Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

from herbs, cannabis, and disinfectants. The popularity of this drug has surged in recent times due to its euphoric effects. However, this became a menace when it was found that adding human bones to this concoction made it even more effective, which might be because of the sulphur content in human bones, kuma shi drug din yanzu yawanci matasa daga shekara 18 zuwa 25 suka fi ta ammali da shi, and yana causes people to fall asleep while walking, to fall over, to bang their heads against hard surfaces and to walk into moving traffic."

Haiydar ya ce, "kwarai ma kuwa kuma The highly addictive mix of marijuana, fentanyl and tramadol has caused hundreds of deaths and psychiatrically damaged scores of users."

Zahra ta bude baki tana, "ah lallai wannan masifa ce mai girma akwai bukatar adau mataki akai sosai musamman jami'an tsaro wannan aikine a gare su domin yin kokari wajen tabbatar da dakilewar hakan."

Khalil ya ce, "eheen kar ku manta yaune ranar karshe sanarwar da muka fidda na tallafin wannan shekarar akwai bukatar mu fara duba sakwanin mutane domin duba wa inda suka cancanta ko da zuwa dare ne."

Deejerh ta ce, "e zai fi gaskiya zuwa daren ma."

★★★★Huda na kwance raɗe-raɗe suna tafka badalarsu.
Zaid ya shiga dakin da sauri baiyi tunanin mutumin nata na ciki ba.
Yana ganinsu wani takaici ya tokareshi a zuciya ji yake kamar yaje ya fisgeta ya masa duka, amman ina ba dama da yaje zai iya jawa kan shi masifar da bazai iya dauka ba agun Huda.

Har zai fita ta kwalla masa kira.
"Zaid... Wait..."
Ta tashi a yadda take tsirara cikin najasa ta karasa gabansa ta dauki hannunsa tasa a cikinta.
"Ya kamata ka fara shiri fa domin jiya naje Hospital na karbo scaning din da nayi kuma an tabbatar da cewa ina da ciki."
Shafa hannun nasa take a cikin ta ci gaba da magana, "ka ga aikin mazaje ko? Shi yasa nace ma tunda kai ka kasa gwanda abawa wasu dama And kuma ka ga result?"

Cikin tsawa ya furta, "Stop... Yana dakatar da ita da hannun shi.
Kafin ya ce, "na bar ki kina abun da kike so, kar kuma ya kan ya zama lagon da zakiyi tunanin zaki iya fada mun komai ki mun komai,ina jure abubuwan nan naki da daliline fa, so Please kar ki kaini bango."
Yana karasa fada ya fisge hannunshi ya fice cikin sauri rai bace.

Yana fita ita kuwa ko a jikinta tayi tsaki sannan ta koma ta ci gaba da abun da ke gabanta.

Shi kuwa ya tafi office yana sauri Domin an tabbatar masa da cewa Kush din da ya yi saffara sun iso.

★★★★Asher na zaune gefen Xavier ya yi shiru hannunsa na baki,kansa a karkace.
Deejerh ta kalleshi ta ce, "Freind yau ba wasa ne? Kuma ba za ka kulani ba?"
Bai ce mata komai ba.
Ta mika masa hannu
Shi ma ya mika mata nasa daga sa tayi gaba-daya ta zaunar da shi kusa da ita kafin ta ce, "me kake so."
Ya girgiza mata kai alamar ba komai.

"Alright, to ka rufe ido muyi wasa."
Ya rufe idanunsa ya bude suna wasa da hannayensu.
Sauran kuma sunata hira palourn ya cika da hayaniya kowa suna yin nasu.
Gashi shi kuma Asher babu abun da ya tsana irin hayaniya.
Tsayawa ya yi da wasan ya bata rai.
Deejerh ta ce, "What Wrong?"

Ya rufe idanunsa gam yana kamewa ba tare da ko motsawa ba.
Jin surutan nasu yake har cikin ransa da ya kasa hakuri yasa hannuwansa a kunne yana sakin wata gigitacciyar ƙara, jikinsa ban da rawa babu abun da yake nan take fatar jikinsa ya canja kala ya yi jajir.
Jin sautin ihunsa yasa duka suka koma gare shi.
Cike da mamaki da tunanin me ya faru.
Xavier ya ce, "Asher...stop... I said stop."
Yana fada kamar yana kara tunxura shi karshe ma ya bige masa hannunsa a jikinsa.

Yana ci gaba da karar cikin wani yanayi, Deejerh ce ta kara binsa ta riko mishi hannu tana sakin numfashi a hankali can shi ma sai ya fara har ya yi shiru da karar.
Yana yin shiru da gudu ya shige daki ya turo kofa.

Zeeyter ta ce, " Spectrum Disoder, Yaron nan na bukatar kulawa sosai fa."

Zahra ta ce, "gaskiya don na lura yanayin na shin ba mai son mutane bane kuma baya son hayaniya, So Noor, Anitha,Anuska ku kiyaye a dunga magana cikin nutsuwa kuma kuna jan shi wasa cikinku."

"In sha Allah Mom."
Dukan su suka fada.

Kin bude kofar ya yi duk bugawan da Suka yi.
Karshe Deejerh ta ce kowa yaje ya zauna zata yi magana da shi.

Windown dakin da ke ta waje ta bi ta sa fuskarta ciki tana kiran sunan shi a hankali.
"Asher .... Asher...Asherr... Kamar ba zai juya ya kalleta ba sai kuma ya daga kai yana juyawa a hankali.

Hannayenta tasa a fuska tana masa fuskar dodon wasa haka tana dariya.
Shi ma bai san lokacin da ya fara dariyan ba ya karasa daidai jikin windown shi ma ya maida fuskarshi yadda ta mai da tata suna kallon juna suna dariya.
Kusan Minti Uku suna haka kafin Deejerh ta ja dogon numfashi , shi ma din ya ja.
Ta......
[4/29, 8:20 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-52

Ta ce, "Oya Smile Handsome Guy."
Washe bakinsa ya yi yana binta da kallo.

Deejerh ta ce, "Gud Boy,." Sai kuma ta shagwabe fuska ta ci gaba da magana, "yanzu zaka bude mun in shigo sai mu ci abinci mu ci gaba da wasan mu?"
Ya girgiza kai alamar e.
Ta ce, "yawwa tom bude mun Freind."

Tashi ya yi yaje ya bude mata,yana budewan ya buya a bayan kofar, yayi irin karar nan wai zai razanar da ita, pretending tayi ta razana don yaji dadi kawai aiko ya kara shekewa da dariya.

Jan shi tayi ta zaunar da shi akan gadon kafin ta ce, "tom ka jirani yanzu zan dawo."

Ya girgiza kai.
Fita tayi taje kitchen ta dibo masu abinci sannan ta koma dakin.
A baki take basa, shima ya ce sai ya bata a baki.
Yana bata, ta tafa masa suna dariya.
Bayan sun gama ci tayi masa wanka ta canja masa kaya, dai-dai lokacin shan maganin sa ya yi ta bashi,yana sha kuwa ya yi barci.

Bayan ta koma palourn Xavier ke sanar mata lokacin shan maganin sa ya yi.
Deejerh tace masa ai ta riga ta bashi har ma ya ya barci.
Dadi Xavier yaji sosai yana fadin, "Thank You Ma'am."

Deejerh ta ce, "Anytime."

Tana zama Noor da su Anitha suka tawo da sauri suna kallonta ita da zahra, Noor ya ce, "Mom me yake damunshi? Me yasa kuka ce mu yi shiru?"

Zahra ta ce, "Autism spectrum disorder (ASD) Cuta ce wacce take hana mutum mu'amula da mutane yadda ya dace, wasu basa ma iya zama cikin mutane sun fi son su ta zaman kadaice,wasu basa son magana da hayaniya yanayinsu dai yawanci zaku gansu a takure kamar yadda Asher yake haka kuma yana developmental disability caused by differences in the brain. Some people with ASD have a known difference, such as a genetic condition. Other causes are not yet known. Scientists believe there are multiple causes of ASD that act together to change the most common ways people develop."

Anitha ta ce, "to shi kenan ba zai ji sauki ba ya dawo kamar mu?"

Zeeyter ta ce, "batun sauki gaskiya yana da wahala,sai dai kawai a daura shi akan magani domin kiyaye lafiyarsa da bashi kulawa ta mussaman and kuma akwai abun mamaki da ke faruwa da irin wa innan masu lalurar yawancin su suna da baiwa ta daban
Kuma The can be whatever the want in life amman yanayinsune kawai dole su kasance cikin shan magani da samun kulawa, cikinsu ana professors har ma da Lawyers they are always the best at what they do, because they think outside the box.


Anuska ta ce, "to me suka fi so tunda ance basa son hayaniya?"

Nan ne Deejerh ta yi magana ta ce, "safety, acceptance and a sense of competence, Ba aso ana kyamatarsu hakan ma sam baya da kyau, domin hakan daga Ubangijine, sannan suna kokarin rayuwa da yanayinsu, wanda hakan abu ne mai kyau shiyasa ba aso ana masu kallon kaskanta ko wani nakaso,kuma suna iya magance matsalolin da lafiyayyun mutane ma basa iyawa, zasu iya kirkiran abun da zato bai taba zata ba na ban mamaki domin tunaninsu na musamman ne ba irin na kowa ba,wanda hakan har wasun su sukan iya zama masu karfafa gwiwa ga al'umma da furucinsu that is Motivational speakers, kamar misali Elon Musk ma da ya kasance mai kudin duniya da muka hada partnership da shi na 5stars Austism Victim Yana da Asperger's syndrome kuma yana da yaro ma mai fama da lalurar kun ga kenan sukan iya zama komai har abun da ba a hasashe ma, don haka yanayinsu ba abun ace za ana tausays masu don yanayin da Allah ya yi su bane, suna so ana mu'amula da su kamar kowa, a ja su a jiki,kada a tsangwamesu kuma ka da a kyaresu a nuna masu soyayya da cewa suma kamar kowa suke a kowanni yanayi Ubangiji ya hallarci mutum ka da ya yi tunanin cewar ba zai iya maida mafarkinsa gaskiya ba tunda ga misalin wani professor yana yaro ya yi fama da Austism sai da ya shekara sha daya kafin ya fara iya magana, rubutu kuwa sai da ya shekara sha biyar kuma duk hakan bai sa shi ko iyayensa sun karaya ba, sun daukeshi tamkar yadda kowani mutum yake sun jajirce sun tsaya masa ya rayu kamar kowa wanda a karshe ga shi ya shiga sahun manyan professors wannan shine Rayuwa, kuma akwai doctors sosai masu ɗauke da lalurar sannan basa karya,yana da matukar wahala a garesu suyi karya komai nasu a bude yake gaskiya da gaskiya."


Anitha ta ce , "Thank You Anty ni kam daga yau ya zama abokina kuma ba zan dunga masa abun da baya so ba."

Anuska da Noor ma suka hada baki da fadin, "In sha Allah.

★★★Dare
Gabadaya 5stars sun hadu suna duba bayanan masu neman jari da suka turo.

Wani jawabine ya tafi da Hankalin Deejerh
Yadda wata matashiyar yar kasuwa ta tsara yadda zata iya sarrafa jarin dubu shida ta hanyar yin alawar madara.
Gullisuwa.
Madara Gwangwani Uku
2,100
Sugar Gwangwani daya
400
Mangyada Gwangwani biyu
800
Ledar packaging
400
Flavour
200
Robar sawa
500
Coal/kerosine
600

Total-5000


Deejerh ta yi mamaki sosai ganin yadda mace matashiyar budurwa ta yi kokarin sarrafa karamin kudi haka cikin karamin lokaci.
Ta ce, "Hi Guys,kun ga abun da na gani kuwa? Wata kawai 5k take bukata domin yin jari."

Farouk ya ce, "Yes nima dai nayi mamaki yanzu nake dubawa,hakan kuma mai yiwuwa ne?"

Zahra ta ce, "bara in duba ingani."
Khalil da Haiydar ma dubawa suka shiga yi.
Bayan Zahra ta duba ta ce, "Sosai ma zai yiwu indai a yadda ta tsaran ne ba tare da an samu wata tangarda ba."

Deejerh ta ce, "to why not daga wannan shekarar mu fidda sabon tsarin bada sadakan karamin tallafi d ga mutane Dari mata matasa da ke sha'awar yin sana'a kamar hakan? Da nufin cewa zamu basu wata shida mu ga yadda lamarin zai tafi indai ya ingata zamu san yin abun da ya dace sai kuma muyi yadda muka saba na duba wa inda za muyi partnership da su daban."

Farouk ya ce, "correct our best Fashion designer dadina ds ke wani lokacin akwai tunani mai kyau da hangen nesa, kin ga musamman mata da ke gida da basu samun damar fita kinga ko a gida irin wannan sana'ar ana samu dama yan mata da ke makaranta ko da can suke kaiwa suna saidawa zasuna iya daukewa kansu wani nauyin musamman yanayin makaranta da ke jan kudi sosai."

Khalil ya ce , "Gaskiya ne wannan hanya ce mai kyau da zamu gwada inda rabo za adace, ina ganin fidda wata sanarwan za ayi ko kuma ince mu bincika da kanmu a samo irin wa innan matan da suke da matukar bukata sai a basu."

Haiydar ya ce, "gaskiya ko nima 100% ina bayan wannan shawarar domin hakan ya yi kuma ya birge tamkar zaburarwa ce zamuyi ga al'umma kan cewa ba sai lallai da kudi mai yawa ake iya taimako a canja rayuwar dan Adam ba, da ƙalilan din kudi ma kan iya haskaka rayuwar al'umma da dama ya ciro su daga duhu i zuwa haske har ma suma wataran su iya zamtowa hasken ga al'ummar dake gare su."

Khalil ya ce, "Alright wannan aikin naku ne, Deejerh , Zahra And Zeeyter mussaman oganniya Yel na san zata shiga lungu da sako ta lalubo mana irinsu,a fara a accepting wannan ta farkon kafin a samo sauran mutanen amman target dinmu zai zama A Undeveloped Countries ne, kamar Nigeria,Chadi,niger,Indonesiya, Thailand, Malaysia "
Dukansu suka amsa da "Noted In Sha Allah Sir."


"zamu iya ci gaba da duban partnership din mu yau ko a bari sai gobe? Ni dai na fara jin barci kuma kun san lamarin nan na bukatar nutsuwa." Khalil ya fada yana duba agogo

Zahra ce ta galla masa harara.
Ya yi murmushi yana, "Sorry Madam Freeya."

Haiydar ya ce, "nima fa na matsu in jini jikin matata mu bari gobe a ci gaba tunda dai yau mun bige da wani sabon lamarin."

Tashi Farouk ya yi yana, "Nima Babies dina na jirana don naga alamar yanzu kullum so kuke kuna bata mini rai, don haka inna tashi mata hudu zanyi at once."

Dariya suka yi duka, kafin suka yi bankwana kowa ya tafi dakinsa.

[5/13, 7:08 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-53

★★★
Gabadayansu sun shirya tsaf zasu fita ganin gari suna zaune a babban palourn suna jiran Ammar shi kadai ne bai gama ba.
Haiydar na nanike da Zeeyter da Aiza.
Farouk kuwa ya sa su a gaba da tsokana.
Dariya zeeyter ta yi ta ce, "wato ku kun fi so ana yin aure shikenan soyayya ta kare ko? Sai dai ata cewa zaman hakuri ake, to ni kam ba haka nake ba, aure ai shine tushen soyayya , a lokacin da mace ta yi aure a lokacin ya kamata ta zage dantse ta gyara zama wajen nuna soyayya da bawa mijinta kulawa ta mussaman ta yadda duk inda yake zuciyarsa na gunta, ba wai fa ba a samun sabanin bane, ana samu kuma ana hakurin amman ka da a maida hakurin cin ciyawar tinkiya kuma,komai bisa tsari da mutunta kai."

Xavier ya ce, "Gaskiya ne,ni kaina na dauke wani darasi zamana da ku, ke da Haiydar,Zahra da Khalil, musamman su da ya kasance ma sun tara yara da yawa hakan bai sa sunji cewa kawai rayuwa suke ta domin yaran na su ba, ni ina ga fa in zan yi aure kawo matata cikinku zan yi kuna yi mata lectures."

Farouk ne ya katse shi da fadin, "Abun da duk ni na masu training na koya masu yadda ake love din,ni nan zaka kama ka ga jawaban soyayya da rike Aure."

Deejerh ta ce, "tab ashe kuwa da Auren bai zaunu ba indai kaine."
Duka suka kyalkyale da dariya, kafin Khalil ya ce, "Gaskiya ko ana daukan rayuwar aure wani abu na daban, ana sawa mutane tsoronsa a zuciya tun kafin shigarsu bayan kuma kowanni Dan Adam shi ke ginawa kan shi rayuwar da ya so kuma ta dace da shi, A duk inda zan kasance a halin yanzu ba zan ji shakkar nuna cewa matata ita ce karfina ba." Ya fada yana kallon Zahra.
Murmushi kawai ta yi masa.

Ya ci gaba da fadin, "Yawancin nasarorin da namiji kan iya samu a rayuwa mace ce kashin bayinsa muddin ka yi dacen samun mace ta gari a bokiyar rayuwa to Ubangiji ya gama yi ma komai domin rayuwar namiji na tafiya ne da rayuwar matarshi sukan zama abu guda a inuwa guda, ya yin da kuwa akai rashin dace akan iya haifan Ɗa mara ido wanda ba ma fata ma."

Yana karasa fada Ammar ya fito.
Farouk ya ce, "Oya lets go don wannan bayanan masu auren na ku ba mai karewa bane."

Suka tashi duka suka fita, sun sha yawo sosai kafin suka koma gida, suna komawa kowa ya ya wanka ganin suna kokarin bajewa kowa ya yi daki Zahra ta katse masu hanzari da fadin, "ba fa tafiya zakuyi ba, bamu da wadataccen lokaci yanata tafiya ya kamata mu waiwayi masu tallafin nan mu ga wake da rabo a wannan shekarar tunda wancen Budget din mun kammala tsara shi wannan dinma ayi a gama."

Farouk ya ce, "da gaskiyar ki Madam ya kamata mu san matsaya a yanzu bara in dauko system mu fara dubawa."

Gabadayansu kowa system dinsa ya sa a gaba suka shiga aiki.

Farouk ne ya fara magana, "Ma Sha Allah kun ga wani business Plan kuwa? Ni dai in so samu wannan ce ke da rabo ta san kan aiki da tsarinsa."

Zahra ta ce, "The Stitchery dinnan ko?"

Farouk ya ce, "Yess ashe kin gani yar guntuwa."
Dukan su shiru suka yi na yan mintuna suna ci gaba da dubawa kafin Khalil ya yi gyaran murya da fadin.
"Wani company ne zabinku?"
Har suna hada baki a tare duka suka ce , "THE STITCHERY."

Murmushi ya yi kafin ya ce, "Gaskiya nima shine zabina, yanayin abubuwan nata sun birgeni kuma in ta samu tallafi abun zaiyi kyau sosai musamman yadda bata yi dogon burin Capital mai yawa ba."

Company Name:The Stitchery
Location: Australia
Business type:Baby Clothing production and sales.
Capital:$50,000
Mission: Provide high-quality, comfortable ans affordable baby clothing for parents who value style and sustainability.

Product/service: The primary focus is on munafacturing and selling baby clothing, including onesies sleepers,bibs, Hats,and more.

Unique selling proposition:Focus on organic materials eco-friendly manufacturing and contemporary design.

Target: Parent, grandparents,and gift-givers for infants and toddlers.

Business structure:sole proprietorship (chose based on your legal need and future growth plans)

Kara karanta masu duka Farouk ya yi kafin ya ce, "an gama da first step zamu tattauna da su,amman kafin nan ya kuke ganin zamu tafiyar da tsarin?"

Deejerh ta ce, "ina da shawara."

Dukansu suka maida hankalinsu ga Deejerh
Ta ci gaba da fadin, "Wannan karan Charity dinmu zai zama ne wa yara kanana kamar yadda kamfanin yake na abubuwa ne da suka shafi yara,in mun basu tallafi to zai kasance duk Shekara a abun da zasu cire mana zai zama kayan yara ne guda dari, mutane hamsin akai gisan marayu murane hamsin kuma a nemi yara marasa galihu ko irin wa inda dai iyayensu suka gaza a raba masu ina tunanin kamar hakan ma wata hanya ce mai inganci da zamu iya sanya murmushi a fuskar kananun yara."

Farouk ne ya fara tafa mata yana, "Dadina dake duk munin ki duk da cewa na fiki kyau amman kina da kaifin basiri da tunani hakan ya burgeni nidai gaskiya ban sani ba ko ku."

Sai a lokacin Haiydar ya yi magana, "100% nima ina bayan tsarin nan ko ba komai ai mun samu ci gaba ne, yadda nan gaba ma zamu so tunani fiye da hakan ya zo."

Take Farouk ya yi accepting business plan din sannan ya yi wa kamfanin sako ta email.

Bayan ya gama ya ce, "yawwa na fidda list din gabadaya yadda tsarin mu ya kasance a Yel da Freeya wanda a yanzu haka muna da komanin $100000 wanda ya shiga cikin asusunmu sannan munyi magana ma elon musk komai na tafiya daidai zamu iya jin shigowar kudi a kowanni lokaci."

Khalil ya ce, "hakan ya yi kyai sosai ina matuƙar jin daɗin yadda kake ƙoƙarin tsayawa kai da fata wajen tabbatar da komai ya tafi daidai duk da cewa kai gauro ne."

Haiydar ne ya katse khalil da fadin, "Shiyasa nake so ai muyi karo karo mu nemo masa wata yar mai sauki koda yar kauyace dai su rufawa juna asiri."

Dariya Khalil, Zahra da Deejerh suka fara harda shidewa.
Farouk kuwa kicin kicin ya bata rai yana, "Ai ba neman kai da kaina nake ba, sanin kanku ne duk na fiku farin jini,ni da mata ma suke bina ina gudu."
Lokacin Zeeyter ta shigo palourn dauke da drinks tana rabawa kowa.
Ta ce, "ya na ji anata dariya?"

Farouk ya ce, "wallahi mutanen nan sun gama rainani amman ba laifinsu bane wai ni ne zasu hada kudi su mun aure kumama auren da yar kauye?"

Zare ido zeeyter ta yi tana, "What? Wuce nan wallahi kai da mata ke bi har za a kawo ma wani wargi? Ka rabu da su duk cikin hassadar basu da farin jini irin naka ne, And kuma mata In sha Allah zasu ganta ta gani a fada zamu zaba."

Murmushi ya yi yana, "Yes Gimbiyata duk kin fisu hankali shiyasa nake ji dake."

Deejerh ta ce, "Excuse Freinds bara inje muyi sallama da Maam da Ammar zasu koma na san yanzu sun kammala shiri 2 jirginsu zai tashi."

★★Bayan ta fita Khalil ya ce, "Yawwa daman ina so mu dan yi magana shawara ce zan bada ban sani ba ko duka muna da lokaci ya kasance dai in ba takura ina so mu da kanmu mu raka Deejerh Mexico wajen iyayenta ya kuke gani?"

Zeeyter ta ce, "Gaskiya nima nayi tunanin hakan kuma ina free ni da Oga indai za da hali zuwan namu zaiyi amfani kuma ita ma zata fi jin dadin zuwa." Ta karasa Maganar tana kallon Haiydar
Ya ce, "Yes In sha Allah zamu kasance a bayan junanmu a kowanni hali na rayuwa we will stand for each other."

Farouk ya ce, "nima dai ban da matsala duk yadda kuka ce ya yi."

Khalil ya kalli Zahra yana mata sigina.
"Madam ya baki ce komai ba?"

Murmushi ta yi ta ce, "ai ka ce komai a madadina."

Gyara zama ya yi kafin ya ce , "Alright rabbie ya kara hada kawunanmu aduk inda zamu kasance zan tsara mana yadda tafiyar zata kasance zuwa jibi zamu tafi In sha Allah kila ma da Xavier zamu tafi tunda har yanzu yana hutu ne amman ba zata san cewa nan zamu ba kawai zamu ce mata ta shirya ne zamu yi tafiya."

★★★Khalil na fita ya kira Zoe ya tambayeta ko tana da time zata iya kai su Mexico daga Paris.

Zoe ta ce, "ehto gaskiya na dau hutu amman tunda team dinku ne zan koma aiki domin kuna birgeni kuma ina jin dadin kasancewa da ku."

Khalil ya ce, "Ma Sha Allah muna godiya sosai kuma muma muna jin dadin kasancewa da ke."

Cikin dare
Misalin karfe daya da rabi.
Idanun Farouk biyu yana duba yanayin duka yadda laptop dinsu ke tafiya da kuma ajiyayyen bayanansu kamar yadda ya saba gudun samun kutse.
Abun mamaki system din kowa lafiya lau tana tafiya da tsari amman kuma ta Deejerh ya nuna akwai matsala akwai wanda ke kwasan bayanan cikinta.
A daren ya mata nocking ya ce ta bashi system din ta ta dake barci na idonta tana bashi ta koma ta kwanta.

Birkicewa Farouk ya yi yana kokarin nemo me kutsen, a zuciyar sa yake raya cewa, "lallai wanda ya yi kutsen nan na kusa da su kuma bazai wuce cikin gidan ba." Ya yi shiru sai can kuma ya tashi.
Dakin Xavier ya je,yana zuwa ya tura kofar da karfi cikin Sa'a kuwa a bude take idonsa biyu shima yana kan system yana aiki.
Dubawa ya yi yaga me yake yi.
Wata kara Farouk ya sake yana shaƙo shi ya ce, "wane ne kai? Kai waye? Me kake nema a wajenmu? Me kake nema a wajen mu? Na ce me kake nema?"
Ya fada yana buga Xavier da bango yana kara jijjiga shi.
Kamar a mafarki Khalil ya ji hayaniya tuni ya tashi ya fita ya nufi dakin.
Haka ma Haiydar yana tashi baiyi ta kan zeeyter ba ya fice.

Farouk ya dage sai dukan Xavier yake har sai da Khalil ya shiga ya dakatar da shi.
Cikin fushi Farouk ya ce, "wannan abokin naka maci amana ne, cutar da mu yake son yi ni dama tun farko ban yarda da shi ba,munafiki ne."
Sai a lokacin Xavier ya ma Farouk wata tsawa yana sake masa mari a fuska , Khalil ya.....
[5/16, 5:17 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-54

Ya ce, "ku bari mana ya kuke abu kamar yara? Dare ne fa kar ku bari su tashi."

"Haba Don Allah Stop this." Haiydar ya fada yana rike hannun Farouk.

Xavier ya kalli Khalil ya ce, "ka fi kowa sanin ba zan taba cutar da wani na kusa da kai ba, aikina nake, and kuma ita suspect ce don haka dole in binciketa in ya kasance tana da laifi hukunci ne zai hau kanta babu shakka."

Farouk zaiyi magana Haiydar ya dakatar da shi.
Xavier ya kunna system dinsa

Please Login or Register in order to submit comment