Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amman kara jaddada miki cewa kisa aranki za ki iya, zaki iya da rayuwarki, zaki gina rayuwarki da tafin hannunki, zaki kunnawa rayuwarki haske da fitilar zuciyarki, ka da kisa tsoron kowa aranki, kinji."

Maganganun da Ammar ya mata sun matukar shiga jikinta hakan yasa ta sake masa murmushi tana ajiyar dogon numfashi.

Shi ma ya maida mata da martanin murmushiin kafin ya ce, "mu je ko."
Ta girgiza masa kai.

Suna zuwa gun Gate din suka nuna pass din da papi ya basu sannan aka barsu suka shiga.

Dake Ammar yasan gurin kai tsaye yaje ya nufi office din Mr Jacques.
Bayan an basu izini sun shiga har sun zauna ma kafin Mr Jacques ya shiga kasancewar ya fita.

Idanunsa akan Deejerh ya fara sauka, ya tsaya yana kallonta magana Ammar ke masa amman ina, hankalin sa na kan Deejerh.
Ita kuma ganin yadda yake bin surarta da kallo yasa ta tsorata jikinta ya fara rawa.

Ammar ya ce, "Barkanmu dai Yallabai , Yallabai, Yallabai."
har sai da ya fada sau uku kafin ya kalli Ammar yana murmushi, "amman dai Design din kayan yarinyar nan ya yi matukar kyau ya ƙayatar dani,da gani za a so shi sosai a kasuwa."

Sai a lokacin Deejerh ta yi ajiyar zuciya aranta tana hamdalar godewa Allah da ya kasance kayan jikinta ne ya birge shi ba,surarta ba.

"Kodayake ba ma kayan ba har mai kayan za aso da alama." Mr Jacques ya fada cikin sigar tsokana yana dariya kafin ya kara fadin , "na ga duk kin tsorata nan ba ma cin naman mutane sai na dabbobi kinji, Welcome to stylish Wordplay fashion School Girl."

Ya fada yana mika mata hannu.
Hada hannunta biyu tayi ta sunkuya ta gaisheshi.
Cikin fara'a ya amsa tare da fadin, "Allah ya yi albarka yasa anzo asa'a."
Ammar ma ya gaida shi, kafin ya ce, "Ya Dr Ali ina fatan yana lafiya?"

Ammar ya ce, "lafiya lau ya ma ce agaidaka."

"Ma sha Allah. Hakan ya yi kyau." Ya kalli Deejerh ya ce, "Girl Da gaske design din kayan ki sunyi matukar kyau Dr Ali ya ban labarinki ina fatan mu ga mafiyin hakan a tattare da ke."
Kanta na kasa ta ce,"In sha Allah Sir."

Mr Jacques ya ce, "Alright Ammar yanzu kai zaka iya tafiya, ke kuma muje ki shiga Class don yanzu ma na an fara."

Tare suka fita Ammar ya tafi su kuma suka nufi Class din.
Jiki na dari dari Deejerh ta shiga ganin yadda duk suka jura mata idanu ana yi mata kallon tara saura kwata.

Class din irin seat mai mutane bibbiyu ne,ya kasance wata a gaba ita kadai Mr Jacques ya ce Deejerh ta je nan ta zauna.
Tana zama suka hada ido da dayar yarinyar ta sake mata wani kasurgumin tsaki tana janye jikinta tare da nuna ƙyama.

Haka Deejerh ta zauna a takure gam da jikinta.
Ita kuwa ta gefen nata Esme sai tsaki take tana kananun mita, har saida ta dauko turare a jakarta ta ta fesa, sannan kuma ta dauki facemasks tasa ta toshe hancinta.
Deejerh na lure da ita amman ta kau da kai tana bin karatun da ake yi masu kawai.

Ana cikin yi malamin nasu ya yi bayanin yadda yake fidda shape din wando jeans na mata, bayan ya gama ya ce ko da wacce zata iya kwatantawa kafin shi ya yi?
Dukkaninsu shiru suka yi har zai wuce Deejerh ta daga hannu jiki a sanyaye.
Ya ce ta tashi taje gaban Whiteboard dinsu ta gwada, kamar wacce akama duka haka take jan kafa har ta karasa.
Cikin zuciyarta na son yi amman a zahiri a tsorace take.
Ko da ta dauki maker dinma hannunta rawa ya fara, tana fara zanen ya karkace yaki tafiya daidai.
Ji tayi kawai gabadaya class din sun kwashe mata da dariya.
Ta daga kai ta kalli zanen, rufe idanunta ta bude, kafin ta ci gaba kan wanda ya karkace din.
Maganganun da Ammar ya fada mata ne kawai ke mata yawo a zuciya tana zanen.
Sabanin dariya da suke yi mata sai kuma ta ji an bige da tafi.
Ita kanta mamakin yadda akai ta zana take bare su kuma.

Malamin ya karba maker hannunta yana, "yau dai kam an bana mamaki rana ta farko da students dina ta yi Designing ba tare da na koya mata ba,kuma design mai wahala domin da dama har maimaicin aji ake samu akan wannan bangaren, can't believe this."
Ya kalli Deejerh kafin ya ce, "Mene ne Sunanki? Daga ina kike?"

Take idanunta suka cicciko hawaye na shirin fara yi mata ambaliya.....


08103080717

*°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-30

Laurent ya ce, "Oh Kukan na mene ne? Alright Sorry, Sorry ,sannu kinji , je ki zauna."
Ya fada yana lallashinta da hannu.

Share hawayen da ke fuskarta ta yi, ta saki murmushi ta daga kai ta kalleshi tare da fadin , "Sunana Khadeeja-Deejerh."

Tana fada ta juya ta je ta zauna a seat dinta.
"Nice Name, Weldone Deejerh,ina fatan wannan ya zama shine mataki na farkon ci gabanki ba tare da kinsa wasa ba."
"In sha Allah." Ta furta a zuciyarta.

Laurent ya ce, "Gaskiya yau ina farinciki matuka,infact ma I'm Speechless, sai nake ji a jikina cewa wannan set din naku zai kasance na musamman da ba a taba yin masu hazaka irinsa ba, na ji cewa zan so ku fiye da yan baya, ina fata addu'ar cewa Allah yasa kar ku bani kunya."

Esme ce karaf ta ce, "Oh Sir ba za mu taba baka kunya ba, wannan 'Yar talakawan ma ta yi abun arziki bare mu."
Ta fada tana yiwa Deejerh kallon tara saura kwata.

Shi ko Laurent cewa ya yi, "Za dai mu gani ai."
Daga nan ya yi masu design din da kansa ya nuna masu, sannan ya cirewa Deejerh inda ya kamata ta dan gyara domin daidaiton tsayuwar wandon.
Bayan sun gama ya basu Assignment kan kowa ya je gida ya yi ya tawo da shi next Class.

Duk da cewa Deejerh a takure take,amman ta ji Dadin karatun matuka kasancewar abun da takeso ne,kuma muradinta take cikawa.

Ana tashi ma haka ta fito zata fita kenan daga Class din Esme ta bangajeta har sai da ta kusan wuntsilawa, ta kalleta tana tauna cingum tare da daga keyn mota a hannu, ta kara sake mata wani kallon banza dauke da tsaki tana, "Poor Girl." Ta wuce cikin takunta na kasaita.

Deejerh ta kau da kai kawai ,ta tashi ta na karkade jikinta ta fita daga School din.

Ta kama hanyar komawa gida, ta yi nisa sosai har ta fara shiga cikin Dajin da zai sadata ga kauyensu, ba kowa shiru ban da kukan tsuntsaye da sautin iska bishiya babu abun da ke tashi.

Tana cikin tafiya ta bayanta kawai taji an zungureta, a zabure ta juya, bata ga kowa ba, ta ci gaba da tafiya cikin sauri,aka kara tabata,
Na ukun tana juyowa ta saki ihu idanunta rufe shima Ammar ya firgita kawai ya saki ihu.
Duka su biyu suka gauraye wajen da ihu.
Sai ita ce ta fara rage sautin nata a hankali ta bude ido kawai ta gan shi ya zake sai ihu yake.

Ajiyar zuciya ta yi tana tsaki,ta duba gefenta ta ga wani icce ta dauka ta maka masa a jiki.
A hargitse ya bude ido ya na waige-waige.
Deejerh ta kara yin wani gajaren tsaki kafin ta ce, "Jarumin jarumai anji jiki, wato madadin ka ban tsoro sai tsoro ya koma kanka?"

Hannu yasa yana sosa keya cikin wayancewa ya ce, "ba wani nan, nima na tayaki ne kawai amman akan me zan tsorata ma."

Kallon shi tayi kawai ta yarda iccen hannunta ta ci gaba da tafiya, ya bi bayanta yana fadin, "ke kin ma gode ai da nazo da yanzu wani dodo ne zai kamaki ya cinye gani na yasa ya gudu."
. Deejerh ta ce, "Umm."

Ya kara fadin, "Fatan komai dai lafiya? An yi karatu lafiya an kammala lafiya?"

"Alhmdu Lillah." Ta furta a gajarce.
Suka ci gaba da tafiya har suka shiga cikin kauyensu.


★★★★Mexico.
Zaune take tana danna Wayar da ke hannunta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,ga dukkan alamu ta ji dadin zaman da tayi,domin ban da murmushi babu abun da ke sauka daga fuskarta.

Nocking kofar da aka yi ne yasa ta daga kai nan da nan fara'ar da ke fuskarta ta dauke tana sakin karamin tsaki tare da fadin, "Yes Shigo."
Zayd ne yana zuwa ya rungumeta ta yi saurin janye jikinta.
Ya kalleta yana, "Mon Cherie ya haka? Kamar baki ji dadin zuwa na ba."

Tabe baki ta yi kafin ta ce, "Umm hutawa nake,kuma kasan in ina hutawa bana son takura sam." Ta karasa maganar tana kara shingidewa jikin kujerar.

Fuskarsa a raunane ya ce, "Me yasa kike mun haka ne Mon Cherie? Kin san bana jure zama ba tare da na ji motsinki kusa dani ba , ban san me na miki ba kike azabtar dani, Please ki fadamin in gyara, ina son farincikinki ina son ganin farinciki a fuskarki ina son kasancewa da ke."
Ya fada yana durkusawa gabanta tare da rike mata hannu.

Hannunta ta janye a hankali tana kara yatsina fuska.
"Nothing fa, ni kawai na fada ma hutu nake so Shiyasa bana son takura,kai kuma ka cika takura da naci wallahi."

Zayd ya ce, "shikenan zan yi kokarin ganin ina baki tazara in har zakiyi farinciki,amman ki sani ni zan cutu a cikin zuciyata,ban da burin da ya zarce ace na malleki, a yanzu kullum cikin fargaba da zillimun rasaki nake, ni dai fatana Don Allah karki barni......

Zata yi magana kenan sai ga wani ya shigo dakin.
Da sauri ta tashi ta rugume shi tana kai masa kiss
"Welcome baby, ina ta jiranka kasa na shirya tuntuni kaki zuwa ko?"
Ta fada cikin shagwaba.

Shi ma kissing din nata ya shiga yi na Tsawon minti guda kafin ya ce, "Sorry Beb sai da na biya office na aje wasu document ne, yanzu dai zamu iya tafiya ko?"

Ta ce, "Yes."
Sannan ta kalli Zayd da ya yi mutuwar tsaye ko ince suman tsaye ban da zufar takaici babu abun da yake , yana huci.

Ta ce, "Zayd zamu fita da Beb in mun dawo da dare zan kiraka ko? And please in ba abun da zaka yi,kadan gyara mun dakin kafin ka fita ko kuma ka kira cleaner."

Tana fada Wancen din ya dauketa cak tana dariya suna wasa suka fice.

Ji Zayd ya yi kamar zuciyarsa zata fashe tsabar zafi da kishi, idanunsa suka kada suka yi jajir , Gabadaya jikinsa ya fara rawa.
Bai san lokacin da ya fara buga kansa da bango ba har sai da jini ya fara bulbula daga goshin shi, ya kwashe kusan minti biyar a gidan yana fama duk ya hargitsa kansa ya ciwo kuma ya hargitsa gidan, daga karshe haka ya bar gidan a galabaice, kai tsaye gidan giya ya nufa ya sha ya yi tatul ya fito yana maye zai tsallaka titi kenan...........

★★★
Paris
Deejerh ta kammala Assignment dinta kuma ta shirya tsaf zata tafi stylish Wordplay fashion School.

Ma'am da kanta ta tashi ta mata Panisses snacks ta sa mata cikin karamin kularsu domin ta tafi dashi, ta zuba mata ruwa a gora, da Apple ganin cewa sai yamma suke tashi dole sai dai mutum yaje da abinci ko ya siya acen bare siya acen din ma sai masu kudi domin restaurant din school din babu kananun abinci na talakawa.
Karba tayi ta rataya jakar ta na yiwa Ma'am sannu da aiki.

Ma'am ta ce, "Adawo lafiya, Allah ya tsare hanya ya bada abun da aka je nema, kisa aranki Ubangiji na tare da ke a duk inda zaki kasance kuma kada ki manta kiyi addu'a kafin ki fita *bismillahi tawakkaltu alallahi wala haula wala*
*kuwatan illa billahi* sannan in kina tafiya har ki isa ki lizimci fadin Astagfirullah tare da karato *Rabbie Inniy Lima Anzalta ilayya min khairin* kinji fatan Alkairi Diyar kirki Deejerhtouna."

Suka rungume Juna kafin Deejerh ta yi mata Bye-bye.

Kai tsaye ta kama hanya tun kan gari ya waye kasancewar tafiyar kafa zata yi kafin ta fita daga kauyen ta hau Bus kuma ita kadai ne, Ammar na da aiki agun papi.

Suna zuwa Kuwa kafin kowa ya shiga lecture room sai ya yi submitting assignment.
Hakan yasa ita ma tana zuwa tayi submitting kafin ta shiga.

Yau ma dai kam Esme bata fasa yi mata kallon banzan ba, harda sa abun raba masu zama yadda jikin wani ba zai taba na wani ba, kuma duk bayan mintuna ta dauko turare ta fesa tana kara goge hanci.


2:30 suke fita Break kowa ya tafi Restaurant ita kam Deejerh ta zauna cikin class din ta bude jakarta ta fara cin abinci.

Sautin dariyar da taji yasa ta daga kanta,wasu mata da maza ne tsaye suna nunata suna dariya.
Ta kallesu maimakon taji Haushi kawai ita ma sai ta bi su da murmushiin da ita kanta bata san dalilin fitar sa ba.
Gabadaya sai suka yi dif suna kallon juna yadda ta maida su sune abun Dariyar hakan yasa Dukansu a sulale suka watse.

Ita kam ta gyara zama ta ci abincinta ta koshi ta kora da ruwa sannan ta tashi ta shiga school toilet din tayi alwala ta dawo class din ta keɓe gefe guda fara sallah.

Ta fara kenan suka fara dawowa daga restaurant mita suka fara yi suna yi mata masifa kan mene ne haka take masu cikin Class.
Deejerh taki katse sallarta duk da masifar da suke har suna janye mata dankwalin da ta shimfida wajen.
Suna cirewa Mr Laurent na shiga ya ce, "Wait... Me kuke yi haka?"

Wani Ne cikinsu ya ce , "Sir ka ga abun da wannan yarinyar take mana a class ai nan ba gurin bauta bane,in bauta takeso sai taje can gun bautarsu tayi mana."

Laurent ya ce, "No. Ku barta ta gama ai bata san ba ayi anan ba ko? Kowa yaje ya zauna."
Ba don sun so ba, suka tafi suna mita.
Deejerh ta idar ta shafa addu'a Mr Laurent ya kalleta ya ce, "Deejerh right?"
Ta girgiza masa kai.
Ya ce, "Yawwa ba a Prayer anan kinji, in zakiyi daga yau ki na zuwa office dina kinji ko?"
Ta ce, "Tom In sha Allah, Thank you sir."

Mr Laurent mutum ne mai saukin kai da son Mutane duk da kasancewar sa Christian baya damuwa da addinin kowa kuma bai so yaga an tauyewa wani hakki sam yana da saukin kai.

Assignment dinsu ya fara dubawa.

Duk a ciki na Asme ya fi na kowa tsaruwa da fita tamkar ayi magana ya fito, Laurent ya kirata gaban Class.
Da rawar jiki ta fito tana wani murmushi.
Ya ce, "kun ga Asme na ta duk yafi fita kuma yafi tsaruwa har ma yafi na jiya da aka yi ,ban ma yi tsammanin samun kwatankwacin wannan ba amman kun bani Mamaki And yanzu zamuyi amfani da lokacin mu ne gabadaya duka kowa ya kara yi yanzu anan ina so in fidda difference ya kasance ana yanzu kowa ya yi fiye da na baya, And wanda akayi yanzu anan da shi zamuyi amfani shine za a fitar da last result kuma duk wanda yafi fita school campany zata buga kuma a rabawa kowa."

Esme na jin haka cikinta ya duri ruwa , domin ba ita tayi ba, biyan kudi ta yi ta bada aka yi mata,ita ko kwantanta yi ma batai ba , domin ta san ba iyawa zata yi ba.

Take yanayinta ya canja murya na rawa ta ce, "Sir me yasa baza ayi amfani da wannan ba? Na ga duk munyi kokari ai kuma kaima ka fada."

Mr Laurent ya ce, "E amman yanzu wanda zakuyi dole zai bambanta da wanda kuka fara, musamman daga gareki ina bukatar ganin canji na daban kuma."

Ajiyar zuciya ta yi kawai tana zare idanu.

"Oyaaa get ready zaku iya using School materials for Now, Let's Go, ka da a bata lokaci you have 30mins Only Lokaci na yi za a datse."

Nan students suka birkice a ka shiga kowa na ta kai ta kai.

Esme kuwa wani zazzabi ne ya lullubeta nan take, ta ma rasa wa zata fara tinkara ba kowa take kulawa ba,bare ta nemi taimakon wasu ,ita masu kudin ma ta raina bare tallakawa.

Zura masu idanu tayi ganin kowa nata abun arziki babu ita Mr Laurent ya ce, "Esme ba time fa kiyi sauri ki fara."
Ya fada yana tafiya yana zaga class din.
Jiki a mace ta fara nata dake kowa an aje masa kayan design dinsa gabansa.
Deejerh kuwq tuni tayi nisa.
Kallon agogo tayi ta kalli Deejerh har ta kusa gamawa kuma sauran 5mins lokaci ya cika, gashi ita ta gagara tsinana komai.
Ta juya ta ga babu mai kallonta ,ta durkusa kasa ta dauko ruwan kala baki, tana dagowa ta bigewa Deejerh pencil dinta, ta durkusa zata dauko kenan, ta zuba mata bakin colour din daidai kan drawing din ya fara caɓewa.
Tayi saurin kau da kai kamar ba ita ba.
Deejerh na dagowa ta......

😻🤍 *Till Monday In Sha Allah, kun san ba update a weekend,And Please Need Ur Prayers As Usual 🙏 Please..........Luvs U OLL.*

08103080717

[1/8, 3:39 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-31

Da sauri Deejerh ta tare sannan ta dauki brush din shafa Colours ta tsame shi, sannan ta bi gabadaya jikin wandon da kalan, ganin ya yi duhu sosai zai iya boye adon,ta dauki farin Colour ta bi ta daura akai a hankali ta dunga shafawa har ya koma Ash, hakan ba karamin karawa wandon kyau ya yi ba,maimakon ɓatawa,duk da cewa sa colour wa Wandon baya cikin abun da aka sa su yi ko ince ake da bukata, amman ita ganin zai iya bata bata duka design din gyarawan ne kawai mafita."

Tunda Esme ta bata mata juyawa tayi,cikin nishadi ta ci gaba da jagwalgwala nata tana sakin murmushi duk da tasan cewa ana gani za a iya fahimtar cewa nata wancen ba ita tayi ba,amman a yanzu ita babban farinciki bai zarce ace Deejerh ma ta fadi ba kuma an disgata, ta tsani talakawa sosai amman tsanar da tayiwa Deejerh ya wuce misali ba tare da sanin dalili ba kawai bata sonta tun ganin farko ta ji ta tsaneta.

Ji tayi kawai Mr Jacques na fadin Pen Off.

Dukanninsu kowa ya tsaya, ita ma ta tsaya kallon ba tare da ta juya ga Deejerh ba.

Da ga bayansu ya fara karba yana dubawa tare da fadin, "Weldone ,ina shan ruwan mamaki dangane da ku,sai kawai nake kara ji araina cewa akwai wani abu na musamman dangane da set dinku."
Ya ci gaba da karba yana yabo.
Yana zuwa kan Deejerh.
Wata kara da ya yi sai da dukansu class din suka zabura.
Esme kuwa kasa kunshe dariyar ta tayi ta baje baki tana yi.
Cike da mamaki sauran students din ke kallon Mr Jacques yadda ya sake baki yana duba design din Deejerhn.
Ita ma kanta ta razana gabanta na faduwa ta rike hannunta biyu gam tana dannawa tare da tsoron furucin da zai fito daga bakinsa.

"Such a Wonderful Design! Can't Believe this." Ya fada cike da mamaki yana kara kallon Deejerh.

Nan Esme ta hade rai da idanunta suka sauka kan Design din, da mamakinta gabadaya ya canja salo, ya fi wanda ma ta bada asalin designers suka mata ya ma taka za ace domin babu hadi.

Kasa hakuri Mr Laurent ya yi, da sauri ya nufi office din Mr Jacques ya nuna masa.
Shi ma Mr Jacques cike da mamaki ya ce, "Gaskiya da mamaki ace student ce tayi wannan aikin, kuma ma sabuwar students,kai ka sani ko a tarihin School dinnan ba a taba samun hakan ba, And wannan shine design mafi ban wahala ga students ma yawanci ai."

"Eheen Abun ya ban mamaki nima fa,kuma kasan wannan yarinyar da ka ce mun Dr Ali ya turota yar kauyensun nan? Ita ce fa tayi." Mr Laurent ya fada.

Murmushi nr ya kara bayyana a fuskar Mr Jacques ya ce, "Tabbas na gane, kuma kasan ni fa tun zuwan yarinyar yanayin shigarta ya birgeni, ta iya shiga mai kyau sosai gaskiya, ka ga ikon Allah kenan Yar kauye ta zo zata danne yan binni."

Tare suka koma Class din.
Mr Jacques ya kalli Deejerh ya ce, "Weldone Daughter, gaskiya zan nemi Dr Ali kodayake ba abun mamaki bane samun mutane kamarku tattare da shi,shi ma haka yake da abun mamaki, And wannan jeans din shi zai zama na farko wanda students tayi Kuma School Company zata buga ta fidda shi kyauta ga dalibai sannan abawa yan kasuwa su saida, sannan ina miki albishir da cewa kina da kyauta ta musamman."

Take a wajen Deejerh ta durkusa tayi sujada ta godewa Ubangiji tana sakin murmushi.
Dukan su suka zura mata idanu har ta tashi.
Kafin ta durkusa gabansu suma tana fadin, "Thank You,Thank you so much Sir, ban taba tunani ko zaton cewa zaiyi ba, domin ina cikin yi ma ya baci da kyar na samu na daidaita, na gode sosai Allah ya saka muku da Alkairi kuma ya biya muku bukatun ku na Alkairi duniya da lahira, na rasa fahimta cewa mafarki nake ko kuwa a zahiri ne, Alhmdu Lillah Allah na gode."

Mr Jacques ya yi Murmushi, "Always Welcome Deejerh."

Mr Laurent ne ya daga Design din Esme yana fadin, "ka ga kuma wani abun ma da ya ban mamaki, Assignment din da na bada nata yafi na kowa kyau,but unfortunately ji abun da tayi a class? Hakan ya sa na fara jin cewa ba ita tayi wancen ba."

Yana fara magana Esme tayi kasa da kai tana sunkuyarwa cikin jin kunya.

Mr Jacques ya ce, "Eheen Then u have to do something."

Mr Laurent ya ce, "aiko dai zai zama first test dinsu ne, so kowa zai girbe abun da ya shuka a result."

Yana fada ta gyatsina fuska tana guntun tsakin irin ko a jikintan nan.

Ranar da farinciki Sosai Deejerh ta koma gida cikin walwala.
Ta sanar Ma'am suka yi farinciki sosai ,Ammar na zuwa ma Ma'am ta fada masa ya taya Deejerh murna sosai yana tsokanarta.

Ita kam bata kulasa ba,tana idar da sallar isha MMA training dinta ta fara yi.
Ammar ya ce, "wai shi wannan training din mene ne amfanin shi? Kullum da dare ki damemu da yi."



Deejerh ta ce, "na jaruman gaske ne ba muna jarumai ba, da zaka taimaki kanka kana yi ma da ka huta ka rage rangwanta wallahi."

Ta fada tana juya jikinta.
Ammar ya tashi yana matsawa daf da ita, "haka kawai sai kace mara aikin yi, da ma ace yana da wani amfanine sai inyi,ni abu in ba na neman kudi ba, miye ya shafeni da yi."

Karaf ta damkesa ta buga da kasa.
Sai da ya saki kara.
Sannan ta kyalkyale da Dariyar mugunta shi kuma ya yi tsurun jin damkar da ta yi mai yana mamaki har ma ya kasa magana.
Dariya ta kara yi ta ce, "kana mamaki ko? Wannan duk aikin MMA ne."

Ammar ya tashi yana karkade jikinsa ya ce, "Ikon Allah wannan damkar da kika mun ai na zata hannun wani katon basamude na shiga, amman kuma bai da wani amfani sai na cin zali ko?."

Deejerh tayi tsaki kafin ta ce, "ance ma wannan din bai da amfani ne? Ko ance ma zanyi abun da bai da amfanine? MMA training ne na kare kai,yadda mutum zai iya kare kansa ga duk wanda ya nemi hanyar cutar da shi ta kowacce hanya."
Ammar na jin haka ya bude baki, "atakaice dai kice mun mutum zaiyi karfi yadda zai iya kare kansa in anzo cutar da shi,koda buga masa abune?"

Deejerh ta daga kai tana, "eheen sosai ma, kuma duk yadda mutum ya bi maka zaka iya kwatar kanka."

"Aiko dai daga yau zanna yi amman kinsan sai kin koyamun ai."
Ammar ya fada.
Tafiya tayi ta canja gu tana abunta ba tare da ta bashi amsa ba.
Ya bita yana, "Please kinji da gaske ina son koya."

Deejerh ta ce, "Alright amman wallahi ka sani inka tsayamun wasa shareka zanyi."

"Aa na yi alkawari zan koya da kyau."

Deejerh ta ce, "yana da matukar muhimmanci ga mace da namiji su san hanyar da zasu bi wajen kare kansu musamman yanzu da a kullum yanayin tsaron kasarmu kara lalacewa yake."

Ammar ya ce, "wannan gaskiya ne, don ko ni akwai wanda indai nayi karfi wallahi sai na taka ruwan cikinsa kawai dai don ba yadda zanyi ne nasan yafi ni,amman training dinnan na shiga jikina sai dai kuji labari na dagargazawa Wani hanjin ciki."

Duk yadda Deejerh taso da makewa sai da dariya ta subuce mata ta ce, "in baka dagargaza masa ba shi ya dagargaza maka,yanzu dai duk abun da nayi ka yi kuma ni ba ina yi don wasa bane ko don cutar da su,don kawai in kare kaina ne daga hadari."

Ammar ya tashi harda cire riga ana gyarawa.
Ya ce,

Please Login or Register in order to submit comment