Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna son yin girki sosai.
Khalil ya ce, "amman dai ban da mu ko? Don ni kam ma ina da aiki a system akwai abun da zanje in yi." Ya fada yana kokarin shigewa."
Janyo hannunsa Zahra ta yi ta rike ta ce, "No yallabai sai fa anje da kai kuma aikin nan kowa sai ya yi shi."

Haka ta sa duka suka yi Resturent aka shige kitchen,rigar girki ta fara mikawa kowa cikinsu yasa kafin ta dauko wata takarda ta yi rubutu ta rufe.
Ta ajiye ta ce, "gashi nan duk wa inda suka dauki abu iri daya to tare za su yi abun."

Kowa ya dauka ya bude na shi, Deejerh na budewa ta ce, " Onion Omelette."

Zahra ta kalli Xavier ta ce, "na ka fa Oga."
Shi ma yana budewa aka ga Onion Omelette.
Wani irin takaici ne ya sarƙafi Deejerh ita da so son ganinsa bata yi taya zai zama ace tare zasuyi aiki.
Ba yadda ta iya haka yaje suka fara.

Abubuwan da suka fara bukata
Egg
Onion
Carror
Garlic chives
Salt
Ground pepper

Fara yanka su Onion din suka yi, Deejerh na cikin yankawa ta yanke hannunta.
Da sauri Xavier ya rike mata hannu tana ihu ya janyo tissue yana goge mata jinin da ya fara yi.
Fisge hannunta tayi tana tsaki.

Zahra da Khalil na ganinsu suka yi kamar basu gani ba suna dariya kasa kasa.

Ya ce, "ki bari in karasa yanka sauran tunda kinji ciwo."
Ta galla masa harara tana, "zan iya abuna."
Ta fada tana daure yatsan ta ci gaba da aikinta.
Haka suka ci gaba suks gama yanka abubuwan duka.
Sannan Deejerh ta dauko kwai ta zuba akai ta hada su waje guda.

Xavier kuma ya hada flour da ruwa ya yi mixing dinta sannan ya kai Deejerh ta zuba akan hadin kwan.

Zuwa ya yi ya zuba butter akan pan ya daura a huta, bayan Deejerh ta gama kara mixing man na zafi ta fara zubawa.
Tare suka soya har suka gama.

Sun gama duka an hada abincin akan dining suka fara ci.
Anuska ta ce, "wooo Ban taba cin Onion Omelette irin wannan ba, ya yi dadi sosai."

"Sosai nima wallahi kamar kullum a dunga yi." Anitha ta fada.

Noor ya ce, "Uncle,Aunty ku koyawa Momy daga yau ta dunga yi mana."
. dariya suka yi duka.

Tun daga ranar Deejerh wasan buya suke da Xavier bata son su hadu ko ganin lokacin dawowarsa ya yi tayi ma tashi take ta gudu ta bar inda take duk don kar su hadu, abun ya fara damunshi sosai hakan yasa ya samu Khalil.
"Na kasa jurewa duk da cewa na san hakan zai faru daman amman don Allah ka mun taimako ka gwada mata magana na tabbatar da cewa yadda kake da mahimmanci a rayuwarta ba za ta ki bani dama ba sanadin ka."
Dariya Khalil ya yi,ya ce, "kai da kace zaka iya kuma?"l

Xavier ya ce, "ka bar wasa Allah ina matukar son Khadijah har cikin raina."

Khalil ya ce , "Ok zan gwada mu ga."

Sai da Khalil ya bari kowa ya yi barci gidan ya yi shiru kafin ya je dakin Deejerh..
Idonta biyu kuwa ta idar da sallah.
Da sallama ya shiga ya zauna a gefe.
Deejerh ta ce, "Allah sa ba laifi na yi ba."
Murmushi Khalil ya yi ya ce , "ku san laifin ne ai domin ina dab da hukunta ki tunda kike son kashe mun aboki da ciwon soyayyarki."

Dariya Deejerh ta yi ta ce, "ni na isa aa."

Khalil ya ce, "kin san dai ni ba zan miki dole ba kuma ba zan so miki abun da zai cutar dake ba, ina ganin kamar lokaci ya yi da zaki ba shi dama in da kwai alkairi tsakanin ku Allah ya tabbatar tunda dai ba rayuwa za ki ci gaba da yi haka ba, akwai bukatar kiyi aure ke ma ki gina rayuwar ki tunanin wani abu arai tuna baya ko hasashe baya da amfani a rayuwarmu ki kasance mai tunanin gobenki kawai ."

Deejerh ta ce, "hakan In sha Allah za a gyara."
Khalil ya ce, "yawwa tom sai da safe nima zan je in kwanta."

Washegari da safe Deejerh bata rufe kanta yadda ta saba ba,ta fito sunyi breakfast duka tare kuma Xavier ya ji dadin hakan sosai, ranar ba aiki duk suna gida yamma na yi Zahra da Khalil suka hada yaran duka suka ce sun tafi shopping.
Daga Xavier sai Deejerh zaune a falon.

Kamar ko jira yake su tafi,suna tafiya ya gyara zama tare da matsawa ya ce , "amman dai kin azabtar dani da yawa rashin ganinki babban cutarwa ne gareni."

Kau da kai Deejerh ta yi kawai bata ce komai ba.

Dukusawa a gabanta Xavier ya yi ya ce , "If You're gonna allow me to love You,
There's a couple things you need to know about me,
One I'm Never gonna love you perfectly
But I am Gonna Love you Intentionaly
I'm Gonna frustrate you
And im gonna irritated you
Just by Being me
But I'm Gonna Love You Consistently
Some Days u gonna wanna run away but i promise that on those days go na do my best to give you a thousand reasons to stay.
I just want you by my side
And I'm Sorry for that love, there's no place to hide, YES I'm alot but i will never be somebody that I'm not.
I will not allow us to go to bed angry at Night And i will be the idiot to tell you I LOVE YOU in the middle of our biggest Flight.
You see all that I want is for you and me Intentionnaly to be we."

Har ya gama maganar ko dagowa ta kalleshi baiyi ba bare ta yi yunkurin ba shi amsa.
Wani murmushin takaici ya yi kafin ya ci gaba da magana, "Ko don ina da Ɗa na shine ba za ki so ni ba? Hmm "
Tashi tsaye ya yi kafin ya ce, "
kina tunanin zan kara miki nauyi akan wanda kike da shi? taki matsalar kuma da tashi? to amman ki sani Asher mahaifiyarsa ce ta mutu ta barshi domin kuwa na tabbata da ace tana raye ba zata taba barinsa ko tunanin guje masa ba bare wahalarsa kuma a kullum ina jin cewa babu wata kyauta da Ubangiji ya mun sama da Asher na barki lafiya."
Sai kawai ya tashi ya fice daga dakin.

Bai dawo gidan ba sai can cikin dare tana tsaye a jikin glass din windown dakinta taga shigewarsa.
Yanayinsa babu walwala sam.
Da ta ga ya shiga daki rufe windown ta yi ta hau gadonta ta kwanta.
Ta rufe ido amman barci ya gagara daukanta ko ta rufe maganganun da ya fada mata ne kawai suke dawowa kunnenta.
Kamar an zabureta ta tashi ta dauki wayarta ta fara rubuta mai sako.

Ya fito daga wanka kenan ya ji karar shigan sakon tsaki ya yi yana kallon wayar kawai ya hango sunan Deejerh.
Bai ci gaba da goge jikin ba ya yarda towel din ya dauki wayar da sauri.

"Look I'm Sorry to tell this,but Somebody lie to You, because the truth is BAGGAGE Does not wear a diapers just because you Are a single Dad Does not mean that you have BAGGAGE no kid Are not BAGGAGE their blessings And can i tell you Secret about the person that meant for you?
The person that meant for you will be favored by this world.
Because you see every Night we go on to our knees and pray for the one person to spend the rest of our lives with,And if I'm Favored this world will send me more than one you see i get to love You more than once.
BAGGAGE Does not wear diapers, blessings Do."

Yana gama karantawa wani irin Murmushi ya fara bai san lokacin da ya yi ƙara ba can kuma sai ya rufe bakinsa da hannu a hankali yana fadin, "Alhmdu Lillah, Alhmdu lillah, Alhmdu Lillah."
[6/10, 7:07 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-70 END

Ranar kwanan farincikin Xavier ya yi, bayan sun dawo daga sallar asuba da Khalil Xavier ya ce, "Oga yau fa barci ba naka bane a gidan nan mune zamu yi komai infact ina so in shiga kitchen da kaina yau inyi abu na musamman ga wacce take ta musamman."

Sake baki Khalil yana kallon Xavier yana, "kamar ya?"

Xavier ya ce, "ko ka zuba ido ka yi kallo ko kuma kai ma yau ka zo in koya ma yadda ake Love ka yi Surprising Madam."

Dariya Khalil ya fara, "ah lallai wai ke ne har zaka koyawa wasu soyayya? Gaskiya na yarda soyayyar da kake yiwa Khadijah ba ta wasa ba ce, Shikenan mu je."

Tare suka shiga kitchen din suka fara hada breakfast.
Bayan sun gama Xavier ya ce, "ba fa a dinning za a jera ba, yau ranar ta musamman ce zamuje ne akaiwa kowa dakinta kawai ta tashi tayi wanka tayi brush ta ci."

Khalil na dariya ya ce, "an gama sabon ango zance ne ko sabon masoyi, yanzu muma muje muyi wanka mu fesa turare sai muje musu muna kamshi ka ga zasu fi jin dadi ai."

Xavier ya ce, "yes dadina da kai akwai tunani."
Tun kan khalil ya fita da sauri Xavier ya fita ya je ya shiga wanka cike da zumudi.

Bayan sunyi wanka shirya kayan abincin suka yi duka kowa ya dauki na shi.

Deejerh na barci kamar a mafarki taji ana buga mata kofa, gyara kwanciyarta tayi ta ci gaba da yi.
Sai da ya kara nocking kafin ta tashi.
Tana bude kofar ta ci karo da Xavier tsaye da kayan breakfast.
Murya kasa ya ce, "Good Morning." Yana murmushi.

Ita ma amsa mai tayi da, "Morning." Tana maida masa martanin murmushin.
Ta bude masa kofar.
Aje mata abincin ya yi kan table din dake gefen gado ya ce, "wannan breakfast dinki ne ,yau da girkina nake so ki fara."
Deejerh ta ce, "Thank you."
Xavier ya ce, "ba thank you nake son ji ba."

Deejerh ta ce, "to me kake son ji?"

"Na farko ki ce na yi kyau na biyu kuma ki furta mun kalmar da tafi komai dadin ji da sauraro daga bakinki ma'ana kina sona."

Wata irin kunya ce ta kama Deejerh ta ce, "To ka yi kyau, amman waccer kalmar ba yanzu ba."
Xavier ya zauna gefen gadon ya ce, "indai baki fada ba kuwa ba zan taba barin dakin nan ba kuma ba zan bari ki fita ba,har sai kin fada."

Deejerh ta ce, "to bara inyi wanka inna gama cin breakfast din zan fada kaje na yi alƙawari."

Xavier ya ce , "in fa kinga na fita to kin fada ne."

Deejerh ta rasa yadda zata yi da shi.
Ta ce , "to mu je ka juya zaka tafi sai in fada maka karka kalleni."

Tashi ya yi ta masa wayo har ya fita a dakin, zata rufe kofar kenan ya tare.
Zare masa idanunta tayi cikin sassanyar muryarta ta ce, "I Love You."
Tana fada ta tura kofar da sauri ta shige toilet.

Shi kuwa wani farinciki ne kara birkita zuciyarsa yana tsaye shi kadai sai sakin murmushi.
Khalil ne yazo ya mai dundu a baya yana, "sai wani murmushi kake kamar sabon ango."

Xavier ya Sosa ƙeyarsa kafin ya ce, "ai kusan hakan ne."
Khalil na dariya ya ce, "kai tunaninka ya yi kyau fa Madam ta ji dadi sosai wallahi ta ce saboda wannan Surprise din har tukwici zata bani."

Xavier ya ce, "You see ba, ai ni dln bana wasa bane."

Khalil ya ce, "Ah yanzu kam na yarda tunda ka yi wuf da zuciyar Vixeen, mu je muma muyi breakfast din."

Suna cikin yin breakfast Xavier ya ce, "Yawwa na ji baka mun maganar canja suna ba na ga yawanci mutane kan canja suna in suka Muslunta."

Khalil ya ce, "eh amman bawai hakan ya wajaba bane ra ayine in kaso zaka iya canjawa in kuma kana so zaka iya ci gaba da amfani da sunanka and agun ma da ake iya samun matsala in mutum zai je ummarah ne in ba cikakken sunan Muslims ba yana iya effecting sai in har da sa hannun imam din da ka karbi shahada wajen shi,to kai ka ga ba ka da wannan Matsalar."

Xavier ya ce, "yes aiko na ji dadi ka ga abun da yake kara samun kaunar addinin musulunci kenan babu tsauri babu takura."

Fitowar Deejerh ds Zahra ne ya katse su.
Zahra ta ce, "lallai yau mun ci dadi a gidan nan,ni anya ma ba haka za a ci gaba ba kullum."

Khalil ya yi saurin cewa , "Ah haba Madam abun naki kuma ya zo da son rai."

Suka yi dariya.
Ta ce, "ah to wa yaki hutu."

Shi kam Xavier ta shi ya yi ya koma inda Deejerh ke zaune ya ce, "Za a iya bani dama?"

Zahra da Khalil na ganin hakan suka tashi suka bar masu wajen.

Deejerh ta ce, "Name fa?"

"Mu fita tare yau,tunda na ga kina shirin tafiya Paris bikin Ammar and ina so mu dan kasance tare kuma a halin yanzu aiki ya dan kara taso mun ba dama in ce zan biki mu je tare, duk da hakan amman ina sa ran kila mu biyo ki daga baya ni da Asher."

Deejerh ta ce, "Ok ba matsala."

"Yawwa yanzu zan dan fita in dawo zuwa anjima da yamma sai mu fita." Xavier ya fada yana tashi.

Deejerh har mamakin kanta ta fara ji domin da ya tafi sai ta ji kamar ta bi shi bata so ya tafi kawai son kasancewa take da shi ta gan shi kusa da ita.

Ta kasa sukuni kawai tunaninsa take, karshe da ta gagara hakuri ba ta san lokacin da ta kira shi ba.
Yana gani kuwa cikin zumudi ya amsa yana.
Assalamu alaikum
Shiru tayi kawai tana saurarensa ta gagara cewa komai.

Xavier ya ce, "Hello.... Kina jina? Kinyi shiru,kiyi magana, is there Anything Wrong? Hello."
Ta gagara cewa komai kawai sai ta ja dogon numfashi ta katse kiran.

Bin kiran nata Xavier ya yi har sai da ya kusan yankewa kafin ta dauka ya ce, "Hello... hello ina fatan dai kina lafiya?"

Ajiyar zuciya ta yi kafin tayi karfin halin fadin , "Nothing."

Xavier ya ce, "da gaske? Ki fadamun gaskiya."
Deejerh ta ce, "I just wanna check on u."
Tana fada ta katse kiran.

Dadi ne da farinciki ya ratsa zuciyar Xavier ya tura mata da message.
"I'm fine kamar yadda nake fatan kema haka, Love You."
Tana karantawq ita ma murmushi ta sake kamar suna ganin juna.

Tana ganin yamma ta fara yi ta tashi ta yi wanka ta shirya.
Ba karamin kyau ta yi ba cikin baby pink din abaya da farin veil, farin takalmi jaka ma fara.

Shima yana dawowa dakin sa ya wuce ya yi wanka ya shirya sanann ya kirata suka fita.

The New Forest ya kaita domin waje ne mai kyau dake dauke da bishiyoyi da flowers tare abubuwan ban sha'awa uwa abu waje ne masoya ke yawan ziyarta.

Suna zaune Xavier ya ce, "sai nake jin nutsuwata a yanzu ta fi ta ko yaushe tamkar wani bangare ne na rayuwa dana rasa ya dawo gareni yanzu."

Deejerh ta ce, "Umm ni kuma ban jin cewa na kai wani bangare na rayuwar wani musamman ds ya kasance lokacin da nake daf da aminta da soyayyar wani sai ya zamana ashe ba hakan bane shi a gunsa ina jin cewa kamar ba za asoni a yadda nake ba soyayya dani zata zama abu mafi ban wahala bisa ga yanayin rayuwata da kuma yadda mutane da duniya ke nuna mun ko ince na ga zahirin ma."

Xavier ya ce, "This world is wrong about you, you are not hard to love.
All that you need is safe space and somebody to recognize that you are enough,you just need somebody to adore.
Somebody that folds you the same way as you poor.
And yeah
Some they might need to pick up your head, you're staring at your feet and remaind you that at the table of hopes and dreams you deserve a seat.
But when you by their side
No matter what this world throws at them together you'll take in your stride.
When this world put them down you'll be the one smiling at them, encouraging them and straightening their crown.
Somebody that will never tell you that you're too much and somebody that will never use your love as a crutch.
Hard to love it's not something that you are.
It's perfect with every wrinkle and every quirk and every scar."

Deejerh ta yi murmushi kafin ta ce, "You've brought out the best in me, and I'm forever grateful.
Your presence in my life has been a game-changer.
You've helped me shed my fears and embrace my true identity, I'm grateful for your unwavering belief in me."

Xavier ya ce, "ka da ki damu kuma kada ki gode mun domin na ji ma karbar ragamarki a gun Iyayenki da tabbatar musu da cewa zan kareki zan tsareki duk tsanani sannan ina so ki sani cewa har yanzu uncle dinki Zaid na bibiyarki wanda bana fidda tsammanin cewa so yake ya cutar da ke ta hanyar daukan tunda yanzu ya san ba zai iya amfani dake ba kin fi karfinsa, ya turo fayez ne duk don ya shiga jikin ki su cutar da ke shine har sukai galabar samun bayanin red diamond na gun taron ku ina bibbiyarki duk da cewa baki sani ba amman ina bin diddigin duk inda kike sa kafa da kuma wanda kike wulda da shi, sannan babban abun da baki sani ba kuma shine farko bincike aka sani yi akan ki kan cewa ana safarar Kush da sunan Companyn ki a ƙarshe kuma mun fahimci duk dai zaid dinne yake shirya hakan , a yanzu baki da matsala domin yaransa na hannu kuma shi ma yana daf da shiga hannu In sha Allah."


Deejerh ta ce, "ban yi mamaki ba kam, Domin Uncle zai iya yin komai akan kudi, to Allah ya kyauta dai."

Xavier ya ce , "Amin amman nidai ban fada miki wa innan abubuwan don ki damu ba Please ba komai kuma ba abun da zai faru nine akan case din."

Murmushi Deejerh ta yi ta ce, "ni ban damu ba ko kadan ko da ace ma zan damu ai indai zan daga idanuna in kalleka zan ji cewa ba komai."

Sun sha hira sosai sunyi hotuna sai can dare kafin suka koma gida.

Kwana biyu kusan koyaushe Suna tare suna hira.
Sun kara shakuwa sosai.

Yau ya kasance ranar zata tafi Paris domin saura kwana daya bikin Ammar.

Ya kaita airport kenan aka kira shi daga office kan yaran zaid sun yi magana sun amsa laifinsu kuma sun fadi inda Zaid yake.

Kafin jirginsu ya tashi da sauri ya koma office.

Alhmdu Lillah
Alhmdu Lillah
Alhmdu lillah

Na san da yawa zasu ce ai basu ga karshen Zaid ba,yo ko a haka aka bar Zaid ai an gama da shi,amman duk da hakan ku karkade kunnuwanku ku gyara zama domin kuwa za a cafko zaidu kuma zaku ga karshen sa a next Novel dina.
Ga wa inda basu sani ba novel dinnan Chronicles ne.
1 sunan shi YEL 2 FREEYA 3 VIXEEN sai kuma 4 kuma last wanda an gama kenan me zuwa In sha Allah.
Kumq anan zaku ji cikakkiyar makomar Zaid duk da dai ina kara fada ko a haka aka bar zaid ai rayuwarsa ta kade😂
Ga wa inds basu karanta sauran ba damace gareku yanzu zaku iya fara karantawa daga kan Yel, Freeya,Vixeen kafin mu kai ga na karshe.
Yanzu zan yi wani Novel na dan barkwanci muyi nishadi kafin inzo mu ci gaba da gashi.
Ka da ku manta ku nemi yel Freeya da Vixeen complete domin da zaran na gama season 4 akwai gangaramun lamari ga Readers din wa innan zafafan taurari.
Ina kaunarku duka😻
Taku har kullum
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-Humaerath
08103080717



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment