Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Yallabai Don Allah gida,ban da lafiya zazzabi nake.... Kafin ta karasa bakinta ya fara bari.
Juan ya taɓe baki kafin ya ce, "Okay." Ya ciro wayarsa ya kira Zayd sannan ya bude masa kofar.
Da kyar ta ja kaya ta maida jikinta, idanunta na rufewa haka ta tashi tana kokarin faduwa ta bi Zayd da ganin ta cikin yanayin ma kadai nishadi ya bashi.
Sai wala gigi take zata fadi kenan tayi saurin dafe bango tana ajiyar zuciya.
Zayd ya yi tsaki, "Kizo mu tafi in ba haka ba ni tafiya ta zan ba tsayawa jiran wannan shirmen naki zanyi ba ni."

Rarrafawa ta yi,ta karasa ta shiga cikin motar tana ji kamar ranta zai fita.
★★suna fita Juan ko kaya bai sa ba ya yi wata sufa ya dane kan gadon yana mai jin dadin ya aikata abin da yake da muradi.
Dariya ce ta koma ihu take fuskarsa ta sauya yadda yaje wasu sukan allurai kamar daga sama.
Tsabar ihu sai da kararsa ta karade gidan gabadaya.
Aguje ma'aikata da masu gida suka nufi dakinsa.
Cikin firgici ya tashi yana zare towel din jikinsa, ji ya yi abubuwa a jikinsa amman ya gagara sanin daga inda suke.

Sai tsalle yake,yaje can ya dawo,ya tsuguna ya tashi, duk sunzo sun taru suna nocking kofar, gashi ya gagara budewa duk ya fice daga hayyacinsa

Yana sa hannu a baya yaji kamar abu ya kara shige masa ciki.
Tsalle da ihu a tare ya fara karamar hauka.
Ganin abun bana kare bane kukan aure da salati hakan yasa suka samo abu suka buga kofar ta bude kawai.
Suna shiga suka rirrikesa yana fadin, "ku duba mun duwawuna abubuwa ne a ciki,allurai,allurai aka turo mun,zasu kasheni."

Kwantar da shi suka yi ta karfi suka dauko wata allura ganin alamun waje biyu sunyi tuda da ja yasa suka zura gun.
Aikuwa karfen yan kunnayen Deejerh kam suka cafko.
Yana kara sakin kara suk danne sa ,sai zufar azaba yake,suna cirewa ya yi wani numfashin fitar azaba.
Tashi ya yi yana kokarin zama,aiko yana daba duwawu ya ji wani irin radadi a dari ya tashi.
Karshe sai rif da ciki ya yi ya kwanta take barcin azaba ya yi awun gaba da shi.

★★★
Suna shiga gidan Zayd ya fice a motar ya barta.
Dakyar ta samu ta bude kofar da rarrafe ta shiga cikin dakinta.
Gagara hawa gadon tayi ta zauna kasan kawai tasa hannunta ta janyo bargon ta lulluɓe jikinta.
Wani irin sanyine yake kara ratsata har cikin ƙashinta, fatarta kuwa har tururin zafi take fiddawa.

Ga barci ya ƙi daukanta. ban da ɓari babu abun da jikinta keyi.
Adduo'in da duk suka zo bakinta kawai take furtawa har saida aka yi kiran sallar asuba kafin barci ya dauketa.


*AYI HAKURI DA WANNAN KILA GOBE DAKYAR KU SAMU UPDATE,HAR YANZU BANJIN DADI*

08103080717
[12/11, 3:44 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-21

Tunda barci ya dauketa har karfe Goma bata farka ba.
Zayd ya fita ya koma gidan, kamar da wasa yana leƙa dakin Kuwa Sai ya ganta kwance a kasa tana sharban barci.
Cizon yatsa ya yi azahiri yana fadin , "Ah Lallai lamarin yarinyar nan kara girmama yake a kullum wato makarantar ma sai ta ga damar zuwa har tana jin cewa tana da yancin kwanciya ta yi barci."

Yana karasa maganar ya daura kafar sa kan fuskarta yana dannawa.
Ji tayi numfashi na kokarin dauke mata hakan yasa ta bude ido tare da tashi a zabure.

Ya daka mata tsawa ta kara gigicewa tana rikeshi.
Riketa ya yi yana jijjigata ganin bata hayyacinta duk da hakan ya sake mata mari.
Take ta tsaya cak.
Sannan ya ce, "wato ke kin gama zama Mai taurin kai ko? Sai abun da kikeso zakiyi? Makarantar ma kin bar zuwa?"
Sai a lokacin tunaninta ya fara dawowa ta kalli agogon hannunta karfe goma harda mintuna.
Ba tare da ta ce masa komai ba tayi saurin shigewa Toilet ta yi alwala ta fito ta fara sallah.
Yana tsaye yana kallonta.
Har sai da ta idar kafin ya ce , "ki shirya maza yanzu ki fita,ban damu da inda zaki je ba,in kinso kije makarantar da kuma ki tafi wani yawon gantalinki nidai burina kije ki saida mun wa incen kwantan drugs din da kika dawo mun da su, sabanin hakan kuma daidai yake da kai rayuwarki ga barzahu." Yana fada ya fice.
Jakar drugs din ta janyo tana kallo a zuciyarta tana fadin, "yanzu ko naje School an riga an rufe get ba yadda za ayi a barni in shiga a kurarraren lokacin nan kuma ni ban san ina zani ba,banma san yadda za ayi in saida wa innan kayan mayen ba,kuma nasan babu shakka zai iya yi mun abun da bana zato kan wannan kayan, dolena na fita,dolena na je ko ina ne ma in nemo masa kudinsa yau kam."

Hakan yasa ta tashi ta dauki jakar ta fice, duk da cewa bata jin dadi amman fitar ta zame mata dole kuma ita kadai ce mafita gareta.

Tafiya kawai take ba tare da tasan ina ta nufa ba,kamar daga sama ta hango cincirindon wasu matasa maza suna ɗiban duwatsu irin fasassun nan suna kaiwa mota.
Ta karasa gun tana tare wani matashi,bayan ta gaisheshi ta ce, "Don Allah nima aikin nan nakeso zanyi abiyani,ina biyanku ake?"

Ya kalleta sama da kasa kafin ya ce, "e kwarai biyanmu ake,amman zaki iya? Akwai wahala fa ,ke kan ma kina mace me zai kaiki daukan dutse kuma yanayinki ma bai nuna na wahala ba."

Cikin raunanniyar fuska Deejerh ta ce, "zan iya wallahi, Don Allah kasa abani dama in kwashe nima ina da bukata please."
Saurayin ya ce, "shikenan ba matsala ki bi bayana."

Janta ya yi zuwa gun ogansu ya sheda masa cewa kanwarsa ce itama tana son aikin Don Allah ya taimaka mata tayi, Ogan ya amince amman sai binta yake da wani irin kallo.
Da aka bata damar diban duwatsun da sauri ta bar gun ta fara diɓa.
A cikin wani bucket mai fadi na karfe ake zubawa suna daurawa akai.
Haka ta karba tana tafiya da kyar tana jan kafa.
Da kyar ta kai na farko.
Na biyun tana dauka jiri ya dibeta ta daina gani Da ita da bucket din dukan suka fada cikin kwata.
Hankulan mutane suka yo kanta da kyar aka samu aka ciro ta ta kurje a gwiwa sai jini.
Mutanen wajen ne suka taimaka suka wanke mata.
Shugaban nasu ya kira gunsa yana fada mata, "kin ga daman irin wannan aikin ai ba na kyawawa irinku bane, akwai dai aikin da ya dace daku,in kinaso zakiyi ko nawa kikeso zan baki zakiyi?."

Deejerh ta ce, "E aikin mene ne? Zan yi."
Wani irin Murmushii ya yi kafin ya ce, "Yawwa Ashe za aje dake, amman ki shigo cikin nan kafin inyi miki bayani."
Ya karasa maganar yana mata nuni da cikin karamin office dinsa.
Ba ta kawo komai aranta ba,hakan yasa ta bi shi ta shige.
Tana shiga kuwa ya yi saurin rufe kofa.
Nan jikinta ya dau karkarwa murya na rawa ta ce, "me..me..meee... Zan yi.."
Hade bakinsa da nata ya yi yana tsotsa ita kuwa Deejerh sai nemsn hanyar kwatar kanta take,yana kara riketa.
Kasancewar doguwar rigace jikinta,ya daga rigar sama yana shafa mata mara, sannan shi ma ya zame wandonsa yana raɗa mata a kunne.
"Ki nutsu a hankali zan miki,ba zan ji miki ciwo ba kuma da mun kammala zan baki 20MXM a hannu nan take."

Deejerh ta ce, "Aa,aaa, Please bana so, bana so..kar ka mun Please."

"Ki nutsu ki bani hadin kai,kiji dadi inji dadi inko kika ƙi zan yi miki ta karfi."
Ganin cewa da gaske Deejerh bata da niyar tsawa yasa shi fara kokarin shigar ta da karfi.
Tana wuntsil-wuntsil ta yi galabar daukan wata karamar sanda kan ya ankare ta buga masa kan abun.
Bai san lokacin da ya saketa ba don a zaba take ya sume agun.
Ita kuwa a birkice ta fice daga office din tana gudu.
Sai da ta tabbatar tayi nisa da gun sannan ta tsaya tana hakki.
Zuciyar ta wasi-wasin ina zata yanzu kuma don dai har yanzu bata isa ta komawa Zayd gida ba tare da kudadensa ba.

Nan zazzaɓi ya kara dawo mata,bata da ko karfin ci gaba da tafiya bare gudu,ga garin ya haɗe da hadiri iska ta ko ina,ruwa ya fara sauka kamar da bakin kwarya kuma babu gun fakewa hakan yasa ta durkusa a gefen titin tana kankame jikinta.
Har sauti bakinta ke fiddawa na rawar ɗari.
Ta rufe idanunta ruwa na sauka akanta kamar da bakin kwarya..
Nawar na mota yazo zai wuceta kamar ance ya tsaya yana lekawa kuwa yaga Deejerh ce tsugune cikin wani hali.
Da sauri ya fito cikin motar ji ta yi kawai an dagata ta bude ido a zabure, Nawar ya ce, "kar ki ji tsoro nine,nutsu kinji."
Ya riketa yasa ta cikin motar sannan shi ma ya koma ciki.
Suna shiga ya cire rigarsa ya ya rufe mata jiki da shi.
Sannan ya dinga driving cikin sauri yana kallonta tana numfashi sama-sama har suka isa.
Da kanshi ya dauketa cak ya shigar cikin gidan
Ya bata wata doguwar jallabiyarsa ya fice.
Yadda ya fita haka ya dawo ta tarar da ita.
A karshe shi ya cire mata jakakkun kayan yasa mata jallabiyar sannan ya bata maganin zazzaɓi ya kwantar da ita.
Har aran shi bai taba jin yana kaunar wata yarinya kuma yana jin tausayinta ba irin Deejerh.
Zura mata idanu ya yi da ta samu barci yana ji aransa dama ciwon dake jikints ya dawo jikinsa.
Baifi barcin minti goma tayi ba ta farka kasancewar yunwar da take ji yanzu abu kadan ke tada mata da Ulcer.
Tana farkawa ya taba fuskarta yana, "mene ne? Ya jikin? Akwai abun da yake miki ciwo ne?"

Murya kasa-kasa Deejerh ta ce, "Yunwa."
Bai gane mai ta ce ba ya kara matsawa gareta yana, "Mene kika ce?"
Ta kara fadin, "Yunwa ina ji."
Tashi ya yi ya fita, can kuma ya dawo golden morn ya hada mata.
Da kanshi ya dagata ya jinginata jikin gadon sannan ya bata Golden morn din sai da ta shanye tas kafin ya ce , "kin koshi ko zaki kara?"
Ta girgiza masa kai tana fadin, "Thank you so much, Allah ya biya ma bukatunka na Alkairi."

Nawar ya ce, "kin manta ni abokinkine? Ai aboki na iya komai domin taimakon abokinsa amman ki fadamun me ya fito da ke cikin ruwan nan bayan kuma baki da lafiya?"

Deejerh ta yi shiru.
Nawar ya ce, "ehwen ki Fadamun ko Zayd dinne ya saki hakan?"
Yana kiran Zayd hantar cikinta ta kada tana sunkuyar da kai.

Nawar ya ce, "Mene ne? Shine ko? Ki fadamun Kinji abokai basa boyewa juna abu ."

Har cikin ranta tana son furtawa amman ko tayi kokarin hakan sai tana hango Zayd na tsara mata azaba.
Hakan yasa dole tai shiru tana jan numfashi.
Nawar ya rike mata hannu ya ce, "fadamun Kinji bai isa ya miki komai ba."
Cikin sarkakiyar murya Deejerh ta ce, "Kudi,in ban kai masa ba zai...zaiim.."
Nawar ya ce, "wani kudi? Kuma me zai miki?"
Ta ja numfashi kafin ta ce, "Aikena ya yi,kudin kuma ya ɓata,shine,shine..na ke tsoro."

Murmushii ya yi kafin ya ce, "Shikenan don kin zubar da kudi sai kina tsoron komawa gida ? Ki daina irin haka kinji zakiyiwa kanki illa kizo ki ta ciwo,kuma ni bana so na ga kina ciwo kinji ko?"
Ta girgiza kai.
Ya kara fadin, "Nawa ne kudin nasa kuma?"

Deejerh ta ce, "20Mxm."
Nawar bai ce komai ba,ya tashi ya je ya bude wardrobe dinsa ya cire 50mxm ya mika mata yana, "gashi nan, 50mxm ne ki bashi 20mxn dinsa sauran canjin kuma ki ajiye yanzu zan kirasa yazo ya dauke ki."

Deejerh ta ce , "amman karka ce na fada ma Ka ji Don Allah."
Nawar ya ce , "ki nutsu ki kwantar da hankalinki wai akwai wani abu da yake miki ne kike jin tsoronsa haka?"

Deejerh ta girgiza kai.
Nawar ya ce, "tom ni bana son tsoro kuma bana kawance da masu tsoro ina so ki zama mace mai kokari tare da jajircewa ki da kisa tsoron komai aranki ki fuskanci kowanni abu d karfin zuciyar ki ni Kawata jarumar mata ce ko?"
Ya fada yana kallonta.
Murmushii ta mai tana amsawa da eh.
Ya ce, "yanzu ni zan kaiki da kaina ba ma zan kirasa ba,ki tashi muje."
Ya karasa maganaar yana rike mata hannu.

Mota ya sata, ya nufi hanyar gidansu.
Suna isa ya bude mota kenan sai ga Momynta da Dadynta.
Shi ma zayd ya fito daga gidan kenan.....

08103080717
Comments and share fisabillahi
[12/12, 11:02 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-22

Juyawar da Zayd zaiyi idonsa suka ci karo da Deejerh tare da Nawar,kan ya farga gefe ma ya hango Momyn Deejerh da Daddynta.
Take ya razana zuciyarsa ta bugawa cikin sauri,hakan yasa shi saurin komawa gefe yana ajiyar zuciya ba tare da ya bari sun hangesa ba.

Dadyn Deejerh da Momynta ma suna ganin Nawar jikinsu ya fara rawa, alamar tsoro ya bayyana karara a fuskar su, domin sun saba jin labarinsa da ganinsa a tv amman basu taba ganinsa a zahiri ba gashi kuma yau shine a gabansu har gida.
Kokarin shigewa gida zasu yi cikin sauri Nawar ya daga masu hannu yana rike hannun Deejerh suka karasa gabansu.
, "mu karasa in gaida su sai in tafi ko."
Deejerh ta ce, "Tom." Ta ce kawai.

Su kuwa jiki ban da ɓari babu abun da yake har jijiyoyin wuyansu saida suka fito.

Da fara'arsa ya mikawa Dadynta hannu suka gaisa, momynta ma suka gaisa sannan ya ce, "ashe bakwa ma gidan,ni abokin Zayd ne kuma ya kan kai Deejerh mu gaisa wani lokacin, sannan dazu ganin ta nayi wai Zayd ya aikata kuma ruwan sama ya barke shine na rakota gida."

A tsorace Dadynta ya mika masa hannun ya ce, "Ayyah Ma Sha Allah sannu da kokari an gode sosai."
Ita kuwa momynta ta ma gagara magana binsa kawai take da kallo.

Nawar na kokarin tafiya yasa hannu a aljihu ya ciro 5mxm yana mika masu.
Da saurin Dadyn Deejerh ya ce, "Aa aa wallahi mun gode Allah saka da Alkairi "
Caraf Momynta ta cafe kudin tana, "umm umm an gode sosai Allah saka da Alkairi,daman daman aiko kamar kasan ba lafiya gareta ba munata zaryan asibiti an gode."

Binta da kallo Nawar ya tsaya yi kawai ya kasa fadin komai,
Ita kuwa ta sunkuyar da kai har cikin ranta tsoron shi take ji amman baza ta iya bari tana kallo wannan makudan kudaden su wuceta ba.
kallon Deejerh ya yi ya mata Murmushi yana mata Bye-bye.

Ya tafi.
Suna shiga gidan Zayd ya yi kamar bai san da dawowarsu ba ya fito daga dakina yana, Ah welcome, Daughter kema kin dawo? Ya akayi kika dade haka?"
Deejerh ta kallesa ta kawar da kai kawai ta karasa gabansa ta mika masa kudin sannan ta wuce dakinta ba tare da ta ce masa ufan ba.

A kullum kara basa mamaki take yadda yanayinta ke kara sauyawa, ganin Dadynta na kallonsa sai ya fara kakalo dariyar dole yana sosa ƙeya ya ce, "Daughter yau yan miskilancin na kusa kenan ba ma magana zaki zo ki sameni ai zamu gamu ne."
Ya karasa yana kara kakulo dariyar da bata kai ciki ba.
★★
Bayan Momynta tayi wanka kitchen ta wuce ta fara hada masu Dinner.
CHICKEN MOLE take wanda ya kasance fevorite food din Dadyn Deejerh.
Ga yadda ta fara
Ingredients
1 tbsp. olive oil
1 large onion, chopped
3 cloves garlic, finely chopped
2 tsp. chili powder
1 c. prepared salsa
1 c. chicken broth
1/2 c. Homemade Nutella
2 lb. assorted dark-meat chicken pieces, skin removed
Kosher salt
Cooked yellow rice, for serving
Sesame seeds and sliced scallions, for sprinkling

Directions
Step 1
Heat oil in a Dutch oven on medium. Add onion, garlic and chili powder and cook until softened, stirring often, about 7 minutes.
Step 2
Stir in salsa and chicken broth, then whisk in Homemade Nutella.
Step 3
Season chicken with 1/2 teaspoon salt and add to the pot. Simmer until chicken is tender and cooked through, about 30 minutes. Serve with yellow rice, sprinkled with sesame seeds and scallions if desired.

Bayan ta kammala ta koma ta sake yin wanka tayi sallah suma duka suka yi sallah.
Sannan ta jera masu abincin akan dining ta je ta kira kowa kamar yadda suka saba.
Deejerh kam ba wata yunwa take ji ba hakan yasa ta diba kadan,kadan dinma ta gagara cinyewa kamar an mintsineta ta tashi ta wuce daki.
Dukansu suka fita da kallo.

tana shiga Dakin kanta ya fara juya mata, tasa hannayenta aka, babu abun da idanunta ke ayyana mata sai dazu data kasance cikin wannan ruwan yana dukanta, take idanunta suka canja kala zuwa jajir, kwalwalarta ta gagara samun sukuni, da karfi ta rufe idanun da tunanin cewa ko zata daina ganinta cikin wannan halin amman ina kamar tana kara tura idannunta da kwakwalwarta kan kara tunatar da ita ne.
Wata kara ta sake.
Suna jin hakan Dukansu suka dunguma zuwa dakin nata.
Gabadaya ta fice a hayyacinta bayan kofar dakin ta shige tana kara kankame kanta ta tsuguna, da kyar ta samu ta fara karanto, "ALLAHUMMA RAHMATAKA ARJU,FALA TAKILNI ILA NAFSI DHARFATA AININ,WA ASLIH LI SHA'ANI KULLAHU,LÃ ILAHA ILLA ANTA."
Addu'a ce ta yaye damuwa da kuncin rayuwa.

Zayd ne ya fara zuwa yana rike ta ya ce, "Daughter mene ne? Mene ne ya faru?"
Dadyn ta ma ya ce, "Me ne ne baki da lafiya ne? Anya babu wani abu boyayye dake damun yarinyar nan?"
Ya fada yana kallon momynta.
Ta ce, "Gaskiya nima na lura kamar ta fara samun matsala kam."

Zayd ya katse su da fadin, "karku damu kuje ku ci abincinku zan ji da ita in sha Allah."

Ba tare da sun masa musu ba kuwa dukan su suka fita.
Suna fita ya kalleta ya ce, "munafuka, duk abunki na so ki tona mun asiri saidai ki tonawa kanki ko ince in kika je lahira kya tona, yanzu zan fita nima kuma Anjima inna dawo ban tarar kin dawo daidai ba sai kinga abun da zan miki."
Ya fita daga dakin.
Yana fita ta kara komawa bayan kofar tana kara rike kanta
Addu'ar ta ci gaba da yi
Tana tayi tana maimaitawa kuwa cikin ikon Allah can sai gashi ta fara samun kanta, tana jin ta fara dawowa daidai wani gigitaccen barci ya fara kawo mata hari.
A wajen ta sulale sai barci.

Can dare Zayd ya shiga dakin ya dinga bincike idanunsa bai sa ya ganta ba, cikin bacin rai ya ce, "Ah Lallai wuyan yar nan ya yi kwari kam gantalin nata har cikin dare wato fita take? Akwai rabon ina daf da balla mata kafa inga kafar fitar matsiyaciyar yarinya kawai." Ya gama sambatunsa ya fice yana huci.
Har wajen gidan ya duddubata amman bai ga ko alamarta ba bare Itan.

Daga karshe haka ya hakura ya koma dakinsa ya kwanta.

Karfe ukun dare daidai ta farka,ta tashi tayo alwala tayi alwala ta zauna kan sallaya kasancewar tana period bata sallah ta yi istigfari sosai sannan ta dunga karanta Amanar-rasulu sai da tayi Sosai bayan ta yi ma ta karanta fatiha sannan tayi salatin Annabi ta nemi gafarar Ubangiji ta nemawa Iyayenta tare da al'umma wa inda suke raye da wa inda suka bar duniya sannan ta kara daga hannun ta sama tana hawaye ta ce, "Ya Ubangiji na ya Allah ka kara mun kwarin gwiwar fuskantar kowanni kalubale da jarabawar da zaka mun a rayuwa, Ubangiji na ina rokon ka Allah kasa kada na taba karaya ko fidda rai da rahamar ka komin tsananin rayuwa.Rabbie ka kawo mini mafita mafi Alkairi a gareni wacce zata zam silar ingatar rayuwata da cirota cikin duhu, Allah na tuba ka yafeni."
Ta karasa tana share hawayen dake fuskar ta hanyar shafa addu'ar.

Tana shafawa ta haye kan gado ta fara barcinta cikin kwanciyar hankali.


Da safe Momynta na gama hada breakfast kafin su fita ta shiga Dakin Deejerh domin dubata ganin yanayin da take jiya.
Abin mamakin shine kalau ta ga Deejerh har tayi wanka ta shirya tasa Uniform dinta na school.

"Good Morning Momy." Deejerh ta fada a gajarce.
Momynta ta ce, "Morning na gama kalaunki ashe Ma Sha Allah,yanzu zamu tafi office ga breakfast din ki cen dana Uncle dinki in kinci Kya tafi School."

Kafin Deejerh ta bude baki tayi magana har ta fice ba tare da tunanin cewa ko tana da wata matsalar da zata iya fada ba.
Tana ficewa kuwa Zayd ya fito kamar an hankadoshi.

Tana ganin sa ta fara jan jiki tana baya.
Yana binta.
Wuyanta ya shake ya turata jikin bangon.
Yana kokarin sheƙeta ta kauce masa.
Cikin Fushi ya ce, "Ina kika je daren jiya? Sannan uban wa ya baki izinin zuwa gun Oga Nawar jiya? Zuwa kika yi kika ce masa ni na turaki samo kudi ko?"

A tsorace ta ce, "Wallahi ban je ko ina ba,kuma jiya ganina ya yi,na ...na..."

Ya kara matsawa zai damkota yana, "kika me?"

"A hanya,a hanya ya ganni nace na yarda ma kudine,shine... shine..ya...ya bani in baka."

Tsaki ya yi ya ce , "Koma miye bai dameni ba,amman kisa aranki muddin naji ya ce mun wani abu daban zan dauki mummunan mataki akanki, kuma ki tabbatar kin dauki drugs dinnan kin saida mun su in ko baki saidai ba kika dawo dasu sai kin shanye su tas."

Deejerh ta ce, "Uncle wallahi basa siya an hana kaiwa kuma an hana sha ko na kai baza su siya ba."

Wani mummunan kallo ya bita da shi kafin ya ce, "Au nufinki inyi ta asara kenan? Iye? To ko saidai in yau ba zaki School din ba ki dauka ki daura aka kije ki saida mun ki dawo mun da kudadena."

Cikin karfin hali Deejerh ta ce, "Uncle Allah basa siya ko na fita ban san inda zan kai ba."

Wata tsawa da ya sake mata saida ta razana.
Ya ce, "ki dauka ki ficemun da gani tun kafin inyi gunduwa gunduwa dake." Yana fada ya fice adakin.
Daukan jakar tayi ta na jan zuciya taje dining da sauri sauri ta dunga tura abincin tana cikin ci sai ga shi ya kara fitowa yana fadin, "inna karaso wajen nan baki fice mun da gani ba sai na ballaki."
Kallonsa tayi kawai ta dauki jakar ta fice ba tare da ta ce masa komai ba.

School dinsu ta nufa kai tsaye ta fara zuwa office din Roman.
Yana ganinta kuwa ya tashi yana fadin, "lafiya kuwa?"
Bata ce komai ba kawai ta bude jakarta tana nuna masa.
Roman ya ce, "na mene ne?"
"Cewa ya yi saina saida na bashi kudin." Tana fadan hakan ta yi shiru.

Roman ya ce, "shi wa? Me yasa zai baki ya ce sai kin saida?"
Shiru tayi ta sunkuyar da kanta.

Ya kada kansa kawai ya dauki jakar yaje ya zuba duka drugs din a kwalbet sannan ya dawo ya ce mata, "ki tafi class in an tashi zan baki kudin, amman karki kara gigin karban wannan abun koma agun waye, ki san matakin da za ki iya karw kanki a ko ina cikin sauki ba tare da samun nasara ba."
Ta girgiza masa kai sannan ta wuce aji.

Lokacin tashi na yi Roman ya bata kudin kamar yadda ya fada sannan ta dauki hanyar gida.
Tana cikin tafiya kamar ance ta daga idonta kawai ta ga kamar an dire mata mutum gaba.
Ta.....
[12/13, 10:33 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-23

Tana daga kanta ta ga Zayd tsaye yana zare mata idanu tare da mika mata hannu.
"Bani kudadena."
Yana fada ta sa hannu cikin jaka ta mika masa kudin.
Har ransa bai so ba,domin hasashensa ta ce babu ne ya yi mata abun da ya ga dama.

Ya ce, "to wuce mu tafi guzumar munafuka daman nazo ne in tabbatar da cewa kinzo School din ko kuwa naki yawon barikin kika tafi,ban ma yarda dake da wannan Teachern naki ba, dole akwai wata kullalliya tsakaninku, ke da ma kika ce ba a siyan drugs din taya kika samu kudi in ba wai bashi kanki kika yi ba? Zan yi maganinku kuwa daga ke har shi tunda ku kananun yan iska ne."

Deejerh kam bata ce masa komai ba ya hankada keyarta gaba yana binta a baya da kafa har suka isa gidan.
Suna isa kafin ya ankare,da gudu ta shige dakinta tasa key ta kulle kofar windownta ma ta kulle.
Cikin bacin rai ya dunga jijjiga mata kofar yana kiran sunanta.
Tun tana jin karar sautinsa har ta gaji ta dau earphone dinta tana sauraren karatu ta daina jiyo sautin sa.
Ganin bata da alamar budewa dole ya hakura ya tafi dakinsa cike da takaici don aranshi ya gama shirya irin muguntar da zaiyi mata kenan.
Tunda ta shiga dakin bata bude ha har safiya.

★★★
Tana tashi ta fice sim sim ba tare da sanin kowa ba , Hopeful Endeavors ta wuce kasancewar yaune ranar da za a kaddaramar da taron su na gargajiya.

Tana zuwa aka bata rigar da tayi Designing nata,tayi

Please Login or Register in order to submit comment