Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya faka motarsa, suka fito daga ciki duka domin shiga.
Daidai kofar da zasu shiga offishin wani Security ya tsare su.
Yana yiwa Deejerh kallon sama da ƙasa, kasancewar Ash din doguwar rigace a jikinta da karamin farin hijab.
Ammar ya ce, "meke damunka ne? Zaka tsaida mu kuma kana binta da kallo?"

Sai a lokacin security din ya daga kai ya kalli Ammar tare da sake tsaki ya na nuna Deejerh ya ce, "ba za ta shiga offishin nan da wannan munafikin abun ba."
Yana nuna hijabinta.

Kafin Ammar ya yi magana karaf Deejerh ta ce, "mene ne munafikin abu? Kana da hankali kuwa? Ka kiyaye furuncin harshenka."
Ta fada tana nuna masa yatsa.
Kokarin rike mata hannu zaiyi Ammar ya dakatar da shi.
Yana, "wannan ba magana ba ce, addininmu ne ya ce mata su suturta jikinsu in naku yazo da bambancin hakan wannan ba damuwarku bane kowa a kasar nan yana damar bin addininsa amman sam ban san me yasa kuke nuna tsana ga Musulunci ba."

Securityn ya ce, "wannan damuwarku ce Addinin ku baya gaba na amman muddin wannan tana son shiga wajen nan sai ta cire abun da ke jikinta a kasin hakan kuma zaku iya komawa duka."

Deejerh ta ce, "ba zan cire ba,kuma ba zan koma ba, sannan dole sai na shiga, wannan abun da kake kira da munafuki shine darajar kowacce mace ta kasance cikin mutunci da kamala wato ku kunfi son ku ga mace na rayuwa tsirara kuna kallon surar jikinta kuna jin dadi Ubangiji na tsine mata? Ba zai yiwu ba a ko ina muke ko da mu biyune musulmi ko ince ko da ni daya ce ba zan ji shakka ko tsoron kare addinana akan na wasu yahudawa ba."
Cikin zafin rai ya daga hannu zai kai mata mari.
Ta rike hannun na shi tana, "ba ka isa ba fa ka ce zaka taba lafiya ta wallahi ka yi kadan."
Ammar ne ya cire hannun Deejerh daga na shi yana, "ki bar ni dashi ban son kina shiga abun nan."
Ganin hakan kawai sai security din ya kama dukan Ammar ya kira Dan Uwansa suka hade masa su biyu.
Deejerh ma kuwa ta hau dukansu shi ma Ammar din ya samu zarafin kwatan kanshi ta hanyar ja wa dayansu kafa ta kasa ya fadi.
Deejerh ma taja dayan.
Haduwa sukai suka musu duka har sai da suka gudu kafin suka shiga office din.

Ta je ta bada bayananta domin ayi mata resident card din ganin cewa tana yawan samun matsala yanzu.
Bayan an karbi jawaban ma'aikatan suka sheda mata sai nan da sati biyu zai fito,hakanma sun nemi alfarma kan cewa suna so da wuri ne domin masu aikin sunce ya kan yi wata guda kafin mutum ya samu katin zama cikakken dan kasar.

Securityn na hango su zasu fito tun daga nesa ya bude masu kofa ya yi gefe,alamar tsoro duk ta bayyana a fuskarsa dayan ma kam kasa dawowa wajen ya yi.

Kallon juna suka yi ita da Ammar kawai suka sake wani hamshakin murmushi a tare kafin suka fice.

★★★★

An fara biyan Deejerh albashi a Companyn da take aiki.
Tana karba tun kafin ta koma kauyensu ta dauki wani kaso cikin kudin ta yi canji ta dunga bin mutane gajiyayyu irin masu zaman kan hanya tana raba musu.
Daga nan bata kara taɓa ko biyar ba, kuma bata sanar da Ammar da Ma'am ba sai dai ya kasance kusan sati guda kullum kafin ta tafi aiki sai taje wani waje.

Wata safiyar juma'a kuwa ta kira Ammar a waya sannan ta cewa Ma'am ta shirya zasu anguwa.
Dukaninsu mamaki suke ko ina zata kai su.
Haka suka bita dai.
Suna zuwa wani waje da aka yi katuwar rumfa wasu engines manya guda biyu, wasu kayan kuma an rufe ta shiga wajen suma tace su shigo.
Sai da suka shiga kafin ta ce, "Wannan gurin mallakinku ne,karamin kamfani ne wanda za a ci gaba da yin gawayi ana Packaging cikin sauki, kasancewar na ga kullum a yanzu kara samun kasuwarsa ake a kauyen nan na yanke shawarar yin hakan, an bani albashi na na farko kuma da shi na yi amfani, akwai ma'aikata su biyu mace da namiji da zasu dunga lura da wajen suna packaging ku dai kawai zakuna lura da yanayin abubuwan nan,naku ne, mallakin kune,duk abun da kukai daidai ne,nidai kawai burina in faranta maku kamar yadda kuke kokarin faranta mun."
Ma'am ta kasa cewa komai bin wajen take da kallo kawai tana hawaye.
Ammar kuwa ya duburbuce, "da gaske? Yanzu wannan wajen mallakinmu ne? Na mu ne? Me yasa baki yiwa kanki wani abu ba? Me yasa ko motar hawa baki fara saiwa kanki ba ke da kike zirga-zirga."
Deejerh ta ce, "inna muku ai shine nawa kaina din kune farincikina kuma kune tushena a yanzu."
Rungumeta Ma'am ta yi tana, "na rasa me zan ce,na rasa ya zanyi, Allah ya miki Albarka kuma ya ci gaba da kare mana ke a duk inda zaki kasance."

Ammar da Ma'am sunyi murna sosai wanda har ya kai ga sun tara mutanen kauyen ana tayasu murna .

★★★Deejerh na sauri zata tafi aiki ta bi Dajin kafin taje ta hau taxi.
Karo ta ci da wata yarinyar da bazata wuce shekara goma ba yashe a kasa jikinta duk jini tana kuka.

Deejerh na dagota taga ashe ma yar cikin kauyensune.
"Subhannallah Me ya sameki? Me ya faru? Me yasa kike kuka?"

Cikin muryar kuka ta ce , "Shine,shine ya mun wani abu zan mutu wayyo cikina."

Deejerh ta ce, "ya miki me? Shi wa?"
"Ban san shi ba,nima ban san shi ba ya rufe fuska, shi ne ya kawo ni nan ya mun..."
Ta karasa maganar tana nuna mata gabanta da hannu.
Yadda jini ke bulbula kamar ruwane ya kara birkita Deejerh ta ce , "Innallillahi wa inna illaihir ra'ji'un."

Kanta ya sara mata kawai sai take tuno tata rayuwar.
Saurin kawar d tunanin tayi,ta dauki yarinyar ta goya a baya ta yi hanyar komawa cikin kauyen da sauri.......
[2/6, 10:20 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-43

Gidan Papi ta wuce da ita kai tsaye.
Ya karbeta da sauri tare da shiga bata taimakon gaggawa.
Ya yi treating dinta da duk abun da ya kamata kafin yasa a ka kira Mahaifiyarta.
Deejerh na zaune bayan Mahaifiyar yarinyar ta zo Papi ke cewa, "Allah ma ya taimaka abun ya dan zo da sauki bata raunana sosai ba,fyade wani mara imanin ya yi mata, a yanzu tana da matukar bukatar kulawar ki na matsayin ki na uwa gareta, sannan a shawarce ku daina barin yara mata suna shiga dajin nan su kadai, kusan kullum yanzu matsalar da ake samu kenan cikin kauyen nan duk anbi yara kanana ana yi masu fyaɗe kuma an gagara sanin masu aikata hakan bare hukunci ya hau kansu kunga kenan ya wajaba a gareku na iyaye ku kiyaye."

Deejerh ta kalli Papi ta ce, "yanzu kenan wata 'Ya mace Musamman yara basu da 'Yancin fita cikin karkarar nan?"

Papi ya ce, "kusan hakan kenan tunda fitar nasu barazanace ga rayuwarsu."

Sallama ta masa kawai ta tashi ta fita jikinta a sanyaye.
Ko da ta isa office ranar kasa aikata komai ta yi gabadaya jikinta a mace ba kwari kallo daya za a mata a fahimci cewa tana cikin damuwa.

Somir ne ya zauna kusa da ita yana yi mata magana amman hankalin ta ko kadan baya jikinta.
Sai da ya dan sa mata hannu a gaban idonta kafin ta dawo hayyacinta tana ajiyar zuciya.
Ya ce, "Lafiya kuwa? Yau na lura bakya cikin yanayi mai dadi ko kadan mene ne yake damunki ne?"

Deejerh ta ce, "Hmm na lura kasar nan akwai babbar barazana ga rayuwar 'Ya'ya mata, mussaman wa inda ke zaman kauye kananun yara ba ji ba gani sai a gurbata masu rayuwa,a illata su,wasu daga nan shikenan rayuwarsu ta ta taɓe, yau kafin in tawo office na ci karo da wata yarinya anyi mata fyade a dajin fita daga kauyenmu abun ya daga mun hankali sosai na kasa samun nutsuwa."

Somir ya ce, "gaskiya kam,kuma mussaman ta wajen kauyenku kam kamar yadda kika fada tun ba yanzu ba ana samun irin wannan matsalar sosai ta zama ruwan dare saidai addu'ar Allah ya kare kawai."

Deejerh ta ce, "Amin ya Allah,amman ni na fara tunanin budewa yan matan kauyen MMA training center haka karami indai zasu samu kwarewar kare kansu babu wani dan iska da zai kara tunanin nufansu da aikata musu wannan mummunan lamarin, matsalar dole sai na samu wanda ya ke da sani sosai akan abun ya guiding dina kafin in fara."

Somir ya ce, "kuma fa kin yi tunani mai kyau ina da wani abokai biyu a Mexico Da naga suna kokarin koyarda hakan suna da kungiya ma guda na dai manta sunan kungiyar indai kin ga ba matsala kuma kina bukata zan hadaki da daya daga cikinsu sai ku tattauna."

Deejerh ta ce, "Why Not? Sosai ma ina bukata wallahi da ko na gode ma ."

Daukan Waya Somir ya yi,ya kira Roman ya masa bayani,Roman ya amsa da babu matsala kan cewa ya bada number.
Bayan sun gama wayar ya bawa Deejerh Number.
Saving tayi kawai tare da nufin sai taje gida zata kira.
Ko sunan shi ma bata tambaya ba, kawai tasa Somir Friend.
★★★Dare
Suna kamfanin Gawayinsu duka har Ma'am.
Ammar ya ce, "wai ya akayi kika gama komai ne ba tare da mun sani ba har takardun task ba ga ni duk kin shiga kin fita."

Deejerh ta ce, "Eheen kasan kasar nan mutum bai isa ya bude Company ba tare da ya yi rigister da komai ba da kuma biyan haraji hakan yasa na fara daga nan domin tabbatar da yadda abun zaizo muku da sauki saidai in lokacin biya ya yi kawai ku biya, yawwa ka ga na tuna ma Somir ya bani number friend dinsa da zai guiding dina kan bude Mma training center."

Daukan wayarta tayi ta shiga kiran Roman.
"Assalamu alaikum."
Jin sautin muryarta da Roman ya yi ya sa shi yin shiru domin tabbatar da abun da kunan sa ke ji.

Ta kara fadin, "Assalamu alaikum."

Ya ma gagara amsawa kawai ya ce, "Khadeeja????"

Tsam Deejerh ta tashi daga zaune ita ma ta ce, "Maestro Roman???"

Dukan su ajiyar zuciya suka yi.
Ita kam sai hawayene ya fara bulbula daga idanunta.
Ganin yadda take kuka mai tsuma zuciya yasa Ma'am da Ammar tambayarta mene ne?
Bata samu ta kula su ba.
Roman ya ce, "Deejerh da gaske kece? Fatan kina cikin koshin lafiya? Babu dai abun da ya sameki ko? Meya faru ranar baki kiramu ba kina ina yanzu?"

Deejerh na kuka ta bashi labarin duk abun da ya faru, jakarta data fadi da ma yadda akayi take zaune gun Ma'am dama aikin da take yi a yanzu.

Roman ya ji dadi sosai shima har hawayen farinciki ya yi,kafin ya sheda mata cewa In sha Allah zai hadata da su Daeej duk zai basu numberta.
Da Nawar ma wanda kusan kullum sai ya kira ya ji ko an samun labarin inda take.
Taji dadi sosai shima yaji dadi da haka suka yi sallama kan cewa in sun kara magana zai mata bayanin yadda zata tafiyar da training center dinta.

Bayan ta gama wayar take fadawa su Ma'am ai Roman ne dake tana yawan yin maganganunsu.
Ammar da Ma'am ma sunyi farinciki kuma sun tayata murna.
Daren ranar don farinciki bata iya barci ba sallah ta dunga yi tana mika godiyar ta ga Ubangiji.

★★
Washegari Roman ya kira su Mira duk suka zo Skul ya basu number Deejerh take suka kirata video call suka dunga hira suna jin dadin ganin juna.
Daga nan da kanshi ya wuce gidan Nawar ya kirata video shi ma nawar suka sha hira ya dunga tsokanar Deejerh kan ta yi kiba ta yi kyau wato tana jin dadin paris ta manta da su.
Ita kam ban da dariya babu abun da take.
Shima ya karba numberta ta ya ajiye a wayarsa sannan ya sheda mata indai tana da matsala ta kirashi kar ta ji nauyin sanar da su.
Deejerh tayi godiya sosai tare da nuna jin dadinta ga ganinsu.
Ranar ko office bata je ba.
Bayan duk sun gama gaisawa kuma kawai sai ta tuna da iyayenta a zuciyar ta tana raya ko ya suke ko suna lafiya ko akasin hakan.
Take yanayinta ya sauya ta shiga damuwa.

Ammar ne ya fara tsokanar ta, "Wato so kike ki tafi ki barmu ko?"
Murmushin dole ta yi ta ce, "kai fa baka da matsala."

★★Mexico

Tun dare bata bar Zayd ya yi barci ba,ban da masifa babu abun da take zabga masa kuma taki barinsa ya fita a gidan.

"Ni fa na fada ma na gaji wallahi na gaji, ka ce lafiyar ka kalau kuma nima lafiyata kalau amman ace ba zan haihu ba? Wannan wani irin abune ? In kai baka da karfin da zaka bani ciki to Wallahi Allah sai dai ke nemo wasu ka biya su su yi abun da zasu bani ciki,ga ka namiji har namiji amman ba amfani? Na fada ma duk yadda za ayi ke nemo ka biya wa inda suka amsa sunan su maza su bani cikin da zan haifa kamar kowa."
Ta fada tana kama masa kwalar riga.
Ya tureta ya ce, "kina cikin hayyacinki kuwa? Kin san abun da kike fada? Ubangiji ne mai bada haihuwar nan bani ba,kuma zai bamu a lokacin da ya so in kinyi hakuri, Amman batun in biya a miki ciki ai bai taso ba,ba ma zai yiwu ba domin ba zan jure ba ke kin sani."

Huda ta ce, "ban gane ba? Bazai yiwu ba? Ka ce bazai yiwu ba? Amman zai yiwu ka sakeni ai ko? Na ce zai yiwu ka sakeni ai ko? to Wallahi kasa aranka cewa indai ba za ka amince da kudirina ba to saidai ka sakeni kumq yanzu ma ba zan zauna a gidan nan ba."
Ta karasa maganar tana kokarin ficewa daga dakin.....
[3/4, 9:33 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-44

Ganin da gaske tafiyan zata yi.
Zayd ya bita ya riketa.
Yana, "ki tsaya ki saurare Please,kin san soyayyar da nake miki ba zan so ganin ki cikin kunci ko damuwa ba ko? Ni kaina abun nan na damuna na zabi dannewa ne kawai domin kada ki damu,amman yanzu shikenan mu koma hospital kuma duk wanda kikeso kika zaba shi zamu je."

Kallon shi tana tana, "Really?"
Ya girgiza mata kai.
Ta ce, "Alright amman yanzu fa zamu tafi."
Zayd ya ce, "E muje." Ya karasa maganar yana daukan keyn motarshi.
Suka fita tare.
★★★
Su Daeej,Mira,Noha, Abiel duk sun gama karatu har sun fara aiki,Mira ma kuwa har tayi aure.
Da suke bawa Deejerh labari taji dadi sosai mussaman da ya kasance rabuwar su daga makaranta bai sa amintarsu ta rabe ba,sai ma kara kokarin rike junansu da suka yi.

Rowan kuwa ya mata bayani sosai yadda zai gamsar da ita na fara Mma training center hakan yasa ta fara zuwa gun papi ta sanar da shi,ya yi maraba da hakan kuma ya yi mata alƙawarin cewa zaiyi mata ƙoƙarin tara Iyaye da yaran kauyen domin sanar da su da kuma nuna masu mahimmancin hakan agaresu dana 'Ya'yansu.
Kasancewar shi babba a kauyen da ake girmama batunsa kamar yadda ya umarta duk an taro.
Hakan yasa ya fara yi musu jawabi tare da bayanar da alfanun Mma training.
Bayan ya gama ya bawa Deejerh damar magana.
Ta ce,
"Wannan training din garkuwane ga rayuwar yan uwanmu,kannenmu, har ma da Yayanmu mata, ba iya ka ga masu kawo harin fyade ba,a ko ina ma da za a iya samun hargitsin wani abu, sannan ina so ku bani dama da an fara gudanar da wannan training din za ana barin yaran suna fita suna shiga wannan dajin da ake yawan samun matsala,ba don komai ba sai don mu kama wa inda ke aikata wannan mummunan lamarin,za ayi shiri sosai da baza su je kara zube ba,kuma ba za asamu matsala ba In Sha Allah domin kuwa a lokacin suna da kwarewar kare kansu."
Karaf wata mata ta katse Deejerh da fadin, "kare kansu kamar ya? Mun aminta da batun training din amman batun a hada baki da su a koma wanda ke wannan lamarin babu shi Domin ko an kamasa babu abun da aka isa yi a karshe ma mu za a kara jefawa cikin wani bala'in kinga angudu ba a tsira ba kenan."

Tana shiru wata ma ta fara, "Gaskiya kam indai sai hakan yafaru gwanda mu hakura da training dinma gabadaya, tun ana illata yaranmu su kadai baza mu kai kanmu inda za a hada damu da mazajenmu ba."

Alamu dai ya nuna cewa suna shakka ds matukar tsoron duk mai aikata wannan badalar kuma akwai yiwuwar cewa wasu sun san shi, tsoro ne ya hanasu bayyanawa bare kuma akai ga tunanin daukan mataki.

Wajen ya kaure da hayaniya, Papi ya dakatar da su da fadin , "in dai kun yarda dani, kuma kun yarda da duk abun da zan kawo gareku bana cutarwa bane, to ina so ku bawa Deejerh hadin kai,sannan batun duk da muka yi anan ya zamana iya mu dinne kadai ke da alhakin jinsi kada ko harafi daya ya fita."

Duk da cewa tsoro ne fal ransu amman kuma sun yarda da papi kuma ba za su iya bijire ma shi ba.
Hakan yasa suka amince.

Deejerh tayi musu godiya sosai da kuma alkawarin cewa da ikon Allah komai zai tafi daidai kuma zasu gyara rayuwar al'ummar kauyen ba tare da kasancewa cikin fargabar zuwa ko ina ba.

Ta cire rana biyu da bata zuwa office suna yiwa yaran training ita da Ammar.

★★★★Deejerh Ganin cewa tana kara samun gaba da matsayi kuma rububin Designing dinta ake ako ina,sannan ogansu gabadaya ya fi ji da ita ta fara samun matsala a wajen aiki.
Har ya kai ga tana zuwa wajen duk zasu watse suna bata fuska sai dai Somir da ya zama mayenta,duk inda zata yi suna tare.

Ranar tana gama aiki daga office ta nufi wani police station babba da ke cikin garin domin kai shigar da karar batun fyaden da ke afkuwa a kauyensu.

Hamida shine babba a wajen gabadaya hakan yasa ta bukaci ganawa da shi kai tsaye.
Da har ya nuna ba zai iya ganawa da kowa ba ganin cewa lokacin tashinsa ya yi,ta window yana ganin Deejerh ya bada izinin ta shiga.
Tana shiga ya bata wajen zama.
Binta yake da kallo tana shiga,ta sanar masa da sunanta da kuma kauyen da take,sannan ta fara yi masa jawabin makasudin zuwanta da kuma abun da take so ayi.

Hamid ya ce, "Ehto Yan mata wannan matsalar babba ce amman kuma ba wacce ake damuwa da hukunci akanta ba, domin kuwa sai adau karamar matsala da bata kaita ba a girmama, yawanci irin cases dinnan baya kaiwa ko ina da an fara akan sa a dikilar domin mafi yawanci masu hannu da shuni ke aikatawa,yanzu kuwa da duniya ke kara tabarbarewa da an bada wani abu,ko anyi wata barazana Shikenan za a rufe abu duk girmansa, saboda ke,zan yi iya yina inyi kokarin ganin anyi abun da kikeso In sha Allah zaki karba numberta in kinje gida ki kirani ma karasa maganar a waya kinga yanzu lokacin tashi a aiki ya yi."
Ya fada fuskarshi sake.
Murmushi ita ma Deejerh ta yi tana yi masa Godiya ta karbi number sannan ta fita ta tafi.

An ci gaba da yiwa Yaran kauyen training a ɓoye kuma suna samun kwarewa sosai ko da Deejerh bata nan Ammar na kokari wajen gabatarwa.

★★★
Lokacin taron Fashion Designers na karshen shekara ya yi,kuma daman duk shekara kowanni kamfani suna tafiya ne da gwarzuwarsu wacce take tashe kuma mutane ke ji da ita domin samo masu kambun kasancewa Best Fashion Design Company.
Domin taro ne na gani a fada da manyan mutane,kasashe daban-daban suke halartar sannan ake tanadar wani kofi na musamman domin baiwa duk companyn da suka ci wasannin da ake tsarawa a wajen sannan kuma sukai shigar da ta birge ko ince babu kamarta.
Wanda suke yiwa lakabi da Coketail Party.

Tunda Mr Charles ya sanar kan cewa da ita kadai zai tafi ta kara fadawa wata matsalar kowa na jin haushinta da jin tsanarta.
Ita kuwa Deejerh aranta ma sam bata wani son zuwa Dubai din ta kudirta cewa zata sanar Mr Charles ya yi hakuri ya dauki wata.
Da ta fadawa Ammar da Ma'am sai suka nuna yin hakan bai kamata ba, ta yi wa ogansu biyayya ta amince ta bishi sannan ta yi addu'a.

Haka ta amince ba don taso ba, Mr Charles da kanshi ya yi mata bayanin irin kayan da zata yi Designing tasa a taron.
Yanayin kayan duk sai ya fitarwa da mutum sura a takaice ma duk kirjin ta zai kasance a wajene.
Bata ce masa komai ba ita dai ta yi Designing din amman ta rufe duk wata kofa da surarta zata fita.
A ka kammala komai suka bi jirgi.

★★DUBAI
Dare ne ranar taron, wanda ya kasance tamkar sallah ga fashion designers din duniya da ke ji da kansu hakan yasa kowa yake kokarinsa iya yi wajen ganin ya birge a wannan ranar.
Shaye-shaye babu irin wanda ba ayi wanda ya zamto masu ma gasa ne kowanni kamfani zasu sha aga wa inda suka fi kowa iya kokarin sha ba tare da sun fice a hayyacinsu duka ba.

Mr Charles na gani shigar da Deejerh ta yi ya bata rai cikin fushi yana jan hannunta tare da fadin, "mene ne hakan? Wannan wacce irin shiga ce kika yi? Kina so ki zubar mun da mutunci? Haka na ce kiyi?"

Deejerh ta ce, "Sir ba zan iya yin waccer shigar da ka umarta ba domin addinana ya haneni ga sanya kayan da zai fiddamun tsaraici waje matsayina na mace."

Cikin Fushi y daga hannu ya sake mata mari a fuska,zai kara sake mata wani tayi saurin dakatar da shi ta hanyar rike masa hannun.

Ya ce, "ki sani wallahi Allah na rantse muddin kika sa wannan damar ta yau ta subuce mana ki kuka da kanki da duk abun da ya biyo baya."
Yana gama fada ya shige dakin taron ita ma ta bi bayanshi.
Kasaƙe Deejerh ta tsaya ganin yadda ake rayuwar badala a wajen.
Wasu matanma kayan jikinsu tamkar babu ne.
Ga shi sai tikar rawa suke da shafe shafen jikin juna.

Jikinta a sanyaye ta karasa tebur da Mr Charles ya zauna ita ma ta zauna suna hada ido yana binta da wani mummunan kallo,duk da cewa a tsoro take amman a zahiri kuma murmushin karfin hali ta sake masa.
Ya kara kula a cikin ransa.
Ba bata lokaci suka fara wasanni taron ta hanyar gabatar da kai.
Deejerh na gabatar da kanta gabadaya binta da wani irin kallo suke na raini ko ince kallon rashin isa.
Daga nan aka fara kawo giya.
Aka ajewa kowa kwalba uku.
Daga mazan har matan kowa kokarin shanyewa yake amman Deejerh ko motsawa batai ba bare tayi kokariin sha.
Mr Charles ya bige kafarta ta kasan tebur.
Ta kalleshi kafin ta girgiza masa kai alamar ba zata sha ba.
Har suka gama sha Deejerh kam ko daga wa batai ba.
Mr Charles ya kara kula ranshi ya ɓaci.
Aka zo aka kawo masu kashi, kashi dai na mutane wanda yake a ka'idar partyn har kashi suke ci.
Nan ma haka sukai tururuwa suna ci tamkar nama, Deejerh kuwa harda toshe hanci ta ki tabawa bare tunanin ci.
A karshe ma tashi tayi ta bar wajen.
Suka bi ta kallo.
Duk wani abu da suke agun kin shiga tayi ta ja gefe.

Kafin a gama ta fice ta hau taxi ta koma hotel dinsu da suka sauka.

Idanun Mr Charles sun canja kala jajir takaici ya rasa inda zai sa kanshi da aka tashi shi ya bi bayanta kai tsaye dakin da take ya fara nufa cikin zafin rai yake nocking kofar......


08103080717
[3/5, 9:55 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-45

Deejerh na budewa ta koma gefen gadon ta zauna.
Cikin fushi Mr Charles ya fara magana, "kin san asarar da kika janyo mun yau kuwa? Na ce kinsan koma bayan da kika jawa company a yau kuwa? Kin manta furuncin da na miki tun farko ko? Ina kara jaddada miki cewa duk abin da ya biyo baya kike kika janyo domin kuwa hukunci mai tsanani ya hau kanki babu tantama, kuma ki shirya gobe zamu bar kasar nan kuma kisa aranki sai kinyi mafiyin abubuwan da kika ki aikatawa a yau in mun koma." Yana gama fada ya fice tare da jan kofar da ƙarfi.

Deejerh kam bata ce komai ba,ta bishi da murmushi kawai.
A cikin ranta kuwa bata jin dadi ko kadan tunani take ta ya zata fuskanci wannan kazamiyar rayuwar tasu a haka.

Bata wani

Please Login or Register in order to submit comment