Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

In sha Allah kuma ina godiya matuka."

Suka yi sallama ya tafi ita ma ta tafi.

★★★ Stylish Wordplay fashion School.
Tun abun da ya faru ranar jikin Esme ya yi sanyi akan Deejerh ,ko sakewa ba ta iya yi bare mata wani mummunan kallo.
Ita kuwa camellia suna hada ido da Deejerh ban da gira babu abun da take daga mata,har sai da ya Deejerh ta gaji ta daina daga kai.
Students sun cika class din da surutai tamkar kasuwa kowa da abun da yake,sabanin Desk din su Deejerh da Esme da dukaninnsu biyu suka mika hankalin su ga waya.

Ranar basu da lecture da Mr Laurent sai Mr Anthony.
Yana shiga Class din ya danna wani ball yana fadin, "Oya One Class Please."
Take suka tsagaita da hayaniyar da suke tare da mika Gabadaya hankalinsu gareshi.

"VINTAGE" Ya rubuta a White Board din nasu kafin ya ce, "Who can Define Vintage for us."

Duk shiru suka yi.
Ya kara fadin, "Nobody?"
Nan ma suka yi shiru.
Ya ce, "Alrigh....
Kafin ya karasa ya ga Deejerh ta daga hannu a hankali.

Team din su Deal da ke gefe suka fara nunata suna magana kasa-kasa.

Mr Anthony ya ce, "Yes,Go On."
Tashi ta yi ta ce, "Definitions. "Vintage" is a colloquialism commonly used to refer to all old styles of clothing. A generally accepted industry standard is that items made between 20 and 100 years ago are considered "vintage" if they clearly reflect the styles and trends of the era they represent."
Tafa mata ya fara yi yana fadin, "Very Good, That's the real Definition of vintage, na san yanzu kowa ya fahimci cewa Vintage na nufin tsofin kaya na da wa inda kakanni ko ince kakannin kakanninmu suka yi amfani da shi kuma har yanzu ana iya kara kirkirarsu har ma ayi amfani da su, yau kuma yanzu ina bukatar kowa ya yi Designing VINTAGE LOOKS Yes ina nufin a zana mun samfuri na tsofin kaya yanzu,kuna da ishashshan lokaci Zan ma fita in barku ku sha iska All I Want Shine in dawo in tarar da Vintage Looks, All The Best." Ya fada yana daga masu hannu tare da murmushi ya fice.

Yana fita kuwa, kowa ya fara ciku-cikun ciro Design Materials dinsa, suka fara, kowa ya fara amman ban da Esme ta ma rasa ta ina zata fara,sai dai ta kalli can,ta kalli nan.
Can Deejerh ta kalleta tayi kasaƙe kawai zaune.
Ta ce, "mene ne ya faru?"
A raunane Esme ta ce, "ban iya ba,ban san ya zan yi ba , na kasa."

Deejerh ta ce, "Alright zan goge nawa, yanzu zanna yi ina miki bayani kina kallo sai kema kiyi, kin gane?"
Esme ta girgiza kai.

Haka Deejerh ta goge nata da take ta fara yi tana yiwa Esme bayani ita ma tana yi har sai da ta tabbatar ta kammala kafin ta kara gogewa ta yi nata ita ma.
Tana gamawa Mr Anthony ya dawo ya na fadin Pen Off.

Suka yi submitting.

An tashi kenan Deejerh zata fita Esme ta taɓata ta baya.
Da sauri ta juyo tana daga hannu a tunaninta Camellia ce.

Sai da Esme ta razana , ta ce, "Sorry, I just wanna Say Thank You."

Murmushi Deejerh ta mata ba ce komai ba kawai ta gyara jakarta a baya ta tafi.

Da sauri ta ke kokarin fita daga Makarantar gudun kar camellia ta biyota.
Tana fita daidai wata karamar kofa bayan an fita a get kawai ta ci karo da team din Mael.
Ga dukkan alamu sun shahu tatil.
Su Bakwai uku sun tsaya gabanta, hudu sun tsaya a bayanta.

Jikinta ne ya fara rawa, kafafunta na kokarin gagara daukarta, ta kalli gabanta, ta kalli bayanta wani Numfashi ta sake tana ajiyar zuciya.

Dariya suka fara yi suna karasawa inda take,tana matsawa suna kara binta har sai da sukai daf da ita.
Daya a cikinsu ne ya fara rike mata fuska yana kissing.
Sauran kuma suka fara shafa mata jiki.
Wasu na lashewa.
Gabadaya tsigar jikinta ya tashi, kwakwalwarta ta fara birkicewa.
Kusan second biyar suna yin abun da suka ga dama ba tare da ta yi kokarin hanna su ba bare tanka masu.
Rufe idonta tayi Sosai, sai ji tayi suna kokarin zare mata kaya, dayan kuma yasa mata hannunshi a mara.
Kara kankame idon tayi ta ja hannunta daidai kan wanda yasa mata a mara ta murda hannun sai da ya yi kara.
Wanda yake mata kiss kuma ta buga goshinshi da nata.
Wanda yake kokarin ja mata sket kafarta ta buga masa a mara.
Sauran ma ta hankada su gabadaya ban da ihu babu abun da suke sakewa musamman wanda yaji bugu a mara da gudu ya bar wajen.

Karkade jikinta tayi ta gyara ta dauki jakarta ta maida baya sannan ta ci gaba da tafiyarta har ta fita wajen taran boss.
Tana zuwa kuwa cikin sa'a ta samu ta hau.

★★Dare kamar kullum zaune suke suna cin Dinner Ammar,Ma'am da Deejerh.
Ma'am ta yi masu Syrian Fatteh.
Ammar sai ci yake yana girgiza kai ya ce, "Ma'am yau kin tuna mun da kasata sai nake ji tamkar acen nake, wannan shine abincin da nafi so, lokacin Mamana tana yawan mun shi sosai musamman da nake karamin yaro kowanni dare shi nake ci a dinner in ba amun shi ba to ba zan ci komai ba."

Ma'am ta ce, "nima ina so sosai gaskiya shiyasa nake yi,wata kawata ce Yar kasarku nima ta koyamun And tunda ta koyamun na yi naji dadinsa."

Ammar ya ce, "Sosai fa ,Sai nake ji kamar yau a syria nake,idanuna na tuna mun da abubuwa sosai na jin dadi da kuma na rashin jin dadi da suka faru, ina fata ace watarana in koma inga kasata ko da sau ɗayane a rayuwa kafin in bar duniya."

Sai a lokacin Deejerh ta daga kai ta kalle shi ta ce, "amman ko yau ba MMA training gaskiya ni labarin Syria zaka ban na ga yadda kaketa kurantata kamar tafi kasata kyau."

Dariya Ammar ya yi, "aiko zan baki labari sosai ma duk abun da kike son sani mu dai gama cin syrian Fatteh."

Sai da suka gama tas, Deejerh ta kwashe kwanukan kafin suka fita tare suka zauna waje.
Ammar ya ce, "Oyaa to me da me kike son sani dangane da syria?"

Deejerh ta ce, "Abubuwa da yawa,amman dai da farko me yasa ka bar Syria din? Sannan Ina Iyayenka da yan uwanka?"

Ammar ya gyara zama ya ce, "to da farko dai ni kadai iyayena suka haifa,na taso cikin rayuwar jin dadi da gata duk da cewa mu ba wasu masu arziki bane,amman muna da rufin da asirin da muka fi karfin bukatunmu domin daga mahaifiyata har mahaifiyana ma'aikatan gomnati ne, silar rashin samun zaman lafiya da tashin hankali aka kashe iyayena da mutane da dama a kasar wanda har saida ya kai ga mu da muka saura wasunmu muka zaɓa yin hijira musamman ga wa inda suka rasa ahalinsu kamar ni dai kinji abun da ya faru."

Jikin Deejerh ya yi sanyi tausayinsa ne ya kamata har cikin ranta wanda sai da yanayinta ya sauya .
Da Ammar ya lura da hakan da ya kalleta sai ya ce, "Amman yanzu gani da wani ahalin ai Ubangiji ya maida mun har ma da 'Yar Uwa duk da dai mummunace amman haka zan lallaba."

Dariya Deejerh ta yi ta ce, "ka ji da shi dai to yanzu fadamun ya Kasar Syria take."

Ammar ya ce, "Syria Kasa ce mai a yanayi,amman tana da yawan mutanen da basa da aikin yi,sannan akwai cin hanci da rashawa sosai tamkar kasuwanci ko ince sun maida hakan ma kasuwanci, sannan mutanen kasar basa da kwanciyar hankali domin Yaƙin da ke kasancewa a ƙasar."

Deejerh ta ce, "Amman dai yanzu an rage Samun tashin hankalin Yaƙin ko?"

"Ehto haka na ji ana fada dai da sauki ba kamar da ba ko za mu je ne?"
Ammar ya fada.

Deejerh ta zaro ido tana.....


08103080717
[1/19, 5:46 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-37

"Cab ni ba inda zani ina nan ai."

Ammar ya ce, "kin ga yanzu ina turawa da kaya gun wani cousin Brother na dake can yana saidawa ana turomin da kudin ina so sai na tsaya da kafafuna na san me na taka ya dai kasance komin kankatar abu zan iya yi wanda zai amfani kasar musamman bangaren marasa karfi da ke buƙatar tallafi."

Deejerh ta ce, "Great abun na birgeni in naga ana taimakon mutane nima ina fatan Watarana Allah ya bani ikon sanya murmushi, Farinciki da walwala a rayuwar wasu,in hakan ya kasance zan ji dadi matuka araina."

Ammar ya ce, "Addu'a ita muke,kuma ita zamu ci gaba da sannu burika na Alkairi wanda muke tsammani da ma wanda ba ma tsammanin zasu tabbata."

Deejerh ta ce, "Hakane In sha Allah nikam, companyny da kake aiki na mene ne wai ma?"

Ammar ya ce, "COLORFUL CREATIONS, shine sunan kamfanin kuma karamin paint company ne, muna hada paint da kanmu sannan mu sayar a kasuwa kinga yanzu sauran kudina bayan na siya mana waya paint din na karba a Company na turawa cousin Brother na a syria."

Deejerh ta ce, "Ma Sha Allah, Allah kara arziki mai albarka, amman dai zaka gyara motarka ko?"

Ammar ya ce, "For Sure,har ma na bada an fara aikin."

"Ya yi kyau,Yau mun sha hira,ya kamata yanzu inje inyi browsing ka da in fara jin barci in gagara katabus." Deejerh ta fada.

Ammar ya ce, "Gaskiya kam, amman watarana nima zaki bani Labarin ki ."

Murmushi Deejerh ta yi,ta ce, "In sha Allah, Good Night have a nice Dream."

★★★★
Stylish Wordplay fashion School sun hada party na zuwansu makarantar kamar yadda kowasu dalibai ke yi.
Gabadaya matan sai suka sa Jeans din da aka basu wanda Deejerh tayi Designing.

Riga kowa ra ayinsa yasa da yawansu wata rigar da suka sa ma tamkar babune domin duk girjinsu a waje yake, musamman camellia.
Ita kuwa Deejerh rigarta blue mai kyau tasa ta kwanta ajikinta kuma ta rufe mata ko ina.

Babban hall din dake School din suka tare.
Ta ko ina sauti ne kawai ke tashi.
Kowa na harkar gabansa.
Masu shaye-shaye na yi masu romance na yi.
Daga mazan har matan.
Deejerh na shiga hall din kanta ya fara bugawa tana kokarin fita a hayyacinta kamar na Free Day.

Har ta ja kafarta zata koma, sai kuma wata zuciyar ta ce ta koma.
"Dolene in yi rayuwa cikinsu,kuma dole ne in jure,in daure ko da cikin raina bana so,abu ɗaya na sani,ba zan taba komawa rayuwar da nayi a baya ba,koma mene ne zai faru zan daure,zan jure,in danne zuciyata da duk abun da kwakwalwata zata ayyana mun." Abun da ta saka kenan a cikin ranta kafin ta shiga.

Jan numfashi ta yi ta duba gurin da ta ga ba kowa ta nufa ta zauna.
Ji tayi kawai ana tabata da fadin, "Hello."
Camille ce tana sake mata. Wani munafukin murmushi.
Tare da ƙoƙarin rungumarta.
Cikin sauri Deejerh ta dakatar da ita da hannunta.
Ta ce, "kin gani,bana son wannan rayuwar,ban sonta kuma bana sha'awar kasancewarta wannan bangaren naku ba tsarina bane, za mu iya zama friends kamar yadda kika bukata a farko amman kada wani lamari haramtacce ya kara shiga tsakanina dake, Addinina da al'adata bata hallata mun cudayan tsakanin jinsi ba,hasali ma hakan haramtaccen abune mai girma,ki tsaya iya matsayinki nima zan tsaya nawa domin ba zan taba jurewa wani abu makamancin irin wanda kike ba."

Camellia ta yi tsaki kafin ta ce, "Ki yi mun shiru ki saurara ni,zan iya biyanki ko nawa kike so,kuma zan iya daukanki muje ko ina kike so, in siya miki duk abun da kikeso, ba wani abu zaki mun ba,kawai ina bukatar kasancewa da ke muyi less, Kuma less din nan ba komai bane kawai jin dadine na tabbata da an fara zaki ji dadi sosai kina samun nishadi da farinciki kuma in kika yarda dani na daina soyayya da kowa sai ke, ke kadai zan ci gaba da so muna farantawa juna."

Wani irin kallo Deejerh ta bita da shi, kafin ta ce, "Wai ke kurma ce? Ba ki ji me na ce miki bane? Bana bukatar komai daga gareki, ki yi rayuwarki nima ki barni cikin nawa shike....
Kafin Deejerh ta karasa sai ji tayi Camellia ta rugumeta da karfi tana jura mata hannu cikin riga.
Tamkar xakin da ya ga abinci haka ta fara cakumar mata Brest da hannu tana matsawa.
Cikin zafin rai Deejerh na daga hannu ba inda ta sauke wani gawurtaccen mari sai fuskar camellia.

Wani irin dirar azaba da daina ganin da idanunta ke shirin yi,a dari ta zare hannunta cikin Rigar Deejerh.
Ta daura hannunta a fuska dai-dai inda Deejerh ta sake mata marin.
Ta kasa bambamcewa hannun Deejerh ne ya yi wannan marin da ke iya dakatar da kwakwalwar mutum ko kuwa wani abune ya daketa a fuska.
Deejerh ta ce, "wannan shine na farko,kuma na karshe , ko da wasa ka da ki kara gigin zuwa gareni da wannan gurbataccen shirmen naki."

Azabar da taji yasa dole jikinta ya mutu,hannunta a fuska har lokacin.
Deejerh ta ci gaba da danna wayarta.
Sai can camellia ta daga kai ta kalleta ta ce, "In dai nice na miki alƙawari sai kin bani da kanki sai kinzo kina kuka da neman amincewata kan less , And a lokacin ni kuma zan baki mamaki za ki gani." Tana fada ta bar wajen da sauri.
Deejerh kuwa ko daga kai batai ba bare ta kulata hasali ma murmushi ta yi aranta kuwa ta ce, "baki isa kimin abun da Ubangijina bai mun ba, sannan addua ita ce babban makamina aduk inda zan kasance."

Mael da yan Team dinsa suna kallon har camellia ta bar wajen.

Meal ya ce, "wannan yarinyar fa VIXEEN ce wallahi zaman lafiyan mutum ya bita a yadda take, yanzu kun ga camellia ta tarowa kanta wutar da bata sani ba."

Miracle ya ce, "Eheen na, ni fa yanzu tsoron yarinyar nan nake over wallahi, ta ci VIXEEN din she can deal with whoever try to take her down."

Warin Drugs da hayakin na kara tada mata hankali amman haka ta zauna dole tana googling da wayarta.
Bayan Esme ta gama cashar rawarta ta zo inda take.
"Excuse me please, zan iya tayaki zama?"
Deejerh ta kalleta da fara 'arta ta ce, "Why Not."

Zama tayi, ta yi shiru tana tunani.
Can ita ma ta dauko wayarta ta fara dannawa .

Tare suka zauna har aka fara cin abinci suka ci tare Esme ta ce Deejerh ta bata numberta.
Ta bata kuwa.
Nan ma ta mata godiya.
Domin yanzu matukar jin nauyin Deejerh take.

★★★★Mexico

Zayd fita ya yi neman kudi ba ji ba gani duk inda yasan zai samu kudi kutsawa yake.
Har ya kai ga ya fara yin kutse cikin dare wa drug Lords.
Ya fara cin amanar wasu yana kashe kananun don ya hau sama.


Bai samu yadda yake so ba amma ya samu kudin da yake tunanin zai wadace shi auren Huda.
Cikin dare kai tsaye gidanta ya nufa yana zuwa kofar dakin a bude bata rufe ba kuwa ya kutsa kai.
Ganinta ya yi kwance daga ita sai wata figigiyar riga da wani pant kwance a jikin wani suna romance.
A fusace ya karasa ya figesa sai da ya fadi kasa,ya kara figan masa riga yana shake masa wuya kamar zai kashe shi.
Ban da nishi babu abun da yake yana huci.
Huda ta rasa inda zata sa ranta, tana kokarin kwatar saurayinta da Zayd ya mata wata tsawa saida jikinta ya fara rawa.

Kara mukuresa ya yi yana dukansa a ciki.....


08103080717

Till Monday bye-bye.

[1/25, 2:46 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-38

Ganin da gaske Zayd shirin yin kisa yake, birkicewa Huda tayi ta fara kuka.
Zayd please, "ka barshi,kar ka kashe shi, Please Don Allah ka ji,zai mutu fa, zai mutu wallahi."

Ina ji yake kamar tana kara tunzura shi, kara dukansa yake har saida ya fara zubar da jini ta baki.

Huda ta gama tsorata kuka take har cikin ranta ta ce, "ka barshi na ce ka barshi Don Allah, wallahi in har ka kashe shi ba zan aureka ba,na fasa,na fasa auren wallahi." Ta fada tana faduwa kasa cikin muryar kuka.

Bai son kukanta ko kadan wanda jin hakan yake har cikin ransa, da sauri ya saketa ya koma gabanta yana daga ta.
Shi kuwa da ya samu ya kubuta daga hannun Zayd ai da rarrafe ya fice a dakin daga shi sai gajaren wando jiki jina-jina.

"Sorry Mon Cherie kinji,kin san ba zan jure ganinki da wani ba, zuciyata zafi take mun,ba za ta jure ba,kiyi hakuri in kika ce kin fasa aurena ji nake numfashina zai iya tsayawa,Ina sonki,ina kaunarki,kuma ina matukar bukatar rayuwa da ke."
Ya fada yana rugumeta.
Bangajesa tayi ta tashi tana shashshekar kuka tare da fadin.
"In kana sona da gaske ai zaka so duk abun da nake so, don haka karya kake baka sona kuma baka kaunata na fasa ka fita mun agida,ni kawai ka tafi mun a gida."

Binta ya yi ya rike hannunta yana durkusawa a gabanta, "ki yi hakuri kinji hakan ba zai kara faruwa ba,na miki alƙawari yanzunma na gagara jurewa ne,ki tashi kiyi wanka ki shirya mu je in siya miki duk wayar da kike so."
Huda ta ji zancen kudi zare ido ta yi tana fadin, "Really?"
Zayd ya dagata yana, "Eheen na,abun da na zo yi kenan daman, sannan kuma za mu je gida asa ranar aure da komai da komai."

Rungume shi tayi tana kai masa kiss tare da fadin, "I love You."

"Love You too, kije ki shirya ina jiranki." Zayd ya fada shi ma yana yi mata kiss din.

Da sauri ta nufi toilet ta yi wanka ta fito ta shirya cikin lokaci kadan.
Tsayawa ta yi a gabanshi tana Kallon shi ta ce, "na yi kyau?"
Zayd ya ce, "Sosai ma,kin san ke mai kyau ce a kullum kuma kodayaushe mu je ko."
Ya fada yana rike mata hannu suka fita tare.

★★★Ganin yadda yake kashe mata kudi ba tare da ko gezau ba, kuma abun da take so kenan,hakan yasa ta amince da maganar aurensa,babu bata lokaci aka daura auren inda suka tare a sabon babban gida na alfarma kamar yadda take da buri.
Washegarin Daurin aurensu da sassafe ta tashi ta fice tun kafin ya farka a barci.
Yana farkawa ya duba ko ina na gidan ya nemeta ya rasa,cikin tashin hankali ya fita ya shiga motarshi yana nemanta.

★★★Paris
Bayan Sati Ɗaya.
Deejerh ta ci gaba da zuwa stylish Wordplay fashion School tun bata jure zama a cikin su har ta saba koma me suke zata shiga ta zauna ko a jikinta ta kama harkar gabanta.

Vixeen kuwa ya fara binta a boye suna kiranta shi,duk wanda zaiyi maganar ta sai dai ya ce Vixeen.
Ita kuwa camellia ta dage tana son bullo da duk wata hanya da zata wajen ganin ta mallaki Deejerh ta fara binta domin a yanzu bata da burin da ya zarce ace Deejerh ta kasance mallakinta.
Esme har sun fara sabawa da Deejerh.

Zaune suke da ita sun fita break.
Tana dauko wayarta a jaka kawai wani tablet ya fadi kasa.
Deejerh ta daga tana ganin sunan da mamaki ta kalli Esme ta ce, "Weight loss drugs for what?"
Ta karasa Maganar tana mata kallon tuhuma.
Esme ta ce, "Bana so in zauna da ƙiba tana bani matsala sosai kuma School dinnan ma basu son a kasance masu jiki , sannan a gida...
Sai kuma tayi shiru.
Deejerh ta ce, "a gida me? Koma mene ne ka da kiyi abun da zaki illata lafiyarki don kawai ki birge wasu ko ki kubuta daga wani abu akwai hanyoyi ingatattu da ya kamata ki bi ai in kibar ce ba kya so ba wai shan wannan drugs din ba."

Esme ta ce, "ya zame mun dole ne, bana da mafita ne."

Deejerh ta kalleta, "bakya da mafita kamar ya?"
Idanunta ne suka canja kala hawaye na shirin taruwa mata.

Ta ce, "wasu abubuwan kawai ina yi ne domin nemawa kaina nishadi da yanci kamar kowa inna fito waje, domin kuwa a gidanmu na rasa wannan 'Yancin na kasancewa kamar kowa, don kawai na kasance mai jikin ƙiba sai ya zamana ana wareni daban, ana hantarata da kushe hallitata tare da fada mini cewa ni mummuna ce mara kyan jiki,hakan yasa dole na zabi kasancewa a wannan school din,kuma na nemi weight loss drugs domin fitowa a siffar da Dangina suka fi darajawa."

Deejerh ta numfasa kafin ta ce, "wannan ba mafita bace sam sam wannan ba mafita ba ce kinsan cewa wannan drugs din da kike sha zai sawa jininki ya hau? Sannan ya iya janyo miki diabetes da nausea, vomiting, diarrhea, constipation da headache sannan kuma yana da mahimmanci kisan cewa weight drugs loss are not magic solution for losing weight,ba zai taba zama ba kuma,in kina bukatar hakan sai dai ki gyara yanayin cin abinci ki sannan kuma ki fidda exercise plan wannan shine kawai mafita a gareku, sannan abu na karshe ki cirewa ranki cewa zakiyi wani abu dan wasu indai ba don Ubangijin da kike bautawa ba, to ba bukatar shigar da rayuwa a hatsari don wasu,ki yi rayuwa da zuciyarki ba ta wasu ba,kiyi abun da ya dace dake kuma zai taimake ki ba wasu ba,ki daina damuwa da maganar mutane ko yan uwanki akan yanayin hallitarki, yanzu abun da ya kamaceki kawai kije kiga doctor ya miki tsarin yanayin abincin da zakina ci sannan ki tsara yanayi da lokacin da zakina motsa jiki na tabbata a wata daya sai kin sha mamaki da ikon Allah hatta yan gidan nakun ma za su yi mamaki matuka."

Share hawayen dake zuba a idanunta ta yi ta rugume Deejerh tana, "na gode,na gode sosai duk da kiyayya da ƙyamar da na nuna miki a farko amman baki nuna mun komai ba, taimakona kawai kike,kinji dadi ke kam kina da zuciya mai kyau,na gode sosai."

Deejerh ta yi Murmushii ta ce, "ke ma zaki iya gyara halin ki ai,kisa aranki cewa talaka da mai kudi duk dayane agun Ubangiji sannan ki cire abun da kika sa a zuciyar ki na cewa zaki rama abun da ake miki a gida a waje ,laifin wani baya shafan wani."
Girgiza kai tayi tana kara yi mata Godiya.

★★Mexico
Zayd neman Huda yake duk inda ya san zai sameta zuwa yake amman babu ita babu labarinta.
Har saida dare ya yi ya koma gida.
Ya kasa zaune ya kasa tsaye ,yaje can ya koma can ba shi da sukuni sam.
Kamar daga sama ya ji anayiwa kofar wani irin bugu na rashin hankali.
Masifa ya fara yana fadin "waye ne?"
Ba a kulashi ba kara buga komar ake kamar za a bintike ta.
Da zafin rai ya bude.
Yana budewa Huda ya gani tsugune ga dukkan alamu bata cikin hayyacinta ta bugu sosai na fitar hankali.
Mika masa hannu ta yi cikin muryar maye tana fadin, "Zai....zaiy...yd

08103080717

*Sai anyi hakuri dani abubuwa ne sun fara yimin yawa bana samun lokacin hutu*

Luvs U OLL
[1/26, 10:30 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-39

"Ka rikeni zan...zan ..zan fadi."
Ta fada tana janyo mishi riga.
Riketa ya yi cikin zuciyar sa kuwa takaici ne ya tarun masa bai taba jin cewa bai son wani ya sha Drugs ba sai Huda.
Ya shigar da ita dakin ya kwantar da ita akan gado zai tashi kenan ta cakumo rigarsa tana, "me me yasa kake bata rai ne? Iyeeee? Ba za ka yi murmushi ba angona, angona ni amarya,,,matar Zayd."

Don takaici bige mata hannu ya yi ya tashi daga kan gadon kawai.
Ta maida kanta tana, "kaki dariya ba,ka ji da shi ai,ni dadi na na ke ji."

Duk da cewa yana daya daga cikin manyan masu safarar drugs amman ji yake aransa koda wasa baya so Huda ta kara kusantar sha,har zafi zuciyarsa ke yi masa.
Ita kuwa barci ne ya kwasheta hankalinta kwance.
Ya koma daf da ita yana shafa fuskarta da gashin kanta.
Kusan kwanan zaune ya yi agun har gari ya waye.
Gani yake kamar in ya yi barci zata kara yi masa irin na jiya.

Tana farkawa ido suka fara hadawa ya sake mata murmushi yana, "Good Morning Mon Cherie."
Cikin muryar barci ta ce, "Morning Zayd."
Tana ƙoƙarin tashi.
Fara sabgar gabanta ta yi kamar babu abun da ya faru.
Zayd ya ce, "Yau ma fitan zakiyi kenan?"
Ta girgiza masa kai kafin ta ce, "zan tsaya a gida mana,jiyan ma Party ne friends dina suka hada mun so akwai bukatar na je tun da wuri kamar yadda suka bukata."
Zayd ya ce, "Amman ai nima akwai bukatar ki sanar dani ko? Kuma indai don bikinmu ne suka shirya miki taro nima ina ciki ai,ya kamata ace muje tare,ki sani fa yanzu ke ba budurwa ba ce kuma....
Juyowa tayi tana daure gashin kanta karaf ta katse shi da fadin, "kuma me? Wai nufinka don

Please Login or Register in order to submit comment