Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

samu damar yin barci ba,har asuba tayi,ta tashi kenan zata yi sallah Mr Charles ya kara shiga dakin yana fadin , "ki fito mu tafi."
Deejerh ta kallesa cikin ladabi ta ce, "Sir bara inyi sallah to."

"What?" Ya fada cikin daga murya.
Deejerh ta ce, "Sallah zanyi sai inzo."

Ya girgiza kai tare da fadin, "Sallah ko? Karki fasa shugabar masu ibada, ni ba zan tsaya jiranki ba,kuma in jirgi ya riga ya tashi sai dai ki nemi yadda zaki yi." Ya fice abunsa.

Ita kuwa Deejerh toilet ta shiga ta dauro alwala ta yi sallarta.
Cikin ikon Allah kuwa har sai da ta isa airport din tana shiga jirgin ya tashi.
A tunanin Mr Charles bata zo ba don tun yana kallon hanya har ya gaji ya Kau da kai.
Yana kallon gefen sa kuwa ya ganta ya yi saurin kawar da kai kamar bai ganta ba.
Domin aransa jin tsantsar tsanarta yake ba don yana tunanin cewa a yanzu Designing dinta na daya daga cikin wa inda ke tashe a Company ba da kudirin da ke ransa gareta sai ya nininka yadda zata gagara komai.
Kwafa ya yi kawai ya ci gaba da karanta jaridar dake hannunsa.

Har suka isa paris Babu wanda ya yiwa wani magana.

Deejerh na shiga kauyensu ta ga Ammar gyara gidan Ma'am sosai ya yi kyau tamkar ba a kauyen.
Ta yi farinciki da sosai har tana tsokanar shi kodai aure yake so ya yi.

Tunda ta dawo taki zuwa gun aiki kuma Mr Charles har sawa ya yi a kirata amman taki zuwa,a karshe ma sai tafi mai da hankali akan yiwa yaran nan MMA TRAINING.

★★★Yamma ta yi yanayin garin ya yi duhu ga wata iska mai dadi dake karadewa, Deejerh ta kira officer kan cewa ko yau zasu gwanda aje yaransu a hanyar fita kauyen domin ganin ko za adace.
Ba musu kuwa ya amsa mata domin daman yana son ganinta har cikin ransa.
Hakan yasa ya dauki mota da kanshi ya ba wa yaran umarnin ta yadda zasu tsaya a zagaye kauyen shi kuma kai tsaye ya karasa gun Deejerhn ya tarar da ita da Ammar.

Daya daga cikin yan matan Deejerh ta tura wacce tafi yarda da kwarewarta a training din.

Tafiya take tamkar ba komai tana sauri mai nunin cewa akwai abun da takeso ta je cikin gari tayi.
Kamar yadda aka saba yiwa sauran matan ji ta yi kawai an rungumeta ta baya,da karfi ana kokarin janye mata wandon da ke jikinta.
Cikin ikon Allah ta juyar da hannunta tana riko fuskarsa.
Tare da buga masa hannunta amara.
Ya saki wata kara yana faduwa.
Takai yan sandan da suka buya suka fito wasu na video wasu kuma na kokarin cefeke shi.
Ganin yan sanda yasa Abdu rikicewa yana kokarin gudu.
Yana fara gudun kuwa suka cafkeshi daidai lokacin da Deejerh da officer suka iso wajen.
Da mamaki Ammar da Deejerh suke binshi da kallo.
Ammar ya ce, "Abdu? Daman kaine kake wannan aika-aikar?"
Fuska duk gumi yana haki ya ce, "wallahi sharrin shedan ne amman daga yau nayi alƙawari ba zan kara ba, na daina wallahi na tuba,ku rufa mun asiri."
Deejerh kam don takaici ma bata iya cewa komai ba.
Haka suka tafi dashi tana yiwa officer godiya.
Ya ce, "godiyar tukunna dai yanzu na baki kyauta amman nima akwai nawa lokacin zan kiraki a waya ko innazo'
Murmushi Deejerh ta yi ta ce, "to Shikenan Allah ya kaimu."

Yana tafiya Ammar ya bata rai, "wai wannan Murmushin fa? Ni fa ban gane miki ba da mutumin nan kamar son shi kike."

Deejerh ta ce, "to waya sani ne ma."
Tana fada ta tafi ta bar Ammar a gun.

Tana shiga daki taga wani sako ta Gmail dinta mai jaddada mata cewa lallai gobe ana nemanta a Company.

Ba yadda ta iya washegari haka taje.
Tana zuwa kai Tsaye office din Mr Charles ta nufa.
Bayan ta gaisheshi,yana amsawa mika mata magazine ya yi na tallen da za ayi da irin kayan da za asa wanda suka saba duk karshen shekara ake domin tallata kayan da suke Designing.

Sunanta ta gani kan wacce zata yi Designing din kuma tasa kayan ta yi tallen.
Ba Designing din bane ya tada mata hankali yanayin kayan ne ya tayar mata da hankali domin gabadaya yanayin kayan da fidda surar jiki ne gabadaya jikinta zai kasance a waje kuma duk kayan iya ka gwiwa ne, gashi babu damar rufe gashi hasali ma sai dai a kara wani gashin ma.
Take yanayinta ya sauya tana gama dubawa ya ce.
"Wannan shine hukuncinki na farko,na biyu kuma akwai wani babban Fashion Designer da ke buƙatar yin hulda dake na wata guda, zai kama muku hotel zaki koma can ku kasance tare."

Cike da mamaki Deejerh ta ce, "Hulda dani as how sir?"

Charles ya ce, "ki zama Girlfriend dinsa ta wani bangaren kuma ince tamkar matarsa domin hakan da zakiyi ne kawai zai iya kwato muna Wancen kambun da kika mana asara."

Ji tayi kanta ya fara yi mata wani azababben ciwo,ta yi saurin dafewa.
Charles ya kara fadin, "ki sani wa innan abubuwan biyu sun wajaba akanki kuma baki isa ki kaurace masu ba, in kuwa kikai attempting hakan tamkar kina yiwa rayuwar ki a kasar nan barazana ne."
Yana fada ya juya mata baya ci gaba da duba files din da ke gabansa.

Wani dishi dishi take gani, haka ta tashi jikinta ba kwari ta fita tana tafiya a hankali.
Kasa shiga office dinta tayi kai tsaye ta shige motar ta ta dafe kai.


Ganin disordern ta shirin motsawa yasa ta nutsu tare da tattalin hankalinta waje guda tana fidda numfashi a hankali.
Har sai da ta ji ta samu nutsuwar sannan ta dara driving ta dauki hanyar shiga kauyensu.

Har yanzu bata so ta fadawa Ma'am da Ammar domin tasan hankalinsu zai tashi Sosai.
Hakan yasa ta daure taki bari su gane.
Washegari da sasafe haka ta kara riskar wani sako mai razanarwa kan cewa lallai indai bata zo ta aiwatar da abun da aka umarceta ba za a kasheta.

Ta dawo kullum bata barci yadda ta ga rana haka take ganin dare.
Ranar ta rasa meke yi mata dadi kawai ta dauki wayarta ta yi posting a timeline dinta.
"I don't know how to explain what I'm feeling right now.
All i can say is that it hurts.
Everything hurts,my heart feels so heavy that all i want is to cry.
Ga shi kuma na gagara kukan.
Yana da matukar daci ya kasance duk kokarin mutum na wajen ganin komai ya tafi daidai ya gagara.
Ina kokarin maida raunani karfi, amman aduk sanda na yi kokarin tabbatar da hakan wani lamarin kan iya shigowa da raunani zai katse karfin.
Na gaji!
Some days really really hard to just move,
It's to hard to get out of the bed.
Its hard to even go outside.
Duk da cewa ni ba mutum ba ce da ke iya fidda abun da ke damunta ko yake ranta kai tsaye, Amman kuma ina bukata zababbun mutanen da zasu iya fahimtar yanayina ba tare da furta komai ba."

Kusan kullum ta kan yi rubutu mai yanayi da hakan a timeline dinta amman babu mai kulata wani lokacinma in tayi sa'a bai zarce ayi mata like a wuce.

Reply din da ta gani ne cikin sauri yasata gyara zama domin dubawa.
Ibrahim Khalil sunan shi.
Ya yi mata reply da fadin, "Yayin da kafa ta yi nauyi aka gaggara dagata daga inda ta kame,ba wai barinta ake da nufin anan za ata zama ba,aa kokarin Dagata ake komin zafi da radadin da za aji domin kuwa hakan na nufin maganin da zaiyi mata aiki yana gaba ne,sannan wannan ciwon kuma rubutaccene da Ubangiji ya kudurta cewa sai anyisa kafin aji sauki, don haka babu babu bukatar fidda tsammani komin tsananin rayuwa akwai sauki, da yawan lamura Ubangiji na jarabtar mu ne ba don baya sonmu ba illa don ya ga ya zamuyi kokarin rayuwa a yanayin da ya sanya mu? Shin zamu karbi kaddarar? Zamu jure? Kuma zamu tuna cewa komai tsanani yana tare da sauki? Ka da ki karaya,in a kwance kike ki tashi,in hawaye kike ,ki maida shi murmushi."
Tana kaiwa karshen ba ta san sanda ta fara goge hawayen da ke fuskarta tana sakin murmushi ba........


*Ashe dai bakuyi fushi ba😻 In sha Allah har Friday zan yi posting daga nan sai mu tafi hutun Ramadan muna dawowa kuma a karasa, Luvs U OLL 😘*

08103080717
[3/6, 11:15 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-46

Ji tayi karfin gwiwarta na dawowa.
Ta yi masa reply da , "Thank you so much, har cikin raina na ji dadin jawabanka sai nake ji cewa tamkar ka san dafin dake cikin zuciyata."

Emojin Murmushi Khalil ya tura mata yana, "Kila kan na shiga cikin zuciyar ki na karanto ne ba tare da kin sani ba."

Ta tura masa emojin zare ido da mamaki tana, "kenan kai Aljanine ba mutum ba, domin ai mutum ba zai iya shiga cikin ran mutum ba."

Khalil ya kara yin dariya ya ce, "Aiko dai ni mutum ne."
Daga nan suka ci gaba da chatting karshe ma suka koma Dm tamkar wa inda suka jima da sanin juna.
Deejerh ji tayi ta aminta da khalil duk da cewa bata taba ganinsa,jin muryarsa ba, bare wani abu illa media da ta ci karo da shi.

Ranar neman damuwarta ta yi ta rasa karshe ma barcin da ta jima batai ba ranar tayi.

A kwana a tashi kamar wasa Deejerh ta saba sosai da Khalil har waya suke.
Ta ba shi labarin abun da ke faruwa da ita a Company har ma da rayuwarta ta gida data bari.
Ya matukar tausaya mata inda yake bata shawara kan ta gwada bude Companyn Fashon design da kanta.

Deejerh ta ce, "lamarin na da girma sai nake jin cewa ba zan iya hakan ba,uwa uba kuma ina gudun hatsarin kamfanin da nake aiki muddin zan zauna kasa daya da su hakan babbar matsala ce gareni."

Khalil ya ce, "ki nutsu, komai mai yiwuwa ne da karfin ikon Ubangiji muddin kika bada yakini, zaki iya,kuma na san zaki iya din kema kin sani tunda har kika iya jurewar rayuwar ki ta baya wannan ba komai bane,sannan batun kamfanin da kike aiki kuma karki sa tsoron su ko shakkarsu arai babban abu mai mahimmanci shine kawai ki dage da addua,kar kiyi wasa, sannan kuma inda hali ma ki bar kasar Gabadaya domin samarwa zuciyarki salama yadda xakiyi komai cikin nutsuwa amman kafin yanke kowanni hukunci kiyi tunani kuma ki nemi shawarar makusantanki."

Deejerh ta ce, "Hakane na gode sosai kuma In Sha Allah zan yi tunani in nemi shawarar xaka ji ni da duk hukuncin da na yanke."
Tana gama magana da Khalil ta kira Nawar tana bashi fada masa hukuncin da take shirin yankewa.

Nawar ya ce, "hakan shawara ce mai kyau kuma na ji dadinta ki nemi kasar da kike ganin zaki ji dadin zamanta bangaren kudi kuma karki damu da shi zan taimaka da wani abun yadda ba za ki sha wahala ba wajen tsara kamfanin."

Deejerh ta numfasa ta ce, "Goyon bayan ku nafi bukata da shawara, na fi so kuna barina ina shan wahalar da kaina, insan cewa e ga hanyar da ake bi kafin samun nasara,sai kuma katin zama yar kasa da zan bukata wajen ka tunda kana da connection din da nasan zan iya samu, da zaran na cire kasar da zan koma sai in fada ma kawai."

Murmushi Nawar ya yi, "ina so kam ki samu kwarewa a kowanni fanni amman duk da hakan bana so ki wahala,in dai kin ga wani abu da ya gagareki just let me Know, And in ma kinga zaki zauna ne a paris din kin san zan iya komai domin tsare lafiyarki ba wanda ya isa ya taba wani abu naki ma bare ke din."

Deejerh ta yi dariya ta ce, "ana son shagwaba ni da yawa amman nidai sai na zama jarumar gasken nan."

Da wasa da dariya suka rabu sannan Ammar yazo da daddare take basu labarin shawar da ta yanke shi da Ma'am


Duk da cewa dukansu basa so tai nisa da su amman sun zabi cewa ta koma wata kasar ta fara business dinta .

Ma'am ta ce, "amman kusa da Paris yadda zaki iya zuwa ganin mu aduk lokacin da muka bukaceki kinsan dai zanta jin kewarki."

Karaf Ammar ya ce, "Austaralia, ta koma cen kawai domin na san zata ji dadin zaman cen fiye da nan ma domin cen sun fi sauƙin rayuwa da tsari."
Sun sha hira sosai kafin Ammar ya tafi.
★★★
Bincike Deejerh ta fara yi kan Australia.
Ammar ya rakata ta yi visa.
Ta sanar da Nawar cen ta yanke shawarar zuwa domin ayi mata takardan tabbatar da zama.

Shirye-shiryen barin Paris ta fara.
Sai da ta yi koma nata cikin tsari kafin ta shirya zata tafi.

Ma'am ta ce, "Abu biyu zuwa uku zan tunatar da ke, domin na san kin sani amman matsayina na tamkar uwa gareki ya wajaba in kara jaddada miki su, na Ɗaya kiji tsoron Allah aduk abun da zaki yi da inda zaki kasance,na biyu ki rike mutuncinki da kimarki na matsayin 'Ya mace, Kuma ka da kiyi wasa da ibada aduk halin da zaki tsinci kanki,na uku ka da ki karaya duk rintsi duk wahala kisa aranki akwai sauki."

Rungume Juna suka yi suna kuka.
Papi ya ce, "Tabbas wa innan abubuwan da Ma'am ta fada ya isheki har karshen rayuwa kuma ina sa rai da cewa zaki rikesu bisa zaton alkairin da nake miki ko ince muke miki."

Ammar ne ya katse su da fadin, "Mummuna nidai ba wani kewarki zanyi ba kuma abar kukan nan haka muje jirginku saura 30mins ya tashi."

Shiga motarta tayi tana yiwa su Papi da Ma'am bye-bye suka nufi airport.

Sai da Ammar ya tabbatar jirginsu Deejerh ya tashi kafin ya bar Airport din.

★★★

AUSTRALIA
St George Ranges WA Street.
Anguwa ce ta masu matsakaicin karfi.
Duk da cewa talakawa ne suka cikata amman tana da kyau har ma da kyan yanayin rayuwa.
Nan Deejerh ta sauka ta kama hanyan karamin gida.
Tayi wanka ta huta kafin ta fita ta siyo abinci.
Bayan taci tayi sallah, kafin ta dauki wayarta suna chatting da khalil.

Kwananta Uku ta fara fafutar bude Company, wanda a karshe da abubuwan suka mata yawa har sai da Ammar yaje Australian ya tayata wasu abubuwan.
Karamin kamfani ta bude a gidan da take dake ita kadai ce ciki.
Sai da komai ya kammala kafin Ammar ya tafi.
Daga nan ta fara daukan yan matan anguwar tana koya masu domin bata da karfin daukan wasu aiki a halin da take ciki sai dai tayi taimakon koya wa yaran anguwar ganin cewa wasu ko makaranta basa zuwa saboda iyayensu basu da wadatar biya.

Ta fara jin dadin rayuwa sosai wanda har ya kai ga ta fara mantawa da wasu matsalolin rayuwarta sai dai duk da hakan ta kan tuna kuma ciwonts ya kan motsa ba dai kamar da din ba.

Sun kara sabawa sosai da Khalil har ya gabatar da ita ga abokanansa, Zahra,Haiydar da Faruq kuma suma ta saba da su sosai har sun fara shirye-shiryen bude Company babba mai taken 5STAR EXPENSIVE COMPANY.
Gyara zama tayi ta na gumi lokacin da ta gama tunano gwagwarmayar rayuwarta ta, wayarta ta ga na riging sunan Zeeyter da ta gani ne ya sata sakin murmushi tana dagawa.....

[3/7, 10:01 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-47

"Madam,Mrs Haiydar, Yel,kuma Oum Aiza sannan Uwar gida,Amaryarmu dai na hanya."
Dariya Zeeyter ta yi har sautin na fita cikin wayar ta ce, "kwaji da shi dai,in har kun isa kuyi amare uku ma ba daya ba,bai dameni ba."

Deejerh ta ce, "zance ma kenan ai da tuni kin canja kala."

"Never, ni kam ba ma wannan ba, tun dazu inata kiranki da aka gama meeting din nan bakya dauka ince dai lafiya ko?." Zeeyter ta fada.

Deejerh ta ce, "kalau wallahi na shiga duniyar tuna rayuwar bayane."

Zeeyter ta numfasa kafin ta ce, "Kin san dai ba aso ki yawaita tuna abubuwa marasa dadi ko? Ki rufa mana asiri ki ci gaba da rayuwa a VIXEN ɗinki kada mu ga ko mu ji sauyi."

"In sha Allah kuna tare dani ,kuma Ubangiji na tare dani, komai mai saukine kuma komai mai yiwuwa ne,zan ci gaba da amsa sunan VIXEN har karshen numfashina Da ikon Allah."

Zeeyter ta ce, "Yawwa Baby Dress nake so a Designing wa Aiza."

Deejerh ta ce, "Ok to ya kikeso ya kasance?"

Zeeyter ta ce , "Na bar miki wuka da naman na san zakiyi fiye da tunani so na bar komai a hannunki amana kaman kala biyar kuma.....
Bata karasa maganar ba dariya ta barke mata.
Haiydar ne da Aiza suke mata cakulkulu, cikin muryar dariya ta ce, "Oh... Father and Daughter u wan kill me ba?....ta ci gaba da Dariyar kafin ta ce, "Sorry sister i will call you letter." Ta karasa maganar tana kara fashewa da dariya yadda gabadayansu suka birkata mata jiki da cakulkulu.
Ganin basu da niyar dainawa rugume Haiydar din kawai ta yi ta kwanta a jikinshi.

Sai kuma duka suka rugumeta, Aiza na ci gaba da kyalkyala dariya.
Zeeyter ta shaki numfashi kafin ta ce, "Ahalinaa...ina kaunarku duk da cewa bakwa ji kun fiye rigima." Ta karasa maganar tana kaiwa Haiydar kiss, sannan tawa Aiza ma tana shafa mata kumatu ta ce, "Dady's Girl."
Maimaita hakan Aiza ta ta yi tana dariya kasancewar yanzu ta fara magana bata wani iya ba sai gwaranci.

★★★★
Mexico.
Karfe Biyun dare Huda tsaye take kan Zayd ta na zabga masa uban masifa da sambatu.

"Na gaji na ce na gaji, I can't take this, ba zai yiwu ba ace kwanaki na ta tafiya ina kara girma amman ban da Ɗa ko 'Yar da zan gani jinina, wannan zancen asibitin na ka duk ban yarda da shi ba, ga dukkan alamu kai kam baka zama cikakken Ɗa namiji ba, ba zai yiwu inyi rayuwa da mace 'Yar uwata ba,in ma hakan nake so in nemi asalin jininsin mana,yau ita rana ta ƙarshe da zan iya hakurin zama da kai muddin ba ka nema mun mafita ba sai ka ga takaddar neman saki daga court gobe."

Duk masifar nan da take da bakaken maganganun da take masa, har lokacin ji yake ba zai iya rabuwa da ita ba,kuma ba zai iya rayuwa babu ita ba, hasali ma kara jin kaunarta yake aransa.

Da ta gama masifar bai kula ba komawa ta yi gefen gado ta kifa kanta da hannu.
Jiki a sanyaye ya tashi ya durkusa gabanta yana, "Kin san dai ko me zaki mun,ko me zaki ce,in ba wai rayuwata ce ta bar gangar jikina ba,ba zan taba iya rabuwa dake ba,ki fadamun duk wani abu da kike so muddin zaki rayu dani zan miki domin farincikinki."

Huda ta dago kai ta kalleshi ta ce, "abun da na fada ma tun farko,ka biya kudi azo amun ciki."

Tana fada ya yi shiru yana tafiya wata duniyar tunani.

Ta kalli kafin ta kara fadin, "ba dole bane fa ni in ba za ka yi hakan ba kawai ka sakeni."

Da sauri Zayd ya katseta da fadin, "Aa za ayi yadda kike so,amman ki samo wanda xa a biya din."

Take ta fara murmushi tana daukan wayarta, "yanzu ma kuwa akwai wa inda zan iya kira yanzu su zo ka ga su biyu da kai duk wanda aka dace shikenan."

Zayd ya ce, "yanzu? Cikin daren nan?"

Huda ta ce, "eheen to mene ne?"

Ya ce, "kar ki kuskura ki kira mun wasu cikin gida muddin ba kina so in bata miki rai bane."

Ba don taso ba haka ta hakura tana cuna baki ta kwanta.

Ya ce, "kuma sai anyi yarjejeniya anyi signing ba za ayi mun wannan shirmen da ka ba,son da nake miki ba shi ke nufin zan iya jure komai da kike min ba, ki kiyayeni a zauna lafiya."

Bata ce komai ba ta gyara kwanciyar ta kawai.
Washegari
★★Yana komawa gida daga Office Huda ta dire masa wasu takardu.
Shi har ma ya manta cikin yanayin rashin fahimta ya daga kai yana kallonta.
Da fadin, "What is this?"

Ta zauna kusa da shi tana, "Welcome Dear, ta kardun yarjejeniyar da ka ce za ayi ne, ka yi signing suma zasu zo yanzu suna hanya."
Ajiyewa ya yi kawai bai ce komai ba.

Ta ci gaba da fadin, "zasu zo sai muyi dinner tare ko?"

Nan ma bai ce mata komai ba.

Ita kuwa kiransu tayi, bai wuce 30mins ba sai gasu suna nocking.
Da kanta taje ta bude masu suka shigo.
Suka gaishe da Zayd fuska a murtuke babu annuri ya amsa.
Huda ta ce, "mu karasa dining area ko."
Fara'arsu suka tashi suka je.
Zayd na zaune ta dawo ta rike mishi hannu tana, "muje mana."

Ita tayi savin din su duka da kanta suna cikin cin abinci ta sako maganar, tana, "Dear ka ga sune,ina fatan Sunma,in kuma basu maka ba sai a canja wasu."
Zayd ya kauda kai tare da fadin, "Don't Worry Go On."

Ta ce, "na musu bayanin komai, kuma na sanar da su cewa duk yaran da za a haifa mallakinmune ba na su ba, bare ma ai namunne domin duka za ku participating so ba mu da matsala da wannan,yanzu zasu sa hannu domin tabbatar da amincewar su."
Ta fada ta na mika masu takardar.

Suna Signing ta ci gaba da fadin, "Kowannen su suna da salary duk karshen wata har zuwa lokacin da zamu nemi da su dakata."

Zayd na jinta amman shi kam danna wayarsa ma yake.
Taba shi ta yi,cikin salalalliyar murya ta ce, "Ka fada nawa zakana biyansu kafin suyi signing din."

Zayd ya ce, "koma nawa ne ki tsayar yadda ya miki."

Washe baki ta yi tana, "Alright, Thank you ina ganin ai 500MXM ya yi ko?"

Da , "Okay ya amsa mata kawai."
Ya ci gaba da danna wayarsa.
Bayan sunyi signing ita ma tayi, sannan ta mikawa zayd din shi ma ya yi.

Bayan sun gama Huda cikin kissa ta ce, "Dear yau xa a fara fa kasan na matsu dai, kuma da kai zamuje kai kana shan sperm din,in na farko ya yi ya gama sai dayan ma ya yi ,sai su tafi ko? Yau ba sai sun kwana ba tunda yau aka fara ."

Kafeta ya yi da ido yanayin sa gabadaya ya sauya.
Ta yi kasa da murya araunane ta ce, "Please ka ji."

Haka ta lallaba shi suka tafi daki dukan su suka yi tsirara.
Kuma kamar yadda ta umarta haka yake shanye sperm din ba yadda ya iya.
Takaici kamar zuciyarsa zata buga kiri-kiri shi ke shan sperm din wani garden namiji, sai kawai yake tuno Deejerh a idanunsa yana jin takaicin cewa duk ita ce silar abun da ke faruwa da shi a yanzu.
Kara kudurtawa yake aransa lallai ko ina take a duniya ya wajaba a gareshi ya nemota domin daukan fansa.

★★★ 5stars Expensive Company.

Shirye-shiryen birthday wa Deejerh suke ba tare da ta sani ba a boye.
Zahra da Zeeyter ne kan gaba, ita kuwa Deejerhnma ta manta da batun birthday din nata.

Zahra da Khalil na zaune suka kira Zeeyter ita ma kuwa tana office tare da Haiydar.
Zeeyter na dagawa ta ce, "
[3/8, 10:03 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-48

★Dare.
Deejerh na cikin barci ta farka kamar an tsikareta kawai ta nufi toilet ta yi wanka.
Bayan ta gama wankan ta dauki sabulun wanke hannu ta wanke hannayenta, zata fita ma ta kara komawa ta wanke sai da tayi hakan kusan sau hudu kafin ta fita gabadaya.
Wani kayan barcin daban ta dauka tasa duk da cewa wanda ta cire na jikinta ma da zata kwanta ne ta sa kuma kwanciyar ta da tashinta yanzu bai fi awa daya da rabi, ji take ba ta yarda da kayan ba kamar wani datti ya kamasa wanda cuta zata iya shiga jikinta, hakan yasa kai tsaye ta turasa cikin kayan wanki.

Zata koma ta kwanta kenan sai kuma ta nufa Kitchen domin taji sha'awar shan kayan fruit.
Tana zuwa ta dauki Mango da orange ta dau wuka zata yanka,ta daura kenan akai sai kuma ta ji jikinta na mata wani iri a zahiri ta furta, "yanzu in ni aka yanka da wukar nan ya zan ji? Su ma ai ba za su ji dadi ba inna yanka su."
Sai kawai ta maida su Fridge din ta rufe.
Ta dauki gorar Ruwa ta tafi da shi daki.
Tana hawa kan gadon ta bude ruwan ta sha sannan ta kwanta.
Tana kwanciya sai taji idanunta ya kafe kam babu alamar barci.
Tashi ta yi ta dauki Qur'ana ta karanta Suratul Tauba sai da ta karanceta har karshe kafin ta karanta Fatiha da Amanar Rasulu sannan ta koma ta kwanta.
Tana kwanciyar kuwa barci ya saceta.

★★★Mexico

Zayd zaune yake cikin dare a office dinsa

Please Login or Register in order to submit comment