Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da suke ciki ɗaya, tana kula da ita, ita da mijin ta suka kai Mufeeda Asibiti, aka bata magunguna aka tabbatar musu da jinin ta ya hau, ta rage damuwa ga ulcer da tayi mata mugun kamu saboda rashin cin Abinci, Mijin Anty Maryam se mita yake yace
"Ummu Iman wannan ƙanin naki Halinsa se shi, Ya samu yarinya me haƙuri amma ze wasa da damar sa yana nema ya kashe musu 'ya"

Anty Maryam tace  "ƙyaleshi zega tsiya sena koya masa hankali"

Da sassafe Ammar ya shirya ya tafi gidan Anty Maryam, gaba ɗaya yana cikin kiɗima yace
"Maryam na rasa inda zan saka zuciya ta rashin ganin Mufeeda, wallahi ina cikin tashin hankali"
"Illar Fushi kenan da rashin bincike, seka kiyaye gaba"
"Maryam yanzu ba lokacin wannan bane, na yanke shawarar inje in gayawa Abba, tun kafin lokaci ya ƙure in karɓi duk hukuncin daze min"

Har ya juya ze tafi Anty Maryam tace  "badan halinka ba na gano inda take"

Da sauri ya juyo a gigice yace 
"dan Allah tana ina?"

"Babu ruwan ka da inda take, Amma na ganta har munyi magana"

Ajiyar zuciya ya sauke yace "Alhamdilillah dan Allah ki bar batun wasa tana ina?"

"Sanin inda take bashi da Amfani a gurin ka, dan tace min ita da gidan ka har Abada ba zata koma ba"

"Ƙarya ne ba dai Mufeeda ce ta gaya miki haka ba, ba zata taɓa faɗin haka ba"




PLEASE IF YOU READ IT HELP ME TO SHARE IT,
DON'T FORGET TO VOTE AND COMMENT

JIYA NA KUSA CIN DUKA A WAJEN MASOYA MUFEEDA 🤣


Domin Sharhi gyara ko shawara you are free to contact me via my what's App Number
Ayshercool
.. ✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨

( *Sai Mata* )

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

Please follow me on Wattpad, vote and Comment

ELEGANT ONLINE WRITER'S

         

                        Page 25

Mufeeda tana fama da laulayi Sosai, har gwara 'yan kwanakin nan ta ɗanji sauƙi, Ammar kam kullum cikin sintiri yake gidan Anty Maryam, Amma bata saurarar sa duk lokacin da yaje haka ze dawo gwiwa ba ƙwari.

Yanzu ma Sallama yayi sedai yau Anty Maryam bata nan, Mufeeda ce kawai se 'yar Anty Maryam wadda ba tafi shekaru uku ba suna kallo da Mufeeda a falo, A hankali Mufeeda ta amsa Sallamar Ammar ɗin, ya shigo falon da suke ya tarar da Mufeeda a falon, kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kai.
Ɗan Murmushi Ammar yayi yace  "Lallai Auta Sauƙi ya fara samuwa, yau kina falo wannan kwalliya haka"

Bata ce masa komai ba sema maida hankali da ta sake yi akan Tv, 'yar Anty Maryam Ammar ya bawa biscuit yace  "Amrah ina Umminki?"

Cikin maganar yara tace 
"ta tafi unguwa ta bammu nida Anty Mufeeda"
"Shikenan maza jeki ɗaki kici biscuit ɗinki keda teddynki"
Cikin murna yarinyar ta tashi ta tafi ɗakin su na Yara tana murna, Yaran Anty Maryam duk suna makarantar kwana ne (boarding) , daga ita se Yarinyar ta ƙarama.

Ammar ya zauna a kusa da Mufeeda yana ƙare mata kallo, ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tayi taƙi kallon sa.

"Mufeeda nine bakya son gani ko?"
Tura baki tayi taƙi kallon sa.

"you look so beautiful Masha Allah"

Da sauri ta kalle shi tace "Ka manta ne ƙwaila fa kake wa magana kar in rainaka fa naji kana cewa nayi kyau"

Ƙasa yayi da murya yace  "Eh nasan ƙwailar ce, Nace kiyi hakuri please mu koma gida, nima fa bani da lafiya koda yake naga kin dena sona Amma ayi haƙuri dan Allah"

Cikin tsiwa tace "Dan Allah nika matsa daga kusa dani, na gaya maka daga gidan nan se gidanmu zan wuce, bazan sake zama da kai kanamin faɗa kullum ba"

"Mufeeda nine fa"

Shiru tayi tana zumɓura baki, Janyo ta yayi yana ƙoƙarin kissing ɗin ta, ta dinga ture shi tana girgiza masa kai.

Sallamar Anty Maryam ce tasa shi sakin ta yana maida numfashi, miƙewa Yayi Da Sauri, Anty Maryam ta kawo kai ɗakin ta tsaya tana yiwa Ammar kallon tuhuma.

Basarwa Yayi yabi gefen Anty Maryam ya fice ba tare da ya kula ta ba, ta kalli Mufeeda da tayi kicin kicin da fuska tace
"Lafiya kuwa Mufeeda?"
"lafiya ƙalau"
"Kodai Akwai matsala ne?"
Girgiza mata kai Mufeeda tayi, bata son ci gaba da takura mata dan haka ta ƙyaleta.

*********************

Bayan barin Mufeeda gida wata mata ta sake tarewa a jikin gidan Mufeeda, tunda ta shiga gidan Su Maman Amir taga take taken basu da mutunci, basu da Aiki se gulma da zagin mutane, kuma da wata ta tashi a cikin su zasu hau yi da ita.

Ammar yana kwance a falo yaji ana knocking, kamar kar ya tashi amma ya miƙe yaje ya buɗe, yana buɗewa yaga Fa'iza a tsaye, Murtuke Fuska yayi yace  "Malama lafiya?"
Murmushi tayi tace 
"laa Yaya dama kana gida? Ziyara na kawo maka"
"Nagode, Amma bata nan dan haka zaki iya tafiya"
"Amma Yaya Ammar ai ko ruwa ka bari Insha, na kwaso rana da gajiya wallahi"
"Baki da hankali ne? Bakije me nace ba? bata nan, ya zaki shigo gida Alhalin matar gidan bata nan, daga ni seke? Ki tsaya anan in miƙo miki ruwa amma ba zaki shigo ba"
Haka tabi Ammar da kallo ya rufe ƙofar sa ya shiga gida ya miƙo mata ruwa ya koma.
Jinjina kai Fa'iza ta shiga yi kafin daga bisani ta bar gurin tana wani tunani a ranta.

Bayan Su Anty Maryam sun kammala cin Abincin dare, ta lura kamar akwai magana a bakin Mufeeda, ta kalle ta tace  "Mufeeda ya akayi ne?"
Ɗan shiru Mufeeda tayi sannan tace  "Dama Anty.. Inn.. Ina so in koma ne"

"Kin gaji da zaman nan kina kewar mijin ki ko?"
Saurin girgiza mata kai Mufeeda tayi tace  "A'a Anty Maryam, naga bashi da lafiya ne ko Abinci ba yaci, kuma ya bani haƙuri yayi nadamar abunda yayi"

"ki gayamin gaskiya, ko dai shi ne ya takura miki yace sekin koma?"

"A'a Anty be takuramin ba sam, kawai dai.."
Anty Maryam ta katse ta ta hanyar cewa "Shikenan naji, amma karki gaya masa zaki koma, zanga yadda za'ayi ki koma ɗin, koba komai ai mun hora shi"

*****************
Wasa2 Saima rashin lafiya take sosai, Amma Jabir kawai cewa yake rakine irin nata, ta kumbura sosai ga damuwa tayi mata Yawa komai da ƙyar take yi, Jabir kam yana ta rawar ƙafa akan Fatiyya dukda kasancewar ta 'yar masu kuɗi hakan be hanashi yin bajinta yana kashe mata kuɗi ba, yayin da tsakanin sa da Saima se ido, kullum yana kan waya ko chatting, gani yake gaba ɗaya Saima ta koma masa wani iri, ta dena kwalliya kullum cikin larura take, gashi ta raina shi shiyasa sam baya saurararta.
Yanzu ma yana zaune yana chatting ɗin sa se dariyar sa yake, Saima ta kalle shi tace
"Jabir yanzu haka zamu ci gaba da zama? Tsakanina da kai se ido ina fama da rashin lafiya ko a jikin ka sedai ka kalleni, ko kuma ka zauna kayi chatting da mata, babu ruwan ka da halin da nake ciki? Jabir kaji tsoron Allah"

"kinga Malama ya isheki, me kike so in miki? Zan cire miki ciwone? Ko kuma ni na ɗora miki? Kuma kina batun ina chatting da Mata danme ba zanyi ba? Kalli yadda kika koma kin Zama wata ƙatuwa kwalliyar ma kin dena, Kullum ke kenan cikin ciwo, nan ciwo can ciwo kaman akan ki aka fara ciki, nace kije gidan ku idan kika haihu seki dawo amma kin nace kinƙi tafiya, ya kike so in miki? Ba dai Abinci kikeyi wa ba, gashi nan na siya na ajiye kiyi taci"

Share Hawaye Saima tayi tace  "Jabir da ina da gata da tuni na barma gidan ka, kasan bani da kowa se Allah se kai, da na sa ran na samu mijin marainiya ashe ba haka bane, kake zancen kullum cikin ciwo nake bana kwalliya, da a haka ka ganni kace kana so? Kaifa ka maidani haka, kuma da kayi haƙuri na ɗan lokaci ne dana haihu Insha Allah zan koma yadda nake, Amma ina rabaka da Auren kwaɗayi Jabir, wallahi kaji tsoron Allah "

" Ubanwa yace miki Auren kwaɗayi zanyi? "
" karka sake ka zagi Ubana, kuma ba uban wani ne ya gayamin ba da kunne na naji, za'a baka gida da Mota saboda rashin zuciya, duk Ni'imar da Allah yayi maka kana da gidan kanka, kana da Mota Amma kana hange, wallahi Jabir haƙƙi na baze barka ba"
"Oho ke kika sani, 'yar baƙin ciki dan kinga faƙiran' yan gidan ku basu kawo ki da wani abun Arziki ba shine kikewa wasu Hassada, ko gishiri da Sunan gara ba'a kawo ki da ita ba"

"Yanzu Jabir hadda Gori zakayi min? Amma ai haƙƙin ciyar dani a wuyan ka yake"

"Dalla rufemin baki, Aure ne se nayi kuma chatting yanzu na fara"

"Shikenan Jabir kayi abunda kake so, Amma wallahi se Allah ya sakamin, dan bazan taɓa yafe maka ba, Azzalumi mayaudari ka lallaɓani ka Aure ni da daɗin baki da Komai, Shine yanzu ka samu abunda kake so, zaka Auro wata har tana ba zata zauna dani ba, kaje ka yi indai kaine gaka gata nan, dana haihu ka sawwaƙemin yadda za kuji daɗin zama"

Tsaki yayi ya wuce ya barta a falon tana kuka.

****************
Ammar har baya so ya tunkari komawa gida, musamman idan ya tuna Mufeeda bata gidan. Yanzu ma ba yadda zeyi ne, haka nan ya tunkari gidan yana komawa ya shiga da Napep ɗinsa harabar gidan yayi parking, Amma se yaji kaman ƙamshin turaren wuta, da sauri ya ƙarasa cikin falon ya tararar da komai tsaf se tashin ƙamshi falon yake, Ajiyar zuciya yayi ya lumshe ido yace
"ta dawo kenan" ya nufi ɗakin Mufeeda da Sauri, yana zuwa ya tura ƙofar ɗakin Amma yaga bata nan.
"Mufeeda" ya kira sunan ta da ɗan ƙarfi.
Gyaran murya tayi masa alamar tana banɗaki.
Guri ya samu ya zauna a gefen gadon ta yana jiran fitowar ta.
A ƙalla ya kai mintuna goma sha biyar  a zaune sannan Mufeeda ta buɗe ƙofar toilet ɗin ta fito.
Ba tasan yana ɗakin ba dan haka daga ita se towel ta fito, tana fitowa suka haɗa ido, ɗauke idon ta tayi tai gaba abun ta, shikam Ammar binta yayi da ido, tun daga sama bayan ta ƙugunta zuwa ƙafafunta, se sheƙi fatar ta take kamar wata tarwaɗa, kasa Magana Ammar yayi, Mufeeda ta tafi gaba wardrobe ɗinta ta ɗakko zumbulelen Hijjabi ta zura ta nemi guri tayi zaman ta.
Mamaki Ammar yake, Yarinyar da wata shigar idan tayi wataran sedai yabar mata falo, shine yau ta wani basar tasa Hijjabi, sharewa Yayi yace
"Ashe kin dawo?" maimakon ta amsa masa seta kalle shi kawai.
"Dakin min Waya nazo na taho dake, tunda baki da lafiya"
"Hmm to koma dai mene ne, ai gani na dawo"
"Ki tashi kisa kayanki mana, kinsa Hijjabi kin duƙunƙune ko har yanzu jikin ne?"
"toni kazo kana ta kallona, a haka zansa kayan?"
Ammar yace "Hmm shikenan bari in baki guri, ko akwai abunda kike buƙata in siyo miki?"
Girgiza masa kai tayi alamar A'a, ya tashi ya fice.

Yana zuwa ɗakin sa ya tarar da Abinci, wani murmushi yayi yai salla, sannan ya zauna yaci Abincin, rabon da yaci Abinci haka har ya manta, yayi missing ɗin Abincin ta sosai.

Har yanzu Mufeeda basar da Ammar take, taƙi sakin jiki dashi kamar da, yana rage mata ayyukan gida sosai saboda tana fama da laulayi sosai, Amma a hakan kafin ya dawo take masa girki ta gyara ko'ina.
Sam Mufeeda bata iya cin Abinci se 'yan kame kame yana matuƙar tausayin ta yadda take fama da laulayi amma ko inda take bata so yaje.

Yau Ammar be dawo da wuri ba dan se dare ya koma gida, yana komawa ya tarar bata falo ya bita ɗakin ta, yana zuwa ya tarar ta kwanta dan harta fara bacci, gaban gadon ta ya ƙarasa ya durƙusa yana kallon fuskarta data faɗa sedai fatar ta data ƙara haske, Zuba mata idanuwan sa yayi yana kuma ƙare mata kallo, Sosai Ammar yake jin Mufeeda a ransa, ƙamshin turaren Ammar ne yasa ta farka, A hankali ta buɗe nata idanuwan da suka yi mata nauyi saboda bacci kallon sa ta ɗanyi ta mayar da idon ta ta lumshe.

"Sannu ya jiki?"

"Da sauƙi" ta faɗa ba tare da ta buɗe idon ta ba.
"Ki tashi ga Maltina da fruit na kawo miki ko zaki iya ci, tunda ba kya iya cin Abinci" girgiza masa kai tayi tace
"Na ƙoshi"
Gaba ɗaya Ammar baya jin daɗin wannan Mood ɗin nata, ya kuma ƙasa da murya yace 
"har yanzu baki huce ba fushi kike dani ko?"
Girgiza masa kai tayi.
"to dan Allah ki tashi kici Abinci, bana jin daɗin yanayin da nake ganin ki, nayi nadamar maganganun dana gaya miki, Amma kiyi haƙuri bazan sake ba Insha Allah"
"Ai nima ya wuce a gurina"
"Banga alamar hakan ba tunda har yanzu bakya kulani kamar da, kin dena Yimin Addu'a, kin dena sakin jiki dani, ko sena bada cin hanci ne? Biscuit ko chocolate, gayamin wanne kike so?" Yai maganar yana sake langaɓar da kai cikin sigar rarrashi
Murmushi tayi tace 
"Ai am still under punishment, ko kaman ta ne?"
"Baki haƙuran ba kenan?"
Miƙewa zaune tayi ta kalle shi
"eh gaskiya ban haƙura ba"
"Meyasa?"
"Saboda baka sona"
Ɗan zaro ido yayi yace 
"Nine nace bana son ki?"
Cikin shagwaɓa tace "to ka taɓa cewa kana sona ne?"
Murmushi yayi yace  "Hmm wayo zakimin ko? Ni dai kiyi hakuri kidena wannan fushin"
Faɗawa tayi jikin sa ta rungume shi tace  "Nifa ya wuce"
Yasa hannayen sa ya ƙara rungume ta a jikin sa yace  "I miss you ƙwailata"
Murmushi tayi tace
"bazaka dena cemin ƙwaila ba ko?"
"Eh mana har yanzu ke ƙwaila ce"
"Hmm zan rama ne"

Daga nan suka jone abunsu ya sata a gaba yana bata Fruit

(Note: kayan marmari mussaman ga mace me ciki yana da amfani da kuma ƙara mata lafiya, yana dawo da test ɗin baki da sukan rasa mussman a first trimester wato watannin ukun farko)

Ammar yace" Anty Maryam ta wahal dani, nasan da dagani seke ne zamu sasanta da wuri, please idan mun samu Saɓani ki bari mu dinga gyarawa a tsakanin mu base wani yaji ba"
"Yaya Ammar nima ba haka naso ba, naso ka saurareni a lokacin amma kaƙi, kuma bayan fitarka naji kamar zan mutu shine na tafi gidan Yaya Amina"

"Hakane raina ne ya ɓaci sosai, nasan kina haƙuri da ni amma ki ƙara kinji Jaririya ta, ban san ina sonki haka ba seda na zauna a 'yan kwanakin nan babu ke, kin mun wayo kin shiga raina ba tare da na sani ba"

Murmushi tayi masa tare da kwanciya a jikin sa tace  "Yaya Ammar nima nasan kana haƙuri dani, duba ga yanayin ƙuruciya ta da kuma shirme na wani lokacin, Allah ya ƙara mana haƙuri da juna"

"Ameen, Amma ya aka yi haka ta faru baki sanar dani ba, hankali na ya tashi sosai akan abunda ya faru"

Nan ta zauna ta warware masa abunda ya faru tsaf tun daga ranar da aka fara kiran ta, Sannan ta ɗora da cewa
"Abunda yasa ban gaya maka ba, nasan halinka Yaya Ammar kallo ɗaya kake wa abu kayi masa hukunci, baka fiye tsawaita bincike ba, kana Amfani ne da abunda zuciyar ka ta gaya maka ko abunda idonka ya gani"
Ammar yace
"shikenan abunda za'ayi zaki bani layin da kike Amfani da shi, zan canza miki wani Insha Allah, Sannan zan duba matakin da zan ɗauka, Sannan gobe insha Allah zan maida ke Asibiti gaskiya, rashin cin Abincin nan yana damuna"

Haka suka shirya suka jone abunsu, dukda rashin lafiyar Mufeeda, be hana Ammar shan Shagalin sa ba, he show's her how much he miss her, Mufeeda kam taga ta kanta, yana ce mata ƙwaila Amma a hakan.... 🤭🤭, seda ya nutsu ya dawo hankalin sa, sannan kuma yaga yadda ya tara mata gajiya, ya taimaka mata ta gyara jikin ta ta kwanta  sannan ya tafi ɗakin sa.

*****************

Saima se tayi Sati ba ta riƙe naira ɗari biyu ba, Jabir baze kaita Asibiti ba dan haka befi sau biyu taje awon ciki ba, yauma da ta tashi maimakon yadda take ji ana faɗa daga alamomin Naƙuda akwai zubar ruwa se ita taga Jini, bata ɗauka matsala bane dan haka ta ci gaba da harkokinta sama sama, Sosai Marar ta ta fara ciwo, ga baya ya riƙe se jiri da take ji idon ta yana mata duhu,  Jabir ya fito falo yana gyara links ɗin rigarsa, kunnen sa ɗauke da wayar salula yana magana

"Haba my Fatiyya, kiyi haƙuri dan Allah, yanzu zaki ganni zanzo in kaiki da kaina, kina dani meye sekin jira driver ɗinku, ki jira gani nan yanzun nan zaki ganni"

Saima tace "Jabir dan girman Allah ka kaini Asibiti, wallahi ina ga haihuwa zanyi, bayana kamar ya ɓalle"

"to uwar ciwo, baki ma tabattar da naƙudar bace, ina EDD ɗinki se ƙarshen wata za kice wani naƙuda kike, ga ɗari biyu kije Asibitin in haihuwar ce se kimin waya"

Shiru tayi tana binsa da ido ya ɗau mukullin motar sa ya fice, duhu ta ci gaba da gani a idon ta dan haka ta nemi guri ta kwanta akan kujera

******************

Mufeeda taƙi yadda Ammar ya maida ita Asibiti tace ita likita yace se cikin ta yayi wata huɗu sannan zata fara zuwa Awo haka ya haƙura ya ƙyale ta.

Bayan fitar Ammar sega su Maman Amir sun shigo mata.
Fuska ba yabo ba fallasa Mufeeda ta karɓe su,
Maman Amir tace  "Mufeeda ashe baki da lafiya kina gida? Hankalin mu ya tashi kwana biyu bama ganin ki, shine muka tambayi mijin ki yace mana kina gida babu lafiya"

Mufeeda tace  "Eh banji daɗi bane ba"

Maman Sadiq tace  "Allah sarki sannu, munso muje gidan naku duba ki ai, to kin san halin Mijin naki bashi da fuska shiyasa bamu tambaye shi ba"

Mufeeda tace  "Ai na warware ma Alhamdilillah"

Maman Amir tace  "Aikam dai mijin ki bashi da fuska, ai Sa'idu me kayan miya ne ya gaya mana a gaban sa kika wuce kika hau A daidaita sahu kaman ba kya hayyacin ki, kina ta kuka bayan fitar shi mijin naki, shine hankalin mu ya tashi muka ce bari mu biyo muga ko lafiya, shine ya gaya mana ai baki da lafiya kina gida "

Mufeeda tace " Sa'idu me kayan miya kuma? "

Maman Amir tace " Eh wallahi munje cefane yake ga yamana "

Jinjina kai Mufeeda tayi ba tace komai ba, suka ƙaraci soki burutsun su, ciki hadda yi da Maman Nur wadda ta kasance a cikin su, Mufeeda ba tace musu komai ba, ganin Mufeeda bata da niyyar kulasu yasa su kayi mata sallama suka fita.

Ta biyo su tana ƙoƙarin rufe gate ɗinta taga ɗan gidan Maman Nur ya zubara mata da ƙanzo a ƙofar gida, kanta tsaye babu fargabar komai a gaba su Maman Amir, dukda tasan zasu gayawa uwassa tace seya kwashe, idan ya kuma zuba mata ƙanzo a ƙofar gida seta zane shi, haka yaron ya durƙusa ya kwashe yana kumbura fuska yace
"nifa ba barmu ce tace inzo in zubar anan"
Mufeeda tace  "ka koma ka gaya mata ƙofar gidana ba bola bace, ta dinga zubarwa a ƙofar nata gidan da yafi kama da bola akan nawa, idan na kuma ganin ka zuba min ƙanzo a ƙofar gida sena mareka"
Mufeeda tana sane ta faɗi wannan maganganun dan tasan se sun gayawa Maman Nur, tana shirin rufe gate ɗinta sega wata mata, za tayi shekaru Ashirin da bakwai ta kalli Mufeeda tace
"Baiwar Allah, kece Matar gidan nan dan Allah?"
Mufeeda tace  "Eh nice"
Matar tace  "Yawwa dama nice na tare a nan kusa da gidan ki, nazo mu gaisa bakya nan suna na Hajara"
Mufeeda tayi murmushi tai mata maraba suka shiga cikin gidan, suka zauna a falo, suka ɗan taɓa hirar rayuwa da hirar gida, Matar tace  "Amma sam banji daɗin zuwa na unguwar nan ba wallahi"
Mufeeda tace  "Saboda me?"
Hajara tace  "kwata2 matan layin nan kaman Awaki haka suke, naga basu da kintsi sam, tunda nazo suke ƙoƙarin shigemin nagane duk take taken su, idan basu yi wasa ba se nawa mace shegen duka da taɓarya"

"Subhanallah haba Anty Hajara, ai baza akai ga haka ba, maganin abun kawai ki fita sabgar su"

Mufeeda tayi ƙoƙari ta karkatar da hirar tasu, a yanayin maganar Hajara zaka san tayi gwagwarmaya rayuwa, bata da tsoro kuma a tsaye take, Mufeeda ta lallaɓa suka yi sallama.

Gaba ɗaya batun wai Sa'idu me kayan miya ne yake yamaɗiɗin ya ganta ta bar gidan ta tana kuka shine ya tsaya mata a zuciya, ina ruwan sa da ita daze mata haka, zuciyar ta ji take kaman taje taci uban sa, amma seta ga hakan ba mutuncinta bane a matsayin ta na matar Aure, da tana budurwa ne ba uban daze hana tayi masa tijara, da se tayi watsi da kayan miyar nan da cinikin da yayi sedai a kwao ƙarar ta Baba ya biya.

*****************
Tun daga tsakar gida Jabir yake Sallama amma Saima bata amsa ba, hakan yasa ya harzuƙa ya shiga falon da niyyar ya zazzaga mata rashin mutunci, amma me yana shiga ya tarar da Saima a ruf da ciki a ƙasa.

"ke Saima baki da hankali, wannan wace irin kwanciya ce haka? Sekin kashe min ɗa"
Shiru bata amsa masa ba, dubawa yayi se yaga Jini face face a ƙasan ƙafar ta da sauri ya ƙarasa ya ɗago ta, gaba ɗaya bakin ta ya karkace bakin ta duk bushashiyar kumfa tare da jini da ta daddatse harshen ta da alama jijjiga tayi babu alamar rai Sam a tare da ita.
"Na shiga uku SAIMA!!!"

****************

Mufeeda tayi deciding ko tayi wa Ammar maganar Sa'idu me kayan miya, fasawa tayi dan ta san halin Ammar ba haƙuri amma abun ya dame ta, ina ruwansa da ita? Ita ba shiga sabgarsa take ba amma har ya iya gayawa mutane ga a halin da ya ganta, dana sanin fita ta shiga yi a wannan yanayin daya ganta.

Haka Ammar ya dawo ya same ta, ya takura ta da tambaya akan meke damun ta, amma taƙi gaya masa.
Tana zaune a kusa da shi, yana cin Abinci ita kuma tana cin Aya danba ƙaramin daɗi Ayar  take mata ba.

Ƙwace ledar Ayar yayi yace "Mufeeda wai ba zaki Abinci ba se wannan tarkacen? Ni bana son wannan kayan shiritar da kike ci me zasu ƙara miki?"
Ya janyo ta jikim sa ya dinga ɗura mata Abinci ta naci tana kuka dan sam bata jim daɗin Abincin, aikuwa yana gama bata Abincin ta amayar dashi gaba ɗaya, Ammar shiru yayi ya rasa abunyi shi be taɓa zaton haka mata ke shan wahalar ciki ba, haka ya zage ya wanke kayan da tayi aman a jiki ya bata wasu ta canza.

Mufeeda ta kalle shi tace  "Yaya Ammar ko in koma gida ne kaima ka ɗan huta, idan na samu sauƙi se in dawo kana wajan dayawa"

"Na nuna miki na gaji ne? Lokacin dana Aure ki ai ba'a haka aka auramin ke ba, da lafiyar ki na Aure ki, ni yakamata in kula dake ba 'yan gidan Kuba, nifa Impact bana son kowa yasan da cikin nan, nafi so in kin haihu a gani"

Da sauri ta kalle shi tace  "Amma me yasa?

"Au meyasa ma kike tambaya? Haba ai da kunya a ganki da cikin nan, and am responsible for it, se aganni wani iri"

Kallon sa tayi da tana so ta gaya masa magana amma ta fasa, ya kalle ta yace "Ya dai?"
"bakomai ta bashi amsa"

Wayarsa ce ta fara ringing, ya ɗaga yayi sallama, Aminu ne cikin tashin hankali yace
"Ammar, Jabir ya kashe Saima"
A firgice Ammar yace  "Kamar ya ya kashe Saima?"
Aminu yace "toni mema zance maka ne? Ya fita ya barta taita jijjiga a gida ba kowa se ita kaɗai, ya kirani yanzu muna Asibiti, da naje gidan ko motsi ba tayi, a Yanzu babu me tabbacin tana raye"

Da ƙarfi Mufeeda tace
"Innalillahi wa innalillahi raji'un"

Ammar yayi jifa da wayar yace "Mufeeda ki kwantar da hankalin ki bata mutu ba ai, likitoci na duba ta"



AYI HAƘURI NAYI

Please Login or Register in order to submit comment