Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take yi, fitowa tayi tsakar gida ta tarar ya haɗa kan kayan sa da nata ya wanke, duk ya shanya yana wanke adaidaita sahunsa.

Da sauri ta nufi inda yake tace "Yaya Ammar dan Allah kayi haƙuri, ban san ya'akayi ban tashi da wuri ba yau"

"to ni nace kinyi laifi ne?"

"A'a amma bekamata ace kai kayi aikin gida ba yau"

Ɗan kallon ta yayi ya ɗauke kansa ya ci gaba da aikin da yake yi, rigar bacci ce a jikin ta iya gwiwar ta.

"Allah dai yasaka maka da Aljanna mijin so, har wanki kayi mana ni har kunya nake ji idan naga ka wanke min kaya na, ni yakamata in wanke naka"

Ya ɗago ya kalle ta yace "Nakin ma in kin wanke ba fita za suyi ba, balle ki wanke nawa"
Murmushi tayi tace "bari inzo in tayaka wankewa"

"No nagode kije kiyi breakfast ɗinki rana tayi"

Ƙarasawa tayi ta riƙe duster da yake goge ruwan jikin Napep ɗin tace

"My love wai baka son in dinga samun ladane? Komai seka hanani yi"

"Aike ba afara baki lada ba, in kinyi abun kirki sedai a rubutawa su Mama"

Wani irin kallo tayi masa, wanda seda ya sashi yin murmushi be shirya ba yace
"Au Sorry namanta ashe fa ta isa afara rubuta mata lada da zunubi, ni shedane ma"

Zumɓura baki tayi tana kallon sa, aikin sa ya cigaba da yi, ya ɗago yaga still tana tsaye
"waiba cewa nayi kije ki karya bane?"

Juyawa tayi ta koma, taje ta zauna ta karya, seda ta gama sannan ya shigo falon ya kalleta yace

"Prof a haɗa min ruwa zanyi wanka"

Ba tace komai ba ta miƙe, taje kitchen ta ɗakko ruwan zafi ta shiga ɗakin sa, ya tuɓe gajeren wando ne a jikin sa, ya tsuguna a hanyar da zata wuce yana duba wani abu, ɗagowa yayi ya kalleta yace
"Wuce mana"
Se wani Sunkuyar da kai take kamar mara gaskiya.

Ta wuce shi ta shiga toilet, ta haɗa masa har zata fito yace
"tsaya inzo in duba, nafi son shi da zafi sosai"

Sauri take ta fito daga banɗakin ta bashi guri, amma ya riga ya shiga, ya kalli ruwan yaga yana tururi ya taɓa yaji da zafi, ya ɗago ze mata magana yaga tana ta sunkuyar da kai bata son kallon sa.

"duba kan Mirror ki bani sabulu"

Da gudu gudu ta fice daga banɗakin dan a matuƙar tsorace take, Ammar yana kallon yanayin ta, da ta ɗakko sabulun ƙofar toilet ɗin taje ta tsaya, kaman za tayi kuka ta ɗan zira sabulun tace
"gashi"

"Idan ba zaki miƙomin ba ki mayar bana so"

"to ai gashi ina miƙo maka"

Shammatarta yayi ya janyo ta cikin banɗakin.

A firgice tace "Wayyo Allah na Mama"

Ya riƙo ta gam yana kallon ta, gaba ɗaya a firgice take, jikin Ammar lulluɓe yake da gashi, ƙato ne na gaske, jikin sa a murɗe yake, kallo ɗaya zaka masa kasan ƙaƙƙarfan Namiji ne.

A hankali yace "wai meye hakane?, se wani sunkuyar da kai kike kaman kinga abun tsoro?"

Zazzare ido take tana ta sauke numfashi,

"Dan Allah Yaya Ammar ka cikani kayi wankan ka, ni bana son ganinka a haka"

"Meye ba kyason ganin?"

"dan Allah ka cikani"

Hannu yasa ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, Kaman yayi dariya yadda take rarraba ido, amma ya maze yace
"Ki jirani a ɗakin nan, idan kuma kika sake kika tafi nida kene"

Haka ta fito ta zauna a gefen gadonsa tana maida numfashi.

Ammar ya daɗe sannan ya fito, yana fitowa kaman ɗazu ta ɗauke idon ta daga kansa, basarwa yayi yaje ya ci gaba da shirin sa, juya masa baya tayi ta rintse idon ta ita a dole karta kalle shi.

"taso kizo"
Ta juyo a hankali taga ya saka dogon wando da shirt, tasowa tayi ta nufi inda yake tana raɓe raɓe, ya dube ta yace
"Mara kunya kawai, lokacin da kike yawo da underwear da nace kidena cewa kika yi sedai a raba falo, shine yau kike wani sinne kai, to ai nan ɗakina ne dole insa abunda nake so"

Zumɓura baki tayi, yace
"ni kike zumɓurawa baki?"

Da sauri ta girgiza kai tace "Nifa ba zumɓura baki nake ba"

"ƙarya nayi kenan?"

Da sauri ta girgiza kai tace
"A'a yi haƙuri"

Mufeeda akwai bada haƙuri, da ance tayi laifi za tace Allah ya bada haƙuri.

"zo nan ki zauna" ya nuna mata bakin gado.
Ta ƙarasa taje ta zauna, ya durƙusa ya buɗe drower ɗin jikin Mudubinsa ya fito da wata leda.

Wata jaka ce silver me matuƙar kyau ya ciro ya miƙo mata, yace

"Wannan ce Jakar da kika saka a status ɗinki?"

Zare ido tayi tace "Amma Yaya Ammar ai ba cewa nayi ka saimin ba"

"tambayar ki nayi itace?"

Jinjina masa kai tayi alamar Eh, idon ta cike da hawaye.

Ammar Yace
"to gata nan a kashe lafiya, lokacin da kika saka bani da kuɗin ta ne, Amma a kwanan nan Alhamdilillah idan na fita ina samun ciniki sosai"

Kasa magana tayi, kawai ta faɗa jikin sa ta rungume shi
"Allah ya biya ka da Aljanna mijina, Allah ya ƙara sutura da Arziki, Allah ya ƙara wa su Umma lafiya da nisan kwana, nagode, nagode"
Ji yayi kaman ya rungume ta sosai, se ya tuna za'a iya samun matsala dan haka yace
"to sarkin kuka, ke komai ma sekin masa kuka, godiyar ta isa haka"
Girgiza kai tayi tace

"ai babu kalaman da zanyi Amfani dasu da zasu nuna godiya ta a gare ka Hubby na"

"Wai kin gama jin tsoron nawane  da kika rungume ni? Mara kunya"

Cikashi tayi tana rufe ido, haka suka yi sallama ya fita.

Abunda ta lura shi ne duk lokacin da tayi wa Ammar wani abu da ya ji dadi baze nuna mata ya ji dadi ba, sedai zeta ƙoƙarin yi mata kyauta, ko wani abu da zeta farinciki.

Kamar yadda ya mata Alƙawari sati ya zagayo, ta shirya ya kaita taga gida,
Kaman Yadda Mufeeda ta tsara a ranar suka shirya zasu haɗu da yayyen ta a gida.

Ammar ya shiga da niyyar su gaisa dasu Baba, ya shiga ya gaida Baba, sun daɗe suna hira da Baba sannan ya fito ya shiga falon Mama, Su Yaya Fadeela, Anty Murja da Yaya Amina duk suna falon, Ammar ya shigo har ƙasa ya durƙusa ya gaida Mama
Mama tace

"Sannu Ammar ya gida, ya haƙuri da Auta?"
Murmushi yayi yace "Alhamdilillah"

Suka gaisa da su Anty Murja ma, an ɗan taɓa hira da shi kaɗan, yace ze tafi, Mufeeda ta tashi ta bi bayan sa

Seda sukace gareji tace
"Hubby yaushe zaka dawo mu tafi?"

"Se magariba insha Allah, yau ki huta sosai a gida"

Tai murmushi tace
"to ya za'ayi da Abincin rana fa?"

"Don't mind me, sena dawo ɗaukar ki"

"Shikenan I will miss you for the whole day Honey, take a good care of yourself"

Juyawa yayi yana murmushi ya fice.

Ta koma cikin gidan, tana zuwa Yaya Fadeela tace
"Shegiya Auta se da kika samu jakar nan, waye ya saimiki?"

"Mijina mana"

Yaya Amina tace
"kai Auta Jakar nan fa da tsada amma kika takura masa ya saimiki"

"Yaya Amina kema kin san bazan takura masa ba, gani yai na ɗora a status, kawai shekaranjiya ya bani"

Anty murja tace "Lallai 'yar gatan miji, gwangwajewa, kuma dan Allah yana sakin jiki ya miki hira? Baya son Magana"

"Nida sauran Mutane ɗaya ne da ba zamuyi hira ba?"

Yaya Fadeela tace "Oh ni Fadeela Allah rahimi, wai yau Autace a cikin mu ake hirar miji dake, Allah me iko"

Nan suka dinga hirar yaushe rabo, daga Auren ta zuwa yanzu ta ƙara ƙiba sosai kamar ba ita ba.

Cikin hikima Mama take bugun cikin Mufeeda don taji yanayin zaman ta da Ammar, amma yadda Mufeeda ke mata bayani ya tabattar mata Mufeeda na cikin kwanciyar hankali.
Mama tace
"Mufeeda mijin ki akwai tsatstsauran ra'ayi, ranar da yazo gidan nan ya gaishe mu, na bashi bushashshen kifi da Nono da aka kawo daga munjibir ya kawo miki, amma yaƙi karɓa wai basu kawo ba baze karɓe mana ba"

Mufeeda tace "to aini be gayamin yazo gidan nan ba"

"Yazo ya gaishe mu, ya kawo mana kayan miya fal"

"hmm be gayamin ba, Haka halin sa yake baya son aga gazawarsa ta ko ina, inaga ranar ne ya zomin da ƙaton kwalin madara, ko a zaton sa nina tambayeki"

"aini yaron ya birgeni, haka ake son magidanci ya zama me wadatar zuci, sannan kema tunda kinsan halinsa ki kiyaye duk wani abu da zakiyi daze nuna ya gaza miki a wani abun"

"Insha Allah Mama zan kula, kuma kinsan ni bame kwaɗayi bace"

"hakane amma duk da haka ya kamata ace na ƙara gayamiki"

Mufeeda ta tafi gurin Baba, nan ma ta shan take sukaita hira da mahaifinta wadda ke nuna yadda suka yi kewar juna, seda Baba ze fita da azahar sannan ta baro ɗakin sa.

Gurin su Anty murja ta koma suka ci gaba da hirarsu, taji daɗin haɗuwa da 'yan uwan ta yau, Ga masu ƙaramin ciki ga ƙananan yara haka aka dinga ɗora tukunya ana saukewa, Mama tasha hidima da' ya'yanta da kuma jikokin ta.

Ammar be dawo ba se bayan isha'i yazo ɗaukar Mufeeda, Mama tace aje ace masa "ya shigo yaci Abinci sannan su tafi"

Bahaka yaso ba dan yana matuƙar jin kunya, haka ya shiga sitting room ya zauna, Mufeeda ta kai masa Abinci.

Ammar yace "Nifa gaskiya inajin nauyi inci Abincin nan anan, kizo mu tafi gida se inci a can"

Haɗe rai tayi tace "nice mara kunya da naje gidan Umma har na zage na dafa na ci ko, Bansan me yasa kake haka ba Yaya Ammar, Iyayena ɗa suka ɗauke ka ba sirirki ba, kaman Yanda su Umma suka ɗaukeni 'ya, basa jin daɗin yadda kake yi ɗin nan fa"

Ɗan Ajiyar zuciya yayi yace "bahaka bane, ni tun asali irin wannan yana bani wahala, kuma ina matuƙar jin nauyin su ne, ba wani dalili yasa nake hakan ba"

"to yanzu dai in koma ince mata kace ba zaka ci Abinci a gidan ta ba?"

"zuba inci"

Ta zuba masa Abincin, Amma da ƙyar yaci se kace mace.

Mufeeda tayi shirin tafiya ta haɗa bagco guda na shirgi zata tafi da shi, kome ta gani a gida seta ɗauka tana so sukai ta faɗa da Yaya Fadeela akan seta ajiye kayan data ɗiba amma taƙi.

Mama tace "dan Allah ki ƙyaleta karku yi faɗa, ke se kace kece sakuwar ta ba Amina ba"

"Mama kenan da wani ne a cikin mu bazaki bamu ba, amma da yake Auta ce ai kin bata"

Mufeeda tace
"baki ji ba auta fa kika ce"

Ammar yai Sallama a ƙofar falon yace "Mama zamu tafi"

Mama tace "shigo mana muyi sallama"

Ya shiga ya zauna a gefe Mama tace "Ammar naji daɗin yadda naga Mufeeda Allah ya ƙara muku zaman lafiya, Amma dan Allah idan muka bada abu daga gidan nan, ba mun bayar bane saboda ka gaza, da kai da Mufeeda duk 'ya' yan mune, A cigaba da haƙuri"

Ammar yace "To Mama Insha Allah, nagode sosai"

Fadeela ji take kaman tayi dariya idan ta kalli Mufeeda wai Ammar ne mijin ta, koya take da shi oho?.

Ta ɗakko kayan ta, ta fito guri ta samu ta zauna zata saka takalmi da yake takalmin me igiya ne ga tsini, ganin da Ammar yayi zata ɓata masa lokaci yasa ya durƙusa yana taya ta saka takalmin, ya gama samata sannan ya ɗagota tsaye suka fita.

Anty Murja ce ta fara hango su ta window ta nunawa Amina, sun sha dariya sosai, Amina tace "ai nasani indai da Mufeeda ze zauna duk wannan izzar ze dena ta ne"

*********************

Kwanci tashi asarar rai, Mufeeda ta cika watanni huɗu cif a gidan Aure, a zaman ta da Ammar ta gama karantar sa fiye da yadda yake tunani, ta san fushinsa tasan farincikin sa, Ammar be tsaya iya sana'ar tuƙa a daidaita sahu ba duk wata sana'a da yasan zeyi ya samu kuɗi yana yi, iya yinsa yake ƙoƙarin ganin ya sauke duk wasu buƙatun gidan sa dana gidan iyayen sa.
Dukda a fari baya son Auren yana ganin Matar tasa tayi ƙanƙanta da Aure, Amma a ransa yana jinjina tarbiyya da haƙurin ta, bata da damuwa sam ita dai kullum burin ta ta jadadda masa tana sonshi, laifi ko ita tayi koba ita bace, idan taga ya ɗau zafi se tayi shiru, kuma ta bashi haƙuri dan a zauna lafiya kuma dan kar ransa ya ɓaci, dukda a wasu lokutan shike da laifin ba ita ba amma seta karɓi laifin.

'yan kwanakin nan Ammar ya lura kamar akwai abunda Mufeeda take shiryawa, amma ya kasa gano menene, be takura mata baya son yawan damunta, da tana so ya sani da tuni ta gaya masa.

Aka sanar dashi Jidda babu lafiya, ta kwan biyu a kwance, dan haka yasa Mufeeda ta shirya suje su duba ta, dan tunda yasan Jidda bata ƙaunar Mufeeda beyi gangancin kaita gidan ta ba.

Koda suka je gidan Ammar ya tsaya gyara parking din Napep ɗinsa ita kuma ta riga shi yin gaba ta shiga gidan.

'Ya'yan Anty Jidda ta tarar a falo, se wata mata a zaune a falon, Jidda tana bedroom din ta .

Mufeeda ta gaida matar dukda matar ma ba wata babba bace, Matar se kallon ta take.

Babu tsammani Jidda ta fito daga ɗaki taga Mufeeda, aikuwa take ta wani haɗe rai kamar taga kashi.

Mufeeda tace "Anty Jidda ina wuni"

"Lafiya"
"Ya jikin naki?"
"lafiya kalau"

Jidda ta kalli ta falon tace
"Zainab gafa Amaryar ku, matar Ammar"

Ai da sauri Zainab ta kalli Mufeeda tace
"Wannan ɗin? To ai wannan da Auren wuri Ammar yayi da ya haifeta"
"to gata nan dai"
Zainab tace "to aini Anty Jidda banga abun so anan ba, wannan ai bata kai macen da Ammar ze kalla ba balle ya aura, amma dai a ƙauye take ko?"

Jidda tace "A'a 'yar cikin birni ce, wataƙila ta gallabi iyayen ne shiyasa suka aurar da ita"

"Amma dai Ammar ya bada maza wallahi, meze samu a jikin wannan' yar kaman mutum mutumi? Kalleta fa"

Da farko Mufeeda tai shiru taƙi kula su, amma ta fara ƙuluwa dan haka ta zumɓura baki tace

"Abunda ake samu a jikin ko wace mace"

Zainab tace "ke karki sake kimin rashin kunya wallahi, yanzun nan se in tattaka ki, aini wallahi Anty Jidda wannan abun kunya ne inyi kishi da ita wallahi"

Sallamar Ammar ce ta katse Zainab dan sam basu san tare suke ba.

Yadda Zainab take Zaune jikin ta babu mayafi da wata pitted shirt haka Ammar ya shigo ya same ta bata rufe jikin ta ba, Mufeeda ta koma gefe ta haɗe rai.

Ya samu guri ya zauna a gefen Mufeeda, Ya kalli Jidda yace
"Sannu ya jikin naki?"
"Da sauƙi Alhamdilillah nama warware"
"To Allah ya ƙara lafiya"

Zainab ta kalle shi tace "Ammar ina wuni"
Ɗaga kai yayi ya kalleta yace
"lafiya kalau, ya me jikin?"

"gata nan taji sauƙi Alhamdilillah, Amma ta sha jiki"

Ammar yace "banga alama ba dan ƙiba ma tayi"

Jidda tace "a hakan ne ban rame ba, ai kuwa na rame sosai"

Zainab tace "Haba Ammar ka kalleta fa da kyau, Allah Anty na ta rame sosai, kalli fa na fita ƙiba yanzu" tai maganar tana wani girgiza jikin ta

Ammar yace "mhmm hakane"

Ya kalli inda Mufeeda take ta haɗe rai tai kicin kicin, tsagwaron kishi ne kwance a fuskar ta, ya ɗan matso kusa da ita yace
"Ya dai? Meke damunki ne?"
"Bakomai" ta bashi amsa

Ƙara ƙasa yayi da muryar shi yana leƙa fuskarta yace
"gayamin a kunne na meyafaru ne? "
Girgiza kai tayi tana tura baki.
"ko chocolate ɗince?" yai maganar yana murmushi.

Sam Ammar yama manta ba a gida suke ba, ba Zainab ba hatta Jidda kallon Ammar take da mamaki, Ammar ya zauna yana wannan murmushin sedai in a cikin abokan sa yake.

Mufeeda cikin shagwaba tace "ni mutafi gida"

"Anƙi a tafin, se da magariba zamu tafi, ga Zainab nan seta ta yaki hira"

Wata uwar harara tayi masa, ta yunƙura zata tashi ya riƙe ta yana dariya. Ɗaga kai yayi yaga yadda Jidda da Zainab ke hararar su.

Miƙewa yayi yace "bari mu tafi, Allah ya ƙara afuwa, ga wannan ki sai wani abun" ya ajiyewa Jidda kuɗi.

Jidda kasa cewa komai tayi se binsu da kallo, Mufeeda tace
"Anty Jidda, Allah ya ƙara sauƙi"
Tai waje abun ta.

Zainab ce ta biyo su da sauri tace "Ammar dan Allah ina son muyi magana"

Yace "yi sauri ina jinki, Prof ta fara gajiya"
Harar Mufeeda tayi ta tabe baki, kallon su Mufeeda tayi tai tsaki tai gaba abun ta.

Ba tasan me Zainab ta cewa Ammar ba, ya fito daga soron ya kunna Napep din suka tafi.

Suna zuwa gida ta fice daga a daidaita sahun tai tafiyar ta ɗaki, bata ko tsaya ta saurare shi ba.

Abincin daren sa a falo ta ajiye masa bata ko bi ta kan sa ba.

Da safe ma be sata a idon sa ba, dan haka ya bita ɗakin ta, tana kwance tayi rigingine tana kallon roofing ɗakin.

Ya kalleta yace "Azo a taimakeni da ruwan wanka in ba damuwa"

Juyowa tayi ta kalle shi, ba tace komai ba ta fito ta wuce shi, taje kitchen ta dafa masa ruwan ta kai masa banɗakinsa, ta fice seda ta tabbatar ya shiga banɗakin sannan ta koma ɗakin nasa tana gyara masa dan yayi ƙura.

Wayarsa ce take ta ringing, bata damu ba balle ta duba me kiran, Ammar ya fito daga banɗakin yana goge ruwan jikin sa yace
"bakyajin wayata tana ringing ne, miƙomin tunda ke bazaki ɗaga ba"

Ganin sunan Zainab akan screen ɗin wayar yasa ta ɗakko wayar hannun ta na rawa ta jefa masa a ƙirjinsa ta fice.

Binta yayi da kallo yana jinjina wannan kishi na Mufeeda, ɗaki ta tafi taje taita kuka saboda ɓacin rai, gani tayi kuka baze fishesheta ba dan haka ta fito falo tayi aikace aikacen ta.

Amma ta tarar Ammar yana waya a falon, ta daure ta tafi kitchen, ta kuma fitowa taga still waya yake, kuma alamu sun nuna da mace yake wayar, har tayi gaba kawai ta juyo a zuciye ta fizge wayar daga hannun sa ta buga ta da ƙasa.

Ɗagowa yayi a matuƙar zuciye cike da Masifa, ya kalle ta se huci take Hawaye na bin fuskarta.


Share please



Domin sharhi, gyara ko shawara
Ayshercool
07063065680.[08/07, 10:48 PM] Ayshercool: ✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

Please follow me on Wattpad, vote and Comment


https://www.wattpad.com/1096499534?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Ayshercool7724&wp_originator=NWkhlySuZ8Eug%2BopXFfcycv2JGS3axjaccC5%2FbUYT6YzeXAYV4ybw7FnTr8fHQDwo5ncF8TNfQfelSdeR5t0OZi0%2FKAiAcvwuLa561y0j%2BMpxBPI15z3EyzU4ZruY9KP




 

ELEGANT ONLINE WRITER'S

             

           

                  

                        Page 19

Binta da ido Ammar yayi, a fusace yace

"baki da hankali ne? Meye hakan kikayi? Ɗazu kin jefomin waya na ƙyale ki yanzu kuma kin fasamin waya kin kyauta kenan? Wace irin Yarinya ce ke haka? Wane irin hali ne wannan? "

Ta ɗago manyan idanun ta ta kae shi tace
"Nice bani da hankali ko? Nagode bani da hankali na Yadda"
ta juya da sauri tabar masa falon, binta yayi da kallo yana mamaki, ta masa laifi kuma tayi fushi

(Nikam nace ashe babu daɗi, mutum yayi lefi ya maze ya ɗorawa abokin zamansa laifin da gangan"

Har Ammar ya kammala shirin sa ya fice be kuma ganin ta ba, shima da ya fita be dawo gida ba se bayan magariba, bayan magariban ma daya dawo bega Mufeeda ba, ta ajiye masa duk abunda ya kamata wanda ze buƙata, amma bata falon.

*************

Washegari bayan fitar Ammar sannan Mufeeda ta fito falon, ta kammala ayyukan gidan ta zata ɗora girki amma taga bata da kayan miya, gashi bata kula Ammar ba balle ta gaya masa babu kayan miya, shiryawa tayi ta fita yin cefane, tunda ta fito kan babban layin taga Wata ƙatuwar Mota tana binta, bata kawo komai a ranta ba ta cigaba da tafiya.

Taje gurin Sa'idu me kayan miya domin Siyayyar kayan miyan, Sa'idu yace
"ko kece Amaryar kusa da gidan Maman Nur?"
"Eh Nice" ta bashi amsa a taƙaice.
"Allah sarki, da alama naga ke ba irin halinku ɗaya ba, kina da nutsuwa da hankali, amma yakamata ki kula sosai kiyi taka tsantsan dasu dan basu da kirki sam basu san ciwon kansu ba"
"to ni jna ruwa na? Ko tambayar ka nayi?"
"A'a naga kina da nutsuwa ne, shiyasa nace bari in miki magana kiyi hankali da su"

"Malam dan Allah bana buƙatar jin wannan maganganun naka, ka sallameni in tafi dan Allah"

"to shikenan, amma ni gaskiya na gaya miki"

Tsaki Mufeeda tayi ta karɓi kayan miyan ta tace
"Riƙe gaskiyar ka bana so" tai gaba abunta.

Biyo bayan ta me motar nan ya ci gaba dayi yana mata horn, juyowa tayi domin ganin dalilin da yasa ake mata horn bayan ta bashi hanyar daze wuce.
Parking me motar yayi, me ya buɗe murfin Motar ya fito, Babban Mutum ne a ƙalla ze shekara Arba'in da biyar, ya ƙaraso inda Mufeeda take yana wani ƙarama ta kallo yana murmushi, Sanye take da dogon Hijjabi tun daga Sama har ƙasa, ya gyara tsayuwar sa yace

"Baby tun ɗazu nake binki, ina ƙoƙarin yi miki magana amma ban samu dama ba"

Banza tayi masa tana ƙoƙarin wucewa, Ya kuma shan gaban ta kaman zasu haɗe yace "Haba 'Yar kyakywa, ya ina miki magana kinƙi saurara ta, ki tsaya kiji dame nazo mana"

"Malam meye hakane? Nifa matar Aure ce ka dena bi na dan Allah"

Kallon ta yayi daga Sama har ƙasa yace"Ke ɗince matar Aure? Nima ai mijin Aure ne, dan Allah ki bani lokacin ki two minutes kawai Beb, Akwai saƙo me girma da nake ɗauke dashi daga zuciya ta zuwa gare ki dan Allah ki saurareni mana, Kyakywar Baby kamar ki nasan bazaki wuce your sixteen age ba, baki dace da tafiya a wannan ranar ba"

A fusace ta kalle shi tace "Tir da Wannan saƙon naka, mara mutunci Ka kiyaye ni na gaya maka ina da Aure dan me zaka dinga bina haka? Wallahi zan maka tijara in taraka mutane a gurin nan na gaya maka, dalla ban hanya wuce dattijon banza kawai, wanda be san darajar Aure ba"

Ganin Mufeeda ta haƙiƙance ne yasa ya bata hanya karta tara masa jama'a, aikuwa da gudu2 sauri2 ta ƙarasa gida se haki take.

Duk abun nan daya faru akan idon Sa'idu me kayan miya, riƙe baki yai yana jinjina kai, Yace

"Au dama duk ustazancin nata na ƙarya ne, ance me Napep ne mijin ta me kuma ya haɗa ta da wannan me motar? Taɓɗijan mata na abunda suke so a duniya, Fuska biyu da rana tsaka lallai yau akwai zazzafar Jarida a majalissa" Nan ya ci gaba da ƙanan surutan sa.

Koda ta koma gida, mita ta ci gaba dayi da mamakin maganganun wannan shashashan mutumin mara mutunci, Seda tayi salla ta huta sannan ta ɗora girki, loka2 idan ta tuna abunda mutumin nan yai mata ta kan yi tsaki.

Sosai take missing ɗin Ammar, tayi kewar murmushin sa, da sauran Nishaɗin da yakan sata, amma idan ta tuna abunda Zainab ta dingayi masa ranar, da kuma Yadda take kiran sa a waya se haushi ya kamata.

Yauma ya gaji sosai bayan isha'i ya dawo gida, gaba ɗaya kwanakin nan da Mufeeda ta watsar da shi se yaga gidan yayi masa faɗi, gidan baya masa daɗi, kosan fitowa falon ba yayi ko Abincin ya fara ci se yaji baya masa daɗin ci, gashi yanzu duk wanda ze bashi Abinci inba na gidan sa ba ba yajin daɗin sa.
Abunda yake ƙara bashi mamaki be wuce Yadda take takatsan tsan gurin kiyaye ɓacin ransa ba, Amma ƙiri Ƙiri tayi masa laifi amma ta maze tana fushi, to zuwa ze ya rarrashe ta ko kuwa?
Wata

Please Login or Register in order to submit comment