Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kyauna,sirrin adona,kuma hasken shigata ta yau,na tabbata zata iya aikata mafiyin hakan ma ga wasu."
Murmushin dole Deejerh kawai take kakalowa domin ranar sam tun safe ta tashi cikin wani yanayi rayuwarta na gida kawai take dawo mata tana ganin abubuwan zuciyarta.
Tana tsaye kanta ya fara sarawa hankalinta na kokarin gushewa, sautin wata waka mai kama da wa'azine ya rike ta,tayi saurin jingina ta zauna a kujera ba tare da kowa ya ankare ba.
Wakar Danny gokey stay strong
Wacce yake fadin
"God you taught me trust you
Showed me how to believe
You're the author and the finisher of what you start in me.
So I'm not gonna doubt it
I'm gonna hold on to peace
'Cause if i have you nothing else i still have everything
'Cause if i never see the promise on this side of the grave
My hope might be shaken
But my faith will never break
Because I know the day is coming when you'll right all of the wrong
So I'll praise you in the waiting And the my faith will stay strong
I'll count it joy when i am tested
Cause you bring Beauty form my pain
It's never wasted
But if i never see the promise on the side of the grave
My hope might be shaken but my faith will never break
Because I know the day is coming when you you'll right all of the wrong.
So I'll praise you in the waiting and my faith will stay strong
Because i know my the day is coming when you'll right all the wrong
So I'll prise you in the waiting and my faith will stay strong
Will stay strong."

Ji take aranta tamkar ita ake furtawa kalaman hakan yasa ta ji wani sanyi na ratsa mata zuciya.
Maganar Ammar ne ya dawo da tunaninta wajen yana tsokanarta, "Mummuna ke baza ki ci abincin bane ko sai ya kare kizo neman nawa? Ba dai sammiki zan ba."

Deejerh ta galla masa harara kafin ta ce, "ni ko ana cin abincin wani ai ba zan ci na rago ba,ka sa nima na zama raguwa."

Ammar na sosa ƙyeya yana dariya ya ce, "To jarumar mata zan yi maganinki nima dai in kashe bakin nan."

Abinci taje ta diba ta ci abinta hankali kwance.
Sun ci,sun sha,ansha hira sosai kuma sun tattauna akan ci gaban kauyen da aka samu musamman Papi da ya jinjinawa Deejerh bisa kokarinta na samar da sauki wajen siyan gawayi a yi girki.
Abdu ya gagara rike hassadarsa sai da ya tashi shima ya yi nasa jawabin yana fadin gawayin Deejerh na dauke da wasu cutuka da in aka ci gaba da girki da shi zai iya kawo barazanar rai ga al'ummar cikin kauyen gabadaya.

Karaf Ammar ya ce, "aiko dai in har gawayinta zai iya kawo wata cuta da zata sa arasa rai to babu shakka kai ma asalin gawayin da kake kawowa zai iya, domin kuwa nata ma ya fi samun inganci yadda ake yinsa da kayan yin har busarwa."

Abdu na binsa da wani kallo ko a jikinsa har saida ya idda maganar sa.

Papi ma ya ce , "Da ace akwai abun cutarwa ko ni ba zan taba yin shiru ba,ina tunanin ma nine mutum na farko da ya fara amfani da gawayin kafin wasu a cikin nan kuma na yi bincike na tabbatar ba ya tattare da wata matsala kamar yadda Ammar ya fada ta wani bangaren ma ya fi naka inganci."

Cikin fushi Abdu ya ce, "Taya za ayi ace kayan da aka samo a shara ya fi asalin kaya kyau da inganci? Wannan dai kawai son zuciya ne da kyashin cewa ina kasuwanci ba a son ci gaba na,amman a zahirin gaskiya ai duk wata shara cuta ce."

Madam Nasy ce ta katse shi da fadin, "kai ko Abdu akwai rigima na lura saukin da muke samune baka so,kuma naga kai nakan ma ba daina siya akai ba, gabadaya gidan biredi ke siyewa kuma basu fasa ba,mu talakawan mu dara mu dan ji dadin rayuwa kake wa hassada? To ahir dinka kawai."

A fusace ya bar wajen taron ba tare da ya ce komai ba yana wuci.
Yana tafiya yana sakawa a zuciya, "Tabbas duk yadda za ayi sai nasan yadda na yi na tarwatsa rayuwar yarinyar nan a kauyen nan,kamar yadda take son dauke mun jin dadin rayuwa ita ma sai na dauke mata da ikon Allah."

Da ya tafi ba wanda ya kara tada maganar karasa shagalin su sukai cikin nutsuwa da kwanciyar hankali har a ka gama kowa ya watse.

Bayan sun tashi Deejerh ta sanar da Ma'am tana so ta dan shiga cikin gari ta siyo drawing book da colors dinta.

Ma'am ta ce sai dai Ammar ya rakata.
Ba don taso ba haka ta bi shi,shi kuwa yanata kurari da fadin, "ai zai kareta ,ma'am ma tasan shi jarumin namijine shiyasa take hadata da shi."

Haka suka je tare ta siyo duk abubuwan bukatar ta kafin suka koma kauyensu.

Suna komawa tayi wanka ta yi sallah dake dare ya riga ya yi kuma sun ci abinci agun taro tea kawai Ma'am ta dafa masu suka sha.

Deejerh ta shimfida taburma ta Zuba drawing materials dinta sannan ta zauna ta fara zanen.
Tana yi Ammar ya isheta da tambayoyi daga karshe da ta gaji ta masa wani kallo sai da jikinsa ya amsa ya yi shiru kawai yana binta da kallon.

Wata irin Baby Dress ta fara yin Designing ta na bin zuciyarta duk yadda ta tsara mata, tazo daidai gun wuyan kenan ta kame tamkar wacce aka zarewa rai,numfashinta ya tsaya cak......

*Ina sane da wa inda suka ki yi mun Comments jiya,ina sane, na ce ina sane da ku*

08103080717
[1/3, 12:35 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-28

Ammar ya kalleta ya ce , "ke kalau? Ma'am ko 'Yar taki tana da farfadiya ne ba mu sani ba? Ji yadda ta kame tana wani abu?" Ya karasa maganar cikin sigar tsokana yana kallon Ma'am.
Sai a lokacin ta lura ta tashi da sauri tana dafa kafadar Deejerh.
Idonta kan Drawing book din ta ci karo da tana karama koriya shar.

"Subhannallah." Ta fada sannan cikin sauri taje ta kade tanar ta yar.
Ta ja Deejerh jikinta tana shafa mata baya tare da karanta mata Adduo'i.

Cikin zakuwa Ammar ya ce, "Ma'am lafiya? Me ya faru ne? Na ga kamar da gaske ta fita a hayyacinta."

Ma'am ta ce, "Kasan babu abun da ta tsana kuma take tsoro sama da tana, akan tana wani lokacin har suma take,ban san dalili ba amma sam bata son abun ko abinci take ci indai zata gani shikenan ta koshi ta kuma fice a hayyacinta."

Ammar ya ce, "Ayyah Ikon Allah kenan kuma ranar maciji fa ta bige ko a jikinta amman wannan karamin abun ace yana firgitata , Kodayake ba abun mamaki bane kowa da yanayinsa."

Barci ne ya dauke Deejerh, Ma'am ta gyara mata kwanciya.
Ammar ya tashi ya tattara mata kayan aikin nata kafin shi ma ya tafi.

★★★
Mexico
Zayd tun yana neman Deejerh har ya gaji ya hakura a garin yawon nasa ya hadu da wata 'Yar duniyar da ta fi shi duniyanci sunanta Huda , Allah ya jarabceshi da masifar kaunarta wanda bai jin cewa zai iya rayuwa ba tare da ita ba,babban tashin hankalinsa bai zarce ace ya ga bacin ranta nan da nan zai fita a hayyacinsa.
Duk sanda zai fito mata da maganar aure ta kan nuna har yanzu bai mallaki arzikin da zai iya dauke bukatunta ba.
Domin Huda irin matan nan ce masu jini a jika da suka amsa sunan mata,baza asata sahun wasu mata masu kyau ba,amman indai sanin darajar kai da gyara ne aka zo gunta an gama domin mace ce yar kwalisa mai takun kasaita gami da jin izza, irin matan nan ne da Ubangiji ke arawa lokaci wajen juya duk wani namijin da ya fada hannunsu cikin sauki.
Bata jin tsoron kashe naira kamar yadda Naira bata mata wuyar samu ta san manya sosai kuma sannun cikin Mexico yadda ta kan iya cin karanta babu babbaka.
Hakan ke kara razana Zayd domin gani yake zata iya yi masa kafa ta tafi ta barshi, ya shiga rububin ci gaba da neman kudi ta inda yake hawa bata nan yake sauka ba duk dan ganin ya samu galaba akan ta amince ta aure shi.



★★Zaune take,ta yi tagumi gabadaya duk ta kara jemewa ta fice a hayyacinta.
Shigar Dadyn Deejerh gidan kenan ga dukkan alamu ya dawo daga office ne, shi ma duk yanayinsa ya canja ya rame sosai sai dai kasancewar sa na Da Namiji ya yi kokarin danne damuwarsa.
Har ya zauna kusa da ita bata ankare ba ta shiga duniyar tunani.
Sai da ya dafata kafin ta zabura hawaye masu zafi na zuba daga fuskarta.
Ya yi saurin share mata yana fadin, "Wannan kukan, wannan kuncin, wannan damuwar ba sune mafita garemu, kin daina walwala a rayuwarki,kin bar zuwa wajen aiki,kin daina shiga jama'a duk kin takura kanki kina tunanin hakan mafita ne wai? Aa fa,yanzu abu daya Deejerh ke bida wajenmu tana raye ko tana mace addua sannan kuma mu dukufa wajen neman gafarar Ubangiji domin kuwa duk abun da ya faru mune sila mune silar komai ,da hannunmu muka siya wukar yanka rayuwar 'Yar mu, zuciyar mu ta ingizamu wajen tarwatsa mata ginin da mu muka fara gina sa cikin tsari, ki daina kuka."
Nan ta kara fashewa da kuka tana rungume shi ta ce, "babu abun da ke bani takaice sai inna tuna lokacin da ta kawo mun karar Zayd na musa mata har ina dukanta, duk lokacin da tayi wani yunkurin nuna abun da yake mata ni nake hanawa har ta gaji ta daina, ta sha zuwa tana son fadamun magana in ki sauraren ta,dama ace yanzu tazo ta fadamun mana,dama ace yanzu zan iya magance mata damuwarta mana,dama ace yanzu ina da damar share hawayen da ke zuba a idanun 'Yata mana, dama ace yanzu zan ganta dana ajiye duk wani kwadayi da buri tare da son zuciya na ingata mata rayuwa mana, babban abun takaicin wai Dan Uwana,dan uwana na jini fa, Allah na tuba ka yafeni, Allah na tuba ka yafeni,ka tsaremun rayuwar 'Yata aduk inda zata kasance." Ta karasa maganar cikin kuka mai tsuma zuciya.

Dadyn Deejerh ya kara dagata yana nuna mata wayarsa ya ce, "Yawwa kin ga ma ko ga addu'ar iyaye ga yaransu na samo mana daga shafin Sheikh Ibrahim Daurawa bara in karanta kiji sai muna yiwa Daughter ko?"
Ya fada tana kallonsa ta girgiza masa kai kafin ya fara karantawa.

اللهم بارك لي في أولادي، و وفقهم لبطاعتك، وارزقني برهم.

Allahumma bărikli fii aulădi, wa waffiqhum bi ðă'atika, warzuqni birrahum.

اللهم يا معلم موس علمهم، و يا مفهم سليمان فهمهم، و يا مؤتل لقمان الحكمة آتهم الحكمة و فصل الخطاب.

Allahumma Ya Mu'allima Musa Allimhum, wa Ya mufahhima Sulaimana Fahhimhum, Wa Yamu'uta Lukmănal hikmata ătihimul hikmata wa fassalal khidăb.

اللهم علمهم ما جحلوا، وذكرهم ما نسوا، وفتح عليهم من بركات السماوات والأرض، إنك سميع مجيب.

Allahumma Allimhum măjahilu, Wa zakkirhum mănasuh, waftah alaihim min barakatis samawati wal ardi innaka sami'un mujib.

اللهم أسألك لهم التوفيق وقوة الحفظ وسرعة الفهم وصفاء الذهن.
Allahumma as'aluka lahum taofiqa wa quwatal hifz wasara'al fahmifahmi
اللهم اجعلهم هداة مهتدين.
Allahummaj alhum hudatan muhtadin.
اللهم حبب إليهم الإيمان وزينه في قلوبهم وكره إليهم الكفر والفسوق والعصيان واجعلهم من الراشدين.
Allahumma habbib ilaihimul imana wa zayyinhu fii qulubihim wa karrih ilaihimul kufra wal fusuqa wal isyan waj'alhum minarrashidin.

اللهم حسن أخلاقهم واملا قلوبهم نورا وحكمة.
Allahumma hassin akhlaqahum wamla'a qulubahum nuran wa hikmah

اللهم طهر قلوبهم من الرياء.
Allahumma dahhir qulubahum minarriya'i.

اللهم حصن فروجهم من الزنا واللواط والسحاق وكل الجرائم
Allahumma hassin furujahum minaz zina wal luwadi wassihaqi wakullil jară'im
اللهم اجعلهم حفظة لكتابك و سنة نبيك صلى الله عليه وسلم.
Allahumma aj'alhum hafazatan likitabika wa sunnata nabiyika (S.A.W).

اللهم ارزقهم القناعة والرضا.
Allahumma arzuquhumul qana'ata warridha.

اللهم ارزقهم حبك و حب نبيك صلى الله عليه وسلم وحب كل من يحبك وحب كل عمل يقربهم إلى حبك.
Allahummar zuquhum hubbaka wa hubba nabiyika wa hubba kulli man yuhibbuka wa hubba kulli amalin yuqarribhum ilă hubbik.

اللهم افتح عليهم أبواب رزقك الحلال من فضلك واكفهم حلالك عن حرامك واغنهم بفضلك عمن سواك.
Allahummaf taha alaihim abwaba rizqika alhalălika min fadlika wakfihim halalika an halalika wagnihim bi fadlika amman siwak.

اللهم جنبهم رفقاء السوء والفواحش والمحن.
Allahumma jannibhum rafaqă'as Suu walfawăhisha wal mihan

اللهم عافهم في أبدانهم وأسماعهم وأبصارهم وأنفسهم وجوارحهم ياأرحم الراحمين.
Allahumma aafihim fî abdănihim, wa'asmă'ihimwa'asmă'ihim wajawărihihim ya arhamurrahimin.

Kin ga ance inda hali sallar dare na karfe ukun nan iyaye suna karantawa yaransu ita, kuma ni ina ji a jikina Daughter na cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali da ikon Allah inaga kuma mun kara tayata da addua kin san adduar iyaye ga yaransu tamkar yankan wuka ce."

Sai a lokacin Momyn Deejerh ta yi Murmushii.
Ya ce, "Yawwa ko ke fa, ga wata Adduar ma neman gafarar Ubangiji, (Allahumma anta rabbi la ilaha illa anta, khalaqtani wa ana abduka, wa ana ala ahdika wa wa'dika mastata'tu.) Kin ga daga yau ba barci ko? Zamuna tashi muna yi ma Daughter addu'a kuma muna neman gafarar Ubangijinmu."

Kara girgiza masa kai ta yi, tana sakin wani murmushin shi ma ya maida mata da shi yana kissing dinta.

★★
Paris
Tunda Deejerh ta fara barci bata farka ba har saida asuba tayi Ma'am ta tada ta yin sallah.

Bayan ta idar kuwa kamar yadda ta saba bata koma ba ta fara aikin gyara masu gida,sai da ta gyara tas ta daura masu abun karyawa kafin ta dauki drawing materials dinta ta ci gaba da Designing din da ta fara.

Ta gama kenan sai ga Papi yazo gun Ma'am suna gaisawa idanunsa suka sauka kan book din.
Karasawa ya yi,ya daga yana fadin, "Woo ke kika yi kuma Daughter?"

Kafin Deejerh tai magana Ma'am ta ce, "Ita ta yi Dr Ali ta iya zanen kaya fa sosai yanzu ka ga wannan kamar a mata magana ta fito asa ba karamin kyau ta yi ba."

Yana kara bi da kallo ya zauna ya ce, "aiko wannan ke dama fashion School kika shiga yadda kike Designing dinnan tun yanzu nasan zasu ji dadinki matuka ko ba kya so?"

Deejerh ta ce, "Ina so." A gajarce.

"Akwai wata sabuwar Fashion School a cikin gari da wani yarona cikin founders din zan yi masa magana ko muje tare ma In sha Allah acen zaki kara kwarewa kuma baiwarki ta miki aiki, kamar sunan school dinma
_Stylish Wordplay fashion School_
In sha Allah yanzu ina komawa gida ma zan kirashi."

Har cikin ranta Deejerh ta ji dadi sosai ta ce, "Na gode sosai Papi Allah ya saka da Alkairi."
Ma'am ma ta yi masa Godiya sosai kafin suka gama maganar su ya tafi.

Yana tafiya kuwa ya kira ya bincika kan batun Fashion School da duk yadda za ayi.

Ranar suna da Therapy class da yamma hakan yasa bayan ta kammala komai ta nufi can.

Har ma lokaci ya kure Papi ya fara yi masu jawabi ta nemi waje ta zauna.
Sai dai abun da ya bata mamaki aranar shine ta lura Ammar na cikin damuwa sosai domin ko da ta shiga class din ya mata Murmushi sau daya shikenan bai kara kulata ba,ga dukkan alamu yana cikin damuwa wasu irin tunani yake.

Deejerh na hankalce da shi haka aka tashi, ya mata sallama ya tafi ba dai hargagi kamar yadda ya saba, hakan yasa ta bi bayansa.
Yana cikin tafiya yaji alamar ana binsa ya tsaya,juyawan da zaiyi sai suka hada ido, a tare suka sakewa juna murmushi.
Ya tsaya yana, "ina zaki kuma? Baki tafi ba?"

Deejerh ta ce, "kai na biyo, zamu iya zama?" Ta yi maganar tana nuna masa kan wani iccen bishiya.
Girgiza mata kai ya yi suka zauna yana daukan wani ganye yana wasa da shi a hannunshi.

Deejerh ta ce, "mene ne yake damunka yau? Na ganka a takure kamar kana da wata damuwa?"

Wani takaitaccen Murmushi ya yi kafin ya ce, "Aa ba komai kawai yanayin ne dai."

Deejerh ta ce, "Umm ba za dai ka Fadamun ba, amman dole akwai abun da ke damunka,ai ba haka kake ba,kuma ba haka ka saba ba, kila ba za ka iya fadamun damuwarka ba,amman zan iya shiga rayuwarka in baka Shawara?"

Daga kai ya yi suka hada idanu kusan second uku yana kura mata ido sai da ta sunkuyar da kai kafin ya ce, "e mai zai hana, ke fa kawatace."

Deejerh ta ce, "Tom Kasan Ayar karshe na suratul bakara? Da kuma Surar farko na Al-Qur'ani Fatiha?"

Da sauri ya amsa , "E mana sosai ma, Fatiha da Amanar Rasulu ba."

Deejerh ta gyara zama.
"Su din nake nufi , ina so ka rike su,ko ince ka lizimci yin su tamkar babu gobe, ace a kullum zaka karanta fatiha da Amanar Rasulu ka roƙi Ubangiji damuwarka, ka kai kukanka gareshi ina mai tabbatar maka dukkanin duhun dake gabanka zai zama haske, duk dacin da ke ranka zai zama zaki, inda hali ace kullum ka karanta da safe ko da dare hakan ma ba karamar kariya bane ga jikinka sosai."

Ammar ya ce, "to amman ai daman ni na saba karanta fatiha."
Deejerh ta ce, "eheen kana karantawa amman baka san alfanunta da girmanta ba, kana daukarta a kawai abu da zaka karanta fisha, ka kudirta aranta aduk sanda zaka karanta fatiha da Amanar Rasulu zaka roki Ubangiji zai biya ma bukatunka muddin kasa aranka hakan babu makawa zai tabbata, wasu Adduo'in muna daukansu kananu da jin cewa mun iya ai ba komai bane,amman bamu san tasiri da girman su ba. Duk wata damuwa,duk wani tsanani duk wani ciwo a yanzu ka dogara da karanta wa innan ayoyin biyu na tabbatar da cewa watarana zaka ban labari, zaka karanta su kafin ka tashi agun in Ubangiji yaso kudirarsa take burinka da ka roka zasu cika har ma da wa inda baka hasashe."

Ammar ya yi shiru kafin ya ce, "kuma hakane fa na Gode sosai kuma In sha Allah daga yau zan lizimci karanta su kamar yadda kika bani shawara hirar mu ma kadai tasani na ji sanyi araina bare kuma nayi abun da kika ce, na gode yar mummuna mai tunanin manya."

Deejerh ta galla masa harara tana fadin, "Ko a duhu ai ansan kai ne mummuna." Ta karasa maganar tana tafiya.
Tashi ya yi,ya bita yana tsokanarta yana dariya....


08103080717

*°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-29

★★Papi ya kammala yiwa Deejerh registration din stylish Wordplay fashion School saura materials din da zatana amfani da su ne kawai bai siya ba, duk da cewa Registration dinma basu yi zaton zai biya ba sai kwatsam kawai yazo mata da komai cikakke.
Ma'am ta yi murna sosai kuma sun gode masa matuka tare da nuna Farincikin su ga hakan.
Ya cewa Deejerh yanzu ta maida hankali ta tabbatar ta tara kudin da zata siya Materials din domin in bata mallaka ba baza a taba barin ta ta ci gaba da zama a ajin ba da zaran ta yi sati biyu in mutum bai mallaka ba suke kora don karatun baya taba tafiya ba tare da kayan ba, atakaice ma kayan sune karatun.


Aranar kuwa Ma'am ta fita ta ga wasu kayan gwanjo masu kyau riga ce har gwiwa da karamin wando tare da gyale,dukka farare ne kal sai dan adon jiki brown da golden amman irin sun fara farfashewan nan kamar kwashen kaya, canjin Hannunta kenan amman ta zaɓa siyawa Deejerh domin ya kasance kaya na farko da ta siya mata kuma zata fara Zuwa da shi School.

Aiko tana kai mata,ta karba da murna cike da nuna jin dadi tana yi mata godiya,take ta wanke su ta goge, ta gyara duk guraren da suka yage ta dinke ta zare ya zama ado.

★★Yau ne ranar ta ta farko ga fara zuwa Stylish Wordplay fashion kafin komai da sassafe sai da ta tara yara ta yi masu sadakan sweet, kafin ta fara aiki cikin nutsuwa da zakuwa tana jin farinciki aranta wanda ko daga fuska ma kallo daya za a mata a fahimci halin da take ciki na tsantsan jin dadi.

Sai da ta kammala komai kafin ta fito cikin shigar ta, kayan ba karamin kyau sukai mata ba,tamkar a jikinta aka tsara su, kyan su da nata sai ya haɗe waje guda ya bada wani salo.

Ta yi wa Ma'am sallama, ta fita fuskarta dauke da murmushi tana tafiya cikin nutsuwa zata je gun Ammar su tafi dake papi ya ce Ammar ne zai kaita.
Tana cikin tafiya kamar daga sama taji an zubo mata abu ta baya, daga kan da zata yi gabadaya kasan wandonta ya baci da ruwan laka har ya fara taba rigar ma.
Abdu tsaye da bikiti yana yi mata dariya cikin issa da izza.

Ji tayi zuciyarta ta fara daukan zafi,kamar zata durkusa sai kuma ta tashi ta karasa gabansa yana ci gaba da dariya tare da fadin, "Haba mana karkiyi kuka mai gawayi ai ba gawayi aka rasa masu siya ba ko? Ki je ki canja wasu kayan kar ki makara don wa innan kam sun gama." Ya fada yana taba mata kasan riga.
A fusace tayi wani juyi ta sake masa mari a fuska, ta kara daga hannu ta sake masa biyu zafafa a jere.
Ya ma gagara motsawa kawai yana kallonta hannunsa dauke kan kumatu.
Daidai lokacin Ammar ya fito kenan sai da gabansa ya yi mummunan faduwa.
Zuciyar ta a tsorace take tana bugu amman a zahirance ta dage wajen bayyanar da jarumtarta.

Da sauri Ammar yaje yana janyeta gefe, "ke baki da hankali ne? Lafiyar ki? Me yasa zaki maresa? ke baki san halin shi ba ko?"

Deejerh ba ta ce masa komai ba, Abdu ya kalleta ya yi kwafa ya tafi.
Yana tafiya ta kalli Ammar ta ce, "mu koma gidan Ma'am in gyara kayana.

Ammar ya kalleta sama da kasa kamar dariya zata subuce masa sai kuma ya make ya ce, "gyara? Mu je, wannan kayan ai saidai a cire sa kuma ya gama aiki."

Bata ce masa komai ba har suka koma,suna shiga Ma'am ta tashi da sauri cike da mamaki tana tambayar me ya faru.
Atakaice Deejerh ta ce, "Abdu ne ya bata mun kaya."

Daga nan bata ce komai ba ta shige.
Sai da Ammar ya ga ta shige kafin ya bawa Ma'am labarin abun da ya faru yana.

Har lokacin mamakinta yake ta yadda akai ta mari Abdu ba tare da nuna shakka ba kuma ta ci gaba da harkar da ke gabanta.

Tana shiga ta cire wandon ta dauki almakashi ta yanke gabadaya wajen da ya bata mata, sannan ta kara bi ta fidda kasan ya zama kamar star kananu ta dauki golden din zare tasa a jikin allura ta dunga bin bakin stars tana dinkewa da zaren kan kace miye ta kammala wando ya fita da wani style din.
Rigar ma dake iya bayane ya taba kuma kadan nan ma yankewq ta yi ta maida stars din ta bi.


Da sauri sauri ta yi cikin minti 20 ta kammala, tana fita Ammar da Ma'am suka kura mata idanu cike da zillimun ina ta samo wasu kayan.

"Wa innan kayan fa? Daman kina da wasu ne?"

Cikin Murmushi Deejerh ta ce, "Sune fa na gyara." Ta fada tana juyawa.
Sannan ta kara fadin, "Ammar mu tafi ka ji mun makara fa."

Kafin ma'am tayi magana ta mata kiss ta na kara rataya jaka ta fice, Ammar ya bita shi ma da gudu suka tafi.

Suna tafiya yana mata surutan da ya saba.
"Amman ko kinga yadda kika yi kyau? Har ma fa kin fi dazun nan wallahi, da Abdu zai ganki yanzu ina ga suma zaiyi,ni na fara ma tunanin fa sonki yake ysn kish....

Idanunta da ta sauke kan nashi yasa ya yi saurin dakatar da karasa maganar ba don ya so ba, ya wayance da in-ina yana, "Umm ba wani kyau ma kika yi ba ai kawai kayan ne ya sa miki kyau,kayan ne masu kyau ba ke din ba."

Har suka isa shi kadai yake kidansa yake rawansa.

Tun daga Gate din Stylish Wordplay fashion School za ka fara hango yan kwalisa maza da mata , isassu kuma yaran isassu masu jini a jika, daga zafafan motoci sai irin mashin dinnan kananu irin na matan da suka amsa sunansu mata.
Kallo Daya Deejerh ta yiwa Get din da mutanen da ke shigar sa gabanta ya yi wani mummunan faduwa.

Ammar ya fahimci hakan ya kalleta kafin ya ce, "Kisa aranki zaki iya abun da kikazo yi,ba ruwanki da mutanen wajen, ba ruwanki da yanayinsu,ba ruwanki da sun fiki gata ko wani abu dukkanin mu daidai muke wajen Ubangiji, na san ba za ki karaya ba,ke jaruma ce,

Please Login or Register in order to submit comment