Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuba naki kici"

Murmushi kawai Mufeeda tayi tace "Shikenan zanci, gama cin naka"

Ammar yaci bredin nan sosai dan ba ƙaramin daɗi yayi ba, se yaji da'aka sarrafa bredin zuwa wani abun daban yafi bredin daɗi ma, amma be iya buɗe baki yace yayi daɗi ba.

Ya kammala ci ta miƙa masa tissue ya goge hannun sa da bakin sa, har ze tashi ta kalle shi cikin salon kashe murya tace

"Mijin baby ba kace komai ba, yayi daɗi kuwa?"

Ɗan kallon ta yayi ya maze tare da ɗan tsuke fuska yace "ba wani daɗi na dai cine kawai maganin Yunwa"

Murmushi tayi tace "Tunda dai har ya wuce cikin ka ba kayi amai ba ai shikenan" tai maganar tana murmushi, ta tattare Kwanukan taje kitchen ta wanke.

Ta dawo ta tarar da shi a zaune a falon be tashi ba "Yaya Ammar ya haka ba zaka fita bane?"

"Se an jima zan fita" ya bata amsa

"shikenan Allah ya kaimu anjiman, ai gara ka zauna in ta kallon abuna ko?" tai maganar tana kashe masa ido ɗaya.

Hararar ta yayi ya kauda kansa daga kallon ta, tai murmushi ta zauna tana facing ɗinsa, lokaci lokaci suna haɗa ido se yayi sauri ya kau da kansa.

Ta tattara attention ɗin ta tana ƙoƙarin gano meya hana shi fita yau da wuri, kullum yana gama karyawa yake fi cewa, Amma yau yaƙi fita kuma yana zaune a falo, abun mamakin kuma se satar kallon ta yake, sake ɗaga ido yayi suka haɗa ido, ya ɗan maze yace

"lafiya kike min wannan kallon ƙurillan?"

A ranta tace "sekace shiba ni yake kallo ba" amma seta ta taso daga inda take tazo kusa da shi ta zauna ta kalle shi tace

"Kasan menene? So nake in taɓa gemun ka, shike tsolemin ido"

Ɗan buɗe baki yayi yana kallon ta, lallai yarinyar nan ta mugun raina shi, kawai ya ɗauke kansa yace

"tashi daga kusa dani mara kunya"

ƙara narkewa tayi a jikin sa tace
"dan Allah Yaya Ammar sau ɗaya fa zan taɓa dan Allah"

Juyowa yayi yana kallon bakin ta, wanda yayi raɗau da jan baki, se ɗaukar ido yake, dukda kitson kanta ya fara tsufa amma har yanzu yana ɗaukar hankalin Ammar, Yadda take maganar very serious kamar 'yar yarinya.

Ta kuma cewa "in taɓa dan Allah ?"

"Tashi kije kiyi breakfast seki zo ki taɓa"
Murmushi tayi tace "to"

Ta miƙe tana fara' a ta haɗa breakfast ta zauna tana karyawa, ta nayi tana kallon sa tana murmushi, ta kammala ta tattare Kwanukan, tana dawowa ta tarar ya ɗakko mukullin sa ze fita.

Ta ɗan ɓata fuska tace "haba Mijin bebi, haka muka yi da kai? Banfa taɓa ba"

"Ke bana son shiririta, ni fita zanyi Ungo wannan" ya miƙo mata kuɗi ɗari biyar

"Me zanyi da wannan? Naga ka siyo komai na amfani ai"

"Eh baki nayi ko zaki sai wani abun"

"ni babu abunda zan siya"

"Ke ki karɓa meye haka?" ya ɗanyi maganar a hasale.

Durƙusawa tayi tasa hannu biyu ta karɓa tace

"Nagode Allah ya ƙara Arziki, yaja da ran su Umma"

"Ameen"

Suka yi Sallama ya fice.

**********************

Fa'iza ce keta kaiwa tana komowa a ɗakin ta tarasa meke mata daɗi, tana ƙoƙarin tuna menene mafita akan halin da take ciki tabbas tana son Ammar kuma tunda har ya iya Aure ƙaramar yarinya kaman wannan to tabbas itama zata iya jarraba sa'arta akansa amma ta yaya? "

Fitowa tayi falo ta tarar da Maman ta tayi baƙuwa, ba tare da ta kalli inda baƙuwar take ba tace "Mami dan Allah zan fita anguwa, zanje gidan su Nasreen"

"To kiyi sauri karki daɗe, bana son babanku ya dawo yaita min mitar ba kwa nan"

(Nasreen ɗin 'yar ƙanin mahaifiyar Fa' iza ce)

"Ok"

Baƙuwar tace "Ahh Fa'iza ba magana?"

Fa'iza ta ɗan juyo ta kalli matar tace "Ohh sannu" a ƙalla matar tayi sa'ar mahaifiyar Fa'iza, bata kuma bi takan Matar ba ta wuce ɗakin ta.

A gurguje ta watsa ruwa ta shirya ta fice daga gidan, ba ta tsaya ko ina ba seda taje gidan su Nasreen, ta shiga da sallama tayi sa'a Nasreen ɗin tana tsakar gida tana mopping, Nasreen na ganin ta tace "hajiya fa'iza wannan zuwa haka babu waya, anjima nake tunanin in zo gidan ku fa"

"Kinga gurin ki nazo dan Allah ina Umma?"

"ba ta nan tana Islamiyya"

"Muje ɗaki dan Allah ina cikin damuwa"

Ɗaki suka shiga kaman yadda Fa' iza ta buƙata.

"Nasreen wallahi nayi sakacin kasa ga yawa Ammar abunda yake cikin raina, saboda ina ganin baze soni ba, se gashi ance yarinya ƙarama ya aura"

Nasreen tace "Wallahi yarinya ce sosai, ai ke baki je gurin dinner ba, mu munje munga komai wallahi yarinyar nan bata fi shekara sha shida ba, 'yar ƙarama da ita se iyayi in gaya miki tsaf zaki iya goya wannan' yar abar"

"dan Allah ba wannan ba meye abunyi yanzu? Wallahi Nasreen baki ji yadda nake ji a raina ba, ina son Ammar sosai fa ba da wasa ba"

"Aikuwa seki ɗau haƙuri tunda ya riga yai Aure"

Hararar ta Fa' iza tayi tace  "haba Nasreen Ammar mijin mace huɗu ne fa, dan me zan haƙura?"

"to da sana'ar Adaidaita sahun ze riƙe ku ku biyu, kiyi tunani mana Fa'iza"

"Taɓɗijan ubanwa ya gaya miki mu biyu zamu zauna, ta isa in zauna da ita inyi kishi da 'yar mitsitsiyar Yarinya, wallahi sena fara da korar ta daga gidan tukuna, in saka Daddy na ya bashi aikin yi, dan bazan aure shi a dinga miji na ɗan a daidaita sahu bane"

"ta yaya?" Nasreen ta tambaye ta

"koma ta ina ne, sena fara da kora ta tukuna ni kuma zan shige"

"Naji amma kin san meze faru?"

"A' a sekin faɗa"

"Yanzu ki bari se an jima, ki shirya muje gidan su Yaya Ammar, semu sa Halima ta raka mu gidan sa dan nima banje gidan sa ba, muje kiga yarinyar muga yanayin kamun ludayin ta daga nan semu san ta ina zamu fara"

"Yawwa Nasreen naji daɗi Sosai, ina nan bazan koma gida ba, gama abunda kike, bari in ɗora girki idan yasa anjima se mu tafin"

"shikenan bari in samo Almajiri yai mana cefane kafin Umma ta dawo".

Haka kuwa akayi, bayan sun gama girki Maman su Nasreen ta dawo suka yi mata sallama cewar za suje gidan Yaya Ammar.

Maman Nasreen tace "Aikuwa kwa gano min gidan dan dama ban samu naje ba nima, dan Allah kuce ina gaishe su kafin inzo"

Nasreen tace "to Umma zamu gaya musu Insha Allah"
Daga nan suka fice basu tsaya ko ina ba se gidan su Ammar.

Mahaifihar Ammar taji daɗi da taji sunce gidan Ammar zasu je, da iyayen su da mahaifin Ammar uwa ɗaya uba ɗaya, Dan haka Umma tasa Halima ta shirya ta raka su gidan nasa, ta bada kayan kuka da su zogale tace akaiwa Mufeeda.

Sam Su Fa'iza basu nuna akwai wani abu a ƙasan ransu ba game da zjwan su gidan Ammar dan haka Halima ba taji komai ba ta shirya domin ta raka su.

**************************

Koda Mufeeda ta kammala gyaran gidan ta, ba wani abu da zata yi bata da tabbacin Ammar ze dawo da rana ko baze dawo ba dan haka ta gyara masa ɗakin sa ko ina tsafa se ƙamshi yake, ta samu takadda ta rubuta masa

"My love to you is endless Baby, good night, have a very sound sleep tonight i will be with you in your dreams, I Love you, mijina" ta ajiye masa a kan gadon sa

Daga nan ta nemi guri ta zauna ta fara tsifar kanta dan a ganin ta ya tsufa.

Ta fara tayi nisa a tsifar dan harta tsefe rabi taji ta gaji, ta tufke rabin data tsefe, ta ajiye tsifar tayi kwanciyar ta a falo, bacci ne ya ɗauke ta bata farka ba se ƙarfe ɗaya, ta tashi taji tana jin Yunwa dan haka ta haɗa cornflakes ta sha sannan ta tafi yin Salla.

Tayi raka'a biyu taji ana buga gate ɗin, bata yanke sallar ba ta ci gaba da sallar ta, seda ta idar sannan ta ɗakko Hijjabi ta tafi buɗewa.

Har sun fara zage2 "wai dan wulaƙanci tana ji suna buga ƙofa amma anyi banza da su an barsu a waje"

Halima tace "wataƙila tana wani abunne"

Ta ƙaraso cikin sassanyar muryar ta tace "Waye?"

Halima tace "Mune Anty Mufeeda" ai gaba ɗaya suka kalli Halima "Anty kuma?"

Mufeeda ta buɗe ƙofar, Halima ta gane a cikin su dan tazo gurin bikin ta ranar kamu da kuma dinner, ta faɗaɗa murmushin fuskarta tace "Bismillah ku shigo"

Suka shiga tai musu jagora zuwa falon ta, suna tafe suna hararar bayan ta.

Tai musu jagora har cikin falon ta, ko ina na gida ƙal da shi, se ƙamshi ne ke ratsa kafofin hancin su.

Suka nemi guri suka zauna suna kuma ƙarewa falon nata kallo a wulaƙance, Kayan kujerun ta suka kalla hakan ya tabattar musu da Mufeeda ba 'yar matsiya ta ce ba, dan kayan ta masu tsada ne.

Mufeeda tace "Sannun ku da zuwa kun kwaso rana, Yaya Halima naita sa ido inga kinzo amma baki zoba se yau ko? Nikam nayi fushi"

Halima tai murmushi tace "haba Anth Mufeeda washegarin da' ak kawo ki Umma ta bada Abinci akawo muku, har mun shirya zamu zo, na kira Yaya Ammar amma yace kar muzo bacci kike"

Mufeeda tai murmushi tace  "Hmm Yaya Ammar kenan, bari in kawo muku ruwa kun kwaso rana"

Ta tashi ta tafi kitchen, ita kam fa'iza mamaki da baƙin ciki ne suka haɗu suka hana ta magana, duk yadda ake faɗin yarintar matar Ammar bata zaci zata ganta a haka ba, ga Yarinyar da kyau ga wani iyayi da take yi abun haushi.

Mufeeda ta ɗakko musu ruwa da lemo me sanyi a fridge, ta ɗebo musu snacks ta kawo musu tace

"ku fara da wannan bari in shiga kitchen in ɗora muku girki"

Ta koma kitchen tana ƙoƙarin ɗora musu girki, Nasreen tace

"Ya kika ga kamun Luda yin ta, kinga dai matar Ammar"

Fa'iza tace "Nagan ta kam, amma Ammar ya bani kunya duk wannan jiji da kan nasa kalli abar da ya auro"

"ba wannan ya kamata ki duba ba, mafita ya kamata ki nema"

Halima tace "wai Yaya fa'iza me kuke yi hakane? Ya zamuzo har gidan ta ku dinga munafuncin ta"

Nasreen tace "dalla rufewa mutane baki, ina ruwanki kema munafuka wai Anty Mufeeda meye wani Anty, wallahi kin girme ta"

"to dan na girme ta ai ƙanin mahaifiya ta take aure, kuma nima ai tana bani girma na dukda haka, ni banga aibun ta ba wallahi"

Fa'iza tace "dalla ƙyaleta mu ci gaba da zancen mu"

Ana haka Mufeeda ta fito daga kitchen ta dawo tace "bari in kunna muku yv kafin abincin ya dahu"

Halima tace "to Anty Mufeeda ko in taso in kama miki wani abun ne, mun saki aiki rana tsaka"

"laa kinji Yaya halima da wani batu wai kun sani aiki ba wani aiki"

Ta tafi tana kunna tv, sarai Mufeeda ta lura da wank irin mugun kallon banzar da Fa'iza da Nasreen suke mata, Amma ta maze ta kunna tv ta dawo ta zauna tace

"nikam Halima wannan Antyn nawa  ban gane taba" ta faɗa tana nuna fa'iza sanna ta nuna Nasreen tace
"har gara wannan na ganku tare ranar kamu amma na manta sunan ta, Amma ita ban gane ta ba"

Halima tace "wannan Antu Fa'iza ce, wannan kuma Anty Nasreen duk cousin's ɗin Uncle Ammar ne"

Mufeeda tace "Masha Allah, Sannun ku fa"

Nasreen ta ɗan taɓe baki sannan tace "yawwa"

Mufeeda a ranta tace

"ashe cousins ɗin sane, wannan wani abun ne ya kawo su, akwai wani abu a ransu, amma bari inga iya gudun ruwan su, zan ɗago inda suka dosa kafin su tafi "

Fa'iza tace "Nikam a jinki nawa akayi miki aure haka?"

Mufeeda tai murmushi tace "Jss 2 nake"

Nasreen tace "da alama kam, ke gidan ku ba'a karatu ne? Aka miki aure da ƙananun shekaru? Sekace a ƙauye"

"anayi mana nima har zan ci gaba da karatuna amma Allah beyi ba, Allah ya haɗa ni da Yaya Ammar yace na ƙarasa in muna tare tunda muna son juna baze iya jira in gama ba, kuma duk wanda yaje Islamjyya yasan origin ɗin Auren wuri, ai ba wai ɗabi'a ce ta mutanen ƙauye ba, yana da asali a addinin musulunci, bari in dubo girki na karya ƙone"

Kallon juna Fa'iza da Nasreen suka yi tare da jinjina kai.

Ta kammala dafa farar taliya dama tana da Miya, dan haka ɗumama miyar kawai tayi ta zubo musu.

Ta kawo musu manyan kuloli da cokula ta ajiye, Fa'iza tace
"Ke duk wannan Abincin kika dafa? Abincin naki kuwa ze ciyu?"

Mufeeda tace "indai har Yaya Ammar zeci Abincin dana dafa to komai matsayin mutum zeci wannan Abincin, sedai kuma in mutum be niyyar ci ba, Yaya Halima sakko muci Abinci naga su Anty Nasreen ba Yunwa suke ji ba"

Halima sam bata ji Daɗin abunda su Nasreen ɗin sukayi ba, da ta san haka za suyi da bata rako su ba, ta sakko suka kwashi girki it da Mufeeda, Nasreen taga kaji a miya kuma ranta ya biya dan haka ita ma ta sakko, ita kuwa Fa'iza se haɗe rai take.

Se la'asar suka shirya zasu tafi, Nasreen tace "kin san da'aka kawo ki bamu zo ganin gida ba, zo ki nuna mana, ta shiga dasu ko ina amma tai mirsisi ta hana su shiga ɗakin Ammar.

Fa'iza hadda baƙaƙen maganganu Amma Mufeeda tace baza su shiga ɗakin mijin ta ba, da dai sunzo kafin akawo tane shikenan, Amma tunda Ammar ya fara kwanciya a ɗakin babu wanda ze shigar masa ɗaki ko waye kuwa.

Haka suka tafi, Halima taji daɗin abunda Mufeeda tayi sosai, ɗari Biyar ɗin da Ammar ya bata kafin ya fita ita ta takurawa Halima ta karɓa.

******************

Yauma Ammar se bayan isha'i ya shigo gidan, yauma da kaya niƙi niƙi a hannun sa ya shigo, Mufeeda tayi masa sannu da zuwa ta taya shi shiga da kayan, ya zauna a falo akan carfet ya mimmiƙe ƙafafuwan sa, dan ya gaji sosai.
Ta kawo masa ruwa me ɗan sanyi ta bashi ya karɓa ya sha, yana lumshe ido saboda gajiya.

Mufeeda ta zauna wajen ƙafafuwan sa tana ja masa yatsun ƙafan

Tace "Sannu mijin bebi" jinjina mata kai yayi yana jin daɗin yadda take jan yatsun ƙafafuwan nasa.

"Nasan kayi salla a waje, a kawo Abinci ne?"

Ammar yace "yanzun ma wani girkin kika kuma yi?"

Ta miƙe tsaye tace ina zuwa, taje kitchen ta kawo masa Abinci, ya kalli taliyar tana ta tururi a cikin flask, bece komai ba, ta zuba masa ta miƙa masa ya karɓa ya jujjuya taliyar yana kallo sannan ya fara ci, aikuwa turawa kawai yake, yaji daɗin taliyar nan sosai, gashi tunda ya fita ruwa kawai ya iya siya ya sha.

Mufeeda kallon sa take yi, tausayinsa ne ya kamata da ganin yadda yake cin Abincin kasan yana jin yunwa sosai, tun safe yake yawo a gari neman halak ba tare da ya dawo gida ya huta ba, dole duk inda ya samu yayi bacci.

Ta ture ɗankwalin kanta gefe dan zafi ya ishe ta, ya kalli kan yaga ta tsefe rabi, kitson da yake matuƙar so, ajiye fork ɗin yayi yana kallon ta, seda tace

"ya dai naga kana kallo na? Ko nayi laifi ne?"
da sauri ya basar yace

"kwashe kayan Abincin nan na ƙoshi"

Murmushi tayi masa tace "to Mijin so"

Ta kwashe kayan ta shiga ɗakin ta, ta fito da kibiya da mataji zata ci gaba da tsifa dan tuni Mufeeda ta gano Ammar yana matuƙar begen kitson kanta, wanda shi sam besan ta gane ba.

Ta fito falo ta zauna ta fara tsifa, Ammar yace "me kike yi hakane? Me yasa kike tsefewa?"

"ya tsufa ne, dama kuma na gaji da tsifar dan Allah  ka tayani tsefewa" tai maganar tana miƙa masa comb.

"ke na miki kama dame saloon ne? Ta yaya zan iya wani tsefe miki kai? Ni bazan taɓa wannan ƙazamin kan naki ba, ban iya wani tsifa ba"

Tura masa baki tayi tace "Aini kaine me Saloon ɗina, kuma zaka dinga tayani tsifa wallahi ko in bar kan yaita zama a haka bazan ƙara tsefe ko guda ɗaya ba ko ze shekara"

"Saboda kin iya ƙazanta ko. Idan kuma gashin ya zube fa?"

"Shikenan na huta dama damuna yake da zafi, ji nake kaman in ɗan rage shi da almakashi aini yarinya ce Allah ze yafe min, au ni namanta ma na kulaka bayan ɗazu da safe nace zan taɓa gemunka ka hanani"

Ɗan taɓe baki Ammar yayi ya miƙe tsaye, wannan Yarinyar bata rabo da Rikici.

Ta jingina da kujera tace "Yau bazaka sha shayin naka bane? Ko so kake kayi Tumbi? Kaci Abinci fa yanzu kuma za kaje ka kwanta"

"bazan sha ba" ya bata amsa.

Har ze shiga ɗakin sa yaji tace  "Mijina Dan Allah Wacece Fa'iza a family ɗinku?"

Ji yayi gaban sa ya faɗi ya waigo da sauri yace "kamar Yaya wace Fa'iza?"

"Ɗazu suka zo suda Yaya Halima, mun daɗe dasu anan tare"

Be amsa mata ba ya shige ɗaki abunsa, ƙyale shi tayi dan taga alamar gajiya a tare da shi, amma ta barwa ranta dole Ammar ya gaya mata matsayin fa'iza da Nasreen a gurin sa.

Yana zuwa ze kwanta yaga takaddar data ajiye, ya ɗauka ya karanta, ɗan murmushi yayi ya ajiye takaddar a akan side bed ya kwanta.

****************

Motsin da Ammar ya dinga ji a banɗakin sane ya sa shi farkawa daga baccin da yake yi.

Shiru yayi ya lumshe ido yana tunanin meye yake motsi a toilet ɗinsa, be gama tunanin ba Mufeeda ta fito jikin ta ɗaure da towel kan ta babu ɗankwali ta gama tsefe kanta ta wanke shi.

Ammar ya buɗe ido da sauri yace "Ke meye haka? Me ya kawo ki banɗaki na?"

Murmushinta me ƙayatarwa tayi masa tace "tap ɗina ne yaƙi zuwa, ni kuma bazan iya kai ruwa toilet ɗina ba kaga ni ƙarama ce bazan iya ɗaga babban bucket ba shiyasa nazo nan nayi wankan"

Tsaki yayi yace "to jeki maza fitar min daga ɗaki"

maimakon ta fita seta girgiza gashin kanta da yake jiƙe da ruwan wanka, ai kuwa ruwan har fuskar Ammar

"Wai Mufeeda meke damunki ne, ya haka?"

Cikin kalar Halayar Yara tace "Yi haƙuri  kanne ya jiƙe, shine nake jijijjigawa dan ruwan ya fita, ka dubamin idan kan ya fita dama jiya kace kaina ƙazamine"

Girgiza kai Ammar yayi ya ja bargo ya rufe kansa ya juya mata baya.
Murmushi Mufeeda tayi a ranta tace "Yaya Ammar kenan ai ka gamu da yarinta kenan"

Ta zaga gurin ƙafar sa da ya bari a waje, taja yatsansa na tsakiya tace

"ai ka bar ƙafar ka a waje"

Banza yai mata yaƙi kula ta, yana ji tana jan yatsun ƙafarsa, kawai Mufeeda ta kalli gashin ƙafarsa ta ja ɗaya be kula ta ba, ta ƙara jan wani ai ba shiri Ammar ya miƙe zaune yace

"Meke damunki ne?"

Ta ɗan kwaɓe fuskarta tace "bakomai fa, so nake ka tashi ka karya"

"Naji amma yanzu fita kije kisa kaya, sannan karki ƙara zuwarmin ɗaki kiyi wanka in zaki yi wankan ki gayamin in kai miki ruwan"

"to shikenan naji zan tafi, Amma in ka fito sena taɓa gemunka dan ban manta ba"

Ta kashe masa ido, ta juya ta fice tana girgiza gashin kanta yana fidda ruwan dake jikin sa.

Yayin da Ammar yabi bayan ta da kallo zuwa kan santala santalan ƙafafuwan ta, tunda ga kan gashinta har ƙafafunta ɗigar da ruwan wanka suke.

Ammar ya dafe kai yace "kai wannan 'yar mitsitsiyar Yarinyar se rigimar tsiya, wai gemu na zata taɓa, wani lokacin kamar me hankali amma shirmen ta yayi yawa, dama nasan nikam na auri ƙuruciya da rawar kaine kawai, ni da ko ɗaukar ƙana nan yara ba nayi, amma wai gemuna zata taɓa"


Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

     

ELEGANT ONLINE WRITER'S

             

           

     

    Page 12



Ammar ya sakko daga kan gado ya shiga a gurguje yai wanka ya fito falo, kamar ko yaushe falon ta tasaf tayi turaren wuta, ta ajiye kayan breakfast a falon, se dai ita bata falon zama yayi ya haɗa ya fara karyawa, har ya kammala bata fito ba abun ya bashi mamaki, yana daf da fitane sannan ta fito cikin doguwar rigar ta, ta atamfa ta tsikara ɗaurin ɗan kwali a gaban goshin ta, masha Allah, Ba ƙaramin kyau tayi ba dukda bata saka jambaki ba yau fuskarta ba kwalliya amma tayi kyau, kaman Ammar yayi magana amma ya fasa.

"Hubby har kayi breakfast kai kaɗai, shiryawa fa nake yi amma har kayi shirin fita?"

"Eh na makara yau, zan tafi"

"Amma nifa yau kai zaka bani Abinci, amma zaka tafi gashi ko ganinka ban gama yi ba"
tai maganar cikin sigar shagwaba da rararshi, ta ƙaraso gaban sa ta riƙo hannayen sa tace

"please My Ammar ka tsaya inyi breakfast seka tafi, Allah ban ganka ba sosai"

"Ke wai duk wani salon damun mutum kin sani, ni tafiya zanyi ba kiga na makara ba"

Tura baki tayi ta ɗan haɗe rai "dan Allah Yaya Ammar ka zauna inyi breakfast seka tafi, in ka tafi Allah bazan ci ba"

Ammar yace "karki ci ɗin cikin kine ai ba nawa ba"

Ya ƙwace hannun sa ze tafi, ta riƙe shi gam, idon ta har ya fara kawo ruwa za tayi kuka, Ammar ya girgiza kai yace
"Shikenan ni karki min kuka, muje ki zuba in kuma ba kiyi sauri ba zanyi tafiya ta ne"

Murmushi tayi tace "zanma yi saurin"

Haka Ammar ya dawo ya zauna, ta haɗa breakfast ta nayi, rigar ta cif a jikin ta kaman a jikin ta tela ya ɗinka.

Haka Ammar ya zauna jaririyarsa ta gama cin Abincin ta, seda ya miƙe ze fita ta cire ɗankwalin kanta taje gaban sa tace

"Yaya Ammar ka dubamin idan gashi na ya fita"

dama gashin nan ya daɗe yana tsolewa Ammar ido. Ajiyar zuciya yayi yace

"Ke na gaji, ki bari idan na dawo zan duba miki"
yayi waje da sauri, Yayin da Mufeeda ta bishi tai masa addu'ar da ta saba yi masa.

A ƙasan zuciyar sa yana jin dama ya taɓa gashin nan, dan har ya bushe ta shafe shi da mai.

************
Su fa'iza kam bayan sun tafi jiya suna tafe suna zagin Mufeeda suna tsine mata.
Daddare suna chatting ita da Nasreen, Nasreen tace
"ke yanzu na samo mana wata mafita"

Cikin zaƙuwa Fa'iza tace "wace mafita ce haka?"

"Kin san Anty jidda ma ba son Auren nan take ba"

"haba dai?"

"Wallahi dagaske nake, yanzu abunda za muyi shine, muje gidan ta mu zigata, muce Yarinyar tayi mana wulaƙanci mu dai ɓata ta sosai a gurin ta, tunda kinga ba zamu tunkari umman sa mu gaya mata ba mussman inda wannan banzar haliman"

"haka za'ayi Nasreen, Allah ya kaimu gobe gidan Jidda zamu je".

Haka kuwa akayi Washegari haka suka wanke ƙafa zuwa gidan Jidda, tayi murnar ganin su suka baje ana ta hira Fa'iza tace
"Anty jiya fa mukaje gidan Yaya Ammar, wallahi Anty Ammar ya bada maza ke kinga matar tasa kuwa?

Jidda tace
"na ganta mana ya zan masa tunda shi ya zaɓo ta"

Nasreen tace "haba Anty jidda me wannan 'yar yarinyar zata morawa Ammar banda abun namiji dai?"

Jidda tace "ba shi yace yana so ba, itace ta ganshi ta nace masa sekace mayya seda ya aure ta, da akwai wata bazawara nan kusa dani ita yake so, amma ya koma ya auri wannan yarinyar"

Kallon juna Nasreen da Fa'iza suka yi, suka maze Nasreen tace

"'hmm ai baki ga abu ba Anty, kinga wulaƙanci da tayi mana? Munfi minti goma sha biyar a ƙofar gida muna bugu taƙi buɗewa, ke kinga kallon banza da take

Please Login or Register in order to submit comment