Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana nuna masu bayanan zaiyd da batattun kayan da suke shigowa da shi,a yanayin yadda bincike ya nuna da sunan Fashion companynta ake shiga da abubuwa da dama wa inda suka zama babbar illa da barazana ga rayuwar yan Adam a yanzu, in baka manta ba ranar da ku muke kallo a labarai ana magana akan kush to wannan case din da ya zama kan kamfaninta dauke yake da cewa suna cikin manyan da ke safarar kayan a duniya."

Dubawa Khalil ya yi, ya ce, "amman kuma na ga ai ba da Austaraliya suke amfani ba, Mexico ne and baka samun sunan wani ba?"

Xavier ya ce, "Yes Mexico ne lamarin an rufesa sosai yadda zamu sha wahalar binciken ne akwai sunan kamar wanda ya kasance yana rolling team din Zayd amman ya nuna tsarin cewa ita wannan takun ce Founder kuma shugabar boye."

Khalil ya kara maimaita sunan, "Zayd?... Zayd....zayd.. kamar na taba jin sunan nan agun Deejerh kuwa."

Ya yi shiru, sai can kuma ya ce, "Yes! Na gano kan abun Uncle dinta ne tabbas shine yake amfani da sunan kamfaninta yake wannan lamarin."

Xavier ya ce, "Kamar ya? Ka bani in details mana."

Khalil ya ce , "No ka tambaya wannan ni dai abun da zan fada maka shine babu ruwanmu a batun safarar kush ba ma ta da lokacin yin wannan harkar ba ta ma san ya zata yi ba, don haka ka cireta a sahun wannan batun."

Farouk ya ce, "Eheen gwanda ka fada masa kuma ya cire bibiyar da yake yiwa system dinta."

"Komai dai ya wuce daman rashin fahimta ne yanzu abar batun kawai."
Haiydar ya fada.

Khalil ya ce, "Yes, mu je mu kwanta kafin wa innancen su fahimci wani abu."

Haka suka koma kowa ya tafi dakinsa.

Washegari da safe
Khalil da kan shi ya sanar masu da cewa zasu yi tafiya duka.
Da sauri Noor ya ce, "dad ina zamu je?"

Khalil ya ce, "ba zan fadawa kowa ina ne ba ku dai kawai ku kasance cikin shiri gobe, kila yau Zoe zata tawo daga SINGAFUR ita ce zata kai mu In sha Allah."
Murna da rawa yaran suka fara suna tsalle.
Anitha ta ce, "Dad amman da Asherr zamu tafi ko?"

Khalil ya girgiza mata kai alamar e.
Nan suka fita da gudu suna murna da ke Asher ya dan fara sakewa cikinsu amman kuma duk da hakan yafi sakewa da Deejerh suna wasa tare.

Sun fara shirin tafiya Mexico kamar yadda Khalil ya umarta.
Duk da cewa har lokacin Deejerh bata san cewa kasarsu za a aje ba.

Khalil ya nemi Maestro Roman da Nawar duk ya sanar da su zuwa su.

Adaren Ranar Zoe ta isa Austaraliya
Dake Khalil ya tura mata adress din kai tsaye tana aje jirgin a airport ta nufi gidan da suke.
Sai da ta yi wanka ta ci abinci ta huta kafin ta je palourn da suke duka zaune.
Farouk ya ce, "Yammata wai ya naga sai wani kara fresh kike ne kina kyau? Kina jin dadi da yawa fa."

Zoe ta yi murmushi ta ce, "ban kai ka ba ai, yau tsokanar taka ta dawo kaina kenan,ina gimbiyar taka?"

Tana fada sai ga zeeyter ta shigo tana, "gani nan wa ya taba mun aboki."

Farouk ya ce, "No kawai yau ta ganni ba ke ne bata ga muna yar gulma ba."
Zeeyter tayi dariya ta zauna kusa da Farouk din cikin kasa kasa da murya ta ce, "na lura fa kallon da kake mata tunda ta shigo ba na wasa bane, anya kuwa babu wani abu da kake boye mun?"

Dariya Farouk ya yi,ya ce, "haba dai babu komai kema kin san da ace da kwai wani abu da tuni ke zan fara sanarwa muyi shawarar just kawai kin san halina ai ko ba haka ba?"

Dariya suka yi duka tare.


Sun sha hira sosai.
Zoe ta tashi ta ce zata tafi ta kwanta, karaf Farouk ya ce, "in dai kina jin tsoron barci ke daya akwai mai gadi da taya kwana."

Zoe ta ce, "ina yake?"

"Gani nan tsaf sai inyi gadinki ki biyani."
Farouk ya fada.

Dariya suka yi ta tafi ta kwanta abunta.

★★Da wuri suka tashi suka fara shirin tafiya Mexico

Sun hau jirgi sun fara tafiya Deejerh dai ta ga kamar Mexico suka nufa, tana so ta yi magana sai kuma ta yi shiru tana tunanin kamar ba hakan bane.

Har sai da suka isa.
Jirgi na sauka kowa ya fita ita ce karshe tana zuwa tasa kafarta kenan zata fita ganin tabbacin a Mexico take ta kame bata san lokacin da hawaye ya fara kwarara daga idanunta ba, ta rasa meke yi mata.
Benito Juarez International Airport dake private jet ne ba mutane agun sai iya su da suke sauka a jirgin
Zeeyter ce ta juyo ta kalli Deejerh kame.
Da sauri ta karasa ta riko hannunta tana sake mata murmushi.
Kakalo murmushin ita ma Deejerh tayi duk da cewa jikinta ya gama sanyi idanunta ya cika da ruwa amman ta hana hawayen fita bare ya zuba.
Rayuwar da tayi a kasar Mexico kawai take gani zuciyarta na saka mata.

Zeeyter ta ce, "bana so ki ji babu dadi aranki ko kiji rashin kyautuwar zuwanmu nan, domin kuwa lallai yana da mahimmanci a gareki,ki cire komai aranki ki ji cewa zaki iya wuce kowanni mataki."

Bata ce komai ba,amman kallo daya zaka yi mata kasan cewa jikinta a sanyaye yake gabadaya babu laka a jikinta.

Hango Nawar da Maestro ne yasa hawayen idanunta zuba da murmushin su suka tawo gareta duk girma ya kamasu su kara zama manyan mutane.

Roman ta fara rungumewa tana kuka, ya shafa bayanta, "Deejerhtou na ta girma ta zama yan mata amman halin kukan ba a daina ba."

Ya karasa maganar yana share mata hawaye.
Rungume Nawar ma ta yi shima cikin murmushi da fara'a ya ce, "Kawata ta kara kyau sosai abunta na ji dadin ganinki a wannan yanayin."

Gaisawa suka yi da sauran 5stars duka kafin suka hau motar tafiya gidansu Deejerh har da su Nawwar din.

Deejerh ce ta fara zuwa bakin kofar dakin dake get din a bude yake ta fara nocking.
Idanun momynta jajir ta gama shan kuka tana zaune tana karatun Qur'ani ta ji ana buga kofar, tashi tayi tana kara share hawayen dake idanunta ta je ta bude kofar.
Idonta cikin idanun Deejerh jinta tayi tamkar ta suma ta kara kura idanunta domin tabbatar da ba Mafarki take ba.
Gani tayi da gaske dai Deejerhn ce tsaye gabanta.
Kara fashewa tayi da wani kuka mai tsuma zuciya.
Zata rungumeta ta fadi tana kwallawa Dadyn Deejerhn kira.
Cikin sauri ya fito daga toilet saboda yanayin yadda yaji muryarta ta.

Deejerh na kuka Momynta na yi ta dagata suka rungume Juna.
Dadynta ya fito yana, "mene ne?"
Ganin Deejerh yasa numfashinsa tsaya na yan seconds.

A lokacin 5stars suka shiga suma da sallamarsa.
Janye jiki Momyn Deejerh tayi ta kara sulale kasa kan gwiwarta hannunta rike da na Deejerh ta ce, "ashe zan ganki? Ashe Idanuna zasu kara tozali dake? Ashe zan samu damar neman yafiya a gareki? Tabbas a kullum sai na zubar da hawayen dana sanin halin da na jefaki,ni da kaina da kuma hanuna na siya tikitin tarwatsa miki rayuwa,ni da ya kamata in gina,nina rusa tushen dana fara, Ba don ni ba, Don girman Ubangijin da ya yiyini ya kuma yi ki, ki yafemun ko zan daina jin radadi da zafin ciwon da zuciyata ke yi mun, tabbas ban kasance uwa ta gari ba,kuma jigo ta gari gareki ba,amman ki sani wallahi ina kaunarki har cikin raina, son duniya da son zuciya ne ya rufe mun ido da ganin cewa ai ba wani hali ko yanayin damuwa kike ba, na so kaina ,na kuma so zuciyata ni ban kasance uwa ta gari ba, ki yafe mun ,Ki taimaka ki yafe mun khadija ki yafe mun ko zan ji dadin rayuwa na san zaki iya jin ba wacce kika tsana a duniya sama dani, amman ni dai ki mun alfarmar yafiya gareni ko zanji sa'ida araina."

Cikin Muryar kuka ita ma Deejerh ta ce, "ko ba komai ke mahaifiyata ce,kuma kin raineni tun kan na zo duniya har na zo cikin haka kuma kin bani kulawa a farko kafin zuciyarki ta karkata ga wani kudirin ko da ace zuciyata bata da niyar yafe miki ya zama wajibi gareni domin kin cancanta kuma na ji dadi da kika gane kuskurenki na yafe miki,na yafe miki har bayan Raina domin nasan da cewa duk wata nasara da zan samu arayuwa kune sila , adduarku gareni ta tsallakar dani abubuwa da dama na rayuwa."

Kara rungume juna suka yi, Dadynta ma yaje duka suka rungume juna ya ce, "yau kuka ya kare, kuma addu'ar mu ta karbu Allah abun godiya."

Sai a lokacin momyn Deejerh ta ga Nawar.
A tsorace ta nuna shi tana, "wannan ba Ogan zaiyd ne ba, kar dai har yanzu suna binki? Suna son ci gaba da bata miki rayuwa?"

Murmushi Deejerh ta yi ta ce, "wannan ba halinsa daya da Uncle Zaid ba,hasalima shi yayi sanadin fita a kasar nan ta kubuta daga zaluncin shi."

Jiki na rawa Momyn Deejerh ta kallesu tana "ku zauna mana bara inje in kawo muku ruwa ko? Sai a daura abinci."

Khalil ya ce, "Aa Momy ki huta yau, duka muje restaurant mu ci abinci."

Haka kuwa akayi har da Dadyn Deejerh duka suka nufi restaurant din.

Khalil,Xavier da Roman da Nawar table daya suka zauna.
Suna cikin ci Khalil ya shigo da maganar zaiyd yana tambayar Nawar.

Nawar ya ce, "yana nan ya yi aure da matarshi ya kara zama dila sosai don a yadda na ji labari ma yana daya daga cikin manyan dake safarar kush a kasar nan."

Xavier na ji ya yi saurin daga kai......

[5/18, 9:21 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-55

Ya ce, "Ikon Allah,ni kuwa ina so in ganshi."

Nawar ya yi dariya, "da kamar wahala ai yanzu ko gidan zayd mutum zaije ganinsa zai yi masa wahala yaransa ma boyayyayyune bare kuma shi saidai akwai wani karamin kamfanin su anan cikin gari."

Xavier ya ce, "ko zamu samu adress din? Ina so in ganshi ne nima ina harkar kush din kila mu daidaita."

Nawar ya ce, "ok ba matsala zan tura ma adress din."

Da haka tare suka gama cin abincin suka yi hira sosai kafin suka maida momyn Deejerh da Dadynta gida su kuma suka nufi hotel.
Momyn Deejerh ta so Deejerh ta zauna, da kyar ta hakura kan cewa sai gobe zata dawo.

Bayan sun je hotel Xavier ya kira Khalil gefe yana fadin, "ina son ka bani labarin Deejerh da kuma alakarta da Uncle dinta."

Khalil ya ce, "Aa ni ba zan ce ma komai ba, ka sameta kai da kanka ta baka labari."

Xavier ya ce, "meyasa? Ni fa abokinka ne ban taba neman abu a gunka na rasa ba sai wannan?"

Khalil ya yi murmushi kafin ya ce, "yawancin abun da kake tambaya ni suka shafa wannan kuma sirrin rayuwarta ne ban da hurumin tona maka zai fi kyau in ita da kanta ta gamsu kuma ta amince da sheda kama labarin rayuwarta."


Xavier ya ce, "hakane kana da gaskiya zan gwada sa'ata."

Ya fada yana shigewa ciki.
Dakin da take ya yi nocking
Ta amsa da , "Yes Come in."

Zaune take da Asher suna wasa ,ya ce, "nima zan iya zama muyi wasan?"

Da fara'a a fuskarta ta ce, "Why Not?"

Karasawa ya yi,shima ya zauna yadda suka zauna a kasan.

Suna cikin wasan Xavier ya ce, "Ina son jin labarin rayuwarki atakaice in ba zaki damu ba."

Daga kai Deejerh tayi ta kalleshi sai kuma tayi saurin sunkuyar da kai take yanayin jikinta ya sauya.

Xavier ya ce, "kiyi hakuri Don Allah kar kiji babu dadi indai bakya son maganar na bari sorry."

Deejerh ta yi murmushin karfin hali kafin ta ce, "bari asher ya yi barci zan baka labarin rayuwata duk da cewa ba labari bane me dadin ji ko saurare amman akwai darussan rayuwa da ya kamata Iyaye su dauka ko ince su hankalta akai."

Ba jimawa kuwa Asher ya yi barci dake ya riga ya sha maganinsa kuma lokacin barcin na sa ya yi.

Bayan ya yi barci Deejerh ta fara bawa Xavier labarin tarihin rayuwarta tun daga yarintarta har i zuwa girmanta a yanzu musamman azabar rayuwar da ta sha agun zayd, tana gama bashi a karshe ta ce , "ban jin tsoron ganin uncle a yanzu amman kuma idanuna ba za su taba jure ganinsa ba, domin in akwai abun da na tsani gani a rayuwata bayan shine a halin yanzu ance ya yi aure yana da mata kuma ya kara yin kudi fiye da baya kuma ina jin cewa hakan da Ubangiji ya yi masa talalane kawai babu shakka nasan sai ya girbe abun da ya shuka ina jin hakan a jikina bai tarwatsa mun rayuwa a banza ba dole zai karbi sakamako ko da kuwa bani bace silar amman Ubangiji zai kawo silar da za a bi mun hakkina."

Duk jarumta irinta Xavier jikinsa ya yi sanyi da lamarin Deejerh ya rasa meke yi masa dadi tsantsan tausayinta ya fara ji har cikin ransa yana kara jin cewa lallai zai yi iya yinsa wajen tabbatar da Zaid ya girbe abun da ya shuka.

★★Da tulalen ciki Huda ta nufi dakin Zayd cikin dare, barcinsa yake hankali kwance aiko ta dunga zabga masa duka har sai da ya tashi.

"Haba wai ke bazaki taba barina in huta ba? Cikin daren ma ba zaki barni na dawo in samu barci yadda ya kamata ba?" Zaid ya fada cikin yanayin fushi.

Tsaki Huda ta yi, ta ce, "Tun da kai ba ka da zuciyar yin cikin ai ya zama dole ka yi aiki da wahalarsa wallahi ba za ka yi barci ba, bukata nake da a yanzu kuma."

Juyawa ya yi yana kokarin gyara kwanciya.
Ta haye gadon tana cakumo shi tare da kokarin fara raba shi da kayan jikinsa.

"A daren nan ba yadda za ayi ince zan wani yazo ya biya mun bukata bayan ka ga nan duk da cewa kai dinma fanko ne sadai in rage radadi in samu sukuni."

Ba yadda ya iya haka ta hanashi barci har sai da ta samu ya biya mata bukata kafin ta tashi ta tafi.
Tana tafiya zai kwanta kenan kawai yaga sako ya shigo masa waya, dubawan da zaiyi yaga sakon daya daga cikin yaransa ne yake sheda masa cewa Deejerh na cikin Mexico fa ta shigo yau da safe kuma sun tabbatar da hakan.
Har da hotonta da mutanen da take tare da su duk ya tura mai.
Tashi ya yi, tuni barci ya bar idanunsa takaici ya kara bayyana ƙarara a fuskarsa domin duk da cewa ya san Deejerh na rayuwa cikin kwanciyar hankali amman baiyi tunanin cewa kwanciyar hankali da jin dadin nata har ya kai haka ba.

"Kin sani a kunci da takaicin rayuwa wanda har ya kai ga matata bata mun kallo a matsayin Ɗa namiji bare miji a gareta,amman ke kina nan kina walwala kina jin dadi? Ina ganin Yan mata amman ban da karfin binsu bare jin dadin rayuwa duk saboda ke? Tabbas nine sanadinki sai nayi maganinki duk rintsi duk wuya ko da kuwa komai dana tanada zai kare a rayuwa indai ta dalilinki zan yi."

Kai tsaye kiran Babban yaronsa Rohaan ya yi yana fadin, "Duk yadda za ayi ku kasance a duk inda take kuma duk wani motsinta ya kar ya wuce idanunku a baza yara ta ko ina inda hali ko kyakkyawan numfashi ne da zata yi mu san labarinsa kuma a binciko mun shin suwaye tare da ita mene ne alakarsu da ita da duk wani abu da ya shafesu duka."

Rohaan ya ce, "an gama sir ba ka da matsala komai zai tafi daidai za ayi yadda ka ce."

Zaid ya ce, "Rohaan ina kara fada ma a kula da motsin yarinyar nan Domin tana da mahimmanci a rayuwata in ba wai na kai ga cimma nasara da tabbatar da kudirina a kanta ba akwai babbar matsala zan iya ruguza komai kuyi duk yadda zaku yi ku tsaya tsayin daka wajen ganin kun aiwatar da abun da na sa ku,kuma ku tabbatar babu wanda ya fahimci kuna binta ko ayi tantamar ganinku kuyi taka tsantsan."

Rohaan ya ce, "ba ka da matsala Sir."
Yana fadan hakan zaid ya jefar da wayar kan gado yana dafa kan shi.

Ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kai da kawowa yake a daki karshe ya janyo system dinsa ya kara shiga page din Deejerh na Instagram yana bincike.

Barcin da bai koma da kenan tunani da zillimin yadda zaiyi da Deejerh kawai yake yana kara bincike.

★★Dukaninsu sunyi wanka dake babban hotel ne waje daya suka hadu suna breakfast
Asher na nanike jikin kusa da Deejerh.

Xavier ya ce, "wato yanzu ka yi momy ni an manta ni ko? Ko kulani ma sai ka ga dama kake."

Gyada masa kai ya yi kawai yana kara rike hannun Deejerh.

Cikin tsokana Xavier ya ce, "zamu tafi ai zan ga gunwa zaka na zuwa in baka ganta ba."

Asher ya daga kai ya kalli Deejerh da sauri yana girgiza kansa alamar aa kar ta tafi.
Murmushi ta yi ta ce, "ba inda zanje ka ji, ko da ma zanje wani gun da kai zani."

Asher ya kalli Xavier ya masa Gwalo dukansu sai da suka yi dariya.
Deejerh ta ce, "yawwa ban san ko zaku fita ganin gari ba,ina so innaje gida zan wuce gun Friends dina munyi alƙawari zamu hadu."

Khalil ya ce, "Ok to ba matsala amman ina tunanin ku tafi da Farouk ko? Don ban so kina yawo ke daya a cikin garin nan gudun matsala."

Deejerh ta yi murmushi, "haba dai zan iya kula da kaina ai ba komai kar a takurawa Handsome Guy na san yau yana shirin sumar da matan Mexico da ruwan soyayyarsa."

Da dariya Farouk ya ce, "kamar kuwa kin sani zance kin kwafsa mun kin hana mai farin jini watayawa."

Xavier ya ce, "in ba matsala Ni zan bita muje tunda na san Asher da kyar zai barta,in muka je tare ba zai takura mata ya hanata sakewa ba."

Da sauri Zeeyter ta ce, "Yes Case close tare zaku domin nima ban yarda da fitanta ita kadai ba za a iya samun matsala."

Deejerh dai bata so ba,amman ba yadda ta iya haka tayi murmushin yaƙe, ta tashi ta dauko jakarta suka yi masu sallama suka fita hannunta rike da na Asher.

Suna fita..........
[5/21, 9:37 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-56

Sai ga Yaran Zaid kuwa suna biye da su.
Ganin Xavier daya a cikin su ya ce, "amman dai na so ace ita kadai ta fito domin wannan kana ganin yanayinsa ma ba zai barmu muyi wani abun da muke so ba."

Dayan ya ce, "kar ka damu ai ba sauri muke ba, kawai dai yanzu mu bibiyesu duk inda zasu yi."

Budewa Asher bayan mota suka yi ya shiga,ita kuma ta zauna a gaba, Xavier yake driving dinsu.
Kai tsaye gidansu Deejerh suka fara nufa.

Da murna Momyn Deejerh ta karɓesu tana yiwa Asher wasa.
Fir yaƙita yana naniƙe da Deejerh.
Har suka gama zamansu ko matsawa bai yi ba yana jikinta.
Sunci abinci sun sha hira kafin Deejerh ta ce zasu tafi suje su hado da su Maira.

Xavier ya ce, "yanzu ina zamu nufa?"

Cikin gajerar amsa Deejerh ta ce, "Landscape Demostration garden."

Xavier ya ce, "Alright aiko garden din na da kyau sosai akwai lokacin da muka zo aiki ina yawan zuwa gun kuma ina jin dadin zama."
Sambatunsa ya dunga yi ita dai Deejerh bata kula shi ba, a karshe ma wayarta ta dauko ta fara dannawa.
Kokari yake ya ga ya jata sunyi hira amman sam Deejerh taki har suka isa.

Suna zuwa da gudu Maira da Noha suka rungumeta suna kukan farinciki.
Ita ma Deejerh bata san lokacin da ta fara kukan ba.
Maira ta ce, "ashe za mu ganki? Ashe zamu kara ganawa da juna? Na sha mafarkin ganinki ashe zai tabbata?"

Noha, "ji nake tamkar yanzun ma a mafarkina kawata tayi kyau ta kara kyau kuma ga dukkan alamu ya nuna kina cikin kwanciyar hankali Alhmdu Lillah , Alhamdu Lillah, Alhamdu Lillah, Allah abun godiya."
Noha ta fada tana share hawayen dake zuba a fuskarta.
Daeej da Abiel bayan sun gama gaisawa da Xavier, Daeej ya ce , "to iyayen kuka muma a bari mu gaisa kuma muma munyi kewarta ai ba ku kadai kuka yi ba."

Abiel ma ya ce, "Eh mana sun wani kankameta ku barmu mu sarara Please."
Dariya suka yi duka, Maira ta ce, "amman dai mun fi ku kewarta ai."

Rungume Juna suka yi duka suna gaisawa kafin suka samu waje suka zauna.
Maira ta mikawa Asher Hannu yaki zuwa , murmushi ta yi kafin ta kalli Xavier da ya zauna gefe kafin ta dawo da idonta kan Deejerh ta ce, "Freind kar kice mun kinyi aure ba labari, wannan yaron mune?"


Deejerh ta galla mata harara kafin ta ce, "amman dai baki da seti yaushe har zanyi aure in haifi Asher?"

Daeej ya ce, "waya sani ko a ruwa kika sha har kika haifeshi?"
Dariya suka yi.
Deejerh ta ce, "ba za dai ku canja hali ma, Yaron Xavier ne, And Xavier kuma Freind dina ne Shikenan."

Noha ta ce, "watarana ina zaune inna tuna rayuwarmu A school kawai sai inta dariya."

Maira ta ce, "musamman in muka shiga class mai duhunmu muna lamura sosai fa."

Daeej ya katse su da fadin, "gaskiya nima nayi kewar wannan ranakun amman babban abun da nafi jin dadinsa shine ba mu kammala school ba har sai da muka ajiye gurbTacciyar dabi'ar da mukai kokarin daurawa kanmu."

"Yes wannan kuma kokarin Deejerh ne nima ina jin dadi sosai inna tuna cewa mun jajirce wajen gyara rayuwar da muka bata da kanmu kuma na kan ji tausayin duk wanda na ga yana kokarin sa rayuwar sa cikin wannan gurbin tare da nusar da shi cewa shaye-shaye ba abun yi bane kuma ba madubin inganta rayuwa bane hasali ma sai dai ya tarwatsa."

Sun sha hira sosai sunyi hirar Maestro Roman ma sosai zasu tafi Deejerh ta ce kowannensu ya tura mata account number dinsa.
Aiko sunji dadi sunyi farinciki da kanta taje ta raka su Xavier na zaune da Asher ta dawo kenan ta tsaya
ya ce, "ki zona mana muna mu danyi hirar kafin sai muje can mu same su mu koma gida tare ko kuma mu dan shiga ciki mu kara ganin garden din."

Atakaice Deejerh ta ce, "Ni kawai ka zo mu tafi in kuma ba za ka tafi ba ni zan tafi."
Tana fada ta juya, abun da idanunta ya gani yasata firgicewa cikin kankanin lokaci kafafunta suka fara yimata rawa tana kokarin kasa tsayawa.
Wani irin sarawa kanta ya fara, jikinta na bari, lokaci guda wani irin gumin ya game jikinta, tamkar wacce ruwan sama ya mata duka, tsantsar tsoro da firgici hade da mamaki ne ya bayyana a idanunta.
Cikin kaduwa tayi saurin juyawa har tana shirin faduwa ta kankame Xavier.

Zaid ne tsaye gabanta......
[5/23, 12:58 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-57

Xavier kallo ɗaya ya yiwa zaid zuciyarsa ta raya masa cewa lallai shine Uncle din Deejerh.
Wani irin mummunan kallo yake bin Deejerh da Shi.

Xavier ya kalleta ya rike mata hannu suka tsaya kafin ya ce, "Ki Yarda da kanki kuma ki tunawa ranki cewa babu wani mahaluki da ya isa ya cutar da Dan Adam ba tare da Ubangiji ya rubuta ba, ka da ki yi kokarin maida rauninki kasawarki yi kokarin danne zuciya koda kuwa cikin duhu kike ki tursasawa ranki cewa a haske kike har sai hakan ya tabbata."

Wani kwarin gwiwa taji nan take,ta daga kai suka hada ido da Zaid yana sakin murmushin mugunta.
Ita ma murmushin ta sake masa mai dauke da salo na ban al'ajabi har sai da yaji wani yanayi aransa.

Nuna mata yatsa ya yi ba tare da ya yi magana ba, alamun zasu gamu dinnan kafin ya kara karewa Xavier kallo da Asher.
Ya kara maida kallonsa kan Xavier yana yi masa kallon tara saura kwata ya gyara glass din fuskarsa kafin ya ce, "Carpenter."

Yana fada ya tafi.
Shiko Xavier yana jin ya furta Carpenter nan a zuciyarsa ya ce, "lallai wannan babban kwarone babu shakka ya yi bincike akaina."

Yana tafiya tayi wata ajiyar zuciya,zata tafi Xavier ya riko hannunta, ya zaunar da ita.
"Shine Uncle dinki ko?"
Ta girgiza masa kai alamar e.

"Dole zaki razana kuma ki shiga wani yanayi don kin ganshi a yanzu duk da cewa bai isa ya yi miki komai ba,amman ina so ki kara kokari wajen danne duk wani yanayi da zakiji aduk sanda zaki ganshi ki

Please Login or Register in order to submit comment