai mijina, bana ganin kowa idan ba kai ba, Yaya Ammar Allah daya haɗani da kai shine kaɗai na yadda ze rabamu, ina maka so irin wanda baki be isa ya bayyana ba, ka kwantar da hankalin ka dan Allah, ni kai nake so ba wani mahaluki daze iya raba mu"

Ta ƙara kwantar da murya cikin sigar shagwaɓa da rarrashi tace  "dan Allah ka kwantar da hankalin ka, karka illa ta min kanka, kaji fa Babyn ka ma yana cewa  sorry Daddy we loves you "

Duk da a cikin ɓacin rai Ammar yake seda yayi murmushin abunda ta faɗa yana shafa cikin nata.

Mufeeda tayi iya yinta gurin samarwa da Ammar farinciki tare da gusar masa da dukkanin damuwar da yake ciki, suka nunawa juna tsantsar soyayya da ƙaunar juna.

*****************

Da safe Ammar ya tashi da farinciki yadda Mufeeda keta ƙara bashi kulawa duk dan ya saki ransa, gefe ɗaya idan ya tuna Alhaji Idris se yaji kamar yaje ya ɗau doka a hannun sa, Amma dole in ya fita yanzu yaje Hisba ko gurin 'yan sanda ayi masa tsakani da shi da iyalinsa.

Mufeeda kam idan ta tuna irin kalaman da Ammar yak mata jiya seta jita tamkar a wata sabuwar duniyar masoya, bata taɓa tunanin jinsu daga bakin Ammar ba, bata taɓa zaton yana jin daɗin abubuwan da take masa ba se jiya.
Yanzu ma da kanta take bashi Abinci tana masa hira, ya saki jiki yaci sedai ita Mufeeda ba wani ci tayi ba.

Ya janyo ta jikin sa yana shafata yace  "ƙwailata dan Allah kj dinga cin Abinci karki haifo min  yaro a rame"

Ta tura baki tace 
"Nifa ban gane ba ana cemin ƙwaila kuma a dinga mazewa a zomin ɗaki in dare yayi ba"

Dariya Ammar yayi yace  "tunda kika ce ke Aure kike so ai so kike ki zama babba, gayamin me kike so in siyo miki"

Da sauri tace  "ɗanyen mangwaro"

Ɗan tsuke Fuska yayi yace  "meye wani ɗanyen mangwaro ina maganar arziki kina wani ɗanyen mangwaro"

"Aini maganar Arziki a gurina yanzu ka baani ɗanyen mangwaro"

"kin taɓa ganin mangwaro lokacin sanyi ne? Kinga ɗagani na sai miki wasu kaya idan na dawo zan taho miki dasu, ga kayan Abincin mu sun ƙare ban siyo ba kuma ya kamata in fara tanadi saboda haihuwa"

Za tayi magana aka kira Ammar a waya, ya ɗaga, Umma ce ke kiran
Suka gaisa Umma tace
"Ammar fatan dai komai lafiya ko, ina mufeeda?"
"Umma tana lafiya muna tare ma"
"Yawwa masha Allah, ɗazu munyi waya da Maman Fa'iza tace lallai kaje police station, Ana neman ka"
"Umma me nayi ake nemana? Me nayi nifa bani nasaka Faruk ya mare ta ba"
"Nima bata gayamin ba Amma dai kaje"
Ajiyar zuciya Ammar yayi yace "Shikenan zani Insha Allah"

Ha ajiye wayar tare da dafe kansa, Mufeeda tace  "Ya dai?"
"Abubuwa sunmin yawa Mufeeda, ni ban sanma wanne zanyi ba, wai lallai inje police station akan zancen Fa'iza"

"Kayi haƙuri kaje kaji menene? Kaga 'yar uwakka ce kuma yakamata a nunawa Faruk kuskuren sa"

"Ni masan meye a tsakanin su da ya mare ta?"
"yi haƙuri, ka daure kaje"

******************

Ƙarfe Goma aka shirya Saima za' a shiga da ita tiyata, za'a cire abunda yake cikin ta, an shiryota cikin blue ɗin kaya na theater, Nurses na turo gadon da take, idon ta a buɗe Jabir ya taho da gudu shida ƙanwar maman Saima, dan tunda aka kaita Asibiti be ganta ba se yanzu, ko magana ba tayi Amma da Jabir ya tafi kanta kan a shigar da ita ta kalle shi A hankali tace

"Jabir nasan idan shiga dani aikin nan ko in mutu ne ko inyi rai, dan ban zaci ma zan ƙara buɗe ido a duniya ba, abun da nake so in gaya maka shine nagode da irin riƙon da kayi min, Allah ya baka matar da zata maka abunda kayi min, idan na mutu a gurin theater nan, ina fatan Allah ya karɓi shahada ta, sannan ya fitarmin da haƙƙina akanka, idan kuma na rayu ka tabbatar kafin in farka ka ajiye min takaddar sakina, Azzalumi kawai"

Share please

Domin sharhi, gyara ko kuma shawara
Ayshercool
07063065680.✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨

( *Sai Mata* )

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

Please follow me on Wattpad, vote and Comment

ELEGANT ONLINE WRITER'S

NOT EDITED

                         Page 28

Shiru Jabir yayi yana bin Saima da kallo Nurses suka tura ta zuwa ɗakin theater.

Reception ya koma ya dafe kansa yana tunani, gaskiya Saima ta so shi kamar babu sauran ɗa namiji da ya rage sai shi kuma shima ya so ta, idan yasake ta a yanzu duniya zata zage shi ace beyi mata Adalci ba, Amma harga Allah yana son Fatiyya, saboda yana kwaɗayin abunda ze samu idan ya Aure ta.

Ammar ba dan ransa yaso ba ya nufi station ɗin da su Fa'iza suke, yana zuwa ya tarar da Abubakar da maman Fa'iza, Faruk se sunkuyar da kai yake, Ammar ya gaisa da su ya fuskanci DPO yace
"Yallaɓai Me yasa aka takura lallai sena zo, Allah yasa ba laifi nayi ba?"

DPO yace "ba laifi kayi ba sedai ma ince kai akayiwa laifi"
Ya waiga ya kalli Faruk yace  "Kai munafuki ɗago kayi masa bayanin abunda kukayi"

Cikin jin kunya Faruk yace "Amm... Inmm... Da farko dai ina me baka haƙuri Ammar, dan...

"Ka gaya masa me kuka yi nace idiot"

DPO Yai maganar a Hasale, Faruk ya gyara zama yace
"Ammar tun lokacin da muka je ɗaurin Aure naga Mufeeda naji ina son ta, yanayin yadda take nuna maka Soyayya yayi bala'in burgeni, se naji kana cewa kai ba sonta kake ba dandai ba yadda za ka yi ne Allah yayi hukuncinsa, tun daga lokacin nake tunanin tunda baka sonta me zanyi wanda zaku rabu ni in Aure ta, kawai se ranar na haɗu da Fa'iza take gayamin ai itama tana sonka mu haɗu mu haɗa kai ka saki Mufeeda, ni in Aure ta kaima ka Aure ta, ta dinga zuwa gidan yayar ka tana zigata, suje gidan ka suyi tayi wa matarka wulaƙanci, ta samomin lambar matarka nake kiran ta, ita kuma take hiding ɗin lamba tana turomaka saƙo akan ka sa ido akan matar ka, wallahi Ammar sharrin sheɗan ne kum........

"Enough!!!"
Ammar ya faɗa a Hasale ya ɗau mukullin babur ɗinsa ya bar station ɗin, ransa cike da baƙin ciki.

Duk zurfin cikin Ammar ji yayi baze iya jurewa ba, dan haja Kai tsaye gidan su ya nufa yana zuwa ya tarar da Jidda a gida ta saka Umma a gaba tana ta kuka kamar ƙaramar yarinya, fuskar Umman ɗauke sa damuwa, da gani

Please Login or Register in order to submit comment