Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na damuwa yasa Ma'am ta yi shiru ba tare da ta kara tada mata zancen ba.

Haka Deejerh ta ci gaba da zama anan su biyu Ma'am na bata kulawa sosai sannan shi ma papi Dr Ali ya kan zo da kan shi ya dubata har ya kai ga ta fara sakin jiki da su.
Amman lokaci zuwa lokaci yanayinta na sauyawa hakan yasa ya cire mata lokaci a kullum ta kan je gunsa domin ya yi mata Therapy kuma ya tabbatar mata da cewa tana dauke da OCD kuma ta amince da hakan tare da ɗaukan dukannin shawarwarin da yake bata.
Har ya kai ga ya sata a Therapy group dinsa domin kara samun horar yadda zata kula da lafiyarta bisa ga lalurar da take dauke da shi.

Ranarta ta farko ga zuwa group din ya gabatar da ita ga sauran group members dinsa sannan ya ce, "Kasancewar maza da mata duk an tattara anan dalilin wannan bakuwar akwai wani sako da nake son sanarwa mai mahimmanci garemu gabadaya, wanda rashin kiyayewa babbar illace ga rayuwarmu da ta matanmu, magana zanyi akan lura da duk wata mace mai juna biyu ko ince ciki kai tsaye, wasu mazan na da kyashin bawa mace kulawa tare amince mata kan cewa tana zuwa asibiti domin duba lafiyarta har yanzu wannan jahilcin na yawo aranmu na cewa ai da kakanninmu basu san asibiti ba kuma babu mai duba su har suke haihuwa lafiya, yanzu fa daban abincinmu ma da yanayin rayuwar mu ya canja dole duk sanda kida ya canja ya wajaba rawa ma ya sauya salo, a daure a dunga zuwa asibiti domin yin awu a tabbatar da cewa ciki da abun da ke ciki na cikin koshin lafiya rashin yin hakan kan iya sawa in wata matsala ta taso a karshe a gagara magancewa musamman yanzu da ake yawan samun matsalar zaman ciki a bayan mahaifa in wannan abun ya afku da yawa mata rasa rayuwarsu suke kai tsaye in ma ko sun rayu su kan sha bakar wahala sosai kafin komai ya daidaita kamar dai Deejerh har na fidda rai da numfashinta sai kuma ya dawo bayan ya dawo dinma saida ta yi kwana uku cir sume kafin ta farfaɗo mu daure mu cire son zuciya, ƙyashi da jahilci mu nemi lafiya domin gujewa afkawa kogin nadama."

Wata matashiyar mata ce ta daga hannu da alamun tana so tayi magana, papi ya bata dama ta ce ,"Na gode sosai,kuma na ji dadin wannan tunasarwan taka domin hakan ya faru ga 'Yata 'Yar cikina har ya kai ga ta rasa ranta wanda kuwa babban abun shine ba mu yarda da batun zuwa awu ko lafiyar mai ciki ba, duk da cewa komai Allah ne mai yi amman wani lokacin sakacinmu ne sanadi, da haka nima ina kara shawartarmu duka yan uwa mata da maza kada ayi wasa da lafiyar duk wata mace mai juna biyu."
Tana gama jawabin suka tafa mata dukanin su sun nuna jin dadinsu da kuma amincewa da maganar papi kafin suka tsunduman cikin Therapy dinsu.

Bayan sun tashi kai tsaye Deejerh ta koma gidan Ma'am.
Tana zaune tayi tagumi ganin cewa kayan abincinsu ya kare kuma gashi inda take aiki sunyi tafiya bare tasa ran samun albashi.

Har ta shiga ta zauna Ma'am bata sani ba tsabar ta shiga duniyar tunani ga babban tashin hankalinma ko gawayi da icen da zasuyi girkin ma in an samu hatsin babu.

Ta zauna shiru tsawon minti guda Ma'am bata lura da ita ba.
Deejerh ta tashi ta dafata tana fadin, "Ma'am lafiya,m baki ganni ba? Ko da ba kya jin dadi ne?"

Sai a lokacin ta dawo hayyacinta ta kalli Deejerh ta ce, "Ayyah har kin dawo? Kuma kina jin yunwa ko? Tunani nake yadda zan samo miki abincin da zaki ci komai namu ya kare gashi ban da kudi."

Deejerh ta ce, "aa karki damu nikam ma bana jin yunwa Bakin da Allah ya tsaga ai bazai hana shi abinci ba."

Ita dai Ma'am bata gamsu ba damuwar ta ta inda zata samowa Deejerh abinci ne.
Deejerh ta tashi ta fita kofar dakin nasu tana kallon waje dake kusa suke da bola ana zubda kayayyaki da yawa.
Sai da ta tsaya tayi tunani na tsawon mintina kafin ta je ta dauko wani bawun ta diba irin diddigar gawayi wanda yake zuwa a karshen buhu da aka zubar a sharar ta zuba ciki, sannan taje can gefe ta diba kashin shanu ma dan daidai ta zuba, can gaba kuma inda kafintoci suke ma taje ta diba dos irin sauran sharar da ake cirewa jikin katako.
Ta hada su waje guda sannan ta koma.
Tana komawa ta diba ruwa ta zauna zata zuba kenan ma'am ta fito tana fadin, "Aa wannan kuma fa?"

Deejerh ta ce, "zan gwada yin gawayine in ya yi sai muna saidawa muns cin abinci kuma muma muna girki da shi kinga mun huta da siyan abun girki ko?"

Ma'am ta girgiza kai, "To fa zan ga ikon Allah, Allah Ya tabbatar da Alkairi amman wa innan duk sharace ai abun da ake zubdawa kika dauko."

Deejerh ta yi Murmushii, "wani abun sai an gwada za aga amfaninsa."

Ta kwaba da ruwa da dan kaurinsa yadda zai iya hade jiki, sannan taje kan wani dutse tana mulmulawa kananan tana sawa har ta kammala.

★★★dake garin da rana sosai ba jimawa ya bushe bayan ya bushe Deejerh ta kulla a ledoji ta daura a Faranti sannan ta diba wani ta zuba cikin murhunsu tana kunnawa kuwa ya kamu Ma'am na ta kallo cike da mamaki aranta ta ce, "Ikon Allah ka ga yar baiwa."
Deejerh ta zuba ruwa a tukunya ta daura sannan ta kalli Ma'am ta ce, "Ma'am kin ga ya kama zanje in saida wannan in an samu masu saya sai mu samu kayan abinci."

Ma'am ta kalleta cike da tausayawa ta ce, "Shikenan Allah ya tsare mun ke,ya dawo da ke lafiya."
Deejerh ta amsa da "Ameen." Kafin ta fita.

Haka ta dunga zagaya kauyen tana neman su siya amman fir suka ki har wasu na bige farantin suna xubar mata,haka ta kwashe ta ci gaba da tafiya suna zaginta da fadin cutar su zata yi taya ma za ayi wannan abun ya yi girki ban da rainin hankali.
Tana cikin tafiya ta hadu da Dr Ali Papi ya tambayeta mene ne wannan
Ta sheda masa cewa gawayi ne tayi take talla ko za asamu mai siya .
Ya ce, "kin tabbatar kuma yana kamawa?"

Deejerh ta ce , "E ko kafin in fito ma na kunna kuma ya yi yana ci ma."
Papi ya ce, "ok shikenan nawa nawa ne?"

Deejerh ta ce, "€5 ne."
Ciri €50 ya yi ya mika mata.
Godiya sosai Deejerh ta mai har tana durkusawa
Papi yasa mata albarka sannan ya ce, "In sha Allah zaki samu masu siya in an gano kinji karki damu."
Aiko yana tafiya ta jura aguje kasuwa ta yi masu siyayyan kayan abinci ta koma ta kaiwa Ma'am.

Ma'am na ganin ta rike da kayan abinci batasan lokacin da ta fashe da kuka ba tana kokarin faduwa, Deejerh tai saurin......


*Yau ina hanya zanyi tafiya a tayani da addu'a tare da fatan Alkairi*
*Sannan typing na ajesa gefe In sha Allah sai na dawo kuma Loves You oll😘😘*

08103080717

Urs Xayyeesherthul-humaerath
[1/1, 1:36 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: https://tiktok.com/@xayyeesherthulhumaerath
*VIXEEN* Family Follow My TikTok Account Please.😫

*°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-26

Rungumeta.
Hawayen da ke sauka daga idanun Ma'am tai saurin gogewa tana fadin, "Allah ya miki Albarka Deejerhtou na, Allah ya kara haskaka rayuwarki da hasken sa, Allah ya tsaremun ke gaba da baya,zahiri da badini, tabbas ban yi rashin haihuwa ba, Ubangiji kadai ya san dalilin Kasancewarmu tare anan,kuma ina fatan hakan ya dauwama cikin Alkairi."

Deejerh ta ce , "ki daina kuka ni bana so kina kuka bana so hawayenki yana zuba."

Murmushi Ma'am ta yi ta ce, "Ai indai dake ba zan yi kuka ba,sai dariya inma na yi kukan sai dai na farinciki domin ke haske ce mai haskaka duhu, kuma inuwace mai dauke rana,sannan ruwa ce mai maganin kishi,ina sonki kinji Deejerhtou na."

Abinci Deejerh ta daura masa, har saida ya yi,ta zuba masu ita da Ma'am suka ci suka koshi sannan ta gyara komai tas tamkar babu abun da aka taba kamar yadda ta saba.
★★★
Kamar wasa a kwana a tashi har yan kauyen sun gane inganci da saukin dake tattare da gawayin Deejerh,hakan yasa har tururuwan siya ake sosai da tayi yake karewa ,wasu har kamawa suke su bada kudi kan tana yi a aje masu.

Saidai kuma ta fara fuskantar kalubale agun wani mutumi dake kawo masu gawayi kauyen suna siya, tunda aka gano nata aka rage yi masa ciniki wanda hakan ba karamin zafi yake ji ba,har ya gagara rike kansa.
Ya ma daina zubar da diddigin nasa gawayin a kauyen sai dai ya zuba cikin rafi ya bi ruwa.
A karshe saida Ma'am ta dauketa suka fara zuwa wasu kauyukan makotansu nemowa hakan ma sai sunci kwakwa suke samu, gashi babu abun hawa saidai su taka a kasa daga zuwa har dawowan.

Ranar sun hadu ita Ma'am sunyi sosai da yawa cikin dare haka suka hana kansu barci saidai suka kammala tas, bayan sun kammala can cikin dare sai wajen karfe uku suka kwanta.
Suna kwanciya Abdu na bibiye da su,sai da ya tabbatar sun kwanta tukun ya lallaba ya je da ruwansa cikin bucket ya kwarara akai ya tattaka sai da ya wargitsa gawayin tas ya koma diddigi kafin ya tafi.

Washegari da safe aka fara kwankwasawa su Ma'am kofa anzo siyan gawayi, hakan yasa Deejerh ta tashi tana magagin barci.
Fitar da tayi zuwa kan dutsen da suke shanya gawayin sai da tayi karamar suman tsaye,tana kara murza ido ta ga shin da gaske abun da ta fara hangowane ko akasinsa.
Gawayi ya zama gari,gari ma mai hade da kasa gabadaya bazaiyi amfani ba.
Ta kalli gawayin ta kalli yaron da ke jiranta kawai ta zauna cikin diddigin ta fashe da kuka.
Domin tama rasa abun yi,da kyar suka samo kayin yin gawayin,bayan sun gama wahala sun hana kansu barci gashi an lalata.
Sautin kukanta da Ma'am taji ne yasata saurin fitowa ita ma tana gani saida ta yi turus.
Ta kalli yaron ta ce, "Ka ga babu gawayin ashe ya kare, ka je zuwa anjima ka dawo."

Ta karasa gaban Deejerh tana dagata ,ta daga fuskarta suna kallon juna,ta ce, "kalleni,"
Sai da ta tabbatar Deejerh na kallon idanunta ta ce, "

"kiyi hakuri kinji, na san yanzu har cikin zuciyarki kuna kike ji mara misaltuwa,amman kau da shi ya zama dole, nima banji dadi ba domin kuwa nasan hakan shirine aka aikata domin a muzanta mana,amman kin san mene ne? Haske na gano mana maimakon duhu,na ji cewa wannan sana'ar zata ci gaba da karbuwa fiye da tunanin mu kuma zata amfanar da al'umma,babu wanda ke hawa tudun nasara ta sauki,dole fa sai an hau ana faduwa har ma a kurje,duk da cewa nasan ke ma kina sane da hakan amman tunatar dake wajibi ne gareni, kuma duk wanda ya yi wannan aikin kan shi ya yi wa, domin kuwa yanzu zamu kara zake damtsen shiga lungu da saƙo domin nemo kayan aiki."
Ta karasa maganar tana sharewa Deejerh hawaye.
Ta kalleta tana kara fadin, "Ki yi murmushi kinji,a kullum ina so hawayenki ya zama silar murmushinki."
Murmushi Deejerh ta yi sosai wanda ya kara fito da kyawunta tana rungume Ma'am.
Sun dauki kusan minti guda kafin Ma'am ta ce, "kin ga yanzu mu je mu hada abun karyawa in muka ci sai mu je wani gu na san inda zamu samo diddigin gawayin har ma da dos In Sha Allah."

Sai da suka nufi inda suke girki ma tukun suka tuna ai ko sauran gawayin ma da zasu yi amfani da shi babu,ya kare tas.
Jiki a mace duka suka tsaya zubawa sarautar Allah ido.
Sun kasa katabus, kamar an jefo Ammar daga sama sai gashi ya zo wucewa dauke da tulin itace ya yo.
Ganinsu turus ya sa shi tsayawa bayan ya gaida Ma'am ya fara tsokanar Deejerh dake sun saba da shi a wajen Papi.
"Ah ya yau na ga ba fara'a ne?"

Ma'am ta ce, "Hmm ai dole Ammar ,ka ga mun tashi mun tarar wani dan albarkan ya rusa mana gawayin da mukai ashe ko na abinci ba mu da wanda za mu yi amfani da shi,kuma jiya da kyar muka samo diddigin kasan an daina zubdawa a wannan kauyen."

Ammar ya sauke itacen yana, "yanzu dai wannan gashi ku diba ku hada ku samu kuyi amfani da shi, sannan yau ma tunda ban da wani aiki zan rakata muje mu samo In sha Allah sai ke ki huta tunda ba ishashshiyar lafiya gareki ba."

Ma'am ta ce, "amman ko dai Allah ya ma albarka Allah ya haskaka rayuwarka ."

Deejerh kam na jin su bata ce komai ba kawai tana binsu da kallo.

Ma'am ce ta karba da kanta ta wura hutar,sannan Deejerh ta shiga aikin ta dafa masu abin da zasu ci,Ammar ma ya je ya kai sauran itacen ya shirya sannan ya dawo da nufin suje su nemo diddigin da Deejerh.
Buhu ya daukan masu manya guda biyu.
Deejerh na kallonsa ta ce, "kai kam ka fiye son zuciya ina zamu samu abun da zamu cika wa innan buhunhunnan?"

Dariya Ammar ya yi,ya ce, "naki wasane yarinya, waya ce miki ana nema da sanyin jikine muje,yau zaki ga mazaje,ba daman kin rainani ba? Zaki ga jarumta irinta mazaje daga yau zamu cire raini tsakanina dake tunda na lura wani gani gani kike mun."

Deejerh ta kyalkyale da dariya kan ta ce, "aiko dai yau za aga rashin mazaje a mazaje."

Ma'am ce ta katse su da fadin, "kun ga wannan shirmen naku nasan sai ku kwana kuna yi baku gaji ba,ni dai yanzu kuje ku samo abubuwan nan zaifi in kun dawo kwa dasa aya a inda kuka tsaya."
Dukansu suna dariya suka tafi suna yiwa Ma'am sallama.

Haka suka dunga shiga ƙauyuka suna neman diddigin gawayi tun safe har wajen karfe biyu na rana amman basu samu, da kyar suka samu a wani kauye shima bai yi ko rabin buhun ba,bayan sun samu suka je diban dos.
Suna cikin diba Ammar ya sake wata kara ya tashi yana sankamewa, ciki ya duri ruwa ban da sauti babu abun da ke fita,ga fitsari na tsiyaya kamar famfo cikin kankanin lokaci gumi ya gama jika shi ya gama ficewa a hayyacinsa.

Da mamaki Deejerh ke kallon sa jiki ban da rawa babu abun da yake yi, sai da ta kalli inda yake kallo tukun ta lura da cewa ashe macijine ya kafesa da ido ya yi wannan razanar.
Ban da dariya me Deejerh take,har ma ta manta gajiyar da tai, sufa ta fara cikin dos din tana dariya tare da fadin, "Mazaje kenan,mazaje anji jiki,yanzu macijin dake gefe don ya kura ma ido kawai zai rikitaka? To inaga kuma ya bi jikinka?"
Duk abunnan da Deejerh take Ammar bai ma san tana yi ba, don gabadaya ya riga da ya gama firgita.
Ganin da gaske baya hayyacinsa ne yasa ta dauki sanda ta makawa macijin ,tana maka masa kuwa ya gudu.
Tukun Ammar ya fara sake jiki yana waige-waige.
Ita kuwa kara tintsirewa ta yi da dariya.
"Yau mazaje fa sun hadu da mazaje,an bawa hammata iska kai dai kam anji kunya aradun Allah."

Tsakin kunya ya yi ya ce, "ba wani nan daman gwadaki na yi ai, inga ko kema jarumarce Don ina so in taimake ki in aureki,saboda ni ba zan auri raguwa ba shiyasa na gwada ki,ni ne fa na kirasa ma na ce yazo nan don in gwadaki gwanda ma kiji ehee."

Deejerh ta yi dariya, "ai kuwa kam Shiyasa na ga tsabar jarumta harda fitsari a wando."

Ammar ya kauda kai yana tashi ya ce, "ba wani fitsari yarinya gumi ne irin na manyan jarumai,kin ga mu kwashe kayan nan mu tafi na ga garin hadari da alamun za ayi ruwa."

Shi ya dauki babban buhun,ita kuma ta dauki karami suka kama hanya, aiko suna cikin tafiyar ma ruwa ya tsinke sosai kamar da bakin kwarya, haka ya cire suwaitarsa ya bata ta saka suka ci gaba da tafiya har suka isa.
Ya ajiye mata buhun kafin ya yi sauri ya tafi Gida ganin cewa ciwon shi ya shirin tashi sam bai son sanyi da ruwa, kuma shi bai sanar da ita ba, ji yake lafiyarta ta fiye masa tashi hakan yasa ya cire kayan sa ya bata.

Tana shiga Ma'am ta ce, "Subhannallah kune a ruwan nan? Ina Ammar din? Ince dai bai shiga ruwan ba?"

Da kallon mamaki Deejerh ta bita ta ma rasa abun cewa ganin cewa bata fahimci inda ta dosa ba.
Ma"am ta kara fadin, "Ina Ammar din na ce? Tun da naga ruwan nan hankalina ya tashi inata tunaninsa."

Deejerh ta ce, "yana ajiyewa ya tafi gida da sauri."
Ma'am bata ce komai ba ta fice da sauri.
Deejerh ta bi bayanta.
Aiko suna zuwa Ammar na zaune jiki na ta rawar ɗari ya ma gagara cire sauran kayan jikin nasa.
Fita Deejerh tayi ,Ma"am ta taimaka masa ya cire kayan sannan ta sanya masa masu dumi ta gyara masa kwanciya ya shiga bargo, sannan ta fito ta sanar da Deejerh kan ta hado gaushi ta kawo asa adakin ya yi dumi.
Bayan Deejerh ta dawo take tambayar Ma'am mene ne ke damun Ammar.
Ma'am ta ce, "yana da ciwon sanyi ne in ruwa ya taba shi ko ya zauna a waje mai sanyi sosai ya kan bashi matsala ciwon ya motsa."

Ma'am ta kallesa tana fadin, "kaima maimakon da ka ga ruwan ka ce mata baka da lafiya ku tsaya sai ka biye mata bayan kasan cewa zaka cutu?"

Ammar ya ce, "aa Ma'am nice na ce mu tawo ganin kar dare ya yi mana a hanya za a iya samun matsala kasancewar ta mace a irin gurin nan."

Cike da tausayawa Deejerh ta kalle shi sannan ta sunkuyar da kanta kasa har cikin ranta tana jin tsantsan tausayinsa.
Ma'am ta sanar da ita kan taje ta dafa masa ruwan tea, hakan kuwa aka yi taje ta dafa masa ta kawo masa ya sha.
Ma'am ta ce, "yawwa to yanzu kin ga tashi muje mu hada kayan aikin cen muyi tunda naga alama da sauki."

Tsam Ammar ya tashi yana, "nima zan tayaku jikina ya ware ma'am."

Ma'am ta ce, "Aa kai da baka da lafiya, ka zauna ka huta ka ji dan albarka,mun gode."

Shagwabewa ya yi,yana rike hannun Ma'am, "Please wallahi zan iya ina jina daidai sosai yanzu kam."

Ba yadda ta iya haka ta barshi suka tafi tare.

A daren ranar ma basu yi barci ba, dukan su ,su ukun haka suka ta fama har sai da suka kammala bayan sun gama ranar basu bari a waje ba suka shigar cikin dakin su.
Kafin suka ci abinci tare suka yi sallama da Ammar ya tafi suna yi masa Godiya.

Yana fita zai tafi kenan sai ga Abdu ya tare masa hanya bayan Deejerh ta koma.

Saukar bugu ta baya kawai Ammar ya ji....

Urs Xayyeesherthul-humaerath
08103080717
[1/2, 1:32 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-27
Ya juya yana rike baya, Abdu ya kara buga masa, "kai karamin munafuki inaga mata ko? Har kana rawar jiki kana tayata aiki kuma kana rakata nemo diddigi ko?"

Sai a lokacin Ammar ya gane Abdu ne , ya kallesa sau daya sannan ya sunkuyar da kai kasa.
Abdu ya sa hannu yana cakumar fuskar Ammar cikin iko da gadara gami da izza ya ce, "Daga yau,kuma daga yanzu kar in kara ganin ka yi tunanin taimakon waccer matsiyaciyar yarinyar ko ince tsintacciyar magen cen,in kuwa ka gagara hakan ina mai tabbatar maka da cewa tamkar kana wasa da Numfashin da ke fita a jikinka ne."

Ammar ya ce, "Ni ni ni..." Ya gagara karasa maganar sai da Abdu ya kara buga masa wani katako kafin ya kara sakin kara.

"Wawa shashasha in kara ganinka da ita ka ga." Ya karasa maganar yana kara hankadasa ya tafi ya barsa agun.
Radadi yake ji har cikin ransa domin ya gama farfasa masa baya duk ya ji ciwo.
Da kyar ya ja kafa ya ci gaba da tafiya har ya isa dakinsa ya lallaba ya zauna domin kwanciyar ma gagara yinta ya yi,barci sam ya dauke daga idanunsa.

Yadda ya ga dare haka ya ga rana.
Safiya har dare Ma'am ta ga babu shi,kuma babu labarinsa tasan ko don ya tsokani Deejerh yana zuwa gunsu amman har yamma ta fara yi,kuma suna da meeting na yan kauyen da suke,kowa na ta shiri amman babu alamar Ammar.

Ma'am ta gaji da zancen zuci ta cewa Deejerh, "Anya yau Ammar kalau kuwa? na ji shi shiru fa."

Deejerh ta kalleta kafin ta ce, "Kalau kai yanzu haka yana cen yana sharara karyarsa da ya saba." Ta fada a gajarce tare da nuna ko in kula ta ci gaba da aikin gabanta.

Ma'am ta ce, "ga lokaci nata tafiya,kin san wannan karan Town meeting din ya hadu biyune da na kauye da kuma taya Madam Nasy Murnar cikarta shekara 90 ya kamata muyi mu gama girkin nan mu tafi."

Suna cikin maganar kenan sai ga Madam Nasy ta tawo cikin yanayin damuwa, kasancewar bata da wata kawar da ta zarce ma'am hakan yasa duk wata matsalarta gunta take fara dumfara.
Da sauri Ma'am ta tashi tana rike ta tare da fadin , "Lafiya? Ya naga baki ko shirya ba? Ni inata sauri lokaci na kurewa kuma ke na ga ma ba kya shirin?"

A gajarce Madam Nasy ta ce, "ban da kayan da zansa na rasa wacce irin shiga zanyi duk kayana fa kinsan sun mutu,na siya wani sabon riga da niyar zansa kawai ina guga yanzu ta kone gabadaya kuma ban da kudi bare ince zan siya wata ko ma ina da shi ba samu zan yi cikin kauyen nan ba." Ta karasa maganar jiki a sanyaye.

Sunyi jigum jigum an rasa mafita sai daga karshe Deejerh ta ce, "ina rigar take?"

Madam Nasy ta ce, "tana cen nikam ma don takaici agun na barta ai."

Deejerh ta tashi ba tare da ta ce masu komai ba ta je ta dauko rigar ta duba ta ga tsakiyan ne ya kone.

Ta shiga daki ta cire fil din da ke jikin rigar sanyinta, ta kara cire igiyar dake jikin takalminta.

Ta sa fil din ta kame daidai cikin inda ya kone din sannan ta zura igiyar ta kalli Madam Nasy da suka tsaya kallonta ta ce, "Madam yanzu zaki iya sawa,ko in nuna miki."

Da sauri Madam ta girgiza kai alamar e.
Deejerh ce ta taimaka mata tasa ta daure mata igiyar ta ciki sannan ta ja rigar sama.
Rigar ta fita sosai kamar ba ita ce ta kone ba, atakaice ma kara yin kyau tayi fiye da yadda take a farko.
Mamaki da farinciki ya kasa barin Madam Nasy ta rufe baki murmushi kawai take tana fadin, "Ikon Allah Kawata ki kalla rigar har tafi yadda na siya ma kyau, kamar an canja ta fa , jini? Ji yadda na yi kyau." Ta karasa maganaar tana rugume Deejerh ta ce, "Ke yar baiwa ce,kuma ke albarka ce,sannan ke Alkairi ce aduk inda zaki kasance,na gode sosai 'Yata." Ta karasa maganar tana yi mata kiss ta fice da sauri tana zumudin taje ta karasa shiri.

Murmushi ne ya sauka daga fuskar Ma'am ta dafa kan Deejerh kafin ta ce, "Alkairi."

Deejerh ma ta maida mata da Murmushin sannan suka ci gaba da aikinsu tare.
Har suka kammala suma suka shirya.

Zasu tafi kenan sai ga Ammar ya lallaba jikinsa shima ya fito yana sauri.
Ganin jikinsa duk a kumbure Ma'am ta ce, "Lafiya? Yau baka fito ba tun safe ga jikinka ma duk a kumbure kamar wanda aka ma duka?"

Deejerh ta daga kai ta kallesa sannan ta sunkuyar da kanta kasa ba tare da ta ce komai ba.

Ya ce, "Umm ba komai kawai bigewa na yi ne amman yanzu Normal ai, ke yar mummuna miskilancin ya motsa ne? Ko sannu da zuwa baza amun ba?"

Deejerh ta kallesa ta ce, "Umm ." Kawai ta yi shiru tana kara kawar da kanta.
Sanin halinta yasa ko damuwa da hakan bai ba, sai ma murmushi da ya sake yana, "watarana dai zan cire miki wannan miskilancin in jefar ateko muga ta yi." Ya karba kayan hannun Ma'am suna dariya suka tafi har suka isa gun suna hira ita kuwa Deejerh jinsu kawai take ba tare da ta ce Komai ba.

Suna zuwa suka tarar sai yabon kayan jikin Madam Nasy ake,aiko tana ganin Deejerh ta janyota tana nunawa sauran kawayen nata ta ce, "wannan ita ce sirrin

Please Login or Register in order to submit comment