Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafi nikam wannan surutun naka sai mu kai dare anan."

Ammar ya ce, "amman tsaya ,ki karbi kudinnan na baki mallakinki ne ba nawa ba,in kikace kin dawo mun da su bazan ji dadi ba,."

Deejerh ta ce, "to ai amfanin da za ayi da su an riga an samu, gwanda ka ajiye kayi amfani da su nasan kai ma kana da bukata ga gyaran motarka ma."

Ammar ya ce, "ni dai na riga na baki ban damu da me zakiyi da su ba,ko ma mene ne kawai ki rike."
Ya fada yana mika mata.
Karba ta yi ta ce, "Na gode sosai Jarumi a inda babu jarumai."

Dariya kawai ya yi, ya daukan mata babban box din ta diba sauran kayan suka tafi.

Suna zuwa Ma'am na ganin su ta fara rawar murna.
Ammar ma ajiyewa ya yi,yana tayata yana bata labari.

Zama Deejerh ta yi ta fara bude box din design materials din.
Abun mamaki, babban School box dinne wanda malamai ke amfani da shi ba ma na students.
Kayan masu kyau sosai cikin tsari harda yadina da za a ayi amfani da su wajen Design kala biyar masu kyau da tsada."

Ma'am ta daga hannu sama tana, "Allah kaine abun Godiya,mun gode maka,kuma muna kara gode maka a kullum har karshen numfashi Da ikonka, Deejerhtouna a kullum kina kara hawa matakin nasara wanda hawansa daman sai an jure,kuma na san ke jaruma ce, kisa aranki cewa zaki iya fuskantar komai kuma zaki iya fuskantar kowa a yanzu, Addua babu wasa duk da nasan cewa ba wasan kike ba amman komai zai iya faruwa a yanzu da kike kokarin hawa bene domin ɗaya kacal kika hau akwai saura gaba kila kina hawa zakita samun tuntube,ki fadi,har ma kiji ciwo, maimakon zubda hawaye yayin jin ciwon nan kiyi murmushi kuma kisa aranki zaki ci gaba da tafiya haka,har kikai ga isa inda ya dace, na yarda da ke,kuma na san zuciyar ki bata fatan kowa da sharri ina miki fatan dauwama a haka."

Tana karasa fada hawaye ya zuba mata daga idanunta,da sauri Deejerh ta goge mata tana rungumeta.

★★★Mexico.
Da sauri ta shiga cikin gidan,da ya ji muryarta har wani murmushi ya fara yana kokarin tashi duk da jikinsa ya masa tsami.

Ko kallonsa batai ba ta mika masa hannu tana, "Kudi nake so.....


*ANA WATA GA WATA😂 SABUWAR CAKWAKIYA ON THE ROAD ZAN CE MA KO IN THE ROAD? KU TUNA MINI😂*

Let's go 💃


08103080717
[1/12, 10:13 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-34

Take dariya da Murmushin dake fuskar Zayd ta dauke, cikin yanayin bacin rai ya ce, "Haba Huda shin kin lura ma da yanayin da nake ciki? Kwana nawa rabon da kiga naje gidan ki? Ko a jikinki, inna kira wayarki ma bakya dagawa, yanzu ma kinzo ke ta kudi kike ba ta duban lafiyata ba? Ina saida lafiya ake neman kudin? To ban da shi." Ya fada yana kau da kai.

Cikin salon kisa da kisisina take Huda ta canja salo da yanayi,ta shagwabe fuska tana kwantawa jikinsa.
Murya kasa-kasa take fadin, "Shine zaka mun fada? Bayan ni ban san baka da lafiya ba,kuma wayata samun matsala ta yi, so nake inje in siyo wata shine nazo ka ban kudi ummm Love, ko inje wani ya bani?"

Da sauri Zayd ya ce, "Aa, amman dai kin san bakya kyautawa ai sai tun da kika jini shiru kizo ki ga ko lafiya kuma ki sanar dani kina son waya,yanzu ki jira inyi wanka tunda na fara jin karfin jikina sai mu fita a siyo wayar."

Da sauri ta zare ido tana shafa masa kirji a hankali cikin yanayin da dole jikinsa ya amsa ta ce, "Umm ni bana so ka wahala kasan ina sonka , ka zauna kawai ni zanje in dawo anan ma zan kwana."
Washe baki Zayd ya yi yana tashi daga kwanciyar da yake.
"Really?"
Ta girgiza masa kai tare da yi masa fari da ido.
Murya na rawa ya ce, "to yanzu nawa kikeso?"

Ta ce, "ban san nawa wayar zata causing ba kuma kasan nidai bana rike karamar waya eheen."

Murmushi ya yi ya ce, "nima bana so ki rike karamar ai, but ban da kudi a hannu sai dai in baki card dina kije ki siya tunda kince anan zaki kwana."

Wani irin makirtaccen murmushi tayi a zahiri,cikin ranta kuwa ta ce, "Yesssss Hakan na fi so ai."
Yana mika mata card dinsa ta tashi ta rungumesa tare da dire masa wani Hot Kiss tana masa kallo mai dauke hankali tare da gigitarwa.

Yama gagara magana kawai binta da kallo yake yana kara washe baki kamar wanda ya yi arba da wawan zama.

Tana fita tayi tsaki tana kara gyara jikinta.
Da sauri ta karasa bakin titi saurayinta na jira a mota ta shiga suka yi tafiyarsu.

Zuwa tayi ta dunga yiwa saurayin nata siyayya duk abun da yake so da wanda take so , Zayd na zaune ban da ruwan Debit alert babu abun da yake gani,kamar wasa har an kwamushe rabin kudin cikin account din.
Rikicewa ya yi,wata irin zufa ta fara yanko masa.
Domin kudin data cire ya wuce misali.
Wayarsa ya dauko ya dinga kiranta amma sam taki picking da ma ya isheta da kira kashe wayar tayi gabadaya.
Ya kasa zaune ya kasa tsaye zarya yake kawai cikin dakin ya kai ya kawo shi kadai ya rasa meke yi masa dadi , kudadene da ya dauki tsawon lokaci yana tarawa take kokarin tarwatsawa.

Sai da ta gama watayawa da saurayinta can karfe biyun dare kafin taje tana yi masa nocking.
Rai ɓace ya bude idanunsa sunyi jajir tana ganin haka ta kara shiryawa yanayin da tazo da shi, fadawa kirjin sa tayi tana kuka.
"Love na je siyan wayan yan fashi suka fasa Company din suka shiga,shine suka dinga cire ma kudi ni ko wayar ma ban siya ba,da kyar muka tsira."
Ta kara kankamesa tana kuka kamar ranta zai fita.

Soyayyar da yake mata ya wuce tunaninsa da hasashensa wanda ko kadan bai son ganin wani abu ya raɓeta bare wanda zai sata a damuwa, tuni ya sa batun kudi a gefe ya kara rugumeta jikinsa suka shiga dakin ya rufe kofa.

"Sorry Mon Cherie kinji,ina dai basu miki komai ba ko? Indai basu taba mun lafiyarki ba ai Shikenan ki daina kuka Please har cikin raina nake ji kinji."

Cikin kissa ta ce, "to kudinka fa kudinmune na aure ina? Ummm na shiga uku." Ta kara fashewa da kuka.
Birkicewa ya yi yana rarrashinta har ma ya rasa abun cewa yana share mata hawaye yana shafa mata baya.
Ita kuwa kallon gefe tayi tana sakin wata irin makirar dariya, sai can kuma ta ci gaba da kukan.
Da kyar ya lallabata ta yi shiru.
Ya zaunar da ita,jiki na rawa ya shiga kitchen ya dafa mata coffe ya kawo mata tasha, bayan ta gama sha da kanshi ya kwantar da ita ya lullubeta, ta shiga bargon ma tana kara sakin wata makirar dariya.
Shafa mata kai ya dunga yi a hankali sai da ya tabbatar ta yi barci kafin ya barta.

Tagumi ya yi,ya zauna ya yi shiru a bakin gadon sai wajen karfe biyu da rabi kafin ya kwanta yana kwanciya kuwa barci ya kwashe shi.
Huda na ganin barci ya kwashi shi tsam ta tashi ta zaro wayarta a jikinta ta kira saurayinta tana dariya tana bashi labarin yadda ta shirgawa Zayd karya kuma ya yarda.
Haka suka dinga dariya suna labarin Zayd din sai da taga yana motsi kafin tayi sauri ta katse kiran ta koma ta kwanta.

★★★Paris

Tun daga kofar lecture room din hayaƙi ya fara dakan hancinta da wani irin wari dake fita.

Tana sa kafarta ciki kuwa ya kara dakan hancinta,ban da hayaki da wari babu abun da ke tashi, ga kuma sautin waka, kamar zata janye kafarta sai kuma kawai ta danne zuciyarta ta shiga.

Tana shiga kuwa ta gansu kowa da yanayin da yake ciki, ga dukkan alamu dai yawancin sun sun shahu,sun bugu sunata tikar rawa, wasu matan kuma na gefe manne da juna suna tattaɓa jikinsu, maza da matanma da ke rawa rungume rungume suke da da shafe shafe ana kissing juna,wani team guda kuwa kwalaban giyoyi kawai suka sa a gaba suna dirka.

Kokarin fara ficewa tayi a hayyacin tayi saurin dafe kanta tare da ja gefe ta zauna tana kokarin daidaita nutsuwarta.
Ji tayi kawai camellia ta fara shafa mata jiki.
A zabure ta juyo.
Camellia ta sake mata wani irin Murmushii tana fadin, "Welcome Sweetheart." Ta karasa maganar tana kokarin rungumeta.

Da sauri Deejerh ta kauce tana fice a class din cikin sauri.
Tana fita kuwa ta fara zabga amai kamar hanjin cikinta zai zube ban da nishi babu abun da take yi.

Famfo taje ta wanke fuskarta ta kuskure bakinta.
Sannan ta je School garden din ta zauna a takure.

Mr Laurent zai wuce kenan ya ganta ya tsaya da fara'arsa yake fadin, "Ah Deejerh me kike anan? Ke bazaki je kiji dadin naki bane? Yau Free Day ne fa zaki iya yin duk wani abu da kikeso,ki saki jiki ki sha duk abin da kikeso kuma kiyi abin da kikeso kina da wannan 'Yancin."

A sanyaye ta ce , "Okay Thank You Sir."

"Always Welcome." Ya fada yana murmushi ya wuce.

Tana zaune ita kadai sai wani matashi ya karaso ya zauna daf da ita.
Ya yi shiru sai can ya ce, "Barka dai Friend, Sunana Mael duk da cewa na san kin sanni a ido amman baki san sunana ba sabanin ni da na san naki, kila bakya son hayaniya shiyasa kika bar Class ,ni kuma na zabi biyoki nan domin mika miki tayi na musamman."
Tun da ya fara maganar nan ko daga kai Deejerh bata yi ba bare ta kalleshi.

Ya ci gaba da magana, "na san kina jina,ki cire wani kumbiya kumbiya yau ina gyayatarki dakina muje mu kwana tare, karki damu zan dauki nauyinki har ma da kudin kashewa in kina so."
Sai a lokacin ta daga kai tana kallonsa.
A zabure ta zura masa manyan idanunta cikin nasa, shi kan shi sai da jikinsa ya amsa.
Kusan Second Biyar tana kallonsa kafin ta kau da kanta kasa.
Kan ta ankare ji tayi kawai an fara lalubar mata jiki.
Cikin zafin rai tana daga hannu ta saki masa wani duka a gefen kafadarsa.
Ya saki wata kara shima cikin zafin rai ya daga kai yana kokarin janta dole.

Deejerh ta.....

Okay Byeee Till Monday 😻
Luvs U OLL
08103080717
[1/16, 11:46 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-35

Ta fisge jikinta.
Sa hannunsa ya yi jikinta yana kokawa da ita tare da kokarin cire mata kaya.
Kafin ya ankare ta damke hannun shi ta juya shi ta baya har sai da kashin hannun ya kara shi ma ya sake ƙara take idanunsa suka canja kala.
Azaba da mamaki sun dabaibaye sa taya za ace wanan 'Yar yarinyar ta gagareshi har ta fara kokarin illata shi.
Kokarin zamewa ya fara yi yana jan hannunshi da ta rike gam.
Aiko tana sake masa ya arce da gudu kafa mai naci ban baka ba, duk da cewa Deejerh na cikin yanayi mara dadi amman yadda ya gudu sai da abun ya bata dariya kamar wanda ya ci karo da mutuwa.

Yana tafiya ta koma zauna abun ta.
Warin giyar da ta shaƙane yake dawo mata sabo, kanta na sarawa tana jinta ba daidai ba.
Haka ta kara tashi da sauri taje gun famfon ta kara wanke bakinta da hannunta da ma fuskar gabadaya.
Amman sai take kara jin warin kamar karuwa yake yi.
Haka ta dunga wankewa har fuskarta da idannunta duk suka canja kala, ita kanta ma ta fice a hayyacinta, ji take kamar ta kwala ihu ko ta tafi da gudu.
Kokarin daidaita kanta ta fara yi, tasa hannu aka ta durkusa waje guda tana jan numfashi.

Haka ta ci gaba da Jan numfashi har sai da taji ta fara dawowa daidai tukun ta koma garden din, bata so ta zauna shiru ta kara fadawa wani kogin tunanin hakan ya sa ta bude box dinta ta ciro design materials dinta ta fara Designing.

Tana cikin yin abunta cikin nutsuwa ji tayi kawai an take mata kafa,ba tare da ta dago taga wacece ba ta ja kafar.
Sai cikin swimming pool.
Dake akwai Swimming pool a school garden din kuma daf da nan Deejerh ta zauna.
Bata ma san daga kafar da tayi ta jefa ta ciki ba ta ci gaba da abun da ke gabanta sai da taji saukin murya ana kuka da fadin, "Help, Help please."
Esme ce tsundum-tsundum cikin ruwan hankali tashe domin ita bata iya ruwa ba a rayuwarta ma babu abun da take tsoro sama da ruwa gata tsamo tsamo ciki.
Tana da Aquaphobia tun tana karama, kuma Aquaphobia shine, tsoron ruwa,mutanen da suke da wannan cutar suna da matuƙar tsoron ruwa sosai,wanda har ya kai ga suna iya jin tsoron yin wanka,da ma shan ruwan,da kuma kasancewa aduk wajen da yake da ruwa mai yawa." (Aquaphobia is a fear of water. People with aquaphobia have severe fear when they see or think about water. They may be afraid of baths or showers, drinking water, large bodies of water or swimming pools)

Sai kokarin daga kanta take sama tana ihu,hawaye da majina na bin juna.
Deejerh na kallonta kuma sai ta bata tausayi, da kamar bazata tashi ba sai kuma ta tashi ta mika mata hannu da sauri Esme ta cafe.
Janyota tayi ta fito da ita daga cikin ruwan, tana fito da ita ta koma ta zauna ta ci gaba da harkan dake gabanta.

Garin kokarin fita daga ruwan da ihun da tayi ashe gaban rigarta daidai kirji ya yage, kuma irin rigunan ne masu shara-shara.
Tana kokarin tsame ruwan jikinta kawai taga kirji a waje.
Tana daga kai taga wani na tawowa inda take yana suɗe baki.

Cikin sauri ta fara kokarin jan rigar.
Amman ina kafin ta ankare ya karaso yana cakumar mata kirji.
Kuka ta fara tana, "Stop, Please,Stop,ka daina ka bari."

Kokarin sa bakinsa yake yana, "ya kike abu kamar bakya sone,dalla ki bari muji dadinmu mana."

Ta gagara kwace kanta sai kuka kawai take.
Deejerh kamar bazata daga kai ba, da taji sautin kukan ya yi yawa tayi tsaki tana daga kai.
Fama suke tana kokarin kwatar kanta ta gagara shi kuma sai kara latsata yake.
Wani irin bacin rai ne ya bayyana a fuskar Deejerh sai idanunta ke bata tamkar ita ce ake yiwa hakan, tana zuwa ta fincike Esme,shi kuma ta fara sake masa wasu zafafan maruka har sai da ya nemi hanya ya tsare.
Esme ta rike riga tana kuka ta rasa yadda zata yi.
Deejerh ta kalleta ta ce, "zan iya taimaka miki in gyara miki rigar?"
Kanta na kasa ta girgiza alamar e ba tare da ta iya hada ido da ita ba.
"To muje."
Suka karasa inda ta zauna ta cewa Esme ta zauna ita ma.
Jiki ba kwari ta zauna.
Ta duba cikin box dinta ta dauko wani fashion links mai beat da ake adon kaya da shi.

Ta bi gaban rigar ta linking mata guda uku take riga ta fita tsaf harda karin ado.

Murya ciki ciki tana rawa ta ce, "Thank you."

Deejerh ta yi mata murmushi tare da fadin, "Any time, zaki iya tafiya yanzu."
Tana tashi motarta ta wuce kai tsaye ta fice a school din.

Deejerh kuwa Designing dinta ta karasa sai da lokacin sallah ya yi,taji an kira sannan taje office din Mr Laurent zata yi.
Yana ganinta ya ce, "Ah Deejerh ke yau wai bakya free Day dinne?"
Murmushi ta yi ta ce, "Sir ni kam free na shine na yi abun da zai ingata mun rayuwata ta yanzu nan gaba,har ma da ta al'umma, dukkanin abun da nasan ba zai amfane ni ba,bana son jin cewa inyi ma bare tunanin yi."

Ya ce , "Good Girl, ina miki fatan Alkairi Ubangiji ya baki ikon ci gaba da rayuwa a haka kinji."

"Amin Na gode Sir." Ta karasa maganaar tana shimfida sallayarta.

Mael kuwa komawa ya yi lecture room dinsu ya zauna tsit ya yi tagumi.
Banda haki babu abun da yake yi.
Da abokansa suka tambayesa me ya faru cikin fushi ya ce, "wannan village girl dincen ke sun illata ni don kawai na ce mata yau ina inviting dinta dakina tazo mu kwana, yarinyar akwai kauyenci ga wani karfi na ban mamaki wallahi wani riko da ta mun na aza mutuwa zanyi na zata zare raina za ayi fa."

Dariya suka fara suna karyata shi kan cewa shidai rago ne.
Wani acikinsu kuma ya ce, "daman taya zakayi tunanin yar kauyen nan tana da wayon karban gyayatar ka? Ai sai dai a wayar da ita a hankali."

Mael ya ce, "Wa? Wani irin wayarwa? Ni kam na yafe,gata da siffar mata amman karfin maza ne da ita wannan sai ta kashe mutum ai."

Duka suka tintsire da dariya kafin dayan ya ce, "kai dai rago ne wallahi,duk karfinta na banza ne indai mace ce tsaf zamu iya biyan buƙatar mu da ita ba,barin ma yadda taken nan fa kasan akwai shagali,ka nutsu inaga shan abun da kayine jikinka ya mutu ba kwari kake tunanin wani karfi gareta, za mu hada mata gadar zare tana school dinnan ai muma kuma muna ciki zamu gani."

Mael ya ce, "kuma fa hakane kwari na san ku da iya kulla mugunta salo salo."

"Au mu kadai ban da kai?"

Meal ya ce, "mu to."

Suka yi dariya tare da fara shirin kulla irin gadar zaren da zasuwa Deejerh.

Ita kuwa Tayi sallah ta idar ta koma ta ci garden din sai da ta tabbatar da lokacin tashi ya yi,kafin kama hanyar komawa kauyen su.

Ranar kam Ammar bai tsaya jiranta a bus stop ba, tun daga cikin Bus din take lekensa har ta fito bata ganshi ba, hakan kawai sai yasa ta ji babu dadi aranta duk da cewa bata san dalili ba.
Fara'ar fuskarta ta dauke gabadaya haka ta kama hanyar shiga cikin kauyen.
Da sauri-sauri har ta isa, aiko tana zuwa gida da shi ta fara cin karo yana sake mata murmushi,ta kau da kanta gefe tana kara bata rai zata wuce shi.
Ammar ya ce, "ina zaki, ki tsaya mana,ki rufe Idonka Don Allah."

Deejerh ta bisa da wani kallo zata wuce, ya rike mata hannu ta kara daga idanunta sama.
Araunane ya ce, "Please."
Tsayawa tayi tana kallon gefe har lokacin bata sake fuskarta ba.

Ammar ya ce, "to ki sake fuskarki mana,kuma ki rufe ido abu zan nuna miki."
Deejerh ta ce, "Ka ga na dawo na gaji ni fa hutuwa nake so inyi."

Ammar ya ce, "yanzu zaki huta nidai Don Allah ki rufe idon to."

Ta rufe idon duk da haka dai fuska babu walwala.
Tana rufewa ya ciro kwalin wayar da ya boye a bayansa ya mika mata yana, "bude to."
Tana budewa ya ce, "surprise,ban sani ba ko ta miki na dai siyo mana kala daya kuma na san zata taimaka miki wajen binciken wasu abubuwan na School."
Tsabar farinciki Deejerh ta gagara rufe bakinta.
Karban wayar tayi tana budewa cikin rawar murya ta ce, "Subhannallah!
Ya Allah ya akayi ka san target dina? Oh , Thank you so much."
Ta dago ta kallesa shi kafin ta ci gaba da magana, "kalmomin bakina baza su iya misalta farincikin da nake ji a yanzu ba, I'm out of words wallah, na gode sosai Allah ya saka ma da Alkairi da dai fushi nake da kai amman yanzu na sauko."
Dariya Ammar ya yi ya ce, "Amin, kuma Alhmdu Lillah tunda dai kin sauko da kin kumbura kamar sabon bread."
Deejerh ta watsa ma shi harara tana, "kai ne bread din ai."
Kiran sallah aka fara.
Ammar ya ce, "kinga har an fara kiran sallah na tafi masallaci."
Deejerh ta ce, "Adawo lafiya." Tana shigewa ciki.
Tana shiga ta nunawa Ma'am wayar.
Ma'am ta ce, "Ammar ai yaron kirki ne yana da hankali da tunani sosai Allah ya kara inganta maku rayuwa duka."
Deejerh ta amsa da. , "Ameen."

Mexico
★★★
Zayd warewan dole ya yi, damuwarsa Kada huda ta ce zata tafi hakan yasa tun safe ya tashi yake nan nan da ita, hatta abinci cewa tayi ba za ta ci na restaurant ba sai dai shi ya girka mata.
Haka kuwa ya shiga kitchen ya girka.
Tana kwance a jikinsa cikin yanayin kissa ta langwabe a dole har lokacin wai bata gama dawowa daidai ba, jiya ta tsorata sosai.

Zayd ya ce, "Mon Cherie please ki bani dama yanzu, na gaji,na kasa daurewa ,kin fi kowa sanin cewa ban da burin da ya wuce ace na mallake ki."
Huda ta taɓe baki ta ce, "Amman ai gamu tare yanzu ko? So what do you want after this?"

Zayd ya ce, "ki zama tawa,Mine ni kadai,ki daina kula kowa ki dawo rayuwa dani, kullum mu kasance tare shine abun da nake so."

Ta numfasa kafin ta ce, "To da wani kudin? Kasan nidai kuma ba zan zauna a wannan gidan ba."

Zayd ya kalli dakin da suke ciki kafin ya ce, "mene ne aibun nan gidan? Alright shikenan za a nemi wani, wanda kikeso, maganar kudi kuma zan saida mota ta."
Wani kallo ta masa tana mikewa tsam tare da furta, "Allah ya sawake ba ma zai yiwu ba harkar tsiya da karanta kasan bana gun, Saboda mu muka fi kowa son aure ko? Kuma ana yawo dani na auri matsiyaci ko....?

08103080717
[1/17, 12:21 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-36

Zayd ya ce, "Matsiyaci kamar ya? Yanzu duk wadatar da nake da bai miki ba,har zakiyi tunanin za a min kallon matsiyaci? Ko da ace yau zan saida duk abun da na mallaka na tabbatar da cewa zan maida su babu haufi, yanzu ma abar batun saida mota ko wani abu, na ji na yarda zan fita in kara neman kudi inyi abubuwan da kikeso har ma da wanda ba kya zato amman da sharadin kin yarda kin amince zamu yi aure babu fashi."

Huda ta ce, "Eheen ni dai kasan ba zan iya rayuwar talauci ba,kuma hakan na daya daga cikin abun da yasa na ki amincewa inyi aure,amman indai zaka yi abun da ya dace ai Shikenan ban da matsala."

Zayd ya ce, "alright ni kuma na miki alƙawari zaki sha mamaki."

Dariya ta yi, "nima zan so sha ai har in koshi ma."

Daukan key din motarsa ya yi,zai fita.
Huda ta ce, "Ah Ina zaka kuma?"

Ya amsa da , "Neman arziki." Yana karasa fada ya fita ba tare da ya jira amsarta ba.
Dariya Huda ta yi tana tashi daga kan gadon tare da fadin, "Wahala bata isheka ba."

Wayarta ta ciro ta gyara zama tare da fadawa duniyar chatting da samarinta harda video call.

★★★Paris.
Ba karamin Jin dadin wayar nan Deejerh ta yi ba domin har ta fara bincike kan design tana kara duba abubuwa sosai musamman wa inda bata fahimta ba.

Wasa wasa Ammar ya fara kwarewa MMA training duk abun da Deejerh ta ce ya yi , ya kan yi kokarin yi ba tare da haufi ko tsoro ba, acewarta yanzu ne ya ke kokarin zama Namiji amman ada muna namiji ne.
Kamar kullum yau ma training din suke Deejerh ta gaji cikin Nishi ta ce, "ka ga ni kam na gaji ga wani barci da nake ji na dawo School ban wani huta ba zan je in kwanta."

Ammar ya daga kai yana kallonta, "ki tsaya wasa in fi ki karfi wallahi naga alamar so kike ki zama raguwa."
Gajeran murmushi Deejerh ta yi ta ce, "yoo ni ko da ace zan yi wata guda ban yi training din nan ba,ai ban jin cewa akwai abin da zai iya shan gabana in gagara, kawai dai stress ne ya mun yawa, so ina bukatar hutu Don haka jarumi kuma mazaje masu ji da karfi sai a kwana anayi." Ta fada tana kokarin tafiya.

Tashi ya yi da gudu ya sha gabanta yana, "cab yaushe zan ci gaba ni daya ba ke,ni ma na hakura hakan , Allah ya kaimu gobe."

Deejerh tai dariya, "mazaje to kar dai amanta da addua,na ma tuna bara in baka wannan,ka daure kana yi kullum kafin ka kwanta, "Subhanaka Allahumma rabbiy bika wada'atu
janbiy wa bika arfa'uhu, in-amsakta nafsiy
fagfir laha, wa-in arsaltaha fahfaz'ha
bima-tahfazu bihi ibadas-saliheena"
Ma'anar Addu'ar ita ce
(Tsarki ya tabbata gareka ya Allah, da sunanka na
kwantar da hakarkarina kuma da sunanka nake
tashinsa, idan ka karbi rayuwata, to kayi mata
gafara, idan kuma ka saketa, to ka kiyayeta da
abinda kake kiyaye bayinka salihai) ka ga kenan Addua ce mai mahimmaci da kuma tasiri sannan ka da ka manta da yin alwala ma kafin ka kwantan."

Ammar ya yi murmushi ya kalleta ya ce, "Na gode sosai , In kina fada mun wasu kalmomin sai inji tamkar mahaifiyata ce gabana, aduk wani abu da zaki nusar na Alkairi ba kya shayin fadi, zan yi su

Please Login or Register in order to submit comment