Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duniya ta yi masa zafi ga lamarin Huda ga kuma lamarin kamfaninsa da aka sawa ido yanzu ba dama suyi kwakkwaran motsi abubuwa na shirin tsaya masu cak.
Daukan wayarsa ya yi ya fara searching Companies a internet ko da wanda zai iya amfani da sunanshi da komai na shi suna fitar da kaya cikin kwanciyar hankali ba tare da an kawo masu hari ba.
Yana cikin dubawa kuwa kawai sai ya ci karo da wani fashion Design Company "Deejerh's Couture"
Ganin kamfanin na da mabiya sosai a internet hakan ya tabbatar da cewa sananne da sauri ya tashi yana Farincikin ya samu inda zai rabu ya yi kasuwancinsa a sininnike.
Shiga bayanan kamfanin ya yi, abun da ya fara ganine yasa shi saurin tashi cike da mamaki har yana kokarin faduwa,Hoton Deejerh ne agun matsayin shugabar Kamfanin.
Kasa rike mamakinsa ya yi cikin dagun murya ya ce, "What? Deejerh? Yarinyar nan? Ita ? Ita ce fa, tana raye?"
Har Glass din idonsa ya cire domin tabbatar da cewa itan ce ko kuwa gizo ne.
Babu shakka Deejerh ce domin kuwa duk da ta girma amman kamaninta sam bai sauya ba sai ma kara fitowa da yake.

Can kuma sai ya fara dariyar mugunta.

"Ya ma zo cikin sauki,yanzu ne zanyi business yadda raina ke so, ko da bincike zai tashi ba za a taba tunani ba ba ma za asan waye ni ba,wato yarinyar nan tana raye,ta je tayi kudi har tana kokarin fina, ni ina nan ina shan wahala da fargaba, Hmm mafita tazo."
Wani irin kayataccen Murmushi yake sakewa take ya dau keyn motarsa ya rufe office din ya nufi gida.

★★Momyn Deejerh har yanzu bata da wani nutsuwa da walwala a tare da ita, a duk lokacin da ta zauna ita kadai cikin kadaici,babu abun da take tunani sai Deejerh da kara jin cewa duk abun da ya faru da Deejerh ita ce sanadi,alhaki akanta hakan yasa ta kasa samun sukuni sam.
Aduk sanda tai tunaninta tayi kuka ta kan share hawayen ta kafin ta daga hannunta sama ta roki Ubangiji kan ya kare Deejerh kuma ya tsareta aduk inda zata kasance a fadin duniya.

5Stars Expensive Company
Farouk ne ya hada musu conference call su biyar, Zeeyter,Zahra, Haiydar,Khalil sai shi suna tattauna kan yadda tafiyar su Australia zata kasance da ma abubuwan da ya kamata su yi.

Zahra ta ce, "Inda hali tunaninmu ya kai ga abubuwan da zasu bata mamaki su sata farinciki matuka."

Khalil ya ce, "Yes Kun san Disordern ta ya kan motsa so ina tunanin in aka yi abun da ya faranta mata rai sosai zata dan fi samun nutsuwa da walwala."

Farouk ya ce, "Sosai ma duka zamu kasance tare kuma a lokaci guda wannan aikin nakune Yar Guntuwa da Gimbiyata ku tsara kamar nawa muke bukata sannan ku rabawa kowa aikinsa."

Karaf Haiydar ya katsesa da fadin, "Ni ban ji kuna batun girke girken da za ayi ba ranar ko nufinku da yunwa zamu zauna?"
Dukansu basu san sanda suka tintsire da dariya ba.

"Food Master ba za dai ka canja halinka ba, wannan sai azata bana baka food dinne ai." Zeeyter ta fada tana galla masa harara.

Shi ma ya maida mata harar yana, "e mana bakya bani yaushe rabonki da ki min girki da kanki?"
Filo ta dauka ta jefa masa yana mata gwalo.
Ganin tana kokarin tashi tazo inda yake da gudu ya tashi ya shige dakinsa yana dariya tare da fadin, "Hey Farouk ka yiwa Friend dinka warning fa tun kafin in zauneta."

Dariya Farouk ya yi ya ce, "zaunewa kam ai saidai abaki amman kasan Gimbiyata tafi ƙarfinka."

Zahra ta ce, "Wa innan mutanen fa baza su tsufa ba, kullum cikin rigimar soyayya suke wani kuwa kullum cikin ciwon barci yake."
ta fada tana kallon khalil.

Dariya ya mata ya matsa daf da ita yana yi mata kiss kafin ya ce, "muma ai kullum cikin soyayyar muke kuma kina raina har cikin barcin ma mafarkinki kawai nake."

Farouk ya ce, "eheem bara dai in katse wayar nan kuje kuyi fin hakan ma naga alama cin fuska ake son yi min dole in nemo ko yar bazawara ce mu sasanta."

Dukansu suka kyalkyale da dariya.

Farouk ya katse kiran Su Noor suna shiga dakin sun dawo daga School kenan.
Da sauri Anitha da Anushka suka je suka rugeme Khalil har suna bige Zahra.
Tsayawa tayi tana kallonsu ta ce, "eheen ni da mijina za a tureni a jikinshi?"
Anushka ta ce, "Ai dadynmu ne mu kadai."

Noor ne ya rike ma zahra hannu sannan ya rugumeta yana, "ke ma Momyna ce ke kadai kowa ya rike na shi."
Suka tafa.

Zahra ta je daidai kunnen Noor ta fada masa wani abu.
Da karfi ya ce, "Wooo Alhmdu Lillah, Thank you Mom, Thank you so much,Love You ya fada yana kara rugumeta."

Nan hankalinsu Anushka ya dawo gun don sun san tabbas da wani abu da aka shiryawa Noor.

Da suka zura masa ido ya ce, "mene ne? Ba kun rike Dadyn ku ba? Mom ta mun Fevorite food dina kuma sai kuje dad ya muku." Ya na fada ya musu gwalo ya nufi kitchen.

Cikin yanayin shagwaba suka kalli Zahra suna, "Please Mom...

Murmushi ta musu kawqi ita ma ta tashi tabi Noor.
Suka kalli Khalil kamar zasu yi kuka.
Ya ce, "aa fa kar kuyi kuka nasan me zan yi zamuje mu dauke abincin ne mu buya mu cinye."

Aiko sai da Noor ya diba suka fito daga kitchen din suka yi dining area tare.

Sai da suka gama ci.
Zahra ta shiga daki tana duba kaya,shi ma Noor bayan ya yi sallah ya dauko Game yana yi.

Suma Anuska duk saida suka yi sallar.
Kafin Khalil ya lallaba ya shiga kitchen suna yi masa gadin Zahra da Noor ya dibe masu kafin ya je su suka fita.
Motarshi suka shiga suna ci suna dariya.

Zahra ta fito zata nunawa Khalil abu ta nemesu sama da kasa bata gansu ba.
Tana duba kitchen ta ga wayam abubuwan da ta rage.
Aiko da sauri ta fita.
Ta kara dubawa bata gansu.
Kamar zata koma ciki sai kuma ta kara fitan tana juyawa daidai gun motar Khalil taja kofar ta bude dake sun manta basu rufe ba.
Tana budewa duka idanun su akanta.
Tsuru-tsuru suka yi alamun rashin gaskiya Zahra ta....

★★★

*SAI BAYAN SALLAH IN SHA ALLAH ZAMU CI GABA MU KARASA A GYARA ZAMA 😻💃INA KAUNARKU DUKANKU MASOYAN VIXEEN, ALLAH BIYA BUKATUNMU NA ALKAIRI ALLAH SA AYI KARBABBIYAR IBADA.*
08103080717

[4/29, 8:20 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-49

"Oh Allahna, wato Uba da 'Ya'ya duk halinsu daya? To na kama ku, kuma zaku sani."
Dukansu a tare suka kwashe da dariya harda zahran.
Khalil ya ce, "ba ni da yarana za ama rowa ba, dole mu dau mataki."

"Allah ya shiryaku duka,ku zo mu je ciki kunsan dai muna da batun tafiya Austaraliya so akwai shirye-shiryen da ya kamata mu karasa ina tunanin ma zamu kasuwa."

Dukansu suka hada baki a lokaci guda suka ce, "Alright Madam."
Zahra ta yi murmushi kawai ta shige cikin gida suna binta a baya.
★★
Zayd na nan ya gama tsara komai nasa yadda zai na shigo da gurbataccen kasusuwan hada cream dinsa na kari da kuma drugs da sunan kamfanin Deejerh abubuwa na tafiya masa daidai kuma yana jin dadi.

★★★
Khalil na zama a palour sai ga kiran Xavier.
Ya yake video call ya kira yana amsawa Khalil ya hango Asher gefe dauke da peper da pen yana ta Designing jagwalwalonsa.
Khalil ya ce, "Emm Hi Asher, How are you?"

Ya daga kai ya kalli Khalil ya ce, "I'm fine."
Yana fada ya sunkuyar da kansa ya ci gaba da abun da yake yi.

Khalil ya kalli Xavier ya ce, "har yanzu dai yaron nan bai sakewa."

Xavier ya girgiza kai yana fadin, "kin ga nutsuwar shi to in bar shi yana wancen zane zanen anan ne kawai zaka ga har shi kadai yana murmushi wani lokacin amma kasan shi sarai wani lokacin ko nine zan masa magana in bai so ba ba zai taba kulawa ba."

Khalil ya ce, "ba matsala a hankali dai Indai zai samu yata zanen zai dan daidaita Ina Sha Allah."

Xavier ya ce, "I hope so, yawwa na ce ba,na dauki hutu wajen aikine,nima ina son zuwa Austaraliya dani za aje ya tsarin shirye-shiryen tafiyar taku yake ne?"

Khalil ya gyara zama, "Austaraliya? Woo amman ko na ji dadi sosai ko ba komai Asher zai shiga cikinsu Noor ya dan sake, tafiya muna kan shiri kenan zuwa next week monday."

Xavier ya ce, "Ok to ina ga zamu hada tafiyar kawai"

"Alright ." Khalil ya fada.

Hirarsu suka dan ci gaba da yi sannan
Da haka suka yi sallama.
★★
Deejerh zaune sai ga Ammar ya shigo domin daman yana gidan yaje mata weekend.
Zama ya yi yana tsaki.
Deejerh ta kallishi ta ce, "ya dai lafiya?"
Ya daga wayarsa yana, "kin ga ban san yaushe yarinyar nan zata yi hankali ta gane cewa kinfi karfin inyi soyayya dake ba,sai dai kasancewar mu ta tamkar yan uwa jini daya, ta dage akan cewa lallai soyayya muke wai ana danne mata haki."

Dariya Deejerh ta yi ta ce, "Au da wasa muke? Me yasa baka fada mata gaskiya ba? Ni to bara in kirata in fada mata."
Sake baki kawai Ammar Ya yi yana bin Deejerh da kallo ta karbi wayarsa ta kirata.
Tana dauka ta ce, "Kin san mene ne? Labarine zan fada miki kuma gaskiyar da in kika dauka kin hutawa ranki , Ammar ya zarce masoyi aguna sai dai ince jinina,kinga kenan mun zama ɗaya,in zaki iya zama damu haka shikenan in kuma ba zaki iya ba saidai kiyi hakuri,ni nama fiki kishin nan fa kawai daga miki kafa nake ina kawar da kai." Tana gama fadan hakan ta mika masa wayar ta tashi ta shige cikin daki.

★★★
Bayan kwana hudu..
Zeeyter,Haiydar tare da baby Aiza sun dauki hanyar Austaraliya.
Haka ma Zahra, Khalil da su Noor, da Farouk ,Xavier ma da Asher sun bi su Khalil.
Amman duk sun shirya sauka a hotel ne tare sai sun gama haduwa kafin su wuce gidan Deejerh.

Hakanne kuwa ya kasance
Hotel fate suka sauka duka,sai da suka yi wanka suka ci abinci kafin suka nufi hanyar gidan Deejerh.
Asher na tare da Xavier yaki sakewa sam yara nata wasansu amman ban da shi.
Zeeyter kuwa Uwar yara gaba daya yaran sun baibayeta anata wasa da dariya.

Jin alamun shigar motoci gidan yasa Deejerh saurin daga labule tana lekowa ganin motoci uku yasa ta kasa hakuri da mamaki ta fito cikin zumudin ganin su waye ne.

Suna fara fitowa kuwa wani irin ihu ta sake na farinciki tama rasa yadda zata yi tana rike baki.
Can kawai ta karasa da gudu ta rungume Zahra, sannan ta rungume Zeeyter.
Cikin salon tsokana Farouk ya ce, "ki bar wani murna tafiya zamuyi ba gunki muka zo ba."
Galla masa harara tayi ta ce, "Aiko saidai in kai kadai zaka tafi."
Su Anitha da gudu suka rungumeta.
Ganin Asher tsaye jikin Xavier yasa ta je ta durkusa gabansa tana miki masa hannu fuskarta dauke da murmushi.
"Hi sabon aboki."
Kura mata idanu ya yi kawai ba tare da ya ce komai ba.
Wani murmushin ta sake yi masa sannan tasa hannunta ta daukesa.
Sai da Xavier ya yi mamaki ganin yadda ta daukeshi ba musu ya yarda da ita.
Shiga gidan suka yi duka ana wasa da dariya.
Ammar ma ya dawo duk suka hade.

Deejerh ta ce, "amman dai kun shammaceni matuka,koda wasa banyi tunanin zuwanku ba."

Tashi Khalil ya yi ya ce, "ni dai abani keyn daki ina so inyi barci."
Ta ce, "aiko dai ba barcin da zaka yi yadda kowa ke zaune anan haka kai ma zaka zauna kana jina ko?"

Farouk ya yi dariya kafin ya ce, "To mijin Hajiya, hajiya ta ce ba barci sai a zauna ko."
Dukansu suka yi dariya.
Xavier ya kalli Zahra ya ce, "Madam a mana hakuri a bamu keyn nan nima ina so in dan shiga daki."
Zahra ta ce, "kawai saboda kaine yallabai."
Deejerh ta dauki keyn dakin ta mika masu suka shige.

Haiydar kuwa yana kwance da kansa cinyar Zeeyter ya yi dare-dare yana danna waya.
Farouk ya kallesa ya ce, "kai kam wai ba za ka mun gimbiya ta huta bane? Kai fa ka fiye na ci."
Zeeyter ta ce, "kamar cingum ba, har gwanda mun Aiza akan wannan in bai so ba,ba zai taba bari inyi abun da ya dace ba."

Haiydar ya gyara kwanciyarsa yana fadin, "Umm kwaji da shi dai ."

Xavier na shiga dakin ya bude system dinsa yana bincike.
Khalil ya kallesa ya ce, "a hutun ma sai anyi aikine?"
Murmushi Xavier ya yi,ya ce, "ba wani babban aiki bane, duba abu zan yi kawai."

Khalil ya girgiza kai kawai ya juya.

Zahra da Deejerh kuwa shiga kitchen suka yi, suka fara hada abun da zasu yi dinner da shi.

Daga karshe zeeyter ma ta bi bayansu Haiydar da Farouk tare da Ammar suka fita karamin garden din gidan suna hutawa.

Lokacin sallah nayi Khalil ya cewa Xavier zaije suyi sallah.
Xavier ya ce , "Ok bara nima in fito ko iska na sha."

Alwala duka suka yi a wajen alwalar da aka tanada a garden din.
Sannan Deejerh ta shimfida masu wani katon carpet.
Xavier na zaune yana kallonsu.
Aran shi yana kara jadadda cewa rayuwar musulunci na matukar birgeshi.
Khalil ne ya ja su.
Su mazan na gaba matan na baya, gashi dukkanin su matan sun sanya doguwar abayar da ta rufe musu surar jiki da gashin kansu.
Har suka idar idanunsa na kansu.
Bayan sun idar yake fadin, "ni fa kullum kara birgeni addinin nan naku yake,komai naku cikin tsari , gashi kun nutsu kuna bautawa Ubangiji nima dai inaga zan gwada watarana ko anjima in za ku yi."

Zeeyter ta ce, "Why Not? Aiko ka gwada na san zaka ji dadin hakan sosai har cikin ranka sai ka ji wata irin nutsuwa da baka taba samun kanka ciki ba, addinin musulunci addinine mai dadi da son kyautatawa zan so ace ka kasance cikinmu."

Shiru Xavier ya yi daga nan bai kara cewa komai ba.
Zasu tashi kenan Zeeyter ta kalli Noor ta ce, "Oyaa Young Shiek a mana addua tukunna ko."
Noor ya zauna ya daga hannunsa sama su Anitha ma suka daga ya fara da.
"Allahumma antassalam waminkassalam tabarakta ya zaljalali wal ikram Allahumma Salli ‘ala Muhammadin wa ‘ala aali Muhammadin, kama sallaita ‘ala Ibrahima wa ‘ala aali Ibrahima innaka Hamidum-Majeed. Allahumma barik ‘ala Muhammadin wa ‘ala aali Muhammadin kama barakta ‘ala Ibrahima wa ‘ala aali Ibrahima innaka Hameedum-Majeed.
Rabbana-ghfirlī wa liwālidayya wa lilmu'minīna yauma yaqūmul-hisāb."

Duka suka amsa da Ameen kafin suka tashi da gudu suka shige cikin gidan.

Abinci ya yi Zahra ce ta shirya musu komai kan daining
Suka zauna suka ci tare ana wasa da dariya.
Bayan sun gama.
Yara suka yi dakinsu.
Khalil da zahra , Haiydar da zeeyter suka shiga nasu, Farouk da Ammar ma kowa dakinsu daban kamar yadda tsarin gidan yake, Xavier da Asher daki daya suka zaune domin Asher yaki yarda ya bi su Noor sai da Deejerh ta tabbatar kowa ya kwanta a makwancinsa kafin ita ma tayi nata.

Dare ya fara yi sosai wajen karfe biyu Deejerh ta farka tana jin ƙishiruwa ta sha ruwan zata koma ta kwanta kenan ta ga kamar inuwar mutum a palour a hankali take tafiya har ta fita.
Tana zuwa kuwa taga Asher ne tsaye jikin bango yanata zane zane kansa kauce bakinsa a bude kamar yadda yake.
Ta fi minti biyar tana tsaye tana kallonsa.....


08103080717
[4/29, 8:20 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-50

Can sai ta karasa kusa da shi tana kiran sunan shi , Asher..Asher."
A hankali ya juyar da kanshi ya kalleta sai kuma ya kara juyawa ya ci gaba da zanensa.
Da taga yaki kulata sai ta dauki daya daga cikin pencil din da yake zane da su ita ma ta fara zanen a bango.
Da yaga ta fara sai ya sake baki ya tsaya yana kallonta.
Ita kuma ta ci gaba duk da cewa kawai zanen take ita kanta bata ma san me take zanawa ba.
Can hannunsa ya daura kan nata yana controlling hannun yana bin zanen da take sai gani tayi ya maida jagwalwalonta zanen flower.
Tsaya tayi tana kallonsa cike da mamaki suna hada ido ya kyalkyale mata da dariya.

Itama tayi masa dariyan tana rike hannunsa suka zauna ta ce, "wato abun da kake so kenan?"

Ya girgiza mata kai alamar e .
Ta kara fadin, "zaka na koyamun?"
Ya kara girgiza kai ba tare da ya ce komai ba yana sa hannunsa a baki.

Deejerh ta ce, "to zamu iya zama abokai daga yau ni da kai?"
Nan ma kara girgiza mata kan kawai ya yi .
Ta mika masa yatsun hannunta tana, "to mu kulla abokata, abokai na har abada."
Da dariyarsa a fuska ya ya mika suka hada hannun suna dagawa sama kafin suka sauke.
Daidai lokacin da Xavier ya fito nemansa.

Dukansu suka hada ido musamman Xavier ya kura masu ido yana kara bayyanar da tsantsan mamakinsa yadda Asher ya yarda da Deejerh.

Deejerh ce ta katse shi da fadin, "ka duba baka ganshi ba ko? Ai muna nan muna shirya yadda abokantakarmu zata kasance ne ko Asher?"
Ta fada tana kallon sa.
Asher ya ce, "umm."
Xavier ya ce, "to kenan ni an wareni banda ni cikin abokan?"
Asher ya gyada kai alamar e.
Dariya suka yi duka kafin Xavier ya ce, "shikenan tunda ni dai ba a sona, muje ka taken medicine dinka time ya yi ."

Deejerh ta ce, "to bara in raka abokina da kaina."
Ta daukeshi sai da ta kai shi dakin Xavier ya bashi maganin ya sha kafin ta ce, "Tom byee bye freind, take care of yourself for me ka ji,kuma kayi barci mai dadi ka mana mafarkin Flowers irin wa innan muka yi dazu."
Washe mata baki ya yi yana dariya da hannu kuma yana yi mata bye-bye ta fice.

Har cikin ranta ji tayi tana matukar tausayin yaron kuma tana sonshi mussaman da ya kasance mai nakasa ko ince me irin yanayinta ta wani bangaren.

★★★Xavier baiyi barci ba daren ranar dukufa ya yi yana ci gaba da bincike har gari ya waye.

Bayan sunyi sallar asuba Kafin kowa ya tashi Zahra ce ta fara tashi ta fara taya ma'aikatan gidan aiki suka gyara tsaf girki ma suka shiga kitchen tare kamar yadda suka yi jiya sai dai su taya da wasu abubuwan.

Misalin karfe tara kowa ya yi wanka kuma breakfast ya yi ready.
Haiydar ne ya fara zama kan daining yana kokarin saving kansa.
Deejerh na dariya ta ce, "Food Master, Madam wannan mijin naki ba zai canja ba fa."

Zeeyter ta ce, "To kuma dai kar asa mana ido da yawa abar min miji ya sarara ya yi kumurmur nafiso inga yanata kumatu ina wasa da shi."
Dukansu suka kyalkyale da dariya.

Yaran na fitowa duka suka bi su suna gaishesu sannan suka zauna suma zeeyter ta zuba masu abinci.
Suna cikin ci Zahra ta kalli Deejerh tana fadin, "Za ki rakani mu danje shopping yau ina so inyiwa su Noor siyayya."

Deejerh ta ce, "Oh to ba sai muje duka ba harda Yel."

Zeeyter ta ce, "aa ni fa zama zan yau mu sha soyayya da mijina."
Tana fada suka yiwa juna sigina ita da Haiydar.

Farouk ya ce, "umm tsuntsayen soyayya nima dai na kusa yin zuciya ko wannan Vixeen dince ku bani sadakarta."

Deejerh ta hararashe tana, "Sadaka ko? Kai kafi kowa sanin nafi karfin sadaka ai."

Bayan sun gama hakan kuwa akayi Zahra ta ja Deejerh suka tafi shopping Zeeyter da su Farouk suka tsaya gyaran gida da shirye-shiryen birthday.


Su Deejerh na fita Ammar da Farouk suka tafi Airport suka dauko ma'am.
Zeeyter kuma da sauran yaran suka fara decoration din gidan suna gyarawa.

Bayan sun gams suka je suka hada snacks da duk abubuwan da za a ci.

Sun kara gyara gidan ya yi kyau sosai kuma ya tsaru.

Zahra kuwa sai kara jan Deejerh take suna kara kutsawa daga siyan wannan sai siyan wancen.
Sai da dare ya fara yi kafin suka koma.
Kuma koda suka koma ba a barta ta shiga bangaren da za ayi shagalin ba shi babban palourn gidan sai dayan palourn suka zauna duka.

Can sai ga Xavier da budurwasa sun shigo.
Sunanta Sona
Yar Austaraliya ce
Kuma ita ma Christian ce.
Hannunsu rike da juna suka shiga suna dariya.
Ta gaisa da su duka cikin Wasa da dariya.
Xavier ya ce, "Yau munyi bakuwa anan zata kwana."

Zeeyter ta ce, "Ma sha Allah welcome kawata amman sai kayi hankali fa saboda Abokina baya wasa da mata."
Ta fada tana nuna Farouk da ido.
Shi ko dariya ya yi ya ce, "aiko dai ki fada masa in ya yi wasa kwaceta zanyi domin tayi kalata wannan kalatace."

Nan akayi wasa akayi dariya suka ci abinci har lokacin ba a nunawa Deejerh Ma'am ba.
Sunje kowa ya kwanta karfe 12 nayi duka suka tashi.
Zeeyter da Zahra suka je dakinta suka fara nocking.
A tsorace ta bude tana, "Subhanallahi me ya faru? Waye ba lafiya? Ku fadamun."
Ba su ce mata komai ba kawai suka jata.
Tana, "Don Allah ku fadamun lafiya?"
Ganin yadda hutar gidan ta dauke take hakan yasa ta kara tsorata.
Riketa suka yi suka shigar da ita palourn suna shiga a ka kunna wutar.
Gaba-daya ta rikice yadda taga dakin komai kyalekyale yasha ado da Happy Birthday Deejerh ga Ma'am.
Rufe idanunta tayi da hannu ta rasa yadda zata yi,ta bude kuma taje ta rungume Ma'am da gudu sai hawaye.
Fara tafi suka yi suna mata Happy Birthday Ma'am ta rike mata hannu suka yanka cake.
Ma'am ta fara bawa kafin ta bi yaran ta ba sannan sauran manyan.

Xavier da Sona ne suka shiga fila suka sha rawa sosai, Zeeyter ma ba a bawa rawa kunya haka ta aje Aiza gefe ita da Haiydar suka shiga suka sha rawa.

Daga karshe Zahra ta dakatar da su ta ce Deejerh taje tasa kaya.
Bayan tasa kaya suka fara game aka ajiye takardu yara zasu dauka duk topic din da suka dauka zasu yi magana akai.
Za a fara kenan Xavier ya cewa sona ta zauna shi kuma ya wuce daki ya nufi system dinsa.

Asher ne ya fara dauka.
Yana budewa ya ce, "FORGIVENESS."

Gyada kansa ya yi yana gyara wa ya ce, "Forgiveness is the best thing, especially when it comes to family and people you Love , Reconcile as much as u can for Allah (SWT) encourages us to Reconcile and make it up with People who have become distant from us.
If making up with them is better.
Some People you can make a boundary.
Some People you can limit your contact with them see what benefits you and all is good IN SHA ALLAH So long as its Done for right reason and Allah knows Your intentions.
Happy Birthday Momma Wish You Long Life And.......
Kafin ya karasa ta rungumeshi tana kuka.
Har cikin zuciyarta ji take ya fama mata tabon iyayenta.
Da Khalil yaga ta fara kuka ya ce, "If You forgive a person but you hang on to the anger,the pain is and the hurt and You say you forgive the person then You don't understand what forgiveness really is, because forgiveness is not for the other person Its for you."

Ma'am ta rungumeta tana......

08103080717
[4/29, 8:20 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-51

Tana share mata hawaye.
"Ki daina kuka kinji ka da ki manta ke jarumar mata ce,kin rayu a lokaci mai matukar wuya,kin rike numfashinki a lokacin da yake kokarin sabuce miki, kinyi murmushi lokacin da hawaye a idanunki kuma kin tashi a lokacin da kika fadi yanzu lokacin ci gaba da tafiya ne ba tare da tsayawa ba."

Ammar ya ce, "Happy Birthday VIXEEN Allah kara yiwa rayuwa albarka ya kara arziki da lafiya kuma Allah kawo miji na gari koda nine."
Yana fada suka fara dariya.
Deejerh kuwa ta galla masa harara.
Farouk ya ce, "koda nine dai wannan ai kalata ce ba taka ba."

Zeeyter ta katse su da fadin, "sai mun durza dukanku baku mana ba."

Ci gaba da wishing dinta suka yi suka bata gifts , sun ci , sun sha kuma sun sha rawa sosai.


★★★★Washegari suna zaune bayan sun gama breakfast Deejerh take cewa Khalil , "Ina so in je Mexico in ga Iyayena."

Tsabar farinciki sai da murmushi ya bayyana a fuskar Khalil ya ce, "Da gaske?"
Ta gyada masa kai alamar e.

Khalil ya ce, "amman ko na ji dadi sosai kin ga in zamu wuce zamu iya zuwa can duka mu rakaki."

Deejerh ta ce, "e duk yadda kuka ce."

Jawabin Farouk ne ya katse su ganin abun da ake magana akai a tv.

"Wannan Kush din fa ya fara zama annoba a duniya gaba-daya kusan kowacce kasa ya bazu yanzu."

Zahra ta ce, "kamar ya? To menene Kush din?"

Farouk ya yi dariya kafin ya ce, "ka ji yar guntuwa yar kauye Kush is made

Please Login or Register in order to submit comment