Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gurin nan, na barwa Allah"




Mufeeda na Adaidaita sahu zata koma gida tana ta kuka a Napep ɗin, Aminu ya kira ta ya sanar da ita abunda Ammar yace, tace
"to bari in ƙarasa gidan, se in turo maka"

A titi ta sauka ta biya me Napep kuɗin sa, ta fara tafiya sedai tana zuwa bakin layin taci karo da motar Alhaji Idris yana zaune akan motar, yana ganin ta ya sakko da Ƙaton cikin sa yana wangale mata baki yace
" 'yan matan daga ina haka? Naga kamar kina kuka, da safe naga fitar ki, shine na zauna ina jiran dawowarki"

Shiru tayi masa tana ƙoƙarin raɓawa ta gefe ta wuce, amma ya sha gaban ta yace
"Naji labarin ashema mijin naki ɗan ta' adda ne, yana hannun 'yan sanda, matsalar Auren mutane irin mijin nan naki kenan, ki kwantar da hankalin ki, kici Arziki ki barshi a inda yake, ni me ƙaunar kine, tunda an riga an kama shi ki manta da shi kawai"

Cike da ɓacin rai Mufeeda tace
 "Kaji labari ko kuma kasa aka kama min Miji saboda son zuciyar ka? , kuma kasan baya gida kazo gidana cikin dare kana ƙwanƙwasamin ƙofa, kasa an cajemu kuɗi masu yawa, to insha Allah Ammar baze ƙara kwana a hannun hukuma ba, ze fito, kuma kasani shi Allah baya bacci idan har dasa hannun ka akan abunda ya samu mijina, ko bance komai ba Allah yana kallon ka"
Ta ƙarasa maganar cikin hawaye, ta raɓa gefen motarsa ta wuce, ya girgiza kai yace 
"wannan Yarinyar akwai shegen taurin kak, baki da rabo amma muje zuwa da kanki zaki kawo kanki, dan talauci masifa ne, sannan bazan iya haƙura da yarinyar nan ba"

Mufeeda tana zuwa gida ta turawa Aminu kuɗin nan, tana kuka gami da tausayin Ammar ta tura kuɗin nan. Ammar yana matuƙar ƙoƙari da gwagwarmayar neman halak, ya tara kuɗinsa da ƙyar beci ba be sha ba, A banza an raba shi da haƙƙin sa, sosai ta dinga kuka tana tunanin wannan wane irin zalunci ne haka?

Bayan ta tura kuɗin ne ta shiga kitchen ta duba me zata girkawa Ammar kafin ya dawo, kayan Abincin su duk sun ƙare, ranar daza'a kama shi yace mata tayi masa list ɗin abunda ya ƙare ya siyo, Amma wannan ƙaddarar ta haushi.




Aminu ne ya cika kusan dubu Arba'in sannan kuɗin suka cika ya biya, da zasu taho daga station ɗin Ammar yace a bashi mukullin Babur ɗinsa, amma suka ce ba zasu bashi ba, zasu riƙe Babur ɗin se sun kammala bincike.


Mufeeda ta shiga tana duba kitchen, Taliyace da ita guda biyu ta ɗauki ɗaya ta dafa, tana da sauran miya ta gyara ta, ta zuzzuba a Flask ta ajiye masa tana dakon dawowarsa, se la'asar sannan taji ana knocking ɗin gate, da sauri ta tashi taje ta buɗe, Ammar ne shida Aminu, suna shigowa Mufeeda ta rungume Ammar tana kuka tace
"Allah ya saka mana Yaya Ammar, Allah ya ƙwatar maka haƙƙin ka, duk wanda yayi maka sharrin nan Allah ya saka maka"
Sosai suka bawa Aminu tausayi, Mutum me ƙaramin ƙarfi kamar Ammar ya tara 'yan kuɗaɗen sa da ƙyar Amma lokaci ɗaya a raba shi dasu abun da tausayi.

Aminu ya Jajanta musu, Sannan yace Insha Allah ze cigaba da bibiyar case ɗin a samu Ammar ya karɓi babur ɗinsa, Ammar yayi masa godiya da irin gudunmuwar da ya basu.

Ammar yayi wanka ya fito amma Mufeeda kuka take bata dena ba, ya zauna ya dinga rarrashinta, shi yanzu babban abunda ya dame shi shine babur ɗinsa da'aka riƙe, da Allah ya dogara da babur ɗin nan ya dogara, gashi kusan komai nasu na Abinci ya ƙare, ya daɗe yana tara kuɗaɗen sa gashi dare ɗaya babu su.

*******************

Saima ta fara samun Sauƙi, tunda akayi wannan sa'insar tsakanin kawunta da gwaggonta, gidan mariƙanta babu wanda ya sake zuwa duba ta, gwaggonta ce kawai a gurin ta take ta kula da ita se sauran wanda ba'a rasa ba, Jabir ma ya ɗauke ƙafarsa ya dena zuwa, ya samu Nutsuwar ci gaba da neman Auren Fatiyya.

Da'aka Sallameta tabi gwaggonta gidan ta, dukda itama me ƙaramin ƙarfice ga nata marayun Amma haka ta tafi da Saima tace Allah baze hanata yadda zata yi ta riƙe su gaba ɗaya ba.

******************

Rayuwa ta fara yiwa su Ammar wahala, da ƙyar yake iya samo abunda zasu ci inya fita, wataran sedai ya samo abunda Mufeeda zata ci shikuma ya haƙura.
Duk wata Sana'a da Ammar zeyi ta ƙarfi dan ya samu ya riƙe gidan sa yanayi komai ƙasƙancinta, Cikin Mufeeda ya shiga wata na biyar, ga wani irin yawan cin Abinci da take yi.

Duk Abunda ya kawo ya bata, bata raina wa hannu biyu take karɓa da murna tana Godiya koda kuwa abun be mata ba.
Itace ma take ƙoƙarin kwantar masa da hankali.

Gari ya waye da Safe, Ammar yana kallon ta ta ɗakko tuwon masara ta yayyankashi ƙanana tasa masa gishiri ta zauna tana cin Abunta da uwar safaiyar nan, saboda babu abunda zasu ci da Safen, tana yi tana kallon bollywood da suke wani shiri, yadda aketa sarrafa Naman kaji, tai shiru tana kallo gwanin ban tausayi da alama tana son ci ne. Ammar ji yayi kamar yayi kuka, gaba ɗaya tausayinta ya kama shi.

Ammar a rayuwar sa idan akwai abunda ya tsana be wuce ya keta bullensa yayi roƙo ba, tun yana ƙarami yake da wannan ɗabi'ar, idan har kaga ya nemi taimakon wani sedai idan ya rasa yadda zeyi ne abubuwa sunyi matuƙar ƙure masa

A hankali ya kalli ta yace  "Mufeeda"
Ta juyo ta kalle shi, tare da yi masa murmushi tace
"Na'am my sugar"
"Dan Allah kiyi haƙuri, ni kaina bana jin daɗin halin da muke ciki, a halin da kike ciki be kamata ace kina cin wannan Abincin da sassafen nan ba, Dan Allah ki ƙara haƙuri Mufeeda, sannan naji daɗi da kika rufamin Asiri baki gayawa kowa halin da muke ciki ba, Insha Allah komai ze wuce"
Ya ƙarasa maganar kamar zuciyar sa ta fashe dan ɓacin rai.

Mufeeda tayi masa shiru ta cigaba da cin Abincin ta, tuwon data ci ma ba ƙoshi tayi ba, taci ta ƙarasa da ruwa,  ta kalle shi tace
"Mijina, idan har na gujeka kona ɗaga maka hankali saboda yanayin da muke ciki Allah ma baze barni ba, duk abunda ya same ka ni ya sama, lokacin da kake samu dukda ba ƙarfi ne da kai ba, daidai gwargwado babu abunda baka bani na jin daɗin rayuwa iya ƙarfin ka, to wani dalili ne zesa in ɗaga maka hankali a yanzu, Jarrabawa ce Allah ne ya jarabce mu ina fatan Allah ya kawo mana mafita "

Shiru Ammar yayi yana kallon ta, ya kasa cewa komai.

"Yaya Ammar rufin Asirin ka nawa ne, Ina sonka Yaya Ammar fiye da yadda kake tunani, zan iya zama da kai a duk halin da kake ciki,saboda haka duk abunda ka kawo ka bani zan karɓa inyi Amfani da shi komai ƙanƙantar sa, sannan ina Amarya lokacin da su Baba suka zo sun ban dubu Goma, ban gaya maka ba saboda nasan zakamin faɗa kace meyasa na karɓa, shiyasa na haɗa da kuɗin da wanda kake bani kusan dubu goma sha biyar na bawa Yaya Amina nace ta yi Business dashi, idan ina buƙata zan mata magana, yanzu nayi mata magana na bata Account Number ɗinka zata sakomin kuɗin, seka ɗau dubu goma ka bani biyar tunda fridge ɗina biyu ne kuma ana samun wuta se in fara saida kayan sanyi, Amma me kace? "

Ajiyar zuciya yayi yace "zaki iya sana'a a haka? Karki wahalar da kanki fa"

"zan iya Yaya Ammar, zaman haka baze yuwu ba, kaga da ina Sana'a da abun yazo mana da sauƙi"

"Shikenan, Amma be kamata in karɓar miki kuɗi ba, sedai ko rance in Allah ya hore in mayar miki"

Haɗe rai tayi tace "Niba rance zan baka ba, kyauta zan baka kayi abunda ya dace dasu, kaga da Abba ze yadda a cikin dabbobi na ya baka ka siyar da wasu ka haɗa"

"A'a kin san halin Abba, baze yadda ba, Naji daɗi Sosai Mufeeda Nagode, Nag.....

"Shhhhh babu wannan tsakani na da abun sona, dan Allah Yaya Ammar ka kwantar da hankalin ka kaji, ni ba zan ɗaga maka hankali ba, mubi komai A sannu, Allah yasa haka shine mafi Alkhairi"

Ya amsa mata da Ameen, sannan yace  "ranar Litinin ya kamata ki koma awo, amma baki je ba, Amma in Allah ya kaimu sati me zuwa zaki koma Awo ina sane, Insha Allah"

Jinjina masa kai tayi tana masa murmushi.

*******************
Mijin Jidda ya dage kai da fata seya ƙara Aure, duk wani abu data san zata yi ta tayar masa ds hankali tayi amma kamar tana ƙara ziga shi, haka ta haƙura ta shiga gyare2, ya gina sabon gidan sa inda zasu koma gaba ɗaya ya haɗe su.

Tana so ta koma da sababbun furnitures, tace ya canza mata yace bashi da kuɗi, ita kuma kuɗinta ba zasu kai ba, tace bari taje tasa Ammar a gaba ya cika mata.

Sedai da taje ta tarar Ammar baya nan, Rashin mutuncin nata dai data sabawa yiwa Mufeeda bata dena ba, taita zuba ido Mufeeda ta zubo mata Abinci amma shiru nan ma ta samu nayi, ita dai Mufeeda ko uffan ba tace mata ba, ana haka Ammar ya dawo ya tarar da Jidda.

Se wani harare hararw take tana hura hanci ita ga me ɗan uwa, Bayan sun gaisa ta gaya masa abunda takeso yayi mata.

Ammar yace  "A gaskiya Jidda sedai kiyi haƙuri, bani da hali a yanzu bani da kuɗi, naga kayan kujerun naki aiba wani abun suka yi ba, ki tare dasu mana"

"dalla Yimin shiru, kace dai bazaka bani ba, ka taɓe a gindin mace se abunda take so, tunda kayi Auren nan ko ɗan Alherin da kakewa Mutane ka dena, Saboda wannan lotsatsiyar Yarinyar mara hankali"

"Ya isheki Yaya Jidda, a baya da ne miki babu nauyin kowa a kaina, kuma kinsan ina miki, yanzu kuma Akwai Nauyin Mufeeda a kaina, A yanzu idan na tauye haƙƙin ta nayi miki se Allah ya tambayeni, balle kuma bani da shi"

Abun ya nemi ya koma musu faɗa suka yi baran baran ta koma ta zage Mufeeda tsaf, Ammar yana tare mata, da haka ta bar gidan.

Ammar yaita rarrashin Mufeeda yana bata haƙuri akan irin abubuwan da Jidda take mata, Mufeeda tace
"Bakomai Yaya Ammar, ai wataran se labari nasan ze wuce"

"Yawwa 'yar Aljanna, ɗazu bayan fita ta Amina ta turo kuɗin nan, amma dubu Ashirin da biyar ta turo'"

Mufeeda tace  "Eh munyi waya da ita, wai a ribar data samu ne nima ta sanmin, seka bani dubu goma ka siyomin ruwan leda, se in rubuta maka kayan lemon da nake buƙata, in sanar da mutane na fara saida kayan sanyi"

Ammar yayi murmushi yace  "Shikenan, Allah yasa Albarka, Gobe in Allah ya kaimu da sassafe zan shiga kasuwa ana sauke kaya daga trailer, inje abunda na samu in ƙara da kuɗin hannu na se in siyo ko Omo ne da Sabulu a hannun 'yan sari in fito bakin kasuwa in siyar"

Idon Mufeeda fal ƙwalla tace  "Yaya Ammar zaka iya wannan aikin me wahala kuwa?"

Murmushi yayi yace
"Nifa namiji ne, da aikin soja zan tafi dan dai Baba baya so ne, karki damu zan iya kije ɗakin tsakar gida na siyo miki nama kici, ki ƙara haƙuri Mufeeda Insha Allah komai ze wuce"

"Yaya Ammar seda ka siyo Naman nan"

"Eh mana nasan kina so, kin daɗe baki ciba"

Allah sarki Ammar, harda fruit ya haɗa ya siyo mata, duk yadda tayi dashi yaci ƙi yayi, Amma yaji daɗin ganin murmushi a fuskar ta, sanadin wannan Nama data ci.

Tun Ammar yana sintiri akan Napep ɗinsa har ya haƙura,
Kullum da sassafe yake tafiya kasuwar singa, haka ze zage yaita sauke manyan buhunhunan kayan Abinci, abun da ya samu haka ze haɗa da kuɗin hannun sa ya sai ƙanan abubuwa kamar Omo da su Sabulu a hannun 'yan sari ya fito bakin kasuwa ya siyar.
Ammar duk sana' ar daya san zeyi ya samu kuɗi babu ruwan sa yin abarsa yake, wataran ya samu riba wataran ya faɗi amma hakan baya hana gobe ma ya fita.

Kamar wasa Mufeeda ta fara Saida kayan sanyin nan, dama kafin su fara seda taita gayawa Allah, abu kamar wasa wuni ake zuwa siyan ruwan sanyi da lemo, randa babu wuta ta bayar a siyo mata mai ta kunna inji, Sosai take ciniki.

Ranar da taga ta samu riba da yawa bayan Ammar ya dawo ya huta tace
"Yaya Ammar ya kamata ka siyo mana banki, kullum mudinga ajiye ɗari biyu, duk sati dubu ɗaya, zasu temaka mana wataran"

Ammar yace "hakane kin kawo shawara Jaririya ta, Insha Allah zan siyo mana mudinga ajiyewa"

Duk wannan hali da suka shiga Babu wanda suka gayawa, tare suke ta faɗi tashin su, randa suka samu suci me kyau randa babu suci abunda ya samu.
Allah yasa musu Nasibi akan sana'ar, Mufeeda tana daga gida amma tana cinikin ta sosai.

Kwana biyu Ammar beje gida ba saboda bashi da kuɗin daze musu alheri idan yaje, ranar wata Asabar yasa Mufeeda ta shirya suje, su fara zuwa gidan su Ammar idan yaso da Azahar, se suje gidan su Mufeeda.
Haka kuwa aka yi, suna Zuwa gidan su Ammar suka tarar da Abba a tsakar gida, suka gaisa.
Abba yace 
"Aikuwa Halima tana Islamiyyar safe, ita kuma taje wata barka nan ƙasa amma yanzu zata dawo, Ina A daidaita sahun naka ne?"

Ammar yace
"tana gurin gyara, Amma zan karɓo Insha Allah "

Abba yace "To Allah ya dafa, 'yata fatan kuna lafiya?"

"Lafiya ƙalau Abba"

"Masha Allah, tunda Allah yasa yau kinzo kafin ku tafi kya je kiga dabbobin ki"

Mufeeda tace  "To Abba nagode sosai Allah ya ƙara girma"

Abba yace  "Bakomai Mufeeda, Allah yayi muku Albarka, ni zan fita nasan ba daɗewa zata yi ba, zata dawo"

Ammar yace  "Shikenan Abba adawo lafiya"

"Allah yasa Ammar"  Abba ya fice

Mufeeda da Ammar suka zauna suna Hirar su, ɗakinsa na gwauranta dake cikin gidan ya buɗe musu suka shiga, Mufeeda tace
"Yaya Ammar wannan ƙatuwar katifar fa kamar ta Amarya?, bari in kwanta akai"

Ammar yace "Yi a hankali karki lotsamin katifa da wannan ƙaton cikin naki"

"Sena lotsa ɗin, ai da bani da nauyi, kaika mayar dani me nauyin"

Dariya yake mata yazo ya kwanta a kusa da ita yace
"Allah sarki Jaririya ta, ta kusa zama Mum koya zata yi raino"

"Ai baka tuna ni Jaririyar bace, ka haɗani da aiki"

Hirar su suka dinga yi cike da ƙaunar juna, wani lokacin Ammar yana kallon yadda cikin yake motsawa mussman idan tana bacci, ya ɗora hannun sa akan cikin nata, yana jin yadda yake ɗan motsawa, Da haka bacci ya ɗauke su.

Koda Umma ta dawo tayi mamakin ganin gidan a buɗe ba kowa, tana shigowa ta tarar da ɗakin Ammar a buɗe ga takalma a ƙofar ɗakin, tai magana kusan sau uku taji shiru, ta ɗaga labule, bacci suke sosai Umma ta  sauke labulen tana ɗan murmushi.

Aikace2 ta shiga yi, Ta ɗora girki Amma duk su Ammar basu san tana yi ba, Mufeeda bata samun bacci sosai, tana raba dare gurin Ibada da kaiwa Allah kukan su, sannan idan tayi sallar Asuba bata komawa bacci saboda Ammar da wuri yake fita, wani lokacin shida da rabi ya bar gida, da rana ta ɗan ɗaga kuma an dinga sintirin siyen ruwa da lemo kenan, dan haka basa samun ishashen bacci, mussman Ammar da yake Aikin ƙarfi.

Jiddace tayi sallama idon ta Jawur kamar wadda aka koro, Umma ta kalleta tace "Jidda lafiya kuwa?"

Fashewa da kuka tayi, tace

"Umma na shiga uku, Baban su Haidar wai Zainab ze Aura ashe? Ɗazu na samu labari, na shiga uku Umma, ta gama sanin Sirri na ta shisshige min, na yadda da ita Amma taci Amana ta, Nusaiba na taje har gida ta mata rashin Mutunci baki ga dukan da da baban ta yayi mata ba, na shiga Uku Umma.




Wata ta biyo ni private tace "Gaskiya baiwar Allah kin fiye tsananta masifa"
🤣 🤣 🤣 🤣 🤣  Sorry labarin ne yazo a haka. Ina godiya da Comments da shawara.



Ina Masoya na, lokaci yayi da zaku min kara ku nunamin ƙauna, kamar yadda kuka sani na shiga Gasar Matasan marubuta 2021, A gobe in Allah ya kaimu Asabar, 31 ga watan July rukuni na 7,wanda shine rukunin da nake ciki zamu saki litattafan Gasarmu, masu ɗauke da kalmomi 2500.
Na shiga gasa da littafi na me suna BAƘIN TABO, ku kasance dani domin ji ya taka ya a cikin wannan gajeren labari, ina fatan idan lokacin zaɓen labarin Gasar Yayi, zaku zaɓi labarina na BAƘIN TABO,
https://chat.whatsapp.com/J3lB9LvDu174M3yeR56BoK Mata kawai banda maza

Ina Alfahari daku Masoya a duk inda kuke.



Domin Sharhi Gyara, ko Shawara
Ayshercool
07063065680
✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨

( *Sai Mata* )

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

Please follow me on Wattpad, vote and Comment

ELEGANT ONLINE WRITER'S

NOT EDITED

                         Page 30

Hargowar Jidda ce tasa Ammar ya farka, yai shiru yana sauraron abunda Jidda take faɗa, rungume Mufeeda ya sake yi a jikin sa yana tunani, a ransa yace
"Allah nagode maka da ba Zainab na Aura ba, da ita na aura nasan tabbas ba zata iya  haƙuri da halin da nake ciki ba"
ya cigaba da shafa kan Mufeeda yana kallon ƙanƙantar ta, Amma akwai haƙuri da hangen nesa, tana yiwa Ammar so na gaskiya da zuciya ɗaya.

A hankali Mufeeda ta fara motsawa itama sakamakon kukan Anty Jidda, ta kalli Ammar tace
"Yaya Ammar su Umma sun dawo"

Ammar yace "tun ɗazu suka dawo ai"
"amma me yasa baka tasheni ba? Yanzu an gan mu tare muna bacci, yanzu ya zamuyi mu fita?"
Murmushi yayi yace 
"Ya zakiyi ki fita dai, ni ficewa ta zan yi"
Ta kalli agogon dake ɗakin ta ɗan zare ido tace
"Yaya Ammar lokaci ya ja fa, kalli Azahar tayi"
Ammar yace  "Eh tashi muje muyi salla"
"Yaya Ammar kunyar fita nake ji, Amma kamar muryar Anty Jidda nake ji fa"

"Eh ita ce" ya bata Amsa

Mufeeda tace "Kamar kuka fa naji ta nayi"

Ammar bece komai ba ya miƙe, ya basar ya fito tsakar gida, ya gaida Mama yai alwala ya fice masallaci.

Da ƙyar Mufeeda ta fito cike da jin nauyi, Jidda na ganin ta, wani baƙin ciki ya tokare mata zuciya.

Mufeeda ta durƙusa tace  "Umma ina wuni"

"Lafiya ƙalau Mufeeda, kin tashi ashe?"

Cike da jin Kunya Mufeeda tace"Eh Umma"

Umma ta fuskanci Mufeeda nauyin ta take ji sosai dan haka tace  "to yi salla kizo kici Abinci"

Mufeeda tace "to Umma, Anty Jidda ina wuni"

Banza Jidda tayi da ita, Mufeeda ta tashi ta tafi yin Alwala.

Umma ta kalli Jidda tace  "Ke kina jin matar ɗan uwan ki tana gaishe ki amma baki amsa ba"

"Umma ba dole in mata banza ba, yarinyar nan ta cuceni ba dan Ammar ya Santa ba da tuni Zainab ya aura, Amma yanzu kalli ya Aure ta, ni kuma zata Auremin miji na shiga uku Umma"

"Haba Jidda, da bakin ki kike cewa kin shiga uku? Ki fawallawa Allah lamarin ki mana, sannan kija girman ki, karki shiga sabgar ta balle inya aurota ta raina ki"

"Haba Umma ya kike wannan maganar, yarinyar Zainab nan ba sirrina da bata sani ba, wataran a gida na take wuni, kawai seta ci Amana ta"

Duk haƙurin Umma seda ta ƙule tace
"to Ubanwa yasa kike gaya mata sirrin ki? ashe har yanzu baki da hankali, kina girma kina shiga dawa, waya gaya miki ana haka? Ai koni da nake mahaifiyar ki ba komai yakamata in sani ba game da zaman Auren ki, Amma kinje kina gayawa wata sirrin Auren ki, watanma bazawara, yanzu kinzo kinamin kuka, ai kinyi kuskuren da baze taɓa gyaruwa ba, kuma karki ƙara zargin Mufeeda ba ita tayi miki ba, dama can Allah ya rubuta Ammar ita ze Aura"

Mufeeda ta fito daga banɗaki tazo ta tada Salla, ana haka Sega Yaya Maryam tazo, tana zuwa ta tarar da Mufeeda ta idar da salla suka shiga Hirar su, tamkar bata san halin da Jidda take ciki ba, suka cigaba da hira hadda Umma suka ƙyaleta.

Jidda tace "Wai Maryam baki san hakin da nake ciki bane?"

Maryam tace  "koma na sani mezan iyayi akai? Tun farko ni dama wannan Zainab ɗin ba tayi min ba, na baki shawara shaƙuwarki da ita tayi yawa, Amma kika ƙi ji, Abunda haƙuri be baki ba rashinsa baze baki ba, kuma wallahi in baki nutsu ba Abba yaji labarin yadda kike ɗagawa mijin ki hankali kin san sauran"

Sallamar Ammar ce ta hana su ci gaba da Hirar, ya shigo ɗakin ya zauna, ya kalli Yaya Maryam
yace
"Sarakan yawo, daga Yaya Jidda tazo shine kema kika taho ko?"

Anty Maryam tayi dariya tace
"A'a zuwan ta daban nawa daban, kawai mun haɗu ne, Ai bansan tare kuke da Mufeeda ba, banga babur ɗinka a waje ba"

"Eh yana gurin gyara ne"

Ya kalli Umma yace  "Umma me kika dafa ne, muna jin Yunwa fa, daga nan wani gurin zamu tafi"

Jidda tace  "Ammar shine kazo ka kula kowa, Amma ni ka shareni kamar baka ganni ba, balle ka tambayi halin da nake ciki, koda yake ba abun mamaki bane, tunda ka fi ƙaunar matar ka a kanmu, damuwar ta itace damuwa 'yar gwal"

"Wallahi tafi gwal"
Ammar ya bata Amsa kai tsaye cike da basarwa.

"Ni kake gayawa Matar ka tafi gwal ko?"
Shiru yayi mata yaƙi bata Amsa, a fusace tace
"Ai dama nasani, ba yau kasaba wulaƙantani ba akan Yarinyar nan, ƙiri ƙiri naje gidanka da buƙata amma kaƙi saurara ta, ko Abinci ya gagara a bani a gidan ka, kuma kana kallo ba kace komai ba"
Shiru Ammar yayi yana mamakin wani irin hali ne haka da Jidda.

Yaya Maryam tace "Haba Yaya Jidda, kema fa ɗan wasu kike Aure, kuma Yayan wasu, sannan ƙanin wasu, shekaru Ashirin da biyu yana miki bauta ya wahalta miki kamar besan ciwon nema ba, shikenan ke kuma wata ba zata mori ɗan uwanmu ba? Mu yiwa kanmu Adalci mana, me Ammar yake dashi wanda yake wahaltawa Mufeeda da har kike iƙrarin ya tare a gurin ta? Ita kin san halaccin da take masa? Kin san ita ɗawainiyar da take da shi, ai macen ma da zata iya Zama da ɗan uwan mu da irin halinsa na Fushi da zuciya, Yabo ya kamata ta samu"

gaba ɗaya Mufeeda ta takura taji babu daɗi abubuwan da suke faruwa duk a dalilin ta, Umma kuwa ta hau yiwa Jidda Faɗa, jiki a sanyaye Mufeeda ta bar ɗakin dan bekamata ta cigaba da zama ana rigima a kanta ba.
Tana fita Ammar ma ya miƙe yabi bayan ta, Abinci ya zubo ya jata ɗakin sa suka zauna yana bata, sedai sam hankalin ta ba'a kan Abincin yake ba.

Yana bata yana mata hira, Amma sam taƙi sakin Jiki, ganin haka yasa Ammar yace
"Shirya muje kiyi musu sallama, mu tafi"
Ta jinjina masa kai, haka aka yi jiki ba ƙwari Mufeeda taje tayi wa su Umma Sallama, ta zaci Umma zata canza mata Fuska ko wani abun, Amma taga saɓanin hakan.
Mufeeda tasa hannu a Jakarta ta ɗakko dubu uku tace "Umma ga wannan, ki ɗau dubu ɗaya a ajiyewa Abba dubu biyu"
Girgiza kai Umma tayi tace  "A'a Mufeeda, Nagode Allah yayi Albarka, Amma ai sunyi yawa, ki riƙe Abun ki, ga hidima tana tunkarar ku Allah ya raba lafiya"

Kunya ce ta kama Mufeeda, dan ba tayi zaton Umma ta gane tana da ciki ba, saboda bata cire hijjabin jikin ta ba.
Ammar kam ba kunya caraf ya amsa da "Ameen ya Allah Umma"
Mufeeda a ɗan Shagwaɓe tace  "Amma Umma meyasa idan Yaya Ammar ya baki kike

Please Login or Register in order to submit comment