Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace "yaushe kukaje gidana keda su Fa'iza?"

"wancan satin ran Asabar" ta bashi amsa

"Da kukaje akwai abunda ya faru da ku kaje ne?"

"A'a ba abunda ya faru, sedai su Yaya Nasreen ne suka dinga gaya mata baƙar magana, da zamu tafi suka ce zasu ga gida, ta shiga dasu ko ina tace ba zasu shiga ɗakin da kake kwana ba, shine suka dinga zagin ta, kuma bata kulasu ba, tace dai kome za suyi suyi ba zasu shiga ba"

Jinjina kai Yayi yace "Shikenan jeki, se an jima" daga nan ya hau Napep ɗin sa ya tafi.

A hanya ya haɗu da Aminu, ya tsaya suna gaisawa, Aminu yace "lallai mutumin nan wato tunda Allah yasa aka kaimaka ƙwailar ka, ko neman mu baka sake yi ba, kaga yadda kayi wani shar da kai dan Allah me take baka ne?"

Ammar yace "ban sani ba, na shigo rannan naje gidan ka baka nan, Jabir ma kunyar sa nake ji, ina so muje gidan sa nida Mufeeda sannan kaima in kaita gidan ka, tunda Jabir yai Aure sau ɗaya naje gidan sa se dai mu haɗu a unguwa"

Aminu yace "Kai Ammar ƙyale wannan Auren na Jabir, ƙaniyar sa kawai yake ci, Allah ya kiyaye kar auren nan ya mutu"

Da sauri Ammar yace "haba dai, saboda me auren da befi watanni huɗu ba zuwa biyar ba, shine ze mutu?"

"Ammar abun ne ba'a cewa komai, su matan se a hankali muma mazan hakan take, kasan halin Jabir shi kawai kyau da body structure na yarinyar yabi ya aure ta, amma she's not wife material at all, Sam bata ganin girman sa, rannan yake gayamin faɗa cikin dare shi da ita zagi in zaga"

"Subhanallah garin yaya haka ta faru da Jabir, sam bemun zancen ba"

"Ai zancen ne babu daɗi dan haka ba lallai yai maka ba, sedai mun haɗu zancen nada tsayi, Amma Jabir na buƙatar mafita"
Hama sukayi sallama da Aminu, Ammar ya tafi yana tunani a ransa, yayi zagi in zaga da mace kuma ya ci gaba da zama da ita baze yuwu ba, yana daga cikin illar Auren yaran nan da basu gama hankali ba. Wunin ranar haka yai ta saƙe saƙe, gefe yana tunanin yaze warware matsalar sa da Mufeeda.

Bayan sallar isha'i ya koma gida, Tana jin dawowarsa amma bata fito ba, yana ta tunani me yakamata yayi ne, yana son ya ganta amma sam bata fito falon bama balle ya ganta.

Yayi tunanin ze iya zama makircin su Nasreen ne abunda suka faɗawa Jidda, Amma baze iya tunkarar Mufeeda ya bata haƙuri ba, idan yayi hakan zata raina shi, ko kuma ta samu damar wulaƙanta su anan gaba, Amma yadda take kukan nan ya kamata ace ya ganta.

Tashi yayi ya nufi ɗakin ta, ya tura ƙofar ɗakin a hankali, akan dadduma ya hango ta ta duƙunƙune a cikin hijjabi, da alama kukan take, tausayinta ya mamaye zuciyar sa, ya ɗanyi gyaran murya yace

"ba'asan na dawo bane?"

Juyowa tayi ta kalle shi a sanyaye tace "bana so in fito kaƙi kulani ne" tai maganar wasu Hawayen na fitowa daga idon ta.

"Azo a bani Abinci, ina jin Yunwa"
Ai da sauri ta miƙe tsaye ta cire hijjabin jikin ta tare da ƙaƙalo murmushi tana goge hawayen ta tace

"dagaske ka haƙura zaka ci Abincin?"
Jinjina mata kai yayi alamar "Eh"

Cikin sauri tace "bari inje kitchen in ɗora yanzu zan gama"

"Shikenan ina falo ina jiranki" ya juya ya yafice daga ɗakin, farinciki yasa ta kasa dena kukan da take, ta fito falo ta ɗakko masa ruwa da cup ta kai masa kaman yadda take masa in ya dawo.

Yasa hannu ya karɓa sannan ya zaunar da ita a kusa dashi, yasa hannu yana goge mata Hawayen fuskar ta, yace
"kin san bana son kuka ko?"
Jinjina masa kai tayi, yace
"to me yasa kikeyi dan ki ƙara ɓatamin rai?"
"Ai kaine kake fushi dani kuma na baka haƙuri kaƙi haƙura"

"to ai yanzu na haƙura, sedai abunda nake so dake, ko a nan gaba karki kuskura kiyiwa wani wulaƙanci a cikin 'yan uwana, sannan duk wanda ya wulaƙanta ki ko ya miki wani abu ki gayamin zan ɗau mataki akai"

Girgiza masa kai tayi tace  "A' a Yaya Ammar idan sunmin wani abun ma ni bazan gaya maka ba, bana son in dinga ɓata maka rai ko wani abu na ɓacin rai ya shiga tsakanin ka dasu na ɓacin rai saboda ni, kuma ni ba wani abu da suka yi min da zesa in kawo ƙararsu gurin ka, ni ɗinma da suka ce na musu ba daidai ba, ba ina sane bane kuma nace ka basu haƙuri "

Gaba ɗaya mamakin maganganun ta yake, ga wani tausayinta da ya kama shi, ita dai kar ransa ya ɓaci shine babban burin ta.

Ya kalle ta yace "kina cin Abinci kuwa? Naga kin rame"

Shiru tayi ba tace komai ba se kallon sa da take yi.
"je ki ɗora mana Abinci ina jin Yunwa kwana biyu nayi missing jagwalgwalonki, Umma tace a gaisheki wai jagolgwalon Abincin ki da daɗi"

Murmushi tayi tace "Yawwa gara da umma ta faɗa ai, nasan Abinci na da daɗi ai"

Ɗan Murmushi yayi yace "dama kin kai musu Abinci ban sani ba? Ai shikenan tunda an wareni suna ta godiya, nima nagode sosai naga kaman ma sunfi sonki yanzu akai na"

"Idan na kuma yiwa su Umma abu kayi min godiya, zamu ɓata da kai zan dena kula ka, ni su Umma iyaye na" tai maganar tana ɗan zumɓura baki.

Ammar ba ƙaramin jin daɗin abunda ta faɗa yayi ba.
Yau taƙi zuwa ta zauna kusa dashi sosai balle ya shaƙi wannan dadaɗan ƙamshin turaren na jikin ta.

Ta miƙe da sauri tace "bari inje in ɗora Abincin nasan kana jin yunwa sosai"

Ta tafi kitchen ta ɗora sanwa, cike da farincikin yau mijin ta ya sakko daga fushin da yake da ita, yana nan zaune ya kallo wayarsa ta fara ringing baƙuwar lamba ce dan haka ya ɗaga tare da yin sallama, Muryar Zainab ce ta amsa sallamar, haɗe rai Yayi yace "ya akayi?"

"Shikenan Ammar bazan kira ka mu gaisa ba? Har yanzu ina nan ina dakon soyayyarka a raina na kasa mantawa da kai"

"baki san nayi Aure bane zaki dinga kirana duk lokacin da kika ga dama?"

Mufeeda dake kitchen ce ta fito zata je tsakar gida ta ɗakko tsintsiya, karaf taji yana waya da mace, turus tayi ta tsaya tana kallon sa, shima ɗaga kai yayi suka haɗa ido, wani banzan kallo tayi masa ta fice ta ci gaba da aikin ta, dukda jikin Ammar Yayi sanyi da irin kallon da tayi masa, amma be kawo komai a ransa ba ya ci gaba da wayar sa.

"Look zainab bana son shirirta, idan Allah ya baki miji kiyi haƙuri kiyi Aure kawai, ni bani da halin riƙe mata biyu" zata kuma magana ya katse kiran.

Mufeeda da ta koma kitchen kawai ta tsinci kanta da zubda Hawaye, dukda kasancewar ta yarinya ƙarama kuma me kawaici tana da matukar rauni a ɓangaren kishi.

Ta kammala ta zubo masa Abincin ta kawo gaban sa ta ajiye masa komai ta juya zata tafi, yace
"ke ba zaki ci Abincin ba?"
"Na ƙoshi" ta bashi amsa tana ƙoƙarin tafiya ɗakin ta.

"idan ba zaki ci ba, zoki ɗauke Abincin ki nima bana ci"

Dawowa tayi ta zauna, ta zuba masa Abincin ta miƙa masa.

Nasihar Mahaifinsa ya tuna akan yayi haƙuri ya kula da Matarsa ƙaramar Yarinya ce, kar ya dinga nuna mata wannan yawan fushin nasa.

Ammar neman shiri yake da Mufeeda dan haka ya Karɓa  ya matso kusa da ita, ya ɗebo Abincin a cokali ya kai bakin ta
"maza ungo karɓi kici, nasan kema kina jin Yunwa"
Girgiza masa kai tayi hawaye na bin idon ta tace
"Ni na ƙoshi"

"Haba Ƙwailar kar muyi haka dake mana, kince bana baki Abinci a baki, nace zan baki kuma kince ba kya so" ya kuma kai cokalin bakin ta, Amma ta ɗauke kanta tana kuka.

Sosai ta komawa Ammar ƙaramar Yarinya, har mamaki take bashi ace Yarinya kaman Mufeeda take kuka haka saboda kishi, ajiye spoon ɗin yayi ya ɗan zuba mata ido, sannan ya janyo ta jikin sa yace

"kiyi shiru bana son kukan nan, in baki ci Abincin nan ba, nima bazan ci ba"

A hankali cikin raɗa yace mata
"ina da chocolate a aljihuna in kika ci zan baki, kinji Jaririya ta"

ganin Ammar duk jin kan nasa ya zage yana rarrashi ne yasa ta saki fuskarta tayi murmushi, Ammar ne ya bata Abincin cikin salo na rarrashi, gaba ɗaya ta manta da ɓacin ran da take ciki, dan ita wannan rarrashin nata da yake da bata Abinci yasa ta manta da komai.

Seda ya tabbatar taci da yawa ta ƙoshi, Sannan ya ƙyaleta shima yaci nasa, karshe a jikin Ammar tayi bacci, ya ɗauke ta ya kaita ɗakin ta ya kwantar da ita.

Seda ya tsaya ya ɗan zuba mata ido, haka nan yake jin tausayinta, she's simple minded ita dai burin ta kar yayi fushi da ita, ya daɗe yana kallon ta sannan ya tashi ya tafi ɗakin sa, da yaje ɗakin nasa ma tsaf da shi ta canza masa bedsheets, ta rubuta masa takadda ta ajiye masa, takaddar ɗauke take da kalaman soyayya dana ban haƙuri.

Ɗan murmushi yayi yace "She's so kind" ya ajiye takaddar a ƙasan filon sa ya kwanta.

Da safe Ammar yana ta shirin fita ya buɗe wardrobe ɗinsa ze ɗauki kaya, Mufeeda ta shirya masa wardrobe ɗin tsaf, amma bega inner wears ɗinsa ba, wayarsa ya ɗauka ya kira Mufeeda tana kitchen taga kiran Ammar, ta ɗaga wayar tace
"Hello Baby na ka tashi lafiya?"

"lafiya ƙalau, Amma Niba baby bane, ina kika ajiyemin inner wears ɗina?"

"Ina kitchen ne, zanzo in ɗakko maka"

"Ok" suna gama Waya Ammar ya shiga wanka.

Seda ta kammala ta tafi ɗakin Ammar zata ɗakko masa kayan da yake nema, tana zuwa ta duba wardrobe ɗinsa ta ɗakko masa

"Hmm Yaya Ammar kenan ga kayan anan kusa amma wai be gansu ba, ko ina ya duba oho"

Tana ɗagowa taga ya fito daga wanka, boxers ne kawai a jikin sa yana goge ruwan wanka.

Tsorata Mufeeda tayi ta zare ido, bata taɓa ganin namiji a haka ba, wasu zara zaran gashi ne a jikin sa, tun daga kansa ƙirjinsa zuwa ƙafafuwan sa, taga yayi wani irin girma da kwarjini, nan ta shiga zazzare ido.


Ammar sarai ya ga tsoro a fuskar Mufeeda
Ammar yace "Yawwa kin ɗakko min?"

Jinjina masa kai kawai tayi tana kallon sa, yace "miƙomin su nan, ni ba'a nan nake ajiyewa ba"

Jiki a sanyaye tana kallon sa tana ɗauke ido, ta ƙaraso ta miƙo masa kayan, maimakon ya karɓi kayan seya riƙe ta, ƙara zare ido tayi tana jan numfashi.

"Me kike Kallo" girgiza masa kai tayi tace "bakomai fa" tai maganar kaman za tayi kuka

"A'a sekin gayamin me kike kallo?"

"wallahi bakomai, ba kallon ka nake ba"

"ki gayamin ba abunda zan miki"

"Wallahi bango nake kallo ba kai ba"

Murmushi ya ɗanyi a ransa yana tuna yadda take masa rangwaɗa da shagwaba ashe ma matsoraciya ce haka.

Ya ɗan kashe mata ido yace "ko zaki taɓa gemun ne?"

"A'a aikace ba yanzu ba"

"A'a na canza ra'ayi ki taɓa mana"

Noƙe kafaɗa tayi tace
"A'a Abinci na ze ƙone"

Sakin ta yayi ta fita da sauri hada haɗawa da gudu, sosai ta bawa Ammar Dariya.

Har ya shirya ya fito bata son kallon sa sosai, ko surutun yau babu, da taga zasu haɗa ido seta sunkuyar da kai, idan kuwa suka haɗa ido se Ammar yace "ko in zone? .

Da sauri take cewa A'a

Haka ya karya ya fice yana dariyar yadda tayi da ido daya riƙe ta.








Domin sharhi, Gyara ko Shawara
Ayshercool
07063065680

✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

     

ELEGANT ONLINE WRITER'S

             

           

                  

                        Page 14

Ammar be kai dare ba yau tun azahar ya dawo gida, amma yana zuwa ya tarar da Mufeeda a falo kwance akan kujera, da ƙyar ta iya amsa masa sallamar sa ya kalleta yace
"ya dai?" tace
"bakomai ya naga ka dawo da wuri yau?"
"kince in dena kaiwa dare, na dawo da wuri kuma kina tambaya ta"

Ɗan murmushi tayi tace "ai ban san zaka dawo yanzu ba, ban girki ba"

"haka kike zama da yunwa in ba na nan, salon Ace bana baki Abinci?"

"Ai bana jin yunwa ne, kuma ga cornflakes can, idan naci ya isheni, Abincin yafi daɗi idan ina ci ina kallon ka"

Murmushi yayi yace "yanzu me zaki ban, ina jin Yunwa"

"ina da miya, bari inje kitchen ɗin in gani"

Ammar ya lura da ita kaman jikin ta babu ƙwari, a hankali take komai, ta dafo masa Abinci ta kawo masa, ta koma kan kujera ta kwanta.

Ammar yace "wai meke damunki ne?"

"Ciki nane yake min ciwo fa"

"Shine kike ta faman haɗe rai haka, wannan ciye ciyen naki ma ya isa su saki ciwon cikin ai"

Shiru tayi masa ta lumshe idon ta, ya kalle ta yace
"ki sakko kici Abinci seki sha magani"

Girgiza masa kai tayi alamar A'a,.
Ammar yaci Abincin sa ya ƙoshi, ya ture Kwanukan gefe, ya ɗakko wayarsa yana game, a tunanin sa Mufeeda ba dagaske take ba.

Can ta ɗan fara juyi tana riƙe cikin ta, tana numfarfashi.

Ya kalleta yace "idan banɗaki zaki shiga ki tashi ki tafi mana"

Haushi ne ya kamata, tana fama da kanta amma yana mata wata maganar daban, a hasale tace
"Idan banɗakin zani ai na sani, ko na taɓa fitsari a falo ne? In haka kake gudu seka dinga samun pampers kar in ɓata maka guri tunda dama ni Jaririya ce"

Mamaki ne ya kama Ammar, ko da wasa be taɓa tunanin Mufeeda zata gaya masa baƙar magana ba.

Ƙara riƙe cikin ta tayi tana rintse ido, Ammar binta yake da ido kawai, miƙewa tayi tana durƙusawa ta tafi ɗakin ta.

Ɗan taɓe baki yayi ya ci gaba da danna wayarsa, idon sane ya sauka a inda Mufeeda ta tashi, tayi staining na jini a gurin, ɗan zare ido yayi, dama Mufeeda ta isa fara period ne? 🙄

Miƙewa yayi ya samo ruwa da Omo ya goge gurin, da yake bada yawane inda ta ɓata ɗin ba, shi da farko ya ɗauka kawai rigima take ji, se yanzu ya tabattar bata jin daɗi ne.

Ya bita ɗakin dan ganin halin da take ciki, yana shiga ɗakin nata ya tarar ta cire kayan jikin ta, daga ita se underwear hatta ribbon ɗin kanta ta cire shi, gashin ta a wargatse tana durƙushe a gaban gado, ta tattaro bedsheet ɗin kan gadon ta tada kai dashi tana kuka, ga fanka se gudu take amma ita ta haɗa gumi sosai se kace me naƙuda.

Daidaita nutsuwar sa yayi, ya ƙarasa da sauri ya ɗago ta, ya ƙare mata kallo, Mufeeda ba farace tas ba amma chocolate ce me haske, fatar ta tana da matukar ɗaukar ido se sheƙi take, ga wannan sassanyan ƙamshin da take me kashe masa jiki

A hankali yace " sannu ban zaci abun ya kai haka ba, daure kisa kayan ki se muje Asibiti"

Ɗan ƙura masa ido tayi sannan ta ƙara kwanciya a jikin sa tace
"bazan iya tafiya yanzu ba, ka bari ya lafamin, kuma ma daka ƙyaleni ze dena fa"
"No gara muje Asibitin dai"
Ɗan lumshe ido tareda yamutsa fuska alamar tana jin jiki, a hankali kaman me raɗa tace
"bari ya ɗan lafamin, yanzu ina jin ciwon sosai"

"shikenan sannu"
Bata iya amsawa ba se lumshe ido da tayi, a hankali Ammar ya kai hannun sa kan gashin ta yana shafawa, zuciyar Ammar ta shiga bugawa da ƙarfi tana raya masa abubuwa da dama akan Mufeeda, Amma wani ɓangaren na zuciyar sa na ƙoƙarin kawar masa da tunanin da yake.

Ɗan yamutsa fuska ta kuma yi tana miƙe ƙafafuwan ta tace
"Yaya Ammar Ciwo"
Ya riƙe hannayen ta yace "Sannu ze dena Insha Allah"

Gaba ɗaya tausayi take bashi, yana tuna wani littafi daya taɓa karantawa me suna (MATA A LOKACIN HAILA)

Mata na shiga mawuyacin hali a wannan lokacin, wani yanayi ne wanda inba wanda yake jinin ba baze gane ba, sukan shiga halin takura, yawan ƙunci, kasala tashin zuciya, yawan faɗa da saurin fusata, kwaɗayi kaman masu ƙaramin ciki, yawan kuka ko san kaɗaici da dai sauran su, ga uwa uba Wannan ciwon da wasu matan kan yi, ciwo ne me wahala matuƙa wata duk lokacin da za tayi seta kwanta rashin lafiya sosai, ciwon mara me haɗe da ciwon ciki da gudawa, ko kuma ciwon baya da ƙafafuwa, wasu kuma hada amai da zazzabi ƙuraje su fito su ɓata musu fuska, wannan ma ya ishesu shiga damuwa, wata idan tana wannan ciwon kaman zararriya haka take, wata harta gama Al'ada bata san saka kaya, se dai marasa nauyi, wata kuma komai sanyi zata dinga kwanciya a guri me sanyi ko cin abu me matukar sanyi, da dai sauran su.
  Dan haka yake da mahimmanci miji kokuma wanda yake tare da Mace ya gane idan mace tana irin wannan yanayin ayi mata uzuri, ba kowane lokaci mata suke wani abun suna sane ba, sedai dan kusan gaba ɗaya rayuwar su cikin yanayi ne na hormones da suke sauyasu lokacin al'ada, lokacin da suke da ƙaramin ciki ko kuma idan cikin ya tsufa.

Kallon ta ya ci gaba daya, bacci ne yayi gaba da ita, dan haka Ammar yasa mata filo ya kwantar da ita ya fita.

Se la'asar sannan ta farka, ta shiga tayi wanka ta samu ta saka kaya a jikin ta, ta gyara gadon ta ta nemi guri ta zauna.

Ammar ya dawo ɗakin yaga har tayi wanka ta canza kaya, ya kalle ta yace "ya jikin?"
"Da sauƙi Alhamdilillah"
"Saka hijjabinki kizo mu tafi"

Kaman tace masa A'a amma ta fasa saboda yanzu seya ɓata rai, haka ta saka hijjabi ta fito.

A hankali take tafiyar, Ammar ya riƙo ta suka fito zuwa cikin a daidai ta sahunsa, Matan layin da yake sana'ar su ce leƙen ƙofar gida suna gulma, suna ganin Ammar ya riƙo Mufeeda sun fito gaba ɗaya hankalin su ya koma kansu, yasa Mufeeda a babur ɗin ya zagaya ya zauna a mazaunin direba ya kunna suka tafi.

Suna tafiya matan layin suka dasa gulmar su, wasu suna itace matar gidan, wasu suna ba ita bace ba sedai ko baƙuwa suka yi ko 'yar uwassa ce, da yake basu san itace matar gidan ba.

Wani Clinic na kuɗi ya kaita, suna zuwa ta samu guri ta zauna Ammar yaje aka buɗe mata file, sannan suka shiga gurin ganin likita.

Suka gaisa da Likitan, ya kalle su yace "to kai ta kawo ko kai ka kawo ta"

Ammar yace "itace ba lafiya"

Likitan ya kalleta yace  "meya ke damun ki ne?"

Kallon Ammar tayi tai shiru, Ammar yace "kiyi magana mana"
"Ciki nane yake min ciwo"

Ammar yace "ba ciki ba dai mara ko?"
Kunya ce ta kamata tai shiru tare da sunkuyar da kai.

Likitan yai murmushi yace "Nagane, menstrual cramp ne, yaushe kika fara?"

"haka yake min idan zanyi"

"Yaushe kika fara menstruation?"

"four years back"

Ba Likitan ba har Ammar seda ya kalleta  Ammar yace "are you sure?"

"Very sure" ta bashi amsa

Likitan yace
"Ok hakan ba wani abun damuwa bane, mata suna shiga wannan yanayin idan suna Al'ada, sedai a kula da ita da abubuwan da zata ci, Sannan idan ta samu ma nemi a mata Aure, idan akayi musu Aure in akayi sa'a wasu yana raguwa koma su rabu dashi baki ɗaya"

Ita dai Mufeeda ba tace komai ba.
Likitan yace
"tsakanin magani da Allura wanne kike so?"
Kafin tayi magana Ammar yace "Allura zaka rubuta mata"
Zare ido tayi tace "Haba Yaya Ammar wallahi bana son Allura, dan Allah kar ayimin"
"Likita rubuta mata Allura, Allura tafi quick Action, in ba haka ba muka koma gida zuwa zata yi ta cigaba da lanƙwashewa"
Mufeeda tuni ta fara kuka, liktan yace "We have to respect her autonomy, tunda magani take so a rubuta mata"
Ammar yace "No Allura zaka rubuta mata"
Haka likitan ya rubuta mata Allura da sauran magungunan, ya kalle Mufeeda yace
"Sorry Baby Allura ba zafi fa, Wannan Yayan naki yace se an miki Allura"

Basu kuma kulashi ba, Ammar ya sunkuya yace mata "gobe ma ki ƙara min rashin kunya, ina sane nace a miki Allura" zumɓura baki tayi suka fito daga OPD ɗin, Ammar yace ta zauna ya siyo maganin, ta zauna tana jiran sa.

Bayan ya siyo maganin ne yaci karo da Faruk, suka gaisa Faruk yace  "Ahh mutumina me kake anan?"

"Mufeeda ce bata jin daɗi na kawo ta A duba ta"

"Allah sarki, nima nazo in duba wasu patients ɗina ne da na yiwa CS jiya, muje semu gaisa tunda kuka tare ko leƙoku ban kuma yi ba"

Suka tafi tare suna hira, Faruk yaga Mufeeda ta ƙara ƙiba, dukda kuka take amma tayi wani fresh da ita, Faruk yace "Madam har yanzu ba'a dena rikici ba? Hala laulayi ne?"

Ammar yace "Haihuwa zata yi ba laulayi ba"

Ganin irin kallon da Faruk ke mata yasa Mufeeda tace "Na gaji Mu tafi"

Ammar yace "to Faruk se anjima se munyi waya" ya kama hannun Mufeeda suka tafi Injection room.

Fafur Mufeeda taƙi shiga Nurses suyi mata allurar, Ammar ya fara ƙulewa ya janyo ta zuwa cikin gurin, kuka take sosai kamar wadda za'a yanka.

Ammar yace "haba Autar Baba sonake ki warke da wuri shiyasa nace ayi miki allurar ai, hug me you won't feel the pain"

Ya buɗe mata hannayen sa, a hankali ta ƙarasa ta kwanta a jikin sa, ya riƙe ta, Nurse ɗin tace
"Ikon Allah, dan Allah ƙanwarka ce ko matar ka?" da yake babbar mace ce dan haka Ammar ya bata amsa
"Mata ta ce"

"gaskiya ran haihuwa da kallo, Allura kawai tana wannan abun, Allah ya ƙara maka haƙuri ɗan nan, kana fama da shagwaba" murmushi kawai Ammar yayi.

A hakan ma da ƙyar ta tsaya aka yi, Hawaye sharkaf fuskarta, maimakon da'aka gama ta tashi sema ƙara narke masa da tayi a jiki tana kuka.
Ammar yace
"ya isa haka harfa an gama, Insha Allah yanzu zaki dena jin ciwon"

"Wallahi Allurar da zafi sosai"

"to ai zafin kaɗan ne akan ciwon da kike ciki"
Nan ta shiga zabga shagwaɓarta, ƙarshe nurse ɗin se fita tayi tabar musu room ɗin.

Ammar yace "ki tashi mu tafi kinji an fara kiran sallar magariba"

Noƙe masa kafaɗa tayi,
"idan munje gida zan baki biscuit ai zaki ci ko Jariri ya ta?"
Murmushi tayi masa tana lumshe ido, a hankali ta miƙe ta biyo shi suka fito, suka hau babur ɗin su zuwa gida.

Da sukaje gida Mufeeda tace ita ba zata iya tafiya ba, ƙafar ta ta sage jikin ta babu ƙwari, ƙarshe seda Ammar ya ɗauke ta ya kaita har kan gadon ta a ranta tace
"tunda kasa akamin Allura se kayi jinya kaima"

Ammar yaje yayi salla, ya dafo mata tea ya kawo mata, ta karɓa ta sha sannan ya miƙo mata ledar pharmacy yace
"gashi nan pampers ɗin da kika ce in sai miki ne" ta kalle shi tace
"Pampers kuma?"
"Eh mana ko kin manta ne?"
Karɓar ledar tayi ta duba, pad ce guda uku da sababbin pants guda biyar, wata kunyace ta kama ta, banda abun Ammar panties ɗinta kona lefe bata taɓa ba amma ya sai wasu. Sunkuyar da kai tayi taƙi ɗagowa su haɗa ido.

Yace "zanje masallaci idan nayi sallar isha'i zan ɗan za gaya, kinga yau ban samu nayi aiki ba yadda yakamata"

"Shikenan amma karka yi dare sosai dan Allah"
Jinjina mata kai yayi, ya miƙe ya fita.

Bayan ya idar da Sallar isha'ine Aminu ya kira shi yace "yana so su haɗu za suje gidan Jabir"

Haka kuwa

Please Login or Register in order to submit comment