Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ya fada cikin in'inar muryarsa.

Deejerh ta ce, "Yes kuma muna fita zan siya ma sweet dinka."
Ta karasa maganar tana wasa da kumatunsa.
Asher ya kalli Xavier ya ce , "Dady kai ma za...za ka siya mun ko?"

Girgiza masa kai tare da murmushi Xavier ya yi alamar e.

An gama shagalin ranar har mutane sun fara watsewa, Deejerh ta kalli Xavier ta ce, "ban san a ina kuka sauka ba, ko zan iya tafiya da Asher in ba damuwa?"

"Why Not? And nima binku zanyi sai in kama daki a hotel din da kika sauka kamar hakan zaifi domin zamu jira har ki gama in zaki wuce Australia sai muma mu wuce gida." Xavier ya fada.

Deejerh ta ce, "Alright zan samu lokaci sosai da Baby Friend dina ashe." Ta karasa maganar tana kallon Asher.
Mika mata hannu ya yi yana dariya.
Tare suka fita ta siyawa Asher Sweet da chocolate zata biya kudin kenan Xavier ya biya bata ce masa komai ba suka yi bakin titi suka tari taxi suka hau.
Direct hotel din suka nufa.
Suna shiga Deejerh ta ja Asher suka yi dakinta shi kuma Khalil ya je kama na shi dakin, sai da ya bincika daki kusa da na Deejerh kafin ya karba.

Ta fito daga wanka kenan sai ta ji ana nocking kofar.
A tunaninta masu kawo abinci ne dake ta kira su kuma ta san mata ne, hakan yasa kai tsaye ta bude kofar tana goge ruwan da ke kanta.
Wani irin kallo Xavier ya bita da shi,daga sama har ƙasa, yanayinsa ne ya fara sauyawa.
Deejerh da ta kalli jikinta ta kalleshi bata san lokacin da ta saki ihu ba tana yarda karamin towel din dake hannunta ta tura kofar da karfi, ganin yadda take ihu Asher ma ihun ya fara yana riketa.
Da kyar ta iya controlling kanta ta sa shi ya yi shiru sannan cikin sauri ta je tasa kaya.

Shi ko Xavier na tsaye kamar ya suma idanunsa babu abun da ke gani sai Deejerh sanye da towel.

Sai da ta gama gyara jikinta kafin ta je ta bude mai kofar aiko har lokacin yana tsaye.
Tana buɗe masa ta koma ciki.
Jikinsa a mace ya shiga domin ya kasa gasgata cewa cikin mafarki ne ya ganta hakan ko kuwa zahiri.

Duk inda ta yi binta yake da kallo ita kuwa tana kaucewa har aka kawo abinci suka ci.
Ganin ta takura ta ce masa zasu kwanta.
Sallama ya masu ita da Asher din ya tafi nasa dakin.

Shi ko Asher ban da danna tablet din da Deejerh ta bashi babu abun da yake yi, sai Fayez ya kirata yake bata.

Wasa wasa har ya kasance yaune ranar karshe na fashion week din kuma shine ranar da Deejerh zasu yi na su show ur talent din.

Da wuri Deejerh ta shirya cikin Bakar Riga mai adon golden,yanayin rigar ya zauna a jikinta sosai kuma bai fidda mata sura ba kamar yadda ta saba ta rufe jikinta daidai gwargwado kwalliya ma bata yi kamar yadda sauran keyi ba,Light Makeup ta yi.
Tare da Asher suka je wajen Xavier ya shiga gari kan cewa zai zo ya same su a wajen.

Ta shiga tana kara shiryawa Asher na zaune yana game da tablet wasu maza suka zauna kusa da shi suka zagaye shi.
Daya a cikin su ne ya ce, "Boy wasa kake?"
Kallonsa Asher ya yi ya kawar da kai.

Ya kara fadin, "Game ne? Nima na iya ai,inzo muyi?"

Nan ma Asher bai kula shi ba.
Zaro wata tablet din ya yi sak irinta Asher ya ce , "ka ga tawa ma tafi taka kyau,ko muyi canje?"

Asher ya girgiza kai.
Alamar aa.

Dubawa suka yi ,kowa hankalinsa na kan stage, ya fisge wayar hannun Asher ya mika masa dayar.
Wata kara Asher ya sake.
Da sauri suka mika masa tashi.
Duk da yadda suka so da su kwace wayar sun gagara.
Wata tsimma suka dauka suka daure masa baki ,a hankali suka dauke shi suka fitar da shi daga gun taron suna fita bayan sun sa shi a motarsu sai ga Xavier na shiga gun taron.
Ita ma Deejerh ta dawo gun da ta bar Asher din kenan.
Kallon Xavier ta yi tana, "Asher din fa? Ina yake?"

Cike da mamaki Xavier ya ce, "Kamar ya? Ina Asher kuma? Ba tare na barku ba."

Take idanun Deejerh ya dau hawaye babu abun da take furta ba sai, "La illaha illa anta Subhanaka inni kuntu minal zalimin, Innalillahi wa inna illaihir ra'ji'un."

A birkice ta fara nemanshi tana hawaye, shi ma Xavier din shiga nemansa ya yi yana kiran sunansa.
Har securities sun tambaya amman babu wanda ya ce ya ga Asher.

Xavier da Deejerh suyi nan suyi can sun kasa zaune sun kasa tsaye.
Gashi sai kiran sunanta ake anzo kanta amman sam taki saurara ma.

Xavier ya ce taje zai ci gaba da nemansa taki ji fir , "Asher...." Abun da take furta wa kenan kawai.

Sai da Xavier ya mata wata irin tsawa yana, "Asher na nan zai fito kije kiyi abun nan,kije kiyi karki manta ya ce ki masa alkawarin zaki cinye in baki je kin ciyo masa kambun ba ko da an gansa babu amfani kenan."

Faduwa tayi kan gwiwarta tana tuna abun da ya fada mata kafin su tawo gun, "Ki...ki...ci mana Award in ba ki ci ba,ni ba ruwana da ke,ko ko ... Dady?" Ya fada yana kallon Xavier.

Tana gama tunawa kara fashewq tayi da kuka.
Xavier ya dagata ya share mata hawayen kafin ya ce, "Go On."

Jikinta a sanyaye ba karfi,fuska ba walwala haka taje ta fara,tana tafiya yin abun kawai take amman zuciyarta da tunaninta na gun Asher tana yin adduar Allah sa a ganshi kuma yana cikin koshin lafiya.

Tana gamawa ta sauka da sauri ta fice a gun, ai kuwa ta na zuwa sai ga Asher nan ya she da suka kwace wayar sai suka jefar da shi , Yana jikin Xavier a sume.
Da gudu ts karasa ta karbesa ta rungumeshi tana kuka.
Dake wajen fal yake da yan jaridu har an fara yi masu hotuna.
Yana bude ido ana kiranta a gun taron.
Daukanshi tayi suka shiga.
Abun mamaki.
Award aka bata na Vogue Talent Award.
Tana karba ta mikawa Asher.
Nan ma haka aka dunga masu hotuna.
Kan kace miye sun bazu a duniya da caption din wacce ta yi nasarar Vogue Talent Award na shekarar 2024 ashe tana da Ɗan da ta boye.

Bayan sun sauka kan stage din Xavier ke tambayar Asher su waye suka dauke shi, kafin Asher ya fara magana wajen taron ya karade da wani irin hayaƙi.....
[6/9, 8:55 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-67

Takai takai aka fara kowa na neman mafita da hanyar fita.
Xavier ya dauki Deejerh da Asher ya fitar da su sai da ya tabbatar ya sama masu wajen da zasu zauna kafin ya koma ciki, an masu kashe huta da jami'an tsaro sun mamaye gurin musamman da ya kasance box din tsaron Red Diamond din dake wajen ya fara yin wuta alamun ana ƙoƙarin kai masa hari.
Xavier na shiga kamar ance ya kalli kasan sa ya ga wannan tablet din Asher din a kasa tana yin wuta sak irin ta wajen gold din.
Dagawa ya yi ya kunna.
Gabadaya an tsaya tablet din ne yadda zata dunga bada direction din wajen da gold din yake da kuma yadda zata gano makullen sirrin bude akwatin Red Diamond din.
Rikewa ya yi da sauri ya shige ya ci gaba da taya jami'an tsaron wajen bincike.
Yana tsaye wani yazo da lullube kansa da riga zai wuce, Xavier ya bangaje shi bai sani ba,irin wayar ce ta subuce daga hannun mutumin ta fadi kasa, da sauri Xavier ya daga yana mika masa tare da fadin , "Sorry."
Sai da ya mika masa har ya juya zai tafi sai Xavier ya tuna irin tablet din da ya gani a gunsa.

, "hee, hee you."
Xavier ya fara kwallara masa kira.
Sauri ya kara da ya ga alamar Xavier na binsa ya fara gudu.
Shi ma gudun Xavier ta fara.
Sai da suka zagaye filin nan da kyar Xavier ya yi nasarar kama shi.
Securities din suka zagaye shi.
Aka fito da wasu biyu ma an kama.

Bayan Xavier ya mika masu wanda ya kama ya nuna masu card dinsa sannan kuma ya sheda masu cewa akwai wani abu agunsa zai dan kara zurfafa bincike kafin ya zo masu da bayani.
Sun ji dadin taimakon da ya masu sosai.

Asher ya shaƙi hayakin Sosai wanda har ya fara ficewa daga hayyacinsa kuma ga abun da faru da shi kafin hakan, dole sai da suka biya ta asibiti aka bashi magani aka kara duba shi kafin suka wuce hotel.

Bayan sunje fayez yake tambayar Deejerh waye ya bata wayar hannunta.
Deejerh ta ce, "Fayez ne da zan tawo ya bani."

Xavier ya maimaita, "Fayez?"

Deejerh ta ce, "Yes Me ya faru?"

"Shi din waye? Kuma har kin aminta da shi da zaki karbi kyauta agunsa?" Xavier ya fada.

Cikin bacin rai Deejerh ta ce, "ban gane ba, sai na nemi umarni agunka kake nufi ko yaya?"

Xavier ya ce, "Nop amman kisan da irin mutanen da zakiyi hulda domin shi wannan fayez din ba komai yake so da ke ba illa ya yi amfani dake ya yi nasara ya kuma cutar da ke."

Da mamaki Deejerh ta kalleshi, "ban gane ba cutar dani? Amfani dani? Kamar ya?"
Ta fada kanta na sara mata.

Daga tablet din ya yi,ya nuna mata kafin ya ce, "wannan tablet din ba ta komai bace illa ta bin diddigin da za ayi a saci Red Diamond a gun fashion week dinku ke kika yo masa dakon daukan bayanan da suka samu har suka tarwatsa taro, Allah ne kawai ya takaita aka kama yaran, sauran bayanan kuma zanzo miki da su inna gama bincike ko ince in kin bukata." Ya karasa maganar yana ficewa daga dakin.
Jiki na rawa Deejerh ta dauki waya tana kiran Fayez amman fur yaki dauka, daga karshe ma kashe wayar ya yi.
Da ta kira secretary dinta ta tambayeta ko yana zuwa Company ta sheda mata cewa tunda ta tafi milan bai kara zuwa ba.
Tsabar tashin hankali da mamaki wani irin zazzabi ne ya dauke Deejerh ta kwanta a kan gado ta gagara ma jan bargo ta rufu sai rawar sanyi take.

Xavier ne ya shigo ya ganta hakan ya ja mata bargon ya rufeta sannan ya kashe masu wutar dakin ya fice.

Can cikin dare bayan ta gama jimaminta tashi tayi ,ta yi sallah raka'a biyu ta kai wa Allah kukanta.
Bata tashi kan sallayar ba sai da ta ji zuciyarta tayi mata sanyi kuma karfinta ya dawo tare da jin cewa ba wanda ya isa ya cutar da ita da ikon Allah.

Har safiya jikin Asher ba karfi yanayin sa ya canja hakan yasa Xavier sheda mata cewa zasu koma uk domin ya kai shi ya ga likitansa acen.

Deejerh ta ce, "ina neman alfarma Please."
Xavier ya ce, "Ok ina ji."

"Ba zan iya rabuwa da Asher a halin da yake ciki ba, in babu matsala zan biku Uk din in naga jikinsa ya daidaita zan wuce daga nan."

Xavier ya ce, "Why not, ki shirya kawai daman private jet zamu bi."

Shiryawa Deejerh ta yi suka tafi tare.
Tunda suka hau jirgin har suka sauka Asher na jikinta.

Asibitin suka fara wucewa sai da Dr din ya masa allura ya bashi gado ya dan samu hutu.
Xavier da kanshi ya kira Khalil ya sanar masa ai kuwa ba jimawa sai gashi da Zahra.

Zahra na ganin Deejerh ta rungumeta don murna da farinciki.
Take suka fara hira.
Shi kuma Xavier suka fita da Khalil.

Suna zaune Xavier ya ce, "Daman ko ina son ganinka inata tunanin in mun dawo zanzo gida in sameka mu yi magana."

Khalil ya ce, "wa ta magana kenan?"

Xavier ya yi shiru.

Khalil ya ce, "ka fada mana,ko akwai matsala ne?"

Xavier ya ce, "Ina ..... Sai kuma ya yi shiru.
Sai da ya yi ajiyar zuciya kafin ya ce, "Ina so in musulunta ne."

Wani irin farinciki mara misaltawa Khalil ya shiga ya rungumeshi yana, "Really?" Xavier ya girgiza masa kai.
Khalil ya ce, "amman ko da na fi kowa jin dadin wannan amman zanzo inji wani dalili ne yasa ka ji kwadayin dawowa musulunci."

Xavier ya yi murmushi kafin ya ce , "mu zauna tukunna."
Bayan sun zauna ya ce, "ina yawan tunanin abubuwa da dama mussaman yadda rayuwarku take ta Muslim babu tsangwama, duk da cewa kasan ba addininmu daya ba amman baka taba nuna mun kyamata ba har ma da sauran yan uwanka da yan team dinka,
Da kuma tsarin rayuwarka babu hassada babu kyashi ga son kyautata wa sannan mu Christianity dole kuma wajibi agun mu muna cire tide sabanin ku da ya kasance sadaka sai kunyi niya wanda har ka taba cemun ma babu bukatar mutum ya yi sadaka indai bai da niyar hakan a zuciya ko da kuwa a masallaci ne, haka kuma masallaci na kowa ne wanda ya gina baya nuna damuwa ko cewa sai anyi wani abu dole amman mu Church na mutum ɗayane kuma sai ya bude a wasu gurare daban daban ga tsare tsare wa inda ko kadan basu shafi mutane ba bare rayuwarsu.

Sannan kuma na zo na ci karo da wani
Debate da na ji Shiek Ibrahim Abdallah From Uganda
Yana cewa,

Why did you says jesus is not God and he die for our sin
If Jesus is dead then who is your God as of that time?

Ishaiah 40:28
I am God and everlasting God Who does'nt died.
God Never died
Allahu la ila ha illa huwal hayuum kayyum.

Mathew 27:45
Jesus cried :My God, my God why have you forsaken me?

John 5:30
I can do nothing of my self but the permission of God.

John 14:28
The father is greater than i.
John 20:21.
The Father sent me.

Ya kara bayyanar da ni duhun da nake ciki domin kuwa tabbas da ace Jesus shine Ubangijinmu da bai mutu ba, kuma shi kan shi Jesus ya tabbatar mana da cewa ba zai iya yin komai ba, ba tare da umarnin Ubangiji ba, shi ya nuna Allah ne Ubangijinsa mune zamu bijire? Kuma ya sanar da mu cewa Allah ne ya aikosa, Ubangiji ai ba zai taba aiko kan shi ba, sannan kuma bai taba hada kansa da Ubangiji ba,sai mune zamu hada shi? Na yarda da cewa ada barci ne ya rufe mun idanuna nake jin cewa addinina shine daidai bayan ba hakan bane

Haka akwai wani Muslim da muka je kamawa yana sallah da ya ganmu ko motsawa baiyi ba bare ya yi tunanin gudu har sai da ya tsaya ya yi sallahn ya idar ya yi addu'a,sannan ina gani da yawa irin yan ta'addan nan indai aka hadasu da musulmai a jail a karshe sumu musulunta suke,taya zan ƙi wa kaina inuwa ina ganinta da idanuna? Dole in nemawa kaina rahama in bi hanyar gaskiya."

Khalil ya ce, "Alhmdu Lillah , Alhamdu Lillah, Alhmdu Lillah Addua ta ta karbo kuma na yi matukar farinciki daga nan ba za mu wuce ko ina ba sai masallaci ka karbi kalmar shahada, to yanzu kuma saura batun Aure."

Xavier ya ce , "Aure ? Tukunna dai wannan zamuyi maganar daga baya."

Khalil ya ce , "Ok to Allah sa muji alkairi, ka ga yanzu lokacin sallar la'asar ma ya yi so mu je masallacin kawai."

Tare suka fita suka nufi masallacin....
[6/10, 3:43 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-68

Sai da Xavier ya karbi kalmar shahada kafin suka dawo asibitin.
Suna zuwa kuwa Deejerh take sanar da Xavier ance zasu iya tafiya gida jikin Asher din ya yi kyau.

Khalil ya ce, "ku dakata,ku dakata albishirinku."

Deejerh da Zahra suka ce goro cikin zakuwa.

Ya ce, "Xavier dai musulmi ne a yanzu kuma a yau sannan har karshen numfashi domin ya karbi shahada."

Da fara'a Zahra ta ce, "Woo Congratulations barka da kasancewa cikin rayuwa mai dadi da aminci May Allah guide and bless you on your spiritual journey
Alhamdu lillah."

Deejerh ma ta ce, "May Your Decision be a source of joy and strength for you. Congratulations and welcome to ummah."

Xavier ya ce, "Thank You all,Thank you so much."

Khalil ya ce, "yawwa to sai mu tafi gida ko, ya kamata Duka mu tafi gidanmune har da kai saboda mu je mu fara karatu da duk abun da ya kamata ko da na yan kwanaki ne tunda yanzu ba ka da aiki sosai."

Zahra ta ce, "gaskiya kam kuma Asher ma zai so su dan zauna da Sister kafin ta koma."

Hakan aka yi duka suka tafi gidansu Khalil, suna zuwa Noor, Anitha da Anushka suka rungume Deejerh suna murna.
Noor ya kalli Deejerh da Asher da Xavier ya ce, "woo Uncle Xavier kar dai zuwa ka yi ka sato mana Auntynmu?"

Dariya duka suka yi kafin Zahra ta kada su ciki tace su je su canja kaya dake uniform ne a jikinsu duka.

Restaurant dinta Zahra taje tasa a kawo masu abinci suka ci.
★★Khalil da Xavier sun yi nisa a karatu dayake daman Xavier yana yawan bibiyar abun musulmai sai ya kasance baya wani shan wahala wajen fahimta da dauka.

Suna zaune bayan sun gama Xavier yake cewa, "ranar ka mun maganar aure,ina da wacce nake so kuma ina zaton kai ma zan samu goyon bayanka dari bisa dari."

Khalil ya ce, "wace ce? zan so in santa kuwa"

Shiru Xavier ya yi ya tafi wani guntun tunani.
Khalil ya taba shi yana, "kana mun magana ka yi shiru kuma, ina saurarenka ne fa."

"Deejerh." Xavier ya fada a takaice.
Take Khalil ya bata rai.

"Zan bi bayanka akan komai amman ban da nan ni ban amince ba." Khalil ya fada. Ya fada yana tashi tsaye

Xavier ya ce , "kamar ya? Aiko dai ni ina sonta kuma zan tareta in fada mata."

Khalil ya ce, "kar ka kuskura ma ka yi hakan."

Xavier ya ce, "Ah kasan fadi tashin da nayi akanta? Aa kam wallahi ko da muka je Mexico na nemi izinin iyayenta da Nawwar da kuma Mestro Roman sannan duk sun bani goyon baya don haka na ci gaba da bibiyarta hatta yaron da Zaid ya tura mata Fayez ina biye da shi kan komai ada har na tada hankali tunanin mai sonta na gaskiya ne da na fahimci cewa duk plan ne sai kawai na ci gaba da bibiyarsu duk da cewa ina jin kishi, wanda gashi ma a karshe har sata suka so yi ta hanyar amfani da ita, yaran shi yanzu haka na hannu ina so a hankali har a kai ga matakin da zamu kamashi cikin sauki, ni ina sonta ne ba don komai ba sai don in rayu da ita kuma in bata kariya aduk inda zata kasance ."

Khalil ya ce, "Duk da hakan dai ina ji maka cewa da kamar wuya kasancewar hakan, kuma ni ba zan iya baka goyon baya kamar yadda kake bukata ba kenan ma don ita ka dage kake son dawowa musulunci?."

Yanayin Xavier ya canja alamun bacin rai ya bayyana a fuskar shi, cikin fushi ya ce, "ka riga da ka sani ina yin abune don ra ayina da kuma cancantarsa ba don komai ba,kuma sai da na baka hujjar dalilan da yasa nake sha'awar musulunta and wannan Ubangiji ya sani da zuciya daya nayi, Soyayyar Khadija dake raina kuma daban."

Khalil ya ce, "Har yanzu dai ni ba zan ce zan goya maka baya ba, sai dai inyi maka fatan alkairi inta amince shikenan."

Xavier ya ce, "In Sha Allah zan gwada indai mu alkairi ne ga juna na tabbatar da cewa duk rintsi zata aminta dani."

Khalil ya ce, "All the best."

Xavier har a cikin ransa yana jin nauyi da fargaban yiwa Deejerh magana,amman aduk sanda ya ganta kara jin tsantsar kaunarta yake aransa.

Khalil ya fita, Zahra ta tafi Resturent shi ma Xavier ya fita office ya tuna ya manta da wasu file a gidan.

Deejerh ce kadai a gidan hatta yaran sun tafi School duka.
Tun tana chatting a wayarta har barci ya kwasheta a kan kujera.

Da sauri ya shiga palourn bai ma lura da ita ba ya wuce daki bayan ya dauko files din zai fita kenan idanunsa akanta.
Tsayawa ya yi kawai yana kura mata kallo.
Karshe ma yaje gaban ta daf da ita ya tsaya yana kallonta tare da sheƙan kamshin jikinta.
Zuciyarsa raya masa take ya rungumeta ko ya yi kissing dinta har ya durkusa sai ya tuna cewa musulunci ya haramta namiji ya taɓa macen da ba mu'harrramarsa ba.

Kamar a mafarki Deejerh ta ji mutum a kanta tana bude ido kuwa suka kalli juna, da sauri ta tashi tana gyara zama tare da kau da kai.

Murya na rawa Xavier ya ce, "Na na... Manta files ne na zo dauka."
Bata ce masa komai ba.
Ya fita da sauri.
Har yaje zai shiga motarsa sai kuma ya rufe ya koma ciki.

Tsayawa ya yi yana kallonta ya ce, "Ina so muyi magana Don Allah in ba damuwa."

Deejerh ta ce, "Ok ina jinka." Ta fada tana danna wayarta.

Xavier ya ce, "duk da cewa ina jin nauyin furta wa amman kuma nauyin da zaman sa yake a zuciyata ya fi na furtawan azaba, na kasa jurewa, duk wata jarumtata na nemeta na rasa,ba zan iya ci gaba da dauka ba domin ya mun nauyi,Ina sonki kuma ina kaunarki sannan ina fatan mu kasance tare har karshen numfashi in zaki bani dama Don Allah."

Deejerh na jin hakan wani irin kallo ta bishi da shi, ta na, "So?? Ni? Aa wannan kam wasa ne ba dai ni ba, ba so na kake ba,na san ba sona kake ba,ka da ka yi mun wasa da hankali ka da tadamun tabon da ke zuciyata, ka da ka sani cikin matsala."

Xavier ya ce, "kar ki mai da soyayyata silar wani kunci naki ko karya, akan me zan so ki don karya? Akan me zan kaunace ki da karya? Me zai sa bana sonki ince ina sonki? Don Allah ki aminta dani mu rayu a tare."

Deejerh ta tashi tana matsawa daga inda yake, "bani kake so ba, so kake ka aureni don Asher, don asher kawai kake sona ba don zuciyarka na kaunata ba,kuma ba don tana son rayuwa dani ba."


Xavier ya ce, "ki yarda dani, alakarki da Asher daban tamu daban, in Asher na bukatar 30% to ni 70% nake bukatar ki a rayuwata don Allah kar ki ce mun aa kuma kar ki guje mun kar ƙi ni
."

"Aaaaa, aaa karya ne,aaa." Deejerh ta fada ta karfi tana gudu ta shige daki ta turo kofa.

Duk yadda Xavier xaiyi ta bude kofar nan fur taki.
Yana jikin kofar ya ci gaba fadin, "I am OverThinker ,but i love every torturing second it.
They say when over thinker tell you they love You, you can take it to the bank, because they thought every single reasons or two so when i ask you out i've already heard you say no 1000 time in my head ,yet i am, because you Are the worth it.
When i ask you to spend life with me
I've watch You walk away million times.
I've felt you break my heart millions times but its worth every single time
You see i was Born for this, i was born to love You unconditionally because i've lived life of condition in my head 100times."
Kin bude kofar tayi har ya gama maganarsa tana saurare.
sai da aka fara kiran sa a office ana jira haka ya tafi.
Ita kuwa kwanciya tayi a kan gado ban da kuka babu abun da take.
[6/10, 3:43 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

PAGE-69

Sai da ta tabbatar ya tafi kafin ta tashi ta wanke fuskarta.
Azababben ciwon da kanta ya fara yi mata ne yasa dole ta nemi magani ta sha ta kara komawa ta kwanta, har sai da su Noor suka dawo daga School kafin ta tashi da Asher yazo yana ja mata gashi.
Hada ido suka yi yana yi mata dariya ita ma dariyar ta masa ta tashi tana, "welcome baby friend an dawo."
Ya girgiza mata kai.

Tashi ta yi ta cire masa uniform din tasa masa kaya yaje ya yi alwala ya fara sallah.
Dake shi ma an sa shi a islamiyya kuma Deejerh na koya masa wasu abubuwan..

Khalil da Xavier tare suka shigo gidan bayan sallar magrib.
Duka suna zaune a palour.
Deejerh ko kallon inda Xavier yake bata son yi sai kau da kanta take.
Zahra ta ce, "Hi, mutanen gidan nan,ina so inyi magana kowa ya bani aron hankalinsa anan."

Duka daga kai suka yi suna kallonta.
Zahra ta ce, "yau fa ba girki a gidannan tashi zakuyi mu je Resturent kowa abashi aikin da zaiyi ayi shagali."

Murna da rawa su Anuska suka fara domin

Please Login or Register in order to submit comment