Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Meyasa na kira baki ɗaga ba"

Kawai ta fashe da kuka, tsaki Ammar yayi yace "meya haka? Meye na kuka kuma? Kinsan abunda ba naso kenan"

"Yaya Ammar ji nake kaman inje in cewa Baba na fasa Auren nan"

Maimakon yayi farinciki da abunda tace se yaji ƙirjinsa yayi mummunar bugawa da ƙarfin gaske

Cikin kuka ta cigaba da magana

"Yaya Ammar meyasa kake wahal dani haka? Yaya Ammar ba laifi na bane da nace ina sonka, Ana ta tambaya ta me muke shiryawa game da shirin biki bani da amsa ko ganin ka kaƙi kazo inyi"
ta kasa ƙarasa maganar se fashewa da ta sake yi da kuka, shiru Ammar yayi yace

"Zaki gayamin sunan ne ko zaki cigaba da kukan?"

Cikin fushi tace "bazan faɗa ba ɗin kuka zan cigaba, kuma Insha Allah sena dena sonka tunda baka da tausayi" ta kashe wayar ta.

Sam irin wannan matsalolin Ammar yake gudu shiyasa sam baya soyayya yake mata kallon shirita, musamman Soyayya da ƙanƙanuwar yarinya, banda wannan dalilin akwai abunda zesa yarinya ƙarama kamar Mufeeda tayi masa tsawa haka? Ƙwafa yayi ya ajiye wayar tare da jan ƙaramin tsaki

Daga baya mufeeda taga rashin kyautawar abunda tayi ta zauna ta tsarawa Ammar message ɗin ban haƙuri ta tura masa.

Yayi mamakin abunda tayi beyi zaton zata bashi haƙuri ba, maimakon yayi responding seya shareta daga nan bata ƙara neman sa ba shima kuma be ƙara neman ta ba.

Baba ya biyawa Mufeeda kuɗin WAEC da NECO tana ta zuwa extra lesson, duk yadda suke da Fatee da irin surutun Mufeeda bata gaya mata Ammar ya kawo kuɗin Aure ba.

Mazewa kawai take yi, bata jin daɗin yadda bata samun damar jin muryar Ammar, sam baya nuna damuwar sa game da ita, amma ta dake ta watsar da shi ta ci gaba da Addu'a, dukda ba ƙaramin azabtar da zuciyar ta take ba, Amma hakan baya hana ta ta tura masa saƙonin barka da safiya, barka da juma'a ko kuma saƙonin kwanciya bacci tare da yi masa addu'oin tsari.

Ammar yana gani amma baya tankawa, amma duk lokacin da ya ga saƙonin yana jin daɗi, duk lokacin daya ga tayi jinkirin turo masa saƙo ya dinga duba wayar sa kenan, Amma fa baze iya ce mata ya gode ba, ko kuma yaji daɗin ganin saƙon ba.

Mama tayi mitar tayi tambayar harta gaji akan dalilin da yasa Ammar baya zuwa, ta zuba mata ido tana taya 'yar tata da addua, dan sam ta kasa gane inda wannan al' amri ya dosa ga tana yin magana mahaifin Mufeeda zece tana sukar lamarin auren ne.
Sam walwalar Mufeeda tayi baya, duk ta rame.

Yauma tana kwance akan gadonta ta zubawa fankar dake saman ɗakin ta Ido Mama ta shigo ɗakin ta kalleta tace
"to seki tashi yau yaga damar zuwa, yace ai masa sallama dake"

Mufeeda najin haka ta miƙe zaune da sauri, Mama ta kalle ta ta girgiza kai, Mufeeda bata taɓa tunanin Ammar zezo ba, ba tayi zatonsa a wannan lokacin ba.

Mufeeda ta shiga ta wanke fuskarta, ta zira doguwar rigar material baƙi da ja tayi rolling da mayafi baƙi ta fesa turare ta fita.

Yau shida wani ta ganshi sunzo wanda bata san wanene ba, suna ƙofar gida a tsaye, a hankali ta ƙarasa inda suke ta kalli abokin nasa tace "ina wuni?"

Jabir ya kalleta yace "lafiya ƙalau Amaryar mu, ya haƙuri da abokin mu?"

Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba.

Ammar ya lura tayi rama kome ke damunta oho? So yake su haɗa ido amma taƙi dan ƙwalla ce a idon ta, a hankali tace

"mu shiga ciki"

Jabir yace "ina nan a sha soyayya lafiya"
Hararar Jabir Ammar yayi sannan yabi bayan Mufeeda cikin takunsa na ƙasaita.

Cikin sitting room dake harabar gidan ta shiga yana biye da ita.
Gaba ɗaya ɗakin ya gauraye da ƙamshin turaren sa, Guri Ammar ya samu ya zauna, Mufeeda ta samu guri itama ta zauna.

Ba tare da ta kalle shi ba tace
  "ina wuni?"
"lafiya, ya Mutan gidan?"

Goge hawayen ta tayi tace "suna lafiya"
Ɗan ƙura mata ido yayi sannan yace "ke wai ke kuka baya baki wahala ne? Me kuma nayi miki yanzu?"

Tura baki tayi tace  "ni meye ma ba kayi min ba, Yaya Ammar yaushe rabon da in ganka? In tura maka saƙo babu reply, baka kira na a waya, ji nake kaman in haƙura kowa cemin yake baka sona"

Ƙura mata ido yayi yadda take magana tana tura baki, tana shagwaɓe fuska tana wani lanƙwasa wuya kaman karta dena.

Ammar ya kalleta yace  "Aini dama ban iya soyayya ba, ban san yadda ake yi ba, ke kikace kina sona, ni dama irin wannan shirmen ƙuruciyar ne bana so shiyasa nake son in auri babbar mace wadda ta gama hankali"

Murmushi tayi dukda fuskarta da guntun hawaye tace
  "Hmmm ni bani da hankali kenan?"

"ina me hankali ze zauna yaita kuka kaman ƙaramin yaro koda yake ai yarinyar ce, dan baki fi a sa zani goya ki ba"

A ranta tace aikuwa zaka ga yarinta yadda ya kamata, Sosai tayi dariya tace  "daza'a goya ni da naji daɗima, dana dena kukan"

Ɗan murmushi yayi abunda bata taɓa gani yayi kenan ba, dama idan yayi murmushi yana matuƙar yin kyau haka?

Leda ya miƙa mata bata karɓa ba tace "menene wannan?"

"karɓi ki gani mana"

Hannu tasa ta karɓa, shi kuma ya miƙe ze tafi ita ma ta miƙe da sauri
"Haba Yaya Ammar mintunanka nawa zaka tafi? Ni dan Allah karka tafi yanzu"

Ɗan tsuke fuska yayi yace  "Zaki fara ko?"

"Yaya Ammar yaushe zaka dawo?"

"Se wani lokacin"

"idan ka tafi seka daɗe baka zoba fa"

"Me zanzo inyi miki? Kallon wannan shiriritar taki da yarintar ta kokuwa?"

"Nice nake shiritar ko? Shikenan ka gaida Mama, Nagode sosai Allah ya ƙara Arziki"

Be amsa ba ya juya ze fice tace "Yaya Ammar"

Ya waigo, ta tako gaban sa, ta ɗan ɗauke idon ta daga kallon cikin idon sa tace

"I Love you so much My Ammar" ji yayi zuciyar sa ta shiga bugawa da sauri da sauri.

Ta raɓa ta gefen sa ta wuce





Ayshercool
07063065680

✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

     

ELEGANT ONLINE WRITER'S



             

                      Page 7





Gida Mufeeda ta shige dauke da ledar da Ammar ya bata ta nufi ɗakin Mama ta ajiye mata ledar

Mama tace "wannan fa?"
"shine ya bani"
Mama tasa hannu ta buɗe ledar, keyholder ne da sticker na engagement se kuma cingam da tarkacen chocolates, Mufeeda ba ƙaramin jin daɗi kyautukan nan tayi ba, ta koma ɗakin ta ta dinga murna.

Ammar kam Jabir ya sashi a gaba da tsokana

"gaskiya Ammar yarinyar nan tana da kyau tubarkallah kayi dacen mata, fatana Allah yasa ka riƙe ta amana"

Ammar yace "wannan ce matar? Anyi dacen haɗani da raino dai dan banda yarinta da shiririta babu abunda ta iya"

"kai kake ganin haka, Amma ni banga ƙanƙantar nan ba da kake ta faɗa sedai tana da ƙarancin shekaru kam"

"Hmm bazaka gane ba, ni nasan halin ta, amma ina wannan 'yar yarinyar ta isa aure, yarinya ƙarama da ita sedai ayi rainon ta"

Jabir yayi dariya yace "idan aka gama rainon nata sekuma me?"

"Sekuma ƙaniyar ka" Ammar ya bashi amsa, sosai Jabir yake dariya yana son ganin yadda wannan dramar zata kaya



Mufeeda ta rubutawa Ammar saƙo

"Babyn baby naga saƙonka nagode sosai Allah ya ƙara buɗi kaman kasan ina son chocolates sosai nagode agaida Mama"





Washegari Mufeeda taje makaranta, ajinsu yayi tsit babu malami a ajin, ana rubuta sunan masu surutu kowa yaja bakin sa ya tsuke, banda Mufeeda da bakin ta yaƙi rufuwa saboda farincikin da take ciki, ta ɗakko leda ta ajiyewa Ƙawarta fatee akan cinyar ta.
Fatee ta buɗe leda taga sticker da key holder da yawa a ciki, ta ɗakko keyholder ta karanta ganin sunan Ammar da Mufeeda a jiki yasa ta sakin wani ihu, gaba ɗaya attention ɗin 'yan aji ya dawo kansu, fatee tayi saurin toshe bakin ta, ta kalli Mufeeda cikin mamaki tace
"Mufeeda ni har kin fara bani tsoro, dan Allah dagaske wannan me napep ɗin ne ya kawo miki kuɗin aure? Ke kuwa me kika yi masa haka, ya amince dake?"

Mufeeda tace "Allah ne ya haɗa ba wayona ko dabara ta ba"

Fatee tace "shekaru nawa aka sa?"
Mufeeda ta Harare ta tace "six months yanzu saura wata huɗu da rabi ma"

"Amma Mufeeda lokacin ai ko ss3 bamu shiga ba, kuma karatun naki fa? Wallahi kinyi ƙarama da Aure"

"ke kika ga nayi ƙarama, karatu kuma na cigaba a gidan Yaya Ammar, wannan ki rabawa 'yan aji"

Haka kuwa aka yi Fatee ta bi mutane ta raba musu, nan da nan aji ya ɗau sowa, da hayaniya Mufeeda zata yi aure, kowa da abunda yake faɗa ita kuwa ta maze ta haɗe fuska.



***************
Gidan su Ammar suna ta shir sosai, dukda Ammar ba farinciki yake da auren ba amma yana ta ƙoƙari akan abunda ze haɗa na kayan lefe, dan baya son an kai kuɗin aure kaɗan kuma ace kayan lefe ma na kirki ya kasa samuwa, akwai wani gidan mahaifiyarsa na gado tace yaje ya gyara can ya zauna ko ya siyar a sai wani a wajen gari, haka kuwa aka yi aka saida gidan kuma yayi daraja sosai ya sai wani  a wajen gari ɗan matsakaici me kyau, sauran kuɗin ya ci gaba da shirye2.



Kasancewar Unguwar su Mufeeda ma cike take da masu ƙaramin ƙarfi nan da nan unguwar ta ɗauka akaita surutai wai wannan 'yar yarinyar mara kunya za' ayiwa Aure, kuma abun kunya duk bokon baban su ace ɗan a daidaita sahu zata aura, hada wanda suka tari mahaifinta wai mezesa ya aurar da ƙanƙanuwar yarinya kaman Mufeeda, shi kuma ya kan basu amsa da 

"wannan abune da ya shafi iyalina, kuma nan duniya duk wanda ze ƙauna cesu a bayana yake, dan haka banga laifin hakan ba"
Hatta malaman su Mufeeda sunyi mamakin jin aurar da Mufeeda za'ayi kasancewar mahaifinta ɗan boko wanda yasan mahimmancin Ilimi, shima seda suka gayyace shi makarantar amma ya ƙara tabbatar musu da baze canza ra'ayin sa ba, ba wanda ya gayawa Mufeeda da kanta ta nuna aure take so.


Haka mufeeda ta cigaba da fama da Ammar, mutum ne da baya son raini shi gani yake idan har ya sakewa Mufeeda raini ne ze shiga tsakanin su dan sam ba sa'ar auren sa bace, kaman yadda ya barwa zuciyar sa wannan ba aure zeyi ba kawai dai an hada shi da aiki ne.

Ita kuma Mufeeda ta sawa ranta cewar idan harta shiga gidan Ammar zata tabbatar masa da wata kissar se mata, seta sauke masa wannan zafin kan nasa, zata nuna masa itafa mace mace ce, komai ƙanƙantar ta kuwa.

Idan ta kwana biyu bata ji muryar sa ba, duk seta damu seta kira shi kota tura masa saƙo, dan harta gaji da magiyar yazo inda take, shima ɓangaren sa idan aka kwana biyu beji ɗuriyar ta ba se yaji babu daɗi amma baze iya kiran ta ba gani yake idan yayi hakan tamkar ya faɗo ne.

Mufeeda ta fara zana jarrabawar ta ta WAEC, ta dawo gida ta gaji ta tarar da 'yan uwan baban su na ƙauye sunzo.

Mahaifin Mufeeda ɗan garin garko ne dake jihar kano, yayi karatun sa na boko dana arabiya, Matar sa cousin sister ɗinsa ce duk' yan uwane bayan ya kammala degree ɗin sa na farko ya samu aiki ya dawo cikin gari zama, yana da yara bakwai huɗu mata uku maza Mufeeda itace ƙarama.

Mufeeda na zuwa ta tarar dasu, suka dinga mata guɗa suna ga amaryar su.
Mufeeda ta shiga suka gaisa ta wuce ɗakin ta tai wanka ta zubo Abinci Mama tace "ya jarrabawar?"

"Alhamdilillah Mama Jarrabawa tazo da sauƙi na amsa mafi yawa daga tambayoyin"

"Allah ya bada sa'a"

"Ameen Mama"

Mama ta fita 'yan uwan Baba suna ta tsokanar Mufeeda, wata ƙanwar baban ta tace

"ya kamata kizo in fara koya miki yadda rayuwar aure take tunda ke an saka naki auren a ƙurarren lokaci, kuma ke kaman har yanzu baki gama wayo ba balle kisan dabarun zama da miji"

Mufeeda ta ɗago ta kalleta tace "ki koyamin mene gwaggo? Taɓɗijan ai na haddace irin wannan faɗan naku da akaita nanatawa Yaya Amina yi nayi bari na bari, wannan karatun naku na mutan da ai munce wannan ƙarnin"

"Au haka ma zakice?"

"Eh mana ko akwai wani bayan wannan?"

Gwaggo safiya tace "hmm ai wannan yarinyar in baki rage wannan kaifin bakin naki ba da tsiwa wahala zaki sha a gidan aure lokacin mu, ai ƙasa ƙasa akewa miji magana, har tsuma kake karka yi wani kuskure daze ɓata masa rai"

Mufeeda ta ƙyalƙyale da dariya tace "Hajiya gwaggo ashe kuma kun iya iyayi, aini gani nake zamanin ku tsoron mazanku kuke ji, ni mijina baze zama abun tsoro a gurina ba, zan masa biyayya amma ba dai inji tsoron sa ba, saboda shine Abokin wasa na, Abokin shawara ta kuma Abokin kuka na"

Gwaggo sahura tace "ai kinji irin ta shiyasa auren yanzu baya zuwa ko ina"

Mufeeda tace "haba gwaggo sahura akan me zan auri miji bazan dinga wasa da shi ba se dai in dinga jin tsoron sa? Ba dani ba"

Gwaggo safiya tace "ba cewa akai kiji tsoron sa ba, ki girmama shi, zamanin mu kinga kwanon abincin miji kawai da butar sa  girmama su muke bama son wani abu ma ya taɓa su balle mijin"

Gwaggo sahura tace "ai Safiya mu miji na bisa mu muna ƙasa a zaune, idan magana yake duk nutsuwar mu muke tattarawa muna sauraren sa, miji na kujera mu muna ƙasa a zaune"

Mufeeda ta kwashe da dariya tace "Wallahi baze zauna akan kujera in zauna a ƙasa ba se kace zaman fada, ai yana kan kujera ni kuma ina kan cinyarsa" tai maganar tana watsa shinkafar ta a baki, ai gaba ɗaya suka ɗau salati, ta ɗago tana kallon su tace
"wai Salatin me kuke haka?"

Gwaggo safiya tace  "A'a bakomai ke wannan sha'anin naki babba ne"

Mufeeda tai murmushi a ranta tace  "ai maganin ku zan dinga yi ba zaku takuramin da wannan faɗan ba, ni se an koyamin wani zama da miji na haddace wanda aka koyawa su Yaya, yaushe zakumin huɗubar mutan da, shikenan bazan yi walwala da miji ba"



****************

Mufeeda tana ta Jarrabawa, Ammar har yayi ɗan wuya dan shirin aure ba na rago bane, dukda 'yan uwa da abokan arziki na tallafa masa amma shirin aure a gurin me ƙaramin ƙarfi abun akwai tausayi.

Ɓangaren su Mufeeda suna ta shiri suma, Yayyen ta har sun gaji da tsangwamar ta akan batun aure duk shawarar da zata yi akan shirin bikin ta da Baba take yi ko Yaya Amina.
Mama kam ta kasa sakin jiki tayi wa Mufeeda bayani sosai akan Aure da ƙalubalen dake cikin sa, kaman yadda take wa 'yan uwan ta a baya tana ganin ƙanƙantar Mufeeda sosai sedai lokaci2 tana gaya mata abunda ba'a rasa ba.

Se Mufeeda tayi sa' ar gaske ta haɗa da mita sannan Ammar zezo, idan yazo baya fin mintuna biyar ze tafi.

Babban abunda yake bashi mamaki yake kuma burge Ammar da Mufeeda bata taɓa ce masa ya sai mata abun naira biyar ba, ba ruwan ta da wannan bata roƙar sa komai, yana jin yadda Jabir ke complain akan yawan roƙon sa da wadda ze aura take yi amma sam Mufeeda bata wannan, yakanga Haliman gidan su da abubuwa tace saurayine ya bata amma shi ba wani abu da yake bawa Mufeeda amma sam bata taɓa masa magana akan hakan ba, sannan ko gurin ta yaje ta dinga murna kenan tana godiya, sannan wataran da yaje haka za ta haɗoshi da kayan ciye2.



Mufeeda Ta kammala Waec tana jiran lokacin fara Neco ta tura masa saƙon ta kammala jarrabawar Waec, yaga saƙon amma bece mata komai ba dan haka ta kira shi a waya

"Yaya Ammar shine nace maka na gama Jarrabawa ko kayi min Addu'a ko?"

"Na miki addu'a ai ɗazu da nayi salla"

"dagaske nagode sosai, ya kake yasu Mama?"

"lafiya ƙalau, zan ci gaba da tuƙi yanzu se anjima" ya kashe wayar sa, ɗan ƙaramin tsaki tayi ta ajiye wayar.



Daddare ta kasa bacci ta ɗau wayar ta seta ga Ammar ya turo mata da katin naira dubu biyu seda ta zare ido, har zata tura masa message ɗin godiya amma ta basar dole ta nunawa Ammar itama mace ce me cikakken aji.

ta buɗe data hira take da ƙawayen ta suna ta tsara yadda bikin Mufeeda ze kasance hirar tayi mata daɗi Sosai dan haka har bayan sha ɗaya tana chatting.

Ammar yayi mamakin ganin ta online kuma bata tura masa saƙo ba, dan haka ya tura mata

  "what are you doing online by       this time?"

"chatting nake" ta bashi amsa
"keda wa?"
"Me sona wanda ya damu dani yake bani kulawa"

Dummm zuciyar Ammar tayi be ƙara tura mata komai ba, ya kashe wayar gaba ɗaya, Abun mamaki bacci ya gagari Ammar yaji zuciyar sa tayi masa babu daɗi sam beji daɗin baccin yau ba.

Washegari da ya fita ma daya tuna abunda Mufeeda tace masa se yaji ransa ya ɓaci
"da kuɗin auren nawa akan ta take gayamin haka?" Ammar ya yanke shawarar zeje gidan su yau.

Mufeeda bata san da zuwan Ammar ba da yamma ta shirya taje ta kai ɗinkita gurin ƙanin mijin yayar ta Naziru da yake a anguwar su Yaya murja gidan nasa yake

Naziru yace  "Mufeeda se naji wai aure zaki yi wallahi ba amana, duk yadda na dinga nuna ina riƙo ina jira ki kammala secondary in bayyana manufa ta amma kawai inji wannan mummunan labarin"

Mufeeda tace "a gurin ka yake mummunan labari amma a gurina me daɗi ne, kuma ranar da nazo na karɓi ɗinkina da bikin yaya Amina a ɗan gaban shagon ka muka haɗu da shi"

Naziru yace "wallahi Mufeeda banji daɗi ba, nima ina so fa"

Mufeeda tace "sekuma kayi kana son nawa ne idan aka kawo ɗinkin gidan mu ka ɗinka na kowa kaƙi ɗinkamin nawa"

Kwastomomin dake shagon da abokan aikin sa suka saka dariya sun san dayake sun san Mufeeda sosai

Naziru yace "Ai duk cikin son naki ne, ina son inga kina wannan tsiwar ne shiyasa se in ajiye ɗinkin naki in ƙiyi miki"

"wallahi zaka sa in raina ka, ka kiyayeni"

"Raini na nawa kuma? Ai kin daɗe da rainani, tijarar da kikayi min da bikin Amina ma ai ta isa in san kin rainani, amma ai inada  kyau ko? Har Anty Murja fa na gayawa ina kamu"

"Kai Naziru dan na dena ce maka Yayan, wallahi mijina yafi ka komai kyakkyawan gaske ne in gaya maka, kuma ka nemi wata ko ka jira idan na haihu in baka 'yata"

Dariya Naziru ya dinga yi  "lallai kin gama raina ni Autar amma nikam ba gudu ba ja da baya"

Ganin abun Naziru bane ƙarewa bane ya sata fice tayi tafiyar ta, gidan yaya murja ta tsaya seda aka yi sallar magariba Mijin Yayar ta ya dawo shima tsokanar ta yake
"Allah sarki autar mu ta kusa zama amarya, amma mijinki zeyi fama da wannan bakin naki"

Anty murja tace "Kuma wallahi idan ka ganshi ko fara'ar kirki ba yayi, yazo ɗaurin auren Amina dan dai ba lallai ka gane shi bane, Amma wannan banga alamar yana son hayaniya ba, naga yadda za'ayi wannan zaman, gashi da wani jin kai"

"Ni ban san me Ammar ɗina ya tsare miki ba wallahi duk kinsa mana ido, haka nake son abuna"

Mijin Anty murja yace "ƙyale Antyn nan taki ki cigaba da son abunki, Allah ya baku zaman lafiya, aishi namiji indai yana son mace duk wata izza baze mata ba"

Haka ya ci gaba da zigata, se wajen sallar isha'i sannan Mijin Anty Murja ya maida Mufeeda gida a motar sa da rakiyar ɗansa.



Ammar tun sallar magariba yake unguwar su Mufeeda akace bata nan taje gidan Yayar ta, daya ke ba da napep ɗinsa yazo ba ya samu guri yana jiran ta, amma ga mamakin sa ya hango Mufeeda ta fito daga motar wani, seda ta ɗan tsaya suka yi sallama da me motar ta ɗaga masa hannu sannan ta shige gida.

Ammar ji yayi duniyar tayi masa zafi yaji zuciyar sa tamkar ta fasa ƙirjin sa wani abu ya tokare masa rai.

Har ya yanke shwarar yayi tafiyar sa amma ya fasa ya kira ta a waya, seda yayi mata missed calls uku wayar tana cikin jakar ta a ɗakin ta bata sani ba, kaman wadda aka mintsila ta ɗakko jakar ta taga wayar ta na ringing ta ɗaga da sauri tace
"Am Sorry My Ammar wayar tana cikin jakata ne"

"Ina kofar gidan ku" shine abunda ya furta da ƙyar.

Da murna ta ajiye wayar ta kalli kanta a mudubi, tsaf da ita kwalliyar fuskarta tana nan, janbaki ta ƙara ta sake gyara ɗaurin kanta ta fesa turare ta leƙa ɗakin Mama tace

"Mama Yaya Ammar ne yazo bari inje"

Mama tace "au be tafi ba dama, tun magariba yazo ai na ɗauka ya tafi"

Mufeeda tace "Allah sarki Yaya Ammar ɗina, Allah yasa saurk be cije shi ba"

Ƙwas ƙwas da takalmin ta me tsini tai waje da sauri.

Tana zuwa ta leƙa bata ganshi ba, ta kira shi a waya, se gashi ya ɓullo ta lungun dake kallon gidan su Mufeeda ta juya ta koma sitting room inda idan yazo take saukar sa.


Yana shigowa ta fara magana cikin shagwaɓa Yaya Ammar ashe tun ɗazu kazo baka kirani a waya ba, yau Allah yayi zan ganka ba tare da nayi magiya ba, kallon sa tayi taga fuskarsa a ɗaure babu annuri hakan yasa tasha jinin jikin ta.

Ammar yayi niyyar ya nuna mata ainihin waye Ammar amma maimakon haka seya kasa yi mata faɗa yadda ya ƙudurta a ransa, gani yayi ma yau tayi wani irin kyau sosai ko dan yau ba kukan take ba, amma daya tuna a motar wani yaga an sauke ta se ya ɗaure fuska sosai cikin kakkausar murya yace
"Daga ina kike?"
"ɗinki na kai" ta bashi amsa cike da fargaba

"ɗinkin ne se yanzu zaki dawo? Daga motar wa kika fito?"

Ya faɗa yana ɗan ɗaga murya, gaba ɗaya mamaki ya lulluɓe Mufeeda tace
"Wace motar kuma?"

"Tambaya ta ma kike yi? Waye ya sauke ki a mota? Sannan ina kika je? Bari kiji in gaya miki bazan ɗauki rainin hankali ba, tun wuri idan kin san abun da zaki dinga yi kenan ki koma ki janye batun auren mu, bana son rawar kai, saboda kin rainamin hankali jiya har sha biyun dare kina chatting na tambaye ki kince wai dame sonki kike chatting, yau kuma dan ki tabbatar min shine aka sauke ki a mota ko? Tun farko inkin san me motar kike so meye na cewa kina sona har in kawo kuɗin aure, me yasa baki tsaya a me motar ba kika ce kina son talaka kamata, idan har kinsan kina da hange karki soma yadda da aure na" ya tako har gaban ta ya kusa haɗe ta da bango yace
ki gayamin waye ya sauke ki a mota"

Gaba ɗaya jikin ta ya mutu, wani irin ƙamshin turare yake me daɗin gaske, yayin da shima dakewa yayi dan ƙasan zuciyar sa na yaba kyawun da tayi.
Idonsa ta tsaya tana kallo taji zafin maganganun sa, amma tana iya ganin tsagwaron kishin ta a cikin idon sa, a ranta tace Ammar kenan a fili kuwa tuni hawaye ya wanke mata fuska.

"ina tambayarki kina min kuka, kin san abunda bana so kenan, ki gayamin abunda na tambaye ki"

"tabbas da ina da hange kuma so zemin adalci dabe yi gigin kaini ga afkawa son wanda bana gaban sa ba, idan har ina

Please Login or Register in order to submit comment