Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nayi aure na rasa 'Yanci da ikon yin abun da nake so ne? Never ba fa zai yiwu ba gwanda ka sani tun yanzu, And maganar zuwa taro da kai, kai jellatane? Don kawai na aureka sai ka na bina duk inda zani? In fadawa duniya Ni ina da miji ma kenan,akwai fa abubuwan da ,da yawa ba zan dauka ba , in kuma kai ma bazaka iya hakan ba kofa abude take za a iya kunce auren kowa ya huta."

Zayd na jin maganar kunce aure da sauri ya ce, "abar maganat nan ya wuce kin san dai ina sonki kuma kinfi mun dukkanin matan duniyar nan."
Wani murmushi ta sake tana daga masa gira, "Eheen now ko kai fa."

★★★Paris.
Sun gama lectures ana fita break camellia taje Sit din su Deejerh da Esme.
Dake a class suke barin jaka kuma sai Esme ta raka Deejerh tayi sallah kafin suke dawowa su ci abinci tare.
Hakan yasa ta lallaba ta dauki jakar ta lalubo robar drinks din Deejerh ta jefa mata wani magani ta jijiga sannan da sauri ta koma gunta kamar ba ita ba.
Ranar kin fita tayi a class din har sai da suka dawo taga sun ciro abincinsu suna ci.
Tare suka ci abincin amman drinks kowa na shi ya sha.
Ai kuwa Deejerh tun kan ta gama cin abincin jikinta ya fara mutuwa ta fara jin wani iri.
Camellia na fahimtar hakan tashi tayi ta fita can ta dawo ta ce wa Mr Jacques na Kiran Esme a office dinsa.
Kallon Deejerh ta yi ta ga yanayinta ya canja ta ce "lafiya kuwa?"
Cike da karfin hali Deejerh ta ce, "lafiya kalau kije ki dawo."
Esme na fita Camellia ta kulle kofar class din ƙam.

Ta karasa Gun Deejerh tana hadiye yawo kamar wacce ta ga gashsshiyar kaza.
Tana zuwa ta fara kissing dinta tana matsa mata jiki , "Kinga yau kin shigo hannuna ko? Ba damar mari kuma babu damar hanani abun da nake so." Ta fada tana wata irin dariyar mugunta.

Jikin Deejerh ya gama mutuwa jinta take ta gagara wani kwakkwaran motsi, gashi yadda ta rufe kofar nan tasan ko tayi kara babu me jinta, bare ma ba ta da karfin daga muryar.
Idanunta ne ya fara cika ganin cewa bata da mafita.

Bilhakki Camellia da gaske so take sai ta biya bukatarta da Deejerh.
Yanayinta har canjawa ya yi tana wani irin nishi da gurnani.
Musamman da ta ga Deejerh bata da damar hanata abun da take so.

Daga mata riga tayi tasa bakinta tana sha mata Brest har wasu sambatu take tana shafata.
Tana gamawa ta sauko ta janye mata Wando nan ma tasa bakinta a gabanta tana tsotsa.
Hawayene ya fara kwarara daga idanun Deejerh kokarin danne zuciyarta tayi ta fara karanta Addu'ar neman kariya daga masifa da bala'i .
(Allahumma inni a uzu bika min jahdil-bala'i wa darakish-shaqaa'i, wa su'il qadhaa'i,wa shamaatatil-a'ada.)
Ita ta dunga karantarwa tana maimaitawa.

Tana kokarin sa tusa mata hannu gabanta kenan Allah ya bata ikon daga kafa ta bigeta har saida ta bige fuskarta da bango.
Da karfin ikon Allah ta ji karfin jikinta ya dawo duk sakewan da ya yi ta dawo daidai.
Ta tashi ta kama camellia ta dunga duka har sai da ta ji mata ciwo a fuska.
Duk yadda taso da ta kwaci kanta ta gagara har sai da Deejerh ta gaji ta saketa.
"Wannan shine kashedi na ƙarshe,ka da ki kuskura ki kara ko tunanin taba wata fata ne a jikina, inko hakan ya faru ki tabbatar da cewa a wannan ranar zan karya kazamin hannunnan naki, zuciyar ki kazamiya ce da duk wani abu dake tare dake muddin kina gabar yin wannan mummunar dabi'ar abu mafi muni da Ubangiji ya tsana, ki tura kanki ga halaka, ki tarwatsa rayuwar ki? Kije ki illata kanki da kanki? Wannan abun fa Yana haifar da yaɗuwar ciwon sanyi,yana sa ƙyaiƙayin farji,yana kawo cutar ƙanjamau,wato (AIDS) sannan yana haifar da ciwon mara,haka kuma yana haifar da ciwon ruhi (spiritual problem)
Annabi Muhammad Mai Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata Agare Shi, Yana Cewa Wallahi inda Za'a Baki Ladan Annabawa Su 70 gashi dai ko Ladan Annabi ɗaya aka Baki Ana Ƙyautata Zaton Zaki Shiga Aljannah, Zaki ma Shiga. Amma Wallahi Manzon Allah Yace Ladan Waɗannan Annabawa 70 nan Ba Zai Taɓa Sanya Ranki Ya Samu Natsuwa ba in ba dai kin ga Kanki a Cikin Gidan Aljannah ba. duba fah Ki Gani Wannan fa Irin Tashin Hankali da Bala'in da Yake a Ranan Alkiyama ne Annabi yasa ya Faɗi Haka, Don Allah Wani Irin Ayyukan Lada ko ibadah da Kike yi a Kullum Wanda Ladan ki Zai iya Rinjayar Ayyukan Zunuban da Kullum kike Aikata Su? Menene Amfanin baɗi ba rai? Bin yar uwar ki mace don kawai kiji dadin duniya na ɗan lokaci? A addinan ce hukuncin masu aikata wannan badalar kisa ne, ko dan kawai kunga yanzu ba a amfani da hukuncin yasa kuke kara jin dadin kasancewa ciki? Ki sani in babu hukunci anan akwai na lahira wanda yafi kowanne kiji tsoron Allah,kuma ki karbi darajar da Ubangiji ya baki matsayinki na 'Ya mace kada ki zubda."

Tunda ta kifa kanta bata dago ba, azaba take ji ta ko ina kuma tana sauraren duk abun da Deejerh ke fada.
Tashi tafiya Deejerh tayi ta bude kofa ta fice mata daga class din.
Tana fita ta ga Mael.
Subutar baki yasa shi fadin, "Vixeen Esme nata nemanki."

Da mamaki ta dago ta kalleshi tana maimaita sunan, "Vixeen?"
Sai a lokacin ya ankare ya ce, "Oh Sorry Deejerh, Esme na garden tana jiranki."
Yana fada ya tafi da sauri.

Ci gaba da tafiya tayi taje ta samu Esme.
Ta ce, "na je office dinsa a kulle kuma na dawo naga class dinma a kulle ina kika yi ne?"

Deejerh ta zauna tana, "bari kawai na dan fita ne."
Suna zaune Camellia tazo wucewa zata shiga motarta tana tafiya da kyar, fuskarta duk ciwo.
Esme ta ce, "kalli mutuniyar ki? Meya sameta kuma oho."
Kau da kai Deejerh ta yi ta ce, "rabu da ita Kinji ita ta sani."

Deejerh na juyowa suka hada ido da sauri ta kau da kai har tana kokarin faduwa haka ta lallaba ta shige motarta.
Ranar ba a karashe masu lectures da ita ba.
★★
Deejerh na sauka a bus ta kama hanyar shiga kauyensu sai da taje daidai tsakiyan jeji kanta ya fara sarawa jiri ya dibeta ta fadi lokaci guda......



08103080717

*Till Monday🥺sai hakuri fa da haka za mu rarrafa har a gama lokaci ne yyi karanci*

[1/30, 6:48 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-40

Sanyi sai kaɗawa yake,ban da sautin bishiyoyi da kukan tsuntsaye babu abun da ke tashi.

Ita kadai yashe a kasa iska na kaɗata.
Tun gari na da haske har ya yi duhu.
Hankalin Ma'am ya matukar tashi da ta ga lokacin da Deejerh ta saba dawowa har ya wuce bata dawo ba.

Hakan yasa ta tashi ta fita, tana hanyar zuwa neman Ammar kenan sai gashi shima yana kokarin zuwa gidanta.
Ganinta da ya yi cikin yanayin damuwa yasa shi saurin karasawa yana, "Lafiya kuwa Ma'am? Gunku na nufa yanzu daman."

Ma'am ta ce, "Wai daman bakwa tare da Deejerh? Bata dawo gida ba fa,kamar wasa na zata kuna tare tunda naga kai ma baka zo ba."

Ammar ya ce, "Ya Allah! Ni ina gun aiki yau aiki ya mana yawa ban samu na fito da wuri akwai wa inda sukai ordern faint to amman yanzu ma ina taje to? Nasan dai ba wani guri da ta sani bare ince tana cen."

"Nima abun da ya daure mun kai kenan nasan lafiya dai baza ki dawowa lafiya kalau ba,dole akwai matsala ina ji a jikina." Ma'am ta fada cikin yanayin damuwa matuka.

Da saurin murya Ammar ya ce, "ina ga akwai bukatar muje Gaskiya mu bi hanyar mu gani ko lafiya in ma bamu ganta ba ina ga School din zamu wuce kawai."

Ma'am ta ce, "zaifi kam muje kawai."

Dajin suka fara kutsawa, Ammar na haska masu da torch light din wayarsa.
Sun zo daidai inda Deejerhn take kwance amman basu lura ba har ya taka ƙafarsa akanta.
Sai da suka yi gaba kafin zuciyarsa ta saƙa masa kan cewa ya fa taka wani abu,wani abu ne wannan? Akwai bukatar su koma ya duba.

Ya cewa Ma'am, "Maa Please bara in haska cen in gani naji kamar na taka abu." Ya fada yana komawa da baya.

Yana zuwa kuwa ya haska mai zai gani ban da Deejerh kwance iskar sanyi na hurata.
Da karfi ya kwarawa Ma'am kira.
Ta karasa jikinta na rawa.
Shi kam ya rasa abun cewa daukan Deejerh ya yi kawai ya saɓa a baya.

Cikin firgici Ma'am ta taɓa jikin Deejerh ta ji sanyi kamar kankara, sai da ta taba kirjinta da hancinta ta tabbatar tana numfasa kafin tayi ajiyar zuciya da fadin, "Ya Allah, ka dubi wannan baiwa taka, ka bata ingantacciyar lafiyar da zata amfane ta ta amfani al'umma, Ubangijina ina rokonka da ka bata kariya da kariyarka,ka tsareta da tsarewarka,ka kara mata kwarin gwiwa tare da karfin buskantar kowanni kalubale na rayuwa ba tare da gajiyawa ba."

Ta cire mayafin ta da ta rufu ta rufe Deejerhn da shi a bayan Ammar.

Da haka har suka karasa gidan,ya kwantar da ita gado, Ma'am ta hada gaushin gawayi dakin ya fara daukan dumi,kuma suka lullubeta da bargo.
Sannan Ammar ya je ya kira Papi.
Yazo ya dubata sannan ya ce, "abarta kar a mata komai yanzu zata dawo daidai."
Har cikin dare Ammar bai tafi ba suna zaune da Ma'am sun saka Deejerh agaba bata farka ba.
Tunaninta da Adduo'in da ta bashi yake,take ya karanta Fatiha da Amanar Rasulu ya roki Allah da ya bata lafiya kuma yasa ta farka..
Yadda suka ga rana haka su ka ga daren ranar.
Sai wajen karfe uku da rabi da ta farka wanda daman a ƙa'idar ta kan tashi lokacin ta roki Ubangiji daga nan kuma bata komawa barci ta kan kama duk wani aikine tayi.

Zata tashi Ma'am tayi saurin riketa.
Deejerh ta yi Murmushii tana, "Maa me ya faru? Kai kuma Jarumin dole me kake cikin daren nan anan?"

Ammar ya ce, "kar ki tashi ki fadi ki nutsu kinga baki da lafiya."
Deejerh ta ce , "Aa nikam ina da lafiya ji na nake Normal ba wani canji."

Ma'am ta ce, "Ma Sha Allah amman me ya faru baki dawo gida ba, a hanya fa muka tsinceki."

Deejerh tayi shiru,sai a lokacin ta tuna da abun da y faru ta ce, "oh nidai kawai nasan bayan na sauka a bus na ji jiri daga nan kuma ban san meke faruwa ba,sai yanzu dana farka."
Ammar ya ce, "Okay amman kina tafiya da magungunanki na gun papi ki daina wasa da sha kinji please,duk da ke mummuna ce amman bama so ki mutu yanzu.".
Harara ta bishi da shi kafin ta ce, "to an fara kiran sallah sai atafi masallaci."
Ta fada tana tashi.

★★★ko da gari ya waye Deejerh bata da Lectures ranar aikin Packaging coal dinta suke da Ma'am da Ammar.
Suna cikin yi ta ce, "ka ji abun da ya ban mamaki a School kawai na ji ana cemun Vixen, female fox fa kenan."

Ammar ya yi dariya, "ai kin ci Vixeen dinne Shiyasa suka kiraki da hakan nima daga yau Vixen zanna ce miki matsalar dai female fox kyakkyawace ba irinki ba."

Deejerh ta ce, "kai ka bar dariya serious taya za ana dangantani female fox."

Ammar ya tsaya da aikin da yake ya ce, "ba suna nufin Female fox ce ke ba,bari kiji cikakken bayani akan Vixen na tabbata hakan suke nufi yasa suke dangantaki da ita, VIXEN Female foxes are very intelligent and adaptable creatures. They're often solitary animals, and they can survive in a wide range of habitats. Vixens are excellent hunters, and they can catch a variety of prey, including small mammals, birds, and reptiles. They're also good climbers and swimmers, which allows them to escape from danger and find food in difficult terrain. In addition to their physical abilities, vixens are also very vocal animals. They make a variety of different sounds, including barks, yips, and whines.
Also female (Vixeen) Vixens are known for being cunning, clever, and very smart. They're also known for their agility and speed, and they're often seen as symbols of grace and cunning. In popular culture, they're often portrayed as sly tricksters who use their wits to outsmart their opponents.(a takaice dai ana nufin mace nutsattsiya,mai wayo,da kuma saurin gane abu ko ince iyawa kuma zasu iya rayuwa a ko ina tare da kubutar da kansu a cikin kowanni hadarin rayuwa,suna da kula da tausayi, amman sam basa daukan wargi ga duk wanda ya yi kokarin danne su ko cutar da su suna da zuciya mai zafi sosai ta wannan bangaren sannan suna kokarin koyarda duk wani na kasa da su salon yadda zasu kubutar da kansu a wani haɗari ko in wani yazo cutar da su) so kinga baki da wata cikakkiyar maraba da Vixeen, ke Vixen ce amman ba female fox ba."

Deejerh ta kalleshi kawai ta sunkuyar da kai.

Ci gaba da aikin su suka yi.
Can Ammar zai mata magana ya ce, "Vixen."
Daga kai tayi ta kara sake masa harara.
Ya yi dariya kafin ya ce, "kin ga kiyi sauri tunda yau kina free yawo zamuje muga gari kar yamma tayi muna nan."

Deejerh da taji maganar yawo tuni ta kara daga kanta ta ce, "Yes yanzu ma kuwa kamar kasan ina son yawo wallahi."
Dariya ya yi ya ce, "um yawo ba."

Yamma nayi Deejerh ta shirya cikin shigarta na doguwar riga baka da karamin gyalen fari ta tayi Rolling duk da cewa bata yi kwalliya ba bayan sunyi sallar la'asar kafin Ammar yazo da motarshi.
Duk da kasancewar bai san shigar da tayi ba amman sai ya zamana kamar sun hada baki.
Bakin Jeans yasa da farar t-shirt.

Dukansu sai suka tsaya kallon juna,shi ya katse shirun da fadin , "Eheen Vixeen wato kin bi kin laɓe kin ga irin kayan da zansa kin sa ko?"
Deejerh ta ce, "Umm nikam mu tafi amman zamu aje motar ne mu dan tattaka da kafa ko?"

Ammar ya shiga yana, "As You Wish Vixeen."

Ta galla masa harara, "na bi Vixeen da gudu."

Cikin gari suka nufa.
Deejerh ta ga sai tafiya suke ba kakkautawa.
Ta ce, "ni kam wai ina zamune? Tafiya taki ci taki cinyewa?"
Ammar ya yi murmushi.
"Kadai kawai ki zuba ido,mun kusa."

Kai Tsaye bakin shiga Effel Tower Ammar ya tsaya da motar sa.
Cike da mamaki Deejerh ta furta, "Wooow Effel Tower gurin da na sha mafarkin zuwa,ina yawan jin labarin gurin nan agun mutane gashi ma tun daga waje na fara ganin kyansa fiye da yadda suke bada labari, gaskiya ka shammaceni nayi farinciki matuka."
Ammar ya ce, "eheen waje ne na musamman dake cikin garin Paris, and yana daya daga cikin wajen shakatawan da mutane suka fi kaiwa ziyara a duniya gabadaya, haka kuma yana dauke da matattakalu har guda dari bakwai, Effel Tower wajene da duk wanda yazo cikinsa ba zai taba mantawa da shi ba,domin wajene na jin dadi,samun nutsuwa da nishadi."
Deejerh ta girgiza kai fuskarta dauke da murmushi ta ce, "Eheen mu shiga to mana nifa na matsu."

Shiga ya yi da motar suka fara zagaya gurin suna shiga suna fita yana yiwa Deejerhn hoto wani gun kuma ya musu Video.
Ta hau kan stairs yana yi mata hoto kenan wasu securities biyu suka katse su da fadin su bada ID card dinsu.
Ammar ya nuna na shi.
Ita kuwa Deejerh suman tsaye tayi domin bata da shi kuma bata san hanyar nemowa a yanzu ba.
Dayan ya ce, "tunda alamu sun nuna cewa ita bata da shi to zamu dauki hotonku duka a yanzu domin tabbatar da cewa kun shigo mana kasa ko ince ka shigo mana da ita kasa ta gurbatacciyar hanya,sannan dukanku zamu tafi da ku domin tabbatar da bincike akanku a halin yanzu akwai alamar tambaya akan ku."
Ya karasa maganar yana kokarin sawa Deejerh ankwa a hannu.....
[1/31, 7:43 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-41

Ammar ya yi saurin dakatar da shi da fadin, "No Sir tana zaune ne a karamin kauyemu take, kuma yar uwata ce,so ba a kai ga yi mata ID card ba yanzu muna shirin yine a nan cikin garin."

Securityn ya ce, "karya ne wannan zancen karya ne kuma dukanku sai an kulleku sannan sai anci tararku."

"Ah! Ina fahimtar da ku amman sam kun gagara fahimta? Ko sai na muku ta hanyar da zaku fi saurin fahimta ne?"

Dayan yaja hannun Deejerh da karfi zai daure mata.
Daga hannun da Ammar zaiyi ya bankare masa hannu yana, "kar ka kuskura, na ce kar ma ku kuskura, yadda kuke da yanci a kasar nan haka muma muke da shi,don haka yanzu zan rubuta jawabin abin da kuke shirin yi damu da ku zan ga wa inda za a kama da har za a kulle."

Kokarin kwace hannunsa yake amman ya gagara sakamakon mummunan rikon da Ammar ya masa.
Dayan kuwa yana ganin hakan a hankali ya sabule ya gudu.

Shima yana samu ya kubuta daga hannun Ammar ya arce.
Kallon Deejerh Ammar ya yi ya ce, "Yar kauye kawai duk ta birkita."
Deejerh ta ce, "eheen duk abuna ai ban isa in taba hukuma ba,in tabaso in tabowa kaina jalala gwanda kai cikakken ɗan kasa ne."

Dariya ya kariya ya ce, "bawani nan yar kauye dai kin razana."

Ci gaba da za gaya wajen sukai sai yamma kafin suka koma kauyensu.

★★★★kwanci tashi ba wuya, kamar wasa yau ya kasance ranar da za a yaye su Deejerh daga Stylish Wordplay fashion School.
Taro aka hada gangarimi wanda aka bawa dukkanin students din damar Designing kayan da zasu sanya aranar da kansu.
Hakan kuwa ya kasance sai dai Deejerh ta fita daban kamar yadda take daban haka ta fito daban a asalin Vixen dinta.
Riga t-shirts tayi da wandon Jeans wanda akayiwa rigar ado da kalan Jeans din.
Bata yi wani ado yar batse ba hakan yasa ya matukar fitar kyan kayan a jikinta sosai.
An karramata kamar yadda aka fara bata Best student of year a farkon farawarsu haka aranar kammalawan aka bata kambun most outstanding student of year,da kyautttuka sannan School din suka recommending dinta ga wani Company babba da suke neman kwararriyar fashion designer (Chill Couture) shine sunan compyanin.
Ammar da Papi tare Ma'am duk sunje mata.
Ana bata kyaututtukan sauka tayi a stage fuskarta dauke da hawaye ta karasa gabansu.
Duka ta hada hannayensu waje guda tare da sanya masu kambun karramawar ta ce,"wannan kambun naku ne,ku ya cancanci in mikawa domin kuwa kune kuka kasance mun haske a lokacin da duniya ta mun duhu, haka kuma kune kuke zame mun bangon jingina a lokacin da na rasa wajen jingina,kune matakin kowacce nasarata a yanzu na rayuwa , taya zance zan manta da ku?"
Dukan su rugumeta suka yi Ma'am ta share mata hawaye tana, "ka da ki dauke mu bare a gareki mu ahalin ki ne,kuma ko wanni hali,kowanni yanayi zamu kasance a tare da ke da dukkan wani abu da muka mallaka na rayuwa."
Papi ya ce, "sosai ma,ji nake tamkar jinin jikina 'Yata dana haifa ,ina alfahari dake kuma a ko ina ba zan ji shakkar tsaya miki ko kareki a matsayin uba ba."

Ammar ya ce, "Vixeen yau dai daya zan ce miki kyakkyawa."

Dukansu dariya suka yi kafin suka zauna suka ci abinci bayan an gama suka kama hanyar gida.

Hutun wata guda Deejerh tayi a gida ta fara aiki a Chill Couture Company.
Tana kara goge Sosai musamman da ta kara tsintar kanta cikin manyan fashion designers.
Sai dai abun takaicin shine yawanci dabi'un da ta tarar munana wasu na yi a Stylish Wordplay anan dinma wasu da yawa nayi wanda ya tabbatar mata da cewa kasancewar mutum a fashion industry sai ya dage kuma ya daure tare danne zuciyarsa kan wasu lamuran.
Hakan yasa ta ci gaba da rayuwarta ba tare da lura da rayuwar kowa ba.
Sai dai kuma namiji guda da ya manne mata da nufin soyayya Somir.
Musulmi ne cikakken dan Paris farar fata kuma kyakkyawa amman shi ma yana cikin tsarin bin mata da burin yin sex kawai.
Amman ita kuma Deejerh ya je mata da lamarin inta amince shi aurenta kawai zaiyi kuma ya daina abun da ma yake.

Duk da cewa ita ce mafi karamin shekaru cikin industry din amman yanayin yadda take rayuwa hatta manyan girmama ta da shakkarta suke da gudun aikata mata wani abun da ba daidai ba.
★★★mexico
Kara neman kudi Zayd yake fafur ba ji ba gani wanda har ya kai ga ya bude Companyn drugs na weight loss drugs.
Ita kuwa Huda kara tsula tsiyarta take kamar wacce ake sakewa burki.

Kwance suke kamar an zaburi Huda ta tashi tana, "Zayd
Muna kusan shekara biyu fa da aure amman abun mamaki har yanzu ciki bai shigeni ba kuma na cire planing din da na yi,so meke faruwa ne? Akwai bukatar muje muga doctor fa."
Tana fada gabansa ya yi wani irin mummunan faduwa wanda sai da yanayin sa ya sauya.
Ta kalle shi tana ta ci gaba da magana , "ko da matsala ne? Na ga yanayin ka ya canja."
Cikin in ina ya ce, "N....n...no kawai dai nima na ji mamaki ne."
"Okay ni dai gaskiya ina so in haihu yanzu ina son ganin yarana fa gobe kawai ka zo muje hospital."

Zufa ce ta fara keto masa yana gogewa.
Ya ce, "e...ee..to ke kije ni ina da meeting s company goben inna gama sai inzo in sameki."

Yana gama maganar ya tashi ya fita.
Binshi tayi da kallo a zuciyar tana fadin, "ko me ya same shi oho."
Ta ci gaba da danna wayarta.

Shi kuwa hankalin sa tashe ya shiga motarsa.
★★★
Paris
Zaune Deejerh take tana hutawa, Somir ya zauna kusa da ita yana fadin, "Assalamu alaikum our Vixeen xan iya zama?

Dake tun daga Stylish Wordplay vixen ya bita kusan mutane da yawa yanzu da shi suke kiranta.
Ta kalleshi ta ce, "Wasallam alaikum,Why not?"

Zama ya yi yana fadin, "Thank you."
Ya yi shiru ita kam hankalin ta na kan wayar ta,sai cen kuma ya ce, "maganata daya ce a kullum a jikaina Aban dama,na yi alkawari duk abun da kika ce in daina zan daina."
Deejerh ta yi Murmushii ta na aje wayar ta ta kalleshi.
"Duk wani abu da kasan kana yi ba dai-dai ba na fi so ka daina don ra ayin tsoron Ubangiji ba don ni ba, and ni kuma na fada ma ba fa zanyi aure ba,ni ba ma zan iya rayuwar auren ba maganar kenan kuma ina fatan ka gane."

Ya ce, "taya zakiyi rayuwa babu aure? Dole zakiyi kuma ni zaki au....
Jin sautin wata murya ya yi ana katse shi da , "In bana raye kenan."
Daga kan da zasu yi duka biyu su ka yi ido hudu da.....
[2/5, 9:35 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-42

Daga idon da zata yi Deejerh ta ga Ammar na sake mata murmushi.
Mikawa Somir hannu ya yi,yana fadin, "Assalamu alaikum."
Ciki-ciki Somir ya amsa dauke da takaici mussaman yadda ya ga ganin Ammar kawai yasa Deejerh sake fuska aransa ya ke radin, "ya tabbata dai kenan wannan matsiyacin take so? Aiko duk sai na yi yadda zan yi in kwaceta."

Ya kallesu duka kafin ya tashi ya bar gurin ba tare da ya musu ko sallama ba.
Yana tafiya Deejerh ta yi dariya tana , "ka zo a daidai kuwa kamar ka san na rasa yadda zan yi da mutumin nan."

Ammar ya ce, "na san ai halinki sarai ne,amman ni da na sani ma na bari ya gwada sa'arsa kila ya dace kuma fa gashi kyakkyawa ba irin ki ba, ya ma miki kira ne yake ta biki ai."
Deejerh ta harareshi tana murmushi, "ko ba kara ba? Ni ban son karar to ya rike abarsa,kafi kowa sanin ji nake na tsani wani batun aure ko soyayya kamar yadda ban son rasa wani nawa."

"Na sani,amman ina fatan gaba komai ya daidaita ke mace ce kuma kina bukatar yin aure duk rintsi ba zan so ki zauna haka ba, gashi ni ma kin hanani auren ai tunda kinki amincewa dani in rufa miki asiri in taimakeki." Ya fada cikin sigar tsokana.

Deejerh ta ce, "ka ji dashi dai da tarin yan matanka ka rasa wacce zaka tsayar."

Ammar ya yi dariya yana, "ina fatan dai kin kammala aikin yau din zamu iya tafiya yin Resident card din ko?"

"Yes, bara inje inyi Sign Out." Deejerh ta fada tana daukan jakarta da gyara mini Hijab din da ke jikinta.

Zuwa tayi tai signing din kafin ta dawo suka tafi.
Suna zuwa Office din Ammar

Please Login or Register in order to submit comment