Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta yi sannan ta karasa daf da yarinyar ta durkusa ita ma kafin ta daura hannunta a bayan yarinyar a hankali.
Da sauri yarinyar ta dago kai tana share hawayen dake fuskarta.

Deejerh ta ce, "Baby mene ne kike kuka? Me ya same ki?"

Murya na rawa ta ce, "Yau ChildrenDay ana yin party a skul dinmu kowa na zuwa da sabon kaya ni kuma mamana bata samu kudin da zata siya mun ba,shine dana je school din suketa mun dariya suna korata sunki yin wasa dani wai ni ban da sabon kaya kuma Mamana bata sona"

Deejerh ta dafa ta dagata ta tashi tsaye.
Gaba-daya shi kan shi kayan da ke jikinta a kode yake kuma duk ya yayyage ya gama jin jiki wanda ana tabawq zai iya datsewa.

Deejerh tasa hannu ta kara share mata hawayen dake zuba a fuskarta kafin ta ce, "ki mun alkawari ba za ki kara kuka ba kuma duk wanda ya ce miki mamanki bata sonki kice tana sonki sosai."
Girgiza mata kai ta yi.
Deejerh ta ce, "Gud Girl yanzu zamu je in baki sabon kayan da zaki sa yau kije School har ma da wasu kina so ai ko?"

Kara girgiza mata kai tayi fuskarta dauke da murmushi.
Deejerh ta bude mata mota ta shiga
Kai tsaye suka nufi campany
Bangaren kayan yara suka yi Deejerh ta zaban mata kaya sosai masu kyau sannan ta dauketa ta maidata mota.

Gidan su yarinyar Deejerh tasa ta nuna mata .
Suna zuwa ta shiga da gudu Mamanta na kwance ita ma kukan take a zuciyarta tana jin radadin yadda ta gaza samun abun da zata farantawa yarta gaba-daya zuciyarta babu dadi.
Tana ganin yarinyar ta tashi tsaye da sauri ta gaza fahimtar mafarki ne ko zahiri rufe idonta tayi ta kara budewa domin tabbatar da abun da take gani.
Domin kayane na alfarma aka sawa yar wanda bazata iya misalta kudinsu ba.
Da gudu taje ta rugumeta tana, "Momy kin ga Aunty ta bani kaya."
Suna hada ido da Deejerh ta sake mata wani ƙayataccen murmushi.
Da sauri ta ce, "Anyy ina kika samu kayan nan wannan wace ce?"

Yarinyar ta ce, "dana je school ne suketa mun dariya suna korata shine na fito waje ina kuka Aunty ta ganni ta je ta canja mun kaya kuma ta ban wasu da yawa."

Da sauri Momyn Anny taje gaban Deejerh harda guntun hawayenta tana fadin, "Mun Gode sosai Allah ya saka da alkairi wallahi na rasa samun kudin da zan siya mata sabon kayan da zata sa yau hankali na tashe yake ta tafi makarantar amman tunanin yadda zata kasance cikin yara kowa ya yi ado ban da ita ya hanani sukuni mun gode sosai Allah saka da alkairi."

Deejerh ta ce , "babu komai yanzu muje in kaiki makarantar sai in tafi ko? Ga wannan kayan a ajiye miki."

Karban kayan Momynta tayi cike da farinciki.
Su kuma suka fita suka tafi school din.
Sauran yaran suna ganin Anny kuwa sai binta da kallo suke masu gulma na yi suna mamakin yadda aka yi ta samu kaya mai kyau wanda ya fi na su ma.

Deejerh na School din bata tafi ba, anata wasa tana zaune tana kallonsu.
An basu dama yaran inda me magana ya fito ya yi ko bada labari.
Anny ta daga hannu.
Hankalin kowa ya koma kanta.
Tana karban Mic din bayan ta yi gaisuwa ta ce, "Ni dai zan ce dariya babu kyau ga kowa adaina yiwa wanda bai da abu dariya domin watarana zai iya samu kuma mamana tana yawan fadamun bawa baya taba kaucewa kaddararshi,ta ce mun a kullum na kasance mai mutunta mutane ka da na wulakanta kowa nima Ubangiji ba zai taba bari in wulakanta ba."
Tana kaiwa nan ta tsaya.
Deejerh ce ta fara tafa mata tana mamakin yadda yarinyar ta iya furta wa innan furucin.
Sauran staffs dinma da yara tafa mata suka fara.
Kawayenta kuwa da suka mata dariya dazu jikinsu ya yi sanyi duka suka sunkuyar da kai.
Binta suka yi suka sa hannu a kunnensu suka kama kafin suka ce, "Sorry Anny, ba za mu kara ba kinji ko."

Murmushi ta yi musu kafin ta ce, "is okay."

Deejerh ta ji dadin kasancewa a School din sosai domin kuwa anan ta yi wuninta har sai da suka gama wasa ta maida Anny gida kafin ita ma ta tafi gidanta.

Bayan tayi parking mota tana sa kafarta zata shiga daidai palourn.......


[6/1, 10:18 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-60

Kafarta ta ci karo da wata flower.
Kamshin flowern ne ya rinjayeta tayi saurin dauka tana shaka tare da ajiyar zuciya.
Can kuma sai ta furta a zahiri, "Waye ya kawo kuma ya ajiye anan?"
Ganin bata da amsar tambayar yasa ta kwallawa mai aikinta kira.
Da gudu ta karaso gareta.
Deejerh ta nuna mata flowern tana, "wannan fa? Na waye? Kuma waye ya kawo?"

Cike da mamaki mai aikin ta kalli flowern kafin ta ce, "No Madam ban sani ba,ni ban ma san da ita anan ba,yanzu na gani a gunki."

Deejerh ta ce, "Ok koma aikinki."
Ajiyewa tayi kan Centre table kafin ta shige cikin dakinta.

Wanka tayi ta fito kenan tana goge kanta da towel ta ji alamar shigan sako wayarta.
Tana janyo wayar sai ta ga an rubuta, "Barka da dawowa kyakkyawa ina fatan dukkanin sakonnina sun iskeki kuma kin kasance cikin farinciki da maraba da su, ko da ace ba za ki amshi soyayyata ba indai murmushi zai ci gaba da bayyana a fuskar ki hakan ma kadai zai sanya zuciyata cikin shauki bare kuma ina ji a jikina cewa zuciyoyinmu yan uwan juna ne lokacin haɗuwar su ne yazo a yanzu kuma dole su rungumi juna,kar ki manta ina kaunarki."

Ajiye wayan Deejerh ta yi a zuciyarta tana fadin, "wake son takurawa rayuwata hakane." Ta yi tsaki kafin ta ci gaba da gyaran kanta.

Kamar wasa kullum Deejerh sai ta iske sako cikin wayarta a kowanni safiya kuma an sa mata flower a cikin motarta amman an daina kai mata envelope office.

Safiyar yau tunda ta tashi ta duba wayarta kasancewar ta saba tana dubawa zata ga sakon barka da safiya sai bata ga komai ba.
A zahiri ta ce, "to lafiya kuwa? Kullum kafin in tashi yake turo sakon amman yau gashi har na makara ma sosai kuma bai turo ba, Allah sa lafiya dai"
Sai can kuma ta yi tsaki, "to ina ruwana ma ai hutawa na yi da na cinsa koma waye can ta matse masa, akan me zan damu da shi."
Cillar da wayar gefe tayi ta je ta yi wanka ta fito ta shirya tana breakfast amman tana kara duba wayarta a zatonta ko shima ya makara ne zai tashi ya turo mata sakon.

Gagara cin abincin yadda ya kamata tayi kawai ta dauki keyn mota ta fita.
Da saurinta ta bude tana zakuwar fara cin karo da Rose Flowern da ta saba gani, sai dai shi ma din yau babu ba asa ba.

A fili ta ce, "yau har Flowern ma babu? To me ya same shi?" Sai kuma ta yi tsaki tana dafe kai.
"Oh Deejerh me zai sa ki damu da lafiyar wani wanda baki sani ba,wanda ma yake takura miki, ke me zakiyi a soyayya? Ta ya ma zaki iya soyayya? Ba za ki iya ba, soyayya ba taki ba ce." Ta karasa maganar tana ajiyar zuciya kafin ta tada motar cikin sauri ta bar gidan.

Ranar kasa aikata abun kirki ta yi a office ta rasa meke yi mata dadi jikinta a sanyaye wanda ita kanta bata san dalili ba.
A karshe waje ta fita ta zauna tana kallon bishiyoyi kawai tayi shiru.
Har lokacin tashinsu ya yi bata iya tsinana komai ba, haka ta shirya ta koma gida.

Dare
Wayarta hannu tana kallo da tunanin ko sako zai shigo mata har barci ya kwasheta dake in za a turo sakon rufe number ake bata gani hakan yasa babu hanyar da zata bi ta gwada tura sakon ita ma.
Can cikin dare kamar a mafarki taji sautin shigar sako wayarta take ta farka tsabar tasa abun aranta, tana daga wayar kuwa ta ga sakon da taketa mararin zuwansa ne.
Ba ta san lokacin da ta sake wani ƙayataccen murmushi ba tana tashi tare da gyara zama akan gadon.
Kamar haka ya rubuta mata.
"Kyakkyawa, ina fatan kinyi kewata kamar yadda nima na yi naki a yau domin kuwa na gaza samun sukunu Kasancewar zuciyoyinmu basu samu damar zantawa da juna ba, Ina fatan kina lafiya? Kuma murmushin nan na fuskarki na nan bai yi kaura ba,zan so ace kin samu barci mai nutsuwa gami da ni'ima tare da jin cewa aranki lallai ni din mai sonki ne,kuma mai kaunarki ne a kowanni hali ko ince yanayi na rayuwa,mu kwana lafiya, ka da ki manta kiyi addu'a."

Deejerh na gama karantawa ta ji wani irin farinciki aranta wanda ita kanta ba ta san dalilinsa ba kuma ba za ta iya kintatashi ba.

Da wayar a jikinta wani barci mai dadi ya yi awun gaba da ita fuskarta fal da fara'a.

★★★★Monday
Ranar Deejerh tana da Meeting da wani Company da ke son yin hadin gwiwa da ita suyi Designing wani kaya.
Hakan yasa da wuri ta shirya ta nufi Company.
Tana zuwa ta tattarar secondry ta kammala shirya komai hakan yasa kai tsaye ta wuce office din.
Karfe 11am daidai zasu fara.
Haka kuma karfe 10:55 aka sanar da ita cewa bakon nata ya iso.
Duba agogon hannunta ta yi kafin ta ce, "ga dukkan alamu wannan yana girmama lokaci."
Ta bada umarnin ya shigo.
Da sallamarsa ya shiga cikin nutsuwa wanda ya kasance matashi ne wanda a ko ina zai iya amsa sunansa na cikakken Ɗa namiji,kwarjininsa a bayyane yake bisa yanayin kamalarsa da shigarsa gami da nutsuwar da ya yi.
Tsayawa ya yi sai da ta bashi izini kafin ya ja kujerar ya zauna.
Bayan ya zauna ma sai da ta bashi izinin magana.
Duk abun nan Deejerh bata bari sun hada ido ba abun da ke gabanta kawai take yi.

Ya ce , "Ni dai Sunana Fayez Abdul-Amaan Manager Companyn Stitching Dreams, kamar yadda kika sani ko ince muka turo letter mun bayyanar da cewa muna so muyi haddin gwiwa da companynku wajen samar da sabon Design din kaya wanda muka turo da yanayin abun da muke fatan yi,kuma a yanzu ma gashi nan na zo da shi."
Ya karasa maganar yana budewa Deejerh file din da yazo da shi.
Ta karba ta bude ta gani kafin ta ce , "Ok to duk na ji bayanan ka amman ina so inyi ma wata tambaya."

Fayez ya gyara zama yana, "ina saurarenki ranki ya dade."
Deejerh ta ce, "me yasa kuka zabi yin hadin gwiwa da companynan bayan cewa akwai wasu da yawa a kasar nan tsofaffi ma da suka riga mu kasancewa a harkar."

Murmushi Fayez ya yi kafin ya ce, "Madam sai na ga kamar kin fi kowa sanin amsar tambayar da kika yi,amman duk da hakan zan baki amsa ko ince ma zan kara tunatar da ke, kasancewarku na musamman da ke kokarin fidda sabin design a kowani lokaci da kuma jajircewarku, haka zalika anyi muku shedar cewa bakwa yin abun banza kuma bakwa abu da cutarwa ma'ana bakwa taba yin kayan bogi kuna da kyawawan Qaulities din da kowanni Company ke bukata wanda nasan kin fini saninsu ma,mu dai babban burinmu da fatanmu a yanzu ku amince ku bamu dama muyi wannan aikin tare."

Sun tattauna sosai kuma Deejerh ta basu dama har ma ta sa hannu.

Bayan ta koma gida da dare lokacin da aka saba turo mata sako na yi aka turo kamar kullum.
Da zumudi ta fara karantawa.
"Yau ina cikin farinciki sosai mara misaltawa wanda nake ji dama ya kasance mun hakan a kullum, numfashina sun yi karo da numfashin muradin raina kuma burin rayuwata,haka ma zuciyoyinmu sun buga a tare, daga yau ban jin cewa zan iya ci gaba da boye kaina domin ba zuciyata bazata iya ɗauka ba."
Deejerh na gama karantawa sai ga kira da wata sabuwar number.....
[6/2, 5:40 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-61

"Assalamu alaikum."
Sautin da ta ya fara sauka kenan cikin nutsuwa a kunnenta.

Riskar kanta da kasa furta komai ta yi na yan seconds sai da ya kara yin wata sallamar a karo na biyu kafin ta amsa cikin sanyayyar Muryarta.

Ajiyar zuciya Fayez ya yi wanda sautin sai da ya ratsa cikin wayar kafin ya ce, "Tsira da aminci su tabbata ga Ubangijin da hallaci wannan baiwa dauke da dadadɗiyar murya mai sanya nutsuwa da annashuwa, na san hankalinki ya rabu gida biyu tunaninki ya kasu daban daban wanda ni kuma na gagara samun nutsuwa bisa kasancewar haduwar numfashinmu guda a lokaci daya, ba zan iya ci gaba da boye kaina ba, domin indai hakan zai faru ba makawa za a iya riskar gawata na tabbatar da cewa kaunarki ba wai ra ayina ne kawai ba,dole nane domin kuwa ke din bangare ce ta rayuwata, Na zabi turo miki da saƙonni domin gudun fuskantar ki kai tsaye sai kuma akai nasara ace kece mai kamfanin da muke son yin hadin gwiwa da shi, ada bani za a turo ba amman tunda na san kece na wajabtawa kaina zuwa domin kara yin tozali dake.

Ba wai kawai don kyawunki da siffar ki naka so ba, ina sonki ne domin rayuwata har karshen numfashi mu zamewa juna bango abun jingina kuma masu tsayawa juna a ko ina duk rintsi duk wuya zan kasance da ke kuma mai goyon bayanki.

Ina rokon ki alfarma Don girman Allah ka da kice ba za ki amince dani ba domin hakan babbar barazana ce a gareni da rayuwata."

Yana fadan hakan ya yi shiru.
Ita ma Deejerh har lokacin bata ce komai ba ta yi shiru tana saurarensa.

Ganin bata da niyar magana Fayez ya ce, "Don Allah ki amsani ko zanji dadi araina."

Deejerh ta rasa abun cewa daga bisani wani ƙayataccen murmushi tayi wanda sai da ya ratsa wayar.
Yana jin sautin murmushinta ya yi ajiyar zuciya da fadin, "ko da ba ki ce komai ba, murmushinki kadai ya isa ya bayyanar da cewa na samu nasara."

Kara wani murmushin tayi tana gyara rike kankame filon da ke hannunta ta ce, "aa kam da saura, har yanzu ban ji komai da kai a cikin raina ba, ka ga kuwa zuciya ba zata taba amincewa abun da bata gamsu da shi ba, zan dai baka dama ka gwada in har zuciyata ta amince da kai fine a kasin hakan kuwa sai dai ince da kai sorry."

Fayez ya ce, "Alright na amince indai wannan ne, amman da sharadin zamu dunga haduwa, za muna hira kuma zakina sake mun fuska."

Deejerh ta ce, "ba ka da matsala da wannan, haduwa kuma ai zamuyi aiki tare ko ka manta ne?"

Fayez ya ce, "Nop haduwar aiki daban haduwarmu daban, ina so ki bani lokaci."

Deejerh ta amsa da , "Okay In sha Allah."

Murmushi Fayez ya yi kafin ya ce, "Maddallah da ke ina matukar godiya Bilby."

Cike da bayyanar da yanayin mamaki Deejerh ta maimaita maganarsa da alamar tambaya, "Bilby?"

"Eheen da shi zanna kiranki daga yanzu Bilby (An adorable Australian marsupial, for a unique and cute girlfriend)." Fayez ya fada.

Deejerh ta ce, "Hmm to ai ban zama girlfriend din taka ba."

Fayez ya ce, "Zaki zama ai saura kiris da ikon Allah, umm Sorry ko, kar in hana ki barci, Nighty Night Bilby."

Ya katse wayar yana katsewa ta tashi ta shiga toilet tayi wanka,ta daura alwala ta yi sallar nafila raka'a biyu bayan ta idar ta karanta Fatiha da Amanar rasul ta yi salati ga Annabi Muhammad SAW sannan ta roki Allah da ya yi mata zabi na alkairi.
"Ya Ubangiji na ya Allah indai wannan bawan naka Alkairi ne a gareni ka kara kusanta zuciyata da tashi in kuwa akasin hakan ya Ar-rahman ina rokonka da ka lullube zuciyata da rahamarka tare da gujewa kasancewa da shi a kowanni lokaci, ya Allah kar ka bawa zuciyata damar aminta da wanda bai dace da ita ba, Allah ka bani ikon kasancewa abar alfahari ga duk wanda zaka zaɓa mun."
Sai da ta gama adduarta ta shafa sannan ta hau kan gado ta karanta adduar kwanciya barci , "Subhanaka Allahumma rabbiy bika wada'atu janbiy wa bika arfa'uhu, in-amsakta nafsiy fagfir laha, wa-in arsaltaha fahfaz'ha bima-tahfazu bihi ibadas-saliheena."
Ta shafa kafin ta kwanta cike da nutsuwa.

★★★★Bangaren zaid kuwa ya ci gaba da bincike kan Deejerh da bibiyarta tare da takaicin ta bar Mexico ba tare da ya samu ya aiwatar da mummunan muradinsa kanta ba.

Haka kuma duk da cewa yasan arean da Su Momyn Deejerh suka koma amman bai isa ya je ko ya tura ayi musu jagaliyanci ba,domin anguwace mai dauke da cikakken tsaro sai da su Khalil suka tabbatar da security din arean kafin suka amince aka yi komai.

Barci yake yi, hankalinsa kwance kawai ya ji bugu kamar daga sama.
Huda ce tana numfarfashi.
Cikin dagon murya ta ce, "Zaid ka tashi, zan haihu ,mu tafi asibiti, zan haihuwa."
Ta karasa maganar tana kara dukansa.
Tashi ya yi cikin sauri ya fara kiran waya drivern gidan ya tada mota kafin ya rike ta suka fita.
Kai tsaye suka yi asibiti.
Ko da suka je cikin sauri aka karbesu bayan an duba Ta Nurse din ta sheda masu cewa ta dan ci gaba da zagaya asibitin akwai dan saura kadan.
Zaid ne ya rike mata hannu suna tafiyan can ta tirje yana mata magana ta gantsara masa cizo tana fadin , "Mugu azzalumi da na san haka cikin nan yake da ban yi ba, gashi zan mutu."
Ta karasa maganar tana faduwa kasa gabadaya ta baje.
Fuska hawaye da majina duk sun hade ta ci gaba da sambatu.
"Ashe daman in anyi cikin mutuwa ake, aiko ban karawa,wallahi na hakura,ni wanna ma inda yadda za ayi su cire mun shi ba sai na haihuwa ba ka fada masu, su zo su cire kawai,na hakura, wallahi na hakura da haihuwar."

Shi dai Zaid tsayawa ya yi kawai yana binta da kallo a gefe.
Ganin ya maidata abun kallo ta janyo kafarshi sai da ya kusan faduwa cikin kuka da dagun murya ta kara fadin, "na ce maka ka je ka ce masu su zo su cire cikin na hakura da haihuwar, na hakura, wai ba za ka je ba?" Ta karasa maganar tana jefa masa takalminta.

Wata irin ƙara ta yi wacce sai da ta karade ilahirin asibitin.....
[6/5, 12:17 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-62

Kai ne ya fara bullowa.
Cikin sauri nurses din suka zo suka dauke ta aka shigar da ita dakin haihuwa.
Cikin ikon Allah bayan an ciro kan da fara fitowa wacce ta kasance 'Ya mace sai ga wani ma Namiji anyi nasarar cirowa.
Duk da cewa ta haihu amman bata daina hargagi da ihun cewa tana jin zafi ba har sai da ya kai ga nurse din ta kafa mata wani gigitaccen mari kafin ta samu nutsuwa hadi da yin shirun dole.

Bata kara ko gigin yin magana ba har suka gama shirya babies din ita ma suka gama kintsata.
Bayan ta dan samu hutu aka bawa Zaid damar shiga ya ganta.
Yana shiga idanunsa akan Yaran wani irin sanyi da bai taba zato ba bare tsammani shi ya ratsa masa zuciya, har cikin ransa lokaci guda yaje tsantsar so da kaunar wa innan yaran ya kamashi.
Hannunsa ya kai zai shafa masu fuska kafin ya ankare yaji saukar hannun Huda tana bige masa hannu.
Ya dago yana kallonta cikin yanayin tambayar me ya kawo hakan.

Wani irin kallon raini da baka isa ba ta mai tana fadin, "Yaran da baka iya kokarin komai akan zuwansu duniya har kana da karfin kallonsu ne bare daukan su? da sake fa ina fada maka koda zaka samu yancin taɓa yaran nan sai anyi yarjejeniya ka biyani aikin renon cikinsu da wahalar da na sha wajen haihuwarsu, in ko hakan ba zai samu ba,to su din yarana ne na har abada ni kadai."

Gabadaya neman farincikin da ke zuciyarsa ya yi, take bacin rai da wani ɗaci ya mamayeta dauke da takaici, Deejerh ya fara gani a idanunsa da Asher ya yi ma bakin sa wani irin cizon takaici.
Idanunsa sunyi jajir kallo guda za ayi masa a tabbatar da lallai yana cikin ɓacin rai mai girma.

Cikin wani irin sauti mai kauri da bayyanar da damuwa ya ce, "Please Huda, ki barni in tabasu ki bar ni inji cewa ni ma uba ne garesu kamar yadda kike uwa garesu zan biya ko nawa kike so indai zaki amince da su kira ni da sunan mahaifi kuma in amsa ka da kisa gazawar dana danne a zuciyata ta fito fili ta yiwa rayuwata illa."

Wata harara ta zabga masa ta gefe tana cire hannunta akan na shi kafin ta ce, "ni rayuwar ka bata dameni ba, kudi sune a gaba na and indai kasan zaka bani kudi shikenan ban da matsala amman dai kar a kurje mun yara domin ni da wa inda mukai wahalarsu kadai muka san zafinsu."

Maganar ta yi masa zafi sosai amman ba yadda zaiyi kuma bai da zaɓi illa ya ji yaran daf da shi kuma gareshi, hakan yasa ya kau da kai da duk wani furucin Huda ya taba yaran yana yi masu wasa, har a lokacin ban da tsantsar kaunar su babu abun da yake ji na kara ratsa masa zuciya.

★★★
Zaune Deejerh take a office.
Suna video call da Asher kamar yadda suka saba kullum sai sunyi waya kafin yake tafiya School.
Aka yi Nocking ta amsa.
Fayez ne ya shiga fuskarsa dauke da murmushi yana yi mata sallama.
Ta daga kai ta kalleshi tare da fadin, "Barka da zuwa."

Fayez ya ce, "barkanmu dai Bilby zan iya zama?"

Girgiza masa kai tayi alamar eh.
Ya zauna yana fadin, "Thank you."

Kallon Asher ya yi a tablet din da suke wayar ya ce, "Hi friend."
Ya fada yana daga masa hannu.
Kame jiki Asher ya yi yana kau da kai.
Deejerh ta ce, "Asher Uncle ne ka gaisheshi ka ji Abokina ne."

Juyo da kai ya yi yana daga masa hannu a hankali ba tare da ya ce komai.
Deejerh ta ce, "Yawwa Good boy."

Fayez ya ce, "How are you Friend?"

Muryar Asher ƙasa ya ce, "I'm Fine."

Deejerh ta ce, "Oya to lokacin tafiya School dinka ya yi, byee byee Take care, Love You."
Ta fada tana daga masa hannu.
Shi ma daga mata hannu ya yi, yana murmushi ya ce, "Byee."

Bayan ta katse wayar Deejerh ta kalli fayez ta ce, "Sorry Please wayar na sa matuƙar mahimmanci ne gareni."

Fayez ya ce, "Ba matsala ai kamar yadda take da mahimmanci gare ki nima yana da mahimmanci gareni domin duk abun da ya shafe ki nima ya shafe ni."

Murmushi Deejerh ta yi ta ce, "mu je ko nasan an kammala hada komai muje a duba domin tabbatar da sun fara aikin kan tsari."

Tashi ya yi yana, "Duk yadda kika ce haka za ayi Madam."
Shi ya bude mata kofar ta fita kafin shi ma ya bi bayanta.

Bayan sunje Dakin da ake fidda designs din sun tabbatar komai na tafiya yadda suka tsara zata koma office kenan fayez ya ce, "a mun taimako daya ko uzuri zance ne,kamar yadda na furta miki ina son na dunga samun lokacin kasancewa dake, tunda na san ba aikine da ke yau ba, Please ki bani dama ina so mu je mu dan zauna ya kasance daga ni sai ke koda kuwa coffe ne mu sha muna dan tattaunawa a coffee shop din da ke opposite da wannan companyn."

Deejerh ta ce, "Saboda me? Zamu iya zama anan ma ai kuma muna da coffe zan iya sawa a kawo mana,in ma zaman office dinne baka so sai muje Garden."

Fayez ya ce, "Aa Please ni nafi son can ki bani wannan damar."

Deejerh ta ce, "shikenan."

"Yesss Godiya nake Bilby muje ko." Ya karasa maganar yana nuna mata hanya da hannu.

Haka Deejerh ta tashi suka tafi coffe shop din ba don ta so ba sai don na ci irin na Fayez.

Sanyawa ya yi aka kawo masu coffe,sai da suka fara sha kafin ya ce, "kin ga nan gurin shine daidai da masoya zasu zauna su ji dadi tare da samun nutsuwa a zuciyoyinsu babban buri da fatana a yanzu bai zarce ace kiji cewa kin amince da cewa zaki iya rayuwa dani ba."

Deejerh ta ce, "Hmm, kana bani mamaki in kana ce kana so kuma zaka iya rayuwa dani, domin kuwa ni ba budurwa ba ce kamar yadda kake zato ko hasashe."

Fayez ya ce, "Saboda me fa?"

Deejerh ta ce, "ka ga wannan yaron dazu da muke video call da shi mai

Please Login or Register in order to submit comment