Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"nima zan koya ina kare kaina har ma da ke."

Deejerh ta zauna,ta tankwasa kafarta daya,ta kara tankwasa dayar.
Shi ma ya yi.
Sannan ta hada hanayyenta biyu ta dafa kasa.

Shima ya yi.
Amman take ya fara ficewa a hayyacinsa yanayin zaman a takure yake.

Deejerh ta ce, "yanzu haka,zaka kudirta kamar daure ka aka yi za ayi maka wani abu da bai dace ba,kana bukatar kwantan kanka,to abu na farko da zaka yi shine ka yi kokarin duk yadda zaka yi jikinka ya motsa, sannan ka fara kokarin daga kafarka ta baya."

Deejerh na jawabi yana jinta sanyi ake amman tsabar wahala da ragwanta zuface ta fara ketowa Ammar ta ko ina, fuskarsa duk ta jike da ruwa tamkar wanda ruwan sama ya kare akansa.

Shi dai amsata yake kawai da, "Tom...tommm...to..

Tana ci gaba da jawabi tana nuna masa,juyowan da zata yi ta ga mutum kamar wanda aka masa duka, mai Deejerh zata yi ban da dariya harda dungurawa.
Shi kam gyarawa ya yi daga position din ta bashi ban da haki babu abun da yake.

Sai da ta gama shan dariyarta kafin ta ce, "Yanzu Don Allah haka zaka zama jarumin? Da haka zaka iya wargitsawa wani hanjin ciki?." Take kuma ta bata rai kafin ta ci gaba da magana, "a haka zaka iya bani kariya in wani yazo cutar dani? Kai ma a haka zaka iya bawa kanka kariya? Bare kuma sauran al'ummar karkarar nan? Abar batun wasa ka fara batamun rai fa kana abu kamar ba Namiji ba? Miye hakan? Ni ba zan iya wannan shirmen ba." Ta karasa maganar cikin fushi tana tashi zata tafi.

Da sauri ya sha gabanta ,ya ce, "ni koma mene ne dai ban so inga kina bata rai, hankali na tashi yake Please ki saki ranki kuma yanzu nima abar batun wasa duk yadda kika yi zanyi In Sha Allah."

Deejerh ta kallesa, tsawon second uku suna kallon juna kafin ta kawar da kai tana, "shikenan let's go."

Abun mamakin kuwa daga lokacin duk yadda tayi sai ya yi ba tare da nuna raki ba har ya kai ga ita ta gaji daga karshe ma ta ce tana jin barci tu kun ya tafi suka yi sallama.

★★★wani mai taxi ne ya bigesa har saida ya kurje a fuska da hannu
Kuma ya bigesa bai tsaya ba ya gudu.
Haka ya tashi yaja kafarsa ya na bin gefen hanya yana tafiya yana tangal-tangal.

Da haka har ya samu karamin Medicine Store aka yi masa dressing inda jini ke zuba,tukun ya koma gidansa.

Kusan Kullum sai su Maira,Noha, Abiel da Daeej sun sa Meastro Roman gaba kan ya kira Nawar ko Ansan Inda Deejerh take.
Tun suna zuwa gidansu Deejerhn har sun gaji hakan yasa suke tarewa Roman tunda suka ga yana kiran Nawar ya ji ko ya samu kira daga gun Deejerh.

Yanzunma haka ba yadda ya iya haka ya kira Nawar din.

Duk da cewa kullum shima Nawar din cikin zillimin amsa kiran Roman yake da tunanin cewa zai sanar da shi anji labarin Deejerh.

Bayan sun gaisa Roman ya ce, "har yanzu dai baka ji wani motsin Deejerh ba ko?"

Nawar ya numfasa kafin ya ce, "kamar dai kai wallahi shirune,amman na yanke shawarar zan gwada tura yarana su dubata ko Allah zai sa a dace gaskiya ina yawan tunanin yarinyar nan zuciyata ta gagara samun sa'ida."

Roman ya ce, "ehto hakan ma mafita ce sosai, Allah yasa muji Alkairi."

Bayan sunyi sallama Roman ya kalli su Daeej kafin ya ce, "kun san dai ban son damuwarku kuma a halin yanzu kuna daf da zana Exams dinku na karshe ne da zaku kammala makaranta, ku cire damuwa aranku kuyi hakuri And Deejerh babu abun da take bukata a wajenku da ya zarce addua shine babban gatan da zaku mata taji dadi kuma ta gasgata cewa ku masoyantane na hakika duk halin da zata shiga." Da wa innan kalaman ya sanyaya masu jiki har suka hakura suka koma Class.

Mexico.

Cikin dare Deejerh kamar an tsikareta taji ta tsam idanunta sun bude,barcin ya tafi, duk yadda taso da ta koma barcin nan fir gagara ta yi, a karshe ma ta fara kokarin fita a hayyacinta,idanunta kawai Zayd ke nuna mata yana sex da ita,kuma sai take ji a cikin jikinta tamkar lokacin abun ke faruwa.
Tana ta kokarin kare kanta ta gagara ta sa hannu ta rufe kanta da jikinta tare da sakin wata irin gigitacciyar kara......

*Na shiga garari😭🥺na yi busy,ina cikin cakwakiya😭*

08103080717
[1/10, 11:10 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-32

Saida Ma'am ta farka a zabure kafin ta ga Deejerhn ta kankame kanta waje guda.

"Subhannallah! Sannu kinji Deejerhtou kiyi addu'a,."

Girgiza mata kai kawai tayi,ta tashi taje ta wanke hannunta,ta wanke fuskarta.
Har zata koma ta zauna ta kara komawa ta wanke, sai da ta wanke sau uku kafin ta fita a tsakar daren ta zauna tana daga kanta tana kallon sararin samaniya.
Kamar yadda Papi ya sanar masu duk rintsi suna kokarin rike kansu yanayin da hankalinsu yake kokarin gucewa, zasu daure da duk yanayin da suke ji,kuma ba kowani abu da Zuciyarsu ke laburta masu zasu yi ba, su danne wani domin tabbatar da cewa sun dawo cikin hayyacinsu cikin sauki ba tare da samun wata matsala ba.

Haka ta zauna tana kallon sama, duk wani tunani mara kyau da zai zo mata sai tayi saurin kawarwa aranta tana tursasawa kanta tuna abun farinciki,hakan yasa babu abun da take gani a sararin samaniya sai zane zane na kaya da ya zam muradinta.

Ma'am ma gagara komawa barci tayi ta fito wajen ta zauna a gefenta, har sai da gari ya kusa wayewa ta ji ta komawa daidai kafin ta kalli Ma'am ta ce, "mu koma ki kwanta nima yanzu zan iya barcin In sha Allah."

Ma'am ta ce, "indai kinji daidai barci bai ganmu ba ai sai munyi sallah ko da raka'ah biyune mun nemi gafarar Ubangijinmu,mun gode masa sannan kuma mu fada masa bukatunmu tare da kai kukanmu gareShi."

Hakan ne kuwa ya kasance Ma'am bata bari sun kwanta ba har sai da sukayi sallah raka'a biyu kafin suka koma suka kwanta cikin sa'a kuwa barcin ya kwashe su duka nan take.

Da safe kuwa ta tashi kamar ba ita ba, Aikin gawayi suka shiga yi tun sanyin safiya sai da suka kammala kafin suka yi abun karyawa suka ci.

Ranar dake ba School gida ta wuni tare da Ma'am da Ammar suna faman packaging gawayin bayan ya bushe.

Dake ta wajene bakin hanya mutane na wucewa, suna cikin aikin sai ga Abdu shi ma ya dauko buhun gawayinsa a baya zai wuce.

Ga hanya nan amman yaki wucewa ta gefe,ya bi tsakiyan su daidai kan kafar Deejerh ya taka.
Kafin ya ankare daga shi har buhun gawayin jinsu ya yi kamar an daga da sama an dire.
Take kansa ya yi wata irin gigitacciyar sarawa bakinsa kuwa jini ne ya fara kwarara.

Ma'am da Ammar tsabar tsurewa da tsoro sun rasa abun cewa gabadaya sun sake cikin yanayin tsoro.

Ita kuwa Deejerh ko a jikinta yi tayi kamar bata san ma meke faruwa ba ta ci gaba da aikinta.

Shi ko Abdu yana sa hannu a baki da yaga jini tashi ya yi da gudu yana ihu ya bar gun.
Sai a lokacin Deejerh ta saki wani gajeren murmushi tana kara packaging gawayinta.

Ma'am ta karasa gabanta tana, "Haba Deejerhtouna kin san hadarin mutumin nan kuwa? Me yasa da ya taki ki baki dauke kafar ba kawai,kinga haka na ji ma ranar kin mare shi,ga yau kuma kin dagasa kin dire ina tsoron kada ya cutar mun da ke,mugune."

Ammar ya ce, "Cab wannan lamari nidai da ace ba a idanuna ya faru ba aka fadamun zance karyane wallahi,abu kamar a film? Ni kam dai ni kaina da nake namiji ba zan iya wannan kasadar ba ai,ji yadda fa ta daga shi kamar ba mutum ba,ni na fara zarginma hanya kwana biyu Aljanu ba su shige ki ba ?"


Sai a lokacin Deejerh ta daga kanta ta kalli Ma'am kafin ta ce, "In har za ana zalinci kuma a ci gaba da shiru da tunanin cewa shine mafita, rayuwar mu ba zata taba ingata ba,kuma kullum zamu kasance a kasa ba tare da mun san darajar kanmu ba, bare muyi kokarin kareta, nikam dai na san bai isa ya mun abun da Ubangijina bai mun ba, kuma araina ina jin cewa yanzu lokaci ne da ya kamata raunina ya zama karfina kamar yadda kike kokarin karfafa mun a kullum."


Ammar ya ce, "tab duk da haka dai wallahi kiji tsoron Abdu."

Wani kallo da Deejerh tayi masa take ya yi shiru yana ajiyar zuciya.

Ma'am ta ce, "kina da gaskiya amman nidai ki kiyaye lafiyar ki tafi Komai Mahimmanci."


★★Bayan Sati Ɗaya.
Ya kasance Weekend Deejerh na gida ba su da School kuma daman a Weekend Papi yake masu Therapy Session.

Hakan yasa ta shirya ta tafi.

Ranar kuma ya kasance ranace da ya ware masu domin yin tambayoyi game da yanayin da sukan iya shiga da ma komai.

Deejerh ce ta yi tambaya kan cewa, "Shin Mutum na iya warkewa gabadaya daga Ocd disorder?"

Papi ya ce, "Nop! U can get it under control,but at present time there's no cure sai dai mutum ya yi kokarin kiyayewa ta hanyar karbar Therapy kamar yadda muke yi,amman maganar tafiyar cutar Gabadaya babu ita Therapy shine mafitanta kuma maganinta muddin mutum zai karbi shawarwari kuma ya yi aiki da su yadda ya dace zai rayu kamar kowa da ikon Allah."

Ammar ne ya daga hannu da fadin, "Can People with Ocd Fall In Love?" (Masu dauke da cutar zasu iya fadawa soyayya)

Yana fada duka sauran mutanen suka kwashe da Deejerh kuwa ta kalleshi ta kau da kai, Shi kan shi Papi sai da ya yi kafin ya ce, "Su ba mutane bane? OCD petient don't need to feel paralyzed by their symptoms and can go on to engage in healthy, fulfilling relationships (masu dauke da cutar ocd babu bukatar suji cewa su nakassune ta wani bari da alamominsa,kai tsaye zasu iya fadawa soyayya cikin lumana da kaunar juna kuma soyayyarsu mai inganci ma kuwa) kila har su fi wa inda basa da cutar iyawa da tsarawa.."

Nan wata ma ta daga hannu tana tambayar, "But Sir Does Ocd go away if you ignore it?"

"Ignoring symptoms of OCD will not cause them to disappear, and they're not going to just go away. That's not the way OCD works. In fact, ignoring symptoms, telling yourself that you're not really that bad and you can manage the disorder by trying self-help for OCD will only exacerbate the situation (Share Alamomi ko ince banzantar da alamomin wannan cutar ba zai taba sawa cutar ta tafi ba,ba zata taba tafiya ba,don hakan ba ya taba aiki, Don haka duk mai tunanin wannan cutar na iya tafiya gabadaya don an shareta ma ya daina, Ataimaka ma yin burus da alamun babban hadari ne da zai kara habbadakar da cutar ga wanda yake ganin cewa bai dauke da ita)
koda ace ana kula da ita sai dai asamu daidaito ba dai waraka duka ba kamar yadda na fada a amsar tambayar da akayi a farko."Papi ya fada.

Da wannan tambayar suka tashi kasancewar lokaci ya yi.

Suna cikin tafiya Ammar ya ce, "ni fa Sauri-sauri nake yau mu koma da wuri inje muyi MMA training dincen ya fara bin jikina har ban jin dadi in banyi ba."

Ko kallon shi bata yi ba ta ci gaba da tafiyarta.
Ya kara fadin, "Allah kuwa yanzu nafi jin dadin jikina ma fiye da baya yanzu ne na fara jin cewa ni din namiji ne."

Deejerh ta masa shiru yanayin fuskarta duk ya sauya.
Ammar ya yi kasa da murya kafin ya ce, "yi hakuri inni na bata miki rai,na ga kamar Ranki ya baci nayi shiru."
Ta girgiza masa kai alamar aa.

"To mene ne? Don Allah ki Fadamun damuwarki ni kuma nayi alkawarin magance miki ita indai bata fi karfina ba da ikon Allah."

Deejerh ta ce, "Gobe 2weeks kenan da fara zuwana Stylish Wordplay fashion School kuma gobene rana ta karshe ga duk wani Students dai bai sai Design Materials dinsa ba,kudin gawayin da muke tarawa har yanzu ko rabi bai kai ba, kuma kasan a School din ake siya,so yanzu ban san yadda zanyi ba,babu mafita."

Ammar bai ji dadi ba,har cikin zuciyar sa yake jin cewa dama da yadda zaiyi ya taimaka mata kasa magana ya yi sai cen sun ci gaba da tafiya ya ce, "Ubangijinmu na tare damu kuma na san ba zai bamu kunya ba,In Sha Allah kafin zuwa safiyan za asamu mafita kije ki biya karki damu kinji Don Allah ki cire damuwa aranki Duk yadda Allah ya tsara shine daidai kuma Alkairi bare ina ji a jikina cewa samun ne Alkairi."

Da haka suka isa har gida yana kwantar mata da hankali.

Dake a gidan Ma'am yake cin abinci yana gama ci ya ce zai tafi.
Deejerh ta ce, "Ah ba zaka tsaya training din yau ba?"

Ammar ya ce, "Na tuna ne dazu papi ya ban sako inje in kai ,inna dawo da wuri zan Dawo muyi." Ya fada ya na wucewa da sauri.

Deejerh bata bari Ma'am tasan kudin nan bai kai mata na siyan kayan ba, hakan yasa ta kwanta tayi shiru kamar tana barci wanda ba barcin take ba kawai dai ta rufe ido ne gudun bata so ta fahimci tana cikin damuwa ita ma ta shiga.

Ammar na fita kuwa kai tsaye dakinsa ya nufa ya tona wani rami da ya ajiye Coin (tsohon kudi na karfe) dinsa na gado,shi kadai ne abun da babansa ya bar masa gado ya adana wani mutum nata binsa ya siyar masa sam yaki duk da cewa lokuta da dama bukata kan taso masa amman ya zabi hakuri yau kam ya yanke hukuncin shiga cikin gari ya kaiwa mutumin ya siyar masa domin tabbatar da cikuwar burin Deejerh.

Ga yanayin garin hazo ne sosai da wani irin sanyi mai taba ƙasusuwa Amman hakan ya yi shigar sanyi ya fara naƙar hanya kasancewar dare ya yi bazai samu abun hawa daga kauyen zuwa cikin gari ba.
Kuma motarshi ta samu matsala tana ajiye.
Haka ya dunga tafiya cikin sanyi shi kadai.

Sanyin na kara busawa sosai wanda zai iya taba lafiyarsa har ciwon sa ya tashi,

Sanyi na kadawa jikinsa na ɓari haka ya ci gaba da aikin,zuciyarsa babu abun da ke hangowa sai farantawa Deejerh.
Kafin ya isa dare ya tsala sosai saidai sa'arsa daya mutumin na shagon sa bai rufe ba.
Hakan yasa ya shiga ya basa ya caske masa kudin sa €500 cikin Farinciki domin Real Coin ne asalin masu kyan da ake nema.

A hanyar sa ta komawa asuba tayi,ya tsaya ya yi sallah.

Yana komawa kauyen kuwa kai tsaye gidansu Ma'am ya nufa yana leke,cikin sa'a kuwa ya hangi Deejerh ta fito alwala.
Kwala mata kira ya yi a hankali.
Ta daga kai ta ganshi da mamakin ta ta karasa gabansa tana tambayar ko lafiya.
Ciro kudin ya yi kawai ya mika mata, "gasu nan zasu yi miki aiko?"

Bude baki Deejerh ta yi ta ce, "€500fa, ina ka samo su?"

Ammar ya yi murmushi ya ce, "Coin din gadona na Saida ."
Deejerh ta ce, "What? Meyasa to? Kuma a wannan sanyinma ka fita? Ciwonka zai iya tashi, gaskiya in gari ya waye zamuje mu koma a karbo a basu kudinsu."

Murmushi ya mata kafin ya ce, "Allah zai kare,nidai fatana kudin nan ya biya miki bukatunki domin ba maidawa za a ayi ba,kuma in kikace bazaki karba ba, kin nuna mun cewa ni ban da wani matsayi agunki kenan."


ta yi shiru sai kuma can ta daga kudin kafin ta ce, "Daman akwai €50 kuma €150 shikenan kudin sun kai ka rike sauran €400 ta mika masa."

Ammar ya ce , "Alhmdu Lillah." Yana daga hannunsa sama.

Deejerh ta kalli shi kafin ta ce , "Na gode sosai Allah ya saka da Alkairi."
Murmushi ya mata kawai ya tafi.

Yana tafiya kuwa kafin ya isa gida numfashinsa ya fara kokarin daukewa da kyar ya rarrafa ya shiga dakinsa.

Deejerh farinciki tama rasa ina zata sa ranta, cikin sauri taje ta hada kudin da Wancen gu daya.

Ta yi sallah sannan ta fara aikinta da farinciki har gari ya waye ta shirya tsaf ta nufi School.
Tun daga bakin Gate din School din ta fara hango abun mamaki zuciyarta ta fara bugawa.......


08103080717
[1/11, 1:36 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-33

Musamman yadda ta ga gabadaya sauran students da staffs din duk sun maida hankalinsu kanta kowa ya zuba mata na mujiya.

Ta sunkuyar da kanta kasa jiki a sanyaye tana tafiya har ta karasa daidai gate din ta tsaya ganin ba hanyar wucewa.

Jin saukar Steamer Ak ta yi ta ko ina yana bade mata fuska da jiki.

Kan kace wani abu gurin ya bade da tafi.
Cikin yanayin rashin fahimta take binsu da kallo.

Mr Jacques ne ya tsaya gabanta da Mr Laurent agefe sai kuma wani staff dinsu ma Anthony.

Mr Jacques ne ya fara magana, "Congratulations Dear, Kinyi matukar kokari,kin kara tada mana daraja da kimar makaranta cikin al'umma, atakaice mun kara zamtowa na musamman sanadinki kuma silarki wanda a yanzu kaf Paris mune sahun gaba a best fashion School So Here is Your Gifts."
Ya mika mata wani Box wanda samansa ya sha ado gefe guda kuma aka rubuta Stylish Wordplay fashion School Design Materials.

Kasa rufe baki ta yi don Farinciki kawai tana binsu da kallo,ga wani hawaye dake ambaliya a fuskarta da bata da ikon tsaida sa.

Mr Laurent ya daga wani tag da aka rubuta Stylish Wordplay fashion best student
Ya sanya mata yana, "Congratulations once again Dear, mun dauki design dinki mun fidda wanda fitarsa har ya yi inda ba mu yi zato ba bare tsammani, muna matukar alfahari dake tare da yi miki fatan Alkairi sannan muna fatan samun mafiyin hakan daga gareki."
Girgiza masu kai take kawai ta rasa abun cewa.

Mr Anthony ma ya mika mata wani karamin Box yana , "Congratulations Girl na maki murna matuka kasancewarki mai karancin shekaru kuma da baiwa yanzu lokacin kine so kada kiyi wasa da ita Please Stylish Wordplay fashion School are proud of you."

Sai a lokacin ta iya furta thank you cikin rawar murya tana share hawaye.
Haka sauran students din suka dinga zuwa suna mata murna da masu yi da zuciya daya da masu yin na bakin ciki domin Esme ma kinyi mata tayi ta gagara danne zuciyarta kai tsaye ta tafi Class.

Bayan an gama Mr Laurent ne yasa aka kwashe mata Gifts din duka aka hada waje guda tare da fada mata cewa in an tashi ta dauka ta tafi da su.

★★★Clothes Idol ya tsaida gaban lecture room din.
Kafin ya ce, "Duka ina bukatar hankulanku da nutsuwarku nan, Karatun mu na yau zai kasance practical ne, kuma a yanzu za mu yi,mu gama, Gown , da farko muna bukatar sanin ita kanta ma Gown din mece ce?
:a distinctive robe worn by a professional or academic person, a woman's dress,yes shiga ce ta mata kamar yadda kowa ya sani, And duk da haka ma muna bukatar sanin What type of dress is a gown? wani irin shiga ne gown? Oya let's go...
A gown, from the Saxon word, gunna, is a usually loose outer garment from knee-to-full-length worn by men and women in Europe from the Early Middle Ages to the 17th century, and continuing today in certain professions; later, the term gown was applied to any full-length woman's garment consisting of a bodice,ina fatan kuna tare dani?"

Suka amsa da yes Sir.
Kafin ya ci gaba da jawabinsa, "Oyaa , What are the 3 types of dress?
These three types of dresses vary according to the length of the dress. Mini, being short and above the knee. Midi is mid-calf length, and maxi is a full length to the ankles style of dress.
But muna bukatar sanin bambancin dress da kuma Gown An essential difference between gowns and dresses is that a gown is often for a more formal setting, whereas women can wear a dress for both. In other words, A gown can only be a gown, but a dress can be a dress and a gown.
Yanzu za muyi simple middle gown.
Wacce za a iya zuwa da ita party kuma za a iya sawa normal a gida.
As u can see zamuyi amfani da clothes idol Dinnan ne,ga material dinmu nan plan yard bai da hayaniya amman Daga ido ma ya na daukar hankali kasancewarsa Unique.


Bayan ya yanka ya nuna masu,Jikin Idol din ya sa Yard din sannan ya dannesa da Stick ya cire hannun ma ta sama yana yi yana yi masu bayani sannan yazo daidai gaban rigar ya yi bending yard din step by step ya kwanta sosai ya fidda ado wanda ya fita sosai ba hayaniya.
Cikin 30 mins ya kammala rigar kuma ta fita sosai.

Ya ce, "Rigar ta fita sosai jikin Idol dinnan amman kun san cewa zata fi fita ajikin mutum?"

Suka ce, "Yes Sir."

"Yawwa tom yanzu zan ciro Gown din, Deejerh zata je ta sanya ta a jikinta yadda zamuyi observing final results of our today's class."

Ya cire ya bata ta fita ta sanya.
Gabadaya Gown din ta fito mata sharp din jikinta kuma sai ta tafi da jikinta daidai tamkar wacce aka yi dominta ko ince tamkar a jikinta aka dinka, musamman Kasancewar tana da diri mai kyau hakan sai ya kara fito da surarta Sosai.

Kanta a kasa ta fito jikinta na mata dardar har ta koma lecture room din nasu.
Tana shiga kuwa kamar an dauke ruwa dukaninsu suka yi shiru suna binta da kallo,daga mazan har matan harda masu sake baki.
Sunyi matukar mamaki wani namiji bai san lokacin da ya furta ba, "Ashe yarinyar nan boye kyanta take? Oh My God."

Wata Camille kuwa ta ce, "Hot Girl."
Ta fada tana wani irin ajiyar Numfashi.

Sai a lokacin Mr Laurent ya ce, "Great we got what we want, kamar yadda kuke gani rigar ta fito da dukkanin wani sharp da aka yi mata ta hanyar bin jiki ko ince tafiya da jikinta, da ace wani abu bai yi daidai ba dole anan zai nuna but komai ya tafi ,zamu iya ci gaba da tafiya."
Ya kalli Deejerh dake tsaye cikin takura kanta na kasa ya ce, "Thank You Girl zaki iya maida kayanki."

Yana fada kuwa da sauri har tana hardewa ta shige ta canja kafin ta koma seat dinta ta zauna.
Esme ta kalleta tana galla mata harara ita kuwa ta sake mata murmushi.

Suna fita daga lectures Deejerh ta kwashi kayanta tana sauri kar ta rasa Bus ,ji tayi kawai an rugumeta ana shige mata jiki, cikin tsoro da firgici ta kauce , Camille ta rike mata hannu tana murza tare da fadin, "Sorry Dear, I Just Need To Hug You, in ban yi hakan ba bazan ji sanyi araina ba."

Kokarin kwace hannunta Deejerh take amman sam ta gagara kwacewa.
Camellia ta kara fadin, "Kina da kyau sosai , zan iya zama kawarki Please?" Ta karasa maganar a raunace.

Girgiza mata kai kawai Deejerh tayi domin babbar damuwarta bai zarce ta sake mata hannu ta tafi ba.

Ta kara sakin wani gajeran murmushi kafin ta ce, "Thank you, na ga kamar kin gaji gobe zamu hadu kinji,take care of yourself for me please."
Ta saketa tana kissing mata hannu tukun ta tafi.

Tana tafiya Deejerh tayi ajiyar zuciya tare da furta, "la ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz-zalimin."
Addu'ar da ta ci gaba da furtawa kenan har ta samu ta karasa fita ta samu Bus ta shiga.

Tana zuwa daidai indai bus stop dinsu yake na shiga kauyen ta hango Ammar zaune yana gyangyadi.
Murmushi tayi ta samu wani tsinke ta sa masa a kunne.
Tuni ya saki wata kara yana tashi, da ya ga ita ce kuma sai ya wayance.
"Ke mummunarnan bakya jin magana."

Yana fada kuma sai yaga tarin kaya gabanta.
Da sauri ya durkusa yana, "Ah wa innan abubuwan fa?"

Ta sa hannu a aljihunta ta ciro kudin da ya bata ta danka masa a hannu kafin ta ce, "A school amun kyautar kayan aikin saboda Jeans dinnan da na baka labari na yi, ka ga ma harda award da wani abu acikin box shine ban san mene ne ba."

Washe baki Ammar ua fara yi yana fadin, "Alhmdu Lillah, Alhmdu Lillah, Alhmdu Lillah , Allah abun godiya gaskiya na ji dadi sosai kin ga ke fa muninki a fili ne kawai amman kwakwalwarki kyakkyawace inaga filinma zan miki addua kiyi kyau."
Deejerh ta ce, "ka ji dashi dai, mu

Please Login or Register in order to submit comment